Cutarwa complete by ayshercool - Chapter 19
Cutarwa complete by ayshercool Chapter 19: Cutarwa complete by ayshercool Chapter 19. Ganin cin mutuncin da take yi masa a gabansu, ya sanya Abdul tashi ya…
3,338 words
Ganin cin mutuncin da take yi masa a gabansu, ya sanya Abdul tashi ya bar wurin. Cikin miyagun maganganun da take yi masa, har da gugar zanar ko wani abu ne tsakanin sa da ummi, da ya sanya shi bawa al'amarinta muhimmanci har haka.
Ta dire noor ta tashi ta bar masa falon.
Ummi kuwa da sauri ta wanke hannunta, ta hau naman nan da ci, dan tun ana suyarsa ƙamshin ya cika mata ciki, ranta ya biya.
Sai tayi aikin abinci da nama ba adadi, da ta gama rahama ta shiga ta raba abincin, ta kwashe naman ta hanata, koma ta bar da ɗan kaɗan sai dai ta haɗa da ƙanzo, dan haka nama tana kallo ba za a bata ba.
Ta fito falo, dan samun tsinken sakace, ta tarar da kawunta rungume da jaririya tana ta tsala uban ihu.
Da sauri ta ƙarasa in da yake ta ce "Kawu bani ita, ban taɓa ɗaukarta ba".
Ya miƙa wa ummi ita ya ce "Gata nan mai sunan mamanki, ina fatan ita ta so ki, kuma ta din ga ɗebe miki kewar mamanki"
Da sauri ta ce "Amin ya Allah, Allah yasa" ta karɓi yarinyar ta ce "Mamana ki daina kuka, mama tana da haƙuri, kawu ta zama kakarka kenan? Maman mama ko?"
Sai da ya ɗan dara ya ce "Tsohuwa ce kenan?"
Ummi ta ɗorata a kafaɗarta, tana jin soyayyar yarinyar a ranta, da aka saka mata sunan mamanta.
Haka ummi ta din ga zagaye da ita a falon, tun tana tsala ihun har tayi bacci.
Dr. Ya ce "Lallai ummana kin iya raino, tun da har gashi kakata tayi bacci, kawota ki je ki kwanta"
Ta bashi ita, tana kallon fuskar yarinyar, gashinta har goshi, jawur da ita.
Ya kalli ummi ya ce "Na ga ƙunarki da sauƙi, in sha Allah ranar monday zaki koma school gaba ɗaya"
Ta ce "To Allah ya kaimu"
"Amin, ki je ki kwanta sai da safe" ta juya ta nufi hanyar ɗakinta, kamar ta ce ya bata ƴar su kwana tare.
Ranar Litinin ta koma ta cigaba da zuwa makaranta, ranar da ta je islamiyya, Maryam ce ta fara ganinta, da sauri ta tashi ta nufi ummi ta ce "ya jiki?".
Ummi ta ce "Na ji sauƙi"
"Kin warke duka ƙonuwar ta warke?"
Ummi ta jinjina mata kai alamar eh.
Ta ce "Alhamdilillah, dan Allah ki yi haƙuri, tun ranar da abun ya faru na kasa mantawa, kuma ban san gidanku ba, na gaya wa mamanmu ta din ga yi mini faɗa, ba ina sane na tureki ba ta ce in nemi yafiyarki".
Ummi ta yi murmushi ta ce "Ai bakomai, na samu sauƙi".
"Amma ya aka yi ki ka ƙone a ciki da ruwan zafi?".
Ummi ta ce "Zubo mini yayi".
"To Allah ya ƙara afuwa"
Ummi ta amsa da "Amin".
Maryam ta liƙewa ummi, sai dai ummi sai ɗari-ɗari take yi da ita, saboda ba ta son wani abu ya haɗa su tayi mata tijara da tashin hankali, saboda ita bata iya faɗa ba, maryam kuwa dage ce, akwai masifa.
Ga maryam da azabar kashe-kashen kuɗi, banda kayan ciye-ciye da take zuwa da su.
Komai za ta ci sai ta bawa ummi, ummi kuma ta ce ba zata ci ba.
Tun tana ɗan ɗari-ɗari da ita, har ta ɗan fara sabawa da ita kaɗan.
Can gida kuwa kawu yahaya ya sanar musu matarsa an yi mata aiki, an ciro ƴa mace, sai dai likitoci sun ce sai matar ta huta sosai za azo dubiya. Saboda yana gudun su zo barka, Iya ta faɗi wani abun, da zai yi wa ummi mummunan tabo a nan. Dama kuma gashi ba shiri suke yi da farida ba, dan ita da Iya kar ta san kar ne, iyan za ta iya zuwa ta bar ta a falo ta cigaba da sabgoginta ba tare da ta bata ko ruwa ba.
Ummi ta ɗauki soyayyar duniya ta ɗorawa jaririya noor, idan uwar ta yasar da ita, sai ta ɗauke ta ta goyata, tayi ta jijjigata tana aikin gidan da ita a bayanta, dan ko da yarinyar ta fara dariya ummi ta fara yi wa.
Duk wannan soyayyar da ummi ke nunawa ƴar farida, bai sanya ta sassauta mata daga baƙar azaba da mugunta ba, da ita da ƴaƴanta da ƙanwarta, dan ummi ba sabon abu bane a wurinta, kaiwa ƙarfe ɗaya na dare ba ta kwanta ba, saboda azabar aiki.
Ga wani sabon salon zalunci, har maƙwabta sai su aiko ummi ta je, a sakata aiki, har wankin labulaye da carfet, sai a sakata, gyaran kaji da fige su, sai a saka ummi.
Makaranta kuma maryam na ta sake shishshigewa ummi, sai dai ummi ta fuskanci maryam ɗin na ƙoƙarin mayar da ita ƙarƙashin ta ta din ga mulkata ta zama kamar ƴar korenta, ummi ta cigaba da janye jikinta, maryam ta kasa samun damar hakan, saboda ummin na da mugun gudun abun hannunta. Wasu lokutan haka ummi za ta zo ba ta ci abinci ba, maryam ta zo da abinci na alfarma amma fafur taƙi ci.
Kusan wata uku da haihuwar noor, kawu yahaya ya ce idan suka tashi suka koma sabon gida, sai su iya su zo, su ga noor, kuma su ga sabon gida.
Dan yana tsoron Iya ta zo ta saki baki ta faɗi wani abu da zata ɓata ummi, dan ya ƙudurce a ransa sai ya je yayi mata kashedi a kan ummi kan su zo, kuma gashi ba jituwa suke yi da iyalinsa ba, duk zuwa sai Iya ta ce an yi mata laifi, duk zalamar iya da son abun duniyarta ba ta ƙaunar zuwa gidan yahaya, wannan karon ma shi kawun ne ya takura su zo, kar abun ya zama surutu, an yi mata aiki ba su zo ba, ga kuma tariya a sabon gida.
Ɓangaren ummi kuwa sumul ta samu lafiya, kamar ba ta taɓa yin larurar sanyi ba, kuma lokaci zuwa lokaci, kawu yahaya ko bai sayi abu ya bata ba saboda matarsa, ya kan ɗan bata kuɗi ta sai abun da take buƙata.
Suka fara shirin tashi daga gidan, dama ƴan kayan ummi ba su da yawa tuni ta tattare su ta ƙulle.
Hatta su intee ummi ce ta haɗa musu kayansu, sannan ta koma ta haɗa na rahama, ga yau noor sai koke-koke take yi zazzaɓi na damunta, kai ka ce ummi ce ta haifeta, ta bata magani ta haɗa madara ta bata, sannan ta cigaba da aikin da ita a bayanta.
Suka gama haɗa kaya cif, washegari tun safe mota ta zo ta kwashi kayan su, zuwa sabon gida.
Gidan da suka koma, ƙato ne yafi wancan girma da kyau, a ɗan gaban unguwar da suke da yake, ƴan uwan su farida suka cika gidan, ummi na ganinsu suna ta binne-binne.
An canza furnitures, duk ta rabawa ƴan uwanta tsofaffin, ummi kuwa da tsohuwar katifarta ta dawo gidan, sai dai hakan ko a jikinta, ɗakinta shi ne na farko, baya cikin ainihin falon da zai sadaka da sashen kowa, Abdul sashinsa daban ba a cikin falon ba, da kitchen ɗin sa da banɗaki, a can gefe ɗaya.
Gidan ya ƙawatu yayi kyau matuƙa, ko ina ya sha flowers, sai ƙamshin sabunta yake yi.
Hatta ɗakin su intee kamar ɗakin wata amaryar, dr. Yayi ƙoƙari sosai da sosai, dama mutum ne mai hidimtawa iyalinsa sosai da sosai.
Bayan magariba ummi ta gaji matuƙa, har wani jiri take ji, ga ciwo da mararta take yi, wanda tun da take bata taɓa jin irin ciwon ba.
Tana ta ƙoƙarin gyara nata ɗakin, dan kuwa ba ta gyara komai ba, tana ta fama da aiki, da rigimar noor.
Ƴan uwan farida suna ta cewa ta karɓe ƴar ta daga hannun ummi, kar ta shafa mata baƙi da muni.
"Ke!"
Ummi ta waiwayo ta kalli rahama da ke tsaye.
Ta ce "Bani kuɗin nan da zobena"
Ummi tayi saroro ta ce "Wane kuɗin?"
"Ba ke kika haɗa mini kayana ba?"
"Eh nice" ummi ta amsa.
"Kuɗin da suke cikin wardrobe ɗina, kuɗin anty farida ne"
Ummi cikin faɗuwar gaba ta ce "A'a anty rahama, ban ga kuɗi ba wallahi, kayanki kawai na haɗa miki a cikin akwatin da sauran kayanki a cikin jakunkunan da ki ka bani, dubu biyun nan ce kawai kuma kin ɗauketa, amma ban ga kuɗinki ba".
"Ke rufe mini baki ko na dalla miki mari, kuɗin anty farida ne dubu hamsin"
"Wallahi wallahi anty rahama ban gani ba, ki cajeni ki caje kayana, wallahi ban ɗauka ba" ummi tayi maganar jikinta yana rawa tana tuna irin tozarcin da aka yi mata lokacin da iya ta ce ta yi mata sata.
"Rahama ina kuɗin ne? Ta baki?"
"A'a fa sai kin zo da kanki, ta ce ita ba ta ɗauka ba".
Farida ta ce "Ke, ina kuɗina?"
"Anty ban ɗauka ba" ta faɗa kamar numfashin ta zai ƙwace, saboda fargaba da tashin hankali.
Ashar ɗin da farida ta yi mata cikin tsawa ya sake gigita ta, ta ma rasa me za ta ce.
Shaƙeta rahama ta yi tana zazzaro mata ido ta ce "Zaki faɗa ko sai na kashe ki" girgiza kai kawai ummi take yi.
Farida ta ce "Rahama ƙyaleta, kar ta ja miki bala'i, ta riƙe miki kurwa kamar yadda ta yi mini, wallahi sai ya biyani kuɗina, kuma a wannan karon ko ubanta zai fito daga kabari ta din ga yawo da shi, sai ta bar mini gida ta koma in da ta fito, ba zan zauna da ɓarauniya ba, ga sata ga maita ba zai yiwu ba".
"Antyn dan Muhammadurasulillah ki yi haƙuri, dan Allah kar ki mayar da ni ƙauye, wallahi ban taɓa sata ba, ban san menene maita ba"
"Zaki santa yau, ɗaukko ƙullin kayanki ki wuce, ba zai yiwu ba"
Suka hankaɗo ummi waje, duk attention ɗin mutanen gidan ya dawo kansu, noor da ta fara dariya, tana hango ummi ta hau dariya tana ɗaga mata hannu.
"Lallai farida an haɗaki da masifa, satar kuɗi kuma, wannan wataran sai ta ganki a makara hankalinta zai kwanta" a tsakiyar falon suka zazzage mata kayanta, sai ga dubu ɗaya sabuwa fil wadda kawunta ne ya bata.
Rahama ta ce "Anty ta fito da sauran, suna wurinta wallahi, kalli dubu ɗaya fa a ina ta samu".
Inteesar ta ce "Tashi a caje ki, olay" kausar ta ƙyalƙyale da dariya tana maimaita olay.
Dr. Yayi sallama tare da Abdul ya tarar da ummi a durƙushe, tana ta gursheƙen kuka, noor sai zillo take ummi ta ɗauke ta.
"Lafiya kuwa?"
"Dr. Ni fa na gaji, da abun da yarinyar nan take yi mini, daga bawa rahama ajiyar kuɗi ta kwashe, ta bani kuɗi tun da girma da arziki amma taƙi".
"Shi ne zaki ajiyeta a gaban mutane kina tozarta ta haka? Idan yaranki ne haka zaki yi handling ɗin su? Nawa ne kuɗin?"
Cikin mamaki ta ce "Au haka ma zaka ce?"
"Na ce nawa ne kuɗin?"
"Dubu hamsin" ta bashi amsa tana riƙe ƙugu.
"Sana'ar me ki ke yi da har ki ka tara dubu hamsin? Idan ma akwaita na san a jikina aka sameta, zan biya na kashe maganar nan daga yau, kuma daga yanzu. Ummi ba ɓarauniya ba ce ba halin ta bane". Ta yinƙura za ta sake magana ya tari numfashin ta ta hanyar cewa "Na ce na kashe maganar nan"
Ya dubi ummi ya ce "Ummana, tashi kiyi tafiyarki"
Ba tare da ummi ta yi zuciya ba, ta dubi yarinyar da take ta zillo tana kuka, ta ƙarasa ta ɗauketa, ta nufi ɗaki da ita.
Abdul ya durƙusa yana kwashewa ummi kayanta.
"Farida anya maganin nan yayi kuwa? Kin ga fa abun da yayi miki".
Farida ta kasa magana saboda takaici, yau ta ƙuduri aniyar ummi ta bar mata gida, tun da yau sun yi sababbin ayyuka a gidan.
Ummi kuwa zuruuu tayi da ido, tana kallon noor da ke ta ɓangale baki tana yi mata dariya.
Cikin kuka take yi wa noor surutai, ta ce "Mamana, kin gani ko, tun tafiyarki ban taɓa kwanan farinciki ba, dan Allah mama ki dawo, ko ina ne ki tafi da ni, mama kamar in sha guba in mutu" tayi maganar tana kifa kanta a kan ƴan ƙafafuwan noor, tana wani irin kuka mai sauti"
FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK.
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
Masu neman free books ɗina, da free pages duk akwai a kan watpad account ɗina. Irinsu Abduljalal Wata kissar sai mata Wuta a masaƙa Cutarwa Ƙanwar maza Gaba da gabanta Aƙidata Ruɗin ƙuruciya
Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata. 08081012143.
And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link. https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Ayshercool.
Ayshercool 08081012143
*CUTARWA!"
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
P17
FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK.
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
Masu neman free books ɗina, da free pages duk akwai a kan watpad account ɗina. Irinsu Abduljalal Wata kissar sai mata Wuta a masaƙa Cutarwa Ƙanwar maza Gaba da gabanta Aƙidata Ruɗin ƙuruciya
Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata. 08081012143.
And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link. https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Ayshercool.
PAID ADVERT!.
Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi. Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku
Oll types of Turaran wuta Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra Kulakcha Dilke da kalta Kayan Garan jiki Muna turara Kaya Kujerar garan jiki Kannada Madarorin turare masu kamshi Man garan gashi Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921
*TALLA!TALLA!TALLA!* *INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*. *BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU* *MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA*
BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI
P17
Shiru noor tayi, tamkar tana jin abun da ummi take faɗa.
Sosai ummi ke kuka, tamkar za ta shiɗe, duk da ba wannan ne karon farko da aka yi mata ƙazafin sata ba, amma na yau yayi mata zafi da ciwo ba kaɗan ba.
Ji tayi an dafa ta, ta ɗago da sauri dan ba ta ji shigowar mutum ba.
Abdul ta gani a bayanta da kayanta a hannunsa, cikin damuwa ya ce "Dan Allah yaya ummi kiyi haƙuri, na san ba zaki yi sata ba, amma ki yi haƙuri dan Allah ki daina kuka, kar kanki yayi ciwo".
"Yaya Abdul, ya aka yi kai ka yadda ba zan sata ba, amma anty farida da rahama suka ɗora mini sata? Suka ci mutuncina a gaban mutane?" ya durƙusa ya ce "Na san babu daɗi, kiyi haƙuri dai dan Allah"
Ta jinjina masa kai, dan kuwa tana ganin mutuncin Abdul sosai da sosai.
Ya ɗora da cewa "Kar ki ga ɗakinki a haka, mun yi magana da abba ne, ya ce a bari mu tare ya ga ɗakin da maama zata baki, sai ayi miki furnitures, kar a saka miki ta hanaki ɗakin".
Ummi ta girgiza kai ta ce "Dan Allah kar ka bari yayi mini, ya kashe kuɗi da yawa, ni katifata ta isheni, duk kyan furnitures ɗin da za a saka mini, ƙarshe a tsakiyar ƙasa za a binne ni, hakan ma ya isa"
Shiru yayi yana kallon ummi, ta kwanta a kusa da noor, ta sanya hannunta ta riƙe ɗan ƙaramin hannun jaririyar.
Abdul ya tashi ya fita yana waiwayenta, duk abun da aka yi mata, bai sanya tayi zuciya taƙi kula noor ba.
Kasancewar a gajiye take, wani irin nannauyan bacci yayi awon gaba da ita, baccin da rabon da tayi makamancinsa har ta manta.
Kwanki uku da tarewarsu, aka kawo wa ummi ƙatuwar katifa, da wardrobe mai biyu, sai ɗan mudubi da stool.
Ba ƙaramar murna ummi tayi ba, tare da wani farinciki, wai duk wannan nata ne abun mamaki.
Kawu yahaya ya fara deciding zuwa ƙauye, ya gaida Iya, dan haka ya tambayi ummi ko za ta bi shi, ta je a gaggaisa.
Amma tayi shiru ba ta ce komai ba.
"Ummana baki ce komai ba"
"Kawu ka ce ina gaishe su, ba sai na je ba" tayi maganar tana addu'a a zuciyarta, kar ya matsa ya ce sai ya tafi da ita, saboda tana tsoron ya tafi da ita, Iya ta sake cewa ba zata biyo shi ba.
"Ƙauyen ne ba kya son zuwa ko ummana?"
Ummi ta gyaɗa masa kai alamar eh.
Yayi murmushi ya ce "Kwantar da hankalinki kyakywar uwa, abun da ki ke so shi za a yi, zan sanar da su saƙon gaisuwarki, ko ni ba zan so ki je ba, sai kin zama cikakkiyar mutum, da babu wanda zai tursasaki yin abun da ba kya so a rayuwarki".
Kawu yahaya da kansa ya je ƙauye dan ya ɗaukko iya, ta zo ta ga sabon gidansa da jaririya, amma ta ce ba zata ba, saboda matarsa ba ta da mutunci.
Hashim kuwa yana ganin kawu yahaya ummi ya fara tambayarsa.
Ya ce "Ummi na nan lafiya ƙalau Alhamdilillah, tana nan tana karatunta duk ta ce a gaishe ku"
"Allah sarki ummi, muna amsawa".
Iya ta ce "To wai yaushe zaka dawo mini da ita ne?"
Kawu yahaya yayi murmushi ya ce "Ai Ummi sai Allah ya kaimu lokacin aurenta zamu gayyace ku, ba zata sake zuwa gagarawa ba".
A ɗan hasale ta ce "Saboda me?"
"Saboda babu abun da za ta zo tayi muku"
"Kai yahaya bana son sakarci, zumuncin fa? So kake ka raba mini kan iyali?"
Ya girgiza kai ya ce "Ba haka bane ba, na nemi iznin zuwa da ita, ta ce in gaishe ku, saboda makarantar ta"
"Innalillahi wa Innalillahi raziƙuna, ita ummun ce ta faɗi haka? Ta fifita boko a kaina?"
Magaji ya ce "Iya wa Innalillahi raji'un ake cewa ba raziƙuna ba"
"Zan ci uwarka idan na sake magana ka tsoma mini baki, tun kan a haifi uwarka haka ake faɗa, ba damar mutum ya motsa sai ka ce zaka ci gyaransa?"
Ganin Iya na son dasa faifan cin zarafin ummi da iyayenta, ya sanya shi bawa Iya abun da zai bata ya tashi ya ce zai tafi.
Har mota hashim ya raka dr., Ya ce a cewa ummi yana gaisheta, tayi karatu da kyau.
Kawu yahaya yayi alƙawarin isar da saƙonsa ga ummi.
Kasancewar fitar sassafe yayi, yana gama abun da zai yi ya dawo kano, a falo ya yada zango, ummi tuni ta gama girki tayi shirin tafiya islamiyya, ya tsareta a falon yana bata labarin saƙon ƴan gidan na gaisuwa a gareta.
Ganin yadda ummi ta ɗan sake da kawu yahaya, har tana tambayarsa wasu daga mutanen gidan, ya sanya farida yi mata tsawa, ta ce ta tashi ta tafi makaranta.
Abdul ya shigo da noor a hannunsa, ummi tayi saurin karɓarta, ta ɗan ɗagata sama ta ce "Mamana tafi ta kowa" noor kuwa ta buɗe baki tana dariya.
Wata irin zabura farida tayi, tun da ummi take kiran noor da maman wasu lokutan, ba ta taɓa kawo sunan mahaifiyar ummi bane ba sai yanzu, tayi wata irin zabura ta ce "Dr. Sunan matar ƙaninka ka saka wa noor? Babar ummi?".
Kai tsaye ya ce "Yes"
"Saboda me? Meye alaƙata da ita? Ita tayi mini cikin? Ko ita ta haufa mini, wai tsaya meye alaƙarka da ita?".