Cizon yatsa book 1&2 complete - Chapter 26
Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 26: Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 26. ALHAMDULILLAH Allah SWT Ya sake kawo mu karshen kasha na biyu a cikin…
1,552 words
ALHAMDULILLAH Allah SWT Ya sake kawo mu karshen kasha na biyu a cikin wannan labari. Domin jin sirrin da Alh. Audi yake ta boyewa da ma yadda za ta kaya gabadaya ku nemi kasha na uku kuma na karshe a labarin CIZON YATSA.
SonSo Batul Mamman. [2/23, 7:34 PM] Nasma: Ganin su Dada da iyayensa da ya daɗe rabon da ya saka su a ido yasa shi sakin jiki. Jansa kawai ake yi ta kowane ɓangare ba mazan ba, ba matan ba. Bai san ta yadda zai kwatanta farincikinsa ba. Amma a haka yayi ta raba idanu yana neman ɗan uwansa rabin jiki. Ayi faɗa a shirya duk da haka basu da kamar junansu. Ta bayansa yaji an rungumo shi da ƙarfi ana dukan kafaɗarsa. "Big Broooo." Ba kowa bane ya sani sai wanda yake ta nema. Haɗe rai ya yi yana cewa ya sake shi. "Kai kuwa Arƙam yaron nan wuni ya yi yana zancen dawowarka amma shi ne kake korarsa haka. Zo nan kaji Jamal." Anti Rabi'a ta janye shi ya ɗora kansa a kafaɗarta yana yiwa Arƙam gwalo. Dariya ya bashi ya fasa mitar me ya hana shi zuwa ɗaukarsa daga airport saboda ganin wani yana masa murmushi. Kallo ɗaya ya gane shi duk da ko a hoto bai taɓa ganinsa ba. "Brother Shaheed yau dai mun haɗu." ya ce yana miƙa masa hannu tare da mayar masa da martanin murmushinsa. Mamakin kamaninsa da Haj. Manga Shaheed yake yi ya ce masa, "Ko a waje na ganka ni dai zan kamoka na kawo gida saboda kamaninka da Nanna." Kamar wasu daɗaɗɗun abokai suka taɓa hira. Shaheed ya gabatar masa da iyalinsa suka gaisa da Sariat sannan ya tambayi yaran sunayensu. Gefensu an jera kujeru da tebura manya guda uku wadanda zasu dauke duka mutanen. Ga abinci ana ta jerawa domin gabatar da karamar walimar cikin gida ta murnar dawowar Arqam da aurensa da Tauhidat. Haji Lawalli ne da wannan kokarin saboda ya tunatar dasu cewa sunna ne gabatar da walima bayan ɗaurin aure. Babu zancen biki yanzu duba da yanayin da aka ɗaura auren a ciki. Abu ne na gaggawa sannan kuma idan suka yi wani abu duniya ma sai ta zagesu ace anyi rasuwa ga ruɗanin da ake ciki na batun sata da Shamsu a gadon asibiti. Dakatawar dai ita tafi. Hannunsa Jamal yaja zuwa cikin gidan har ɗakin Haj. Manga. Suna shigowa Tauhidat ta tashi daga kan abin sallah inda ta yi sallar Isha ta fice ta basu wuri. Da ido Jamal ya bita ya koma hararar yayan nasa ko ya yi mata wani abu tunda tun jiya ya fuskanci ransa ya ɓaci. Haj. Manga ta shigo suka gaisa ta tambaye shi aiki da abokan arziƙi su Abu Usama. "Nanna ina ne ɗakina zan yi wanka kafin nayi sallah." Arƙam ya ce lokacin da ya tashi. Zaunar dashi ta yi ta ce akwai bayanan da take son yi masa tukunna saboda idan bata yi ba suka fita cikin ƴan uwa dole wani zai faɗa. Hankalinsa ya tattara gareta yana sauraron jawabinsu game da abinda ya faru a gidan Alh. Audi. Shi ko haka bata faru ba dama bai zo da niyar ragawa Kawun nasu ba. Abubuwan da suka faru a baya ciki kuwa harda raba shi da mahaifarsa sai ya nuna masa cewa shi ba kanwar lasa bane. Yawon da yake yi a ƙasashen da ake yaƙe-yaƙe ya daɗa buɗe masa ido da fahimtar zalunci da son zuciya na ɗan Adam. Abu na biyu kuwa rufe ido ya yi ya dinga yiwa Jamal faɗa akan shaye-shaye. A ganinsa wannan ne ya bada damar Alh. Audi ya ɗora masa abinda bai ji ba bai gani ba. Duk mai shaye-shaye ai abin rainawa ne don kuwa bashi da wani kwarjini a idon jama'a. Haj. Manga bata hana shi ba a matsayinsa na yayan Jamal. Shi kuwa sai bada haƙuri yake yi yana nanata alƙawarin ya dena. Haƙurin nasa bai burge Arƙam da zuciya ta gama cinsa ba. Ganin haka ya tashi ya fita ya barsu. Ɗakin da Aidan yake ciki ya shiga don ya tabbatar Tauhidat tana can. Ai kuwa tausa ya sameta tana yiwa Aidan saboda mutane a gidan sunƙi fitar dashi daga ɗaki. Wani ko bai yi niyya ba zai iya faɗin abinda zai iya janyo matsala bisa kuskure. Shi yasa suka zaɓi ɓoye shi ga kowa. Dada da Umma ne kaɗai suka san yana gidan. "Haka kawai mutum daga dawowarsa zai zo yana bamu attitude, waye bai iya faɗa ba?" Taji Jamal yace yana gunaguni. "Yayana kai da wa?" "Wa kuwa banda..." ya dan riƙe baki, "mijinki ne fa yanzu sai ki nuna min baki ji daɗi ba gara kawai nayi shiru." Dariya ta yi, "fadi abinka nima kafin mu iso gida har ƙwalla sai da ya sani." Wata muguwar dariya Jamal ya saki harda buga ƙafafgunsa, "ahh ki ce ni dake sammakal. Bari na zauna kawai muyi gulmarsa ko ma huce." Kwatanta yadda Arƙam ya dinga yi masa faɗa ya yi suka sha dariyarsu harda Aidan. Sai daga baya Tauhidat ta ce amma dai gaskiya ya dena shan komai ko don lafiyarsa. Taɓe baki ya yi, "ahaf ai na sani. Kare masa zaki yi tun baki kwana da aurensa ba. Nan da wayewar gari ƙarshenta sai kin tambayeni suna na ma. Gara nima dai na nemo wata Celine Dion na aura." Dariya ta yi mai isarta sannan ta tashi domin sauka ƙasa. *** A ɗakin Haj. Manga kuma bayan fitar Jamal zancen Tauhidat ta sako masa. Ya ɗage mata gira "Jamal ya faɗa min karatu ta zauna yi da sa hannunki. Kinga Nanna mu bar zancenta bari nayi wanka jikina ba dadi." "Oh ni wannan yaro kamar ba a gasa masa baki ba da yana jinjiri." Ta ce tana girgiza kai. Murmushin dole tasa Arƙam, "its not too late zan gasa masa da iron." "Naji amma kafin ku fara shirmenku ka sani cewa ɗazu aka ɗaura aurenka da Tauhidat." Dariyar da yake mata ce ta ɗauke kamar an zare masa batir ya ce, "aure fa ki ka ce Nanna?" Gyaɗa kai ta yi ta koro masa bayanin komai yadda zai fahimta. Rasa inda zai ajiye zancen ya yi a zuciyarsa. Ya yi murna sosai amma sauran jawaban na kutsen da Alh. Audi yake neman sake yi masa sai da ya yiwa zuciyarsa dabaibayi. Can ya nisa ya ce, "Ta san cewa an ɗaura mana aure?" "Ina faɗa mata na turosu ɗaukarka da direba." "So ta sani dai?" Bata san me yake tunani ba ta kuma cewa ta sani amma bata daɗe da sanin ba. Da gaske ransa ya sosu ya ce, "amma shi ne taƙi faɗa min tun a can?" "Ikon Allah, to ni ba gashi na faɗa maka ba yanzu." Cewar Haj. Manga tana harararsa. Tunowa ya yi da yadda ya dinga yaƙi da gangar jiki da ruhinsa akan tsare mutumcinsu su biyun bai rungumeta a gaban mutane ba lokacin da idanunsa suka sauka a kanta. Shi kaɗai ya san halin da ya shiga amma don mugunta Tauhidat ta kama bakinta ta rufe. A sanyaye ya ce, "atleast da sai ta faɗa min." "Meye marabar airport ɗin da nan ne Arƙam? Ni ba gashi na faɗa maka ba. Kunya kuma ai ado ce a wurin mace. So kayi kana fitowa tace maka sannu da zuwa maigida ko me?" Zube mata ya yi akan gado don ya gaji da zaman ya kwanta, "that was the longest drive of my life (wannan shi ne mafi nisan tafiyar motar da na taɓa yi)." Haj. Manga ta riƙe baki, "kai Arƙam kaji tsoron Allah. Tafiyar da bata kai awa guda ba kake cewa tafi kowacce da ka taɓa yi. Kai da a wannan ƙasar taku daga nan zuwa can sai mutum yaji kamar bangon duniya za a kaishi." Murmushin gefen baki ya yi daga kwance, "ba zaki gane bane Nanna, you don't know how much I love her (baki san irin son da nake mata ba)." "Ban sani ba" ta ce tana ture shi daga kan gadonta, "tashi ka fice min daga ɗaki. Ga key can kusa da jakata ka ɗauka na ɗakinka ne. Jamal zai nuna maka a ƙasa." Fita ya yi yana murmushi bakinsa kamar gonar auduga. Bashi da kalmar da zai kwatanta wannan zuwa Nigeria din. Yaji abubuwa marasa daɗi ya kuma ji wanda ya ɗaukeshi ya ɗora a sararin samaniya saboda tsabar daɗi. Wai shi Arƙam ne ya zama mijin Tauhidat. "Finally she is mine." Ya furta a hankali wanda laɓɓansa ne kaɗai suka motsa da wani irin karsashi. Daga bisani kuma ya murmusa. *** Kusan karo suka yi. Ita ta fito daga wurin Aidan da guntuwar dariyarta shi kuma daga wurin Haj. Manga. Ja da baya ta yi da sauri ya tsura mata idanu yana kallonta tare da lumshe idanu. Cikin wata irin siga yake magana kamar wanda aka yiwa duka, "raka ni ɗakina." Da sauri Haj. Manga dake bakin ƙofar ɗakinta ta buɗe da taji abinda ya ce. A ranta tana ayyana rashin kunyar maza. Idan bata yi da gaske ba sai ya nunawa kowa bai tashi cikin masu kunya ba. Ƙofar ɗakin ta nuna masa da hannu,"ga ɗakin naka can. Idan ka shiga falon ɗakuna biyu ne. Na cikin ne naka." Ta kama hannun Tauhidat, "ke kuma wuce muje ki shirya mu sauka. Kun barmu da yunwa dare yana ƙara yi."