Cizon yatsa book 1&2 complete - Chapter 15
Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 15: Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 15. [2/23, 7:34 PM] Nasma: Level 3 Lecture Theatre
3,176 words
[2/23, 7:34 PM] Nasma: Level 3 Lecture Theatre
Gombe State University
A layi na shida cikin wannan ajin da yake cike da ɗalibai sama da sittin, wasu ƴan mata uku suke zaune. Ƙawaye ne ko a kira su da aminai tun ƙuruciya. Suwaida ƴar gayu mai ji da kai wadda bata yarda duk wadda take tare da ita ta fita da wani abu komai ƙanƙantarsa ba. Aisha wadda ta fito daga gidan da yafi na sauran talauci, amma idan ba ta ƙure mata ba bata yarda ta nemi alfarmar Suwaida saboda gudun wulaƙanci. Sai kuma Amina sarkin wayo. Ba wai bata san taimakon da Suwaida take musu don taji daɗin juyasu bane, sai dai ta amince taci bati tunda idan an juyata ba zai fito a jikinta ba. Su ukun kamar sauran ɗaliban ajin duka hankalinsu yana ga malamar dake tsaye a gaba da farar takarda a hannunta. Shiru ajin ya yi kamar ruwa ya cinyesu ta ɗago takardar. "Ga sakamakon assignment ɗin da na baku satin da ya wuce. Kamar yadda na yi muku alƙawari ɗaliban da suka sami makin da ya kai shabiyar zan mayar musu dashi kaso arba'in cikin ɗari na jarabawa." Susu ta gatsina fuska,"mu dai ayi a fara laccar yau don a matse nake da son komawa gida da wuri." Minasco ta soma dariya,"hmmm zaki je ki yiwa Walid girki ko?" Sai da ta juya idanu ta bata amsa, "ya son ranki? Yau zai dawo ya kamata ya sami tarba mai kyau. Na faɗawa Iyalle dai na san duka abinda na ce ina buƙata tasa an siyo." Hannu Aisha ta ɗaga musu, ''ku yi shiru mana muji su waye suka haye." "Su waye zasu haye kuwa banda ƙwarin ajin nan? Kema kinsan cikinsu Class rep ne ko waccan mayyar bokon Surayya" ta nuna wata matashiya sanye da dogon hijabinta. Bayan dogon gargaɗi da malamar ta sake yi musu, akan duk ranar da take koyarwa suka sake damunta da surutu irin wannan aikin zata kuma basu ta shiga karanto makin ɗalibai. Dariya kawai kake ji saboda ko mai maki biyar a cikin ashirin babu. Kusan duka ajin suna ganin wahalar darasin Philosophy. Class rep da ake sawa rai ma da maki tara ya ƙare. Su Susu ana ta zuba basu ji nasu ba kuma basu damu ba saboda sun san babu wani abin azo a gani. "Amina Falalu ita ce ta sami maki goma sha bakwai da ɗigo biyar, sai Surayya Aminu mai shabiyar." Babu mamaki a sunan Surayya ɗin saboda tana da ƙoƙari, amma kafatanin ajin Minasco suke kallo. Susu ta kwashe da wata dariyar rainin hankali tana kallonta. "Kada ma kisa rai ɗigo biyar ɗinne naki sauran tuntuben hannu ne yanzu zaki ji ta gyara." "Amina Falalu sauko mana" malamar ta sake cewa. Jiki a sanyaye ta miƙe don bata yarda makinta bane ita ma. Susu kuwa ta zuba ido domin ganin yadda za a kunyata Minasco ta sami labarin kaiwa bikin wata ƴar layinsu da za'ayi ƙarshen sati. Yabo sosai malamar ta yi mata, akan yadda ta tsara bayanin bisa fahimtarta wadda ta dace da abinda take nema. "Da zaki rage surutu Amina da ba ƙaramin ƙoƙari zaki yi ba. Banda maki ga wannan ki sha lemo" ta kama hannunta ta damƙa mata dubu biyu. A take ajin ya kaure da sowa da tafi. Aisha abin ya mata daɗi tana ta murna ta rungumota da ta dawo ta zauna. Susu kuwa baƙinciki kamar ta mutu. Ita a dole bata ma yarda takardar Minasco bace ta ɗaga hannu don neman izinin magana. "Ma ko zaki bamu takardunmu don kowa ya tabbatar da makinsa?" "Idan mun gama zan aiko muku. Yanzu ma ina sauri na manta." Ƙwafa ta yi don ba haka ta so ba. Minasco dake ta doka murmushi ana miƙo mata hannu suna cafkewa wai nan taya murna ce ta tsaya mata a rai. Gashi tana zama ta basu ɗari biyar biyar ita da Aisha ta soke sauran a jaka. Ji ta yi tafi ƙarfin karɓa daga hannun Minascon da take yi wa alfarma. "Ma tunda Amina ta fahimci Utilitarianism ɗinnan sosai ko zaki bata ta yi mana bayani yadda zamu gane?" Aisha wani irin kallo ta jefeta dashi. Sun san Minasco akwai tsoron magana a gaban aji ga raunin turanci sosai. Kuma ta fahimci bakinciki ne kawai kada wadda ta raina ta fi ta. Marairaicewa Minasco ta yi tana kallonta da ƙwalla, "Haba Susu." "Amina taso ki yi musu bayani da irin yadda ki ka rubuta min." Hantar ciki na kaɗawa ta sauko gaban ajin. Cikin rawar murya ta fara magana malamar tana bata ƙwarin gwuiwa sai gashi ta saki jiki tana kwararo zance rabi da hausa rabi da turancinta da past and present tense suke karo da juna. Da farko dariya ƴan ajin suka soma musamman muryar Susu ke tashi. Kafin ta yi nisa sun nutsu suna ɗaukar bayani. Tana direwa malamar da ɗaliban suka shiga tafa mata. "Da ace ƙasarmu zata yarje mana karatu da yarenmu na tabbata da yaran da suke da ƙwaƙwalwa sun yawaita. Ko a yanzu Amina ragin makin da kika samu na rashin turanci ne. Kinyi ƙoƙari sosai." Wani sabon girma ƴan ajin suke bata har aka gama suka fito. Fuskar Susu kamar an kwaɓa teba don tsabar baƙinciki. Jikin Minasco ba ƙaramin sanyi ya yi ba da ta tabbatar da gaske ba ta murna da nasararta. Haka nan suka bi jerin ɗalibai ƴan uwansu jiran abin hawa. Aisha ta kula da takurar da Minasco ta yi na ganin sauyin Susu sai ta dinga janta da hira. "Ranar exam fa goyani zaki yi don naga alama in ba da wuri na kamaki ba sai na maimaita course ɗinnan." Taji daɗi kuwa ta saki fuska,"ni kuma kinsan Allah ina karanta handout ɗin sau ɗaya na fahimta. Don ma wasu kalmomin sai a hankali da yau kin ji ana Amina Propessor of Filosofi." Wata irin dariyar ban haushi Susu ta kwashe da ita, "wanne ne ba wanne ba. Minasco Propessor ɗin zamu kama ko Filosofi?" Yaƙe Minasco ta iya yi saboda muguwar kunyar da taji. Gefensu ɗaliban da ke jiran mota sun ji kuma sunyi dariya. "Wasa nake fa Fropesor zan ce." Wannan karon da Susu ta fara dariya sai da ta faɗo daga kan kututturen bishiyar da suke zaune a kai. Sosai Minasco ta muzanta ƙwalla ta cicciko mata tana shirin fashewa da kuka. Halin Susu da Aisha ta so ta gane tun da daɗewa kenan bata fahimta ba. Ji tayi a yau sai ta nunawa Susu bata fisu da komai ba. "Ke Minasco kin tuna mutumin nan da nace miki yana ta damuna a school ɗinnan?" Ta gane neman ɗauke mata hankali Aishan za ta yi sai ta biye mata don ƙiris take jira ta fashe da kuka, "Wanda ki ka ce a gabansa ki ka rubuta masa Mai naci a waya amma ya ce wai ƙara sonki ma ya yi?" "Eh, bari na kira shi ya kaimu gida. Da alama yau zamuyi dare a wurin nan. Tun zuwanmu mota ɗaya ce fa ta wuce a cike." Hankalin Susu sai ya dawo garesu, "sai dai ya ɗaukeku ku biyu don babur ya yi mana kaɗan. Da Walid yana nan ma tun ɗazu zan kira shi ya kaimu." A harzuƙe Minasco ta ce,"kuma aka ce miki babur gare shi?" Sai da ta yi musu kallon rainin hankali kafin ta ce, "to me ki ke tunani. Saurayin Aisha ne fa. Idan ba ƴan babura masu lifan ɗin makarantar nan ba waye...?" "Ba sai kin ci min fuska ba Susu. Ke kaɗai ce ki ka cancanci yin saurayi mai mota. Mu ƴaƴan talakawa sai talaka irinmu. Wayarta ta ciro ta kira shi. Yana ganin sunanta ya katse dama ba kuɗi gareta ba ya sake kira. A kunya ce ta gaishe shi sai ta kasa faɗin buƙatarta saboda ba halinta bane. Minasco ta turawa wayar tana ta murmushi. Ita kuwa tuni ta manta da ɓacin ran Susu ta shiga jera masa surutu kamar ta san shi ta faɗa masa halin da suke ciki. Susu sai ta shiga game da sabuwar wayarta da Iyalle ta matsawa babansu ya saya ta zo tana musu karyar Walid ne. Kamar ance ta ɗaga kai kuwa ta hango galleliyar baƙar toyota camry wadda ake yayi a lokacin ta yi gaba kaɗan da wurin ɗaliban ta tsaya. Motar da mai ita ba ƙaramin tsuma zuƙatan ƴan mata da dama suke ba a makarantar. Siririn murmushi ta saki ta taɓo cinyar Aisha. "Ga mutumina can fa ya tsaya. Ƙarshenta saboda ya ganni a nan ne. Ni dai ba don ansa mana rana da Walid ba da tuni na bada kai bori ya hau." "Uhmhum" Aisha ta ce. Minasco tana ta raba ido ta gano masoyin Aisha sai gani suka yi an buɗe motar nan wani kyakkyawan bafillatani ya fito. Masu rawar kai aka fara cewa, "doctor ina wuni?" Hannu kawai ya ɗaga musu ya ƙurawa wurin su Aisha ido yana murmushi. Yau ɗaya ta faranta masa har yana jin kansa kamar yafi kowa sa'a a duniya. Susu gabaɗaya ta gigice don ya bala'in yin kyau cikin manyan kayan da yasa yau. Tana son Dr. Farouk lecturer na faculty of science. Cikin takun burgewa ya shiga tunkaro su. Aisha kunya kamar ta tsaga ƙasa ta shige ta duƙar da kanta. Bai dena tafiya da murmushi ba har ya iske su. Gaban Susu na dukan goma-goma tuni ta gama yanke shawarar hanyar ɓata baikonsu da Walid. Dr. Farouk ya ɗan duƙa saitin Aisha ya kashe murya, "Aysha ko sai na ɗaukeki ne zaki taso?" Damƙe hannun Minasco ta yi wadda ta sandare a zaune ita ma kafin ta saki baki, "Aisha Dr. Farouk ne Mai naci?" Langabe kai ya yi, "ni ne Amina, na baki tausayi ko?" Aisha gaba ta yi don kunya ta barshi da Minasco. Susu ta kalla tana tabe baki.
"Ki tashi mu tafi mana tunda ba me babur ɗin bane." "Kuje kawai za a zo ɗaukana" Ta furta da ƙyar kamar ta tauna flagyl. Suna tafiya tana jin Dr. Farouk yana cewa ya ma sunanta na su biyu yafi riƙewa. Baƙinciki da hassada ne suka hanata binsu ta gwammace ta zauna ayi gudun shiga mota da ita. Ko a jikinsu suka tafi. A hanya Dr. Farouk yake kamun kafa da Minasco akan ƙawarta. "Bamu dace ba don ni ba ƴar kowa bace." Kalamanta basu yi masa daɗi ba. Minasco ya fara saukewa sannan ya kaita gida. Ta zata ya tafi sai bayan anyi sallar Isha ƙaninta ya faɗa mata tana da baƙo. Da ta fita ta ganshi ta yi niyyar sallamarshi don tana tsoron abinda zai sa a wulaƙanta ta saboda talaucinsu. Ga mamakinta Dr. Farouk ya gama bincikensa tuntuni akanta kuma a haka yake matuƙar sonta. Kafin ya tafi dai a ranar ya tashi daga mai naci zuwa masoyin Aisha. Bayan faruwar wannan abu sai da suka kusa sati sannan Susu ta dawo tana kula su sama-sama. Gara ace wata ɗalibar yake nema da ya nemi Aisha. Ana haka kuma sai ga ɗan wan baban Minasco da ya rabu da matarsa an ce ya nemeta. Yaransu biyu matar ta raina samunsa ta dinga yi masa rashin mutumci abu harda iyaye basu tsira ba. Ranar da ta sanar da ƙawayen nata Susu cewa ta yi dama da ita ya dace. Yana faman buga-bugar neman aikinsa ina shi ina waccan matar da suka rabu. Aisha ta yi niyyar mayar mata da baƙar magana Minasco ta girgiza kai. Yanzu sun riga sun dawo daga rakiyarta. Cikin ikon Allah bayan an kawo kuɗinsu da sa rana da sati ɗaya offer ɗinsa ta fito daga CBN an tura shi headquarter reshen Abuja. Aisha da Minasco sun taya juna murna da wannan arziƙi da suka samu lokaci guda. Susu ta susuce ta raina samun Walid. Tsanarsa ma ta yi gabaɗaya tana takaicin waɗanda ƙawayenta zasu aura sunfi nata kuɗi, kyau da duk wani abu da ake nema a wurin namiji. Tana cikin wannan halin ne wata rana ta je gidan ƴar uwarta Alawiyya wadda ta yi headgirl lokacin da suke FGC Bajoga. Tun bikin Alawiyyar ta liƙe mata saboda mijinta mai kuɗi ne. A da ko gaisuwar kirki basa yi saboda ta rainata. Amma tunda ta sansano maiƙon jikin mijin take bibiyarta. A can ta haɗu da Walid abokin mijinta ne har an kusa bikinsu yanzu. Suna cikin hira Alawaiyyan ta nuna mata hoto a jikin jaridar Daily Trust. "Kin tuna yarinyar nan?" Hankalin Susu ba ya kan yarinyar da ake nuna mata. Mutumin da yasha babbar riga a tsakiyar yarinyar da wani matashi ta zubawa idanu. "Alh. Audi Karam ne? Wayyo ni Alh. Audi ne. Kai kuɗi suna inda suke." Ta koma kallon yarinyar da yaron duk ta ruɗe da ganin kuɗi da kyau, "kin ga kayan jikinsu kuwa? Ba dai ƴaƴansa bane? Oh ni ashe da rabon na ga ƴaƴan babban gida." Alawiyya ta kada kai, "kin shiga uku da son kuɗi Suwaida. Ɗansa ne zai yi aure kin tsaya kallo maimakon ki karanta." Susu ta cije lebe, "Allah Ya isanmu. Masu kuɗin nan junansu kaɗai suke aure mu ko ƙurar da ta kwaso su ba ma gani. Ji kyan yarinyar kamar ta sammin." "Ke kuwa ko sunansu ki karanta mana." "Shamsuddeen Audi Karam and Oluwatosin Tauhidat Abayomi. Ƙila ƴar wani Sarkin ce a garin yarbawa." Ta furta tana ƙare musu kallon sha'awa. "Wai kina nufin baki ganeta bane? Ko ni ina ganin sunan na tuna fuskar. Yarinyar nan ce da aka koreku daga FGC fa akan ta. Wadda ku ka sa yin ƙwai a ƙasan gado." Jiki na rawa Susu ta sake kallon jaridar a hargitse. Yadda ta tashi da sauri sai ka rantse wani mugun abu ta gani. Fuskar Shamsu ta ƙarewa kallo ta koma ta zauna daɓas. "Lallai bawan Allah ya sha Agumin yarbawa." "Me kenan?" Alawiyya ta tambayeta tana kallon fuskar tasa. "Ana cewa yarbawa sun ƙware a sihiri sai yau na yarda. Banda haka ina ɗan gidan Alh. Audi zai haɗu da wannan shegiyar. Kin manta ko da muna makaranta ƴar matsiyata ce? To wallahi ance babanta ma walda yake a bakin titin unguwarsu." Kallon tausayawa Alawiyya ta bita dashi, "kin shiga uku Suwaida. Ɗazu kin gama cewa ƙawarki Aisha ma asiri ta yi wa malaminku yanzu kuma kin koma kan wadda babu abinda ya haɗaki da ita." "Ki duba fuskarsa babu wani alamun farinciki. Ina jin Alh. Audi din suka yi wa asirin shi kuma ya yi amfani da matsayinsa na uba ya masa dole. Baki ji yadda tausayinsa ya kamani ba wallahi." Ƙirjinta suka kawai yake don bala'in hassada. Gara ya auri ƴar kowa da wannan yarinyar da ta tsana tun fil azal. Walid ta kira bawan nata yazo ya kaita gida. Yinin ta bata iya ƙarasawa ba kenan saboda yadda ta ɗorawa kanta wahala. Abu kamar wasa sai gashi ranar ta kasa runtsawa. Kwana biyu tana ɗaki ko makaranta ta kasa zuwa. Ta yaya rayuwa za ta yi mata wannan rashin adalcin. Aisha da Minasco ɗin ta suka tsaya mata a maƙoshi tuni sun sauka Tauhidat ta maye gurbin. Idan har wannan ƴar yarbawan za ta iya auren dan gidan Alh. Audi to tabbas ita ma za ta iya auren kece raini. Shamsun da Tauhidat ta samu ita ma shi take muradi tunda an ce shi kaɗai ne dan Alh. Audi. Mene ne ake taƙama dashi sama da asiri. Tsoro ne ya baƙunceta domin kuwa ko gaban malami bata taɓa gurfana neman taimako ba bare boka. Ƙwadayi da halinta na ƙyashi da son doke kowa su suka kwasheta zuwa kasuwa inda ta sayar da zoben da kakarta ta bata na gwal, ta nufi wani ƙauye da take jin labarinsa a wurin shige-shigenta. Tsigar jikinta ke tashi tun kafin ta ƙarasa ƴar bukkar da take ita ɗaya a iya inda ido ke hangowa. Wani irin abu take ji yana bibiyarta kamar ana sansana mata jiki. Sau biyu tana jin kamar ta juya saboda firgici amma tunanin daular da take mafarki ya hana. Mata biyu ta jira a kewayen bukkar kafin ayi mata iso cikin dakin ganawar Boka Maibindi. Wani murɗaɗɗen mutum ta gani zaune, daga shi sai baƙin kyalle da ya daura a ƙugunsa na kare tsiraici. A ido yafi kama da riƙaƙkun ƴan dambe ma'abota one-blow-seven-die. "Suwaida Musa barka da zuwa" ya ce da muryar mata. Bata san lokacin da ta ɗaga kai suka haɗa ido ba. Wannan muryar ko ita albarka. "Kinyi mamaki ko? Kafin ki zauna ina da sharaɗi guda ɗaya. Zamanki alamar amincewa ce." "Na yarda", ta ce kafin ya faɗa ta sami wuri ta zauna. Tunda ta kawo kanta to kuma babu gudu ba ja da baya. "Idan buƙata ta biya ba da kuɗi zaki biyani ba. Abinda zan nema sai lokacin da ya dace zan sanar dake." Tabe baki ta yi. Ta riga ta san labarin ire irensu. Su dai ba wuya su ɗora ido akan mace sai sun nemeta idan suka fuskanci a matse take da biyan buƙata. Idan ma sana'arsa kenan za ta gwada masa ita ƴar zamani ce. Buƙatar ta biya ya nemeta ya rasa. As simple as that. "Kina iya ƙin dawowar ma babu matsala." Taji ya ce da fara'a sosai. Cikinta ya ɗuri ruwa ta fara inda-indar bashi haƙuri. Babu wata alamar ɓacin rai ya buƙaci ta zura hannunta a cikin wata ƙwarya ta ɗebo ƙasa. Da ta tashi sai da ta ciko hannun taf ta juye ƙasar a wani ƙoƙo. Ƙasar ya ɗiba ya burshine fuskarsa da ita, a take fara'ar tasa ta ɗauke. "Yaron nan yana da lalura. Kin tabbata zaki iya aurensa a haka?" Maibindi ya tambayeta. "Allah na tuba a wannan zamanin waye bashi da lalura? Da ka ce sannu zaka ji wuri ya kaure da yauwa." "Ba a kira mana sunan da ki ka faɗa a gidan nan ki kiyaye. Kinsan yana da aure?" "Na sani kuma idan zai yi wu ina son su rabu kafin ayi bikin da ake ta sanarwa a jaridu." Kai ya girgiza, "abinda ya haɗa auren nan da lalurar tasa ba ƙaramin sihiri bane wanda karya shi sai bokan da ya haɗa. Na faɗa miki ba don ki raina aikina ba sai don ki sani ko su waye a tare dashi a tsaye suke sosai." Susu ta shiga gyaɗa kai sama da ƙasa, "dama na faɗa. Babu yadda za ayi ace wai ɗan gidan Alh. Audi guda ya ƙare da ƴar mai walda sai ka ce tatsuniya." Tashi tsaye Maibindi ya yi ya juya mata baya yana fuskantar kayan tsafinsa. Susu na ɗaga kai ta yi mummunan gamo da jelar da ta ɓullo ta cikin ƙyallen da ya ɗaura tana harbin iska kamar a jikin mage. Tsoro ya mamayeta ta ƙanƙame jikinta tare da saka hannu ta toshe mazaunanta kafin jela ta ɓullo mata. Ya ɗan ɗauki lokaci yana zuba surkullensa, sannan ya dawo ya zauna ya yi mata bayanin hanyar da zata bi ta samu Shamsu a tafin hannunta. "Dawowarki nan da kwana uku ita ce alamun nasara. Idan naji shiru kuma bayan na san kin sami abinda ki ke so to ki tsumayi fitowar abinda ki ka fi tsoro a jikinki. Tashi ki tafi."