Cizon yatsa book 1&2 complete - Chapter 22
Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 22: Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 22. Washegari sai da Tauhidat ta gama kimtsa Aidan yaci abinci sannan ta…
4,168 words
Washegari sai da Tauhidat ta gama kimtsa Aidan yaci abinci sannan ta haɗa shi da Iyabo da Sariat ta fita. Da Shaheed ya fito zai tafi nasa office ɗin ko kallonsa baiyi ba. Yadda mahaifiyarsa ta ɓatawa ƙanwarsa suna ba ya jin zuciyarsa tana da wannan ragwantar ta rungumar dan makiyinka da sunan haƙuri. Inspector Badawi yau shi ne ya kai Tauhidat ɗakin ganawa da Susu. Saɓanin yadda ta saba yau bata yi yunƙurin ficewa daga ɗakin ba da suka haɗa ido sai ma saurin isowa gaban Tauhidat da ta yi ta riƙe hannuwanta tana sharbar hawaye. Gara ta kwantar da kai ta nemi sasantawa da ita don komai kankantar damar da ta samu dole ne tayi amfani da ita. A firgice take kallon fuskar Susun wadda ta yi baƙi ta rame ta yi muzu-muzu da ita, babu kyawun gani. Susu kuma ta ɗaga kai ta kalli Inspector Badawi sai ta ga ya yi mata ɗan murmushi abinda bata taɓa gani ba ya gyaɗa kai alamun ta yi yadda ya bata shawara jiya. Sunkuyar da kai ta yi tana rike da hannuwan Tauhidat da mamaki ke neman sumar da ita. Ita kuwa nauyi ya sa ta kasa bata haƙuri sai dai ta sani ita kaɗai ce ta rage mata wadda za ta iya taimakonta. "Tauhidat za ki iya wakilta ta saboda Allah?" "Ni ɗin? Oluwatosin ce fa ƴar yarbawa idan kin manta." Sunkuyar da kai ta yi,"na sani amma ke kaɗai ce za ki iya fito dani daga wannan halin na nemo Aidan kafin shi ma wani abu ya same shi." Mantawa Tauhidat ta yi da duka gargaɗin Shaheed a wannan lokacin sai tunanin samun dama akan Alh. Audi. Abinda zai koro Susu gareta ba abin rainawa bane. Ƙara ƙarfin riƙon hannun Susu ta yi idanunsu cikin na juna ta ce, "zan iya amma sai kin amince kema za ki faɗa min gaskiya tsakanin ki da Allah. Me ya kai ki yunƙurin kashe mijinki?" Wannan tambayar ce ta saka Susu kuka sosai. Hoton abinda ya faru a wannan daren take gani yana gilmawa a gabanta ta yi zaman ƴan bori a ƙasa tana girgiza kai kamar hakan zai sa ranar gabaɗaya ta goge. Muryarta a shaƙe ta ce, "Fyade ya yi wa Mubeen. Tauhidat ashe Shamsu yana neman maza ban sani ba. Mazan ma ya rasa da wanda zai yi sai ɗan cikinsa." Kuka ta fashe dashi sosai jikinta yana wata irin jijjigawa sannan ta cigaba da cewa, "maganar Mammalo ya gudu da Aidan kuwa sai jiya nake ji. Sannan Alhaji ya ce mun haɗa baki da Jamal munyi masa sata. Wallahi bani da masaniya akan komai. Na san ina son kuɗi amma ko Shamsu ba zai ce na taɓa masa kuɗin da bai bani ba." Shawara Tauhidat ta dinga yi da zuciyarta akan ta faɗawa Susu cewa Aidan yana tare da ita ko a'a. Ƙarshe dai ta zaɓi ta yi shiru zuwa lokacin da za ta tabbatar da gaskiyar maganar Susu. Tashi ta yi daga kan kujerar da take zaune tana kallon Susu ta ce, "Ina miki ta'aziyyar Mubeen, Allah Ya jiƙansa. In sha Allahu zan dawo gobe sai ki yi min bayani sosai. Yanzu zan tafi saboda Alhaji ya kirani akan hanyata ta zuwa nan." Zuciyarta cike da ruɗani ta fita daga police station ɗin. Ba wai ta ƙaryata Susu bane sai dai bata gama gaskata ta ba. Da farko ta yi tunanin case ɗin zai hada ɗa Alh. Audi amma yanzu ta fara ganin kamar rigima ce kawai ta mata da miji. A case file ɗin da aka bata an nuna cewa hatsari suka yi da ta ɗauko shi a mota kuma shi ne sanadin rasuwarsa. Bata bar zuciyarta da ƙwaƙwalwa sun huta daga neman zaren kamawa ba har ta isa asibitin da aka kwantar da Shamsu inda Alh. Audi ya ce ta same shi. *** "Yanzu haka ta tafi ganawa da matar Shamsu ɗin amma ina ganin ba daɗewa za ta yi ba tunda Shaheed ya hanata karɓar case ɗin." Cewar Sariat bayan ta tabbatar ita kaɗai ce a ɗakinta kuma ta rufe ƙofa. Daga ɗaya ɓangaren Haj. Manga ta ce,"ki bar maganar case ɗin tukunna yanzu haka an bani belin Jamal na kaishi gida. Damuwata akan Aidan da yake wurinku ne." A tsorace Sariat ta tambayeta ko akwai matsala dangane da zamansa tare dasu. Ta kula jiya ta yi saurin canja akalar zancen da ta ambace shi. "Iyaka mu faɗa musu gaskiya. Yadda ake yawo da hotunansa da na Mammalo ɗin yana bani tsoro..." Bammm taji an turo ƙofar ɗakin da sauri daidai da suɓucewar wayar daga hannunta. Jikinta babu inda ba ya rawa da ta haɗa ido da Shaheed wanda ya dawo saboda mantuwa yana mata mugun kallo. A matuƙar fusace ya nufota ya kaiwa wuyanta shaƙa ta kufce tare da yin baya da sauri tana roƙonsa da yarbanci. "Kada kayi min muguwar fassara da Haj. Manga nake magana." <span [2/23, 7:34 PM] Nasma: *** Madaidaicin office ne mai ɗauke da tebura biyu a ɓangaren hagu da daman ƙofar shiga. Kowanne tebur akwai kujeru biyu ɗaya a gabansa mazaunin baƙi, ɗaya kuma a bayansa mai taya irin ta ma'aikata. Daga gefen kowace kusurwa a jikin bango durowa ce mai ma'ajiya shida duka ƙofofin da wurin saka mukullinsu. Mata biyu ne a ciki kowacce tana zaune a nata ɓangaren ga tarin takardu a gabansu. Hira suke yi cikin nishaɗi da harshen turanci, saboda kasancewarsu basa jin yaren juna. Zuciyar ɗaya cike da farincikin da ta kasa ɓoyewa take tattara tarkacenta tana turawa a jaka. Tashi tsaye ta yi tana dariyar wani abu da abokiyar aikinta ta faɗa, wanda ya yi sanadiyar bayyanar kyakkyawar wushiryar da take ƙawata fuskarta a duk lokacin da haƙoranta su ka bayyana. Sanye take da coat da dogon siket har kasa baƙaƙe ta rufe kanta da ƙaramin hijabi shima baƙi wanda ya zarta ƙirjinta da kaɗan. Kyakkyawar mace ce wankan tarwaɗa mai matsakaicin tsaho da ƴar ƙiba. Ƙatuwar jakarta mai ɗauke da laptop da sauran takardu ta rataya a kafaɗarta sannan ta ɗauki waya da mukullin mota. Fuska ɗauke da murmushi ta dubi ɗaya matar wadda ga dukkan alamu za ta girme mata. "Idan kina da bashin bacci ki kawo nayi miki Chioma" Hararar wasa Chioma din ta sakar mata "sai murna kike yi don an baki hutun kwana uku, kamar yau ne dai za ki ga litinin ɗin ta yi kin dawo" Juyi tayi tana takun rawa "ya son ranki? Ina da ƙarshen yau ga Laraba, Alhamis, Juma'a da ƙarin kwana biyun larshen sati. Woahhh gado da filona gani nan zuwa gareku" Abincin da ta taho dashi akan hanyarta ta dawowa daga kotu awa ɗaya da ta wuce kafin ta san cewa za ta sami hutun nan ta miƙawa Chioma, sannan ta fito daga office ɗin nasu wanda a saman ƙofar aka makala wani kyakkyawan abu mai ɗauke da rubutun sunayen mazauna cikinsa. Tafiya ƙalilan ta yi ta soma cin karo da wasu abokan aikin nata maza da mata suna taya ta murnar samun nasarar da ta yi akan babban case ɗin da aka rufe yau. Shari'ar ta ɗauki hankulan jama'a da dama saboda sarƙaƙiyarta amma cikin ikon Allah bayan wata uku ana gumurzu ta yi amfani da hikima da kaifin basirarta wurin ƙwatarwa mutumin da take karewa haƙƙinsa tare da wanke shi daga dukkan zargi. Bisa wannan dalilin ne Managing Partner ɗinsu wato shugaban ma'aikatarsu ta lauyoyi masu zaman kansu mai suna Write Right Associates, bayan dawowarta daga kotu ya kira taron gaggawa inda ya yaba mata sosai a matsayinta na sabuwar matashiyar ma'aikaciya mai ƙwazo da himma. Alƙawarin kakkauran tukwuici ya yi mata wanda ya ce zai shigo asusunta tare da albashinta na wannan watan nan da sati ɗaya, sannan ya bata hutun sauran kwanakin satin. Motarta ta nufa a zuciyarta tana ayyana abubuwan da zata ta yi domin cin moriyar kwanakin nan. Faffadan murmushi ne ya suɓuce mata da ta tuna cewa yau Shaheed da Sariat su ka yi tafiya domin dubo mahaifiyar da aka yiwa aikin ido. Shaheed ya zama mutum mai tsantseni sosai akan lamuranta tamkar wata ƙanƙanuwar yarinya baya barinta tana yin nesa da gida indai ba akan aikinta ba. Da tafiyar ta taso yanzu babu yadda zai yi sai sun barta a gidan ita kaɗai da mai aiki. Da ace ya san yau zasu gama shari'ar har ta sami hutu tana da yakinin daga tafiyar zaiyi zuwa gobe da safe. Dukan sitiyarin motar ta yi tana ɗan kiɗa da duka hannayenta biyu tare da waƙar da bata da wani tsayayyen kari ga rashin daɗin sauraro saboda rashin nasibin waƙa da bata dashi ko kadan. "Gado da filona gani nan tafe...Tauhidan Papa da Maami za ta huta...Tauhidan Nanna babu ta biyunki."
***** Amran-Yemen Sautin da yake ji sama-sama sh ine ya sanya Arƙam saurin kashe famfon da ya kunna domin yin alwalar sallar azahar. Zuciyarsa wani irin bugu ta shiga yi da ƙarfi, saboda tabbatuwar zarginsa akan sautin amma hakan bai hana shi addu'ar Allah Yasa kunnuwansa ne basu ji daidai ba. Ƙaruwar sautin ta yi daidai ta saurinsa ya leƙa ƙatuwar tagar banɗakin. Jikinsa a take ya yi mugun sanyi da ya hango jiragen yaƙi suna shawagi a sararin samaniya daga nesa. Yana jin alamun buɗe ƙofofi biyu cikin banɗakin wanda yake idan an shigo sink ake fara gani jere da kawunan famfo guda biyar sai kuma wurin da aka keɓe domin biyan buƙata guda shida kowanne da ƙofarsa an raba tsakaninsu da filanki mai farin fenti. Mutanen da su ka fito a gigice sakamakon kusantowar sautin mai firgitarwa. Guda cikinsu sanye yake da falmaran irin wadda take jikin dogon mutumin da yake tsaye a bakin tagar yana leƙawa. Tambari da rubutun jikinta yana nuni da cewa likitoci ne na ƙungiyar agajin nan mai suna Médecins Sans Frontières (MSF) wadda a turance aka fi sani da Doctors Without Borders. Suna cikin asibitinsu da yake yankin Amran a ƙasar Yemen wadda rashin zaman lafiya ya durƙusar da ƙasar akan gwuiwowinta. Al'ummar ƙasar sun shiga mawuyacin yanayi ne tun bayan ɓarkewar rigima tsakanin gwamnati da ƙungiyar tawaye ta Houthi a shekarar 2015. Shekaru huɗun da su ka gabaci wannan tashin hankali sun samar da mutuwar dubban mutanen da sanin haƙiƙanin adadinsu zai yi wuya. Cikin wannan yanayi ne ƙungiyoyin agaji da dama su ke ɓullowa domin kai taimakon da ya dace. MSF ɗaya daga cikinsu ta yi fice wurin kai taimakon kula da lafiya ga ƙasashen da rikici da rashin zaman lafiya ya yi wa farmaki. Ko kuma ɓaraka da yaɗuwar cututtukan ƙare dangi da kan illata mutane da yawa cikin ƙanƙanin lokaci idan ba'a ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki da wuri ba. Ƙasar Faransa ita ce tushen ƙungiyar, kuma zuwa yanzu rassansu sun yi aiki a ƙasashe sama da 70 da taimakon mutane da dama wanda jigonsu jajirtattun likitoci ne da su ka sadaukar da rayuwarsu domin sauya rayuwar mabuƙata. Likitocin biyu da Nos namiji guda ɗaya da su ke cikin banɗakin sun shiga ruɗani ne sakamakon jin saukar bom a harabar asibitin nasu. Cikin ƙanƙanin lokaci wurin ya hargitse da guje-guje da kiraye-kirayen likitoci a ɓangaren emergency. Dama suna ta fama da yawan marasa lafiya a dalilin annobar cutar kwalera da ake ta yaƙi da ita kusan shekaru uku. Airstrike ɗin wato hari daga cikin jirgin sama ya ɗauki aƙalla rabin awa a yankin da suke kafin jaragen su ƙara gaba. Kan kace meye wannan asibitin nasu ya cika da mutanen da su ka jikkata a dalilin harbi ko raunuka saboda zubewar gine-ginen da tashin bomaboman maharan saman ya janyo. Jini ko ta ina likitoci da nurses hadda iyaye ko ƴan uwan marasa lafiyan kowa sai kai kawo yake yi cikin tashin hankali. Arƙam ne tsaye a gefen gadon wani tsoho da bandeji a hannu yana ƙoƙarin tsayar da jinin da yake zubowa daga cikin kunnuwansa duka biyun. Da zafin nama yake yin komai, ya ɗaga muryarsa da bata da ƙarfin kirki yadda wata Nos ƴar asalin ƙasar Yemen ɗin za ta ji abinda yake faɗa, saboda hayaniyar wurin ta yi yawa. Cikin harshen turancinsa da idan ba ka kalli baƙar fatar jikinsa ba zaka rantse cikakken bature ne yake magana ya ce da ita, "Ina tsammanin ya sami tsagewar ƙashin kansa ne (skull), tambayar min ɗan nasa me ya same shi da yanayin da aka ɗauko shi" Da sauri ta faɗawa ɗan mutumin wanda jikinsa yake lulluɓe da dattin ƙasa, ƙura da jini, abinda likitan ya ce da larabci. Bayan ya bata amsa ta fassarawa likitan cewa suna kan babur da baban nasa ginin gabansu ya zube babur ɗin ya hantsila sakamakon dukan wani bulo da su ka yi kuma dukkansu babu mai hular kwano (helmet). Bai tsaya sauraron bayanin har ƙarshe ba ya yi mata alama ta taho. Gadon ya nuna mata ta taimakawa wani paramedic su tura. "Ku kaishi ayi masa CT scan kafin ku gama zan sanar da Director mu gani ko Dr. Hamidi zai iya tahowa yanzu ya duba shi." "Dr. Hamidi ba zai iya zuwa ba yanzu na gama magana da reshenmu na Taiz hanya babu kyau" cewar Director Zhang mutumin Hongkong. "Babu yadda za'ayi mu sami neurologist (likitan ƙwaƙwalwa) nan kusa?" Director Zhang ya san halin likitan nasa da saka abu a rai. Kowane mara lafiya burinsa ya ga sun bashi kulawar da ta dace. Su ma duk tunaninsu kenan sai dai shi wannan likitan har yau bai san haƙuri ba, mutum daya idan ya mutu a dalilin rashin likitan da ya dace ya duba shi ko ƙarancin kayan aiki ko kuma matsalolin da su ka fi karfinsu masu tasowa a irin wannan yanayin kodayaushe sai ya kwana fiye da uku cikin yanayin ƙunci da ganin kamar laifinsa ne. Kafaɗarsa Director Zhang ya dafa "ka bari ayi CT ɗin mu gani ko lallai yana bukatar neurologist din kafin ka yanke hukunci." Kafin yayi magana ya hango ana shigo da yara biyu a guje, ɗaya a hannun wata mace ɗayan kuma a hannun namiji dukkansu jinajina ga abokin aikinsa a bayansu yana nuna musu wurin da zasu kwantar da yaran. "Dr. Karam muna buƙatarka a nan" cewar abokin aikin nasa duk da ya riga ya kusa isa garesu ma. Ambaton sunayen Allah yake yi a zuci, yayin da a zahiri hannunwansa da jikinsa su ke aiki a lokaci guda. Mahaifiyar yaran ce take yi musu bayani cikin gurɓataccen turancinta cewa suna ciin gudun neman tsira ita da yaranta bayan an fara airstrike din harsashi ya sami yarinyar ƴar shekara huɗu wadda yayanta yake goye da ita. Daga tsakiyar bayanta harsashin ya huda ƙirjinta ya fita ya shiga jikin yayanta ta baya. Juya yaron gabansa ya yi idanunsa a rufe suke sai numfashi da yake fitarwa da ƙyar. Yarinyar kuma defibrillator wato na'urar farfaɗo da bugun zuciya ɗaya likitan yake dannawa a ƙirjinta gefensu kuma mahaifiyarsu ce a tsakanin gadajen biyu tana kuka mai shiga rai. "Akwai OR (operating room) da babu kowa a ciki?" Cewar Arƙam bayan ya ɗora hannu akan bayan yaron yana tattaɓawa a nutse a ƙoƙarinsa na ganin zurfin rauni da matsayar harsashin. Babu ita ce amsar da aka bashi. Gumi ne ya karyo masa ganin yaron yana cikin mawuyacin hali idan ba'a fitar da harsashin da wuri ba zai iya cigaba da shigewa jikinsa ya taɓa mahimman sassa wanda faruwar hakan ba alkhairi bane. Labulen da ya raba tsakanin gadajen ya shiga ja zai zagaye gadon yaron mahaifiyarsa da Director Zhang su ka yi kansa da sauri. Hankalinta ya rabu biyu gefe ana ƙoƙarin dawo da numfashin ƴarta nan kuma bata san me zai yiwa ɗan nata ba. "Kada kace min a nan za ka yi masa aiki?" Director Zhang ya tambaye shi duk da ya san amsar tun kafin ya tambaya. Bai ji ko ɗar ba ya cigaba da tattaro kayan da zai buƙata daga store ɗinsu da ya tafi cikin sassarfa daraktan yana biye dashi da sauri. Ɗauko kayan aiki yake yi yana yi masa bayani. "Harsashin ya bar saitin wurin da ya shiga, kowane minti ɗaya mu ka bata zai iya sake sanya rayuwar yaron nan cikin hatsari" Daraktan saita kansa ya soma neman yi saboda baya son ana cikin wannan yanayin su fara rigima da babban likitan nasa. Hadda kwantar da murya don neman su daidaita sannan ya ce "ka san doka ta hana" Mai allurar anasiziya Arƙam ya ƙwalawa kira sannan ya mayar da kallonsa ga Daraktan na daƙiƙa biyu "duk abinda ya biyo baya ka bada sunana amma..." Kukan mahaifiyar yaran tana karanta Innalillahi wa inna ilaihi raji'un shi ya katse shi lokacin da ake lulluɓe fuskar yarinyar Allah Ya yi mata cikawa. Wani irin kallo ya kafe Director Zhang dashi alamun jiran amsa. Ba don ya so ba ya gyaɗa kai sannan ya bar mai allurar ta wuce yana cewa "duk abinda ya biyo baya...." Labulen kawai Arƙam ya ja sannan ya ɗora scanner akan cikin yaron yana neman ainihin inda harsashin yake a yanzu. Ya kwashi kusan minti biyar hankalinsa a tashe sosai yana tsoron miƙawa wannan mata gawa ta biyu. Safar hannu ya sauya saboda ɓaci da ta hannunsa ta yi, Nos ɗin da zasu yi aikin tare ta miƙa masa scalpel tare da matso da wata fitila domin ƙara masa haske. A hankali ya yii madaidaiciyar yanka a ɓangaren dama na cikin yaron. "Irrigation" ya ce da Nos ɗin. Wata na'ura ta saka ta wanke wurin, sannan ta zuƙe jinin shi kuma yana yi yana kula da bugun zuciyarsa ta ECG ɗin da aka sakawa yaron bayan ya fara aikin. Cikin nutsuwa da ƙwarewa yake komai, ya saka wani ƙarfe mai suna retractor ya yi gefe da hanjin sannan ya saka hannu yana neman harsashin. Gumi duk ya karyo masa saboda rashin samun biyan buƙata. Ana haka kuma ECG ɗin ya fara wata ƙara alamun akwai matsala. Daga waje mahaifiyar yaran zama ta yi daɓas kawai a ƙasa ta haɗa kai da guwiwa tana jiran ta sake jin mummunan labari domin dai ta riga ta sadaƙar shiɓma bazai tashi ba. Director Zhang ya dinga kallonsa da yaron a gigice. "Me yake faruwa?" Babu amsa gareshi sai jinin da likitan ya bada umarnin a ƙaro masa leda biyu, ya dage wani ɓangare na hanjin yaron sai ga jini mai yawa yana tunkuɗar juna a guje yana kwarara da feshi har fuskarsa. Saboda rashin wadatar likitoci da nurses gashi ya aiki wadda su ke aikin tare ya dubi Director Zhang fuskarsa babu alamun wasa. "Riƙe min wannan kuma kome zai faru kada kayi motsi komai ƙanƙantarsa" ya nuna masa kan wani retractor ɗin da yake a matsayin kariya ya riƙe hanjin wuri ɗaya kada su sake rufe hanyar wucewar jinin. A dolensa ya riƙe tunda idan ta kwaɓe to hadda shi za ta ɓallowa ruwa. "Internal bleeding ne ka riƙe min da kyau ina son gano sanadin zubar jinin" Cikin minti biyu ya gano jijiyar da ta sami raunin ya ɗinketa a gefe ɗaya ana ƙarawa yaron jini. Bayan ya gama yabyi nasarar ganin ƙqramin harsashin ya fitar dashi sannan aka sake wanke wurin ya fara ɗinki. Sai dai kafin ya gama yaro ya fara jijjiga ya shiga shock. "Defibrillator", yace da ƙarfi Director Zhang da kansa ya fita a guje ya sami ɗaya da aka gama aiki da ita a gaban wani gado ya kawo masa. Hankalinsa da tunaninsa gabaɗaya suna ga yaron nan. Haka ya dinga ɗora hannuwan na'urar suyi caji cikin ƙanƙanin lokaci sannan ya ɗora akan ƙirjin yaron. "Charge! Clear!" Su kaɗai kake iya ji Arƙam yana faɗa a ruɗe yana addu'ar samun nasara. Gasu dai tsaye a wuri daya amma su ukun sun wahala sosai musamman shi da ya koma danna kirjin yaron da hannunsa wanda hakan ba ƙaramin gajiyar da mutum yake yi ba. Director Zhang cikin tausayawa ya dafa kafaɗarsa. "Doctor kayi hakuri haka" Hannun ya doke ya cigaba da danna ƙirjin yana ɗigar da gumi "zai tashi, bai mutu ba..." Bayan ya kwashi mintuna hannuwansa sun soma sagewa babu kuzari sosai kawai zanen layukan komputar ECG ɗin wanda likitoci da dangin sana'arsu su ka san me suke nufi ya chanja yana ƙara dit dit a hankali. Farinciki a take ya mamaye Nos, Director Zhang da uban gayyar likita bokan turai Dr. Arƙam Ibrahim Karam. Hamdala kawai yake yi aka buɗe zagayen labulen inda ya ga mutane sunfi goma hankalinsu a wurin ana jiran tsammani. Mahaifiyar yaran ta ɗago kai a firgice jin shirun wurin ya yi yawa su ka sauka a cikin nasa. Ƙayataccen murmushi ya sakar mata wanda ya sanyaya zuƙatan sauran mutanen kowa ya koma inda ake biɗarsa duk da yawancin masu tsayuwar dama marasa lafiya ne. Da saurinta ta taso ta iso gareshi "this fight four child and husband dead, now you protect Ghassan. Thank you Doctor" Ya fahimceta ya kuma tausaya mata. Mutuwar ƴaƴa huɗu da miji a dalilin wannan tashin hankali ba ƙaramin abu bane ga mace. Bakin gadon ta ƙarasa inda ake ƙarasa gyara wurin kafin komai ya daidaita a kaishi ɗaki sosai. Fuskar yaron data kira da Ghassan take bi tana sumbata tare da kwararowa Arƙam addu'a. Aiki dai kamar lokacin aka fara domin ma'aikatan ba su suka sami kansu ba sai can cikin dare saboda mummunar ɓarnar da maharan na sama su ka yi a yankin. A gajiye ya ɗora haƙarƙarinsa a makwanci ya lumshe idanu sannan ya tuna da alwalar da ya soma yi kafin faruwar komai. Da sauri ya miƙe yaje ya ɗauro alwala ya zo ya gabatar da sallolin la'asar, magariba da isha yana mai yin tir da Allah wadai ga wannan abubuwa da suke faruwa a duniya yanzu. Kusan ko ina musamman ƙasashen musulmi babu zaman lafiya, sai kashe-kashe ake yi da samar da 'yan gudun hijira. Ace wasu suna cikin wannan yanayin amma duniya bata tsaya ba domin daidaita lamura sai dai a dinga kai musu abinci da agaji amma zaman lafiya ya yi ƙaranci. Ya rasa a wace fiɗira duniyar take tafiya yanzu da muke zaman idan jifa ya wuce kanka ya faɗa kan kowa ma. ****** Laraba 16/2/2019 9:40pm "Mammalo yau ma ka kawo Aidan ɗakina mu kwana tare." Cewar Mubeen yana tsaye a ƙofar ɗakin Aidan ɗin. Jiya da shekaranjiya ma haka ya yi masa wai yana jin tsoro suje ɗakinsa ko shi yazo nan su kwana tare. Da yake ya gama karantar Susu ya san ko da wasa bai isa ya shigar mata ɗakin Mubeen ba. Yaron kuma ya kafa naci sai ya kai masa Aidan ɗin ya fita. Cikin dare sau biyu yake tasowa daga ɗakin Aidan yaje ya duba yanayin kwanciyar tasu. Ba zai ƙi ba yau ma tunda ya kula kwana taren yasa Mubeen ya fara ragawa yayan nasa har yana yi masa hira. Jira ya yi sai da suka yi bacci sannan ya fita ya koma ɗakin Aidan. Ƙarfe ɗaya da rabi Alh. Audi ya fito daga nasa ɗakin. Bai bari Fanna ta kwanta a can ba ya fake da aiki yaƙi kashe fitila saboda ya san bata iya bacci da hasken. Sai da safe ta yi masa ta koma nata ɗakin ya sami damar yin yadda yake so. Da sanda ya fita zuwa ɓangaren Shamsu babu haske sai daga fitilun waje. Sanye yake da baƙar jallabiya sai takalminsa irin na gefen gadon nan mai laushi wanda baya bada sauti idan ana tafiya. Ya riga ya faɗawa Shamsu ya bar ƙofa a buɗe zai shigo, idan ya gama ya taya shi gyara jikin Mubeen yadda babu mai gane abinda ya faru. Cikin sa a bai haɗu da kowa ba, har ya isa ƙofa ta biyu a ɓangaren da Shamsu ya faɗa masa nan ɗakunan Aidan da Mubeen suke. Gabanin shigowarsa Mammalo ya shiga ɗakin Mubeen da zummar duba Aidan. Yana zuwa ya same shi ido biyu fitsari ya matse shi ya rasa yadda zai yi ya taɓa Mubeen don ya kira masa Mammalo. Cikin sauri ya ɗauke shi ya kaishi ya yi. Da ya gama suka fito ya kwantar dashi da ƴar tazara tsakaninsa da Mubeen saboda ya kula da ya shigo ya maka masa hannu da ƙafafu. Komawarsa banɗakin don ya yi flushing ke da wuya Alh. Audi ya shigo. Mammalo bai kunna fitila ba sai dai rabin ƙofar a buɗe yake yana ganin cikin ɗakin. Suman tsaye ya yi da ya gane waye ya shigo a cikin daren nan cikin sanda. Da lalube Alh. Audi ya shafa gadon ya kamo Mubeen. Gefensa da yaga tudu ya taɓa sai yaji laushin pilon da Mammalo ya saka tsakaninsa da Aidan. Bai kawo komai ba ya juya Mubeen bayan ya ɗaure masa baki da wani ƙyalle ya danne shi. Duk abinda ya biyo baya akan idanun Aidan da yake kwance a gefe yana kallon yadda ƙaninsa yake kokawa da ɗan ƙarfinsa yana son a ɗaga shi. Mubeen kuka shi ma kuka amma babu damar taimaka masa, hasali ma dai bai san me kakan nasu yake yi ba idan ka cire danne Mubeen din da yaga ya yi. Mammalo kuwa ba ƙaramin firgici da tashin hankali yake ciki ba. Ko a mafarki bai taɓa ganin wannan dabbancin ba sai gashi yau ya gani zahiri kaka ya danne jikansa.