Cizon yatsa book 1&2 complete - Chapter 20
Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 20: Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 20. "Ku duba maganata da kyau" Alh. Audi ya ce da mutane talatin da huɗun…
9,111 words
"Ku duba maganata da kyau" Alh. Audi ya ce da mutane talatin da huɗun da suke tare a matsayin mabiyan Oga. Jiga-jigai ne waɗanda suka yi fice a fannoni da dama a Nigeria. Kowannensu ya kama ƙasa sai dai babu mai kuɗi da suna kamar Alh. Audi Karam. Ya yi wa sauran fintikau ya bar wawakekiyar tazara a tsakaninsa da wanda ake masa kallon na biyu a tafiyar tasu. Su duka sun taru ne a wani keɓantaccen ɗakin taro a cikin Park Hotel Vistnau, ɗaya daga cikin mafi tsadar hotels a ƙssar Switzerland. Alh. Audi ne ya gayyato su domin magana mai mahimmanci. Shiru ɗakin ya yi aka rasa mai cewa komai bayan ya zayyane musu ƙudurinsa. Bashi da niyyar haƙura saboda haka ya sake sabunta bayaninsa kada a samu matsalar rashin fahimta mai kyau. "Ni da ku abu ɗaya ya kaimu wurin Oga. Neman suna da arziƙi. Munyi sa a Maishare mana hawaye tana ƙaunarmu babu wanda aka bari a baya. Kafin kafuwar arziƙin da muke taƙama dashi yanzu waye bai sadaukar da jinin wani ko wata cikin makusantansa ba?" Kallonsu ya dinga yi yana ganin yadda jikinsu ya fara sanyi saboda ya harba kibiyarsa akan gaɓa Ba dai su ce komai ba amma alamu sun nuna zantuƙansa sun fara tasiri. Ya sami ƙwarin gwuiwar ɗorawa daga inda ya tsaya. "Oga ya tsufa sosai kuma muna buƘatar sabon wanda zai jagorance mu. Kada ku yi zaton wai ina magana ne akan kaina, ko ɗaya ba na buƙatar maye kujerarsa. Abinda nake so shi ne a cikinmu ya sanar da mutum ɗaya sirrin bautar Maishare mana hawaye ta yadda ranar da ya gaza kai mata kukanmu wani zai yi." Ɗan Anambra ne ya katse shi da cewa "Ɗan Kano kada ka manta cewa aƙidar ƙungiyar nan shi ne duk lokacin da Oga ya mutu watseta ake yi gabaɗaya. Mabiyan dake ƙarƙashinsa kowa ya kama gabansa sannan a sake sabon zubin wakilan kowace jaha da sabon Ogansu. Wannan abu shi yake bawa Maishare mana hawaye damar samun sababbin mabiya masu jini a jika." Sauran suka dinga gyaɗa kai suna gaskata shi. "Ban tari numfashinka ba" Alh. Audi ya ce ransa ya soma ɓaci "amma kuna ganin ya dace mu tafi a haka? Bayan duka wahalarmu da sadaukarwa yana mutuwa ace duk mu watse?" "Idan mun watse fa babu abinda zai taɓa dukiyarmu. Zamu matsa gefe ne kawai domin wasu su taso su maye gurbinmu." Cewar Ɗan Benue. Duk yadda ya so haska musu su amince a hamɓarar da Oga a bashi shugabanci abu ya faskara. Gani yake kamar idan aka watse ƙungiyar asirinsa zai tonu sannan zai rasa dukiyar da babu abinda yake ƙauna a duniya kwatankwacinta. Da yaga babu wata mafita sai ya wayance ya mayar da abin wasa tare da roƙonsu da su riƙe maganar kada Oga ya ji. A zahiri sun nuna masa cewa zai samu haɗin kansu wurin rufe maganar sai dai zuciyarsa bata kwanta da hakan ba. Da wannan tararrabin ya kwanta yana tunanin hanyar da zai bi ya toshe bakunansu. A daren ranar Oga ya sami cikakken bayani game da shirin Alh. Audi. Kuma dama duka wasu shirye-shiryensa tun kafin su bar ƙasar ya sani. Shi yasa ya riga shi fara nasa aikin da kwana biyu. Girma ya kama shi ya tsufa amma alƙawari ne kafin ya bar duniya sai ya lalata duka wani shirin da yayi masa. Ba tun yau yake nadamar amsarsa a cikinsu ba. Ga kuma suna da ya yi da girman da ake bashi a cikin Nigeria da waje sun tsaya masa. Tunda aka kafa ƙungiyar ba a taɓa samun wanda ya yi kuɗi kamar Alh. Audi ba, amma kuma yafi kowa haɗama. Abinda ya samu kuma yake kan samu yaƙi isarsa. Idanunsa kullum gaba suke hange. Waya ya ɗaga ya kira wata namba ya bada umarnin abinda yake buƘata ayi kafin gari ya waye. Mutumin da zai yi aikin yana gama saurara ya tashi yaransa suka fita. A daren suka aiwatar da komai kamar yadda ya buƙata. Karfe huɗu da rabi na dare wayar Alh. Audi da yake ganawa da iyalinsa ta hau ruri. Tsaki ya yi ganin sunan Fanna. 'Uwar jaraba da naci' ya ce a ransa kafin ya fara tunanin me take so da ba za ta iya jira gari ya waye ba ta kira shi a wannan lokacin. Kukan da ya ji tana yi ne ya dan tsorata shi ya yi ta maza ya tambayeta abinda yake faruwa. "Gabaɗaya gidajen man ka da suke cikin garin nan sun kama da wuta." Zumbur ya tashi kamar wanda ya zauna akan allura. "Gidajen man wa?" Ya ce yana sharce gumin da ya soma tsatstsafo masa da tafin hannunsa. "Naka Alhaji, mun shiga uku. Ance mutane sama da hamsin sun mutu kuma wai don ma cikin dare ne." Ajiye wayar ya yi batare da ya kashe ba jikinsa na rawa. Gidajen man nasa ba irin wanda aka sani ba. Karam Oil a duk inda suke a faɗin Nigeria manya gine gine ne masu kawunan bada mai ashirin da huɗu. Banda haka an gina store babba cike da kaya sannan ga wurin gyara da fentin motoci. Guda goma sha uku ne a cikin Abuja kawai banda ragowar garuruwa. Kuma ya san cewa duk waɗanda suka mutu da wuya idan ba a buƙaci ya biya diyya ba. Ga na asibiti komai yawansu idan yana son kashe maganar suma shi zai ɗauki dawainiya. Banda wannan ma me mutane zasu zarga ace ba gida daya ba, duka a wurare daban daban su kama da wuta a rana ɗaya. Ko shi ya ɗora ayar tambaya bare su. Da duku-duku ya bar hotel ɗin aka kai shi airport. Ƙarfe uku a Nigeria ta yi masa. Jerin gwanon motoci shida ne suka zo ɗaukarsa. Kafin su ƙarasa gida sai ga waya daga Manajan kamfanin takalmansa na Switzerland ɗin. Mutumin kiransa ya yi yazo kamfanin da gaggawa ya faɗa masa ya koma Nigeria saukarsa ma kenan. "Ranka ya daɗe idan da hali ka dawo." "Ko ma meye a dakatar dashi ina da babban uzuri yanzu." Ya bashi amsa. Gwauron numfashi Manajan ya ja sannan ya ce "wuta ce ta kama a kamfanin har yanzu ba a gama kasheta ba. Ta cinye kamfanin duka ta soma bin gine-ginen da suke makotaka damu." Hanjin cikin Alh. Audi a take ya shiga murɗawa ya ce da PA a tsayar da motar. A gefen titi duka motocin suka tsaya ya fito. Masu tsaron lafiyarsa suka firfito ana son jin me yake buƙata. Gaban motar da yake ciki yaje ya finciko direban waje ya shiga mazauninsa. "Ku wuce gida kada wanda ya biyoni." Ya gargaɗesu. Daga haka bai tsaya bata lokaci ba ya cilla motar kan titi sai gidan Oga. Ƙaton gida ne na gaske domin a zahiri Oga ba ƙaramin dattijo bane a ƙasar. Masu gadi ya faɗawa sunansa aka yi sa a sun gane shi duk da bai taɓa zuwa gidan ba. Mamaki suke na ganin mutum kamarsa shi kaɗai ya tuƙo kansa. Haka dai aka yi masa iso har cikin gidan. Oga bai yi mamakin ganinsa ba don sai da ya yi ɓoyayyen murmushi kafin ya tunkare shi cikin tashin hankali. "Alh. Audi ya zaka zo gidana bayan ka san nan ba wurin haɗuwar ƙungiya bane. Tashi mu fita kada iyalina su zargi wani abu." Ƙofar falon Alh. Audi ya rufe da sauri ya durƙusa akan gwuiwoyinsa tare da haɗa hannuwan wuri guda. Hankalinsa a mugun tashe yake ko tunanin kirki ya kasa yi. "Oga kayi min rai, duk abinda aka faɗa maka rashin kyakkyawar fahimta ne amma ba haka nake nufi ba. Idan ka ce zaka horani ta wannan sigar zan shiga gagari." "To ai ni ka ɓatar dani Alhaji." Ya ce tamkar bai san me yake nufi ba. Alh. Audi sai ya shiga ruɗani ya ce, "maganar wuta fa nake maka da ta kama a gidajen mai da kamfani." Sai da Oga ya zauna sannan ya ce dashi. "ban san me yasa kake ta maganganun da bangane ba amma tun daren jiya naso kiranka ban samu ba. Wato Alh. Audi akwai gagarumar matsala da ta tunkaro ka." Kasa zama Alh. Audi ya yi jikinsa gabaɗaya ya saki saboda damuwa. "Matsala wace iri? Oga tunda ina da kai wace irin matsala ce za ta tunkaroni?" "Ɗanka Shamsu ya haɗu da yarinyar nan ..." "Wa? Tauhida? Anya kuwa bayan irin rabuwar da suka yi?" Oga yayi murmushi, firgicin da Alh. Audi ya shiga yana sanyaya masa rai. "Abinda Maishare mana hawaye ta nuna min kenan. Sun haɗu ta bashi wani abu da yasa kwanaki uku a jere bai yi fitsari ba. Idan baka manta ba TASHIN HANKALIN SHAMSU NA LALURAR DA MUKA SAKA MASA shi ne kwanciyar hankalinka akan dukiyar marayu da ka yi babakere a kai." Yawun bakinsa da yake ƙoƙaarin haɗiyewa ne ya tsaya a maƙoshinsa yaki wucewa. Samun lafiyar Shamsu daidai yake da rusa duk wata nutsuwa da kwanciyar hankalinsa. Yaushe zai manta mafarkai da gizo da yake ganin Ibrahim na yi masa masu ban tsoro? "Yaushe suka haɗu? Bai faɗa min ba Oga. Na ce a kasheta ka hana yanzu gashi tana neman kasheni." Oga da ya riga ya lalata aikin da ya yi akan Shamsu ya ce, "danka ya riga ya sami lafiya kuma ya kuɓuta daga duk wani shiri da zamu sake yi masa saboda abinda ta bashi mai ƙarfi ne. Duk da haka kada ka kuskura ka tambayeshi domin hakan zai sa ya soma zarginka. Abu ɗaya ya rage maka Alh. Audi...." Durƙusawa Alh. Audi yayi a gabansa tun kafin ya gama magana ya riƙe masa hannu. "Ko meye zanyi Oga, idan jinin wani ake buƙata zan bayar." Ja masa rai ya dinga yi yana cewa abu ne mai wahala da yake ganin ya yi masa tsauri da yawa. Sai bayan kusan rabin awa lokacin Alh. Audi har hawaye ya zubar sannan ya ce masa. "Jikanka na biyu Maishare mana hawaye ta buƙata." Ai ko gama sauka a kunnuwansa maganar bata yi ba ya ce ya amince. Ya iya bayar da waɗanda Mubeen bai kaisu matsayi ba a zuciyarsa a baya bare kuma shi. Dama Juhaina ce yafi so a cikin jikokin tunda ta tsira shikenan. Amma duk da haka a ganinsa gara ya bada maridin nan Aidan tunda dama ba lafiya gare shi ba. "Oga ayi min haƙuri na bada babban, sai nasa a sato yara ko goma ne a haɗa dashi." 'Bakin mugu' Oga ya ce kafin ya warware masa abinda ake buƙata wanda yasa lallai sai da Mubeen ɗin. Ya ɗora da cewa, "Shi babban da kake son badawa uwarsa ta riga ta biya fansar aikin da wani boka ya yi mata akan auren Shamsu da korar yarinyar nan dashi." A dlɗan razane Alh. Audi ya ce "kana nufin da asiri Suwaida ta shiga rayuwar Shamsu har take da ƙarfin halin bayar da jikana? Kuma da sa hannunta a abinda ya faru ranar da Tauhida ta bar gidan?" Yanayin fuskarsa a hankali ya koma tsantsar ɓacin rai ya ce "Idan kuwa haka ne lallai harda ita zan haɗa domin na riga na gama shawarar cizge Haj. Manga daga jikina dama." Bayanin abinda zai yi ya yi masa sannan ya ƙara da cewa "Kada ka manta idan kayi a wurin zaka bar yaron a kowane yanayi yake." "Me? In barshi asirina ya tono? To me akayi kenan?" Alh. Audi ya ce cikin tashin hankalin da ba zai iya kwatantawa ba. Ɗan guntun gemunsa ya kama yana murzawa cikin ƙasaita sanin cewa yanzu sai abinda ya ce. "Ban san me yasa kake son bin ƙwaƙwaf a duk umarnin Maishare mana hawaye ba." "Tuba nake Oga, gani nayi kamar..." "Ita da kanta ta bada wannan umarnin cewa ɓoye wannan abin shi zai zama sanadin bankaɗa sirrinka. Bayyanawa zaka yi kuma ka tabbatar Shamsu ne mutum na farko da za a zarga. Shi ya bata aikin saboda ƙin bin umarninka saboda haka dashi za a gyara. Sauran bayani zanyi maka idan ka shirya." Kasa amsawa Alh. Audi ya yi. Duk halin da ya jefa Shamsu saboda cikar burinsa ace kuma yanzu ma shi ne zai ɗauki nauyin wannan babban al'amari. Gaskiya da sake! Ficewa ya yi yana tunanin wasu hanyoyin na neman sauƙi batare da ya kuma cutar da tilon ɗansa namiji ba. *** Da gaske kwanaki suke ja kuma Shamsu ya dena fitsari. Susu kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha don tsananin murna. A satin tasa aka canja komai na dakunansu wuri ya koma tamkar ba shi ba. Wannan mayataccen zarni da warin an nemesu an rasa. A ɓangare guda kuma kullum da irin masifar da za a kira Alh. Audi a faɗa masa ta afkawa kadarorinsa. Alh. Ari da ya san komai ya shiga damuwa tunda a jikinsa yake tatsa ya dinga ingiza shi akan ya karɓi shawarar Oga kafin lokaci ya ƙure. Ranar da sati uku ya cika da faruwar waɗannan al'amura a rayuwar Alh. Audi ba shiri ya koma wurin Oga. Abubuwa suna cakuɗe masa ta kowace kusurwa. Banda tsoron talaucewa harda ta abinda zai biyo baya idan allura ta tono garma a gaba. Fanna tuni ta fara tattara abubuwan da ta tara a gefe ta miƙawa Alh. Ari saboda gudun ɓacin rana. Haj. Manga kuwa ko a jikinta wai an mintsini kakkausa. Ta mayar da hankalinta ne ga makarantarta da nemarwa Jamal magani domin raba shi da wannan bala'i na shaye-shaye da yake yi. Sai da Alh. Audi ya haɗa da turawa Oga wasu dattijai cikin ƙungiyar aka samu ya amince zai taimaka masa. Da farko nuna masa yayi cewa ya yi fushi tunda ya ja lokaci bai aiwatar da abinda aka umarce shi ba. Da murnarsa ya koma gida bayan ya yi masa dogon bayani. Da yake ya bada dukkan yardarsa ga shirka sai gashi a ranar Shamsu ya yi fitsari shi kuma ya wayi gari da labarin samun kwangilar miliyoyin kuɗaɗe daga asusun gwamnatin tarayya. Daga Shamsu har Susu a ranar sai da suka zubar da hawaye. Abin sai ya zarce ba a baccin dare ba duk inda ya zauna ya tashi sai danshi. Zuciyarsa na ƙuna ya kira Babansa ya sanar dashi shi kuma ya ce ya same shi a ɗaki. Tausayinsa ya riga ya bar zuciyar Alh. Audi tunda a zatonsa ya iya karɓar abu a hannun Tauhidat da ya janyo masa ganin bala'i a cikin sati uku. Can cikin ɗakin suka shiga ta yadda babu mai jin abinda zasu zanta. Ƙwalla ce fal a idanun Alh. Audi a lokacin da ya miƙawa Shamsu wani bakin ƙyalle mai zanen kan kwarangwal a tsakiyarsa. Shamsu yana buɗe ƙyallen ya yi wurgi dashi a tsorace yana tashi tsaye. "Baba meye wannan?" Ɗauko ƙyallen ya yi ya dunƙule shi ya sake saka masa a tsakiyar hannun sannan ya zaunar dashi hannuwansu a haɗe. "Kwanakin nan Shamsu ai kana kula da irin masifun da suke ta bibiyata ko?" Kai ya gyaɗa idanunsa akan ƙyallen yana son sake sakinsa a ƙasa. "Na bi malamai na bi ƴan tsibbu ƙarshe bisa dole na dangana da wurin wani boka saboda neman mafita." "Boka kuma Baba?" Shamsu ya ce a tsorace. Ƙwallar idanun Alh. Audi sai ta zubo ya ce "dole ce ta kaini. Baka san girman asarar da nayi bane a cikin sati ukun nan. Zuwan kuma ya yi amfani tunda an karya asirin da wani abokin hamayya ya yi min. Kafin na tashi Bokan ya sanar dani cewa wannan mutumin shi yake bibiyarmu tun farko ya yi maka asirin fitsarin kwance..." Buɗe baki Shamsu ya yi Alh. Audi ya dakatar dashi da hannu ya cigaba da magana. "Makarin lalurarka abu ɗaya ne kamar yadda ya faɗa min ya ce sai ka nemi ɗanka na biyu za ka sami lafiya." Duk da a zaune Shamsu yake sai da yaji kamar ya faɗo daga kan kujerar. Bakinsa har yana rawa da saƙeewa ya ce, "na nemi Mubeen in masa me Baba?" "Shi yasa kaga ina kuka" cewar Alh. Audi yana matsar ƙwalla. "Na gaji da ganinka a cikin wannan yanayin tun ƙuruciya har ka zama uba." A fusace Shamsu ya miƙe "in dai irin neman da nake tunanin kana nufi ne gara na mutu ba lafiya." Yana juya baya Alh. Audi ya tsayar dashi ta hanyar nuna masa inda ya tashi. Wurin jike yake da fitsarin da bai san lokacin da ya yi shi ba a dan zamansa a wurin. Ba ƙaramin tashin hankali ne ya bayyana a fuskarsa ba amma duk da haka bai tsaya ba ya fita yana kare jiki. Daga ranar kullum abin karuwa yake yi har ta kai ya soma zargin ko masu aikin ɓangarensu sun gane. Dena saukowa ya yi bare ya fita. Kullum yana daki ya rame sosai babu cin abin kirki. Ruwa kuwa sai da ya kwana biyu idan ya ji kishi cokali ɗaya yake kurɓa don ya jika makoshi. Amma duk da haka bai tsira ba. Idan fitsarin ya zo har ƙasa yake kwanciya. A rana ta huɗu Susu ta baro shi a ɗaki yana kuka sosai lokacin da za ta fita ɗauko masa abinci. Auren gabaɗaya ya fice mata a ka so take kawai ta rabu da alaƙaƙai ta huta. Ko a yanzu kasuwa ta tashi ɗankoli ya ci riba. Ƴaƴa uku ta haifa kuma biyu cikinsu maza ne. Dukiyar Karam ko ana ha maza ha mata suna da babban kaso mai tsoka. Bata hawo da abincin ba sai da ta kira Maibindi ta faɗa masa cewa tana so ya farraƙa tsakaninta da Shamsu. Aikin da ya yi ya haɗasu ya sake wani ya rabasu. Har ta gama faɗin buƙatarta bai amsa ba saboda muddin ya yarda to dolensa ya sakar mata da. Shi kuwa ya riga ya gama saka rai da cewa lokaci yake jira da zai ɗauko Aidan domin ya zama magajinsa. Zai warkar dashi ya koya masa sirrin bokancinsa. Sake nanata masa ta yi ta ƙara da roƙon lallai ya taimaka mata wurin karkato da zukatan iyayenta gareta. Daga kalmar 'To' bai ƙara cewa komai ba ya ajiye wayar. Tana zuwa ƙofar ɗakin Shamsu taji cikin kuka yana cewa ko meye zai yi indai zai sami lafiya. Sai kuma abinda ya ɗaukar mata hankali da ya ce, "A gama komai kafin biyu da rabi na dare gobe? Zan shigo yanzu dai kayi min bayani." Kaya yake sauyawa lokacin da ta shiga ɗakin. Tana tambayarsa ina zai je ya ce wurin Alhaji. Dangwarar da tray ɗin ta yi ta fice bayan dogon tsaki da taja masa. Bashi da lokacinta bare ya kula. A bayan gida suka haɗu wurin dabbobi ya faɗa masa abinda zai yi kuma ya tabbata ya daure fuskarsa da wannan baƙin ƙyallen a lokacin. Ba don zuciya naso ba ya karɓa ya kuma amince zai yi yadda aka ce. *** [2/23, 7:34 PM] Nasma: *** Hayaƙi shisha da taba ya cika ɗakin da wasu matasa biyar suke zaune a ciki. Ga warin giya da kwalabe yashe a ƙqsa babu masaka tsinke. Dukkansu a buge suke sai zantuka suke marasa ma'ana irin na mutanen da basa cikin hayyacinsu. Cikin ƴan shekarun nan tunda Jamal ya gama makaranta ya dawo saboda aikin Doctors without Borders da Arƙam yake tafiya lamuransa suka sake ɓaci. Da gaske Alh. Audi ya tasarma lalata rayuwarsa tunda ya sami labarin Haj. Manga tare da haɗin bakin Haji Lawalli suna shirin kaishi kotu akan raba aurensu. Kafin su gama nasu shirin domin ance mata sai ta yi da gaske kafin a sami alƙalin da zai yarda ya yi hukunci yadda take so shi ne ya sabunta aiki akan Jamal. Cikin ƙankanin lokaci da fara aikinsa a makarantar Haj. Manga ya koma mashiririci bashi da abin yi sama da afa ƙwaya ko busa hayaƙi. Har ciwo ya yi kwanan baya kamar ba zai tashi ba saboda hantarsa ta soma taɓuwa amma yana warkewa ya koma ruwa. Ya koma Tarantula ɗinsa harma da ƙari. Wata yarinya ce ta shigo a guje ta nufi inda yake kishingiɗe a gefen kujera yana busa shisha. Garin sauri har taka shi ta yi ya tashi a fusace ya taɗeta da ƙafa sai da ta faɗi. Rai a ɓace ta mioe ta soma magana, "aikin banza dama wurinka nazo tunda ka mareni kuma ka yiwa kanka" Hankalinsa na kan tukunyar shishar da ta tuntsire a ƙasa yace, "Kinfi kowa sanin bana gayyar mata saboda haka matsa ki bani wuri" Har ta juya za ta tafi sai ta dawo dai a wulaƙance ta jefa masa wayarta. "Wannan kuma fa?" Ya tambaya yana harararta. Sai da ta gama juya idanu da murguɗe-murguɗen baki ta ce, "duba mana dan rainin hankali." "Ke bafa na son rashin kunya. Sai na tattakaki a wuce wurin" Sauran samarin suka taso don ba ƙaramin aikinsa bane ya yiwa ƴar mutane duka. "Kai Tarantula ka dinga haƙuri mana" cewar Manniru ɗaya daga cikin sababbin abokan da ya yi bayan dawowarsa. Dogon tsaki yaja sannan ya fara karanta labarin da ta buɗo masa a shafin labarai. A kiɗime ya kalleta lokaci guda tasirin kayan mayen yana raguwa daga kansa. "Duk yaushe haka ta faru ban sani ba?" Ya ce jiki a sanyaye. Cikin nuna damuwa ta amsa masa da cewa yau ɗinnan ne aka wayi gari da tashin hankalin. Mukullin motarsa ya ɗauko ya yi waje yana tangadi. Yau kwanansa biyar a gidan shaƙatawarsa wanda ya saya ba tare da sanin Haj. Manga ba ko waya bai kunna ba saboda gudun kira daga gareta. Taimakon Allah ne kawai ya kaishi gida inda tun daga waje yake ganin cincirindon motoci da mutane kai kace maigidan ne ya rasu. Hular dake manne da wuyan rigar jikinsa ya kifa a ka ya samu ya zagaya ta baya ya shige ɓangarensa. A gaggauce yabyi wanka ya lalubo wani yadi mara nauyi ya saka kada ayi masa faɗan ƙananan kaya. Gashinsa da ya taru cunkus wanda ba ya tajewa duk a cikin gayu ya ɗauko mataji ya shiga sharcewa yana fidda kwallar wahala. Tunanin abubuwan da ya karanta ne ya dawo masa yaji kwallar gaske ta soma taruwa musamman akan rasuwar Mubeen. Yaron bashi da kunya ko kaɗan, mahaifiyarsa ta ɓata shi shiyasa ba ya shiga harkarsa amma duk da haka mutuwa tafi ƙarfin wasa. Ga Shamsu a asibiti, Susu a hannun ƴan sanda sannan an nemi Aidan an rasa duk a dare ɗaya. Tabbas al'amarin da ya same su ba wanda zai iya kawar da kai bane saboda rashin jituwa tsakaninsu. Ya san zai sha faɗan Nanna ma don dole ta neme shi a cikin kwanakin da baya nan. Ba irin magiyar da bai yi ba akan ta bari ya koma gidan da ta gina a jikin makarantar taƙi. Shi kuma yana buƙatar kaɗaicewa daga jama'a idan zai sha kayansa. Wannan dalilin yasa shi sayen gida bata sani ba. Ya fito yana rufe ɗakinsa yaji hayaniya daga bayansa. Turus ya yi ganin Alh. Audi da Alh. Ari tare da jami'an tsaro suna ɓullowa ta gefen makeken swimming pool ɗin da yake kusa da ɓangaren. Har ƙasa ya durƙusa a ladabce yana kwasar gaisuwa tare da jajanta wannan iftila'i da suka wayi gari a ciki. Cikin fushi Alh. Audi yace, "Jamal ina ka shiga kwana biyar ana nemanka ko a waya ba'a samunka?" Nan ya soma susar ƙeya irin na marasa gaskiya,"Uhmm, uhmmm dama...." Alh. Audi ya sake harzuƙa, "kada kayi min ƙarya mutumin banza. Kana can kana asarar rayuwarka da shashanci gidanku ba lafiya baka sani ba" Inspector Badawi ya yi gyaran murya yana ɗan matsowa gaba, "Alhaji muna buƙatar gabatar da abinda ya kawomu" Hular kansa ya cire yana fifita kamar gaske, "Wai dame kuke so naji ne? Me yaron nan ya yi da zaku ce kunzo tafiya dashi shi kuma?" Daidai nan Haj Manga ta shigo sanye da hijabi an samu wata cikin ƴan zaman makokin ta ga zagayawar su Alh. Audi da ƴan sanda ɓangaren Jamal ta sanar da ita. "Wane yaron za'a kama?" Jamal ya nuna mata lokacin da Inspector Badawi ya ɗauko ankwa tare da kama hannunsa. "Jamal Tarantula you are under arrest. Ana tuhumarka da haɗa baki da Suwaida Musa wurin sace makuɗan kuɗaɗe daga asusun ajiyar Karam Holdings." Haj Manga bata san lokacin da ta fizgo hannunsa daga riƙon ɗan sandan ba ta soma faɗa. "Wallahi ƙarya kuke ɗana ba ɓarawo bane. Yarinyar da ko inuwarta baya ƙaunar gani zaku ce ya hada baki da ita. Alhaji kace su bar gidan nan kafin rayuka su ɓaci" Alh Audi tunda yaji abinda ɗan sandan ya faɗa ya dafa kujera saboda jirin ƙaryar da yake barazanar kwashe shi ya ɗago baki na rawa ya kalli Jamal. "Jamal da kai za'a haɗa baki a cuceni saboda dukiya? To gashi nan kunyi sanadin mutuwar Mubeen, yayanka kuma yana kwance rai a hannun Allah ina tsammanin kamaku ya yi ta caka masa wuƙar. Shi kuma Aidan ko ina ku ka kai min shi oho." Sakin baki Jamal ya yi da ya rasa kalmar da zai yi amfani da ita ya kare kansa ko ya maidawa Alh. Audi martani. Ankwa aka kama hannuwansa za a maƙala ya fizge cikin fushi tare da kai wa ɗan sandan shaƙa rai a matuƙar bace. Kansa sauran suka yo zasu ƙwaci ɗan uwansu ya ji muryar Nanna cikin nutsuwa babu faɗa bare hargagi. "Jamal ka nutsu ka bisu ba na son rashin hankali." Dena kokawar ya yi ya ce,"na bisu fa ki ka ce Nanna? Wallahi duk abinda aka faɗa ƙarya ne." Ɗaure fuska ta yi ta kama hannuwansa ta haɗa wuri guda ta tura gaban Inspector Badawi. "Ga Jamal nan ku tafi dashi amma wallahi ko yatsansa ne ya yi ciwo a hannunku sai na nuna muku cewa Hafsatu Manga ba kanwar lasa bace." Jamal ya san cewa bashi da wata mafita sai ta barin komai ga Allah da yarda da mahaifiyarsa. Ya tabbata ba zata taɓa bari a cutar dashi ba. Ƴar nutsuwar da ya samu a hanyarsu ta fita daga gidan ita ce tunawa da ya yi cewa yana da shaidu wadanda suke tare dashi a gidansa tsawon kwanakin nan. Ɗaya bayan ɗaya kowa ya bar wurin ya rage Haj. Manga, Alh. Audi da Alh. Ari. Kallonsu ta yi su biyun ta yi murmushi sannan ta kaɗa kai ta yi gaba. "Me ka ke tunani game da saurin sallamarwarta Alhaji?" "Burga ce kawai don kada na zata ta karaya. A yadda na santa na tabbata ɗaki za ta shiga ta yi kuka." Alh. Audi bai yi kuskuren fahimta ba domin kuwa ɗakin Haj. Manga ta shiga ta rufe kanta tasha kuka. Sai da ta yi mai isarta ta shiga banɗaki ta yi wanka ta fito ta canja kaya. Shiga ta yi ta alfarma babu yadda za ayi ka ce tana tare da damuwar da take neman taɓa mata zuciya da ƙwaƙwalwa. Yanzu da da ba ɗaya bane ta tunawa kanta a lokacin da ta ɗauki mukullin motarta ta fito daga ɗakin. Bata da wani a samanta wanda za ta faɗawa halin da take ciki ya fahimceta yadda ya dace. Da baffanta yana nan shi kaɗai ne za ta saukewa nauyin zuciyarta ya ce ta koma gida ta kwanta zai yi komai domin kawar mata da matsalolinta. Yanzu kuwa da baya nan ita ɗin dai ce gatan ƴaƴanta. Rauni da gazawa ba nata bane. Sabon gidan nan nata ta wuce amma kafin ta ƙarasa ta kira manajan wani kamfanin interior decoration da suka saba ta faɗa masa ya turo mata wakilinsa tana son a gyara mata gida cikin sati ɗaya. ****** Aiki sosai yau ma ya kacamewa su Arƙam suna ta fama da masu cutar kwalara a ƙasar Yemen. Kamar kullum ya wuni a tsaye sai yamma ya tafi ɓangaren ɗakunansu. A hanya ya tsaya ya duba Ghassan sannan ya shiga ɗaki ya faɗa gado. Ƙarar wayarsa ce ta tayar dashi zaune ya ɗauka da sauri saboda kwana biyu kenan ba ya samunta da Jamal a waya. "Nanna" ya ce cike da shauƙi da farinciki mara misaltuwa. Muryarta babu wata alama da za ta fallasa me yake gudana a cikin zuciyarta ta ce, "Arƙam ka taho Nigeria a satin nan." Ɗif yaji ta kashe wayar kafin ya sami damar sake yi mata magana. Jikinsa ya yi sanyi sosai amma kiran da ta yi masa zuwa ƙasar haihuwarsa bayan shekara ashirin sai ya bashi wata irin ƙwarin gwuiwa. Cike da ɗoki ya fita zuwa ofishin Director Zhang domin sanar dashi uzuri ya taso masa zai tafi gida. ****** "Habaaaa Sir ba haka muka yi da kai ba, hutu ka bani zuwa monday fa" Tauhidat ta sami kanta da marairaicewa ogan nasu da ya kirata yana umartarta da ta taho office yanzun nan. "Na sani amma client ɗin ke yake buƙata. Barrister kiyi min wannan aikin na yi alƙawarin ruɓanya miki albashi" ya alƙawarta mata saboda matsuwarsa da amincewarta. Aidan ta kalla har yanzu bacci yake yi ta kashe wayar a hakan da zumbulin hijabinta ta fita bayan dogon gargaɗi ga Iyabo akan kada ta kuskura ta buɗe ƙofar gidan ga kowa. Tafiya take yi kamar takarda ta sauka ƙasa ta tayar da mota. Ta yi sa'a babu go-slow duk da lokacin tashi daga aiki ya gabato. Wane irin case ne da zai janyo a katse mata hutunta a wannan yanayi na tashin hankali da rashin sanin makama da ta tsinci kanta. Ras, ras taji gabanta yana faɗuwa lokacin da ta yi arba da jerin gwanon motoci masu tambarin suna KARAM a farfajiyar ma aikatar tasu. Gumi ne ya jika mata tafukan hannayenta da ƙyar ta iya parking ɗin motar ta fita. Me ya kawo motocin Alh. Audi nan ta tambayi kanta. Ko dai sun sami labarin Aidan yana wurinta shi ne aka biyota har wurin aiki? Cilla ƙafafu kawai take yi fuskarta ta faɗa lokaci guda saboda tsananin tashin hankali. Abokan aikinta ta gani suna murmushi aka yi mata rakiya har office ɗin shugaban nasu. Sai maganganu suke yi wasu cikinsu suna cewa ina ma sune aka zaɓa. Bata fahimci komai ba ta kama ƙofar da ƙyar ta tura saboda nauyin da ta yi mata a yau. Zuciyarta saura ƙiris ta ballo ƙirjinta ta faɗo lokacin da ta yi arba da Alh Audi Karam. Idanu a waje kamar zasu faɗo tana neman kalmomin bashi haƙuri da rashin sanin dalilin da yasa Mammalo ya kawo mata Aidan. Alh Audi a tsakiyar office ɗin ya tareta, kowa kawai gani ya yi babban mutum kamarsa ya taso shi ma cikin yanayin tsantsar tashin hankali ya riƙe hannuwanta duka biyu ya marairaice. "Ki manta da duk wata alaƙa da ta taba shiga tsakaninmu ki taimakeni ki fitar min da ƴaƴa daga zargi. Tauhidat ke kaɗai za ki iya taimakona." Jikinta sai kyarma yake ta kasa cewa komai saboda kullewa da kanta ya yi. Shugaban nasu da kansa ya miƙo mata wani file da sabon name tag ɗinta saboda wancan ya faɗi a turmutsutsun ƴan jarida a kotu jiya. "Barrister Oluwatosin Tauhidat Abayomi I am counting on you, idanun Nigeria suna kan iyalin Karam suna kanki." Ya ce yana bata wani girma na musamman. Kanta ne taji ya fara juyawa da ta karanto sunan Susu da Jamal a matsayin waɗanda ake son ta kare a kotu. "Me yake faruwa ne?" Ta samu ta ce da ƙyar kamar wadda ta haɗiyi ƙota. Kallon mamaki mataimakin shugaban nasu Mr. Badamasi ya bita dashi, "Ina tsammanin tun jiya kike bacci sai yanzu da ya kira ki ka farka ko?" "A'a" ta ce a daburce saboda mafaɗacin mutum ne shi. Cike da jin haushinta saboda kafin shigowarta ya yi naci har ya gaji akan a bawa ɗansa case ɗin amma kai da fata Alh. Audi ya dage sai Tauhidat ya ce mata, "Kina nufin da gaske baki san me yake faruwa a garin nan ba?" Ganin ta sake shiga ruɗani Alh. Audi ya ja hannunta ya zaunar da ita sannan a tsanake ya faɗa mata halin da su ka tsinci kansu a ciki tun tsakar daren jiya. Tashi tayi da sauri bayan ta gama jin komai tamkar wadda aka tsikara da allura idanunta sun rine sunyi jawur ta shiga girgiza kai, "Allah Ya jikan Mubeen amma kayi haƙuri Alhaji ba zan karɓi case ɗinnan ba." Mr. Badamasi kamar ya zuba ruwa a ƙasa ya sha don farinciki amma sai ya fake da ɓata rai "saboda tun zuwanki kullum ana yaba miki shi ne har ki ke tunanin kin kai matsayin da za'a baki aiki ki ki karɓa?" Shi Ogan tsabar mamaki da ƙulewa ma sun hana shi magana sai Alh. Audi ne ya dakatar da Mr. Badamasi lokacin da Tauhidat ta soma hawaye jikinta babu inda baya rawa. Duk da tana jin haushin abinda Jamal ya yi mata ranar da zata bar gidan da sharrin Susu amma ba sune suka tsorata ta ba. Zuwan Alh. Audi ɗin wurinta da yadda yake kwantar da kai a gaban jama'a ke bata tayar mata da hankali. Susu surukarsa ce amma Jamal fa ɗan Nanna ne matar da yake cuta shekara da shekaru. "Kada ka yi mata faɗa tana da damar yin haka domin sunyi mata laifi." Ita yake kallo idanunsa sunyi ciki ko ba'a faɗa ba kana kallonsa za ka gane yana cikin tashin hankali mai girma, "Ina baƙincikin roƙonki wannan alfarmar bayan irin cutar da Suwaida ta yi miki a baya amma ke kaɗai zan iya damƙawa amanar iyalina akan duk wani abu na shari'a. Na so zuwa makarantarku na baki haƙuri saboda ganowa da nayi sharri ta yi miki sai na fasa saboda bana son ki sake dawowa a sake tozarta min ke.Tauhidat da Allah na dogara da taimakonki..." Tari ya soma yi a hankali yana fitar da numfashi da ƙarfi ana yi masa sannu. Ita kanta Tauhidat saurin juyawa ta yi wurin dispencer ta ɗebo masa ruwa. Da ta kawo masa har lokacin tarin yake yi babu ƙaƙƙaautawa ya saka hannun babbar rigarsa ya kare bakinsa. Idanunsa duk sun firfito da ƙyar tarin ya tsaya ya cire hannun rigar sai ga dishi-dishin jini sannan ya faɗi. Cikin matsanancin firgici Tauhidat ta saki kofin tana tsoron kada wani abu ya same shi a ɗora mata. Waya PA ɗin ya kira sannan aka kwantar da Alhaji akan kujera. Jikinsa babu ƙwari ko kaɗan har motar asibiti ta iso aka shigo da ma'ikatan da likitansa zuwa office ɗin. Gabaɗaya jama'ar Write Right Associates sun shiga tashin hankali Alh. Audi Karam ya faɗi a ma'aikatarsu. Likitan ya nemi kowa ya fita bayan ya sanar dasu damuwa ce ta yiwa Alhajin yawa har ta ke neman taɓa masa zuciya domin daga asibitinsa ma su ke kafin su taho nan. Jigum aka yi a bakin ƙofar sai kallo mai ma'anoni daban daban da ake jifan Tauhidat dasu. Basu daɗe ba likitan ya leko ya kira sunanta ta tashi da sauri ya shigar da ita ciki. Murmushi ya yi mata a wahale sannan ya sake maimaita rokonsa gareta. "Bana son sirrin gidana a hannun kowa sai naki ƴata. Ni da ƴaƴana mu ci albarkacin zaman tare" ya ƙare a raunane tare da yunƙurin danne tarin da ya taso masa. A tsorace take dashi amma duk da haka sai ta sami kanta da amincewa ko don Jamal, "in sha Allah na karɓi case ɗinnan." Farincikinsa a bayyane yake tana ganin yadda ya lumshe idanu a wahalce sannan ya bada umarnin a shigo da PA ɗinsa domin ya sanar da ita inda Suwaida da Jamal su ke sannan a bata duk wani taimako da zata buƙata. Hatta Commissioner an kira shi an sanar dashi zuwanta Louis Edet House gobe da safe domin ganawa da waɗanda ake zargin. Bayan fitarta likitan ya soma yi wa Alh Audi faɗa akan sanya damuwa a ransa har ciwon zuciya na neman kamashi. "Jininka ya hau fiye da ƙima Alhaji na gaji da faɗa maka rayuwarka ba a neman kuɗi kawai za ta kare ba dole ka kula da lafiyarka" Murmushi ta yi kafin ƙofar ta gama rufewa saboda jin muryar Alhajin yana bada haƙuri. Bata san ainihin abinda ke zuciyarsa ba amma tana da yaƙinin ko ta yi rantsuwa ba kaffara cewa ba don Jamal yake yi ba. Akwai wata a ƙasa dai. Office ɗin Mr. Badamasi ta wuce kai tsaye suna jiranta shi da Ogan su. Tambayar farko alaƙarta da Alh. Audi su ka nemi sani taƙi cewa komai sai amincewarta da karɓar case ɗin kawai ta faɗa musu da neman ayi mata uzuri ta koma gida gobe za ta dawo da sassafe. Tunani barkatai babu wanda bai ɗarsu a ranta ba, har ta isa gida. Tana zuwa Iyabo ta miƙa mata wayarta da ta bari akan kujera da missed calls ɗin yayanta ashirin da ɗoriya. Yawu mai dlɗaci ta haɗiya kafin ta kira shi. "Broda Mi." Ta iya cewa cikin sarƙewar murya kafin kuka ya kufce mata. Saurin barin falon ta yi saboda kallon da Aidan yake yi mata kamar zai yi kuka shi ma. Saheed sauraronta ya yi ta gama kukan sannan ya soma rarrashinta. Ya sani ko yaya ta ji wani abu da ya shafi gidan Alh. Audi sai yayi mata fami akan ciwon da zaman gidan ya haddasa musu take boyewa da yawan murmushinta. Da ya fuskanci nutsuwa ta saukar mata ne ya fara cewa kada ta kuskura ta shigar da kanta wani abu da ya danganci gidan. Hatta gaisuwar Mubeen bai yarda taje ba. Ana wata ga wata ta ayyana a zuciyarta. Bata boye masa zuwan Alhajin office dinsu ba amma ya toshe kunnuwansa inda ya ja mata kunne da kakkausar murya akan irin saɓawar da zai yi mata idan yaji labarin ta je ganin waɗanda ake zargi. "Idan abin zai zo da matsala ki rubuta takardar barin aiki ki kai musu kina jina? Ni zan iya ɗaukar duk wata ɗawainiyarki. An mayar da Mama (surukarsa) asibiti ɗazu bai kyautu nayi nisa da Sariat ba da a yau ɗinnan zan dawo. "Nace musu zanyi Broda", Ta sanar dashi yadda al'amura su ka gudana. Ɗaga murya ya yi har sai da ta tsorata, "ki kaiwa Iyabo wayar." Iyabo ɗin ta bawa bayan ta gama yi mata alamu da hannu akan yin shiru da maganar Aidan. Sabuwar amanar Tauhidat ya bata ya ce mata ko bakin bene ta barta ta fita a bakin aikinta. Ta tabbatar da kula masa da ita zai yi ƙoƙarin dawowa da zarar jikin Mama ya yi sauƙi. Ɗaki ta koma bayan sun gama wayar ta kunna ɗaya wayar ta shiga duba kafafen sada zumunta da shafukan labarai. Ko ina zancen gidan Alh. Audi Karam dai ake yi kamar gobarar daji. Iya tunani ta yi akan maganganun yayanta sai dai haka kurum take jin ba za ta iya yin baki biyu ba. Abubuwa da dama sun faru a baya marasa daɗi wannan dama ce guda ɗaya ta samu da za ta sake komawa jikin Alh. Audi domin gano ma'anar sakon da Papa Abayomi ya bar mata. Sannan idan ta yi sa a ta daidaita da Nannanta da rabuwarsu ta bar mata katon giɓi a rayuwa. Muskutawa ta yi hannunta yana dafe da goshinta ta cigaba da tunanin yadda za ta yi amfani da wannan shari'ar ta cimma burinta. Ɗazu tsoro ne da ɓacin rai yasa har ta yi gangancin kin amincewa, da Alh. Audi ya haƙura ai da ba ƙaramin dana sani za ta jefa kanta a ciki ba. A hankali ta furta, "Kowa da ranarsa" ta tashi ta koma falo da kuɗi a hannu. A cinyar Iyabo ta zube su dubu goma sha biyar. Firgigit Iyabo ta dago tana kallonta da neman ƙarin bayani. Sai da ta yiwa kanta mazauni a kusa da Aidan sannan ta ce, "zan koma bakin aikina gobe amma ina so ki dage sosai wurin kula min da yaron nan. Idan Broda Shaheed ya kira ki kada kiyi masa ƙarya idan na fita. Zancen yaron ne kaɗai ban yarda kiyi ba har sai na gano abinda ya kamata nayi dashi." A sanyaye Iyabo ta ce, "Madam Tauhidat kin canja daga dawowarki. Indai don nice kada ki damu ba zan ce komai ba, maganar da ku ka yi da wanda ya kawo shi ba komai na gane ba amma a hausar da nake ji kamar ya ce yaron nan yana cikin matsala ko?" Domin ta ƙara shigar mata da abin ta sake raunana murya, "Haka ya ce, rayuwarsa tana cikin hatsari kuma kinga ba ya magana sannan Mammalo ya tafi, sanin ainihin abinda ya faru sai na koma aiki." Tausayin Tauhidat ne ya kama ta, "Ba zan ci amanarki ba, ni dai ki koma mai sakin fuska wadda tukwane su ke girgiza idan ta shiga kitchen." Ai kuwa ta yi nasarar fito da haƙoran Tauhidat ta kama murmushi. Iyabo tashi ta yi domin aikace aikacenta ta barsu a falon da Aidan. Zaune yake anyi masa kariya da filo hagu da dama sai dai a gicciye yake saboda rashin ƙwarin jiki. "Ka sanni ni?" Ta tambaye shi. "Eeeeehhhh" shi ne amsar da ta fito daga bakinsa tare da murmushi yana yin sama da kasa da kansa. "Mammalo yana baka labarina kenan." "Eehhh" ya koma cewa. Hira ta dinga yi masa ta mayar da kanta kamar wata yarinya. Tana ta bashi labarai yana dariya. A hankali ta canja akalar hirar cikin nutsuwa. "Me yasa Mammalo ya ɗauko ka daga gida?" Alamun tsananin firgici ta gani a fuskarsa ya soma kuka yana waige-waige. Hakan ba ƙaramin sake ɗaga mata hankali ya yi ba. Kenan akwai alaƙa tsakanin ɗauko shi da Mammalo ya yi da laifin da ake zargin su Susu. "Ka ga wani abu ya faru a gidan kafin ku taho?" Sautin kukansa ne ya ƙaru sosai jikinsa yana ta jijjiga ta tashi a tsorace. Iyabo ta kira ta zo ta taimaka mata su ka kaishi ɗakinta. "Ka dena kuka babu mai taɓa min kai a nan. Ina da ƙarfi kamar spiderman da superman ai ka sansu ko?" "Eeehhh" ya ce da ɗan murmushi. Bata sake tayar da zancen ba ta cire masa kaya ta yi masa wanka da taimakon Iyabo ta saka masa wasu kayan baccinta riga da wando na cotton. Laptop ɗinta ta kunna ta nemo masa cartoon a youtube ta koma tunanin gobe. ****** Duk yadda Arƙam ya yi zaton al'amarin tafiyarsa zai kasance ya wuce haka. Na farko dai dole ya jira sati mai zuwa a turo madadinsa sannan kuma samun fita daga ƙasar ma aiki ne mai zaman kansa. Ƙwarai ya shiga damuwa domin sam ba ya ƙaunar abinda zai sa Nanna ta canja shawara akan zuwansa gida. Ingarman namiji mai cikar zati da haiba Dr. Arƙam ya zama irin mutanen nan ne masu kwarjini da ɗaukar hankali. Idan babu sabo a tsakaninku kai tsaye magana dashi ta kan bawa mutane wahala musamman waɗanda suke ƙasa dashi a shekaru. Baƙi ne ma'abocin yalwar gashi a kai da jikinsa. Yana da saje da ya haɗe fuskarsa zuwa gemu da gashin baki. Baya aske gemun duka a lokutan gyaran fuska sai dai ya rage ya daidaita shi. Kusan babu abinda yafi samun kula a jikinsa kamar gashin fuskarsa wanda yake mazaunin kariya babba a gare shi saboda ɓoye kansa da yake yi ga mutanen da suka san shi a matsayin mawaƙi. Wayar da su ke amfani da ita wurin ganawa da ƴan uwansu likitoci ce ta soma wata ƙara a hankali kafin ya fara jin ana kiran sunansa da na wasu likitocin. Director Zhang ne mai maganar cikin tashin hankali, yake sanar dasu zubewar wani gida mai hawa shida a kusa da inda aka yi ɓarin wutar jiragen sama shekaranjiya mutane da dama sun mutu wasu sun jikkata suna buƙatar taimakon gaggawa. A gurguje su ka ɗauki jakunkunan aiki da ake saka kayan buƙata na gaggawa domin irin wannan fitar. Ginin babu nisa sosai da asibitinsu kuma ga rashin kyawun titi ana ta kwashe bululloka daga hanya shiyasa su fitowa su ka hau gudu da ƙafafunsu. Abinda su ka tarar akwai tashin hankali sosai. Ƴan agaji da ƴan kwana kwana sun zo ana ƙoƙarin kashe wutar da ta tashi a wurin ga hayaƙi da ƙurar ƙasa tun daga nesa ake gani. Kafin su isa face mask mai ƙwari ta roba mai taimakawa numfashi suka dinga sakawa domin kare kawunansu daga shakar gurɓatacciyar iskar da ta mamaye wurin. Babu sanya wurin ma'aikatan lafiyar aiki suke yi da jikinsu duk da hatsarin da yake wurin amma burinsu tseratar da rayuwar da yawa cikin mutanen. Yayin da ake ta ɗiiban wasu zuwa asibiti akwai waɗanda dole a wurin za'a fara basu taimako saboda halin sa su ke ciki. Bayan an ƙare ɗauke marasa lafiyan da su ke a sarari ƴan kwana-kwana su ka shiga daga gini domin fitar da masu raunin da gini ya rufe su a cikin kasa. Arƙam yana cikin waɗanda basu koma asibitin ba saboda sauran mutanen wurin. Tafiya su ke yi shi da wani mutum cikin masu taimaka musu yana tambayarsa ko akwai hanyar da za su iya leƙawa cikin taron bulo da ƙasar wurin domin tabbatar da babu sauran mutane yaji shiru mutumin bai amsa ba. Juyawar da zai yi ya ganshi riƙe da wuyansa da hannu biyu yana kokawa da numfashi yayinda fatar jikinsa ta soma sauya kala tana yin facin ja sai ya faɗi a cikin fasassun bulon. Arƙam da ganin haka ya sauke jakar bayansa ya duƙa akan mutumin yana haska fuskarsa da torchlight. Laɓɓan mutumin sun fara kumbura cikin ƙanƙanin lokaci numfashi na neman suɓuce masa. Nos namiji ne ya rugu domin taimakawa masa. Yana durkushe ta saitin kan mutumin ya ɗora kan nasa a cinyarsa da take tanƙware ya faɗawa Nos ɗin me zai miƙo masa daga jakar da sauri. "Miko min epinephrine" Nos ɗin ya zaro idanu a lokaci guda yana laluben allurar da Arƙam yake buƙata. "Doctor ta ƙare." Yace cikin tashin hankali domin ya gane me ya sami mutumin. Da ƙarfi Arƙam ya yi magana yadda sauran likitocin da su ke kusa zasu ji shi "Ina da anaphylactic shock patient muna buƙatar epinephrine injection." Yana maganar ne lokaci guda ya tura wani ƙarfe ta cikin bakin mutumin ya danne masa harshensa da ya kumburo ya hana iska wucewa. Shi kuma Nos ɗin ya ɗaga ƙafafuwan mutumin ya ɗora akan wuyansa domin a samu wucewar jini. Komai cikin sauri su ke yi kada su rasa shi gabaɗaya. Paramedic irin masu fara duba marasa lafiya a motar asibiti ne ya kawo allurar ya yiwa mutumin shi kuma Arƙam yana ta duba jikinsa domin gano dalilin faɗawarsa cikin wannan yanayin. Duk wani abu da zai iya tunani a matsayin silar ya duba bai gani ba. Sai da aka ɗauki mutumin akan abin daukar marasa lafiya sun fara tafiya ya hango hannunsa ɗaya yana lilo inda ya kula da safar hannunsa ta robar latex. Cikin sauri ya miƙe zai bisu saboda sun fara nisa kuma ga wani turnuƙun ƙura da hayaƙi da ya taso ba ya ganin gabansa sosai amma a haka yake gudu yana jefa ƙafafuwansa duk inda ya samu. Bai yi aune ba ƙafarsa ta burma cikin wani tumulin ƙasa ya miƙa hannu ya riƙo wani ɓangaren gini saboda kada ya faɗa gabaɗaya. Idanunsa su ka hango masa wata mata a ƙarƙashin ƙasar gabansa wani abu kamar rodi ya danne mata ƙafafu. Ƙasar wurin ya shiga korewa da hannuwansa cikin sauri yana ji ana kiransa cikin wannan turnuƙun ƙurar ya kasa amsawa saboda azabar ciwon da yake ji a ƙafarsa da ta maƙale. Wani irin murmushin farinciki matar ta yi lokacin da ta soma hango alamun haske yana ɓullowa, "Ku taimaka min" ta ce da larabci tana tari saboda ta shaƙi ƙura da hayaƙi mai yawa. Arƙam da ƙyar ya ke kore ƙasar wurin ya kula da ƙaton cikin da yake jikin matar nan ga ƙafa babu damar motsawa. Mask ɗinsa ya cire batare da tunanin komai ba sai son ya ceci rayuwarta da ta abinda yake cikinta ya cilla mata. "Ki rufe hancinki yanzu za'a zo taimaka mana." "Kai kuma fa?" ta faɗa lokacin da take rufa abin a fuskarta. "Kada...ki, ki ...damu dani." Maganarsa soma katsewa ta yi saboda wahalar numfashin da yake yi. Iskar wurin ko kaɗan ba mai kyau bace. Wani iri ya soma jin kansa kamar yana kan gajimare. Fuskar Nanna ce take yi masa yawo yana ganin kamar ita ce a gabansa. "I love you Nanna." Ya ce muryarsa tana yin ƙasa. Matar da take ƙasan ramin tana jiyo shi ta yi tunanin ya fara sambatu ne kamar yadda ta yi ɗazu da numfashinta ya kusa ɗaukewa. Tattaro ƙarfinta ta yi tana kiransa a tsorace. "DOCTORRR." Can kuma ana nemansa saboda ƙurar ta yi yawa suna son komawa asibiti da iya waɗanda aka samu. Idan ƙura ta lafa ƴan kwana-kwana su cigaba da tona wurin ko akwai wasu masu rai. Nos din da su ke tare ne ya tuna ya baro shi a inda aka ɗauke mutumin yana haɗa kayan jakarsa ya koma tare da wasu mutum biyu. Muryar matar nan ya ji tana cewa doctor can ƙasaƙasa nan su ka garzaya a guje. Arƙam yana kwance turbuɗe da ƙura ga ƙafarsa a rami. Har yanzu ba ya cikin hayyacinsa amma yana jin hannuwa a jikinsa ana zaro masa kafar ya fizgo mutum ɗaya kusa da bakinsa. "Latex...latex a cire masa latex" Kasa ƙarasawa yayi Nos ɗin ya soma jijjiga shi, "Doctor stay with me." "Latex." Ya maimaita a ransa yana ƙarasawa da a cirewa mutumin nan latex gloves ɗin hannunsa amma a zahiri ya kasa faɗa. Har aka kusa isa asibitin latex yake cewa cikin magagi kamar an yiwa Nos dinnan ilhama ya ce,"mai anaphylactic shock za'a cirewa gloves?" Murmushin gefen baki Arƙam ya yi ya ce,"ka wahalar dani" Sannan ya rufe idanunsa. Nos ɗin ma murmushi ya yi ya garzaya gadon da mutumin yake ya zare gloves ɗin. Tun a hanya ake neman abinda ya tayar masa da wannan ciwon wanda akasari yana faruwa ne idan jiki ya hadu da wani abu da baya so. Cikin ƙanƙanin lokaci hanyoyin shiga da fitar iska su ke samun matsala idan ba'ayi da gaske ba mutum ya rasa ransa. Abubuwa da dama su na kawo wannan matsalar musamman ga masu allergy idan mutum ya ci ko taba sinadarin da ba ya so. Latex yana ɗaya daga cikin abubuwan da jikin wasu mutanen suke da allergy ɗinsa. Ɗaki na musamman aka kwantar da Arqam kusan duka abokan aikinsa sun shiga damuwa musamman Director Zhang saboda tsayin lokacin da ya ɗauka kafin ya farfaɗo washegari. Yana tashi kuwa matar nan mai ciki ya fara zuwa dubawa da mutumin da ya kwana dasu a ransa. ****** Wanka Tosin ta yiwa Aidan ta bashi abinci da kanta sannan ta yi shirin tafiya office. Ta barwa Iyabo sallahun kula mata da shi sannan ta sumbaci kumatunsa tana durƙushe gaban gadonta inda yake kwance. "Idan na taso daga wurin aiki zan siyo maka sababbin kaya masu kyau da wheelchair." "Yeeyyyy." Ya faɗa haɗe da dariya yawu na zubowa ta gefen bakinsa ta goge da tissue. Ita ma dariyar tayi ta mike, "wato ka gaji da saka kayan mata, skirt zan siyo maka da dankwali" Aidan ya lanƙwasa kai ya ce ,"ahhhhhh a." "Wasa nake yi kayan maza zan siyo, Iyabo sai na dawo" ta ɗauki jakarta ta fita. Neman dauriyarta ta jiya tayi ta rasa lokacin da ta isa Louis Edet House babbar headquater din ƴan sanda a Abuja. Sai da ta nuna ID card ɗinta da sunan wanda aka umarceta da ta nema aka barta ta wuce bayan an kira shi a waya ya ce a nuna mata office ɗinsa. Yau ma shigarsu ta lauyoyi tayi. Dogon skirt baki da coat baƙa ciki ta saka farar shirt. Kanta kuwa baƙin hijab ne iya ƙirji mai ƙananun duwatsu silver kaɗan zagaye da ƙasansa. Kyakkyawar fuskarta ta nuna zulumi da damuwa amma haka ta daure ta shiga office ɗin ASP Najib da aka nuna mata. A tsaye yake tana shiga su ka gaisa ya ce ta biyo shi. Wani ɗan ɗaki ya nuna mata ta shiga ya sake fita sai bayan kimanin minti goma ya dawo. Suwaida da ta fice daga hayyacinta a kwana ɗaya kawai da ta yi a wurin ba ƙaramin mamaki bane ya kama ta lokacin da su ka yi ido huɗu da Tauhidat tana mata shu'umin murmushi. Saurin ja da baya ta yi rai a jagule ta wurgawa ASP Najib harara. "Wannan ce lawyer din da aka turo min?" Tauhidat ce ta amsa mata tana ɗage gira,"nice lawyer ɗinki Haj Suwaida zauna mana kinsan bamu da lokaci isasshe" "Wasa ku ke yi daga kai har ita" Suwaida ta ce cikin ƙaraji tana duban ASP sannan ta shiga nuna Tauhidat da hannu sama da ƙasa a wulaƙance, "babu wani dalili da zai sa wannan matar ta taimaka min" ASP ya ce, "Kinga ki nutsu wannan ita kaɗai ce damarki ta wanke kanki daga zargi idan ba so kike a yanke miki mummunan hukunci ba." Kasancewar ta kwana cikin ƙunci da ƙunar zuciyar, na rasa ɗanta mafi soyuwa a gareta bai hanata hango zuwan Tauhidat a matsayin lawyer ɗinta bazai kareta da komai ba sai ƙarasa lalacewar al'amura. Ba ta da niyyar zaman kurkuku matsawar mijinta yana da rai kuma ta yi amanna Tauhidat ba zata taɓa fitar da ita ta shaƙi iskar ƴanci ba. Kai ko ita ce Tauhidat ba za ta fitar da kanta ba duba da irin abubuwan da su ka faru tsakaninsu. Juyawa ta yi da hannuwanta cikin ankwa ta murɗa ƙofar za ta fita, "A iya sanina ina da ƴancin ɗaukarwa kaina lawyer" "Kina da shi sai dai kuma ba na jin kina da kuɗin biyansu" ASP ya bata amsa. "Me kake nufi da hakan?" "Ina nufin an rufe accounts ɗinki a safiyar yau kafin a gama bincike akan kuɗin da ku ka sata ke da Tarantula sannan duk wata kadararki anyi miki iyaka da ita." Ba shiri ta dawo Tauhidat ta taɓe baki jin tana cewa babu abinda ya taba haɗata da Jamal. Wani dogon bayani ta soma ɗaukowa ASP Najib ya zura hannuwansa a aljihu, "Suwaida Musa lokacinki ya wuce, Barrister zaki dawo gobe ne?" Murmushi ta yi ta gyaɗa kai sannan ta rage murya daidai kunnen Suwaida, "duniya kenan, yau gareka gobe ga waninka." "Kada ki wahalar da kanki ba zan taɓa yarda ki wakilceni don ki wulaƙanta ni ba" Sake rage murya ta yi, "Suit yourself...ohh and for your information akwai wani abu naki mai matuƙar mahimmanci a tare dani." Kafin Suwaida ta farga Tauhidat ta yi waje abinta ta barta da dogon tunanin me take nufi. ASP yana gaba aka buɗe musu ƙofa za'a mayar da ita cell, nan ta hango Inspector Badawi shi ma ya ganta ya ɗauke kansa yana bin ta da kallon ƙyama ya bar wurin da sauri. A nutse Tauhidat ta ke tafiya kanta a ƙasa tana bin bayan wani Sergent zasu je inda za ta gana da Jamal ta ji takun da bazai taɓa gushewa a ƙwaƙwalwarta ba daga bayanta. Tsayawa ta yi cak ta kasa ɗaga ƙafafunta har takun ya zo daf da ita.