Kenza eBookz

Cizon yatsa book 1&2 complete - Chapter 21

Cizon yatsa book 1&2 complete - Chapter 21

Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 21: Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 21. A gaban ta tsaya Haj. Manga ta tsaya ita kuma ta yi shiru tamkar ruwa…

2,452 words

A gaban ta tsaya Haj. Manga ta tsaya ita kuma ta yi shiru tamkar ruwa ya cinyeta har sai da Inspector Badawi ɗan jagorarta ya yi gyaran murya ganin sun ƙi yiwa juna magana haka kuma sun ƙi tafiya. Kowaccensu zuciyarta ta cika da murna da ɗokin ganin juna amma suna ɓoyewa saboda gudun abinda hakan zai iya haifarwa. "Hajiya mu ƙarasa kinsan fa lokacin da aka baki na ganinsa bashi da yawa." "Wurin wa zaki je?" Ta yi tambayar ga Tauhidat kafin ta amsa ta gyara tambayar, "ina fata ba wurin Jamal ki ka zo ba." Da ƙyar ta ɗaga harshenta muryarta tana ɗan rawa ta ce, "jiya Alhaji ya ɗaukeni a matsayin lawyer ɗinsu shi da Suwaida." Haj Manga matsowa ta yi ta ɗago kan Tauhidat da yake kallon ƙasa, "Tauhida kalleni nan, ni da ke mun san cewa ba za ki taɓa taimakon Jamal ba haka ne ko ba haka bane?" Hawaye ne cike da idanunta na baƙincikin yadda alaƙarsu ta koma a dalilin Alh. Audi. "Haka ne." Ta amsa ba tare da sakayawa ba ganin idanu a kansu. "Ki koma wurin wanda ya ɗaukeki kice ni mahaifiyar Jamal nace ba na buƙatarki na riga na ɗaukarwa ɗana lawyer. Kai Barrister zo muje" Ta yafito wani mutum da ya ke tsaye a gefe. Hawayenta ne ya so ƙwacewa ta daure ta miƙa hannu gareta, "Nanna...." Doke hannun Haj Manga ta yi tare da tsaki ta wuce ta bar Tauhidat tsaye tana kokawa da nauyin zuciya. 'Kiyi hakuri Tauhidana amma ba zan nuna amincewata kai tsaye ba bare Alh. Audi ya ƙirƙiro hanyar hanaki wakiltar yayanki a kotu. Ke kaɗai ce na yi imanin zaki iya wannan aikin da zuciya ɗaya.' Cewar Haj. Manga a zuciyarta bayan sun wuce. *** Yau sati biyu kenan da faruwar wannan al'amari da yafi kama da almara a gidan Alh. Audi Karam. A yau ne Shaheed zai dawo Abuja tare da Sariat bayan jinyar mahaifiyarta da su ka sha fama. Alh. Audi ya yi bakin ƙoƙarinsa amma Suwaida ta dage kan cewa da Tauhidat ta wakilceta gara ta je kotu babu lawyer a bata na gwamnati. A gefe ɗaya Haj Manga ta ɗaukarwa Jamal lawyer mai tsada wanda bai taɓa faɗuwa case ba. Rashin wannan aikin ne ya sanya Tauhidat mayar da hankalinta wurin kula da Aidan da neman Mammalo sai kuma fargabar yadda zasu kwashe ita da Shaheed idan ya ga Aidan a gidansa. A can Sanaa kuma babban birnin Yemen Dr. Arƙam ya ɗauki hanyar USA. Inda ya kasance ainihin wurin aikinsa shiyasa yana jin sauƙi ya yanke shawarar fara zuwa can ya ɗauki dogon hutu bayan ya miƙa report na aikinsa a Yemen sannan ya kama hanyar Nigeria. Kafin tashin jirginsu ya sanar da Abu Usama tasowarsu da lokacin saukar jirgin domin ya zo ɗaukarsa. Aikin Doctors without borders ɗin dama bisa shawarsa ya soma a shekarar da ya gama residency ɗinsa ya fito a cikakken general surgeon. Sakamakon faɗuwarsa a cikin ƙura da ƙasar nan da ya kwantar dashi ne aka aske masa ƙasumbar da yake tarawa domin kada a gane shi. Sunyi haka ne saboda ƙasar wurin tana tattare da sinadarai masu cutarwa. Ƙaramin hauka ya yi musu da ya tashi don tsiya-tsiya su ka rabu da Director Zhang sai a airport su ka shirya. Farar hula irin wadda bahaushe ke kira tashi ka fiye naci ya saka a kansa da mask ya kare rabin fuskarsa duk don kada a gane shi da ya sauka. Ya yi sa a kuwa har ya fita wurin parking babu wanda ya gane shi. Haka yake so dama don ko ya ya aka ganshi sai ya yi ta fama da masu son signing ɗinsa a agency ɗinsu. Shi kuwa ya yi alƙawarin dena waƙa har abada. Ta ƙarshe da ya yi wadda ya rubutawa Tauhidat ce a Saudiyya kuma bai fitar da ita ba. Tana ajiye ne kawai babu ranar da wadda ya yi dominta za ta saurara a tunaninsa. Gidan Abu Usama suka fara wucewa yaci abinci sannan ya kaishi nasa gidan. Washegari da wuri ya yi reporting a asibitin da yake aiki na Josh Hopkins sannan ya bada takardar ɗaukar hutu. A ranar aka kammala cike-ciken da za ayi masa. Bai samu matsalar komai ba saboda an san ba shi da wasa da aiki. Indai ba ka ganshi ba to yana wata kasar kai agaji. Ticket ɗinsa na zuwa Nigeria ya kama nan da kwana biyu bayan dawowar tasa. Shiri yake kamar mai barin ƙasar har abada ya haɗa duk wasu abubuwa da kayansa masu mahimmanci zai tafi gida. Kullum cikin fara'a yake. Haj. Manga bata faɗa masa dalilin kiran ba duk da suna waya kullum. Rashin samun Jamal da yake yi sai ya alaƙanta shi da shiriritarsa ce tasa ba ya ɗaukar waya.

*** Tsaye Tauhidat ta yi a gaban wheelchair ɗin da Aidan yake zaune yana kuka da yin ƴan sautukansa a madadin magana ta juya masa baya tana kallon Shaheed yana sauke mata ruwan masifa kamar zai cinyeta ɗanya. "Kin san irin bala'in da kika jawo mana kuwa idan aka gane yana gidan nan? Nemansa fa ake ruwa a jallo." "Broda..." Katseta ya yi rai a matuƙar ɓace ta hanyar ɗaga hannuwansa, "heyy kada ma ki fara kirana, babu wani daɗin baki da zaki yi min na yarda dake. Saboda rashin sanin darajar kanki wannan yaron da Suwaida ta haifa shi ne kike zubar da hawaye saboda na ce ba zai zauna min a gida ba?" Da ƙyar ya saurareta ta faɗa masa abinda Mammalo ya ce ranar da ya kawo shi. Maimakon ya sassauta sai ya ƙara tunzura. "Kina nufin an ma sanar dake cewa rayuwarsa tana cikin hatsari amma duk da haka ki ka ajiye shi a nan? Hahhh! shikenan bari na kira ƴan uwa na faɗa musu su fara kuka Shaheed da Tauhidat sun kusa mutuwa" Ɓacin ranta bai hanata guntun murmushi ba ta kamo hannunsa zuwa gaban kujerar Aidan. "Broda, ba ka taɓa hanani taimako ba sai yau. Yadda ka ce kada na karɓi case ɗin nayi sa'a da kanta taƙi amincewa. Buƙata ta ɗaya ce shi ne jiran hukuncin da za'a yanke mata kafin na san wa zan kaiwa yaronta." "Yanzu shi Mammalo da ya kawo miki shi duk fadin garin nan ya rasa gidan da zai kaishi sai nawa?" "Kayi haƙuri dai." Ƙara haɗe rai ya yi, "ki bani yaron nan na kaishi ƙofar gidansu na ajiye shi. Ko da wasa bana son wani abu ya sake hadamu da mutanen gidan nan. Ƙazafin zina fa akayi miki Tauhidat kuma ashe babu auren don wulaƙanci suka yi shiru." Gani ta yi sai komawa baya su ke akan magana ɗaya itama kawai sai ta haɗe rai. Allah ma Yasa da yarbanci su ke magana da yaya zai ji ana nuna masa ƙyama da ƙuruciyarsa? "Zan kama mana wurin zama kafin a gama shari'ar, kayi min haƙuri zuwa sati ɗaya ko biyu kafin na sami gida mu tashi." "Lallai Tosin kin girma. Ni kike faɗawa za ki kama gida saboda kinyi kuɗi kin fara ɗaukar albashi? To kizo ku tafi idan kin fita kada na sake ganinki a ƙofar gidan nan" Shaheed ya yi maganar cikin mummunan ɓacin rai. Ba nufinta kenan ba, tana ganin kamar tsoronsa kada a taɓa masa iyali ne shiyasa ta faɗi haka sai gashi ya fassarata da wata manufar. Durƙusawa ta yi a gabansa ta kama ƙafarsa tana kuka sosai da kalmomin ban haƙuri. A haka Sariat ta fito daga ɗaki inda ta kora yaransu saboda bawa wa da ƙanwa damar yin magana cikin nutsuwa. Haƙuri take taya Tauhidat baiwa Saheed da ƙyar ya sauko amma ya ja mata kunne sosai akan cewa ta nesanta kanta da gidan har su ga abinda hali zai yi. Taji daɗi sosai ta tashi ta rungume shi ya tureta da farko sai kuma ya sake janyota shima "ba wai son kiyi taimako ne bana yi ba, ina jiye miki tsoron shiga abinda yafi ƙarfinki ne. Na taɓa faɗa miki ina tsoron Alh. Audi? To wallahi tsoronsa nake ji sosai." Daga ita har Sariat tuntsirewa suka yi da dariyar yadda ya yi da fuska. Biye musu ya yi shi ma ya yi dariyar. Daga baya ya sake komawa yana jan kunnenta akan lallai ta kula sosai saboda harkar gidan tafi ƙarfinsu. "Na sani kuma zan kiyaye. Idan ka amince zan koma wurin Suwaida ko family ɗinta ne ta faɗa min inda zan kai mata shi. Na san ko meye yake faruwa ita dai ba za ta so wani abu ya sami ɗanta ba." Ɗan tunani Shaheed ya yi sannan ya ce ya amince gobe taje suyi magana shima hankalinsa zai fi kwanciya idan an raba shi da yaron. Bayan ta gangara Aidan ɗakinta tana yi masa hira shi kuma Shaheed ya shiga ɗaki Sariat ta ɗauko wayarta ta duba hagu da dama babu kowa sannan ta shige toilet ɗin cikin falon ta rufe da sauri. Numbar Haj. Manga ta kira ta rage murya sosai suka gaisa. Ƴan tambayoyi ta yi mata game da jikin mahaifiyarta ta amsa sannan ta faɗa mata cewa Aidan yana gidan kuma Mammalo ne ya kawo shi. "Mammalo? Tun yaushe??" Haj. Manga ta ce hankali a tashe da jin wannan zance. Abinda ya fara zuwa bakinta ta faɗa da sauri da ta tuna a gida ko office ɗinta na shugabar makaranta babu inda Alh. Audi bai sanya CCTV domin kula da shige da ficenta da maganganunta ba. Bata san tsahon lokacin da ya ɗauka yana bin diddiginta ba sai ranar da suka yi magana da Haji Lawalli akan zuwa kotu raba aure. A makaranta suka yi wayar kuma bata yi zancen da kowa ba amma tana zuwa gida ya tareta da zancen ya kuma ce ta jira abinda zai biyo baya. Tana da yaƙinin ba Haji Lawalli bane ya faɗa masa saboda bai taɓa sonsa ba tun farkon zuwansa daga ƙauye. Sanya Jamal cikin rikirkitaccen al'amarin iyalin Shamsu ya isheta shaida. Banda sauran abubuwan da ya dinga yi a baya waɗanda sai daga baya ta gane ta ina yake samun labari. "Yaushe Mammalon ya kwatanta miki gidan? Ni da na haifi Jamal ma ban san ya sayi gidan ba." Shiru tayi na dan lokaci ta bar Sariat da sakin baki sannan ta ƙara da cewa, "ki bar zancen nan a tsakaninmu bana son maganar ta fito ayi masa sharri ace da kuɗin da ya sata ya saya." Tana gama faɗin haka ta ajiye wayar jiki a sanyaye. Indai Alh. Audi ne ba jimawa zai gano inda Aidan yake kuma ta tabbata masu ɓoye shi ba zasu ji da daɗi ba. Ya zama dole ta bar wata rufa-rufa akan rayuwar Shaheed da Tauhidat ta matso dasu jikinta idan tana son basu kariya. *** Su biyu ne a bayan mota akan hanyarsu ta zuwa ganin Susu. Alh. Ari ne ya soma magana bayan Alh. Audi ya gama wayar da yake yi. "Wai ya zaka yi da yarinyar nan ne Suwaida?" Giyarsa ya ɗan kurɓa ya mayar da kwalbar da kofin ma'ajiyarsu a cikin limousine ɗin sannan ya bashi amsa da cewa, "ƙabarinta ta tona ba wani abu ba. Da farko sata kawai naso ɗora mata tare da Jamal saboda rainin wayon da ta daɗe tana yi min sai kuma ta kaini bango da ta cakawa Shamsu wuƙa. Wato Ari jini jini ne ko yaya yake. Na fifita kaina akan kowa amma duk da haka babu wanda ya isa ya taɓa min ɗa ya kwana lafiya." Da suka isa babu ɓata lokaci aka fito musu da Susu. Ta soma fita hayyacinta don ma Alh. Audi ya ce bai yarda a taɓa lafiyarsu ba ita da Jamal saboda family ɗinsa ne. Duk yadda ta zaci zuciyarta za ta ƙeƙashe idan ta ga Alh. Audi a matsayinsa na baban Shamsu abin bai zo mata da saukƙi ba. Tana ganinsa jikinta ya soma rawa don kallon da yake mata babu annuri ko rahama. Shi ya fara magana cikin isa da izza, "Suwaida har kina da bakin cewa ba kya son lawyer ɗin da na ɗaukar miki bayan abinda ki ka yiwa Shamsu? Kada ki manta daga ranar da ki ka zaɓi aurensa kika rasa gatanki." "Ta kuma watsa maka ƙasa a ido ba" cewar Alh. Ari. Bata ɗago kanta ba saboda mugun tsoron da ya sarƙe mata zuciya. Kashinta ya bushe ta riga ta sani amma fa ba zata yarda a kulleta sanadiyar kin kareta yadda ya kamata da take zargin Tauhidat za ta yi ba. "Kinga babu ruwana idan kina da kuɗin ɗaukar mai kareki abinda nake so shi ne ki faɗa min inda Mammalo ya kai Aidan." Bata san lokacin da ta ɗago kai da sauri ba, "Mammalo kuma? Ina ya kai Aidan ɗin? Ba sa gida?" Da faɗa Alh. Ari ya ce, "kada ki raina mana wayo mana. Tun ranar da ki ka yi yunƙurin kashe masa uba aka nemesu aka rasa." "Tana fita da Mubeen bayan ta cakawa Shamsu wuƙa shi ma ya ɗauke Aidan. Na zata ma ita ta ce su biyota." Zuciyarta ce ta sake ƙuntata. Bata da wani sauran gata fa a duniya yanzu. Iyayenta ƙila basu ma san me yake faruwa ba. Idan sun sani ma da wuya su taimaka mata. Sannan ta yi imanin basu da kuɗin ɗaukar mata lawyer. Abin ya yi mata yawa sai hawaye ba kakkautawa. Tashi Alh. Audi ya yi zasu fita ya ce, "Ki san yadda zaki yi Maibindi ya sakar min jika ko kuma na nuna miki zahirina wanda bana jin zaki iya ɗauka." Maganarsa tasa babu inda bai yi rawa ba a jikinta. A matuƙar tsorace take kallonsa tana mamakin a inda ya san Maibindi. Ficewa suka yi suka barta da faduwar gaba. Bayan tafiyarsu ne ta wuni tana kuka ko abincin da aka bata ta kasa ci. Ashe dama farinciki ya kan juye lokaci guda kaji kamar baka taba sanin me ake kira murmushi ba bare dariya? Barazanar Alh. Audi ta ɗauka har ƙoƙon ranta don idanunsa sun masifar tsorata ta. Ga mamakinta Inspector Badawi ne ya shiga cell ɗinta, shi da ba ya sakar mata fuska amma ya bata shawara cewa idan tana da gaskiya ko tana ganin an zalunceta ne kada ta kuma wasa da damarta. Idan Tauhidat ta sake zuwa ta amince ko ba komai za ta sami mai sauraronta. Su Alh. Audi na fita basu zame ko ina ba sai asibitin Dr. Madaki inda aka kwantar da Shamsu. An gama komai na shirin fita dashi daga ƙasar domin neman lafiya. Tunda aka kawo shi bai buɗe ido ba har yau. Wuraren da Susu ta caka masa wuƙa ba ƙaramar illa suke neman yiwa rayuwarsa ba. A haka Dr. Madaki ya ce masa da wuya ko ya tashi ya iya cigaba da rayuwarsa yadda ya kamata.

***

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull