Kenza eBookz

Cizon yatsa book 1&2 complete - Chapter 28

Cizon yatsa book 1&2 complete - Chapter 28

Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 28: Cizon yatsa book 1&2 complete Chapter 28. A waje Tauhidat ta same su. Ita da Arƙam aka rasa mai yiwa ɗan uwansa…

770 words

A waje Tauhidat ta same su. Ita da Arƙam aka rasa mai yiwa ɗan uwansa magana, sai kallo kowa na yaba kyan da ɗayan ya yi. Shaheed ya dinga godiya ga Allah da yasa bai bijirewa Nanna ba ya amince da auren. Su duka kana iya ganin soyayyar juna a tare dasu, amma bayyanawa ya yi musu wahala. Duk da son da suke yiwa juna yana nan amma dole rabuwarsu ta shafi alaƙarsu yanzu. Babu yadda za ayi ace su ture waɗannan shekarun kamar basu faru ba su ɗora daga inda suka tsaya. Awkardness is to be expected. Motarsa ya nufa yana cewa daga can yana da wurin zuwa su biyo shi a motar Tauhidat. Mukullin motar yana jakarta ta fito dashi ta danna remote ɗin. Kai tsaye Arƙam mazaunin me zaman banza ya shige ya zauna ya barta da sakin baki. "Mijinki ɗan rigima ne" cewar Shaheed yana dariya ya shige tasa motar ya tayar. "Are you coming?" Taji Arƙam ya ce da ita. Ƙwafa ta yi ta shiga mazaunin direba ta zauna. Motar kaɗan ta nemi yi musu ba don rashin fili ba sai don yadda zuƙatansu suke harbawa su duka. Sake shawara ya yi ko ya karɓi tuƙin sai ya fasa don bai san ko ina ba kuma bashi da experience na tuƙin Nigeria. Tura kujerar baya ya yi yadda dogayen kafafunsa zasu sake ya ce, "You drive tunda na kawo miki breakfast da safe so consider us even yanzu." "Fine" ta ce tana tayar da motar. "I wish..." "What?" ta ce tana kallonsa. "Nothing" Ya amsa da saurinsa saboda bai san zancen zuci ya fito ba. A hankali ta fara tuƙin har suka hau titi sannan ta saki jiki tana yin yadda ta saba. Tuƙin ganganci da kutsa kai irin na ƴan kasarmu babu wanda bata iya ba. Salonta ya burge shi sosai ya dinga kallonta kamar wanda ya sami tv. Tana jin yadda idanunsa ke yawo a kanta ta daure rawar da hannunta ke yi don kada ta saki sitiyari. "Karam Mansion." Arƙam ya karanta ƙaton abinda aka kafa a saman gidan mai ɗauke da wannan rubutun. "Akwai ɗakinka kuwa a gidan nan da" Haɗe rai ya yi tare da cewa ya barwa masu gidan suyi kiwon ɓeraye a ciki. Dariyar Tauhidat ta tsaya masa a rai ya ce, "baki canja ba Cuddles. Har yanzu kina da yawan murmushi da dariya. I wonder yadda ki ke yi a court." "Dr. Arƙam ina gayyatarka zamana na gaba domin na baka mamaki." "Zan zo ko babu gayyata." Ƙwanƙwasa gilas ɗin motar Shaheed ya yi yana nuna musu cewa su fito. Takalminta mai tsini ta mayar sannan ta fito. Suna fara tafiya Arƙam ya zura yatsunsa cikin nata suna biye da Shaheed. Wata irin nutsuwa riƙon ya sanya mata bata cire hannunta ba sai a ƙofar falon Alh. Audi. Arƙam yaƙi saki sai ma matso da ita jikinsa da ya yi. A cikin falon Alh. Audi ne da Alh. Ari sai Fanna da ƴaƴanta. An shirya kayan tarbar baƙi wanda Alh. Audi ya gama shirin kalaman da zai yiwa ko ma waye mijin ya tsorata shi akan auren bayan ya nemi su bashi wuri ya gana dashi. Alh. Ari ne ya fara hango irin riƙon da Arƙam ya yiwa Tauhidat ya ce, "kunga marasa kunya, ji wannan runguma kamar a ɗakin baccinsu." Bakin ƙofar Alh. Audi ya kalla daidai lokacin Arƙam ya duka ya zarewa Tauhidat takalman ƙafarta saboda akwai maɗauri. Ita kanta kunya ce ta kamata musamman da taga idanuwansu a kansu kamar su cinye su. Alh. Audi ya ce, "Shaheed ka ce bahaushe ne amma me nake gani haka ko kunya babu yana faman rirriƙeta. Anya kunyi bincike kuwa kafin ayi auren?" Duka maganganunsa sun shiga kunnuwan Arƙam. Shekara ashirin babu yadda za'ayi su gane shi cikin sauri. Ƙarasowa suka yi kamar wasu taurari suna taku ɗaiɗai. Sai da suka iso Alh. Audi ya tashi zumbur saboda wani irin firgici da ya baƙunci zuciyarsa. Yawun bakinsa ne ya ƙafe yana son tuna ina ya san wannan fuska. Da murmushi cikin sanyin maganarsa Arƙam ya miƙa masa hannun damansa na hagun yana cikin na Tauhidat ya ce, "its nice to see you again Kawu." Alh. Ari ya saki baki "Kawu kuma?" Arƙam ya dan shafa bayan kansa sannan ya ce, "forgive my manners ban yi introducing kaina ba. I am Dr. Arƙam Ibrahim Karam mijin Tauhida" ya ƙare maganar yana mata wani irin kallo kamar ya haɗiyeta a wurin. Mutuwar tsaye Alh. Audi ya yi don gabaɗaya gaɓoɓinsa dena komai suka yi sai amsa kuwar sunan Arƙam ke dawo masa da ambaton kansa a matsayin mijin Tauhidat.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull