Cizon yatsa book 1&2 complete - Chapter 25
Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 25: Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 25. Duka mazan tare suka tafi masallacin jikin makaranta bayan sun idar da…
8,117 words
Duka mazan tare suka tafi masallacin jikin makaranta bayan sun idar da sallar la'asar Shaheed ya bada auren Barr. Oluwatosin Tauhidat Abayomi ga Dr. Arƙam Ibrahim Karam wanda Haji Lawalli ya karɓa masa bayan ya biya sadaki naira dubu ɗari lakadan. Ƴaƴan Dada da na Baffa da abokan aikin Shaheed ne suka zama shaidu yayin da limamin masallacin ya shafa Fatiha. Bai iya faɗawa ƴan uwansu ba saboda saurin da suke yi ayi ayi auren. Ya tanadi dogon bayanin ban haƙuri idan ƙura ta lafa sun je gida. Lokacin da Haji Lawalli ya miƙo sadakin Jamal ne ya fara karɓa ya ce idan da kara ai shi ne waliyin Tauhidat. Sai da kowa ya dara aka fito ana taya juna murna. Shaheed dai don farinciki ji yayi kamar an ɗauke dutse daga zuciyarsa. Tun jiya hankalinsa bai kwanta ba saboda tsoron kada ya tashi daga bacci yaji mummunan labari ya kuma afkawa ƴar uwarsa. Da gudu Jamal ya koma gida ya rike hanci yana buga ayiririiii. Nan matar Kashim ta karɓe tana yi Umma ta fito daga daki tace bata iya ba bari ta koya musu. Wato tana karkace baki da Dada ta amsa suka ɗauka tare sai da duka bakin da Nanna ta tara suka firfito falo ana ta murna. Aidan ne kawai take ɓoyo a wani ɗaki kusa da nata da ta cewa mutane store ne. Tauhidat na ciki ta gama bashi abinci ta leƙo ta sama za ta tambayi me ya faru sai ji tayi Anti Nana ta riƙota zuwa ƙasa. Bata ajiyeta ko ina ba sai a jikin Nannanta. Yau abinda basu saba ba suka gani wato matsananciyar kunya daga Haj. Manga harda rufe fuska da laffayarta. Abin sai ya bawa Tauhidat tsoro tana kallonsu tana kallonta. "Nanna an gano gaskiyar Jamal ne?" Ta tambaya don shi take ganin zai sa kowa murna haka. Shaheed ne ya bata amsa da cewa, "In sha Allah wannan ranar ma zamu gani amma yau nayi amfani da matsayina na zaɓa miki abinda nake fatan ya zama alkhairi da kariya a gareki." Jikinta ne ya yi sanyi da Haj. Manga ta kama hannuwanta a gaban kowa ta ce, "a gaban iyaye da ƴan uwana na baki amanar ɗan uwanki yayan Jamal. Idan ya iso gida a gabansu zan bashi taki amanar. Ki shirya direba ya kaiki ku ɗauko shi ya kusa sauka. Saboda idan aka ga Jamal a hanyar airport za a iya zaton guduwa zai yi." Hannuwanta biyu tasa ta riƙe fuskar Tauhidan yadda ta kanyi wasu lokutan "Allah Yasa hukuncinmu bai zama karan tsaye a rayuwarki ba." Kuka Tauhidat ta fashe dashi ta fada jikinta. Maimakon ta bata haƙuri sai ta biye mata. Sariat ce tazo ta rabasu tana cewa Tauhidat taje ta shirya kada su isa a makare. Ɗakin Haj. Manga suka koma inda akwatin da suka taho mata dashi yake na kaya. Tana zaune jikinta na rawa ta gaza gama fahimtar yanayin da ta shiga game da auren. Sariat ta buɗe akwatin tana cewa da ta san haka lamari zai kasance da ta ɗauko mata kaya masu kyau sosai. "Ki gode Allah Tauhidat, ban taɓa ganin mutum mai rike amana da soyayya ta gaskiya ga wanda ba jininsa ba irin Haj. Manga. Bata sati bata kirani don jin lafiyarki ba. Idan Allah Yasa ɗan nata ya karɓi aurenku kiyi iya ƙoƙarinki ki fitar damu kunyarta." Murmushin dole Tauhidat ta ƙaƙalo, "in sha Allah Agent Anti Sariat. Gaskiya kin ƙware a iya riƙe sirri kema. Ban taɓa zargin komai ba." Doguwar riga mai faɗi daga ciki har kasa amma ta kamata daga saman ta wani hadadden material ta bata ta saka tana dariya, "don baki ganni bane jiya da yayanki ya yi min ƙamshin mutuwa." Kalar material din sky da navy blue ne. Santsinsa yasa bata iya ɗaura ɗankwalin ba sai ta yafa wani lallausan mayafi kamar auduga sky blue saboda kalarsa ne mafi ƙarancin adon kayan. Har ta gama shiri Sariat na yaba yadda ta yi kyau ko don amarya ce. Jikinta babu wani ƙwari sai tarin zulumin yadda za ta fuskanci Arƙam. A son ranta ta zauna a gida amma Sariat ta sanar da ita cewa dole ce fitarta saboda Alh. Audi yana hanya kamar yadda ya kira ya sanar da Haj. Manga cewa zai zo. Flat ɗin takalmi fari da purse ta ɗauka ta fito daga ɗakin amma ta kasa sauka sai da Haj. Manga ta hawo da kanta ta fitar da ita waje. A bayan mota ta zauna kamar ruwa ya cinyeta tana zancen zuci. Basu fita daga layin ba sai ga jerin gwanon motocin Alh. Audi sun tunkaro gidan. Ƙasa ta yi da kanta da sauri suka wuce zuga guda. Motocin da ya gani a cikin gidan da aka buɗe musu gate wanda suka sa dole su sai dai suyi packing a waje yake mamaki. Yana da labarin zuwan Dada don musamman zuwan nasa saboda ita ne a yau amma sauran motocin fa? Da suka shiga harabar gidan shi da Alh. Ari ya kasa yin shiru sai da ya ce masa me akeyi a gidan ne haka? "Ina zan sani Alhaji? Mu shiga ciki dai mu gani." An tarbesu kadaran kadahan sannan kowa ya watse aka bar Umma da Dada sai Haj. Manga da kuma Alh. Audi da wazirinsa. Sake gaishe dasu Umma ya yi sannan ya bige da tambayar ko lafiya yaga jama'a da yawa a gidan. "Jikana ake zargin ya yi sata irin wadda hankali ba zai ɗauka ba kaga kuwa zuwa ya zama dole" Umma ta bashi amsa fuska a haɗe. Sunkuyar da kai ya yi cikin sigar munafunci ya ce, "Ayi haƙuri komai zai daidaita don na ɗaukar musu lawyer. Nima fin ƙarfi aka yi min sauran manyan masu hannun jari da abin ya shafa ne suka kai maganar wurin ƴan sanda." "Uhmm" ta ce tana taɓe baki. Dama ya tsani duk wani makusancin Baffa bare ma matarsa shi yasa ya kawar da kansa daga gareta ya fuskanci Dada. Ƙarar Haj. Manga ya kawo mata akan cewa ta gina gida kuma ta tare batare da sani ko izininsa ba. Idan akan abinda ya faru da Jamal ne kada ta manta cewa shi ma ɗansa ne kuma zai yi bakin ƙoƙarinsa wurin ganin cewa babu abinda ya same shi. "Audi" "Naam Dada" ya amsa yana sake kwantar da kai. "Ka sakar min Hafsatu tun kafin nima na shigar da ƙara akanka." Da sauri ya kalleta idanunsa, sun ƙanƙance da ɓacin rai. Oga ya faɗa masa cewa duk abinda ya faɗawa Dada da ita kanta Haj. Mangan idan yazo ba zasu iya yi masa musu ba. To me yake faruwa haka? "Dada ke da zaki yi mata faɗa saboda na san tana jin maganarki sai ki nemi raba auren sunna?" Shewa Umma ta yi ta tashi daga falon da bata da juriyar ganin takaici. Ba ƙaramin aikinta bane ta zazzaga masa masifa. Sai dai tashinta bai dame shi ba kamar kallon da Dada ta yi masa kafin ta ce, "kafin a gama shari'ar Jamal nima zan shigar da tawa ƙarar saboda haka ka sakar min ƴa kawai kada dukan ya zame maka biyu." Bayan Umma tabi ya rage Haj. Manga da Alh. Audi da maganganun Dada suka ɗaure musu kai su duka. A kwanakin nan Dada tana yawan tuna batun gadon ɗanta sai dai kafin ta faɗawa kowa tunanin ke ɓacewa. Da haka zuciyarta ta amince da cewa lallai akwai wani dalili dake kawo mata mantuwar wanda baya rasa nasaba da Alh. Audin. Tashi ya yi kamar zai kifa, ko magana bai yi mata ba ya fita a fusace. Tun kafin ya shiga mota yake dannawa Oga kira yana jin kamar komai nashi ya juye a baibai. *** Saura minti goma jirgin ya sauka Arƙam ya sake kallon agogon hannunsa yana kiyasta mintunan da suka rage ya sake saka Tauhidat a idanunsa bayan shekara goma. Jiya da maganganun Jamal ya kwana kuma ba haƙura ya yi ba da barinsa cikin duhu da suka yi ba amma kewarta ta sake dawo masa da ƙarfinta. Ji yake kamar ya karɓi jirgin ya ƙara masa sauri. 'Allah Yasa babu nisa tsakanin airport da gidan.' Ya cewa kansa shi kaɗai. Sai kuma ya ɗanyi tsaki. Idan ma da nisa ina ruwansa? Ba kulata zai yi ba tunda boko ya fishi taje ta yi ta boko shi ma zai yi hutunsa ne ya koma bakin aikinsa. Yaƙi sosai yake yi da zuciyarsa akan Tauhidat har jirgin ya sauke tayoyinsa a filin jirgi na Nnamdi Azikiwe dake birnin tarayya ƙarfe takwas daidai na dare. Zuciyarsa sai da ta buga yaji wata zazzafar ƙwalla ta taru a idanunsa. Jakarsa ya ɗauko ya fito sanye da rigar da yafi sakawa wato turtle-neck top mai dogon hannu. Pale yellow ce ya ɗora navy blue ɗin blazer da wandonta ya yi matuƙar kyau. Da sauri sauri ya dinga saukowa daga benen jirgin yana shaƙar iskar da ya manta daɗinta. Murmushi ne ɗauke a saman fuskarsa har ya isa wurin immigration aka gama cike-cike saboda passport ɗinsa ba na Nigeria bane. Daga nan ya ɗauko sauran akwatunan kayansa guda biyu aka ɗora kan trolley ya fito. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un." Tuhidat ta ce a hankali domin kafin ya gama fitowa idanunta suka sauka a kansa. Bugun zuciyarta ne ya ƙaru taji daɗaɗɗiyar soyayyar da gudun ɓatawa Nanna rai yasa ta yi ta dako da binneta a rai ta yunƙuro mata gabaɗaya. Gani take kamar a mafarki wai Arƙam ne taku kalilan a tsakaninsu. Waige waigensa yake yi saboda duk a zatonsa Jamal ne zai zo ɗaukarsa. Juyarwa da zai yi idanunsa da na Tauhidat suka sarƙe cikin na juna. Tamkar duniyar ta tsaya cak haka suka kasance suna musayar kallo da saƙwanni ta ido amma an rasa mai motsawa. So yake ta matso gareshi, ya san ba matarsa bace. Amma ko yaya ta ɗaga ƙafa ta ƙara rage tazarar dake tsakaninsu zai iya rage masa wutar soyayyar dake cin zuciyarsa da kuma sauƙaƙa masa fushinsa. Ace shekara goma a banza suka tafi tsakaninsu bayan babu shamakin da ya haramta musu kasancewa ma'aurata. Ita ma tsayuwarta jira take ya ƙaraso. Kunya take ji da nauyi sannan bata manta cewa ɗazu ɗazun nan aka ɗaura musu aure ba. Sun rabu a airport ɗin Jidda cike da damuwar rabuwa da juna gashi sai bayan shekara goma suka sake haɗuwa. Maganar da ya faɗa mata kafin su bar Makka ce ta faɗo mata da yace yana ganin idan ya kuskura ya bar ƙasar bai aureta ba kamar wani abu zai faru. Ashe hasaahensa gaskiya ne. Daga inda yake tsaye yana kallon lokacin da launin idanunta ya sauya, ƙwalla ta taru har ta zubo a duka idanun biyu. So yake ya rungumeta amma dole ya dakatar da kansa. Kamar daga sama muryar direban da ya kawota ta doki kunnenta inda yake tambayarta ko bata ga wanda suka zo ɗauka ba. Arƙam na kallo ta share hawayen da ya zubo akan kyakkyawar fuskarta sannan ta yi masa wannan tsadadden murmushin da bai taɓa mantawa ba. "Gashi nan karɓo jakarsa mu tafi" Yaji tace har sai da muryar da ta haifar masa da kasala da miƙewar tsigar jiki. Kamar mai ɗaga dutse haka ya ɗago ƙafafunsa ya karaso inda suke. Direban yana yi masa barka da zuwa amma ya kasa amsawa sai idanu da ya tsare Tauhidat dasu. Sauke nata idon yaga za ta yi da sauri ya ƙarasa gab da ita ya tsaya. "Don't please! Look at me Cuddles." Ya umarceta. Ita ya bari da tashin tsigar jikin harda rawa ma gabaɗaya, ta dago a hankali amma ta kasa ƙarasa kaiwa ga nasa idanun. Yana nan da wannan tsayin kamar wanda ake ja yasa mutum ya ji ya sake ƙanƙancewa a gabansa. Da tattausan muryar nan tasa ma'abociyar sanyi da daɗin sauraro ya ce, "Ban san me nake jira ba amma for the past 10 years ban taɓa canja layi ba saboda ke. You should have called ko sau ɗaya ne." Buɗe baki ta yi duk da bata san me za ta ce ba amma tana son kare kanta. Ko kalma ɗaya bata furta ba ya ɗaga mata hannu. "Save it, you never cared." Abubuwa da yawa ne suka cushe mata a lokacin. Tana son yin kuka. Tana son bashi haƙuri. Tana son yi masa bayani amma duka bai ma tsaya ba yabi bayan direban suka tafi wurin motar. Bin bayansu tayi jiki a sanyaye har suka isa bakin motar aka fara zuba kayansa a baya. Tana tsaye a jikin ƙofa bata buɗe ba sai jin alamun tsayuwarsa ta yi a bayanta. Hannunsa ya zuro ta gefenta don neman magana zai buɗe ƙofar inda take tsaye. Ɗan baya ta yi don bashi wuri ya buɗe ƙofar sosai taji saura ƙiris ta haɗe da jikinsa. Dakatawa ta yi a inda take don kada ta yi laifi tunda ta kula da rigima ya iso ƙasar. Kansa ya duƙar wurin kunnenta ya shaƙi wani ƙamshi mai sanyi da ratsa zuciya. Kasa daurewa ya yi bai san lokacin da ya ce, "I missed you so much Cuddles" Ya ja numfashi a hankali sannan ya ƙara da, "I wish. I wish I can..." Juyowa ta yi wanda ya yi daidai da barinsa wurin ya buɗe gaba ya shige abinsa. 'I wish i can hug you this minute (ina ma zan iya rungumeki yanzu)' ya ƙarasa zancen da ya fara yi mata a zuci. Daga shi har ita babu wanda ya sake magana har suka isa gida inda iyaye da kakanni suka fito tarbarsa cike da murna. [2/23, 7:34 PM] Nasma: "Kawu are you ok?" Arƙam ya matsa kusa dashi yana ɗan bubbuga masa baya. To a tsaye yake kamar sanda ya kasa komai. Buɗe baki ya yi zai yi magana amma ya kasa cewa komai. Hasalima sai murɗawa da cikinsa yake yi. Fanna da Alh. Ari duk sun miƙe tsaye suna ta cewa Alhaji, Alhaji amma baya jinsu bare ya iya amsawa. Duk inda hannun Arƙam ya taɓa a jikinsa ji yake kamar harshen ita ce ne mai ci da wuta. Shi kuma dan shaƙiyanci bai bar buga masa bayan ba, yana mai bayyana damuwa sosai ya ce da Tauhidat, "Cuddles get him a glass of water." Kamar ta tsaya ta gani ko daga nan zai ƙarasa ya haɗiyi zuciya kowa ya huta, sai dai ta tafi ta ɗebo a dispencer. Kofin ya saka masa a baki ya kuwa shanye ruwan. Yana dawowa hayyacinsa ya yi saurin gyara yanayinsa daga firgici zuwa farinciki. Nan ya shiga matso ƙwallar dole yana bin jikin Arƙam yana shafawa sannan ya ɗaga hannuwa sama. "Allah nagode Maka. Ashe zan sake saka babban ɗana a idanuna kafin na mutu? Alh. Ari ka tayani murna. Arƙam ya dawo garemu" ya ce da amininsa sannan ya sake riƙoshi ya ɗan ɓata rai "Yaushe ka dawo? Ina ka zauna tsahon shekarun nan munata nemanka ni da mahaifiyarka? Ka san irin damuwar da ka sanyamu a ciki kuwa?" "Ni fa kun sakani a duhu" Cewar Fanna "wai kana nufin ɗan wajen Hajiya ne da ake nema? Kodayake ga kama nan amma da gaske shi ne?" "Shi ne Anti" Tauhidat ta bata amsa da murmushi. Alh. Ari zama ya yi, jikinsa babu inda ba ya rawa saboda tsoro. Yadda abubuwa suke tunkaro Alh. Audi yanzu anya babu sa hannun Oga kuwa? Idan kuwa hasashensa gaskiya ne to kashinsa shi ma ya kusa bushewa. Fanna sai murna kamar ta taɓa ganinsa ta dawo kusa dashi ta tsaya, "sannu da zuwa Arƙam. Ni sunana Fanna, antinka ce don bana ce kishiyar Hajiya ba. Muna zamanmu lafiya da ita." Ta gama tambayarsa karatu ko aiki yake sannan ta ce, "Allah Sarki zuwa ka yi saboda abinda ya sami Jamal ko? Ni fa ina ganin idan an tsananta bincike za a gano wannan shegiyar ita kaɗai ta yi komai. Yarinyar bata da mutumci ko kaɗan. Kuɗi ne kawai a gabanta." Haushi ta bawa Alh. Audi ya hau ta da faɗa, "To uwar karaɗi. Shegen baki sai zuba yake kamar ana tatsa nonon tinkiya. Kin haɗa kan ƴaƴanki kun fita ko sai na saɓa miki? Ɗana ya dawo hankalinki bai baki cewa ki bamu wuri mu zanta ba." Kallo suka bishi da shi, yadda yake diri kamar mahaukacin kare. Sai abin ya so bata, mamaki haɗe da dariya. Amma inkiyar da mahaifinta ya yi mata yasa ita da ƴan matanta Kulsum da Aimana da sauri suka tashi zasu fita. Arƙam ya kira yaran. Sunayensu ya tambaya suka faɗa masa a ɗarare saboda kallon da Alh. Ari yake jefa musu. Da fara'arsa saboda daga su har mahaifiyarsu yaji tausayinsu na raɓar Alh. Audi ya zura hannu a aljihu ya ɗauko kuɗin da suka kasance dala, wanda yana da yaƙinin idan aka canjasu anan suna da ɗan kauri, domin be kai ga yin canji ba. Hannun Aimana ya kama yana murmushi, ya damƙa mata wai su sha sweet. "Harda wahala haka?" cewar Fanna ta karɓe kuɗin ta bishi da godiya. Kafin su fita daga falon ta ƙiyasta nawa ne, saboda kuɗi da canji ba baƙinsu bane. A take ta juya darajarsu a kuɗin Nigeria. Ba ƙananan kuɗi bane kuwa. Sake juyawa ta yi ta kalli Arƙam tana jinjina masa da taya Haj. Manga murnar danta ba a tsiyace ya dawo ba. Sai da suka fita ne Alh. Audi ya dena kukan gulmar ya tambayeshi yaushe ya iso kasar ya bashi amsa. Dariyar farinciki ya yi iya leɓe yana neman ƙarin bayani domin kwanciyar hankalinsa, "tsabar ruɗewar ganinka fa da ka yi magana sai ji na yi kamar ka ce Arƙam mijin Tauhida." Ya fuskanci Shaheed "ina mijin nata?" Haɗa baki Alh. Ari da Shaheed suka yi wurin bashi amsar cewa haka Arƙam ɗin ya ce. Zancen ya sake dukansa a karo na biyu da ƙyar ya iya ɓoye ɓacin ransa da wata irin dariya mara fasali. "Wannan shi ake kira dakan ɗaka, shiƙar ɗaka. To amma dama kunsan juna ne ko haɗaku aka yi?" "She is my first love." Arƙam ya bashi amsa yana yi mata wani irin kallo with so much adoration. Kamo hannunta ya yi yana murzawa amma tashin hankalin da take gani a idanun Alh. Audi yasa ta kasa hana shi kamar yadda ta yi niyya. Ganin irin kallon da take masa sai ya soma faɗan rashin sanar dashi auren nasu tunda shi uba ne a garesu duka musamman Arƙam. So yake kawai ya buɗe ido ya dena ganinsu a gabansa, ko ya sami yin tunanin mafita. Koda kuwa samun damar yin magana da Oga ne, amma ba ya son nuna zahirinsa. Dukkansu suka haɗa baki wurin bashi haƙuri, kamar ba zai haƙura ba da farko shi a dole anyi masa laifi. Daga baya kuma ya ce, "Haj. Manga ta san kun yi auren kuwa? Shekara da shekaru tana fushi da marayun yaran nan ba gaira babu dalili." Ya nuna Shaheed da Tauhidat "Idan kuna so nayi mata magana don kada ta kawo muku matsala a gaba kada ku ɓoye min." "Wane maƙaryacin ne ya faɗa maka haka Alhaji?" Shaheed ya faɗa harda zaro idanu wai shi mamaki "bamu taɓa rabuwa da ita ba. Aikin da nake yi ma ita ta sama min kuma yanzu ma haka Tauhidat tana gidanta. Babu wata matsala kada ka damu don Allah." Banda Alh. Ari ya yi saurin danne masa hannu da tashi zai yi ya shaƙe masa wuya. Shi suka rainawa hankali tsahon lokaci yana ganin ya yi nasara ashe sakarai suka mayar dashi. Bai kuma iya cewa komai ba sai yaƙe. Alh. Ari ne uban gulma ya tambayi taron me suka yi jiya aka yi sa a Tauhidat ta bada amsa daidai da ta Umma cewa jaje suka zo. Ta ƙara da cewa gobe kafin su koma zasu biyo domin yi masa ta'aziyya da jajen Shamsu. Da haka Arƙam ya miƙe tare da Tauhidat. "Cuddles its getting late. Ki kaini na duba Shamsu ɗin." Murya a shaƙe kamar ƙozon kwaɗo Alh. Audi ya ce musu ya riga ya bar ƙasar zuwa asibiti tun safe. "Yarinyar nan Suwaida kanta ta cuta ba ni ba. Da kaina na kira mahaifinta na faɗa masa abinda ya faru amma har yau babu wanda yazo. Tunda taƙi yarda ki karɓi case ɗinta kuma ita ta sani." Murmushi ta yi kafin ta sakar masa bayanin da ya sa shi haɗe fuska har suka fita. Tunda ta fara cewa sun daidaita daga ita har Jamal sun amince ta zama lauyansu yaji zufa na keto masa. Da farko ya so amfani da ita ne don ya haɗasu su duka ukun ya kawar dasu sai ya ɓoye hakan a bayan shari'a. Mutum ɗaya ya ɗauka a matsayin lauyan Shamsu da kuma mai wakiltar kamfaninsu da aka yiwa sata. Yafi shekara ashirin yana aiki kuma da wuya ake kayar dashi. Tauhidat ba komai bace a kansa. Amma yanzu da tazo tare da Arƙam ɗin da duka su biyun Oga ya gargaɗe shi a kansu sai yake jin kamar ƙabarinsa ya tona da hannuwansa. Ihu sosai ya saka bayan fitarsu ya dinga bin kayan falon yana fasawa kamar sabon mahaukaci. Alh. Ari ma gefe ya koma don kada a haɗa dashi. Daga waje suna jin ihunsa sai suka ji tsit. Su ukun duka dariya suka dinga yi musamman Shaheed lokacin da Arƙam ya tambaye shi ko Alh. Audi suma ya yi da suka ji shiru. Basu yarda sun ɓata lokaci a cikin gidan ba kowa ya shiga mota suka tafi. Shaheed gidan wani abokinsa zai wuce su kuma su tafi gida. Tafiyar tasu yanzu babu sauri saboda cushewar hanya. Rediyo ta kunna tana neman tashar da zata bar musu saboda shirun ya yi yawa. Idanun Arƙam ke bibiyarta ko kunyar kada ta kama shi baya yi. Ɗazu a tafiya dayake tuƙi take sosai tafi dauriya. Yanzu kuwa sai ayi minti goma mota bata motsa ba. Ta rasa me ya kawo wannan tsaikon ake ta tafiyar hawainiya. Tana nata tunanin shi ma da yake kallonta ransa bai huta ba. Zuciyarsa ta kasa gaskata masa cewa Tauhidat ce a tare dashi kuma a matsayin matarsa ta sunna. Gani yake kamar idan ya ɗauke idanunsa daga gareta zai iya farkawa ya ga ashe jiya da yau duka a mafarki suka faru. Zai so hakan ta kasance a ɓangaren Jamal amma akan abinda ya shafi Tauhidat inama babu abinda ya taɓa rabasu. Kusan a tare suka buɗe baki da niyyar magana sai ta yi shiru ta bashi dama ya fara. Kada kai ya yi "ladies first." "Na bar maka." "Ina bukatar simcard. I need to make an important call tonight (akwai wayar da zanyi mai mahimmamci a daren yau)." Haka kawai taji wani abu ya tokare mata wuya da ta yi tunanin ko mace zai kira. Daga zuwa a tunaninta ko hutawa bai yi ba yake zancen wani sim. "Ka bari sai gobe, wannan hold up ɗin ban san yaushe zamu fita ba kuma ga yamma." "Zan iya amfani da taki kafin goben?" Ya ɗauki wayarta yana juyawa a hannunsa. Hannunta ta miƙa masa tana kallon titi don bata ma son ta kalle shi tace ya bata abarta. Maimakon wayar sai ya ɗora nasa hannun a kai ya dan matsa. "Meye na bata rai ba girlfriend ɗina zan kira ba." Duk yadda taso dannewa sai da murmushi ya subuce mata. Ɗauke kai ta yi ta basar kada yaga kamar ta wani damu dashi fiye da yadda shi yake nuna tasa damuwar. "I don't believe you are jealous Cuddles (ban yarda kishi na kike yi ba). Shekara nawa kin kasa nema na ko sau ɗaya. Abinda kika yi bai yi min daɗi ba seriously." Dama ta san sai ya yi wannan ƙorafin. A matse take su isa gida saboda a ganinta zancen ba na mota bane. Suna buƙatar zama sosai suyi magana ta fahimta. Sai da suka isa gida tace masa, "Ka ari wayar Jamal ko Nanna kayi important call ɗin sai muyi magana akan abinda ya faru a baya idan ka gama." "Wayar tawa sai can dare around midnight so gara muyi maganar da wuri." Kamar ta yi masa kuka ta fita daga motar bayan ta harare shi. Idan ba mace ba wa zai kira cikin dare? Fita ta yi ta leƙo da kanta kafin ta rufe ƙofar. "Kuma ba zan zo ba, gobe zani office da wuri zan kwanta." Ɗage gira ɗaya ya yi cikin halin ko in kula da fushinta bayan a ransa daɗi yake ji ya ce "Na fa san inda kike kwana." "Idan Nanna ta kamaka babu ruwana." Ta wuce tana ƙunƙuni. Sai da ta ɓacewa ganinsa ya bi bayanta. A can wurin dinning table ya hangota tare da Nanna da Jamal tana magana. Ji akayi sun bushe da dariya su biyun sauran mutanen falon suka ce dole ayi dasu, su dawo cikinsu aji labari da kyau. Zamansa ya yi ita kaɗai ke bada labarin harda zaro idanu yadda Alh. Audi ya yi lokacin da ya gane Arƙam. Komai nata yana burge shi. Babu abinda yafi masa daɗi kamar yadda take mu'amala da danginsa. Kowa yana nuna mata so kuma itama halayenta bai ga na kushewa ba. Bayan sun yi sallah ne yake jin cewa washegari gidan zai watse. Umma da Dada ne kawai zasu rage sai kawunnansu biyu. Ɗaya daga Kano ɗaya daga Maiduguri. Jibi zasu tafi Abeokuta tare da Haj. Manga da Shaheed akan auren da aka ɗaura ba tare da sani ko izininsu ba. A take Arƙam ya ce zai bisu Haji Lawalli ya goyi baya. Gara aje dashi su san cewa da gaske yake zai riƙe musu ƴa. Gidan zai rage Tauhidat, Aidan da Jamal sai kuma sabuwar mai aikin da zata fara gobe. Wurin takwas da rabi na dare Tauhidat ta tafi ɗakin baƙi matar Kashim za ta yi mata kitson bare-bari. Sai da ta wanke kan ta yi steaming tunda zuwa salon bai samu ba. Ta sha gyangyaɗi kafin a gama saboda yawansa da ƙanƙanta. Bai fi biyar ya rage a gama ba ta wartsake daga baccin. Su biyu ne ido biyu kowa ya yi kwanta. Lokaci ta duba ta sake ware ido don mamaki. "Anti shadaya fa ta wuce. Guda nawa ki ke yi?" Anti Yakura ta yi dariya, "ban ƙirga ba amma anyi ɗari biyu ina jin. Kitson yafi kyau a irin wannan kan mai cika sosai. Ko gajiya bana yi saboda yana tafiya yadda nake so." "Anti tsifa fa" ta shafa kan tana tausayin kanta ranar da zai tsufa. "Mijinki aikin me yake yi, ba sai ya tsefe miki ba." Shiru Tauhidat ta yi tana murmushi taji Anti Yakura ta ce, "gulmammu kuna so kuna kaiwa kasuwa. Leƙowarsa ɗakin nan ta yi huɗu kina bacci wai aron wayarki zai yi. An bashi amma ya ce kin rufeta. Shi ne yake ta mana sintiri ko kin farka kuma yaƙi yarda a tasheki ki bude masa." Bata manta sun yi zancen waya ba amma ta zata zai karɓi ko ta Jamal ne shi yasa ta tafi kitson hankali kwance. Maganar da ya ce za suyi ce tasa ta so gujewa kitson Umma ta ce sai an gyara mata kai. Tana can tana tunanin ransa ya ɓaci ko bai ɓaci ba Anti Yakura tana yi mata zancen yadda zasu sha biki idan an gama case ɗin Jamal. Shaɗaya da ashirin aka gama kitson ta tashi jiki ya yi tsami. Godiya ta dinga yiwa Anti Yakura ita kuwa tana cewa yiwa kai ne. Sauri take taje tayi wanka ta samu ta kwanta saboda fitar safe gobe. Za ta fita Antin ta bata wata ƙaramar kwalba da bata fi girman ƙaramin yatsa ba mai kyau. "Ki dinga shafawa bayan kinyi wanka da daddare, da safe ko baki saka komai ba in kin yi wanka babu ke babu warin gumi. Kina iya sake sakawa amma fa idan ba zaki fita ba. Dan kaɗan za ki dinga shafawa domin ƙarfi ne dashi." Ta kwatanta mata kaɗan ɗin da yatsa. Sabuwar godiya ta sake yi mata sannan ta fita. Ɗakin da suke kwana ita da Aidan taje. Da tunanin yadda za ta barshi shi kaɗai ta shirya tafiya kitson sai Dada ta shiga ɗakin. Yanzu kuma da ta hau bacci ta same shi suna yi shi da Haj. Manga. Murmushi ta yi tana ƙara yabonta a ranta. Tabbas cikakken musulmi shi ne wanda baya kama wani da laifin wani nasa. Dubi yadda take kaffa-kaffa da jikan Alh. Audi kamar ba shi ne babbar matsalarta a duniya yanzu ba. A hankali ta tasheta ta tafi ɗakinta ita kuma ta shiga wanka. Bayan ta shirya cikin doguwar rigar bacci ta gama ƴan shafe-shafenta ta ɗauko turaren tabi jikinta ta saka. Ƙamshinsa akwai daɗi sai lumshe idanu take a gaban madubi tana kallon kitsonta da suka kwanta yar-yar a kan kamar da inji aka ɗora shi. Alamun taɓa ƙofa taji ta tafi da sauri ta danneta don kada a ga Aidan. "Wa. Waye?" Ta ce daga jikin ƙofar tana kallon agogo. Shabiyun dare lokacin. Rawar da muryarta take yi yasa Arƙam murmushi, "matsoraciya. Buɗe min ko na buga da ƙarfi kowa ya tashi." Maimakon hankalinta ya kwanta sai rawar jikinta ta ƙaru. Me kuma ya kawo shi a daren nan ta tambayi kanta. Da taga babu mai bata amsa sai ta ce ya jira tana zuwa. Kamar ya san abin lulluɓi take son ɗauka kafin ta buɗe masa ya murɗa hannun ƙofar ya shigo. Bata kai ga ɗaukar mayafin ba ya riƙota ta baya ta faɗo jikinsa gabaɗaya sauran kaɗan su kai ƙasa. Shi ya daidaita musu tsayuwa ya duƙar da kansa daidai wuyanta yana shaƙar humran da ta shafa. Magana ya yi mata a kunne wadda duk da kusancin tsayuwarsu ita kanta da ƙyar take iya jin me yake cewa. Tamkar daga bacci ya tashi muryarsa ke fita cikin wani irin salo mai ɗaukar hankali. "This is intoxicating (bugarwa), ina son ƙamshin sosai Cuddles." Tsabar ruɗewar da ta yi sai cewa ta yi, "yanzu aka bani idan kana so gashi can ka ɗauka." Lips ɗinsa taji a kasan kunnenta ya dan ciza a hankali sannan ya ce, "Ba fa turarenki nake so ba Madam..." "To. To. Me kake so?" Ta tambayeshi gabanta na tsananta faɗuwa. "Kinfi kowa sani." Yanayin maganarsa ne yasa tsoronsa ya kamata. Wani abu na kusanci makamancin haka bai taɓa haɗata da wani namiji ba idan ka cire ranar da Shamsu ya far mata a ɗaki. Da ya fuskanci a tsorace take sai ya zura hannuwansa ya rungumota sosai a jikinsa har lokacin tana kallon gabanta. Kwantar da kansa kawai ya yi a tsakanin wuyan nata yana jin nutsuwa da farincikin da bai taɓa tunanin samu ba. Muryarta can ƙasa kamar mai tsoron magana ta ce,"ka cikani kada Aidan ya tashi." Kasa haƙuri ya yi sai da ya bata peck a gefen haɓarta wanda ya ƙarasa firgita zuciyarta da tsoro da kunya. Da gangan ya ce su tafi ɗakinsa don yaji me za zata ce. Ɗif ta haɗiye abinda za ta sake faɗa gudun kada ta tunzura shi. A yadda suke a tsayen ya kama yatsanta ya zuro wayarta ta gabanta ya ɗora a kai. Dama lock ɗin mai sensor ne na yatsan mai ita. Yana ɗorawa wayar ta buɗe. Da yatsan nata dai ya danna wasu lambobi sannan ya saketa. Kamar jira take da sauri ta faɗa kan shimfiɗarta a gefen gadon ta duƙunƙune jikinta. Tana kwanciya Arƙam ya kashe fitilar ɗakin ya dawo inda take ya zauna jingine da gadon. Kanta ya ɗora a cinyarsa yana bin kitson layi layi yana shafawa har aka ɗauki wayar. Jikinta babu inda baya rawa don firgici da wani irin yanayi da bata taba kasancewa cikinsa ba. Ba jin abinda ake faɗa sosai take yi ba amma ta gane muryar namiji ce. Cikin duhun ta saki murmushi duk da halin da ya jefata a ciki. Shi din ma ya daure ne gudun kada ya karasa tasa raunanniyar zuciyar. Da Director Zhang yake wayar. Shi ma ya tafi China jiya. Sun taɓa hira ya tambaye shi lafiyar duka patients ɗin da ya bari a Yemen sannan ya yi masa magana akan wani aiki da suka fara kafin ya taho. Duka hirar abinda ya shafi aikinsa ne. Kusan rabin awa suna tattaunawa sannan suka yi sallama. Gefen fuskarta ya shafa bayan ya gama ya kira sunanta a hankali, "Cuddles." Sake matse idanuwanta ta yi a zuwan bacci take harda dauke numfashi. Da wayar ya haska fuskarta yana kallon yadda take ta sake runtse ido. "I can't leave without saying goodnight gashi kuma kinyi bacci." Zame kanta ya yi daga cinyarsa ya dora akan pillow yana cewa zai kwanta a kusa da ita saboda kada ta farka tace bai kyauta ba. Rasa inda zata saka kanta ta yi da taji ya kwanta a kusa da ita. Kunya ce ta yi masifar lulluɓeta kamar ta tsaga kasan ta bace. Da hannu daya ya tallafi kansa, daya hannun kuma ya cigaba da haske mata fuska. Ƙara hasken ya yi yadda zai dameta ai kuwa ta yi ta ɓata fuska yana murmushi. Basu fi minti biyar ba ta buɗe idanun tasa hannu ta ture wayar daga fuskarta. Har kin gaji kenan." Arƙam ya ce yana dora wayar a bedside drawer. "Ni ka tashi ka tafi." "Cuddles am I nameless to you? (Bani da suna a wurinki?)" ya ce kamar yana fushi, "ina laifi ko Maigida ki dinga kirana." Ya faɗa yana nunata da yatsa, "kuma saura kiyi dariya." Dariyar kuwa ta dinga yi ƙasa-ƙasa kamar ya zuguta. Cikin duhun ta kalli saitin inda yake ta ce "sorry D." "Doctor? Darling? Dear? Dolo? Daskindariɗi?" Tauhidat bata yi ƙoƙarin danne dariyarta ba wannan karon. Banda sunan karshen harda yadda ya faɗa yasa ta dariya tana dai ta ƙoƙari kada sautin ya fito sosai. Bata yi aune ba taji ta a ƙirjinsa ya rungumeta yana mata magana a kunne. "D for Daskindariɗi? Are you serious? Prince ɗin tatsuniyar Dada ne fa" ya ce sounding horrified. Idonta har ƙwalla ya tara don abin yafi ƙarfinta. Ta maimaita Daskindariɗi yafi a ƙirga tana dariya. Shi kuwa ji yake ba don Aidan ba da babu abinda zai hana shi kwana a ɗakin ko yasa ta bishi ƙasa. Cikin ƙanƙanin lokaci ta sake shigewa kowane ɓangare na zuciyarsa. Murmushi yake yi har ta dena dariyar ta ɗan ture shi. "Ka zo ka tafi please kada na kasa tashi da wuri gobe?" "I was trying to be a gentleman, kada na tafi ban yi miki sai da safe ba." Ɗago kanta ta yi daga ƙirjin shi, "Allah Ya tashemu lafiya ni dai ka tafi." "Ki rakani zuwa step na tsakiya sai ki dawo." Ya ce tare da tayar da ita tsaye. Don ya tafi ɗin sai ta amince. Yana riƙe da hannunta suka fito daga ɗakin. Tana tako ƙafarta ƙofar ɗakin hasken fitilar wurin ya sauka akan rigar jikinta. A gigice ta ƙwace hannunta ta turo ƙofar da suka haɗa ido taga irin kallon da yake mata. Wata shu'umar dariya ya yi wadda shi kaɗai ya san ma'anarta ya soma sauka benen. "Arƙam daga ina haka?" Yaji muryar Haj. Manga wadda bugun ƙofar Tauhidat ya taso ta. Sai yanzu yaji kunya da faɗuwar gaba, ya ɗaga hannuwa kamar wanda aka zo kamawa "uhmm, yes, waya ce." Don kada ya tona kansa ya gyara tsayuwa "Nanna waya na ara." "Waya? A tsohon daren nan kuma? To a wurin wa?" Ta tambaya duk da ta riga ta san amsar kuma hakan ya faranta mata rai. Tana ta tsoron kada ya dawo ya watsa mata ƙasa a ido akan auren saboda ƙorafin da ya dinga yi. A hankali yana sosa ƙeya ya ce, "a wurinta. Bani da sim ne kuma wanda na kira yana China, safiya ta yi a can." Riƙe dariyarta ta yi ta harɗe hannuwa a ƙirji, "ita wa kenan?" "Cuddles mana." Haɗe gira ta yi tana masa kallon tuhuma ya yi saurin ƙarawa da cewa, "babu abinda nayi mata fa. Daga aron waya sai ki dinga yi min wannan kallon Nanna its not fair. Da nayi wani abu ne kamar..." Da sauri ta soma kora shi tana cewa, "Sauka ka tafi sai da safe." Yana sauka ya ɗago suka haɗa ido ya kanne mata ido ɗaya. Daƙuwa ta dinga yi masa ya arce ya barta a wurin. "Kaga shakiyin yaro. To duk abinka sai ka jira na shirya. Dama a gwauro ka taho sai ka ƙara haƙuri." Ɗakinsu Tauhidan ta buɗe ita kuma a tunaninta Arƙam ne ya dawo. Daga inda take kwance ta ce "don Allah ka tafi kada Nanna ko wani ya ganka." Haj. Manga taji inama bata fito ba. Wai don ta kashe maganar sai ta ce, "Tauhida nice." Baiwar Allah sai ta sake rikicewa bakinta yana harɗewa ta soma bayani. "Wallahi babu abinda ya yi Nanna. Wayata kawai ya ara ya kira wani." Murmushi Haj. Manga ta yi mata daga bakin ƙofa, "babu komai yi kwanciyarki." Maida kai ta yi niyyar yi kan pillow ta kwanta ta kasa. Zuciyarta ke raya mata kamar Haj. Manga bata yarda da ita ba. Tana rufe musu ƙofar ta buɗe da sauri tabi bayanta da wayar a hannu. "Wallahi Nanna waya yazo karɓa. Kin san bashi da sim ɗin nan. Nima sai da na ce dare ya yi." Tana magana tana danna wayar ta nuno mata call log, "kin gani numbar wata ƙasa ce, ai dai kin san bani da kowa a wata ƙasar. Gashi minti ashirin da shida suka yi shi yasa ya daɗe." "La ilaha illalahu" cewar Haj. Manga tana ɗora hannu ɗaya a ka, "ki dena rantsuwar na yarda. Ko kina da wata uwar da ta fini sanin halinki ne?" Girgiza kai ta yi hankalinta na kwanciya amma duk da haka sai da ta ce, "kin yarda dani ko Nanna?" "Na yarda dake Tauhidana jeki ki kwanta." *** Daga sallar asuba bata koma bacci ba ta yi wanka. Kafin ta gama shiryawa Umma ta shigo zama da Aidan. Idan Haj. Manga ta fito sai ta yi masa wanka ta bashi abinci idan ya tashi. Da taje gaisheta sauran su Anti Nana da masu kwanan ɗakin baƙi duka suna tare an kafa hirar asuba. Tambayar abinda za ɗora na breakfast ta yi Anti Yakura ta ce kada ta damu zasu sauko su ɗora. Ta dafa koma meye iya cikinta. Banda ma dole me zai sa amarya tashin asuba ta fita aiki. Sallama ta yi musu da fatan isa gidajensu lafiya tunda zasu tafi kafin ta dawo. Ta sauko falo kenan taga kira daga Jamal. Tunanin ko zai sake tambayarta ƙarfe nawa zai je office saboda tambayoyin da zata yi masa ta yi. Tana kara wayar a kunnenta taji muryar Arƙam. "Morning Cuddles." Ƙaramar dariyarta yaji kafin ta ce, "Morning D, ka tashi lafiya?" "Daskindariɗi ya tashi lafiya" Ya bata amsa da murmushi. Jamal dake kwance bayan sun dawo daga masallaci bai san lokacin da ya yaye bargon rufarsa ba. "Daskindariɗi? Daskindariɗi dai na assalam salam ɗan yaro?" Ya tura bakinsa jikin wayar "ƙanwata meye haka don Allah? Duk sunayen duniya ki rasa ..." Toshe masa baki Arƙam ya yi ya fita da niyyar komawa nasa ɗakin ya ganta a tsaye ta juya masa baya. Motsin ƙofar ne yasa ta juya suka haɗa ido. Saurin kawar da nata ta yi da ta tuna yadda suka kwashe jiya. Tana kallon ƙasa ya iso gabanta, "D for?" "Idan na dawo zan faɗa maka wanda na zaɓa." "Shikenan ina jira" Ya ce kawai ya kaita zuwa wurin dinning table yaja mata kujera ya ce ta zauna kuma bai yarda ta motsa ba. Umarninsa tabi don bata so su tsawaita magana a sauko a gansu. Tana jiyo alamun yana amfani da kayan kitchen da ƙamshi ta tashi ta leƙa. Ƙwai ta tarar yana soyawa ya zare mata ido tare da nuna mata ta koma inda ya barta. Ba musu ta tafi zuciya da gangar jiki suna ƙara faɗawa soyayyarsa. Tea ya haɗo mata a mug da bread sai ƙwan da ya soya ya ajiye a gabanta. Bai tashi ba sai da ya tabbatar ta ƙoshi ya rakata har bakin mota ta shiga ya rufe ƙofar. "Nagode" ta ce a kunyace. "Ba godiya nake so ba. Do your best to save our bro (ki yi ƙoƙari wurin ceton ɗan uwanmu)." "In sha Allah zanyi ƙoƙari, ka tayani addu'a kaima." "Always Cuddles" Ya shafa fuskarta. Kasa dauke ido ta yi daga kallon da yake mata sai da ya hura mata iskar bakinsa, "still in love with me (Har yanzu kina sona)?" "Always D." Tana bashi amsa ta yi ribas da motar ta fita daga gate ɗin da Maigadi ya buɗe tun fitowarsu. *** "Ki manta da sanin da kika yi min a secondary school. Ki manta da mun taɓa auren miji ɗaya da duka abinda ya biyo baya a rayuwarmu. I am your lawyer, I need you to trust me (ni lauyarki ce, ina bukatar ki amince dani) ki faɗa min gaskiya. Idan kika ce zaki duba waɗancan abubuwan na baya ki ɓoye wani abu ina mai tabbatar miki zaki iya ƙare rayuwarki a kurkuku." Susu kallon yadda Tauhidat ta rikiɗe tana magana babu alamun wasa ko wargi ta yi, taji ta ƙara aminta da zaɓarta da ta yi ta wakilceta. Wannan ba Tauhidan da ta sani bace, lauya ce a gabanta mai zaman kanta wadda ta san kan aikinta. Ajiyar zuciya ta yi, "[dan ban yarda dake ba ma wa ya rage min yanzu? Ban taɓa zaton zan ga rana irin wannan ba. Har yau babu wanda yazo daga gidanmu kuma na san cewa yanzu maganar nan ta zaga ko ina." Ƙwallar da ta soma taruwa a idanunta ce tasa Tauhidat kara tausaya mata. "Amma su kuwa me zai sa su gujeki a wannan yanayin da kike ciki? Musamman ko don baby ɗinki ina ganin kamar mamanki zata fi bata kulawa akan Nanny." "Hmmm Tauhida kenan, iyayena basu gujeni ba, ni na guje musu." "Saboda kin auri mai kuɗi?" "Ɗan maikuɗi ba maikuɗi ba." Gani ta yi zata tonawa kanta asiri sai ta canja zancen da cewa ta yi mata tambayar da ta shafi case ɗin. Ba haka Tauhidat taso ba. So ta yi ta yi maganar da ta danganci nadama domin ta tayata neman sulhu da ƴan uwanta. Abubuwan da ta yi mata a baya musamman sharrin nan yana nan manne da zuciyarta to amma idan suka tafi a haka ribar Alh. Audi ce. Yadda ta san shi zai iya amfani da abinda ta yiwa iyayenta lokacin auren Shamsu ya nuna kwaɗayinta a kotu. Jerin tambayoyin da ta tsara ta fara jero mata tana bata amsa. "Ina son ki faɗa min duk abinda zaki iya tunawa akan Shamsu a ranar da abin ya faru." Bakin gwargwado ta faɗa mata abinda ta tuna ta ƙara da cewa, "abu ɗaya ne ya dameni a cikin ƴan kwanaki kafin abin ya faru." "Me kenan?" "Yana yawan zama shi kaɗai a ɗaki da tunani. Sai kiyi ta magana ma bai ji ba. Na san cewa lokacin lalurarsa ta yi ƙarfi sosai amma duk da haka na lura akwai abinda ke damunsa bayan wannan." "Wace irin lalura ce?" Ta tambaya ba don tana ganin amsar za ta zama da mahimmanci ba. Abinda take ta ɓoyo yau ga sanadin faɗarsa ya taso. Nauyi taji ta ɗan duƙar da kai "yana fitsarin kwance." Tauhidat ta ce, "zancen Shamsu muke yi ba Mubeen ba." "Na sani. Kin yi mamaki ko? Ya ce min tun yana da shekara goma sha shida ya fara." "What?" Ta ce mamaki ya kusa kasheta a zaune. Sai ta tuna a wane matsayi take a wurin ta gyara maganar, "bai neman magani?" Iya neman da ta san sunyi da wanda take yi a gefe ita ɗaya tsakanin bokaye da malamai ta dunƙule ta ce mata suna nema amma ba'a dace ba. Rubutu tayi a ɗan littafin gabanta sannan ta ce, "to amma daga fitsarin kwance Susu sai kuma kawai ki ce ya yiwa Mubeen fyaɗe?" Tsigar jikinta sai da ta tashi da ta tuna yanayin da ta kama shi da ɗan nasu. "Ba sharri nayi masa ba. Abinda yasa ni bin bayansa ma wayar da ya yi ce da rana amma ban san da wa yake yi ba. Naji dai yace ana buƙatar ya gama kafin biyun dare. Ban ɗauki maganar da mahimmanci ba sai da na farka kusan lokacin naga baya ɗakin. Shi ne na bishi na gansu." "Kina da labarin cewa report ɗin ƴan sanda ya nuna hatsari ku ka yi da kika gudu dashi wanda ya yi ajalinsa?" Ƙaryatawa Susu ta yi kamar yadda ta yi tsammanin zata yi ɗin. Bayan waɗannan tambayoyin sai ta koma batun satar kuɗi wanda shari'arsa za a fara yi. Shi ma dai Susu ta yi rantsuwa ta ƙara da cewa bata da account a kowace ƙasa sai Nigeria. Banda kuɗaɗen da Shamsu yake bata a hannu ko transfer akwai kuma allowance da kamfanin Karam Holdings ke tura mata duk wata. Ƴaƴaanta ma kowa nada shi. Abin ya sake zamewa Tauhidat sarƙaƙiya saboda ga shaidar saka hannun Jamal da na Susu akan takardar bankin da suka tura kuɗin. Joint account (na haɗin gwuiwa) suka buɗe ga kuma takardar yarjejeniyar idan kudin ya samu za suyi raba daidai. Agogo ta duba taga lokacin da ta bawa Jamal yaje office ya sameta ya kusa dole ta katse tambayoyin zuwa washegari ta tashi. Kiransa tayi bayan ta fito daga station ɗin taji muryarsa ba yadda ya saba yi mata magana ba. Hankalinta a take ya tashi ta soma yi masa tambayoyi. "Asibitin Dr. Madaki zamu je. Flask ɗin ruwan zafi ne ya faɗowa Arƙam a ƙafa." Allah Yasa bata tayar da motar ba, da ƙila ta dokawa wani saboda fargabar da ta kamata lokaci guda. "Ya ƙone?" Ta tambaye shi a sanyaye cike da fargaba. "Shi dai ya ce bai ƙone ba amma abin cikin flask ɗin ya yanke shi a babban ɗan yatsa." Muryar Dada taji tana cewa Jamal yazo su tafi asibitin kada ya biye masa. Yadda jini yake zuba tana ganin sai anyi ɗinki a yatsan. Maganganunta sun sake tayarwa Tauhidat hankali. Hanyar asibitin ta nufa ko su rigata ko ta rigasu isa. Can kuma a gida anata rigima da Dada da Arqam. Ya dage bai ƙone sosai ba kuma yankan ma babu girma amma ta kafe wai ya zubar da jini ya kusa lita guda. Saboda a kwantar mata da hankali Haj. Manga ta ce suje ko plasta ne a manna masa a kafar su dawo. Suna fita Arƙam ya ce ya kaishi pharmacy sai ga wayar Tauhidat. Tambayar Jamal tayi ko sun kusa isa asibitin don har ta shiga reception ance basu zo ba. "Muje asibitin kawai kaga Tauhida tana can." Rai a ɓace Arƙam ya ce,"faɗa mata kayi? Why?" "Matarka ce fa, kuma kirana ta yi bani na kira don na faɗa ba" shi ma ya sha kunu. Ɗauke hanya suka yi zuwa asibitin suna hararar juna. *** "Ka san Allah Doctor sai ka faɗa min wanda ya ce ka canja report ɗin Mubeen" cewar Shamsu yana cije baki saboda azabar ciwon da yake ji a cikinsa. A tsaye yake ya dafa bango cikin ɗakin da yasa Dr. Madaki ɓoye shi saboda kada ya bar ƙasar. Dr. Madaki yana tsoron fada masa gaskiya bai sani ba ko bakinsu ɗaya tarko ne Alh. Audi ya ɗana masa. "Kaga ni dai idan ba zaka faɗawa Alhaji cewa baka tafi ba jiya kamar yadda ya umarta to ka bar min asibitina. Bana son wani abu ya same ni haka kawai. Abinda na gani na rubuta." Da ƙarfi Shamsu ya ce,"ƙarya kake yi. Da idona na shaida tabbas wani ya yi raping ɗin ɗana. Kuma ga alamu sun nuna ko waye baya son duniya ta sani." Manunin yatsansa ya kai gaban fuskar Dr. Madaki, "hatta uban da ya haifeni bai san waye Shamsu ba. Na sani ban kula da rayuwar yarana ba a baya amma ko zan rasa raina sai na gano abinda yasa ake ɓoye dalilin mutuwar Mubeen." Gwada sa'arsa ya yi cikin dakewar murya Dr. Madaki ya ce, "Shamsu kada ka tona abinda ake son binnewa domin kwanciyar hankalin gidanku." Mummunan kallo ya jefawa Dr. Madaki a lokacin da maganar ta soma fassara kanta a ƙwaƙwalwarsa. Jikinsa na rawa ya ce, "kana nufin Baba ya san ko waye?" Amsar likitan bata kai kunnuwansa ba yaji cikinsa ya bala'in murɗawa. Riƙe wurin ya yi a tare suka kai kallonsu ga cikin sai ga jini ya fara naso a jikin rigar. Neman faɗuwa yake yi Dr. Madaki ya tare shi da sauri ya ɗora akan gado. Yana ɗaga rigar yaga yadda yake zubar da jini alamun an sami matsala a aikin da akayi na farko. Bai san iyakar ciwukan da suke cikin Shamsu ba saboda jinyarsa kawai aka kawo musu. A wani asibitin gwamnati akayi masa operation dmɗin kafin Alh. Audi ya canja masa asibiti. Cikin sauri ya fito daga ɗakin ya sauka neman likitan da zai taya shi aiki don ga dukkan alamu dole a sake buɗe cikinsa.