Cizon yatsa book 1&2 complete - Chapter 18
Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 18: Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 18. "Ina da masaniyar cewa kana ta aiki a kaina domin ka sami bakin magana…
14,259 words
"Ina da masaniyar cewa kana ta aiki a kaina domin ka sami bakin magana ka tona min asiri." Ta ji Alh. Audi ya ce. A tsorace Papa Abayomi ya ja baya wanda hakan yasa ya tabbatar da zarginsa akansa. Tasowa ya yi yazo daf dashi a saitin kunnensa ya faɗi wasu maganganu wanda babu yadda za ayi wani yaji ko da yana cikin ɗakin. Girman maganar ya yiwa Papa Abayomi nauyin da yasa shi zaman ƴan bori batare da ya sani ba. Gumi wani na bin wani ke karyo masa kamar wanda ya yi tsere. Kasa kallon Alh. Audi ya yi saboda ya riga ya fassara shi a matsayin shaiɗani a tsakanin mutane. Alh. Audi kallon yanayinsa ya dinga yi ya kuma yin dariya sannan ya ƙara da cewa "tunda na iya yiwa mutane mafiya mahimmanci a rayuwata haka to kada ka rabe ɗayan biyu duk ranar da ka buɗe bakinka Haj. Mangan da ka ke karewa da ƴaƴanta da naka da kuma kai kanka za ku ga mafi munin tashin hankali. Abayomi na yi maka alƙawarin kai da uwarɗakinka sai anyi muku jifan mazinata kafin ƴaƴanku su biyo bayanku." Innalillahi wa inna ilaihi raji'un ce kalamar da Haj. Manga da Papa Abayomi suke ta maimaitawa cikin tashin hankali. A haka ma don bata ji abinda ya faɗa masa wanda ya sanya ta dena jin motsinsa ba. Jirin dake barazanar zubar da ita ne yasa ta juya da nufin ta bar wurin ta tsinto muryar Papa Abayomi yana tambayarsa me yasa ya faɗa masa wannan magana. "Saboda ka ƙara sanin waye Audi sannan ka kara ja wa ƴarka kunne akan yi min biyayya. Abu na ƙarshe ina maka tuni da cewa ka shiga tsakaninta da Haj. Manga saboda bana son ta gane dole nayi muku ta yi ta nemi janyeta." Jiki ba ƙwari Papa Abayomi ya miƙe murya a dashe ya ce "bayan wannan babu wani abu da ka ke buƙata?" "Babu komai surukina, mu kwana lafiya." Alh. Audi ya ce da murmushi a fuskarsa kamar babu abinda ya faru. Kafin ya fito Haj. Manga da sauri ta koma can babban falo ta zauna wanda ta nan Papa Abayomi zai wuce. Halin da yake ciki yasa ya zo ya wuceta amma bai ganta ba. Tafiya yake kawai yana jefa kafafu duk inda ya samu. Sai da taga fitarsa ta koma ɗakinta ta sauri ta rufe kofa sai hawaye. Duk iya tunaninta rasa me suka tsarewa Alh. Audi ya hanasu zaman lafiya. Haushin kanta take ji saboda ganin a ƙoƙarin ta samarwa kanta ma'aikata makusanta ta yi sanadiyyar tarwatsa rayuwar bawan Allah Abayomi da marayun ƴaƴansa. Allah Sarki Tauhidanta da take kwana take tashi da ita a rai. Ba ta neman wani ƙarin bayani daga Papa Abayomi ta riga ta sani cewa da ita kaɗai da su Arƙam ne za a yi masa barazana. Kuka sosai ta yi akan rayuwar da suke yi abaibai tun bayan rasuwar uban ƴaƴanta zuwa yau. Akwai abubuwa da yawa da ta sani sun faru da rayuwarsu ba yadda ya kamata ba amma ko wuƙa za a saka mata a wuya ba ta ce gasu ba. Tamkar wadda aka kulle cikin ƙwai mara ƙofar fita haka take jin kanta. Ta bin wani abu da bata sani ba kuma ta kasa kamo shi. Idan nesanta kanta dasu Tauhidat zai zama kariya garesu za ta yi fiye da yadda suka yi. Su da suke bare a gidan ma suka iya jurewa bin umarnin Alh. Audi bare ita da ake yi dominsu? *** Mammalo na zaune a bakin gate wurin masu gadi suna hira Papa Abayomi ya fito. Tambayarsa suka yi ko akwai abinda yake buƙata, da ya fito dashi daga zuwansa ya ce ba nisa zai yi ba. Suna kallo ya cigaba da tafiya a gefe hanyar masu tafiyar ƙafa, Mammalo ya ɗora zancensa daga inda ya tsaya. "Wai kana nufin Salmanun ne baka sani ba? Yaron nan fa da ya yi fin ɗin dilki bana, din-din, din-din mane naaaaa." Mai gadin da suke hirar tare ya kwashe da dariya harda riƙe ciki. "Mammalo kenan, to ni kana cewa Salmanu ba sai na zata wani ɗan uwanka bane?" "Ka dai ganeshi ko? Ƴan gidansu da yawa suna fin ai irinsu Amiru da Sheruken. To su ne nake ce maka Yaya Uwani ta ce idan an bi salsala tushenmu ɗaya." "Da wa?" Inji maigadin yana sake bushewa da dariya. Ƙirjinsa ya nuna da jindaɗinsa, "da mu mana, ni da ƴan gidanmu. Karan hancin za ka duba." Mai gadi dai dariya hadda hawaye da Mammalo ya buɗe tsamurarren ƙirjinsa yana cewa ya duba ƙirar jikinsu. "Kuma ka tabbata tushen ba wai tana nufin tushen duka ƴan Adam ba? Wato daga babanmu Annabi Adamu AS" Shiru yaji Mammalo bai amsa ba sai tashi da ya yi da uban sauri yana ihun kiran Papa Abayomi da ya sauka titi bai sani ba. "Fafa, Fafa wayet (wait)." Papa Abayomi ko kusa kunnuwansa ba sa jin komai sai munanan kalaman Alh. Audi da suke ta maimaita kansu a ƙwaƙwalwarsa. Tafiya yake tamkar akan iska ya yi nisa a tunanin mafitar da ya kamata ya nema. Motoci na ta tahowa Mammalo ya kwasa a guje yana kiransa iya ƙarfinsa, sai dai kafin ya isa gareshi wata marsandi ta isko shi. A ƙurarren lokaci hankalin Papa Abayomi ya dawo jikinsa ya rasa inda zai bi ya bar titin. Mai motar ba irin horn ɗin da bai yi ba kuma ɗaya ɓangaren yara ne uku ƴan makaranta zasu tsallaka. Shahada kawai ya yi ya zabi buge mutum ɗaya akan uku. Duk saurin Mammalo da ihunsa yana ji yana gani haka motar nan ta ɗauke Papa Abayomi ta cilla shi gefen titi. Mai motar bai gudu ba don ya yi iya ƙoƙarinsa ya fito da sauri. Jama'a nan da nan suka taru akansa. Mammalo bai ɓaba ganin abinda ya tsorata shi makamancin wannan ba. Jini ne kwance a kan kwalta na baban Tauhidat. Yana ji mutane suna cewa ƙila mutumin kurma ne tunda ana ta masa horn amma bai kula ba. Maigadi ya shiga cikin gidan ya faɗawa abokan aikinsa, kai tsaye ɗakin Shaheed ya wuce. Daga waje yake jin muryar Tauhidat da Shaheed ɗin suna ta faɗa da yarensu. Laluben ya daga tsaya sallama ba ya ce "Anyi hatsari a waje." A tare suka juyo da sauri suka ce "hatsari?" Ya ɗan duƙar da kai "mota ta kaɗe babanku." Shaheed ne ya fara bangaje shi ya fita Tauhidat tana take masa baya. Kafin su fito ashe magana ta karaɗe gidan. Kowa ya fito harda Alh. Audi kuwa da matansa. Shamsu da Susu ne kaɗai basu san me ake ciki ba. Suna fita ana saka shi a motar wanda ya buge shi zasu tafi tare da Mammalo. Motoci biyu suka gani ɗaya Haj. Manga da Fanna ne a baya tare da direba sai kuma wadda Alh. Audi yake ciki. Su biyun suka ɗuru a ta su Haj. Manga suka bi bayan waccan motar. Jina-jina aka fito da Papa Abayomi ko motsi ba ya yi aka shiga dashi cikin asibitin. Shaheed da yake namiji kukansa kaɗai ake ji a inda suke tsaye. Tauhidat kuwa banda kaɗawa da idanunta suka yi babu ɗigon hawaye ko kaɗan a idonta. Ta kasa tunanin komai sai addu'ar Allah Ya tashi kafaɗun mahaifinta. Matsayin Alh. Audi da yadda ya yi ruwa da tsaki a wurin yasa ake bawa Papa Abayomi duk wata kulawa da ta dace. Bayan awa guda likitan ya fito ya yi musu bayanin cewa ya sami karaya a ƙasusuwan ƙirjinsa guda huɗu sai buguwa. "Surukina ne doctor saboda haka kayi masa duk abinda ya dace." Cewar Alh. Audi. Wani irin kallo Haj. Manga ta yi masa sannan ta ɗauke kai tana sauraron bayanin Mammalo da mai mota. "Ganinsa kawai muka yi ya fito yana tafiya kamar ba ya cikin hayyacinsa. Ban kawo akwai matsala ba da tuni na bi bayansa." Inji Mammalo. Mai motar kuma ya faɗa musu yadda ya dinga yi masa horn da ƙoƙarinsa na kauce masa. Duka bayanan nasu Haj. Manga ta alaƙantasu da maganganun da suka yi ne da Alh. Audi. Idan kuwa hakane ya zama wajibi ta gano me suka tattauna wanda bata ji ba. Wace irin magana ce ta fitar da Papa Abayomi daga hayyacinsa har wannan tsautsayi ya same shi? Likitan ne ya sake dawowa ya nemi a nuna masa Tauhidat. "Ga ta nan." Fanna ta nunata da guntun hawayenta na tausayinsu. "Ki shigo yana son magana dake kafin muyi masa allurar bacci." "Ni fa?" Shaheed ya miƙe da sauri yana bin bayanta "bai ce a kira Shaheed ba? Fushi yake dani ko?" Ya ce da ƙaramar murya yana ƙara fashewa da kuka. Tauhidat bata kula shi ba ta shiga ciki. A kwance ta tarar da mahaifinta an naɗe kansa da ƙirji da bandeji. Gaban gadon ta matsa zuciyarta na wata irin bugawa. Tana riƙe hannunsa ya saka dan ƙarfinsa ya janyota yadda za ta ji abinda zai ce. "Biro, takarda" ya ce da ƙyar. Da gudu ta fita sai ganinta suka yi ta kalli hagu ta kalli dama ta rasa ina za ta bi. Shaheed yana tambayar ko baban nasu ya buƙaci yaje ta wuce shi zuwa reception. Mace ta gani tana rubutu a jikin wani form ta fizge biron tare da form ɗin ta juya da sauri ko kiran da suke mata bata ji ba. Ɗakin ta koma ta saita kunnenta a bakinsa bayan ta faɗa masa cewa ta samo. "Jamal." Da mamaki ta kalle shi "Jamal zan rubuta?" Ya gyaɗa kai sannan ya ce, "Daji." Jikinta ne ya yi sanyi ta fara tunanin ko dai kansa ya tabu ne sakamakon buguwar da ya yi. Maimaita kalmar daji ya yi da ƙyar sai ta rubuta ta a kasan Jamal ɗin. "Falgo. Daji Falgo" ya sake cewa da alamun tunani. Ya kasa tuna kalmar sosai amma akwai falgo a ciki. Haka nan ta rubuta tana jin tashin hankalinta na ƙaruwa. Ina za ta saka kanta idan Papa ya sami matsalar ƙwaƙwalwa? Katse mata tunani ya yi taji ya ce, "Alhaji babban sirri." Sai yanzu ta soma samun nutsuwa da taji ya faɗi sunan Alhaji wanda ta gane Alh. Audi yake nufi. Shiru taji ta ɗago kai tana jiran ya cigaba da magana sai ta ga idanunsa sun kakkafe. "Papa?" Ta ce jiki na rawa. Buɗar bakinsa sai ganin jini ta yi yana fitowa harda guda-guda. A take zuciyarta ta tsinke ta zauna akan gadon ta ɗora kansa a cinyarta. Dakewa ta yi ta soma abinda ya kamata cikin ƙarfin hali. "Papa ka ce La'ilaha Illallah." Ya sake buɗe baki sai wani jinin ta baki ta hanci. "La'ilaha Illallah." Sai da ya yi tari jini mai yawa ya fito sannan ya iya maimaitawa. Bata barshi haka ba ta cigaba da faɗa da ƙarfi tana shafa ƙirjinsa da ta kula kamar daga nan yake jin ciwo sosai. Daga waje Shaheed da sauran suka ji muryarta. Shi dasu Haj. Manga da sauri suka shigo. Yanayin da suka riske shi ya tayar musu da hankali matuƙa. Shaheed ya kama hannunsa yana hawaye sosai. "Papa ka yafe min ka tashi wallahi ko ƙauye ka ke son na koma zan je." Murmushin ƙarfin hali Papa Abayomi ya yi ya ɗan matse masa hannu. Tauhidat bata bar laƙƙana masa kalmar shahada ba sai Haj. Manga da Mammalo suka bi sahunta. Fanna da Shaheed dai sai kuka. Likitoci biyu ne a ɗakin amma sun tsaya a gefe saboda sun san cewa babu sauran abinda zasu iya yi masa sai jiran lokaci. Ƙashin ƙirjinsa daya da ya karye ya shige cikin huhunsa da matuƙar wahala ya tashi ko anyi aiki. Alh. Audi yana bakin ƙofa ya kasa haɗa ido da Papa Abayomi. Jira yake kawai ace ya cika ko hankalinsa ya kwanta ya rage guda cikin matsalolinsa batare da ya saɓa zancen Oga ba. Ƙarfin riƙon da Papa Abayomi ya yiwa Shaheed ne ya sassauta ya soma kiransa da ƙarfi tare da jijjiga shi. Idanu a birkice Tauhidat ta riƙe masa hannu tana girgiza kai, "Allah Ya karɓi abinsa Broda. Ka samo mota mu tafi Abeokuta." "Nooo, Doctor do something (A'a, likita kayi wani abu mana.)" Ya ce a gigice yana janyo likitan. Mammalo ne ya ja shi gefe shima kukan yake sosai, "Kayi haƙuri, Allah Ya jiƙan Fafa." Fanna waje ta yi tana kuka ta faɗawa mai motar wanda ya gama rikecewa da ya ga sun shige ciki su duka. Haj. Manga idanunta akan Tauhidat da ta gyarawa gawar mahaifinta kwanciya ta rufe shi da zanin gadon. Shikenan cikin abinda bai kai awa uku da zuwansa garin ba ya tafi kamar yadda Baffa ya yi. Jikin bango ta jingina tana kallon yaran da ko taƙi ko taso sun zama amanarta sannan ta koma ta kalli Alh. Audi da ya kasa ɓoye nutsuwar da rasuwar ta kawo masa. Ko gida basu koma ba daga asibitin Tauhidat da Shaheed suka kama hanya a motar asibitin. Mammalo dasu Haj. Manga da suka koma gidan suma a ranar suka ɗauki hanya don duka duka ko ƙarfe uku bata yi ba lokacin. Da tursasawar Alh. Audi Shamsu ya shirya ya bishi. Susu kuwa duk da jikinta ya yi sanyi saboda mutuwa ba abin wasa bace, amma ko da wasa bata jin za ta iya taka ƙafafunta a garin yarbawa a cewarta. *** A cikin kwanaki biyu da rasuwar Papa Abayomi ko sau ɗaya Tauhidat bata zubar da hawaye ba, kuma bata runtsa ba. Ita ce mai bawa mutane haƙuri idan suna kuka. Idan anci abinci ta tattara kwanuka ta share wurin ko ka ganta tana janyo ruwa a rijiya za ta yi wanke-wanke. Duk wani abu da zai ɗauke mata hankali shi take yi. Idan dare ya yi kowa ya kwanta sai ta ɗauko takardar nan da ta rubuta a asibiti ta yi ta bita kamar karatu tana son gano ma'anar kalmomin. A rana ta uku Shaheed ya kirata gefe ya zabge gabaɗayansa. Hannuwanta ya riƙe ya na kuka. "Tosin rayuwata bata da wani amfani. Papa ya rasu yana fushi dani. Kema na san ba za ki taɓa yafe min ba saboda baƙincikina ya kashe mana uba." Sakin fuska ta yi, "Broda ka dena faɗin haka Papa ya yafe maka." Dariyar farinciki ya yi mai ɗan sauti ga wani hawayen kuma ya ƙanƙameta, "kin tabbata? Kafin na shigo ɗakin ya faɗa?" "Ba da baki ya fada ba amma na sani Papa ba zai taba riƙeka a rai ba." Murmushinsa ne ya ɗauke, "tunda bai faɗa ba nasan cewa tawa ta ƙare." Rungume shi tayi tana bashi baki kamar uwa da ɗanta. A lokacin yaji a ransa ya tsani komai da ya danganci Alh. Audi da iyalansa. Zai nemi aiki batare da taimakonsa ba kuma in sha Allah sai ya san duk wata hanya da zai bi ya kashe auren ƙanwarsa da Shamsu. Akan idon Haj. Manga suka yi komai duk da ba ta jin yaren amma ta gane rarrashin yayanta ta yi. Duk inda Tauhidat ta yi tana biye da ita batare da ta sani ba. Tsoro take ji kada wani mugun abu ya sameta saboda yadda take kullewa kowa damuwarta. Danginsu na uwa da uba kowa yana ta ƙoƙarin kyautata musu amma cikinsu tafi kowa sanin wace ce Tauhidat. Bayan fitar Shaheed dakin ta shiga ta sameta zaune a kasa ta zubawa ƙofa idanu kamar mai jiran wani ya shigo. Tana ganin Haj. Manga ta tashi da sauri. "Nanna kina son wani abu ne?" Ta yi hanyar fita. "Dawo Tauhida." Da kuzarinta ta dawo musamman ta taji kiran irin wanda ta daɗe bata ji bane mai cike da soyayya da kulawa. A gabanta ta zauna tana jiran ta ji abinda za ta ce sai ta miƙa mata wayarta. Sai da ta ɗaga kai suka haɗa ido sannan ta karɓa ta kara a kunne. Muryar Jamal taji yana kuka sosai. A hankali tayi masa sallama. "Ƙanwata", ya ce wani kukan yana taho masa. Ba ƙaramin tausaya mata ya yi ba. Shi ma mutuwar ta doke shi haka bare ita ƴar cikinsa. "Kayi haƙuri addu'a zamu yi masa ba kuka ba." Ta'aziyya ya yi mata tausayinta yana ƙara shiga zuciyarsa. Tana ji ya ce, "Arƙam ga Tauhida." Ƙirjinta a take ya cure zuciyarta da hannuwanta suka soma rawa. Da farko kamar ba zai karɓi wayar ba saboda ya riga ya sakawa ransa cewa yanke kowace irin alaƙa da ita shi ne maslaha a gare shi. Matsayin uba da irin labaransa da ya sha ji daga Nanna, Jamal da ita kanta Tauhidan yasa shi daurewa ya miƙa hannu ya karɓi wayar. Cikin nutsuwa ya dinga magana ta kasa amsawa sai kai da take gyaɗawa kamar yana ganinta. "Everytime we lose someone dear we feel empty and lost. But remember death is a sign of the existance of a better tomorrow for true believers. For as long as you live always include them in your prayers after each salat. Allah Ya gafarta masa" "Amin, nagode." Da sauri ya bawa Jamal wayarsa bayan ya ji amsarta ya bar wurin saboda yanayin da yake neman taso masa. Kalmomi biyu kawai yaji daga gareta amma ya tabbata sun fito daga wurin wadda zuciyarta ta kai maƙura wurin rauni ce. Babu abinda take buƙata a wannan lokacin sama da masoyan da zasu kwantar mata da hankali. Amma tunda tana da miji damuwa akan halin da take ciki ba huruminsa bane ya tunatar da kansa. Kai a kasa ta miƙawa Haj. Manga wayar tare da yi mata godiya. Maimakon ta janyo Tauhidat a jikinta kamar yadda take muradi , sai ta saka hannu ta shafa kumatunta. Abubuwan da suka faru a kwanakin nan sun ƙara tsoratar da ita akan Alh. Audi tana tsoron kada ya gane tana kusantarta ya cutar da ita. Lumshe idanu Tauhidat ta yi, ta ƙara kwantar da kanta a jikin hannun da take kewa. Su duka biyun suna azabtuwa da layin da Alh. Audi ya shata musu. Haj. Manga ce ta yi ƙarfin halin cewa, "Tauhida danne damuwarki ta hanyar nuna kamar babu abinda ya faru ba zai goge halin da ake ciki ba. Allah Ya karɓi ran mahaifinki ba zai dawo ba har duniya ta naɗe. Taurin zuciyarki akan wannan babban tashin hankalin cutarwa ne a gareki. Ki yi kuka, ki bar hawayenki su sauka ko zaki samu salama a cikin ranki." Da murmushi ta ɗago kai suka haɗa ido, "Nanna ina kuka ga wadda bata da mai share mata hawaye? Waye zai fahimci abinda nake ji a zuciyata? Bani da kowa Nanna..." Idanu cike da hawaye Haj. Manga ta ce, "kina da Allah, kuma shi kaɗai Ya isar miki akan kowa da komai. Kina da Sarkin da Ya halicci mutum da aljan, mai hanawa mai bayarwa, mai rayawa mai kashewa ashe baki yarda share miki hawaye Ya maye miki gurbin kukanki da dariya abu ne mai sauƙi a gareShi ba?" Kukan da take ta ɓoyo a zuciyarta ne ya fashe lokaci guda ta ce, "na yarda." "To ki fawwala masa duka lamuranki ki zuba ido ki jira sakamako." Cewar Haj. Manga kuma da wannan kalaman ta fita daga ɗakin kafin nata kukan yaci ƙarfinta. A wurin Tauhidat ta zube ta rungume ƙafafunta, kanta a tsakiyar cinyoyinta ta dinga kuka tana kiran sunan Allah. Tabbas kuka ma aya ce daga cikin ayoyin Allah da Ya sanya sauƙin zuciya ya biyo bayan wanda ya yi shi. Da Haj. Manga ta fita Shaheed ta tura ɗakin ta ce masa Tauhidat na nemansa. Ta yi musu haka ne don su rarrashi juna su kuma rungumi juna domin duk wanda zai so su ya kyautata musu ba kamar su yiwa junansu bane. Yana shiga ya ganta a wannan yanayin sai shi kuma Allah Ya sauko masa da ƙarfin zuciyar da ya rasa tun ranar da akayi rasuwar. Kusa da ita ya zauna ya rungumeta a gefensa ta yi kuka mai isarta bai ce ƙala ba. Can yaji kukan ya tsagaita sai saukar numfashinta da ajiyar zuciya alamun ta samu bacci. Gyara zama ya yi ya ɗora kanta a cinyarsa yana tunanin rayuwar da zasu fara babu uwa babu uba. Ba ya jin kansa a matsayinsa na namiji amma ita fa? Tunda suka zo ko sau ɗaya bai ji ko ya gani ance mijinta na nemanta ba bare a kai ga batun rarrashi. Yana zaune cikin maza a waje amma dayake ba kowa ke jin hausa ba kusan shi kaɗai ya fahimci wayar da yake wuni yana yi da Susu. Daga tambayar ya jikinta sai ta lafiyar bebin su. Sai kuma ƙorafi akan kullum yana canza hotel da sassafe saboda kada a gane ga rashin isasshen bacci. Bai san meye baya son a gane ba shi dai kawai ya san ƙanwarsa bora ce wadda ake zaman dole da ita. Samun aiki da nema mata saki domin su nesanta kansu daga wannan iyalin shi ne babban kudurinsa a yanzu. *** Dawowarsu Abuja da kwana ɗaya bayan sati biyu da rasuwar Tauhidat ta tattara ta koma makaranta. Da ta haɗu da Susu a bakin bene ta yi mata gaisuwa bata nuna jin haushi ko ɓacin rai ba, ta amsa ta wuce. Karatunta ta saka sosai a gaba tana ƙara godewa Haj. Manga da ta zaɓar mata wannan cos ɗin. Shamsu da Susu su kaɗai suke bidirinsu ko a jikinta. Daidai da rana ɗaya bata taɓa jin wani abu mara daɗi game da rashin kulata da yake ba. Da zasu ɗore a haka da tafi kowa jindaɗi. Ko babu soyayyar Arƙam da take yaƙar zuciyarta don ta dena tunaninsa to fa ko don Alh. Audi ba za ta taɓa ƙaunar ɗansa ba. Karatu take tuƙuru saboda ma kada ta dinga samun damar tuna wanda ya yi mata nisa kuma ya haramta a gareta. Shi ma Shaheed kayansa da na mahaifinsa wanda ya yi masa tsaraba akwati biyu manya yazo ya kwashe. Ranar da zai koma Abeokuta Alh. Audi ya aika aka kira masa shi. Takarda ya miƙa masa sai ya ga ya noƙe hannu babu niyyar karɓa. Sakin fuska ya yi ya sake miƙa masa. "Offer ɗinka ce na fasa nema maka aiki a ma'aikatar da ta danganci karatunka, ranar Litinin ka yi reporting a babban reshenmu na nan." Hannuwan Shaheed har lokacin suna bayansa ya ɗan rissina kansa,"nagode Alhaji amma ba zan karɓa ba. Gida zan koma yau ɗin nan ma" "Haƙiƙa rashin uba da ciwo amma Shaheed rayuwa dole taci gaba. Idan kana buƙatar sake hutawa da samun nutsuwa kaje gidan ka dawo wani watan." "Ba haka bane Alhaji. Nagode sosai da ka ɗauki nauyin karatuna amma ba zan so ace komai sai anyi min ba. Zan nemi aikin da kaina a can garinmu." Kallon mai taɓin hankali Alh. Audi ya dinga binsa dashi. Banda hauka ace kamar shi da mutane suke rububi da kwaɗayin samun aiki a ƙarƙashinsa ya bada offer aƙi karɓa? Wani tunani ne ya yi ya ce da shi "Idan kafi son aikin a kusa da gida sai kayi a kamfanin Lagos ko Onitsha. Kaje kayi tunani babu garaje." Godiya kawai ya yi ya fita saboda kada ayi ta jan maganar ma. Matan gida yabi ɗaiɗai ya yi wa sallama yana rayawa a zuciyarsa cewa daga yau ya bar gidan har abada ya fita. *** Cikin Susu ya kusa cika watannin haihuwa, dan haka taketa shiri ba kama hannun yaro. Lokaci ɗaya ta tafi Dubai siyayyar kayan jarirai ita da Fanna. Ba haka dai taso ba amma tunda Shamsu ya dage ba zai je ba sai suka tafi tare saboda zasu hutu da yaranta. Siyayya ta yi tamkar mai buɗe shago saboda kuɗi kam yanzu bata san babu ba akansu. Satinsu ɗaya suka wuce England nan ma ta lodo kaya sosai suka koma gida. Saɓanin yadda masu kuɗi suka saba zuwa turai musamman [2/23, 7:34 PM] Nasma: *** Tuƙi Shamsu yake yi amma ko kaɗan hankalinsa ba ya kan titin. Kallon soyayya yake bin Susu dashi ya kasa mallakar nutsuwarsa. Yana ji a ransa ko bai warke ba wannan yarinya za ta zame masa matar rufin asiri. A ce mace kamar wannan ta san matsalarsa, kuma duk da haka bata guje shi ba shi kuwa meye ba zai yi mata ba na kyautatawa? A ɓangarenta kuwa banda bugun zuciya babu abinda take yi har suka isa. Bata san yaya zasu ƙare ba tunda ya ce zai gabatar da ita ga mahaifinsa ne. A can gidansu kuma ta tabbata yanzu ana faman nemanta, gashi duhun dare ya gabato. Ga ta ga gate ɗin Karam Mansion a karo na biyu a rana ɗaya. Tsoron da take ji kasa ɓoyuwa ya yi da Shamsu ya tura hancin motar ciki. Yawu take ta haɗiya har ta kai matakin jin kamar ya ƙafe babu saura sai busasshen baki. Da ya gyara parking suka fito, sai da ya kira sunanta sau biyu ta ankara da jiranta yake yi. Hanci ta baza tana shaƙar daddadar iska. Ƙyanƙyami gareta da son ƙamshi, shi kuma tun tahowarsu da ya rufe gilasan ya kunna AC iskar motar ta sauya. Satar kallonsa ta dinga yi ko za ta gano silar ɗan hamamin da tsadaddun turarukansa basuyi nasarar ɓoyewa ba. Da ta dawo hayyacinta idanuwa ta shiga baiwa abinci. Motoci ne a wurin kamar ta shiga wurin sayar dasu amma na alfarma ba karabiti ba. Ko shafasu kaɗai ta sami damar yi kafin a korata gida ta san cewa a duniya dai ta ƙure ƙaryar kuɗi. "Mu shiga ciki don a yau nake son ayi a gama komai." Taji muryar Shamsu a kusa da ita. Sai da ta kalli gidan taji cikinta ya bada wani irin sauti sannan ta ce, "Ko dai na jira a nan ka je ka dawo?" "Tare zamu ki yi masa bayani da kanki." Bai jira amsarta ba ya kama hannunta suka nufi ƙofar shiga. Hannuwansu da ke haɗe ta kalla ta jinjina kai. Duk taɓararta bata tashi da ɗabi'ar sakarwa maza jikinta suna taɓawa ba. Shamsu daga haɗuwarsu ya taɓata yafi sau biyu sai taji zuciyarta ta ɗan sosu. Ba don da manufa tazo ba kuma ɗan gidan Alh. Audi bane da sai ta wanke shi da mari. *** Tun lokacin da Haj. Manga ta yi wa Alh. Audi magana, akan babu ruwanta da kowa kuma babu ruwan kowa da ita bata sake saka Tauhidat a ido ba. Idan kaga ta shiga ɓangaren masu gidan dama kira ne daga Fanna. Kiran ba ya wuce akan shirin bikin da aka ɗora mata nauyinsa. Yawanci a ɗaki take samunta ta faɗa mata abinda za ta faɗa, ta tashi da kalmar 'to' kawai. Ɗazu da suka fita da Shaheed wanda musamman Alh. Audi ya kira shi saboda biki gwajin ɗinkunanta taje yi. Kayan da farko Tauhidat size ɗin kayanta ta bada taƙi zuwa a gwadata. Da suka je ta saka a wurin duk sunyi mata burum saboda ramar da ta yi. Maiɗinkin irin wayayyun matan nan ce mai yi wa masu kuɗi ɗinki. Tana ganin yadda take yawo a cikinsu ta ce zasu rage a ƙara matsesu. Fuska a cukule Tauhidat ta ce, "Ki barsu haka nake so." "Ba za kiyi kyau a ciki ba." Matar ta ce cikin damuwa. Idan aka nuna kayan a matsayin nata kuma amarya bata yi kyau ba ai taci baya. "Haɗa min kawai in tafi ana jirana." Duk roƙo da magiyar matar nan bai sa ta amince ko inci ɗaya an rage a kayan ba. Na farko dai bata ga wani yawa da suka yi na tashin hankali ba. Abu na biyu kuma ko da wasa ta saka irin wanda ake so ɗin masu bin jiki kamar a nan aka ɗinka bata jin Nanna za ta yafe mata. Ta tarbiyantar da ita ne akan doron koyarwar addini, ba sangarta da son burgewa saboda kuɗi ba. *** Bayan Magariba tana zaune jigum a ɗakin da ya zama nata yanzu, wayar Fanna ta shigo mata. Kiranta ta yi da ta taho da kayan da ta karɓo. Bata kawo komai a rai ba ta yafa mayafi akan abayarta ta ɗauki ledojin kayan wanda Fanna ɗin ta gani ɗazu ta yaba kafin ta umarceta ta kai ɗaki ta ajiye. Kafin a amsa sallamarta idanunta suka sauka akan Haj. Manga tana zaune da kofin shayi a hannunta. Zaman jiran Alh. Audi da ya ce su jira shi yana son ganinsu ita da Fanna ta yi. Ba don haka ba da tana ɗaki tana bibiyar aikin ginin makarantar ta. Zuciyar Tauhidat sai da ta yi tsalle saboda kwana biyu basu haɗu ba. Duk da idan ta gaisheta yanzu bata amsawa amma bata karaya ba ta je gabanta ta gaisheta. Kai kawai ta ɗaga yayinda zuciyarta ta ƙuntata. Tauhidanta ta rame sosai, kamar wata mara lafiya. Yanzu shi Abayomi ganin ƴarsa a wannan halin shi ne farincikinsa tunda ya zama surukin Alh. Audi? "Ashe abinda ki ka yi a wurin ɗinkin kenan Tauhida? Yanzu ta kirani ta sanar dani cewa kayan sunyi yawa ashe harda buba ki ka sa aka ɗinka don wulaƙanci. Tun muna shiri da juna gobe ki koma a gyarasu." Suka tsinci muryar Fanna a kunnuwansu. Kai ta ɗan sunkuyar don babu niyyar canjawar ta ce, "Anti ba wani yawa ita so take su matseni ne kawai." Kallon sakarai Fanna ta jefa mata, "ji min sokonci, ba haka ake ɗinkunan amaren ba? Kada ki manta ba taro ne na yaku bayi ba. Manyan mutane daga ƙasashe zasu zo bikin nan. So ki ke ki kunyata Alhaji ace surukarsa ƴar ƙauye ce ko me?" "Don Allah Anti a barsu haka." Ta ce kamar za ta yi kuka. "Tashi ki gwada na gani. Shiga can ki saka ɗaya daga cikin dogayen rigunan." Ta nuna mata wani wuri mai ƙofar gilas a cikin falon. Jiki ba kuzari ta ɗauki leda ɗaya ta wuce. Bata daɗe ba ta dawo ta tsaya daga gefe tana satar kallon Haj. Manga. Ita kuwa sai ta ɗauke kai kamar bata kula ba. Fanna na ganin yadda wurin kwankwason da gaban kirjin basu dameta ba ta hau sababi. Tana da son a ƙure gayu sannan bata son abinda zai sa Alh. Audi nadamar sakar mata ragamar bikin nan ko kaɗan. Ba ƙananan kuɗaɗe take caska ba tun farkon shirin. "Hajiya na san ke da ƴar taki yanzu ba shiri ku ke ba, amma don Allah tayani gani. Abu na taron ƴan kwanaki saboda Allah yarinya tana neman watsa min ƙasa a ido." Idan kofin gaban Haj. Manga ya juya to ita ma ta juya. A ganinta tunda anyi auren yaci ace Haj. Manga ta ajiye komai ta kula da Tauhidat indai da gaske ƴa ta ɗauketa. Ana haka Alh. Audi ya shigo sanye da jallabiya da carbi har gwiwarsa kamar gaske. Tauhidat na ganinsa ta rufe jikinta da mayafi. Fanna ta daure fuska "Meye haka, come on buɗe ya gani don ma kada a ɗora min laifin a gaba." Tauhidat sake riƙe mayafin ta yi tana rarraba idanu. Hakan ya hasala Fanna ta soma faɗa tare da miƙewa za ta cire mata da kanta. Tana ɗora hannu kamar an ce ta juya suka haɗa ido da Haj. Manga. Kallon da ta watsa mata na gargaɗi ne yasa ta koma da baya ba shiri. Tauhidat ta ga kallon har ya yi sanadiyar zubowar ƙwalla daga idanunta ganin har yanzu ashe tana ƙaunarta. A nata ɓangaren kuwa duk fushinta da Tauhidat bata jin tana da ƙarfin halin ganin an tozarta ta musamman a gaban Alh. Audi kuma ta ɗauke kai. Kayan Tauhidat ta duƙa tana haɗawa Shamsu ya shigo a gadarance babu neman izini bare sallama. Sai da ya iso tsakiyar falon ya kula Susu bata biyo shi ba. Komawa ya yi ya kamo hannunta suka shigo tare. Nan kallo ya koma kansu ana jiran ƙarin bayani. Kan Susu a ƙasa taƙi ɗagowa tun kallon da ta yi wa Tauhidat daga bakin ƙofa da ya sa ta komawa da baya. Bata zata a gidan za ta sameta ba sannan yanayin da ta ganta ta shammaceta. Da wannan kyakkyawar fuskar ma'abociyar yawan fara'a da ta fara janta gareta shekarun baya ta yi tozali. Hannuwansu dake sarƙafe da juna Alh. Audi ya zubawa idanu rai a ɓace ya ce, "Shamsu meye ma'anar hakan?" "Baba matar da zan aura ce ranar Asabar." Haj. Manga da Fanna gabaɗaya maganar ta girgiza su. Tauhidat kuwa kayan ta kwashe ta yi hanyar fita da sauri. "Ku bamu wuri" Alh. Audi ya nunawa matansa ƙofa cikin fushi kamar ya tashi ya shaƙe Shamsu. "No su tsaya fa suyi shaida" Cewar Shamsu har lokacin yaƙi sakin Susu "gara da Allah Yasa suke nan ma. Na yarda na auri wadda ka ke so ni ma ka amince na auri wadda nake so." Runtse idanu Alh. Audi ya yi yana karkaɗa ƙafa. Idan bai yi haka ba yana ganin zai iya illata gudan jininsa. "Bana son rashin hankali. Ka mayar da ita inda ka samota kazo muyi magana." Murmushi Haj. Manga ta yi daga inda take zaune tana kallonsu. Wato duk yadda take kallon al'amarin gidan nan ya wuce nan. Shamsu shafawa idanunsa toka ya yi ya ce "Baba gara ma ka amince don abinda yasa ka aura min waccan yarinyar da bana so shi ne yasa ni son auren wannan. Ta yi min bayani sosai kuma na yarda ita ce maganin..." "Shamsu!!!" Alh. Audi ya ce da ƙarfi a ƙoƙarin hanashi faɗin abinda zai tona musu asiri. Gajeriyar dariya Haj. Manga ta yi wannan karon. Ba tun yau take zargin uba da ɗan suna ɓoye wani abu da basa son kowa ya sani ba gashi kuwa ta ƙara ganin dahir. Tashi ta yi abinta sai da ta iso kusa dasu ta ce,"amarya barka da zuwa. Ya ya sunanki?" "Suwaida." Ta ce a hankali jikinta na karkarwar fargabar me zai faru. Sai da ta amsa ta ɗago kai domin ganin wace ce wannan da muryarta kaɗai ta kiɗima tunaninta. Tana kallon Haj. Manga ita kuma Tauhidat ta kalleta. A take taji wani abu ya soki zuciyarta. 'Senior Susu' ta ce a zuci cike da matuƙar mamaki. Ko a mafarki ba za ta taɓa manta wannan fuskar ba. A guje ta tabi bayan Haj. Manga. Susu ta yi guntun murmushi kai a ƙasa duk da tana mamakin wace irin makanta ce tasa Shamsu yake cewa ba ya sonta. Ita mace ma duk hassadarta ta san cewa Tauhidat ta kai duk inda ake son mace. Ko kusa baza ta haɗa kai da ita ba. A ƙofar ɗakinta ta iske ta da sauri ta kama hannunta ta riƙe tana ambaliyar hawaye. "Nanna kin tuna lokacin da muka fara haɗuwa? Maami ta rasu ranar da wata senior a hostel ɗinmu ta sakani a kasan gado yin ƙwai." 'Ina zan manta da Susu ɗin da hatta Jamal da Arƙam sun riƙe sunanta?' A fili kuwa gira kawai ta ɗaga mata. Bata ji komai ba saboda halin da ta shiga na ruɗewa ta ce, "Ita ce Shamsu ya shigo da ita." Da ƙyar ta iya ɓoye nata tashin hankalin da mamaki ta ce, "Kina so na koma na hana mijinki aurota ne?" Girgiza kai Tauhidat ta yi da sauri sai ma rawar da jikinta yake yi, "A'a Nanna amma ya zanyi?" Ji ta yi kamar ta rungume ta a lokacin ta faɗa mata cewa ba Susu ba, ko danginta ne kaf basu isa su sake tabata ba matsawar tana numfashi amma ta kasa. Tauhidat ba ƴarta bace kamar yadda Abayomi ya nuna mata iyakarta. Ita auren ma ba shi bane ɓacin ranta kamar wanda ya aurawa da wannan furucin nasa na ta sake uba. Duk da haka ba za ta iya juya mata baya ba a halin da take ciki. "Idan kin so ki ƙarfafi zuciyarki kada ki yi kuka domin idan ki ka yi kuka za a ga gazawarki. Idan aka ga gazawarki kuma za a raina ki." Daga haka bata ƙara cewa komai ba ta shige ɗakinta barta a tsaye tana share hawaye. Kukanta ba na kishi bane don babu wani abu mai kama da so tsakaninta da Shamsu ko ɗigo. Haka kawai ace duk matan duniya amma ya rasa wadda zai kawo yana neman a aura masa kwana biyar kafin a soma bikinsa sai Susu? Bayan fitarta da ido Alh. Audi ya sallami Fanna ta fita ba don rai na so ba. A bakin ƙofa ta laɓe saboda ta sami labarin kaiwa mahaifinta. Tana daga wurin ta ji duka bayanin da Shamsu ya yiwa babansa wanda ya ɗaure mata kai. To wannan wace irin lalura ce? Ashe Tauhidan ma saboda neman magana aka aura masa. "Baba nafi yarda da Malamin da ya tsaya akan Suwaida da aljanun suka tashi akan wanda ya faɗa maka auren waccan ne maganin a Cameroun." Abinda zuciyar Alh. Audi take yi yafi ƙarfin tafasa. Ji yadda Shamsu yake ta ɓarin baki a gaban wannan yarinyar. Yana kallon idanunta ya gano ƙarya take musu sai dai bashi da masaniyar inda taji labarin ciwon. Alh. Ari kuma ko da wasa ya sani ba zai fitar da maganar ba bare ya turo wata. To amma abinda ya hango shi ne tunda taji maganganun nan gara ya bari ayi auren kada ta watsa sirrinsu a waje. Idan ma tana da manufa ko turen maƙiya ce duk babu matsala zai ci kakaninsu ne la'ada waje daga ita har su. Sannan ko babu komai tunda ita ta kawo kanta za ta jurewa lalurar Shamsu. Uwa uba zai sami matar da za ta ɗauke masa hankali daga neman Tauhidat da wani abu. "Fita zanyi magana da ɗana" Ya ce da ita a kausashe ko kallonta bai yi ba. Fanna na jin haka ta bar wurin da sauri , Susu kuma tana fita ta maye gurbinta na labe. Abinda Shamsu ya ce ne yasa ta riƙe baki. "Ita waccan ɗin ko ka manta ne na saketa tun ranar da ka sanar dani auren?" "Na kuma fada maka akwai igiya biyu saura ba." "Baba na san ba wani ilimin addini gareka sosai ba. Irin wannan sakin fa babu gyara saboda babu idda." Alh. Ari ne ya sake faɗo masa a hasale ya ce, "ni kake faɗawa haka? Wane maƙaryacin ne ya baka wannan fatawar?" Shamsu ya yi murmushi, "wani limami na tambaya saboda ina son jin ko akwai yadda zan ƙarasa sakinta cikin ruwan sanyi ba tare da kayi faɗa ba." "Ita wannan yarinyar da ka kawo na tabbata baka santa ba." "Eh amma dai tafi wadda bata san cewa ita ba matata bace. Kaga Baba ka amince min kawai ko na kira waccan ɗin na faɗa mata gaskiya. Na san kana da wani dalilin na aura min ita ƙila saboda matarka. To zan cigaba da riƙe maka ita nima a bani wadda nake so." Tsayin minti goma kafin Alh. Audi ya ce ya kira Susu. Saurin matsawa ta yi can gefe guda ta sunkuyar da kai. Abinda bata sani ba shi ne wannan tsayuwar laɓen a idanun Haj. Manga da Fanna ta yi. Dukkaninsu sun ga yadda ta daɗe da kunne manne da ƙofa da kuma saurin canja wurin tsayuwa lokaci guda har Shamsu ya fito suka koma ciki tare. A ƙasa ta zauna Alh. Audi yana yi mata tambayoyi game da asalinta. Bata ɓoye komai ba sai ma nunawa da ta yi ita ɗin ba ƴar kowa bace. Tambayar ƙarshe da ya yi mata ta tsorata ta da ya ce, "Me yasa ki ka zaɓi auren wanda baki sani ba akan ki yi wa iyayenki biyayya?" Hanci ta ja ta goge wata munafukar ƙwalla. Da ladabin da bata jin ta taɓa yiwa kowa makamancinsa ta bashi amsa da cewa, "Nima ban sani ba Baba. Haka kawai zuciyata take ingizani da taimakon mai neman taimako." "Idan na faɗa miki cewa Shamsu ba jinina bane kuma bashi da gadona zaki iya aurensa?" "Haba Baba!" Shamsu ya furta cikin ɓacin rai. Murmushi ta yi ta ɗago kai a hankali, "idan bashi da kowa da komai zan zauna dashi saboda abinda ya kawoni gare shi ba dukiya ko neman suna bane." 'Shegiya kin kama kanki. Ashe akwai ranar da zan haɗu da mai zalama irina? Shamsu ka yi dace don irin wannan ce kaɗai za ta iya rufa maka asiri ta zauna da kai saboda kuɗin ubanka' ya ce a ransa yana ƙare mata kallo. Fanna ya kira ya ce a bata masauki da abinci sannan ta shirya gobe da sassafe zasu je Gombe. Yadda ya yi maganar babu wata kafa ko damar tambaya ko neman ƙarin bayani. Tana fita bayan ta umarci masu aiki da kula da baƙuwar ta garzaya ɗakin Haj. Manga ta faɗa mata duk abinda taji. "Hajiya idan kina fushi da Tauhida ne don an aura mata Shamsu ya kamata ki dena. Yarinyar nan tun bata tare ba ta koma abar tausayi." "Mahaifinta za ki faɗawa bani ba" Sakin baki ta yi kafin ta ce, "na zata kina da kirki fahimtarki ne ba ayi ba shi yasa na fara sonki. Amma da gaske baki da tausayi ko yafiya?" "Fanna yaushe muka yi sabon da za ki tunkareni da magana irin wannan ne?" Haushi Fanna taji ta fita harda gwara mata ofa. Tana ganin kofar ta rufe hawayen da take ta riƙewa tunda ta soma bata labarin suka sauko. Ko ba Arƙam ba ta yiwa duk wanda Allah Ya baiwa Tauhidat tanadin mace da zai bugi ƙirji ya ce ta fito gidan mutumci. Tarbiya, gyara, iya girki da duk wani abu da take jin zai sa a kira mace da tagari tun farkon haɗuwarsu take koya mata. Sai dai abin takaici ƙaddara ta gifta Tauhida ta faɗa inda bata da daraja da ƙima. Son zuciyar mahaifinta ya kaita inda duka abubuwan da ta koya mata ba lallai suyi tasiri tunda miji ba ya sonta kuma ya nuna a gaban wadda yake son aure. Maganar Baffa da ya taɓa ce mata ta dena saurin yanke hukunci da abinda ido kaɗai ya gani kunne bai ji ba ce ta faɗo mata. Abubuwa da dama sun faru kuma hannu yana nuni da makusantanta ake cutarta. Ji abinda Madam Zainaba ta yi mata akan Arƙam, ga Abayomi ga rasuwar Baffa a dalilin zuwa wurinsa. Kai, ɗauke kai daga lamuransu ya zame mata dole. Lokacin neman amsar abinda yasa ta kasa barin gidan nan ya yi kuma shi za ta saka a gaba. *** Tsalle Susu ta daka ta faɗa kan makeken gadon ɗakin da aka kira da masaukin baƙi. Wani ɓangare ne daban a cikin gidan aka kaita, mai ɗakuna kowanne da banɗaki. Wurin a gyare sai ƙamshin masu kuɗi kamar yadda ta ayyana a ranta. Sai yanzu da ta sami nutsuwa, komai yake dawo mata tiryan-tiryan. Wai yau ita Suwaida Musa ce ta zauna har ta yi magana da Alh. Audi da ɗansa kuma wai gobe zasu je neman aurenta. Matansa da ko a mafarki bata taɓa tunanin gani ba yau ta saka su a ido. Cikinsu babu ta yarwa, bare ma babbar wadda da alama ita ce uwargida. Iyayenta ne suka faɗo mata a rai, nan ta shiga tufka da warwara akan yadda gobe za ta kasance. Bata taho da waya ba dama saboda haka babu halin nemanta. Tana wannan tunanin taji an taɓa ƙofar ɗakin. Kafin ta dakatar da ko ma waye saboda daga ita sai tawul Shamsu ya faɗo. "Oh sorry, kaya na kawo miki" Ya ce babu niyyar komawa ko kauda kai. Ledar hannunsa ya ajiye ya sami wuri ya zauna. Ƙarshen takura da jin kamar an muzanta ta ta tsinci kanta da ji, saboda haka bai taɓa faruwa da ita ba. Wanda ta yi dominsa kuma ko a jikinsa sai ma godiya da yake yi mata na jajircewarta akan sa. Hammar ƙarya ta soma yi ya tashi ya yana cewa ta kwanta gobe fitar wuri zasu yi. Nufota ya yi ta ƙanƙame jikinta wani uban gumi na feso mata, saboda tashin hankali. Goshinta ya sumbata tare da shafa fuskarta. "Nagode Suwaida, ban san da bakin da zan nuna miki farincikina akan zuwanki ba." Da ƙyar ta haɗiyi yawu ta ce, "nima nagode sai da safe." Ba don ya daure ba, da ba zai fita daga ɗakin ba. Ganinta kawai da ya yi ya sa shi jin abinda bai saba ba. Ya daɗe da cire mata a ransa saboda sanin ba zai samu ba sai ga shi yau ya tsinci dami a kala. An tashi da hazo da iska mai ƙarfi washegari, babu damar tafiya a jirgi. Convoy ɗin motoci biyar da ta Alh. Ari cikon ta shida suka yi zuwa garin Gombe. Susu ta ma rasa me yafi burgeta da rayuwar masu kuɗi. Dukkansu suturun jikinsu babu na yarwa. Motocin kuwa ta tabbata guda ɗaya za ta sayi gidansu da motar babanta da baburan yayyenta su biyu. Ga wasu tiƙa-tiƙan maza wai bodyguards, irin abinda take gani a fim yau a gabanta. *** Gidan Alh. Musa babu wanda ya runtsa daren jiya. Tun safe suka farga bata gida aka yi zaton makaranta ta tafi amma shiru. Mama ta kira su Minasco suka ce basa tare. Zuwa yamma ita da Aisha da iyayensu hadda mazan da suke shirin aure suna gidan, an bazama neman Susu. Iyalle kuka hadda majina tana ɗorawa ɗanta laifin tursasawa jikarta auren Walid gashi ta gudu. "Saboda Allah yaro bashi da abin riƙeta ta ce bata yarda da shiga gidan alfarma ba to dole ne? Idan babu hali ya nemi daidai shi mana. Banda ya so wulaƙanta min jika me zai sa ya faɗawa mijin Amina halin da yake ciki?" Walid ƙasa ya yi da kansa saboda kunya. Ga iyayensa a wurin sun zo tare ake komai dasu. Hannunsa Dr. Farouk ya kama suka fita waje yana jin da shi ne Walid ya gama da Susu ko an ɗaura sai an kwance. Abdulaziz kuwa don takaici jijiyar kansa har shati take yi. Saɓanin sauran shi ya santa tun ƙuruciya tunda yana yawan zuwa gidan Kawunsa baban Minasco. Da Walid zai dauki shawararsa da ya haƙura da ita ya nemi wata. A ranar basu huta ba ana ta yawo da buga waya gidajen ƴan uwa da abokan arziƙi. Sun je police station ance sai bayan awa ashirin da huɗu zasu dawo, saboda ba yarinya bace ba za ace kai tsaye ta ɓata ba. Haka aka kwana jigum rayuka babu daɗi, musamman na iyayenta. Duk ƙoƙarinka akan yaro idan ya yi ba daidai ba yatsu kanka zasu fara nuni. Alh. Musa da Mama Talatuwa ba mutanen banza bane amma Allah Ya jarabcesu da ƴa irin Suwaida. Bayan azahar gidan ya soma cika da makusantansu suka ji dirin motoci harda jiniya. Ɗa da iyaye sai Allah haka su Alh. Musa suka fita waje da sauri da fargabar ko motar asibiti ce ta kawo musu ƴarsu. Turus suka yi su duka da ganin jerin gwanon motocin da suka cika layin. Bodyguards ɗin ne suka fara fitowa nan da nan maƙota suka shiga gwara ƙofar gidajensu suna rufewa. Su Alh. Musa ma ba a barsu a baya ba shi da matarsa da maman Aisha da kuma iyayen Minasco. Da shigarsu gida da jin sallamar Suwaida ko cikakken minti ɗaya ba ayi ba. Iyalle ta dogaro sandarta tazo ta rungume shalele. Bata yarda ta haɗa ido da kowa ba ta ce, "Tare da baƙi muke?" Mama da Alh. Musa suka kalli juna, kowa da tunaninsa sannan suka ce ta shigo dasu. Walid dawowarsa gidan kenan yaci karo da manyan mutane suna shiga gidan. Jira ya yi suka wuce sannan yabi bayansu. Ƴan uwanta maza da kowa na zaune Alh. Audi, Alh. Ari, Fanna da Shamsu suka biyo bayan Susu. Duk wani wanda zaman ya shafa yana zaune a tsakar gidan Alh. Musa saboda falonsa ba zai ɗaukesu ba. Alh. Ari ne ya gabatar dasu duk da sun so gane shi saboda ganinsa yau da gobe a tv. "Idan ba za mu takura ku ba muna son magana da mahaifin Suwaida." "Nan da ka ke ganinmu babu bare, ko ka faɗa min ni kaɗai zan sanar dasu. Waɗannan ƴan uwana ne" ya nuna Mal. Falalu da ƴan uwansa biyu "sai iyalina, mahaifiyata, ƴaƴana da kuma wanda zai aureta." Alh. Audi ya ce, "to madallah, Alhaji mun zo da ƙoƙon bara, ina nemawa ɗana Shamsu auren ƴar wajenka. Ban zo da kaina don nuna rashin isarka akan aurar da ita ga wanda ka ke so ba sai dai auren dole bai taɓa haifar da da mai ido ba. Sannan kamar yadda ta yi min bayani a gabanka da malamin da ka kira aljana ta yi muku bayanin dalilin dacewar haɗata da Shamsu." "Ban tari numfashinka ba Alhaji, sai dai gabaɗaya ko kalma ɗaya na kasa fahimta cikin maganarka. Wace aljanar ake magana?" "Shamsu bashi wasiƙar da ta rubuta maka ko zai tuna. Shi ya sa na so muyi maganar cikin sirri." A nutse Alh. Musa ya karance takardar, sai dai karantar fuskarsa ya yi wuya. Jikinsa ya yi matuƙar sanyin da bai san matakin da zai ɗauka akan Susu ba. Jikinta sai ɓari yake ita ma amma ko ana muzuru ana shaho tunda suka biyota sai ta auri Shamsu. Hularsa ya cire ya shafa kansa cikin tashin hankali. "Idan na fahimceka da kyau ita da kanta tazo Abuja wajenku jiya da wannan takardar?" Shamsu ne ya amsa masa, "haka ne kuma ina roƙonka da ka taimakeni ka bani aurenta zan biya ko nawa ne." "Abin bai kai haka ba" cewar Alh. Musa. Iyalle da su Mama sun kasa gane me yake faruwa. Yanayin ɗan nata ya sanyaya mata zuciya ta ce, "wai me aka ce a takardar kuma waye ya rubuta? Naji kuna kiran jinnu me aka yi musu?" "Zanyi muku bayani daga baya." Ya juya yana kallon Alh. Audi cikin raunin murya ya ce, "Alhaji kun taho da sadaki?" "A shirye muke amma kuɗin aure ne zamu bayar ba sadaki ba" Alh. Ari ya ce yana zaro damin kuɗi daga aljihunsa. Ƴan uwansa ya kalla, "cikinku waye zai yi wa Suwaida waliyi a ɗaura auren yanzu su koma da ita?" A razane ta kalli mahaifinta tana son yin magana amma babu fuska. "Alhaji me ya yi zafi ne? Bamu zo don mu ɓata maka rai ba." "Raina bai ɓaci ba. Na auna ne dai na ga nisan tafiya daga Abuja zuwa nan gara ayi kawai na sauƙaƙa muku." Walid da su Salihu suna kallon ikon Allah yadda Alh. Musa ya dage sai fa an ɗaura aure. Mama bata iya magana ba sai tashi da ta yi ta koma cikin gida tana kuka. Duk yadda aka yi ta san cewa wani abu mai girma Susu ta yi. Ran Shamsu a ɓace da yadda ya kula kamar iyayenta basa sonta. Abinda ta faɗa ashe gaskiya ne. Da Alh. Musa ya ga cikin ƴan uwan nasa babu wanda ya yarda ya saka kansa cikin lamarin sai cewa ya yi, "Alh. Audi tunda ku biyu ne na wakilta ka a matsayin waliyin Suwaida mu zamu zama shaidu." "Baba!" Walid ya ce damuwa sosai a fuskarsa. "Kada ka damu dama ba rabonka bace." Kowa ya ga yanayinsa ya san cewa ransa ya kai ƙololuwar ɓaci ne. Alh. Audi da yake son yin amfani da wannan auren ya sakaya na Tauhidat da ya kamata a sanar a ranar da suka ce ta ɗaurin aure ya kwantar da kai. "Alhaji ka duba lamarin nan da kyau. Ka ajiye batun shi wannan yaro bata son shi ka duba rayuwar ƴarka. Bai dace ka aurar da ita a haka kamar wata mara gata ba." "Yanzu ya kuke so ayi?" "Yauwa ko kai fa. Dama akwai ɗaurin aurensa da muka yi a cikin unguwa da ƴar direban matata, na so bayan sha'anin bikin nasu a sake taruwa domin jama'a su shaida. Ka ga yanzu sai a haɗa a ɗaura harda na Suwaida." Murmushi Alh. Musa ya yi wato don gata su biyu ne ma zai aura lokaci guda, "hakan ma ya yi, in sha Allahu maɗaurin aurenta zai biyoku Abujan idan ya karɓi sadakin ya damƙa mata a hannu sai ya dawo." Amincewarsa ta yiwa Susu daɗi sosai, ga ƙarin farinciki ashe Tauhidat ƴar direba ce. Kuma sakakkiya ta ƙara tunawa kanta. Sannu a hankali za ta fahimtar da ita matsayinta a gidan ko ta fita ta bata wuri taci karenta ba babbaka. Shamsu ya so a ɗaura ya tafi da matarsa ita kuma barinta ɗin ya mata daidai saboda samun komawa wurin Maibindi. Maƙudan kuɗaɗe Alh. Ari ya miƙa a matsayin dukiyar aure da alƙawarin zuwa ɗaukanta nan da kwana uku saboda biki zasu aiko da lefe. Har suka fita Fanna tana mamakin wannan abu kamar almara. Bata rabe ɗayan biyu Susu kwadayi ne ya kawota ya sanyata bijirewa iyayenta. Suna fita Alh. Musa ya kirata da ta tashi ba kunya za ta shiga cikin gidan ya miƙa mata kuɗin da aka ajiye. "Baba me zanyi dasu?" Ta tambaye shi saboda ta san ba amarya ke riƙe kuɗin aurenta ba. "Ki jefa a masai" Jiki a sanyaye ta ɗauka don bata ga alamun wasa a tare dashi ba. Jan zancen ba komai zai janyo mata ba sai ɓacin rai. Sum-sum ta wuce ɗakinta babu wanda ya kulata. Sai da ta ɓacewa ganinsu ƙwalla ta cikowa Alh. Musa idanu. Mal. Falalu ya girgiza masa kai, "Kada ka yi mata kuka ta ƙara kangarewa." Wasiƙar ya miƙawa Imam ɗansa na biyu, ya umarce shi da karantawa. Yana kai aya Salihu da Ridwan suka tashi har suna rige-rigen shiga cikin gidan. Ran kowa a ɓace yake musamman Salihu da ya yi dukan amma babu kunya ta laƙabawa mahaifinsu. Tana kwance a ɗaki sai jin su ta yi a kanta. Ridwan ya kulle ƙofar, su biyun suka shiga dukanta ba ji ba gani. Da ƙyar Mal. Falalu ya samu suka fito bayan ya nuna musu cewa dukan ba zai gyara komai ba. Mama taci kuka har ta gode Allah. Iyalle kanta yau ta nuna ɓacin rai kuma ta goyi bayan a hukunta ta sannan kada a bada auren nata. "Aure za a basu Iyalle saboda kada a gaba mu sha kunya ko ta ɓata mana suna. Tunda ta iya yin wannan sake zuwa garesu ba wuya zai yi mata ba. Baƙincikina ɗaya Walid bani da wata ƴar da zan baka in wanke kaina daga bakin fentin da Suwaida ta shafa min." "Ƴa kam kana da ita Alhaji kuma da yardar Allah ba za ta bamu kunya ba. Walid kaje wurin Hanifa ƙanwar Amina idan kun daidaita aurenku babu fashi in Allah Ya so. Duk wata ɗawainiya ta uba Alh. Musa ne yake yi mata tun tana tsumma." Wani abu ne yazo ya tokarewa Alh. Musa maƙoshi. Tabbas Mal. Falalu ya nuna masa halacci. Gyaran murya ya yi ya ce masa yaje ya yi shawara da zuciyarsa da kuma magabatansa. Godiya ya yi musu ya fita yana mai al'ajabin halin Susu. Iyayenta da jama'ar dake kewaye dasu babu abinda zai ce musu sai godiya. Yamma nayi jiki duk ya yi tsami Susu ta saci jiki sai wurin Maibindi. Mama da Habibu ƙaninta sun ga fitarta amma kowa a gidan ya yanke shawarar zuba mata na mujiya. Ita duniya ai tafi bagaruwa iya jima. Wanda bai zo cikinta bane yake da bakin magana amma muddin ka shaƙi iskarta shikenan. Da ƙwarin gwuiwarta taje saboda ta ga amfanin shawararsa. Ba wani ƙulle-ƙulle aikinsa ya tabbata kamar yankan wuƙa. Yau ma bai bata komai ba sai sharaɗin da ya kafa mata na cewa a duk lokacin da ya tashi karɓar ladan aikinsa ta tubure zai warware komai. "Indai ba raina da lafiyata za ka nema ba ka ɗauka na baka. Daular da na gani a gidan Alh. Audi na tabbata babu abinda za ka nema na gagara biya." "To kuwa kisa a ranki cewa Shamsuddeen yana tafin hannunki kuma daga ke ya gama aure." "Akwai yarinyar da aka fara aura masa amma ya saketa. Zaman gidan da babansa yake so ta yi ne bana so gaskiya." Dariya sosai Maibindi ya yi, "idan abu ya shafi Alh. Audi to naki ido ne Suwaida. Kada ki kuskura ki nemi abinda yafi ƙarfinki." Ba haka taso ba amma dole ta haƙura. Abu na ƙarshe da ya faɗa mata shi ne ta tanadi ƙaryar da zata yi wa Shamsu akan rashin warkewar lalurarsa domin ba zai iya warkar dashi ba. Duk yadda taso ya faɗa mata lalurar kuma yaƙi. *** Hanifa bata bawa iyayenta kunya ba musamman bayan shawarwarin Aisha da Minasco. Haka ma iyayen Walid sun nuna halacci wurin karɓar tayin da aka yi musu. Duka kayan da Alh. Musa ya saya na auren Susu haka ya damƙawa Mama ya ce aje a jerawa Hanifa. Da farko ta takurawa kanta da kuka ya yi ta bata baki da cewa Susu ba ita kaɗai suka haifa ba da zasu lalace akanta. Tunda ta iya nunawa duniya basu isa da ita ba bai ga amfanin suyi ta tada jijiyar wuya ba. Ya san ba za su taɓa cireta a rai ba to amma dole su koyi haƙuri. Ranar da aka zo ɗaukarta babu wani danginsu Alh. Audi. A taƙaice ma dai mutanen da aka bawa kwangilar haɗa lefen ne suka kawo da kansu kuma aka ce su taho da ita ayi shirin biki. Wannan abu ya tayar mata da hankali sosai haka ma iyayenta amma sun barta ne duniya ta koya mata darasi. Cikin lefen harda motoci biyu na uwa da uba da mukullin gida banda akwatuna guda ashirin da huɗu. Duka wannan saɓanin tunaninta babu abinda ya burgeta saboda rashin zuwan dangin miji, kuma iyayenta suka ce ta karɓi kayanta basa buƙata. Gwaggwaninta biyu ne suka bisu saboda dai kada ace babu wanda ya san inda take. Fanna kai ya ɗauki zafi, wurin neman inda za ta haɗa kayan da amarya zata saka sai abu yazo da sauƙi. Shamsu har ɗaki ya bi Tauhidat ya umarceta da ta bada kayan wurinta sannan daga ranar har amaryarsa ta tare yana so ta kwanta ciwo. "Idan ma baki yi cuta ba to dai ki sani kika kuskura kika zo wurin wani event sai naci mutumci babanki ba naki ba" Hargaginsa bai bata tsoro ba, sai ma daɗin da hakan ya yi mata. Ba musu ta bada kaya ya kaiwa Fanna wai a gyarawa Suwaida. A ranar ta iso aka kira mai ɗinki ta aunata ta tafi dasu. Tsayinsu kusan ɗaya, fadi ne za a rage daidai da jikinta sai takalma da aka siyo wasu. Yadda suka yi haka ta faɗawa Papa Abayomi, shi kuma ya nunawa danginsa da gaske bata da lafiya. Da suka ji cewa su biyu ne amaren sam basu ji daɗi ba saboda a ganinsu an wulaƙanta musu ƴa ne. Wannan dalilin yasa duka taron da akayi basu damu da rashin zuwanta ba. Wasu ma suka fara ganin laifin babanta suna ganin kamar sayar da ita ya yi don kuɗi. A ranar da za a fara bikin Haj. Manga ta aika aka kira mata Tauhidat zuwa falon Alh. Audi. Cikin shiri ta fito ita da Jamal a ranar zasu tafi wurin Arƙam. Ko da wasa Alh. Audi bai yi yunƙurin hanata tafiya ba don dama ce ya samu ta wanke kansa ya shafa mata kashin kaji. Kamar kullum yau ma bata amsa gaisuwar Tauhidan ba sai envelop da ta miƙa mata a gabansa. "Admission letter ɗinki ce a ciki da takardun kuɗin makaranta. Na riga na biya in sha Allahu har ki gama. Idan an samu ƙarin kuɗin a gaba zasu sanar dani." "Amma Manga kin san cewa karatunta ba huruminki bane yanzu ko?" Cewar Alh. Audi bayan ya karanta takardar. "Tunda tazo gidan nan ban taɓa karbar ƙwandalar kowa akan karatunta ba. Don ta yi aure ba zan fasa abinda nayi niyya ba. Idan ka ga dama ka yaga sammakal inji Jamal ɗina." Murmushi ne ya suɓucewa Tauhidat ita ma Haj. Mangan sai da nata yaso bayyana kansa. "Ke yanzu duk karatun duniya ki rasa wanda kike so sai Law?" Ya tambayi Tauhidat. Kai ta gyaɗa "don Allah ka barni inyi." "Zan nemi izinin mijinki saboda kada a keta alfarmar aure." Ko a jikin Haj. Manga ta ce masa, "ba zan dawo ba sai Jamal ya yi settling a makaranta. Nan ɗin ba abinda yake yi sai shiririta, gara na kai shi inda yayansa zai sa masa ido." Kafin ya tanka, suka fice suna taku kan duga-dugansa cike da kwarjini. *** Biki buduri Susu ta sami abinda take so amma ba yadda taso ba. Kwana bakwai aka kwashe ana events kala-kala. Mutane kullum tururuwa suke amma babu kowa nata sai mutum biyun nan. Habaici kuwa sun ƙulla dashi saboda ko yaya suka haɗa inuwa da Fanna sai ta yi mata. Hotunanta sun baza tashoshin talabijin da jaridu amma babu kowa nata da zai gani ya ce da gaske Suwaida ta wuce sa a. A haka aka ci aka cinye, ranar Asabar babu fashi Mal. Falalu da ɗan uwan Alh. Musa suka zo cikin ɗaruruwan mutane suka bada aurenta akan sadakin gida, mota, kujerar Makka da kuɗi dubu ɗari biyu. Yadda aka basu mukullai, takardu da kuɗin haka suka miƙawa Gwaggwanta ta kai mata har ɗakin da aka yi mata masauki suka fito suka kama hanyar Gombe ko jira a kaita ɓangarenta basu yi ba. Ranta ya ɓaci matuƙa, sai dai ta kula har aka ci aka cinye bikin babu wani da aka ce ɗan uwan Alh. Audi ne ko na babar Shamsu da ya ce mata ta rasu. Duk wanda za a nuna mata ta gaisar dangin Fanna Ari ne. Babu dangin uwargida Haj. Manga babu ita kanta sannan tsirarun mutane ta gani a matsayin ƴan uwan Tauhidat. Sai dai a nasu ɓangaren basu ga abin ɗoki da zumuɗi a auren da ko ba a faɗa ba tuni sun gano tasu ƴar bata da wata ƙima a idon miji. Bayan sallar Isha Fanna ta aika a faɗawa Susu ta shirya, sannan da kanta taje ɗakin Tauhidat ta taimaka mata ta shirya. Tausayinta take ji kuma ganin Haj. Manga fushi yasa ta barta ga kuma Susu ɗin da ta tsana har ranta. Da suka gama wurin Alh. Audi ta kaisu wai ya yi musu faɗa. Babu abinda ya iya cewa sai su zauna lafiya aka fita kaisu ɗakunansu. Katon gini ne aka yiwa Shamsun bene. Ɗakuna huɗu ne a sama da biyu a ƙasa sai kitchen, falo da banɗaki saboda baƙi. Ƙarshen haɗuwa wurin ya yi don babu ce kawai a kayan zamani ba a sa ba. Dakin da yafi girma Fanna ta kai Tauhidat sannan ta nunawa Susu wanda yafi kusa da matattakalar bene ta ce ta shiga shi ne nata. Wannan wariyar da ta gani daga Fanna da danginta sai da taci alwashin fansarsa wata rana. "Kada ki yarda ki ragawa waccan matsiyaciyar yarinyar. Ita Nannan taki ta ɗau zafi shi kuma Alhaji ya dage wai don ya kyautata miki ya haɗa auren nan. To koma dai meye ki kama kanki ki kuma nunawa ƴar banza ke ba sa'arta bace. Idan ta shiga gonarki ki faɗa min mu taru mu ci..." "Haba Fanna haka ake yiwa amarya nasiha? Maimakon ki bisu da addu'a sai huɗubar tsiya." Cewar wata ƴar uwarsu. "To Ya Hajja nayi shiru. Ga wannan maza ki shanye kafin ango ya shigo don kece uwargida wata sai dai ta kwashi ragowa." Kofin Tauhidat ta karɓa daga hannunta tana murmushin dole. Suna fita taje ta juye abin ciki a sink ɗin banɗakinta ta ɗauro alwala tazo ta tada sallah. Babanta ya riga ya faɗa mata ba gidan bacci ta shigo ba gashi gobe zai bar gidan da danginsa saboda an sallame shi da kyauta mai tsoka. Suruki ne shi yanzu dole ya bar aikin a cewar Alh Audi. Ita ma kanta ta san akwai maƙarƙashiyar da ake ƙulla mata. Ɗakin amarya Susu duk kyawunsa bai kai na Tauhidat ba kuma Fanna tana sane ta yi hakan. Tana shiga mayafi ta cire ta ƙarewa ko ina kallo tana murna abu kamar mafarki dai yau ya tabbata. Ƙulle-ƙullen magungunan da ta fara sha tun a Gombe ta ɗauko wata gumba ta cinye kusan rabin leda sannan taje banɗaki ta sha ruwa. Yau fa ango nata ne komai tsiya tunda dai ita kaɗai ce matarsa. Shi ma yana ta ɗokin shigowa yau zai sami Suwaidansa. Ba wasu abokai gare shi na azo a gani ba, saboda yanayinsa shi yasa babu ɗan rakiya ya shigo. Ɗakin farko da ya buɗe a saman yaci karo da abar ƙaunarsa zaune a bakin gado ta yi wani irin kyau a idonsa. Da sauri ya ƙarasa ciki ya rungumeta. "Ban barki ke kaɗai ba ko?" Ya tambayeta yana wasa da yatsunta da suka sha lalle. Langaɓe kai ta yi, "na san kana wurin uwargida ai shi yasa ban damu ba." A take ta ga fuskarsa ta sauya ta saki murmushi a ciki. "Ki dena sakota idan muna magana." "Na dena" ta ce da murmushi. Hannunta ya kama zai kaita gado ta turje, "Sham banyi wanka ba tun na safe saboda taro." Bata rai taga ya yi. "Okay shiga kiyi ina jiranki." Zarginta ko Tauhidat aka kai ɗakinsa sai cewa ta yi, "kai fa? Muje na haɗa maka ruwa sai na dawo nayi a nan." Wani abu ya tuna ya girgiza kai, "zanyi a nan kawai ba sai mun fita ba." Ya gama tsarawa ne a ransa shi zai dinga zuwa ɗakinta, kuma ba zai kwana ba duk dare zai koma nasa. Ita kuma ganin haka ta ƙara ƙarfafa zarginta, "wanne ne ɗakin in ɗauko maka brush ɗinka?" Yadda ya ga ta nace kuma ya tuna cewa ai ta san lalularsa sai kawai ya ce ta taso suje ɗakin nasa su kwana a can. Ko ba komai gara ta saba. Sannan ga fatansa na cewa daga yau komai zai daidaita tunda ta tare. Shi ne a gaba tana biye dashi da kayan baccinta a hannunsa suka shiga ɗakin. Don ƙamshi akwai ƙamshi ya ɓulɓula airfreshner ga AC a kunne tun safe, amma bai ɓoye wani irin bashi-bashi da yake fizgar mutum ba. Ranar da aka gama jera kayansa a bangaren ya dawo nan ya kuma kulle wancan ɗakin bai bari an shiga ba. Maimakon shirin wanka sai ta ga kwanta akan gado. "Cire min takalman nan" Ya turo mata ƙafafunsa. Wani iri taji saboda a iya saninta ita ce abar tarairaya a yau ba shi ba. Sannan bata ga alamun ya shigo da komai irin na cimar da ango kan shiga ɗakin amarya dashi ba. Fuskarta ba yabo ba fallasa ta matsa ta cire masa. Tana duƙawa idanunta suka sauka akan shirgin kayansa a ƙasa can gefe guda. Bata san lokacin da ta haɗe rai ba kuwa. Ta tsani ƙazanta ko kaɗan basa shiri da ita. Bayan ta cire masa ta matsa wurin kayan don ba za ta iya kwana da tunaninsu ba. "Bari na zuba kayan can a wardrobe gobe sai na ninke maka. Idan na wanki ne kuma sai..." Tana ɗora hannu a kai yana dirowa daga kan gadon, "ajiye kar ki taɓa." Aikin gama ya gama tuni ta ɗebosu sai dai daga duƙen ta watsar dasu. Wani irin abu da bata san yadda za ta fasalta shi bane ya shiga hancinta a take cikinta ya hautsine amai ya taho. Da gudu ta ruga inda ta fahimci nan ne banɗaki ta bude WC (masai) ta karkace yadda za ta ji daɗin yin aman. Yadda ya taho da ƙarfinsa haka ta haɗiye shi ba arziki saboda mummunan gamon da ta yi. Ajiyar Shamsu ce ta safe da ya yi saboda ganda da sabo ko flushing baiyi ba ya rufe ya fice. Ya riga ya saba sai zai yi wani yake kora wanda ya gabace shi. Sun kumbura suntum suna miƙa gaisuwa ga amarya Suwaida matar Shamsu Audi Karam. Jikinta na rawa take ambaton na shiga uku na lalace har ya shigo. Fuskarta kawai ya kalla ya tuna me ya ajiye a masan. "Oh sorry bari nayi flushing" Bata ankara ba kuwa ya danna abin nan take uba uban wari ya kusa yin ajalinta. Fita ta yi ko ta kansa bata ƙara bi ba ta koma nata ɗakin. Shi kuwa murmushi ya yi na jin kunya a ransa yana cewa zaki saba ne. Wankansa ya yi ya kimtsa sannan ya tafi ɗakinta. A kwance ya sameta ita ma ta yi wanka ta kuma sha kukan baƙinciki ta juya masa baya. Ga yunwa saboda ɗokin yau ko ruwan kirki bata sha ba. Bai ma san ana yi ba bare ya ce ya manta. Ɗarewa ya yi gadon tana turjiya da komai ya gwangwaje angoncinsa da amarya sabuwa fil. A kunnuwanta aka soma kiran assalatu dama baccin nata bai yi nauyi ba. Gani ta yi ya motsa ta sake lafewa nufinta idan ya tashi duk tsiya ya tarairaiyeta kamar kowace amarya. Shiru bai tashi ba sai janyota da ya yi jikinsa yana gyara kwanciya. Bata cika minti biyu ba taji ɓangaren da take kwance a kai kamar akwai danshi. Hannu ta saka ta taɓa sosai ta tabbatar a cikin ruwa suke ba ma danshi ba. A zabure ta tashi zaune duk da dai akwai duhu a ɗakin tana kallo ceiling ta soma tashinsa. "Sham ceiling ya ɓule tashi ruwa yana ɗigo mana." Da ƙyar ta samu ya buɗe ido ya kai hannu ya kunna fitilar gadon. "Mene ne kika tasheni?" "Ruwa yana ɗigowa a kan gadon" ta ce lokaci guda tana miƙewa da quilt ɗin saboda ta rufe jikinta. Idanunta ƙyar suka sauka akan gadon inda yake zaune ya miƙe ƙafa da dogon wandon bacci jike sharkaf. Gabanta ke dukan uku-uku da ta ƙarewa gadon kallo. Inda yake ne yafi jiƙewar ga wandonsa fari ya nuna mata dahir. Zazzaɓi-zazzaɓi taji yana neman kayar da ita, ga ƙafafunta sun saki saboda tashin hankali. Jingina ta yi da wardrobe ɗinta ta saki nauyinta gabaɗaya ta sulale a wurin. "Fitsarin kwance kayi?" Murtuke fuska ya yi "kika ce kin san lalurata?" A hankali ta dinga gyaɗa kai tana cewa,"uhm na sani, fitsarin kwance ba. Haka tace min dama." Da yararin fitsarin nasa da bai gama tsanewa ba ya taso gabanta yasa hannu ya maƙuro wuyanta ta soma kakari, "ya akayi na sake yi bayan kin ce kece maganin?" [2/23, 7:34 PM] Nasma: Cikin Susu ya kusa cika watannin haihuwa, dan haka taketa shiri ba kama hannun yaro. Lokaci ɗaya ta tafi Dubai siyayyar kayan jarirai ita da Fanna. Ba haka dai taso ba amma tunda Shamsu ya dage ba zai je ba sai suka tafi tare saboda zasu hutu da yaranta. Siyayya ta yi tamkar mai buɗe shago saboda kuɗi kam yanzu bata san babu ba akansu. Satinsu ɗaya suka wuce England nan ma ta lodo kaya sosai suka koma gida. Saɓanin yadda masu kuɗi suka saba zuwa turai musamman America haihuwa ita bata da wannan gatan. Shamsu bai yarda suje ko ina ta haihu ba saboda aikin fitsarinsa zai dawo wuyansa. A gida kuwa duk inda ta huta na kwanaki uku ya san tayi kwarin cigaba a cewarsa. Ba wani abu ya hana shi binta siyayyar ba illa yawan tunanin Tauhidat da yake kwana yake tashi dashi. Wannan cigaba kuwa ya faru ne a dalilin wani zuwa weekend da ta yi ta samu bashi da lafiya. A falonsa ta same shi ta gaishe shi da jiki. Bata san me ya ingizata ba amma da ya buƙaci ta bashi ruwan sha sai ta sami kanta da karanta Ayatusshifa ta tofa sannan ta miƙa masa. Jira ta yi ta gani ko zai watso mata ruwan saboda irin kallon da yake mata kamar na ƙyama sai kuma ya kafa kai ya shanye. Tun yana dan shekara goma sha shida sai a wannan ranar guda daya ne kacal bai yi fitsarin kwance ba. Washegari Susu murna kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha. Shi kuwa ko sallar asuba da ya saba yi idan rana ta take bai tsaya yi ba ya fita zuwa ɗakinta a guje. Wayam ya tarar ta riga ta koma makaranta. Abin baƙinciki sati ya zagayo bata zo ba sai zancen tafiyarsu ya taso shi ne ya fasa. Kullum tana kai kawo a cikin ransa tun yana ɗaukar abin wasa har dai ya yardar wa kansa cewa ta sami wurin tsugunawa ko bata zauna ba a zuciyarsa. Haka kawai yake jin cewa ƙila da bai saketa ba da tuni ya warke daga fitsarin kwancen da yake fama dashi. Bai yi ƙasa a gwuiwa ba bayan tafiyarsu Susu ya sanar da mahaifinsa cewa yana so a sake aura masa ita. Gaba na matsanancin faɗuwa Alh. Audi ya hau shi da faɗa, "Kada na sake jin wannan zancen. Tun farko ban aura maka ita don ina son ku yi zaman aure ba. Tunda ka saketa magana ta riga ta ƙare. Buƙata ta kawai ka zama garkuwa a gareta akan tunanin barin gidan nan." "Bangane ba." Shamsu ya ce a kiɗime. Cikin fushi ya amsa masa da cewa, "Ba kuma za ka gane ba. Akan yarinyar nan zan saɓa maka fiye da zato da tsammaninka." Ƙasa-ƙasa Shamsu yake kallonsa sannan ya ce, "ko dai kaima kana sonta ne?" Wawan mari na fitar hankali Alh. Audi ya zabga masa ya soma faɗa ba ji ba gani. "In rasa wadda zan so sai matarka? Idan ina sonta kana tunanin zan bar maka ita ne da ace da kanka ka nemi aurenta?" Hannu akan kumatunsa ya ɗago idanunsa da suka kaɗa suka yi ja saboda ɓacin rai "sau ɗaya na taɓa karɓar abin hannunta amma a ranar Baba banyi fitsarin kwance ba. Ko bana son Tauhida zan iya yin komai don mallakarta a kusa dani domin samun lafiyata." Bakinsa har kumfa yake don masifa ya ce, "To sai ka nemi aiki ka fara ɗaukar albashi da guminka idan kana tunanin yin komai domin aurenta. Matsawar ci da sha da suturarka da ta iyalinka daga aljihuna zasu fito to bin umarnina ya zama wajibi a gareka. Bace min da gani kafin na saɓa maka." Shamsu na fita jikin Alh. Audi ya kama rawa kamar mazari. A gigice ya tashi ya janyo wayarsa ya kira Oga ya faɗa masa yadda suka yi da Shamsu. "Ka raba yarinyar nan da gidanka idan kana son nesanta kanka daga ɓacin rana." Ita ce amsar da ya bashi. "Idan ta tafi na san me za ta yi daga can? Ba gara tana kusa ba?" "Kusancinku shi ne babban hatsarin da Maishare mana hawaye ta ce na sanar da kai." Daga haka Oga ya ajiye wayar yana fata Alh. Audi ya faɗa tarkon da ya ɗana masa. Idan bai kawar dashi ta hanyar amfani da mutanen nan uku ba ya tabbatar Alh. Audi sai ya kifar dashi ya maye gurbinsa a idanun duka mabiyansa. Da haka ta faru kuwa gara shi ya fara ganin bayansa. A sanyaye ya ajiye wayar yana juya maganganun Oga. "Kai, ba fa zan nesanta ta da gidan nan kamar Arƙam ba in zo lamura su kwaɓe min da wurwuri. Shamsun dai zan ja wa kunne ya fita harkarta." *** Susu bata san wainar da ake toyawa ba har ta dawo. Wannan ɗokin da Shamsu kan nuna akan cikin nata duk babu. Abinda ya fara zuwa ranta bai wuce barinsa da ta yi da aikin ƙazantarsa ba na kwanakin da bata nan. Yanzu da bata da wani gata sama dashi tunda iyayenta sun gujeta dole ta kwantar da kai neman shiri. Ita ce girke-girke da gyaran ɗaki amma ko kaɗan ba ya kulawa. Har Alh. Ari ya nema akan ya taya shi roƙon baban nasa sai ya sha mamakin ganin bakinsu ɗaya. Damuwa ta sarƙe shi ya rasa inda zai saka kansa yaji daɗi. Ga takunkumin da Alh. Audi ya ɗaura masa inda ya ce duk ranar da ya kuskura ya bi Tauhidat makaranta ya tattara komai nasa da na iyalinsa su bar masa gida. Da wannan ya kashe masa gwuiwa saboda bashi da wani abin kansa sai na uba ga tsoronsa yana ji. Ita kuma wadda ake yi dominta bata da masaniyar komai. Waya ce dai Alh. Audin ya yi mata ya ce kada ta zo cikin gari sai ya kirata da kansa. Idan tana buƙatar kuɗi ta neme shi kai tsaye. Ba ya son duk wani abu da zai taɓa mata karatu. Yawan zuwa gidan da take yi ya soke don yafi so ta tattara hankalinta waje guda. Taji daɗin wannan magana saboda dama tana zuwa ne don kada ace bata mutunta aurenta. A can ƙasan zuciyarta kuma tana tunanin karshenta akwai wata boyayyar manufar da tasa ya bata wannan umarnin. Sati uku da dawowarsu Susu ta tashi da naƙuda. Shamsu ne ya kaita asibiti tare da mai aikinsu guda ɗaya. Matan gidan basa nan duka. Fanna ta je gidan iyayenta. Haj. Manga kuma an gama ginin makaranta sai shirin ɗaukar ma'aikata da ɗalibai. Shiyasa kwata-kwata bata da lokacin zama. Sai zirga-zirga yau tana can gobe tana can. A filin jikin makarantar kuma gida ake gina mata na gani a faɗa wanda take burin komawa da ƴaƴanta da zarar ta sami damar raba kanta da Alh. Audi. Bayan awa biyu da zuwansu asibitin a ƙarƙashin kulawar manyan likitoci saboda sanin ko ita wacece Susu ta haifo lafiyayen ɗanta. Ko da yake jariri kana kallonsa ka ga mahaifinsa kamar ya yi kaki. Murnar da ta yi har tafi ta Shamsu saboda ganin ta haifo magajin magajin Alh. Audi. Ana kaita ɗakin hutu ta kira Mama ta faɗa mata. "Allah Ya raya" cewar Mama ba yabo ba fallasa. Yanayin amsar ya sanya wani ƙululun abu ya tsaya mata a wuya, jiki a sanyaye farincikin da take ciki ya juye zuwa ɓacin rai. "Amma zaku zo ko Mama? Wa zaki turo min ta zauna dani?" Girgiza kai Mama Talatuwa ta yi. Ƙarya take idan ta ce bata son ƴarta amma har yau Suwaida bata yi nadamar sharrin da ta yi musu domin auren Shamsu ba. Unguwarsu da cikin dangi duk inda Mama ta zauna ana zunɗenta. Tare da sakar musu maganganu marasa daɗi akan abinda ta yi. Koda sau ɗaya da zata zo gida ta basu haƙuri zasu ji daɗi. Amma ita a tunaninta kuɗinta ne zai karkato dasu don bata ga kuskure a son inganta rayuwarta ba. "Kinsan babanku ba mai son yawo bane ga bikin Salihu sati biyu masu zuwa babu lokaci." Kasa daurewa ta yi sai da hawaye ya zubo mata "yanzu Mama bikin Yaya Salihu za ayi amma babu wanda ya faɗa min? Kun ajiyeni a gefe babu mai waiwayata. Gidan nan har gori ake yi min akan rashin ganin dangina." Jin kukan nata da shigowar Alh. Musa yasa Mama cewa za ta sanar da babansu. Ko da ta faɗa masa shima cewa ya yi Allah Ya raya ya tashi ya bar ɗakin. Ta fahimci nufinsa a bar zancen shi yasa ta kama bakinta tayi shiru. Washegari suna komawa gida aka fara zuwa barka. Duk cikin ɗumbin jama'ar nan babu wanda aka ce dangin Alh. Audi ne ko na mahaifiyar Shamsu. Wannan na ɗaya cikin abinda ke kwantarwa Susu hankali. Idan an tashi gorin dangin ba ita kaɗai za a yiwa ba. Kamar lokacin bikinsu daga na Fanna sai ƙalilan daga ɓangaren Haj. Manga. Ranar da ta kwana uku, sai ga wata mata an rakota har ɗakinta na sama wai Gwaggonta ce daga Gombe. Tana wanka lokacin da suka shigo. Da sauri-sauri ta watsa ruwa ta fito saboda tsananin murna. Matar ta juya mata baya bata ganin komai nata saboda ƙaton mayafin jikinta. Takowa ta yi don ganin ko wacece a cikin kanen iyayenta sai taji jaririnta dake hannun matar ya tsallara wata irin ƙara mai firgitarwa. Sakin ƙaramin tawul ɗin hannunta ta yi, ta zagaya da sauri gabanta. Wata irin bugawa zuciyarta ta yi mararta ta ƙulle lokaci guda da ta yi ido huɗu da ita. "Maibindi?" Ta ce da rawar baki. Cikin ƙanƙanuwar muryarsa ya ce "ashe dai zaki ganeni Suwaida?" "Ban ɗana" ta ce tana miƙa hannuwa tare da matsawa kusa dashi. Maimakon ya miƙa mata sai ya juya shi ta yadda ƙafafunsa kaɗai ya riƙe jikin na lilo a iska. Kuka mai ban tausayi ya saka shi kuma ya nuna shi da ɗaya hannunsa. "Wannan shi ne ladan aikin da nayi na shigowarki gidan nan." "Ladan aiki? Ni kake faɗawa ladan aiki Maibindi? Kada ka manta ko laya baka bani ba yadda naje gabanka haka na taso." "Ashe..." ya kashe ido ɗaya yana dariyar mugunta. Hankalinta in ya yi dubu ya tashi a wannan lokacin. A tsorace take kada wani ya faɗo ɗakin ya gansu. Ga ɗanta yana ta kuka. Maibindi ya jijjiga shi kamar zai yar dashi tsoro ya sake kamata. Kujerar gaban madubi ta ɗauko da niyyar kwaɗa mata, sai kawai ji ta yi ya faɗi wata kalma ɗaya sai ga hannuwanta ɗauke da kujerar sun ƙame a sama. Bakinta bai mutu ba take cewa ya bata ɗanta kafin ta haɗa shi da hukuma. Bai kulata ba sai rufa idon da ya saba yiwa mutane ake ganin kamar akwai bindi (jela) a jikinsa ya yi akan ɗan jinjirin nan. Susu na kallo wata narkekiyar jela ta ɓullo ta saman wandon yaron daidai inda Maibindi ya ɗan saɓule shi. Sauran kaɗan fitsari ya suɓuce mata a wurin. Kallonsa yake cike da so da ƙauna ya ce, "Kamar kowane mutum nima na kasance mai neman wanda zai gajeni ya gaji sana'ata." "Me. Me kake nufi?" Ya cigaba da yi mata bayani yana sakin murmushi "tun kafin ki zo wurina akan auren babansa kasa ta nuna min cewa wanda zai gaji bokancina daga tsatsonku zai fito." Hawaye take sosai tana cewa idan ba tsoro ba ya sakar mata hannu ya gani idan bata zama ajalinsa ba shi kuma yana dariya. Suna cikin wannan yanayi Tauhidat ta shigo da sallama. Kifta ido Maibindi ya yi hannuwan Susu suka sauka. Kafin ta ƙarasa shigowa sun gyara yanayinsu sai jariri da ake ta rarrashi. Ta yi kyau sosai cikin doguwar rigarta ɗinkin bubu na wani leshi mai kyau da taushi. Kyakkyawan murmushi ta yi musu, sannan ta bawa Susu haƙurin shigowa ɗakin kafin a amsa sallamarta. "Na yi sallama yafi sau biyar naji shiru sai kukan baby, shi ne na shigo na duba shi ko kina toilet ne." Murmushin yaƙe Susu ke yi mata saboda ta gama tsorata tana tunanin ko taji zantukansu ga kuma yanayin da ta gansu. "Ƙyale ɗannan naki mai rigima da kukan banza. Rarrashinsa muke yi bamu ji sallamar ba ko Gwaggo?" Ta kalli Maibindi da ya zubawa Tauhidat ido. Kallon nasa ya takurata duk da a iya ganinta mace ce. Dukawa ta yi ta gaishe shi sannan ta karɓi jaririn. "Bari na baki wuri ki shirya" ta ce ta yi hanyar fita da ɗan a hannu. Sai a lokacin Susu ta tuna daga ita sai tawul. Bata iya hanata fita da jaririn ba saboda hankalinta baya jikinta. Tauhidat na fita ta tafi ɗakinta da gudu-gudu tana waigen baya ta rufe ƙofa hadda murɗa mukulli. Tana ƙanƙame da ɗan ta zube a wurin ta zauna jikinta na karkawarwa. Ita kam bata shigo gidan nan a sa a ba ta ayyana a zuciyarta. Daga taji wannan bala'i sai taji wancan masifa. Babu abinda bata ji ba daga maganganun Susu da wadda ta gani a matsayin Gwaggonta. Wannan wace sabuwar masifar ce kuma? Hawaye take sosai tana kuka ta tashi ta kwantar da yaron akan gadonta. Tube shi ta yi ta duba jikinsa tsaf bata ga komai ba da zai tayar mata da hankali. Bayan ta mayar masa da kayan ta ɗora shi akan cinyarta, nan ta dinga karanta Ayatul kursiyyu tana tofa masa a kowace gaba ta jikinsa. Bata san wanda za ta faɗawa wannan magana ba. Sunan Nanna kaɗai ke yawo a ƙwaƙwalwarta sai dai abubuwan da suke gabanta da yawa, bata son kai mata wata matsalar bayan wadda take ciki da bata gama sanin girmant ba. Maibindi na ganin fitar Tauhidat ya ce da Susu ta shiryawa abinda zai biyo baya domin kuwa ta riga ta gama jin abinda suke cewa. "Na bono na lalace, kaga abinda ka jawo min ko?" Ta ɗora hannuwa a ka. "Akwai maganin abinda ki ke gudu amma da sharaɗin wannan ɗa nawa ne. Idan kuma kinƙi ji ba kya ƙi gani ba." Zumar dake ƙunshe a cikin rayuwar masu kuɗi aba ce mai wuyar rabuwa saboda zaƙinta. Sau tari daɗinta kan sa mutum ya rasa tunaninsa, bare yabyi aiki dashi a inda ya dace. A wannan lokacin babu abinda Susu tqke tsoro kamar komawa gida ayi mata dariya bayan an rabata da wannan daula. Zuciya a dake ta ce ta amince ya yi abinda ya dace. Yau ma ba guru ba laya sai maganganun da ya faɗaa mata nan take ta hau kai ta zauna. Ana gobe suna Jamal ya iso Nigeria. Yazo taya Nannansu da harkar makaranta domin komai ya tafi daidai. Karatu dai yanzu yana yi amma batun shaye-shaye da ya zamana aikin asirin Alh. Audi sai abinda ya ƙaru. Indai kaji suna faɗa da Arƙam to bai wuce ya sha wani abin. Zuwansa ya faranta ran Haj. Manga haka ma Tauhidat duk da basu haɗu ba. Tun ranar da taji maganar nan kusan kullum yaron yana hannunta tana masa addua. Ɗakinta kuwa karatun Qur'ani ne yake tashi kodayaushe. Anyi shirin taro irin wanda ba a taɓa yi ba domin murnar haihuwar yaron da yaci sunan kakansa Audi amma Susu ta mayar dashi Aidan. Abinda ya bata mamaki a ranar shi ne zuwan Mama da wasu cikin ƴan uwansu, ga kuma Aisha da Minasco hadda Hanifa matar Walid. Nan da nan taji kanta ya fashe tana ta rawar jikin ganin ta burgesu. Taro za ayi na kece raini Alh. Audi Karam ya yi jika. An ƙawata fargajiyar gidan da kayan decoration ajin ƙarshe wurin kyau da tsada. Ana wannan shirin a gefe guda kuma Gwaggo Maibindi ya gama hura wutar sharrin da zasu ƙullawa Tauhidat. Shamsu na ɓangaren maza ya fara gaisawa da baƙin Alh. Audi yaji babu abinda yake son gani irin Tauhidat. Wata mahaukaciyar soyayyarta ke ruri a zuciyarsa fiye da yadda ya saba ji. Tamkar wanda ake ingiza shi zuciyarsa ke faɗa masa ya tafi ɗakinta tana can. Yana tafiya Maibindi ya ja Susu gefe daga cikin mutane ya faɗa mata cewa ta hau sama aikinsu yaci.