Kenza eBookz

Cizon yatsa book 1&2 complete - Chapter 27

Cizon yatsa book 1&2 complete - Chapter 27

Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 27: Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 27. Tsuke baki Arƙam ya yi ya ɗauki jakar kayansa ya sauka. Da sauri ya yi…

2,930 words

Tsuke baki Arƙam ya yi ya ɗauki jakar kayansa ya sauka. Da sauri ya yi wanka ya shirya ya fito babban falon. Tare da Shaheed suka fito waje kowa yana zaune ana ta hira ga fitilu kamar rana. Tebur ɗaya iyaye maza ne, ɗaya na mata sai kuma na ukun Shaheed ne da matarsa sai Jamal da Arƙam. Daga can gefensu a ƙasa an shimfiɗa kafet mai kyau Dada da Umma sun zauna tare da yaran Shaheed. Iyabo kuma tana wurin Aidan. Fitowar Haj. Manga da Tauhidat ce ta dakatar da hirrakin dake tashi aka fara cewa ga amarya ta fito. Baƙin pencil skirt ta saka da pink tunic top mai dogon hannu wadda ta kai mata ƙwauri. Kanta pink ɗin ƙaramin mayafi ta ɗaura sannan ta yafa baƙi da yafi shi girma ya sauko ƙirjinta kaɗan. Idanun Arƙam na biye da ita har ta ja kujerar kusa da wadda Haj. Manga ta zauna suka ji muryar Jamal, "Ƙanwata ga wurinki nan" Ya ce yana nuna mata kujerar dake tsakanin tasa da ta Sariat. Mugun kallon da Arƙam ya bishi dashi dama yake jira ya kwashe da dariya. Kunya ta kamata haka ta tashi da iyayen suka dage ba zata zauna cikinsu ba. Kafin ta ƙaraso Shaheed ya ja mata kujerar dake tsakaninsa da Arƙam. Ko daidaita zamanta bata gama yi ba, taji yatsun Arƙam sun ratsa tsakanin tattausan hannunta sun yiwa kansu mazauni cikin nata yatsun. Sau ɗaya ta kalle shi gabanta na matsanancin faɗuwa kamar wadda ta yi tsere, shi kuwa ya ɗauke kai. Abincin gabansa ya cigaba da ci, amma hankalinsa ko kaɗan ba a kwance yake ba. Ɗumin hannun Tauhidat da bai taɓa tunanin zai ji ba shi ne yake fizgarsa. "Ki ci abinci mana Tauhidat ko babu abinda ki ke so a nan?" Cewar Sariat. Bowl ɗin farfesun hanta da tumbi Shaheed ya miƙa mata don ya san tana son shi. Hannun damanta yana kurkukun Arƙam sai ta miƙa na hagun za ta karɓa. Shaheed ya ɓata rai yana cewa idan yara suka yi ta iya yi musu faɗa amma ita ta miƙo masa hannun hagu. Jin haka ta ɗan ja na daman amma sai ji ta yi Arƙam ya ƙara karfin riƙon alamun ba zai saki ba. Murmushin dole ta yiwa yayanta ta ce ya ajiye a wurin za ta ɗauka. Gani ya yi tana satar kallon Arƙam sai ya tashi yace bari yaje wurin yara kada su hana kakaninsu cin abinci. Yana tashi Sariat tabi bayansa wai ta gaji bayanta na ciwo. Dama kuma ba kwana zasu yi a gidan ba gara su fara harama. Wuri ya rage su uku. Jamal ya dinga turowa Tauhidat abinci yana cewa ta ɗebi wanda take so. Sai dai ta amsa da to taƙi ɗago hannu. Ɗan ɗago kai ya yi daga inda yake zai leƙa wurin hannun nasu. "Wai lafiya kike kuwa?" Ya ce yana tashi yadda zai gani da kyau. Hanyar cikin gidan Arƙam ya nuna masa,"Get lost Jamal. (ɓace/tafi)" "Duk abin mutum bai isa ya rabani da ƙanwata ba. Shugaban ƴan farraƙun ma muna nan sai mun soya masa aya a hannu." Ya tashi fuskar nan babu annuri. Ya gama shirin baza kunnuwa yaji hirar masoya shi ne dan buƙulu Arƙam ya kore shi. Ita kuma wadda yake taƙama da ita ko ta ɗan tare masa don ya ƙyale shi. Shi ma kan kafet ɗin ya koma wurinsu Dada tunda buƙata bata biya ba. Yana tashi Arƙam ya sakar mata hannu shi ma ya tashi. "Ni kaɗai zan zauna? Yunwa fa nake ji." Ta tambayeshi tana kyaɓe fuska "Ban hanaki cin abinci ba amma ina da abinda zan yi a ɗaki kafin na kwanta." "Amma fa kaine ka riƙe min hannu ka hanani cin abinci tare da mutane." Murmushi ya yi wanda ya bayyana fararen hakoransa " I thought you wanted it (na zata kina so)." Ga mamakinsa sai tayi murmushi ta ce "I do. Now please ka tayani zama naci abinci." Yana son yin dariya yana dannewa kada tace ya damu da yawa. Idan ita bata damu dashi ba shi ma ya iya jan aji. Ƙin zama ya yi ya ce ta nemi mai zama da ita. Da ta ce za ta kai ƙarar shi wurin Nanna ya ce Bismillah. Bai yarda zata yi ba sai da ta buɗe baki ta kirata abinda ya sashi zama da sauri. "Tauhida mene ne?" Dariya take tana kallon yadda yake girgiza kai ta ce, "naji kamar kin kirani ne." "Yi zamanki ba kiranki nake ba." Abincin ta zuba daidai yadda zai isheta ta riƙe cokalin da hannun dama ta kamo hannunsa da na hagunta. Yadda ya yi mata ta yi masa itama ta kuma ɗauke kai kamar bata san yana kallonta ba. Da ƙyar take tura abincin saboda ba ƙaramin takura ta yi ba amma ta dake. Bata son yadda yake mata ɗinnan. Shekarun da yawa, za ta so suyi hira su cike gurbin da ƙaddara ta sanya tsakaninsu. "Ya hanya" ta tambaye shi idanunta akan plate ɗin gabanta. "Lafiya." "Ya aiki?" "Lafiya." "I miss you too." Ta ce tare da sakin hannunsa ta yi gaba. Da saurinsa yabi bayanta maganar na ratsa kowace jijiya a jikinsa. Wurinsu Dada ta tafi ta zauna bata shiga cikin gidan kamar yadda yaso ba. Shi da ya biyota sai ya rasa yadda zai yi. Dole ya sami wuri kusa da Jamal. Kujerun duka an juyasu suna fuskantar su Dada ana ta hira cikin farinciki kamar babu abinda yake damunsu. Kiransa Haj. Manga ta yi da hannu ya koma kusa da ita. Kamar yadda ta ce zata yi kuwa a gaban kowa ta ce, "Ga ƴata nan Arƙam. Marainiyace gaba da baya. Mahaifinta ya sadaukar da rayuwarsa dominmu. Sun haƙura da cin zarafi a ɓoye da Alh. Audi ya yi musu saboda kare rayuwarmu. Ba zan iya saka musu ba, hasali ma dai alfarmarsu na sake shiga da na nema maka aurenta. Akan ce ka haifi ɗa baka haifi halinsa ba, to ni ban haifi Tauhida ba amma na san ta ciki da bai. Arƙam abu ɗaya ne nake so daga gareka, kada ka bari nayi danasanin aura maka ita. Ban ce kullum za a kwana a gado ba amma duk ranar da ku ka faɗo kan tabarma to banda ture-ture." Arƙam ya nuna inda Tauhidat take zaune ya ce, "ni bani da problem da kwanciya akan tabarma ɗin. A Yemen babu inda bama bacci. Kawai dai ki faɗa mata kada ta shureni don nima bana yi." Ai kuwa suka kwashe da dariya. Sariat ce kawai bata fahimta ba ta matsawa Shaheed ya fassara mata. Arƙam ya bisu da kallo don bai san me ya ce da zai saka su dariya haka ba. "Gaskiyata na faɗa fa, or did I say something wrong?" Dariyar suka cigaba ya soma ƙulewa. Kawu Garba ne ya tausaya masa ya ce, "Haj. Manga kin ɓatar dashi da wannan dogon jawabin. Kaga Arƙam tana nufin ka riƙe matarka amana banda rigima." "Ohk Kawu amma kwana akan tabarmar fa yaushe ne? Har na tafi ban taɓa jin wannan tradition (al'adar) ba." Tsabar dariya Jamal ko tsayuwa ya kasa yi da kyau. Tauhidat ce ta fara shigewa ciki tunda bai dace ta yi a gaban surukai ba. Da ɗaiɗai aka watse Shaheed ya haɗa kan iyalinsa suka wuce gida. Mazan su ma tafiya suka yi wani hotel kusa da gidan. Da yake duk an gama gajiya makwanci kowa ya nema. Iyabo ta bi su Shageed ga kuma baki a dakin Haj. Manga saboda haka Tauhidat sai ta ja akwatinta zuwa ɗakin da Aidan yake. Gajiyar da Arƙam ya kwaso bata yi nasarar saka shi baccin da yake tunanin zai yi ba. Tauhidat ke yawo a kowane lungu da sako na zuciyarsa ta hana shi sakat. Yana gama shirin bacci dama buɗe ko ina ya yi a ɗakunan ɓangaren guda biyu neman tabarma. Bai ga komai ba a falo da ɗakinsa. Ɗayan kuma babu komai a cikinsa ko labule ba a saka ba. Hannunsa ɗaya a kugu ɗayan kuma ya riƙe haɓa yana tunanin to a ina tabarmar da zasu kwanta take? Abin haushin ma bashi da sim card na Nigeria kuma babu numbarta bare ya kirata. Gani ya yi zaman ba zai kaishi ko ina ba ya tashi lokacin shabiyu ta gota ya tafi ɗakin Jamal. Kamar ɓangarensa shi ma falon babu kaya sosai a ciki sannan ɗakin farkon babu komai. A na biyun irin nasa ya same shi kwance shame-shame yana bacci. Ɗan duka ya kai masa a baya a hankali. Da yaƙi tashi ya yi masa guda mai shiga sai gashi a zaune yana murza idanu. "Wane ɗaki Cuddles take?" Bubbuga ƙafa ya yi akan gadon saboda takaicin tashinsa da ya yi ,"haba don Allah sai ka tasheni don baka ganta ba. Kaje ka kwanta ƙila ta bi Shaheed." "Bata tafi ba ina wurin ya tafi." Da ya fara wartsakewa sai ya haɗe rai, "wa ka yiwa masifa ɗazu?" Idan ba lallaba shi ya yi ba sai su kwana Jamal na ja masa rai, "kayi haƙuri don Allah tana ina? Na gaji sosai Jamal I just need to see her kafin na kwanta." "Idan ka hau sama ka shiga ɗaki na uku, I repeat na uku. Idan ka shiga ɗakin Nanna ko inda su Dada suke ni babu ruwana." Yana gama faɗa masa ya koma ya kwanta, shi kuma Arƙam ya hau saman kansa tsaye. Tauhidat ta dage sai ta bashi wahala ko tausayinsa bata ji. Haushin kansa yake ji da ya kasa haƙura ya matsu da sake ganin fuskarta kafin ya kwanta. Ƙila ta daɗe da dena son shi shi yasa bata damu ba. A hankali ya buɗe ɗakin ya shigo da sanɗa saboda kada ya tasheta. Motsin ƙofar ya tada Aidan ya buɗe idanu tar yana kallon duhun Arƙam yana tahowa wurin gadon. Abinda kakansu ya yiwa Mubeen wanda ya saka shi kuka ya tuna. Ihu ya saka da ƙarfi wanda ya rikita Arƙam don bai san da wani a ɗakin ba. Tauhidat kuma ta taso a firgice daga kan bargon da ta shimfiɗa a gefen gadon. Cikin duhun ta kai hannu kansa shi ma Arqam ya kai nasa saboda ya fahimci kamar yaro ne. Ba dai ta haihu da Shamsu ba aka rufe masa. Hakan ba zai rage masa sonta ba amma...Muryarta yaji tana cewa, "Shhhh Aidan nice." "Uhmm, uhmm" ya ce cikin kuka. Hannu ta miƙa sai ta kamo na Arƙam. Ihu itama ta saki har yafi na Aidan. "Shit! Cuddles its me" Arƙam ya ce. Zuciyarta bata dena bugawa ba saboda ta riga ta tsorata ta ce ya kunna musu fitila. Kasa gane wurin ya yi ihunsu duk ya ruɗa shi sai da ta tashi da kanta ta kunna. Tsayuwar kallonta ya yi bata ma sani ba tana saurin komawa kan gadon. Kayan bacci ne cotton a jikinta dogon wando da riga sai hula da ta saka. Gadon ta koma ta zauna sannan ta janyo Aidan jikinta. Da ido yake ta bin Arƙam shi ma sai ya zauna daga wurin ƙafafunsa. Yana kallonsa ya gane bashi da lafiya. Tissue ɗin da Tauhidat ta ciro domin goge masa yawu ya karɓa ya goge sannan ya kama kunnuwansa yana yi masa murmushi. "Sorry na baka tsoro." Ya miƙa masa hannu a wayance yana son gane yanayin lalurar tasa batare da ya saka shi jin wani iri ba. Ganin bai iya miƙo nasa ba amma yana murmushi sai ya kama da kan sa. "Ka haƙura?" "Uhm." "Good boy." Sumbatar goshinsa ya yi a lokaci guda yaron na shiga ransa. Kwantar dashi ya yi akan pillow yana shafa kansa har ya soma lumshe idanu. Tauhidat sai ta jingina bayanta da gadon tana kallonsu tana murmushi. Haɗa ido suka yi da Arƙam ta yi saurin runtse nata idanun. Sun ɗauki kusan rabin awa sannan Aidan ya koma bacci. Tun Tauhidat na gyangyaɗi ta buɗe ido da ƙyar har bacci ya yi awon gaba da ita ta kwanta a gadon. Kashe musu fitila Arƙam ya yi ya gyara musu rufa sannan ya fita. Ya daɗe a kwance yana tunanin waye Aidan a gareta kafin bacci ya ɗauke shi cike da mafarkinta. *** Takwas da rabi bayan Tauhidat ta gama shirya Aidan sannan ta shiga ɗakin da su Umma suka yi masauki. Gaishesu ta yi suka tambayeta kwanan Aidan ta ce Alhamdulillah. Daga nan ta shiga ɗakin Haj. Manga ta gaisa da baƙin ciki ta sauko ƙasa. Kitchen ta wuce ta sami Haj. Manga da mutum biyu suna tayata aikin breakfast tunda babu mai aiki a gidan. Bayan sun gaisa ta nemi kama musu suka sallameta wai amarya bata aiki. Sai ta ɗauki tsintsiya ta tafi gyaran falo. Ana kammala abincin ta dibarwa Aidan ta haye sama da sauri su kuwa aka taru harda mazan da suka iso daga masaukinsu zasu ci a falo. Cigiyarta aka dinga yi saboda shiru bata sauko ba. "Kada dai ace Tauhida kunyarmu take ji taki saukowa cin abinci." "Naga ta ɗebi ɗan kaɗan wanda bai fi yaron goye yaci ba ta hau sama." Kunnuwan Arƙam suna garesu ya kasa zuba komai yaji Umma ta ce, "Arƙam jeka ka sauko da matarka nan gidan bata da suruki." Mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki. Ana faɗa ya tashi Jamal yana dariyar shaƙiyanci. Yana son zuwa yana jin haushin ita me yasa bata nuna damuwarta a kansa. Sai wani ɓoye kanta take yi. Jiya ba don gidan ƙato bane kowa ya yi bacci da sai ta tara masa mutane da ihunta. Idan da ta je wurinsa ai ba zai hau saman su tsorata ba. Tsayar dashi wata matar Baffa Bukar da na uku a wurin Baffa ta yi ta haɗa masa abincin a tray. "Ka barta kafin ta gama sakewa ku ci a can." "Baki haɗa masa da tabarma ba" cewar maigidanta. Yana ji suna masa dariya har ya haye saman shi ma yana murmushi. Kafin ya isa ƙofar dakin Haj. Manga ta fito daga nata. Tambayarsa ta yi ina zai je ya nuna mata abincin yana mita wai shi bata bashi ba amma an aiko shi ya kawo mata. Da yake ta kula da take-takensa wai yana fushi tun jiya sai ta rabu dashi ta buɗe masa ƙofar ɗakin suka shiga tare. Aidan na jingine da gado Tauhidat tana bashi abinci. Murmushi ya yi sosai da yaga Haj. Manga ta ƙarasa gabansa ta shafa kansa. "Good morning Aidan." Arƙam kuma ya ce "good morning handsome." Bawan Allah sai ya hau ɓangala dariya. Duka iyayensa babu wanda ya taɓa yaba masa a komai. Ita Susu bata son shi bata kuma damu da lamuransa ba. Shamsu kuma neman lafiyarsa yasa a gaba duka yaran basu dame shi ba. Fork ɗin hannun Tauhidat ya karɓe wadda ta duƙar da kai tun shigowarsu ya cigaba da bashi abincin. Gefe ta koma tana cin wanda ya kawo. Haj. Manga ta faɗa musu cewa ƙarfe uku Shaheed zai zo su je gaishe da Alh. Audi kamar yadda ya buƙata. Jin sunansa ke da wuya Aidan ya soma zabura. Abincin bakinsa ma dawo dashi ya yi. Hankalinsu duka ya tashi da ƙyar aka sami kansa. Jamal aka kira yazo ya zauna dashi suka koma ɗakin Haj. Manga. Ita ta faɗawa Arƙam waye Aidan da dalilin zamansa a gidan. "Da babarsa da Kawu basu san yana nan ba kenan?" "Mammalo bai yiwa Tauhida bayanin komai ba ya tafi. Shi kuma yaro ba baki kaga kuwa bamu san a hannun waye rayuwarsa take cikin hatsari ba." Jinjina lamarin yake yi a kansa yana tunanin wace hanya ya kamata yabi domin communicating dashi. Tabbas akwai abinda yaron ya sani shi yasa aka rabo shi da gidansu. Ga kuma tsoratar da ya yi da yaji sunan Alh. Audi. Bai faɗa musu tunanin da yake ba don me yiwuwa ba tsorata bane. Ƙila ma so yake ya koma gida shi yasa ya yi kukan. Zai cigaba da saka masa ido dai. Kafin uku Shaheed ya iso gidan. Wayar Alh. Audi biyu yana tuna masa cewa lallai yau su zo yaga mijin Tauhidat. Wasu kayan nata Sariat ta bashi ya taho dasu. A ciki ta sami wani lace baƙi mai ratsin adon fari da orange sabo ta saka. Haj. Manga na tsaye a kanta sai da ta yi kwalliya sosai. "Ki dake Tauhida banda rawar jiki ko ta murya. Kada ki kuskura ya hango alamun tsoronsa a tare dake. Idan kunje ki faɗa masa cewa Suwaida da Jamal sun amince zaki wakilcesu a kotu." "Ba zan baki kunya ba fa Nanna." Ta ce tana gyara ɗaurin dankwalinta. "Na sani Tauhida." Sai kuma ta canja akalar zancen zuwa kan Arkam "wancan mijin naki fa fushi yake damu akan ƙin faɗa masa aurenki ya mutu tuntuni." Sankuyar da kanta ta yi cike da kunya. Ita kuwa Haj. Manga ta share tana faɗa mata cewa kada ta bishi idan yana shareta. Mace sai da jan aji. Ta rabu dashi da kansa zai nemi shiri. Bata da abin cewa sai murmushi. A ɗakin Arƙam kuma Jamal da Shaheed ke nuna masa yadda zai naɗe babbar riga. Da yaga abin na neman wahalar dashi ya ɗauki wani yadi mai kyau ruwan goro ya ce shi zai saka. Rigar three quarter ce mai dogon hannu da zagayeyyen wuya mai daga maɓallai daga wurin da aka yi aikin rigar har wuyansa. Baya saka manyan kaya sai sallah-sallah. Sunyi masa kyau sosai bare da ya ɗora hula zanna bukar. Jamal da aka ce ba dashi za a je ba takaici ya kama shi. Faɗi yake idan aka bari ya je zai kawo musu rahoton komai kamar a gabansu akayi. Sai da Haj. Manga ta yi masa jan ido ya haƙura.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull