Kenza eBookz

Cutarwa complete by ayshercool - Chapter 20

Cutarwa complete by ayshercool - Chapter 20

Cutarwa complete by ayshercool Chapter 20: Cutarwa complete by ayshercool Chapter 20. "Alaƙar da ki ka faɗa mana, na kawo miki amanar yarinya kina ta…

3,375 words

"Alaƙar da ki ka faɗa mana, na kawo miki amanar yarinya kina ta wulaƙanta ta, gashi tana ta yi miki bauta kamar baiwar da ki ka sayo da kuɗinki, dan haka na saka mata sunan mahaifiyarta, atleast ta samu ƴar uwa, kuma wadda zata din ga kallo tana jin daɗi".

"Yahaya gaba ɗaya na kasa gane kanka, na rasa in da ka dosa a kan yarinyar nan yanzu saboda tsabar wulaƙanci da rashin mutunci, matar da ban sani ba kawai ka saka wa ƴa ta sunanta? Ni wai wace irin alaƙa ce tsakanin ka da ummin nan, ko zagata ka ke yi ne ban sani ba, da a duniya kullum abun da zai faranta mata kawai ka saka a gaba?".

A fusace ya ce "Wace irin maganar banza ce haka farida"

"Ba wani maganar banza, maganar gaskiya dai, to ga noor ɗin nan na bar mata, ta je ta raine ta na bar mata, tun da sunan uwarta ne ba na uwata ba".

Duk da ummi a tsaorace take rungume da noor, jin kawu yahaya suna faɗa, sai dai jin abun da farida ta faɗa, ya sanya cikin wauta da ƙuruciya, ta risuna ta ce "Anty na gode Allah ya saka da alkhairi, Allah ya jiƙan magabata na gode in sha Allah zan kula da ita, a bani kayanta da abincinta na gode" a zaton ta da gaske ta bar mata noor.

Kawu yahaya duk da a fusace yake, sai da yayi dariya, aikuwa cikin ɓacin rai farida tayi kan ummi, ta fizge noor ta ce "Ai ba uwarki ce tayi mini naƙudar ba"

Kawu yahaya ya ce "Ummana, jeki makarantar ki kin ji" ta ɗauki jakarta, ta fita cikin damuwa.

Ummi ba ta cika makara ba, dan haka da wuri ta je makarantar islamiyya.

Zama tayi ita kaɗai, tayi shiru tana tunani, tana son sake yi wa kawu yahaya maganar ya gano in da mamanta take? Sai dai ta kasa tana jin nauyinsa, shi ya ce mata ta bashi lokaci, dan haka ba ta son cigaba da takura masa.

"Ummi" maryam ta kira sunanta.

"Na'am" ta amsa a taƙaice.

"Taso ga mami can ta zo, ita ta kawo mu, ta ce yau dai tana son ta ganki"

Jin mahaifiyar maryam ce ke son ganinta, ya sanya ta tashi da sauri, dan duk in da aka ce wannan babba ne mussaman sha'anin uwa, ummi na bashi girma sosai da sosai.

A ƙofar makaranta suka tarar da mamin a wata zuƙeƙiyar mota, suka ƙarasa gaban motar, ta buɗe ƙofar motar tana murmushi.

Ummi ta durƙusa ƙasa ta ce "Mami ina wuni"

Matar ta ƙarewa ummi kallo, sannan ta yi murmushi dariya na neman suɓuce mata ta ce "Lafiya lau ummi, ya gida ya makaranta?"

"Lafiya ƙalau, Alhamdilillah"

"Yau Allah yayi na ga ummi, kusan kullum sai tayi zancenki a gida"

Ummi tayi murmushi tare da sunkuyar da kanta ƙasa.

"To Ubangiji Allah yayi muku albarka baki ɗaya, ina fatan wataran kuma zaki kawo mini ziyara gida"

Ummi ta ce "To, zan tambaya idan aka bar ni zan zo in sake gaishe ki"

Tayi murmushi ta ce "Masha Allah, ku koma aji to, Allah ya yi albarka"

Ummi ta amsa da "Amin ya Allah na gode, Allah ya tsare hanya"

Maryam ta ce "Bye bye mami, drive well"

Ta amsa mata da "Thank you dear"

A haƙiƙanin gaskiya maryam bata da aiki sai bayar da labarin baƙin ummi, da gidadancinta da rashin wayo, da yadda take kullum cikin kuka, abu kaɗan sai ta hau kuka, da irin yadda malamai kan yi mata ba'a, ko yadda su kan su ɗaliban ke attacking ɗin ta, amma ba ta iya cewa komai. Babban abun da ya burge mamin da ummi, shi ne nutsuwarta, da kuma gudun duniya da ta gani yau da wanda take jin labari a wurin Maryam.

**** Yau babban burin Idris ya cika, dan kuwa ya hilato hindu shagon wani abokinsa, ya aiwatar da abun da yake muradi a kanta.

Hindu tayi kuka kamar ranta zai fita, sai dai ya zuba mata ido, a tunainsa yanzu hankalinsa zai kwanta, sai dai ina, kasancewa da ummi kawai yake burin yi.

Duk da babu abun da ya shiga tsakaninsa da ummi, yana jin kamar akwai wani abu na musamman da ummi ke da shi, da baya tunanin ya samu a tattare da hindu.

Iya taushin fatar ummi ya isa saka mutum annashuwa, ya daɗe yana jin haushin kansa, da har suka rabu da ummi, bai amfana da ita ba.

Kukan hindu ne ya dawo da shi hayyacin sa, ya din ga lallaɓata yana bata haƙuri, tare da yi mata alƙawarurruka kashi-kashi irin na yaudara.

Tun da farida ta san sunan babar ummi, aka saka mata, ya sanya ta ƙara tsananta ƙiyayyarta ga ummi, azabtarwa iri-iri.

Rayuwa ta cigaba da garawa, sai dai al'amura sun tsananta ga ummi, lokacin da dr. Ya samu canjin wurin aiki, daga Kano zuwa kaduna, wasu lokutan sai yayi wata guda bai zo gida ba, wasu lokutan kuma ya kan zo weekends.

Idan ummi ta karaya ta ji kamar ta mutu ta bar duniya ta huta, sai kuma taga wahalarta ta tashi a banza kenan, ba ta yi acheiving komai a rayuwa ba.

Ko ina babu daɗi, gida azaba da wahala, makarantar boko, ba'a, cin zarafi daga ɗalibai har ma da malamai wasu lokutan, sukan aibata ta ko su muzantata da halittarta.

Sai da ta kai ta kawo, kuɗin makaranta idan dr. Ba ya gari, idan ya turowa farida, ba zata bawa ummi nata ba, har korota ake yi daga makaranta.

A ci mata mutunci, Saboda rashin biyan school fees, sai da ta kai Maryam ta saka babansu biya wa ummi kuɗin makaranta.

Shugaban makarantar ya hana malamai korar ummi, a duk lokacin da ba ta biya kuɗin makaranta ba, sai ya yi wa kawu yahaya waya, sai a lokacin dr. ya san abun da yake faruwa game da kuɗin makarantar ummi da yake bawa farida ba ta bata, daga nan har makarantar boko, direct transfer yake yi musu.

Duk wani aiki ko aike da yakamata namiji yayi ga Abdul, ummi ce za ta yi shi, sayen fetur, cefane, refilling ɗin gas, duk ummi ce ke yin sa, intee da kausar babu abun da suke tsinanawa a gidan nan, ko ɗauke cokali kuwa a kan hanya, saboda azaba har tayar da inji sai da ummi ta iya.

ƙawayensu intee idan suka zo, su yi ta nuna musu ummi a matsayin ƴar aikin gidan su.

Allah ya taimaki ummi, aka sakawa rahama ranar aure, ta din ga murna ta san ko ba komai ta ɗan samu rangwame.

Gefe guda soyayya da shaƙuwa mai ƙarfin gaske ta shiga tsakanin ta da noor, noor komai ummi, kai ka ce ummin ce ta haifeta ba farida ba, dan ita ce ta yaye noor ma.

Ummi na ta aiki a kicin da safe, ta je ɗakinta ta dawo, ta zo ta tarar da ƙwai guda biyu a kan drower kitchen, ita dai ba ta ajiye ƙwai ba, dan haka ta kai hannu ta ɗau ƙwan tana duddubawa, rubutu ne a jiki, an zana wani hatimi da sunan wanda rahama za ta aura, har da zanen kan ƙwarangwal.

"Ke!" Tsawar da farida ta daka mata, ya sanya ta zabura ta saki ƙwan ya faɗi ya fashe, maimakon ruwan ƙwai ya fito, sai jini da wani baƙin abu ya tsiyaye.

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wai wace irin karfa ce ke ne?"

Cikin magiya ummi ta din ga bata haƙuri, amma tsabar mugunta matar nan ta ɗauki muciya ta din ga bugawa ummi.

Abdul yana falo yana video game, ya shigo kitchen ɗin da sauri ya tarar da ita tana ta bugawa ummi muciya, tana ƙoƙarin karewa.

"Maama lafiya, meyasa ki ke dukanta da muciya"

"Dalla rabu da ni, na gaji da abubuwan da yarinyar nan take yi mini"

"Amma maama bai kamata ki dake ta da muciya ba, idan kuma ki ka ji mata ciwo fa?"

Cikin ko in kula ta ce "Na daki banza"

Tayi maganar tana sake kwaɗawa ummi muciyar iya ƙarfin ta.

"Maama dan Allah ki daina cin zalin anty ummi, wannan CUTARWA! ce, maybe tsautsayi ne ya sanya ta yi miki laifin"

A fusace ta ce "Ni ka ke gayawa ina cin zalinta?" Tayi maganar tana nufo shi.

Babu tsoro ko fargaba ya ce "Idan ba CUTARWA! ba ce dai-dai ne Allah ya sa a yi wa intee ko kausar abun da ki ke yi mata" sak tayi tana kallon Abdul, ba ta taɓa zaton wannan maganar daga bakinsa ba. Ta ji jikin ta ya yi sanyi, ta jefar da muciyar ta fice.

Ya girgiza kai shi ma ya fita, dan kunyar ummi ma yake ji, bai san me zai ce mata ba, saboda abun da mahaifiyar su take mata.

BAYAN SHEKARU BIYU ***

Ummi na tsaye a gaban mudubin ɗakinta, tana ta aikin taje gashin ta, ta nemi wuri ta zauna tana kallon kanta a mudubi, gashin duk ya rufeta, ta sunkuya tana cire gashin da yake jikin comb ɗin, ta tare shi a gefe sannan ta nannaɗe gashin kanta ta tufke shi.

Ta sanya doguwar rigar shadda brown, ta kawo dogon hijjabi milk ta saka, ta ɗauki niƙabinta ta sanya.

Ta shashshafa turare, tafin hannunta har ɗaukar ido yake yi, saboda tafin hannunta fari ne ƙal, kamar mata jini a jiki, kuma aka ɗora mata jan lalle a kai.

Ta ɗauki ƴar ƙaramar jakarta ta fito, Abdul ya ce "Inyee ka ga amaren sauka"

Kawu yahaya ya dube ta cikin fara'a ya ce "Congratulations dear, Ubangiji Allah ya sanyawa karatunki albarka, ya ƙara hasken makaranta" ta risuna ta ce "Amin kawu, na gode sosai da sosai"

Ya kalli farida da ƴan matanta da suke ta sabgoginsu, kamar ba su san da zaman su a falon ba ya ce "To mu mun tafi wurin saukar"

"Allah ya tsare" ta faɗa a yatsune.

Kawu yahaya yaji babu daɗi, da yaransa ko mutum ɗaya babu wanda yayi saukar nan, idan baya nan sai sun ga dama suke zuwa makaranta, dan kuwa farida wurin koyon kwalliya ma ta sama musu, maimakon zuwa makarantar.

Ummi gaba ɗaya bakinta yaƙi rufuwa, kaf a ƴan saukar ita ce ƙarama, danma tana da jiki ne, dan ko Maryam shekara biyu ta bata, itakaɗai ce mai shekaru sha shida a cikinsu, maryam na da sha takwas.

Aka gabatar da abubuwan da suka kamata, sannan aka fara raba musu alluna.

Ana bata nata ta nufi rumfar iyaye maza, har da gudu, wurin kawu ta ƙarasa ta durƙusa a gabansa tana cewa "Kawu ka ga"

Ya karɓi allon yana murmushi ya shafa kanta ya ce "Allah ya sanya albarka ummana"

"Amin kawu na gode" tayi maganar cikin tsantsar farinciki.

Abdul ya ce "Rufe bakin mana"

Ta kalleshi ta ce "Ta ina ka san bakina a buɗe yake a cikin niƙab".

"Yadda ki ke magana ne ya sa na gane"

Ta ce "Bari Yaya Abdul, Alqur'ani da daɗi wallahi".

"Wannan gaskiya ne ummana, kalli baƙin ki na waccan rumfar" ummi ta waiwaya ta ɗaga kai.

Wa zata gani? Yaya Magaji da auwwal, har da su Alhassan.

Maimakon ta yi murna sai gabanta ya faɗi, ta kasa magana, dan fatanta Allah ya sa babu Idris suka zo, dan bata ƙaunar ganinsa.

Sunanta aka din ga kira a speaker, ta zo ta karɓi kyautarta ta ɗaliba mai hazaƙa.

A hankali ta tashi ta nufi in da ake kiranta, tafiya take cikin nutsuwa, shugaban makarantar ya ce "Ƙaramar su babbar su, Salma Muhammad Bashir, kun ganta nan duk ita ce ƙarama a ƴan sauka, amma babu ɗalibar da ta kai ta cin maki lokacin screening"

Ummi ta karɓi kyaututtuka daban-daban, na hazaƙa, ladabi da biyayya da sauransu.

Mamin su maryam ummi ta hango, ta tafi wurin da take, dan jan lallen da aka yi mata ma, gidan su maryam ta je, mamin ce ta biya.

Mamin ta rungume ta tana faɗin "Allah yayi albarka ummi, Allah ya sanya wa karatunku albarka"

Ta risuna ta ce "Amin ya Allah"

Sau ɗaya ya ɗaga kai ya kalleta, ya lura da yadda ko iya haɗa ido da mamin ba ta yi, saboda tsananin tarbiyya da girmama manya, ya so ta ɗaga niƙabin ya ga ainihin fuskarta.

Ya dubi Maryam ya ce "Ke ba uban da aka baki? ba na ƙoƙarin, babu na ɗa'ar" yayi maganar yana sake gyara zaman face mask ɗin sa.

Cike da tsiwa Maryam ta ce "Ina ruwanka da ni? Ba a bani ɗin ba sai ka ƙwace allon saukar ma gaba ɗaya, mami ki rabani da shi wallahi, ai da yake ma ba gayyatarka na yi ba, waye ya ce ka zo?"

"Rufen baki kan na ɓarar da ke a wurin nan"

Ummi dai murmushi kawai take yi, duk ta san yayyen Maryam, wannan ne dai bata sani ba, kuma da alama maryam ɗin ta raina shi.

Aka tashi daga filin sauka, su yaya magaji suka nufo su, "Ummi masha Allah, kin ga yadda ki ka girma?" Magaji Yayi maganar yana kallon ta.

Alhassan ya ce "Ummi har kin yi sauka anya ba zuƙu ba ce ba?".

Ummi ta yi murmushi ta ce "Ai makarantar nan ba a saukar zuƙu"

Suka rankaya zuwa gida, suna komawa gida ta tarar da Iya, sai da ta ɗan ci burki, domin kuwa ba ta zaci Iyan za ta zo ba.

Ta ɓoye mamakinta ta ce "Iya sannu da zuwa, dama zaki zo?"

Ta harari ummi ta ce "Eh, da ki ka ce ke ba zaki zo in da nake ba, kar na yanka ki na cinye ko?"

Ummi ta girgiza kai ta ce "A'a makaranta ce take hanani zuwa, ya gida ya kowa da kowa?".

A ciki Iya ta amsa mata da lafiya lau.

Dai-dai gwargwado kawu ya yi wa ummi ƙoƙari, dan naman kasuwa ya sayo fal, ya bata tayi girkin da zata rarrabawa mutane da ƙawayenta.

Ita ummi ma kasancewar ba ta da ƙawaye, sai maƙwabta ta babbawa, sai su Iya da suka zo.

Sam farida ba ta bi ta kan Iya ba, ummi ce take ta ɗawainiya da su, suna ta hirar makaranta da su magaji, sai dai ko da wasa, ba ta nuna musu tana shan wahala a gidan ba ko kaɗan.

Kawu yahaya ya ji daɗin yadda ummi ta samu sakewa yau cikin ƴan uwa, tana hira ba kamar da da kullum a rakuɓe take ba.

Iya kuwa ba dalilin saukar ummi ne ya kawota ba, balli ne ya tashi, Idris ya mayar da hindu tamkar matar da ya aura, tun bata saba ba har suka saba da sheƙe ayarsu. Kwatsam ciki ya bayyana a jikin hindu, suka rasa yadda za su yi da cikin, har sai da iyayen hindun suka farga. Dan haka zance ya fasu a gari, sai faɗuwa ta zo dai-dai da zama, domin kuwa iyayen hindu sun ce sai ya auri hindu, shi kuma ya ce ba ya son ta. Dan kuwa zance ya fara fasuwa, an fara zunɗensu a garin. Baban hindun kuma ya dage ba za a zubar da ciki ba, sai an haifi wannan ɗa ya riƙe, kuma sai ya aureta. shiyasa Iya ta lallaɓo wai kawu yahaya ya ɗauke shi ya sama masa sana'a a nan Kano, a mayar da aurensa da ummi!!!

Iya a ɗakin kawu yahaya ta same shi, ta kora masa wannan jawabin.

Yayi ƙuri da ido yana kallon Iya, har ta gama jawabinta.

Kasancewar ummi na wurin, gabanta yayi wata irin mummunar faɗuwa, kawu yahaya ya kalli Iya ya ce "Amincewar ummi zaki nema, ni ba zan yanke mata hukunci ba, abun da take so shi nake so".

"Zancen banza kenan, wane irin sai ta yarda ko ba ta yarda ba? Ba ɗan uwanta bane ba, rufin asirinmu ba nata bane ba, idan shi ma ya baro garin, suka neme shi suka rasa ba shikenan ba, asiri ya rufu, ai rufa masa asiri za ta yi, ai umarni nake bayarwa ba shawara ba, dauɗar gora ai ciki ka sha ta!"

Ayshercool 08081012143. WHAT'S APP ONLY PLEASE 🙏

18

Kan ka ce kwabo, hawaye ya wanke wa ummi fuska, har wata irin sheshsheƙar kuka take yi, dan kuwa da ace ta koma gidan Idris, gara a yanke mata hukuncin kisa, dan tana kyautatawa Allah zato a dukkan lamuranta, tayi imanin za ta dace da rahamar sa.

Iya cikin masifa ta ce "To kukan uban me ki ke yi, ba taimaka miki zai yi ba? ke a wannan munin naki uban waye zai aure ki? Kalli fuskarki fa kamar buredi ya ƙone ƙurmus, har wani zaɓi ne da ke? Ke gaki nan ba ke ba mutum ba ke ba aljana ba".

Kawu yahaya ya ce "Iya, lokacin da Allah ya halicci ummi fa, bai yi shawara da kowa ba, balle ace laifinta ne, ko wani abu ne ya sanya ubangiji yin halittarta a haka, halittar ummi hurumin ubangiji ne, dan haka bai kyautu a din ga ci nata fuska ba, kuma wallahi ummi ba ta da muni".

"Ka ga ni kar ka yi mini wa'azi, ai maganar gaskiya ce, tun da Allah ya sa ita ba wata mamora ce da ita ba, balle ace za a samu mai kwasa ai duk sai a manta da abun da ya faru a baya ko? Tun da har da kansa ya ce ta dawo ɗin, sai a ja masa kunne"

Dr. Ya kalli in da ummi ke zaune tana ta sheshsheƙar kuka ya ce "Ummana, jeki ɗaki abunki kin kwaso gajiyar sauka" ummi ta tashi zuciyarta na harbawa da sauri, ta tafi ɗakinta tana kuka, tare da adduo'i kala-kala a zuciyarta, tana fatan Allah ya sa kar kawu ya amince da abun da iya take faɗa. Dan har ta mutu ba za ta manta da azabar da ta sha a gidan idris ba, ko maƙiyinta ba ta fatan yayi rayuwa irin wadda ta yi a gidan idris.

Noor ta bita ɗakin tana kiran sunanta.

Kawu ya kalli Iya ya ce "Iya, ko ummi ta amince ko bata amince ba, ba zan sake bawa Idris ita ba, yaron nan gaba ɗaya jahili ne, wallahi da mutumin kirki ne, idan ta gama sakandare sai a mayar da auren, amma ni ba zan goyi bayan a cuci ɗan wani ba, yadda ya yi wa ƴar mutane ciki, ku je can ku nema masa mafita, dan baban yarinya bai yi laifi ba. Iya kin manta lokacin da ya din ga terere da ummi, yana tona mata asiri ga larurar da ke damunta? Shi meyasa ba a tursasa shi ya shanye dauɗar gorar ba, sai ummi? Allah da ya halicceta a haka in dai muna raye, zai bata abokin rayuwa na gari, haka zalika ba zan riƙe ƙato da bai san ciwon kansa kamar idiris ba, can ƙauye ya gagareku balle ni a nan, dan Allah kiyi haƙuri a bar wannan zancen. Ummin ma da kanta ta nuna ba ta so, dan haka dan Allah dan annabi a bar wannan maganar. Kuma ina baku shawarar mayar da idris makaranta kan a kuma bashi wata matar ya aura, dan kuwa jahilci ke ɗawainiya da shi".

Cike da takaici iya ta kalle shi ta ce "Haka ka ce?"

"Ba faɗa na yi dan na ɓata miki rai ba, amma gaskiya ce" Iya ta yi ƙwafa ta ce "Shikenan na tabattar da uwarka ce ba zaka tsallake umarninta ba, kuma da cikin ku ɗaya da baban Idris ba zaka so asirin sa ya tonu ba".

Ya girgiza kai ya ce "Iya ai kin san mu kallon uwa muke yi miki, amma kowa ya ɗebo da zafi bakinsa, kin riga kin sangarta Idris, komai yayi ba zaki bari duniya ta hora shi ba, sai kin kare shi, kema yakamata ki hutawa ranki, ba shikaɗai ne ɗa a dangi ba".

Ba ƙaramin takaici Iya ta kwasa ba, yadda ƙiri-ƙiri yahaya yayi burus da maganarta, ya zaɓi tonuwar asirin su.

Dan haka ta ce masa babu ita babu ummi, tun da haka suka zaɓa, ya ce bakomai, Allhan da ya yi ummin zai kula da ita.

Ko zama ba ta sake yi ba tun da ta tashi, ta ce magaji ya samo musu mota a tasha, kawu yahaya ya biya kuɗin motar, ya basu kuɗin kashewa, suka tafi.

Ummi sai da tayi sujjadar godiya ga Allah, ga saukar Alqur'ani mai girma, ga kuma fasa mayar da aurenta da idris da aka yi.

Readers Also Read