Kenza eBookz

Cizon yatsa book 1&2 complete - Chapter 17

Cizon yatsa book 1&2 complete - Chapter 17

Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 17: Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 17. Da ta kawo da kanta ta zuba mata ita kuma tana ta jujjuya idanu a zuwan…

1,689 words

Da ta kawo da kanta ta zuba mata ita kuma tana ta jujjuya idanu a zuwan tana jin jiki. Ko cikakkun mintuna biyar bata yi ba ta share abincin nan tas. Tauhidat ta juye mata ragowar shi ma kaɗan ta rage ta yi gyatsa. A baƙin halinta taƙi bari a ɗauko Kuku don kada Tauhidat ta mora. Sai gashi yanzu bata iya girki sosai kuma idan ta yi baya mata daɗi. Da daddare Tauhidat sai ta haɗa da ita a girki don tausayi ma harda tambayarta abinda take so. Washegari Lahadi ma haka ta yi. Tunda suna gajeren hutun semester sai wata Lahadin za ta koma, saboda haka girki sai ya dawo wuyanta. Susu ta ƙara mata da aikin amai don ko bata ji sai ta janyo shi kawai don ta bata aiki ta yi a ƙasa. Bayan kwana biyu Susu ta ɓullo da salon idan ta girka abu ta bata sai ta yi ta kakarin amai, ta ce ba shi take so ba. Ba gajiyawa haka Tauhidat za ta je ta sake girki duk don tana ganin babu asara a taimakon mara lafiya. Yau da ta kai mata abincin tana ajiyewa ta koma kitchen ɗin saboda ta ɗora ruwan miyar dare. Tana daga ciki ta ji kamar muryar mai wanke-wankensu sai ta fito da sauri don ta tsayar da ita. Idanunta akan Susu suka sauka tana cin abincin nan hankali kwance. Muryar Shamsu da taji yana kiranta daga sama kuma ta san ba zai wuce ya sata aiki ba sai kawai ta karkace ta zura hannu a baki ta soma kwara amai akan kujera da kafet. Tauhidat tana tsaye a bakin ƙofar kitchen tana kallon ikon Allah har ya sauko. Kuka ta saka masa tana riƙe ƙirji wai abincin akwai ƙarni da yaji. "Idan naci zai iya tayar min da ulcer." Shi kuma cikin damuwa ya ce, "dole ki ci abinci Suwaida ko don lafiyar baby ɗinmu." Ɗga kai ya yi ya shiga kiran Tauhidat ta fito hannuwanta naɗe a kirji tana kallonsu. "Gani." Faɗa ya soma yi mata fuska a haɗe, "Ki gyara wurin nan sannan ki dafa mata wani abincin. Kin san ba lafiya gareta ba akan me za ki yi abinci da yaji kuma babu kula duk ƙarni." Gashin Susu da ya bazu a fuskarta ya tattare mata "me ki ke so ta dafa miki?" "Zan fi son tuwo ko sakwara da miyar agushi saboda zai fi riƙe min ciki." Ɗago kai ya yi ya kalli Tauhidat da bata da niyyar motsawa bare ta fara aikin da ya saka ta, "me ki ke yi ne a tsaye?" Murmushi ta yi har haƙoranta suka bayyana sannan ta sami wuri ta zauna ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya. "Da ace ciwon gaske matarka take yi da babu abinda za ku nema banyi muku ba." Marairaicewa Susu ta yi a ɗan tsorace, Shamsu kuma ya soma faɗa yana ɗaga murya, "me ki ke nufi kenan?" Tashi ta yi sai da ta isa bakin bene sannan ta juyo ta ce, "ina nufin Maami ta koyar dani cewa ribar rayuwar duniya shi ne haƙuri, Nanna kuma ta koya min babban darasin rayuwa shi ne kada ka cuta kuma kada ka bari a cuceka. Matarka ta san me nake nufi tunda a idona ta yi komai." Daga haka ta haye sama abinta ta barsu baki buɗe. Kwanciya ta yi tana ta juye-juye. Nanna take son gani ta faɗa mata damuwarta kuma ta nemi shawara amma yanzu tsakaninsu sai kallo da gaisuwar da ba a amsawa. Da haka ta samarwa kanta lafiya daga Susu har Shamsu suka ɗaga mata ƙafa. Shi ya san ba matarsa ba ce bashi da hurumin takura mata yadda yake so, alhalin mahaifinsa na bayanta. Susu kuma tana tsoron tunzura tsakaninsu ya dawo yana marmarin zaman aure da ita. Saboda ta kula tun ranar da abin ya faru salon kallon da yake yi wa Tauhidat na musamman ne, kallo ne irin na wanda yake ganin abinda yake burge shi. *** Tray ne babba a hannun Tauhidat wanda ta jerawa kwanukan abinci da abin sha. A ƙofar ɗakin mahaifinsu na da wanda Shaheed yake amfani dashi tun bayan dawowarsa wata guda da ya wuce ta tsaya. Sallama ta yi cikin zazzaƙar muryarta ya fito sanye da doguwar riga da alamun ko wanka bai yi ba. Da tray ɗin ta ɗan ture shi yadda za ta ga cikin ɗakin sosai. "Broda kada kace min baka gyara dakin nan ba tun safe gashi Papa ya iso" ta ce da yarbanci. Kallon rashin fahimta ya yi mata "bangane Papa ya iso ba. Zuwa zai yi ko ya zo?" Wannan karon ita ta bishi da kallon rashin fahimta "bai faɗa maka zai zo ba?" Bai iya ɓoye ɓacin ransa ba ya ce "Bai faɗa min komai ba. Me yasa zai zo bayan na ce idan na gama komai a nutse zan je Abeokutan?" Tray ɗin Tauhidat ta ajiye ta soma tattare kayansa da sauri "laifinka ne Broda. Wata ɗaya da dawowarka amma ka kasa zuwa ya ganka. Kullum ya yi magana sai ka bashi excuse kamar baka damu dashi ba." Fuska ya haɗe yana harararta "wace irin magana ce wannan? Kuma da ki ke cewa ina bashi excuse kina son na ɓatawa Alhaji rai ne? Shi ne fa ya dakatar dani." Tsintsiyar da ta ɗauko domin tattare ɗakin ta saki ta riƙe ƙugu "akan Alhaji gara ran Papa ya ɓaci kenan?" "Ni kada ki juya min magana daga faɗar gaskiya. Mutumin nan wace irin ɗawainiya ce bai yi mana ba. Degree da Masters ɗina duka ya ɗauki nauyi a ƙasar waje, sannan na dawo ya ce na jira wurin da zai sama min yin service yana so ya zama inda zan cigaba ne bayan na gama. Babbar maaikata yake so ya samu, shi ya sa fa na zauna idan an gama sai naje wurin Papa. Shi me yasa ba zai min haƙuri na gama a nutse ba. Kullum sai ya kira kuma na faɗa masa amma nema yake ya hanani aiki a nan sai a can." Mamakin kalamansa ne ya kamata ta kaɗa kai hawaye na zubo mata "Broda har akwai ɗawainiyar da ta wuce wadda iyayenmu suka yi maka akan karatu? Ina Alhajin yake lokacin da Papa yake walda a bakin titi yana dakan sakwara a bayan shagonmu? Ina yake lokacin da Maami take sayar da abinci don su haɗa kudin makarantarka?" "Duk abinda suka kashe min ya kai wanda Alhaji ya yi min ne? Meye don na ce ya jira ..." "Kai Broda ka san me ka ke faɗa kuwa?" Ta ce idanunta rufe da ɓacin rai. Tsawar da ta yi masa ta bashi haushi ya ɗaga hannu zai kai mata mari "kada ki ce zaki min rashin kunya don kina auren Shamsu sai na ɓabbalaki." Daga ƙofar ɗakin suka ji muryar Papa Abayomi ya ce da Shaheed "ni kuma idan ka kuskura ka taɓa min ƴa sai na nuna maka ƙaryar rashin kunya ka ke yi." Kunya Shaheed yaji ya soma inda inda sai dai Papa Abayomi bai tsaya sauraronsu ba ya juya. A tare suka bishi da sauri ya ce su koma ɗakin su jira shi yana zuwa. Ƙofar shiga ɓangaren masu gidan ya je ya tambayi mai bawa shuka ruwa ko Alh. Audi yana gida. Mutumin ya yi murnar ganin shi saboda anyi zaman mutumci ya fada masa cewa yana nan. Sun san idan za ayi wa kowa shamakin ganin ubangidan nasu banda surukinsa. Yana sa ƙafa suka yi kiciɓus da PA ɗin Alh. Audi ya nemi ya masa iso wurinsa. Haj. Manga ta ga lokacin da ya shigo yana biye da PA ɗin. Ta san wurin Alh. Audi zasu je sai tabi bayansu da takardun asibitin Dada da take so ya bada kuɗi a fita da ita. Tare yake da babban Accountant ɗin kamfaninsa suna tattauna batutuwa masu mahimmanci amma ya ce ya jira shi a waje zai ga baƙo. Bayan mutumin ya fita dariya ya yi don dama yana jiran Papa Abayomi yazo da kansa ne. Tunda ya bar gidan bayan biki bai kuma waiwayarsa ba. Zuciyarsa sai take ta kitsa masa ko neman hanyar karya masa alkadari yake nema shi ya sa ya hana dansa zuwa gida bayan ya dawo. Tashi ya yi da fara'a ya tarbo shi "my in-law ya hanya? Ban san kana hanya ba ai da tuni nasa an shirya maka tarba ta musamman amma duk da haka ina maka barka da zuwa" Babu wata fargabar tunkarar babban mutum kamar Alh. Audi ya tsaya a gaban kujerar da yake zaune yana huci, "Alhaji me ka ke nufi dani da ƴaƴana ne? Ba don rayukan mutane da dama ba ka sani gara na aurawa Tauhidat talaka irina da ta zama surukarka. Yanzu kuma ɗana ya dawo ka hure masa kunne ka hana shi zuwa inda nake. To na rantse maka baka isa ka mayar da rayuwar ƴaƴana kayan wasanka ba. Allah Yana tare damu kuma Yafi ƙarfin ka." Dakatawa Haj. Manga ta yi jiki a mace ta fasa shiga falon. Kar dai ace maganar Baffa ta zama gaskiya da ya ce kafin ta yankewa Papa Abayomi hukunci bincike ya kamata suyi. Dariyar Alh. Audi ta ji irin wadda yake yi idan yana tunanin nasara akan ƙudurinsa. "Dena rantsuwa Abayomi don aikin gama ya gama. Banda wauta irin taka yaushe yaro zai dawo daga turai ya yarda ka shiga tsakaninsa da alheri? Ka yarda ko kada ka yarda Shaheed ƙasƙantaccen yarona ne wanda bashi da burin da ya wuce farantawa ubangidansa." Yadda yaji zafin kalaman ba don ya san cewa Alh. Audi yafi ƙarfinsa ba da a wurin zai shaƙe shi kowa ya huta da annoba. Sauke fushin ya yi ya ce "me yasa ka ke buƙatarsa bayan Tauhidat? Ko baka aurawa ɗanka ita ba kada ka manta ka riga kayi min abinda ba zan taɓa iya fallasa sirrinka ba." Jikin Haj. Manga rawa ya kama, taji kamar ta banka ƙofar ta shiga. Wane irin sirri ne kuma suke magana a kai? Me Abayomi ya sani game da Alh. Audi wanda ya janyo ya sadaukar da rayuwar Tauhidat? Rayuwar su wa aurenta da Shamsu ya fansa? 'Taki' zuciyarta ta bata amsa da ƙaƙƙarfar kuwwa.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull