Kenza eBookz

Cizon yatsa book 1&2 complete - Chapter 16

Cizon yatsa book 1&2 complete - Chapter 16

Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 16: Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 16. [2/23, 7:34 PM] Nasma: Da yararin fitsarin nasa da bai gama tsanewa ba…

3,621 words

[2/23, 7:34 PM] Nasma: Da yararin fitsarin nasa da bai gama tsanewa ba ya taso gabanta yasa hannu ya maƙuro wuyanta ta soma kakari, "ya akayi na sake yi bayan kin ce kece maganin?" Idanunta tuni suka raina fata , saboda shaƙarr da ta ji. Numfashinta ko sauka baya yi da kyau. Ga wani abin baƙincikin da yasa ta ji kamar ta haɗiyi zuciya a wurin, ɗigar fitsarin jikin wandonsa akan yatsun ƙafarta. Da ƙyar ta samu ta bambare hannunsa daga wuyanta, ta koma gefe tana matsa wurin. Duka wannan tashin hankalin suna yinsa ne a lokacin da ake ta kabbara an tayar da sallar asuba. Ko da suka haɗa ido lokacin da ta ɗago kanta kallon da yake mata ya bata tsoro. Gani take zai iya yi mata komai shi ya sa ta tuna shawarar Maibindi da ya ce ta nemo ƙaryar da za ta yi masa. Ba don ta so ba ta tashi ta rungume shi, don a yanzu kam ko ɗigo bata son shi, dama can bata taɓa son shi ba kuɗi ne ya kawota amma yanzu abin ya ƙaru. "Sham ka manta cuta ce kaɗai take shiga farat ɗaya amma magani sai a hankali?" "Kina nufin ba yanzu zan warke ba?" "Ina nufin mu bi komai a sannu. Ka tuna sati uku da suka wuce bamu san juna ba. Ina da wanda nake so yake so na amma jihadin da na hango zan yi idan na aureka yasa na bijirewa iyayena. Na so Walid sosai amma idan na tuna shekarun da ka ɗauka cikin ƙuncin wannan lalura sai naji zan iya yi maka komai. Sham zan zauna da kai har ƙarshen rayuwata, ko da baka warke ba." Ta ƙarashe zancen tsigar jiki na tashi saboda tsabar ƙyanƙyaminsa da take ji. Zuciyarsa ce ta sauko ya sake ƙanƙameta da kyau, "Suwaida kina ganin za ki iya zama dani ko ban warke ba?" Sai da ta yamutsa fuska tunda ba gani zai yi ba ta ce, "me zai hana? Na riga na sadaukar da rayuwata ga neman farincikinka. A kowane hali ka ke ni mai sonka ce har abada." Maganganun sunyi tasiri sosai a ransa, ya dinga yi mata alƙawura na kyautatawa. Ɗakinsa ya ce taje ta samo masa kayan da zai yi sallah dasu ta fita. Kafin ta isa ta tsaya a korido ɗin da zai sadata da ɗakin nasa ta sha kukanta ta more. Da suka idar da sallah ne take tambayarsa game da kayan da ta gani jiya a dakinsa a kasa. "Kayan baccina ne da zannuwan gado da suka ɓaci. Idan sun taru zubarwa nake yi" A ranta ta ce 'Suka ɓaci ko ka ɓata su?' "Me yasa ba ka bayarwa a wanke?" "Kina so na tonawa kaina asiri kenan? Kinga kada ki damu kanki ga waccan yarinyar sai ta dinga wankewa." Girgiza kai ta yi da sauri "ba ka gudun tonon asirin ashe. Ba wai ina son shiga tsakaninka da matarka bane amma idan da za ka yarda zanfi son ace ni kaɗai na san wannan sirrin. Idan kaje ɗakinta kada ka bari bacci ya dinga ɗaukarka." Kamar ya faɗa mata babu aure tsakaninsu sai dai ya cije ya ce "babu abinda zai haɗamu. A wurina ke kaɗai ce matata ita kuma tunda kwaɗayi yasa babanta ya matsawa Baba ya aura min sai mu jira su gaji su ce na saketa." A wurin Susu kasancewar Tauhidat matarsa kuma suna gida ɗaya ƙoshi ne ya haɗe mata da kwanan yunwa. Idan duniya ta san halin da Shamsu yake ciki dariya za ayi mata. Za ta so Tauhidat ta zama me wanke kayan amma ko ita idan ta sani sai ta yi mata dariya a bayan ido. Gara ta rufawa kanta asiri maganar nan ta mutu a junansu. Ƙarfin dole jikinta ya samu ba don bata buƙatar hutu ba. Zama cikin ƙazantar nan abu ne da ba za ta jura ba ko kaɗan. Ɗaya daga cikin tawul ɗin banɗakin ta ɗauko ta haɗa ruwan kumfa ta goge katifar bayan ta cire manya manyan zanin gadon masu nauyi da ado irin na amare. Da ƙyar ta juya katifar inda fitsarin ya kwanta ta kuma gogewa sannan ta jinginata da bango ta saki fanka da AC. Tana gamawa ɗakinsa ta koma ta samu ya jika kayan baccin nasa. "Yauwa dama ke nake jira ga kayan can na jika miki zan kwanta." "To" ta ce tana binsa da kallon tsana ta shiga ƙazamin banɗakin ta wanke kayan sannan ta wanke shi tas. Tana aikin tana guntun amai da tofar da yawu kamar mai yaron ciki. A kan resting chair ɗin ɗakin ta same shi yana bacci ta yaye zanin gadon da ya yi datti ga zarni. Da ta ɗaga katifar bala'in da ta tarar sai da yasa ta kakarin da ya tashe shi. Don tsabar iya munafunci haka ta haɗiye yawunta ta cigaba da aiki. Tun asuba sai ƙarfe goma Susu ta kammala ta samu ta yi wanka. Ɗakuna biyu katifun duka jingine da bango ta shanya zannuwan gado a banɗakuna da jikin gado. Idan ta kallesu sai taji kamar ta ɗebe ɗan arziƙin da ta samu na auren ta gudu gida. Shamsu da Maibindi da bai faɗa mata gaskiya ba sun sha Allah Ya isa ba iyaka. Irin wannan rana da kowace mace take hasko kanta a matsayin sarauniyar gidan mijinta ita a baibai tazo mata. Daga tashi daga bacci sai wanki da gyaran fitsari ko daɗin ji babu. Ƴar kwanciya da jiran tarairaiyar miji sai dai taji a labari da alama bata da wannan rabon. *** A ɓangaren Tauhidat kuwa ranar ko kaɗan bata runtsa ba sai bayan asuba. Lokaci ya yi gareta da za ta ajiye tausayin kanta da na Nanna ta fara tunanin mafita. Admission letter ɗinta ta tuna dake hannun Alh. Audi ta koma addu'ar Allah Yasa ya barta ta yi karatun. Bata taɓa sha'awar Law ba haka zalika basu taɓa zancensa da Nanna ba shi yasa ta yi mamaki da ta zaɓar mata shi. Ta riga ta ƙudurtawa zuciyarta cewa ba za ta bata kunya ba. Karatu zata yi tuƙuru ta ga nufin Allah akansu. Shi kuma Alh. Audi indai biyayya tana kawo yarda to za ta bishi sau da ƙafa. Sauran sirrukan nasa da basu sani ba take fatan sani ƙila a haka ta samo madafar da za ta zama tubalin gyara ga rayuwar masoyanta. Da wannan tunanin ta ɗauko MP3 ɗin da Arƙam ya bata ta buɗe kasan wani akwati ta ajiye. Tana son jin muryarsa ko sau ɗaya ne amma ta danne zuciyarta taƙi kunnawa saboda martabar igiyar aure. Wayar Fanna ce ta tasheta ta ce ta buɗe ƙofa an kawo musu breakfast. Ba haka taso ba don ba ta son haɗuwa da masu gidan sai dai ba yadda ta iya haka ta saka hijab ta sauka. Masu aiki biyu ta tarar kowacce ɗauke da tray. Ta farkon ta zarce dinning table ta ajiye na hannunta bayan ta sanar da ita cewa na Susu ne. Na hannun ɗayar kuma shi ne nata da Shamsu. Karɓa ta yi ta musu godiya sannan ta ajiye shi kusa da ɗan uwansa ta koma ɗaki. Wankanta ta yi ta shirya cikin wata super ɗinki mai A-shape ta koma kan kujera ta zauna jiran yadda yau ɗin za ta kasance. Susu da Shamsu da suka sauka ƙasa suka tarar da abinci sai ya ce ta kira Tauhidat ta ɗiba. Ɗan ɓata rai ya ga ta yi ya yi murmushi "Kishi ki ke yi da ita?" "Akan me kai da uwargidanka? Gani dai nayi bamu taɓa haɗuwa ba kuma kawai sai naje kiranta cin abinci." "Zan faɗa mata idan an kawo ta dinga ɗiba idan bamu fito ba. Bana son haɗuwa da ita amma kin san Baba yanzu sai ya ɓata min akanta." Hawa saman ya yi Susu ta buga tsaki. Haushinsa taje ji ace ko sau ɗaya bai mata sannun bautar da tasha ba. Babban dalilinta na ƙin zuwa kuwa bai wuce rashin son haɗuwarsu da Tauhidat ta zama a haka ba. Gara ayi a gabansa ta yi abinda ta tsara. Tana aikin tunani wani irin ƙamshi ya iso gareta kafin mai shi ta iso. Duk da babu wani abin kirki da aka yi mata na aure amma rainon Haj. Manga idan bata riƙe ƙamshi ba sai ace anyi asarar kuɗin tara. Susu sai ta dukar da kai sai da suka iso gaban tebur ɗin ta ɗago. Mamakin ƙarya ta nuna tunda basu taɓa haɗuwa a gidan gaba da gaba ba. Ko jiya a gaban Alh. Audi da zai musu nasiha kowacce fuskarta a rufe take. Baki a sake ta buɗe idanu ta dafe ƙirjinta tare da miƙewa tsaye, "Kamar na san fuskar nan. Wayyo Allah ina muka taɓa haɗuwa?" Murmushi Tauhidat ta yi, fuskarta ta ƙara haskawa ta yi kyau. Tsaf ta gama karantar yanayin Susu sannan ta ce, "Oluwatosin ce ko in ce Tauhidat bayerabiya ta FGC Bajoga." Shamsu tsayawa ya yi kallon yadda Susu ta soma rawar jikin ganin Tauhidat har tana cewa bata taɓa zaton zasu sake haɗuwa ba. "Ina fata duk abinda ya faru tsakaninmu a baya zaki manta dashi mu haɗa kai mu samarwa Sham kwanciyar hankali?" "In sha Allah" Tauhidat ta ce saboda zancen ya fara isarta, yana neman fama mata gyambon abinda ya faru da mahaifiyarta a wannan rana. Kamar yadda Susu ta so, Shamsu tambayar me ya haɗasu ya yi. Caraf kuwa ta marairaice fuska ta shiga karanto masa ƙarairayin da ta shirya. "Makaranta ɗaya muka soma. Ina SS1 ta shigo JS1. Ni ce school mummy ɗinta ma." Kujera Tauhidat ta ja jingina ta zuba mata idanu. Bata wani nuna mamaki a fuska ba saboda tun ranar da ta ga fuskarta a falo hankalinta bai kwanta da zuwanta ba. "Ki ce kunsan juna so bani da matsalar rigima kenan" cewar Shamsu. "Haka nake fata" Susu ta ce tana jan hanci babu ɗigon hawaye a idonta, "rabuwar tamu a lokacin bata yi daɗi ba. Tauhidat ki yi haƙuri kinji. Na san tunda ni ki ka samu ina tattara kayan akwatin dole ne ki zargeni a matsayin wadda ta sace miki provision." Ɓata rai Shamsu ya yi ta yi saurin cigaba da bayanin, "hostel na shiga na samu an fasa akwatinta an zubar mata da kaya shi ne ina cikin kwashewa ta ganni. Ta yi zaton ni na buɗe ta kai ƙarata karshe aka koreni washegari." Jawur idanun Shamsu suka yi da ɓacin rai. Tauhidat ta gyara tsayuwarta har lokacin da murmushi a fuskarta ta ce, "Allah Ya bi wa wanda aka cuta haƙƙinsa. Kiran me ka ke yi min?" Ta juya ɓangaren Shamsu. Tsawa ya daka mata bayan ya rungume Susu, ya gama yi mata faɗa sannan ya ce ta koma ɗaki idan sun gama cin abinci tana iya zuwa ta ci amma ba zai ci da ita ba. Ɗan durƙusawa ta yi fuska a sake ta ce, "a tashi lafiya." Ta juya musu baya ta hau sama ko waige babu. Ran Susu in ya yi dubu kuwa ya ɓaci, don so ta yi ta ƙaryata ta ita kuma ta samu ta ƙara wasu ƙarairayin da zasu janyo Shamsu ya gaggauta korarta daga gidan. A baki ya dinga bata abincin tana ta karairaya da langaɓewa a jikinsa. Haƙuri ya bata akan abinda ya faru a baya ya kuma yi mata alƙawarin hora Tauhidat ta inda ba ta zato. *** Tunda su Haj. Manga suka isa wurin Arƙam take ta fama dashi akan canjawar da ya yi. Sai dai abu faskara. Halayyarsa gabaɗaya ta sauya babu wata walwala. Daga aiki sai aiki, hira ma irin ta tsakanin ɗa da mahaifiyarsa ba ya zama suyi. Ya ɗauki damuwar auren Tauhidat ya saka a rai. Dama can shi ba ƙiba ba sai ya sake zugewa. Haushin kansa yake ji da bai dage an ɗaura musu aure kafin ya bar Saudiyya ba. Ga rasuwar Baffa da ta tsaya masa a rai. Shi ne mutum na farko da ya fara ɗora idanu akansa bayan shekarun da ya ɗauka yana rayuwar kaɗaici. Baffa mutum ne da mantawa dashi abu ne da ba zai yiwu a garesu ba. Daƙile zuwansa Nigeria da Haj. Manga ta yi sai yasa yake jin kansa useless. Ita da take mace kuma ga girma tana da kamarsa yana ganin bai kamata ace ita kaɗai take faɗi tashi akan Alh. Audi ba. Da wannan damuwar ya koma Arƙam ɗin da, bambancin kawai shi ne ba ya shan ƙwayoyi kamar yadda ya yi wancan karon. Dawowarsa kenan daga aiki ya gaisheta zai wuce ɗaki kamar yadda ya saba, sai yaji shiru bata amsa ba. Maimaita gaisuwar ya yi taƙi kula shi har sau uku. Jamal ya kallesu su biyun ya ɗanyi murmushi, "Nanna Arƙam na gaisheki." "Ya maganar neman accomodation (wurin kwana) ɗinka don hankalina zai fi kwanciya ace ka samu kafin na tafi." "Ba a nan zamu zauna tare dashi ba?" Arƙam ya tambayeta yana mai mamakin me ya kawo zancen neman wani wurin. "Ina magana kayi shiru ko baka fara nema bane?" Ta sake tambayar Jamal da ya haɗe rai yana tura mata baki. Ya san tana sane take share yayansa kuma ba ya jindaɗai. Ko shi da ba soyayya bace tsakaninsa da Tauhidat yana jin kansa kamar an zare masa wani abu mai mahimmanci ina ga Arƙam da cikin ƙanƙanin lokaci zuciyoyinsu suka zama abu guda? "Nanna ki bar zancen ya nemi wani wurin don Allah. Idan kina ganin gidan nan ya yi nisa da makarantarsu sai na nemi wanda yake kusa." Arƙam ya ce hankalinsa ya soma tashi da share shi da take yi. Tashi ta yi rai a ɓace, "Idan kai ma ban isa da kai bane shi yasa ka kasa bani amsa zan tattara na koma gida. Duk da bani da uba amma ba zan rasa masu ƙaunata ba a can." Ta taɓo su kuwa da kalamanta suka sakata a gaba kamar wasu ƙananun yara suna kuka. Ɗauke kai ta yi dama hakan take so. Tana gani Jamal ya zunguri Arƙam yana cewa, "Duk laifinka ne ka bata haƙuri mana." Shi kuma ya harare shi, "me nayi? Ita fa ta hanani zuwa gida akan wani Kawu Audi." "Kai kuma ka dena sakin fuska saboda Tauhi..." Hannu ta ɗaga musu "ya isheni, kuna abu kamar wasu yara." "Ka girma ne Jamal?" Cewar Arƙam yana kashewa mahaifiyarsa ido don ta yi dariya. "Ina fa, kana ganin yaro sweet sixteen." "To nima sammakel"54 Haj. Manga da Jamal suka kwashe da dariyar yadda ya ce sammakal ɗin a turance. Fara'arta yake buƙata sai yaji hankalinsa ya kwanta ya tashi ya rungumeta. "Cikani" Ta ture hannunsa, "tunda nazo gidan nan ka ke faman ƙunci kamar kai kaɗai aka yi wa laifi. Ni ban kai matsayin ka ɓoye damuwarka akan mace ba idan kana tare dani ko? Don an rabaka da Tauhidat sai ya shafi alaƙarka da mahaifiyarka, ɗan uwanka da duka al'amuran rayuwarka?" "Kiyi hakuri Nanna in sha Allahu daga yau na dena." "Ka cigaba dai sai mu kama gabanmu ka jira wadda take amsa sunan matar waninka." "Kiyi haƙuri mana Nanna sai kin ƙara fama masa ciwon zuciyar?" Inji Jamal. Danne shi Arƙam ya yi akan kujera suka soma kokawa. Tun Haj. Manga na rabo har ta koma gefe tana dariya da ta kula Arƙam ke jin jiki ba autanta ba. Sai da suka gaji don kansu suka bari. Da daddare Arƙam ya bita ɗaki ya sake bata haƙuri. "We are suppose to look after you not the other way round (mu ya kamata mu kula dake ba ke ki kula damu ba). Yana damuna yadda ki ke struggling ke kaɗai kin hanamu yin komai." Kumatunsa ta shafa tana murmushi "ranarku tana zuwa Arƙam, yanzu so nake na ginaku ta yadda ko babu ni rayuwarku ba za ta tagayyara ba." Rungume da juna Jamal yazo ya same su shi ma ya shige tsakiya. Kowanne cikinsu ya ƙuduri niyyar ƙara azama cikin karatunsa domin su farantawa mahaifiyarsu. *** Sati biyu kenan da tarewar amaren Shamsu. Yau Fanna da kanta ta shigo ɓangaren nasu da yamma ta buƙaci ganinsu. Kusan tare suka sauko. Tauhidat ta yi kyau abinta saboda zaman wuri ɗaya. Gashi ta kwantar da hankalinta, tunda ta tabbatar Shamsu na Susu ne ita kaɗai hakan ya yi mata ɗari bisa ɗari. Yadda Tauhidat ke yin kyau tana ƙara cika haka Susu ke motsewa tana yanƙwanewa. Kullum ba fashi Shamsu sai ya yi fitsari kamar ibada. Yanzu ko baccin kirki bata yi saboda tana yawan farkawa ta tashe shi fitsari amma duk da haka sai ya yi mata a kwance. Ranar da ta nuna tana son su raba ɗaki ɓata rai ya yi wai ta fara ƙyamarsa. Ta zo ta kawo shawarar a saka washing machine a bandakin yaki amincewa, wai gani yake kamar najasar ba za ta fita ba kuma ya saka ya yi sallah. Abu ya tarar mata goma da ashirin bata da kwanciyar hankali ko kaɗan. Idan ta ga idon Tauhidat ne take nuna kamar daɗi take ji miji na kula da ita. Saƙon Alh. Audi Fanna ta sanar dasu akan ɗaukan mai girki. "Kowacce tana son a ɗaukar mata kuku ko guda ɗaya za ta wadatar daku?" Susu za ta yi magana ta ji takun Shamsu yana saukowa, sai ta karya murya tana kallon ɓangaren da Tauhidat ta zauna. "Me zamu yi da kuku kuma Anti? Mu biyu a gidan nan ai sai ace mana ragwaye ko Tauhidat?" Kallon banza Fanna ta yi mata kafin ta ce, "Tauhida karatu za ta fara. Shamsu kaje Alhaji yana son ganinka zai baka mukullin gidan da aka kama mata har ta gama." "Bangane ba? Karatu za ta yi amma babu wanda ya faɗa min sai yau?" Tashi ta yi abinta, "kaje ka same shi. Ke kuma idan kina buƙatar kukun ki faɗa min a ɗauko miki." Ta ce da Susu kafin ta fita. Godiya Tauhidat ta yi mata ga murnar karatu da zata yi. Susu jikinta sanyi ya yi saboda sau biyu tana yiwa Shamsu maganar nema mata transfer ta ƙarasa karatunta a nan ya ce idan ta soma karatu waye zai ji da lalurarsa. Da ya je wurin Alh. Audi ma yaso yi masa gardama akan kada Tauhidat ta koma makaranta ya tuna masa cewa ba matarsa bace saboda haka bashi da iko da ita. Karatunta kuma su zai amfana don zai bata aiki ne ta zama lauyan kamfaninsu idan ta gama. Cikin ƙanƙanin lokaci ta haɗa kayanta ta koma ƙaramin flat ɗin da ya kama mata mata a Gwagwalada. Gida ne mai kyau zaman mutum ɗaya ko biyu sai ɗaki mai haɗe da banɗaki ta waje. An saka mata komai a ciki sannan Alh. Audi ya bata mota. Da ta tashi tafiya sai ya haɗata da Mammalo saboda kada ta zama ita kaɗai babu namiji sannan shi zai koya mata tuƙi. Sai kuma mai aiki matashiya ƴar garin da aka ɗaukar mata. Hankalinta kwance kamar tsumma a randa take karatu. A can garinsu Papa Abayomi ya sami nutsuwa da karatun da ta fara shi ma ya buɗe shago a jikin gidansa. Haj. Manga ma ta dawo ginin makarantarta ya kankama. A wata bai fi sau ɗaya ko biyu Tauhidat take zuwa gidan ba kuma da wuya ta wuce Asabar da Lahadi ta tattara ta koma. Bata shiga harkar kowa iyakarta ɗaki sai idan taji yunwa ta sauko. Susu kullum cikin takalarta rigima take amma taƙi bata haɗin kai suyi rigimar da take so. Idan Shamsu yana gida ya shigarwa Susu har ƙasa take durƙusawa ta bada haƙuri. Shi kuma wannan halin nata sai yasa take masa kwarjini ya kasa ci mata mutumci. Wata biyar bayan auren Susu ta fara laulayi. Ta tsinci kanta a mawuyacin hali saboda fitsarin Shamsu da yanayin da take ciki. Abubuwan da suke faruwa da ita babu wanda ta taɓa tsammani zai zo gareta a gidan aure, gidan auren ma irin wannan. Babu hutun gangar jiki da zuciya daidai da rana ɗaya. Iyayenta kuma tamkar sun goge shafinta a rayuwarsu. Idan ta kira waya zasu amsa su tambayeta gida da mijinta daga nan basa ƙarawa. Gashi ta yi kuɗi ta wuce duk sa'o'inta amma ko tsinken hannunta sunƙi karɓa. Kuɗaɗɗen a jibge kawai suke a account tunda bata rasa duk abinda take buƙata ba. Sun zaga ƙasashen turai inda ta bautu fiye da Nigeria. A zaune take bacci a duka hotels ɗin da suke zama. Saboda sabo bata wuce awa guda take tashin Shamsu fitsari don kada a tafka abin kunya. Su da suka tafi wata uku amma satinsu biyu ta matsa masa da ƙaryar ciwo suka dawo. Wata Asabar da ta gaji sosai bayan wankin da ta sha don fitsarin yau har ya taɓa kafet ta sauko ƙasa tana hutawa. Ta yi zurfi a tunanin rayuwarta mara daɗi bata san lokacin da Tauhidat ta wuceta zuwa kitchen ba. Tana zaune ta ji ƙamshin abinci na shiga hancinta ga kyashin ta karɓi abin hannun kishiya. Dama kuma tana jin zafin yadda komai ya ƙare a kanta Tauhidat ta samu kwanciyar hankalin da ya gagareta. Takunta ta ji za ta fito daga kitchen ɗin ta tura hannu a makwogaro ta ƙaƙalo aman dole. Tauhidat na fitowa ta sameta ta yi shame-shame a ƙasa cikin amai. Da sauri ta ajiye plate ɗin hannunta ta tafi ta dafa mata baya har ta gama. Bata nemi mai aiki ba da kanta ta gyara wurin tana ta yi mata sannu har Shamsu ya shigo. Susu na ganinsa ta ƙara narkewa hadda kuka. Shi ma sannu yake mata daga bisani ya ce, "Me ki ke son ci nasa a dafa miki?" Tauhidat da take gefenta tana kallonta da tausayawa ta kalla, "kiyi min alfarma ki zuba min abincinki kafin a dafa wani." Tsakani da Allah ta tausaya mata ta yi saurin miƙewa, "sai kin ce alfarma kamar wani abu mai girma? Bari na ɗauko miki flask ɗin da plate."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull