Kenza eBookz

Cizon yatsa book 1&2 complete - Chapter 23

Cizon yatsa book 1&2 complete - Chapter 23

Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 23: Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 23. Alh. Audi na gamawa ya sa bargo ya lulluɓe Mubeen ya fita. Mammalo bai…

2,696 words

Alh. Audi na gamawa ya sa bargo ya lulluɓe Mubeen ya fita. Mammalo bai ɓata lokaci ba ya fito ya ɗauki Aidan ya kaishi nashi ɗakin sannan ya dawo domin ganin halin da Mubeen yake ciki. Bai ƙarasa ɗakin ba ya hango wani ya taho sai ya laɓe a bayan wata durowa a zatonsa Alh. Audi ne ya dawo. Shamsu na shiga ya ɗaura ƙyallen nan a fuskarsa ya janyo Mubeen wanda ya yi ƴar siririyar ƙara saboda azabar da yake ciki sai zuciyarsa ta karye. Akan neman lafiyarsa ba zai iya yin wannan mummunan abu da ɗan cikinsa ba. Gyara masa kwanciya ya yi zai tashi Mubeen ɗin ya riƙe hannunsa yana kuka mara sauti. Danshin da Shamsu yaji a kusa dashi ne yasa shi kunna fitilar ɗakin da saurinsa. A razane ya yaye bargon ganin idanun Mubeen a kumbure bakinsa kuma a ɗaure. Susu kuma tuna fitarsa taji hankalinta bai kwanta ba saboda wayar da taji yana yi jiya. Ganin ɗakin da ya shiga sai ta juya za ta koma. Bata yi taku biyu ba taji Shamsu ya saki ƙara a razane yana kiran Mubeen da ƙarfinsa. A guje ta shiga ta yi arba da tashin hankali. Mubeen ne kwance cikin jini ga wandonsa a ƙasa. Shamsu kuma ɗaure da wani baƙin ƙyalle mai zanen ƙwarangwal a ƙirji babu kaya a jikinsa. Kasa motsi ta yi na ƴan daƙiƙu jinin jikinta yana gudu kamar zai ratso fatarta ya fito waje don fargaba. Mubeen ɗin ta karɓe daga hannunsa wanda ya riga ya suma ta tabbatar da abinda ya faru sai ta fita har Shamsu yana cewa ta ɗauko mukullin mota. Ya manta da yanayin da yake ciki na rashin sutura sai tunanin halin da Mubeen yake ciki. A falo suka yi kiciɓis ta karɓe ɗanta daga hannunsa idanunta kamar garwashi ta luma masa wuƙar hannunta a ciki sau uku tana wani irin kuka mai ciwo. A wurin Shamsu ya faɗi cikin jini ta ɗauki ɗanta ta tsallake shi ta fita daga ita sai kayan bacci. Alh. Audi da Mammalo kusan a tare suka fito daga mabuyarsu bayan sun ji tashin motarta. Kallon kallo suke yiwa juna a inda tashin farko Alh. Audi yaji wannan mugun firgicin da ya taɓa ji ranar da Mammalo ya fara zuwa gidan. A razane ya bishi da gudu ya faɗa ɗakin Aidan ya saka mukulli. Bugawa yake cikin tashin hankali yana kiran sunansa. "Ka bude muyi magana zan biyaka ko nawa ne." Mammalo danne ƙofar ya yi iya ƙarfinsa saboda bugun Alh. Audi ba na wasa bane. Wani irin kuka suka ji ashe Shamsu ne ya lallaɓo wurin ɗakunan da jan jiki. Nan Alh. Audi ya manta da buga ƙofa ya yi kansa a guje. Mammalo na jin ya bar wurin ya goyo Aidan ko takalmi bai tsaya sawa ba ya fito shima a gujen ya wucesu ya fita. Masu gadi dama sun tashi lokacin fitar Susu suka ganshi goye da yaro. Suna cewa ya tsaya ya samu ya bangaje wanda ya fara tare shi ya fita daga gidan cikin duhun tsakar dare. *** Wuraren ƙarfe biyar da rabi na wayewar garin Laraba Susu ke sharara gudu a motarta kirar Acura ruwan toka. Jifa-jifa take waiwayawa baya tana kallon Mubeen mai kamanin shekaru bakwai da ɗoriya da yake kwance a baya cikin jini babu alamun rai a tare dashi. Hannun damanta ta miƙa baya tana jijjiga shi cikin tsananin ruɗani da fargaba. Murya na rawa ta kira shi da ƙarfi gabanta yana faɗuwa kamar zuciyarta zata fito ta baki, "Mubeen, Mubeen, ka amsa min mana" Shiru taji irin wanda yake tsuma zuciya. Sake taɓa shi ta yi har taso ta manta cewa akan titi take sai da wani mahaukacin horn ya fargar da ita ta yi saurin ɗauke hanya da iyakar ƙarfinta saboda saura kaɗan ta daki motar gabanta. A daburce take babu nutsuwa ko kaɗan a tare da ita ta samu ta gangara gefen titi ta fito da sauri jikinta na rawa ta buɗe ƙofar bayan ta janyo shi tana sambatu. "Mubeen ka san dai ban taɓa dukanka ba ko? To yau zan fara idan ka ki amsa min" Ƴar saman rigar baccinta da ta naɗe masa jiki da ita ta kalla duk da rashin wadatar haske amma tana iya tantance jiƙewarta da jini. Hawayen da bata sami damar yi ba tun kafin su baro gida ta soma zubarwa tana rungume dashi a ƙirjinta. Sai da taji sauƙin rawar jikin ta mayar dashi ta kwantar saboda ganin tsilli tsillin mutane an fara kallon motar ta zagaya da niyyar tafiya asibiti kamar yadda ta yi niyya kawai ta tsinkayi jiniyar motocin ƴan sanda. Cikin ƙanƙanin lokaci biyu sun iso inda take suna neman rufe mata hanya. Dirowa na bayan motar su ka yi kowanne bindiga a saitinta suna faɗa mata kalmar da take jira. "You are under arrest." Murmushi ta yi ga hawaye suna cigaba da zubowa "na sani amma ku barni na ƙarasa da yarona asibiti sai mu tafi." "Ki ɗora hannuwanki a inda zamu iya gani sannan kiyi shiru domin duk abinda kika faɗa a nan zamu iya amfani dashi a mstsayin hujja a kanki a kotu" cewar Inspector Badawi jagoran tawagar. Mugun kallo ta watsa masa lokaci guda tana juyawa bayan motar saboda ganin wani Sergent yana taɓa Mubeen kafin ya sungumo shi ya ɗora a kafaɗa. Kukan kura ta yi ta zabura tana neman ƙwatarsa "kada wanda ya taɓa min ɗa, da kaina zan zo station ɗin naku idan kun barni na kaishi asibiti, don Allah ku taimaka min." ASP Badawi umarni ya bayar na a ɗaura mata ankwa a saka ta a bayan motarsu sannan a rufe mata jiki saboda rigarta da babu duk ɗaya. Ai nan da nan ta birkice musu tana kuka da roƙon a barta ta kai ɗanta asibiti. Sergent ɗin da ya ɗauke shi ya yi mata wani irin kallo kamar na tausayi kafin ya mayar da idanunsa ga Inspector ɗin ya soma magana. "Yallaɓai wannan yaron ya riga ya cika" "Me?" Ta ce kamar mahaukaciya ta bangaje Kofur ɗin da yake ɗaura mata ankwar tabi Sergent ɗin, "karya ne wallahi da ransa suma ya yi, irin doguwar suman nan ya yi amma da ransa" Tuni mutum biyu su ka cafkota kafin ta ƙarasa tana ta hargagi da kuka, zuciyarta ta yi mugun rauni. Roƙonsu take yi da alƙawura na kyauta mai tsoka ita dai a bata ɗanta kawai. Tsawa Inspector Badawi ya daka mata yana bada umarnin a saka masa ita a mota su bar wurin sannan ya ce da Sergent din su wuce da Mubeen asibitin da aka kai babansa shi zai kira Alhaji ya sanar dashi sai su same su a can. Turjiyar da take yi ta dena nan take ta ɗago rinannun idanunta tana kallonsa. "Wai kana nufin bai mutu ba? To me yasa ku ka kamani?" "Haj. Suwaida Musa mijinki bai mutu ba kamar yadda ki ka yi niyya amma mun kamaki ne saboda yunkurin yin kisan kai" Dariya ta kwashe da ita ta yadda dole mutum ya ti mata kallon sabon shigar hauka "Kaga Inspector ka barni naje na ƙarasawa bunsurun abinda na fara idan yaso sai ku kasheni nima. Alfarma ce nake roƙo ku kaini inda yake na kashe shi da hannun" ta ƙare maganar da cije leɓenta na ƙasa. Girgiza kai ya yi yana jin wani irin ɓacin rai na yadda mata suke hallaka mazansu a wannan zamani. Nunawa Sergent Esther ita ya yi yace su kamata su tafi. Motarsu tana gaba wadda aka dauko gawar Mubeen tana bayansu. Asibitin su ka tafi inda Sergent ɗinnan ya yi ruwa ya yi tsaki yaƙi barin kowa ya taɓa yaron sai da likitan da aka bashi umarni daga sama ya iso a gurguje. Ba kowa bane illa Dr. Samson Madaki. Yana zuwa wani ɗaki ya shiga da shi ya gyara masa jiki tsaf da kansa bai nemi taimakon kowa ba sannan ya rubuta report saɓanin ainihin abinda ya sami Mubeen a cikin file. Sai da ya gama komai ya ɗauki waya ya kira Alh. Audi. "An gama" kawai ya ce ya kashe wayarsa. ****** Duk yadda Tauhidat ta so yin bacci har rana ta take abu ya faskara saboda sabo da ta yi da tashin wuri tun bayan da ta fara case ɗinnan. Miƙa ta yi haɗe da salati ta shiga banɗakinta da yake cikin dakin tayi brush sannan ta fita falo. Abinci mai aikinsu Iyabo ta gabatar mata ƙosai da zafinsa saboda lokacin ta gama suya da akamu. Murmushin nan nata ta yi wa Iyabo ta ƙara da kalmomin godiya kafin ta fara kai abincin cikinta. Ba ƙaramin ci ta yi ba ita kanta ta sani amma a cewarta tana cike gurbin da ta bari ne a kwanakin baya. Bayan ta gama wanka ta yi ta sako brown ɗin wando skin tight da riga mara nauyi. Ko mai bata shafa ba saboda zafin gari sai turaren jiki da ta fesa ta rufe gashinta wanda a jerin abubuwan da take son yi hadda kaishi salon a gyare shi. Fuskarta ta kalla a mudubi ta kyabeta tana yiwa kanta kallon tausayi. "Poor girl duk kin faɗa saboda wahala". Sai dai idanunta kaɗai ke ganin faɗawar tana nan yadda take ƴar ɓulɓul. Iyabo ta ƙwalawa kira ta sanar da ita kada ta ɗora komai ita za ta yi girki. Ƴar ƙaramar wayarta ƙirar samsung ta ɗauko bayan ta kashe babbar saboda alƙawarin da ta yi na cewa babu ita babu social media. Hutu zallah, ta ci ta sha ta yi kallo ta yi bacci, faƙat. Kitchen ɗin ta shiga ta ɗora tuwo, Iyabo da take baƙuwa a gidan don bata daɗe da fara aiki ba bata taɓa ganinta a kitchen da sunan girki ba sai mamaki ya kama ta. Gaza ɓoyewa ta yi ta tambayeta. "Madam dama kin iya girki?" Rangwaɗa kai ta shiga yi ta soma yabon kanta "Iyabo ashe fa baki taɓa cin girkina ba, hahhh idan na shiga kitchen tukwane ma girgiza su ke yi ga uwarɗakinsu ta iso" Me Iyabo zata yi kuwa banda dariya harda rike ciki. Zaman hira ta yi har aka gama tuwon da ta ƙulle a ledoji guda shida sannan ta koma ɗaki ta sako dogon hijabi har ƙasa ta fito riƙe da mukullin mota a hannu. "Kasuwa zani ba daɗewa zanyi ba in sha Allah, idan kin kasa jirana akwai miyar kuɓewa da Aunty Sariat ta yi kafin su tafi sai kici tuwon" "Ai jiranki zan yi saboda inci abincinki yadda zan bada labari sosai" Murmushi ta yi na jindaɗi "to jirani zan baki mamaki Iyabo"

Wuse market ta je daga unguwarsu Wuse zone 6 ta siyo naman sa, kifi ɗanye da busasshe, ganda, ganyen ugwu da alayyahu mai yawa ta dawo gida. Tana ƴan waƙe waƙenta marasa daɗi ta haɗa komai domin yin ingantacciyar miyar Edikaikong wadda ta wadatu da sinadaren gina jiki saboda abubuwan da ta ƙunsa na haɗi. Kafin ta kammala Iyabo duk ta ƙosa saboda ƙamshin da ya buwayi hancinta. Ba tare da ɓata lokaci ba kuwa tana ganin an kashe wutar miyar ta miƙo kwanonta cikin salon maganarta da hanci take mata kirari. "Barrister, Barrister sai ki kashe auren da babu soyayya da ƙamshin girkinki kaɗai" Daɗi ne ya kama Tauhidat jin ana yaba mata ta zuba mata tare da cewa ta ɗquki robar lemun da ya yi mata daga fridge. Iyabo duniya sabuwa ta ƙwame a falo tana kwasar gara tana zuba santi yayin da ita kuma ta wuce ta yi sallar azahar. Bayan ta idar ta yi karatun hizfi ɗaya sannan ta fito jiki na rawa domin yawunta ya gama tsinkewa amma a cewarta sai yunwa ta ciwota da kyau za ta ci abinci domin dadinsa ya ratsata da kyau. Sai da ta ajiye komai a gabanta ga tuwo ga miya sannan ga lemo mai sanyi da ruwa ta fita ta tayar da injin da ta taho da mai galan biyu don ma kada ya yanke musu saboda rashin wutar da suke fama dashi a layinsu sakamakon faɗuwar wata waya a dalilin ruwan sama. Tana dawowa abincin yana harararta amma taƙi zama ta wuce gaban tv ta kunna ta nemi tashar da ta yi mata sannan ta hakimce ta kai hannu cikin kwanon miyar kenan taji wani irin mahaukacin bugu a ƙofar gidan nasu. Iyabo da tuni ta gama suɗe yatsu ta ce mata bari ta duba. Ta sake kai hannu wannan karon sai ji tayi banda bugun hadda sunanta ake kira. Miƙewa ta yi tsam ta koma ɗqki ta sako hijabinta ta dawo daidai lokacin da wani siririn mutum ya bangaje Iyabo ya shigo afujajan goye da yaro da zai kai shekaru tara a bayansa. A razane take kallonsa da tarin tambayoyi a bakinta cikin Hausarta da bata gargada bare tangarɗa saɓanin ɗazu da take magana da yarenta na Yarbanci ta ce "Mammalo me kake yi a nan? Waye wannan a bayanka?" Yaron ya kwantar a kan doguwar kujera 3-seater ya gyara masa kwanciya sosai duk akan idanunsu. Ita dai ƙarshen ruɗewa ta yi bakinta yana harɗewa ta nuna yaron. "Aidan. Aidan...Aidan ne?"

Mammalo ya gyaɗa kai yana haki kafin ya kula da ruwan da yake ajiye a kan ƙaramin tebur ɗin da ta ajiye a gabanta da kayan abinci ya ɗauko ya buɗe robar ya dago kan Aidan ya soma bashi. Ruwan yana shiga wani na tsiyaya ta gefen bakinsa haka ya dinga karba da gani yana jin ƙishirwa sosai. Sai da ya tabbatar ya ishe shi sannan ya kafa kai ya shanye sauran. Kasa haƙuri ta yi fuskarta babu digon annuri kamar ba ita ta gama saka Iyabo dariya ba dazu ta kalli Mammalo duk da zuciyarta har ɗan tsallen murna ta yi da ganin yaron amma zuwansa gidansu ba abin farinciki bane "nace me kake yi a gidan nan tare da Aidan?" "Ƴar gidan Fafa kiyiwa Allah da ManzonSa ki riƙe shi a wurinki kafin komai ya lafa domin rayuwarsa tana cikin hatsari" Kallon rashin fahimta ta yi masa tsoro yana bayyana ƙarara a fuskarta "rayuwarsa tana cikin hatsari sai ka kawo min shi? Baka da hankali ne?" "Bani da wurin kaishi ne sai nan ɗin. " A zafafe ta ɗaga masa hannu "Kada ka raina min wayo mana, ina iyayensa da kakansa?" Mammalo da ya yi baƙiƙƙirin da gumi da ƙura ya sadda kai kasa "bani da lokacin yi miki bayani domin zamana a garin nan barazana ne ga rayuwata. Ki riƙe Aidan na san cewa zaki ji komai cikin ƙanƙanin lokaci" Bude baki ta yi za ta sake masa magana ta fasa sakamakon dulmiya hannu da ya yi cikin abincin da ta gama cin buri a kai ya dinga zuba loma manya manya saboda yunwa sannan ya ɗauki lemon ya fice. A guje ta bi bayansa tana ƙwala masa kira kafin ya gama sauka benen ɓangarensu saboda gidan nasu irin mai hawa uku ne guda huɗu a compound ɗaya. Daga benen karshe ya tsaya ya ɗago kai ya kalleta. "Rayuwarsa tana cikin hatsari kada ki yarda ki damƙa shi a hannun kowa sai na Haj. Suwaida" Bata ankara ba ya ƙara gaba ta dinga binsa har bakin gate amma kafin ta fita wajen babu shi babu alamarsa. Abu kamar al'amara komai ya faru cikin ƙanƙanin lokacin da bai gaza mintuna shabiyar ba. Komawa saman ta yi jiki a sanyaye kanta kuwa kamar an cire mata ƙwaƙwalwa an maye gurbinta da kullin tuwonta guda ɗaya-ta kasa tunanin komai! "Ahhh ahhh...uhmmm" shi ne sautin da yake fitowa daga ɓangaren da Aidan yake kwance ta yi saurin isa gareshi. "Me kake so?" Kansa ya lanƙwasa ɓangaren teburin abincin ta yi murmushin kewar miskinin yaron da tun haihuwarsa bai taɓa taka ƙafafunsa ba ko ya yi magana da bakinsa. Hannuwansa ma a iya saninta da ƙyar yake motsa su komai sai dai ayi masa kamar yadda take samun labari a wurin Mammalo. Wani abincin ta zubo ta zauna ta bashi yana tauna wani na zuba tare da yawu tana gogewa da tissue har ya gyaɗa kai alamun ya ƙoshi. Iyabo tana tsaye tana kallon ikon Allah ganin irin kulawar da uwarɗakinta Oluwatosin Tauhidat Abayomi take bawa yaron. Ko minti biyar bai yi da gama cin abincin ba ya ɓingire a wurin bacci ya yi awon gaba da shi.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull