Kenza eBookz

Cizon yatsa book 1&2 complete - Chapter 19

Cizon yatsa book 1&2 complete - Chapter 19

Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 19: Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 19. "Ka rasa lokacin yin wani abu sai yau da ake taro a gidan?" Ta ce cikin…

2,645 words

"Ka rasa lokacin yin wani abu sai yau da ake taro a gidan?" Ta ce cikin fushi. Burinta yau Mama ta ga yadda rayuwarta ta sauya saboda arziƙi. Bai amsata ba sai cewa ya yi "Idan kinyi abinda nace ba zata sake kwana a gidan nan ba. Idan kuma kinƙi kece zaki bi iyayenki" Ko kaɗan bata jidaɗin hakan ba, amma ba yadda ta iya. Wayar Tauhidat da ta ɗauke daga zuwa kai mata kayan Aidan ta shirya shi ta ɗauko daga jakarta ta turawa Shamsu text. Yana hawa bene ya shigo ya duba. Bashi da number ɗinta amma ya gane saƙon daga gareta ne saboda sunan da aka rubuta a ƙasa. Kalmominta sun ɗaure masa kai kamar waɗanda suka saba haɗuwa. Sai dai babu damar dogon nazari saboda yadda zuciyarsa take azalzalarsa. (Sweetheart don Allah kazo dakina zan jiraka sai mu sauka tare. Miss you, Tauhidat.) Ɓangaren da Alh. Audi yake tsaye da abokansa Susu ta nufa ta ɗan tsaya daga gefe ta tura Mammalo yayi mata magana dashi. Yayi mamakin kira daga gareta sai dai kuma ya tabbata haka kawai ba zata kira shi ba. Hakuri ya bawa wanda yake yiwa magana ya ƙaraso inda take tsaye. Dama kafin yazo idanunta sun gama cika da hawaye. "Suwaida lafiya? Ko anyi wani abu da bai gamsar dake bane?" Ya tambayeta. Hawayen ta bari suka sauko ta goge da bayan hannu sannan ta ce "Baba akwai matsala. Tun ranar da na tare a gidan nan Shamsu ya faɗa min babu aure tsakaninsa da Tauhida amma na rasa me take yi masa ƴan kwanakin nan bashi da zance sai nata. Yanzu haka yana ɗakinta inda yake zuwa suna aikata mummunan aiki ko tsoron kada a kamasu baya yi." Ta ƙare da fashewa da kuka. Da farko haukan Shamsu ya gani na faɗawa Susu babu aure tsakaninsa da Tauhidat. Sai kuma maganar yana zuwa ɗakinta ta saukar masa kamar rugugin aradu. Oga ya faɗa masa ya rabasu yaƙi ji yanzu kuwa komai zai iya faruwa. Girman cikinsa da tsayin babbar riga basu hana shi nufar gidan da sassarfa ba yana tafe yana tuntuɓe. Susu na ganin haka tabi bayansa tana jinjina aikin Maibindi. Ya faɗa mata cewa duk yadda take tsoron kasancewar Tauhidat a gidan kada ta tona mata asiri na surukinta yafi tsanani. To shi kuma meye tsakaninsu haka? Alh. Ari da wasu da suka gansu suna saurin ciki kuwa harda Haj. Manga da Jamal da kuma tawagar Mama Talatuwa. Su ma bin bayan nasu suka yi. A lokacin Tauhidat tana ɗaki taje canja kaya kafin ta sauka farfajiyar gidan bayan la'asar inda za ayi babban taron taji an murɗa ƙofar ɗakinta. Rigarta na kan gado tana ɗaura zani ba zato ba tsammani taji an rungumeta ta baya. Hannuwan na namiji ne kuma ko mace ce bata ga dalilin hakan ba. Da sauri ta ƙwace jikinta tana juyawa ta sauke masa tafin hannunta a kumatu kafin ta rarumi hijabi ta saka. Ranta a masifar ɓace yake haka ma na Shamsu da ya fassara marin a matsayin wulakanci. Wuyanta ya shaƙo da hijabin ya janyota jikinsa da ƙarfi. "Ke don baki da mutumci ina matsayin mijinki zaki mareni?" "Don kana mijina sai ka faɗo min ɗaki ba sallama?" Ta mayar masa a zafafe zuciyarta na tafasa. Taɓata da yayi ji take kamar ya watsa mata garwashi. Shigowar tasa bata ɓata mata rai sosai ba kamar kasancewar jinin Alh. Audi ya tabata. Ko tana sonsa babu abinda zaisa ta yarda ta raɓe shi balle kuma bai taɓa samun gurbi a zuciyarta ba. Fusata ya yi ba gaira ba dalili ya jefata akan gado yana cewa yau sai ya ga wanda ya tsaya mata har take jin zata iya yi masa gardama. Yana ƙoƙarin cire mata hijabin da ta riƙe tamkar rai Alh. Audi ya buga ƙofar fa ƙarfi ta buɗe gabaɗayanta ya gansu a wannan yanayin. "Shamsuddeeni me kake yi haka?" Ya daka masa tsawa. Kamar wanda aka tasa daga bacci sai a lokacin Shamsu ya farga da inda yake da abinda yake shirin faruwa. Ɗagata ya yi da sauri saboda tsoron mahaifinsa. Yana tashi ta miƙe tsaye tana gyara hijabin da ya kusan shaƙeta dashi. "Nace me ya kawoka ɗakin nan?" Cewar Alh. Audi idanu a rufe da ɓaci rai. "Wace irin tambaya ce wannan za ka ce me ya kawoshi ɗakin matarsa?" Inji Haj. Manga tata zuciyar na tafasa da ganin Tauhidanta a yanayi irin wannan. A ganinta me zaisa mace da mijinta ayi mata terere. Juyawa ya yi yaga mutanen da suke bayansa kowa ya tsare shi da idanu. Bakinsa yaji ya bushe saboda rasa yadda zai yi. Bai san yadda akayi ya bari fushinsa yayi tasiri ba har ya fito kowa ya gane halin da suke ciki ba. Zai yi amfani da wannan damar wurin korar Tauhidat kada zancen Oga ya tabbata. Hankula sun koma kansa da su Shamsu, Susu ta samu ta ajiye wayar Tauhidat akan wani ƙaramin tebur ɗin gilas sannan ta ɗago tana kuka don so take ayita ta ƙare. Shamsu ta nufa ta riƙe masa wuyan riga tana rizgar kuka kamar wadda ake yankar naman jikinta. "Kace min tun kafin bikinmu ka saki Tauhida kuma a iya sanina ba a sake ɗaura muku aure ba to me ya kawoka ɗakinta har kan gado? Sau nawa ina baka shawarar cewa tunda babu wanda ya san ka saketa ka faɗawa Baba a mayar muku da auren kana cewa baka sonta ashe cin amanta kuke yi." Turus Shamsu ya yi ganin wani mugun kallo da babansa ke jifansa dashi ya soma ƙoƙarin kare kansa. "Ni ɗin Suwaida? Yaushe na faɗa miki haka? Babu wanda ya sani daga ni sai Baba fa." Susu ta sami damar ƙara hura wuta ta ce, "Ita ma ai ta sani tunda bama rabon kwana sai wanda kuke keɓewa kuna aikata saɓo kana bata kuɗi." "Ku rufawa mutane baki" cewar Alh. Audi da sauri. Kowa ya yi mamakin wannan magana musamman Tauhidat da Haj. Manga. Jamal kuwa wani irin abu ne ya tokare masa ƙirji yana ɗaci. Tunda suke bai taɓa ɗagawa Tauhidat murya ba sai yau. Gadan-gadan ya nufeta cikin hargagi. "Why Tauhidat? Akan kuɗi ki ka zaɓi wulaƙanta kanki haka?" Kuka take son yi amma zuciyarta ta bushe. Ta dena mamakin kowane irin sharri daga gidan nan. Kallon da Jamal yake mata yafi komai dagula mata lissafi. A raunane muryarta ke fita ta ce, "Kana cikin mutanen da nake tunanin ko a wane hali ka ganni za ka yi min uzuri." "A hakan?" Ya ce a ƙyamace, "kowa a nan fa ya ganki akan gado da mutumin da babu aure tsakaninku. Har nawa yake baki da ki ka zabi wannan rayuwar akan..."

Baƙinciki mara misaltuwa ne ya sarki zuciyar Tauhidat bata san lokacin da ta mari Jamal ba. Kallon tsana take gani daga idanunsa da na sauran mutanen ɗakin. Ɓangaren da Nanna take kuwa ko da wasa bata kai idanunta wajen ba. Duk duniya tana jin zata haɗiyi komai amma banda ƙazafi mai muni irin wannan kuma daga bakin wanda ta yarda dashi ɗari bisa ɗari. Bata da zaɓin da ya wuce ta kare kanta. "Shamsu bai taɓa zuwa ɗakin nan ba sai yau sannan babu wanda ya faɗa min cewa ya sakeni. Ban san me ya kawoka ba amma ka faɗa musu gaskiya ko don darajar ɗanka kada ya tashi ana zargin mahaifinsa." Kamar wani soko ya kalli Alh. Audi da ya kasa magana saboda al'amarin ya wuce yadda zai iya gyarawa. "Baba da gaske take ban taɓa zuwa ba. Kuma yau ɗin ma saboda text ɗin da ta tura min ne." "Wane irin text?" Susu ta ce tana karɓe wayarsa. Buɗo wurin saƙonni ta yi ta karanto da ƙarfi yadda kowa zai ji. Kallon banza ta yi wa Tauhidat, "ni tausayi ma kike bani saboda kin ɓata rayuwarki a banza." Hankalin Tauhidat a tashe ta shiga neman wayarta tana cewa karya ne ita ko numbarsa bata da ita. Fanna ce ta dauko wayar ta duba sai ga text ya bayyana ta kuma yi saving sunansa da Sweetheart. Kafin kowa ya yi magana Tauhidat ta matsa gaban Shamsu ta yi masa tambayar da amsarta kaɗai take son ji. "Da gaske ka sakeni?" Sai da ya kalli Alh. Audi yaga ya gyaɗa masa kai sannan ya ce mata, "eh". Tana jin haka bata sake cewa komai ba ta ɗauki rigarta ta shiga banɗaki. Ko minti biyu bata yi ba ta fito har lokacin babu wanda ya motsa daga inda yake. Kayanta da za ta iya ɗauka ta zuba a cikin wani akwati. Tana zuwa inda Susu take tsaye ta kalleta sama da ƙasa sannan ta yi murmushi saboda ta gane dalilin wannan sharri da aka ƙulla mata bai wuce maganarsu da Gwaggonta ba. Mukullin motarta da katunan atm na bankuna huɗu ta zuba mata a tsakiyar hannunta da ta riƙo. "Ga wannan babu ko sisinku a jakata kuma ban ɗauki komai ba sai kayan sawa tunda dai ba zanyi yawo tsirara ba ko?" Gaban Haj. Manga ta je ta dan rissina, "Nanna zan sami kuɗin mota zuwa Abeokuta?" Jamal na jin haka ya buɗe wallet ɗinsa ya zaro ƴan ɗari biyar biyar ya miƙa mata. Karɓewa ta yi ta tura a jaka ba godiya sai muguwar hararar da watsa masa sannan ta yi gaba. Ɗakin tsit suna kallo har ta fice aka rasa mai cewa ƙala sai fita da suka dinga yi ɗaya bayan ɗaya. Tauhidat na fita ta kira Mammalo gefe ta roƙe shi alfarmar duk lokacin da ya sami damar ɗaukan Aidan ya dinga karanta masa ayoyin neman tsari da kariya. "Ƴar gidan Fafa ba dai tafiya zaki yi ba kema?" "In Allah Ya yarda ni da gidan nan har abada. Idan na nutsu zan tura a kwashe min kayana daga Gwagwalada. Kada ka manta ka san yadda zaka yi Aidan ya yawaita zama a wurinka." Daga haka ta fita ta nemi taxi zuwa tasha, ta tsaya jiran motar da a daren zata kaita zuwa garinsu. Fitarta daga gidan ba wuya Mama Talatuwa tasa Minasco kiran mijinta yazo ya ɗaukesu don bata son ƙara ko da minti ɗaya cikin gidan. "Mama ya ki ke zancen tafiya kuma daga zuwanku?" Cikin takaici Mama ta ce "ina mai dana sanin roƙon babanku akan muzo miki saboda kada ace baki da dangi. Suwaida kinyi nisa a wannan turba da ki ka ɗora kanki daga yau ki manta da kina da wata uwa a Gombe har sai kin tuba kin bi Allah."Jiki a mace Susu ta ce "Mama me ya kawo wannan maganar kuma?" Amsar da ta bata sai da tasa ta kusa sakin fitsari a wurin. "Akan idona ki ka zaro wayarta daga cikin rigarki kika ajiye akan tebur." *** "Akan idona wannan matar ta Shamsu ta zaro wayarta daga cikin riga ta ajiye akan tebur. Na tabbata ita ta yi text ɗin ta shirya komai" inji Jamal ya bawa Haj. Manga amsar dalilin amfani da zafafan kalamai ga Tauhidat "idan ba tunzuruta na yi ba muna ji muna gani za a ɓullo da wata hanyar mayar da auren. Baki ga idanun maigidan naki ba kamar zai yi kuka?" Dariyar da ta taso mata ta mayar murmushi "Amma duk da haka kalmomin naka sunyi tsauri Jamal na san kafin ku shirya da ƙanwar taka sai an kai ruwa rana." Dariya ya yi ya sami wuri ya zauna ya dauko wayarsa "nima na sani don marin nan ya so zautani. Bari na faɗawa Big Bro ya fara shiri. Ina aura mata shi zamu komai normal." Da sauri ta ƙwace wayar "kar ka soma faɗa masa. Ku ƙyale min yarinya ta yi karatu ta sami foundation mai kyau a rayuwa. Nothing is permanent in life Jamal. Not me, not you...not Arƙam. Tana buƙatar ta tsaya da ƙafarta indai akwai abinda Alhaji yake buƙata daga gareta. Duk yadda nake kwaɗayin ganinta a matsayin matar yayanka her well being comes first. Tauhidat ba kayan wasa bace da za a dinga garata daga nan zuwa can. Sannan kada ka manta har yanzu bamu san dalilin Papa Abayomi na bayar da auren nata ba. Mu cigaba da tafiya a matsayin bama shiri da ita da Shaheed for now." Murmushi ya yi sosai cike da jindaɗin kalamanta ya ce, "Nanna ina sonki wallahi." *** Shaheed da duka makusantansu babu wanda ya ɗaga hankali akan wannan sakin da aka yi. A irin zaman da suka kula tana yi a gidan rabuwarsu ita ce mafi alkhairi. Satinta ɗaya suka koma Abuja ita da yayanta. Makaranta ya kaita inda ya sha baƙar wuya kafin ya sama mata ɗaki a hostel saboda ba farkon semester bane. Sai da ya gama komai suka kwaso kayanta na sakawa daga gidan da Alh. Audi ya kama mata farkon fara karatun. Ita ta sake zage damtse wurin karatunta sosai shi kuma ya bazama neman aiki. Tunda a garin take baya son yin nesa da ita ko kaɗan. Yana ta yawon interview kuɗaɗen hannunsa sun tasarma ƙarewa kwatsam sai ga kira daga wani babban construction company mallakar wani Inyamuri. Ba zato ba tsammani aka ce yaci interview ɗin, nan ya kira Tauhidat suka dinga murna. Litinin ya yi reporting sakatariyar shugaban wurin mai suna Sariat ta jagorance shi zuwa ofishinsa. Mutumin akwai barkwanci da jan mutane a jiki. Haɗuwar farko Shaheed yaji ya burge shi. Bayanin aikinsa ya ce ayi masa sannan aka bashi mukullin mota dana gidan da aka kama masa a wani estate kusa da kamfanin. Yayi musu godiya hadda hawaye ya fita zuwa makarantarsu Tauhidat domin bashi da mai taya shi murna sama da ita. Fitarsa ke da wuya Sariat ta kira Haj. Manga ta fito daga ofishin da yake kusa da na shugaban nasu. "Nagode sosai Mr. Nzeribe." Ta ce tana murmushi. "Ni ke da godiya Hajiya. Babu abinda iyalin Alh. Ibrahim zasu nema a gareni banyi musu ba sai wanda yafi ƙarfina. Yanzu da ki ka nemi taimakona baki ji daɗin da naji ba." Sake roƙarsa ta yi akan kada ya taɓa bari Shaheed ya san cewa ita ta sama masa aikin. Ya mata alƙawari shi da sakatariyar tasa da ta yiwa bayanin komai zasu riƙe mata alƙawari. Shaheed bai bada kunya ba kuwa domin aiki yake tsakaninsa da Allah. Cikin ƙanƙanin lokaci kuma soyayya ta shiga tsakaninsa da Sariat wadda ta kasance bayerabiya musulma ita ma. Shekara ɗaya da rabi da fara aikinsa akayi bikinsu. Babu abinda Haj. Manga bata sani daga bakin Sariat akan rayuwar sa da ta Tauhidat ba. Har kullum burinta kada su nema su rasa kuma kada zuri'ar Abayomi ta wulaƙanta a dalilin rashin kulawa daga gareta. A ɓangare guda kuma Aidan ya soma girma amma ba ya iya motsa kowace gaɓa ta jikinsa sai kai. Babu magana sai dalalar da yawu sannan lokaci zuwa lokaci sai ya dinga abu kamar mai farfaɗiya. Shamsu da farko ya tada hankali suna da yawon asibitoci ba a dace ba. Susu da ta san cewa aikin Maibindi ne sai ta sakawa zuciyarta salama. Gabaɗaya ya fice mata a rai bata son shi saboda tana ganin kamar ya zama boka ya gama. Ko shekara bai yi ba ta sami wani cikin ta haifi Mubeen. Zuciyarta lokacin ta dangana da neman shiri da iyayenta, kwata-kwata sai ta shafesu a babin rayuwarta ta mayar da hankali wurin azurta kanta. Mubeen shi ne sanyin idaniyarta saboda yafi Aidan komai. Ga kyau ga lafiya. Da ya soma wayo da baki babu irin maganar da ba ya faɗawa Aidan ta rashin kunya. Wannan rashin shirin nasu da kuma aƙkawarin da Mammalo ya ɗaukarwa Tauhidat ranar da zata bar gidan yasa ya mayar da hankalinsa kan kula da Aidan. Alh. Audi da kansa ya bada umarnin Mammalo ya bar aikin komai sai na kula da jikan nasa. A ƙasa akayi ɗakunan yaran ɗaya na Mubeen ɗaya kuma na Mammalo da Aidan. Sai bayan shekara shida da haihuwar Mubeen din Susu ta sake haihuwa aka sami Juhaina.

*** BAYAN SHEKARU GOMA. Park Hotel Vitznau, Switzerland.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull