Cutarwa complete by ayshercool - Chapter 3
Cutarwa complete by ayshercool Chapter 3: Cutarwa complete by ayshercool Chapter 3. Mariya ta ƙara tsananta kula da jan ummi a jiki, babanta ya kaita…
3,373 words
Mariya ta ƙara tsananta kula da jan ummi a jiki, babanta ya kaita makaranta, ita kuma ta je ta ɗaukkota, ta daina barin kowa ya raɓi ummi.
Mariya na zaune na ƙoƙarin koyawa ummi assignment a tsakar gida, kasancewar tana aji na uku a sakandare aka yi mata aure, ta iya karatu da rubutu. Iya na zaune suna hira da babarsu magaji da idris.
Ummi taƙi mayar da hankali a kan karatun da mariya take koya mata, sai soshe-soshe take yi, tana ɓata fuska.
"Mamana, wai ba zaki mayar da hankali ba, so ki ke anty ta zane ki?"
"Mama ni bana son makarantar" tayi maganar hawaye na taruwa a idonta.
Cikin damuwa haɗi da kulawa ta ce "Saboda me ummina"
Cike da ƙuriciya ummi ta ce "Tsokanata ake yi, mama dan Allah ki mayar da ni fara, kuma ki rage mini ƙibata"
Mariya ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Ummina, ke fa kyakywar yarinya ce, ai kin san sahabban manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam, da nake yi miki tarihi ko?" Ummi ta jinjina kai ta ce "Eh, Ina son tarihi"
"Yauwwa ummina, mai kiran salla a zamanin Annabi Sallallahu alaihi Wasallam, sayyiduna Bilal radiyallahu an hu, baƙi ne, kuma Annabi bai taɓa ƙyamarsa ba, haka sahabbai ma"
Ummi ta yi shiru ta ce "To mama kin ce in din ga son annabi, to masu tsokanata ba sa son annabi ko?"
Shiru mariya ta yi, tana tunanin wane bayani za ta yi wa ummi, dan duk da rashin sakewarta da mutane, idan tana tare da mamanta, akwai surutu.
Iya ta ce "Kin ga kar ki sakawa yarinya wani tunani daban, ki gaya mata gaskiya kawai, mummuna ce ko ki so ko ki ƙi"
Babar su magaji ta kwashe da dariya ta ce "Iya wannan jika taki, ai tun yanzu yakamata a fara nema mata maganin farin jini, dan za ayi gwagwarmaya kan a samu mai so, dan ina jin Alhassan ranar yana cewa; da zai samu igiya da ya zargawa ummi, ya tafi tashe da ita a matsayin ɗan biri" tayi maganar tana ɓaɓɓaka dariya ita da iya, ba tare da tunanin, ya mariya zata ji a zuciyarta ba ko ita yarinyar, ummi tayi ƙuri tana kallonsu, duk da yarinya ce, ta san cin mutunci.
Mariya ta ce "Biri kuma, ummin za a yi wasan biri da ita, kuma ki ke dariya, shikenan bakomai" tayi maganar cikin ƙunar rai, ta kama hannun ummi suka tafi ɗaki.
"Mama, da gaske ni biri ce? M, for monkey na bayan littafina?"
Mariya ta goge hawaye, ta ce "Ummina ke mutum ce, mai kyau sosai da sosai, kar ki sake haɗa kanki da biri kin ji ko? Kina da kyau sosai, kalli gashinki fa, duk garin nan kin ga mai irin gashinki?"
Ummi ta girgiza kai alamar a'a.
"Yauwwa ummi, idonki ma mai kyau ne, ina son idonki, duk garin nan babu mai irin idonki".
Ummi ta taɓa idonta ta ce "Sai akuya ko?"
"Akuya kuma?"
"Eh, malamarmu ce ta faɗa, ta ce ni da akuya irin idonmu ɗaya, eyes sunan ido da turanci in ji anty"
Mariya ta yi shiru tana kallon ummi, yarinyar na cikin taskun ƙalubale, daban-daban, har a kai ga malamarta na kamanta ta da akuya.
Iya kuwa ta cigaba da hurawa balarabe wuta, da shi da mariya, cin kashin yau daban na gobe daban, har ƴan uwansa ma, ware shi suke a wasu abubuwan saboda ba shi da kuɗi, haka zalika mariya ta cigaba da yi wa iyalan gidan bauta, idan anjima su yi mata rashin mutunci, ko a ci zarafin ƴar ta a gabanta ba.
Kusan kullum sai ummi ta ce ba ta son makaranta, dan kuwa abun da mariya ta fuskanta, ba iya ɗaliban ne ke tsokanarta ba har da malamansu a ciki.
Dan idan ummi ta zo da aikin gida, tayi a gida, sai ta ce ba zata nuna wa malamarsu ba, idan ta tambayeta dalili sai ta ce "Malamarmu cewa take yi in fito gaban Allo, a tafawa ƴar baƙa saran daddawa, ayi mini dariya, ni kuma in yi ta kuka sosai, bana son ana tsokanata"
Ba ƙaramin ɓaci ran mariya yayi ba, Dan haka da kanta ta je makarantar, ta roƙi headmaster, a kan ya taimaka ya tsawatar a kan abun da ake yi wa yarinyar, kar son karatun ya fita daga kanta gaba ɗaya.
Yayi mata alƙawarin yin hakan, sai dai ba ta canza zani ba.
Ummi na ta kaiwa tana komowa a tsakiyar ɗakinsu da safe, kasancewar yau ba makaranta, sai fama take da uban gashinta, taƙi tsayawa a gyara, mariya sai fama take da ita ta nemi wuri ta zauna.
Ta kalli babanta da yake cin abinci ta ce "Baba kafi mama loma" tayi maganar tana dariya.
"Eh mana, baki ga na fita girma ba?"
Ummi tayi dariya ta ce "To ni kuma gaba ɗaya ƴan gidan nan, na fi su loma"
Mariya ta ce "Ke ɗin, sai ka ce abinci ki ke ci"
"Mama nafi duk ƴan yara girma fa"
Babanta ya ce "Kin fi su lafiya ne, kuma kin fi su kyau shalelena"
Ta kama kumatunta ta ce "Iya ta ce bani da kyau ai"
"A'a ke kyakywa ce sosai" miƙewa ummi ta yi ta fita daga ɗakin, tana leƙa baƙon ɗan magen da yake wasa a tsakar gida.
Mariya ta yi ajiyar zuciya ta ce "Baban ummi, kana ganin ummi zata iya samun miji tayi aure?"
Ya kalle ta ya ce "Meyasa zaki faɗi haka? Kina mahaifiyar ta, kema kin fara biyewa surutun mutane na cewar ƴarmu ba ta da kyau mummuna ce?"
"Ba haka bane ba, abun yana taɓa ni sosai da sosai, har malaman su ummi su da zasu tsawatar wai har da su a cikin tsokanarta, babar su magaji wai har da cewa Alhassan ya na kiran ummi da biri, kuma ta faɗa suna dariya"
Jiki a sanyaye ya ce "Biri kuma? Cin mutuncin ya kai haka? Wallahi mariya ummi ba mummuna ba ce ba, tana dai da duhu ne, kuma ƙwayar idonta ce da ba irin tamu ba, amma ba mummuna ba ce ba"
Mariya ta numfasa ta ce "Ni ba wannan ba, duk wanda ya ci zarafin ummi, na san bani na halicceta ba, amma abun da yake damuna, a zamanin nan yarinya ta kai mutuncinta ɗakin aure, ya ta ƙare ina ga idan ummi ta samu miji, gaya masa zamu yi ga abun da ya same ta? Idan muna gaya masa waye shaida babu tabbacin a lokacin dukkaninmu da muka sani muna raye. Idan kuma muka rufa, zai yi mata kallon mutuniyar banza, ummi ta san abun da ya faru da ita mummunan abu ne. Ina tausayawa yarinyar nan abubuwan da suka baibaye rayuwarta, ina tausayawa ƙalubalen da zata fuskanta wataƙila bana nan a lokacin balle na tayata kwasar raɗaɗin, amma ina tausayawa ummi, idan ba ta samu miji mai tawakalli ba, za ta fuskanci wulaƙanci, wa zai so mini ummi tsakani da Allah, ya karɓi ƙaddarar da ta same ta? Wallahi baban ummi ba zan yafe wa yaron nan ba, ya cuce ni ya cutar da rayuwar ummi, ko idan ta ƙara girma zata manta oho, haryanzu bata yadda na bar ta a ɗaki ita ɗaya, an cuce ni" tayi maganar kuka mai ƙarfi yana ƙwace mata.
Balarabe yayi ajiyar zuciya, yana jin ɗaci a zuciyarsa ya ce "Wallahi mariya ni kaina abun nan yana ci mini zuciya, ba yadda na iya, mahaifiyata ta riga ta yi mini kandagarki, ƙetare maganar ta na iya shafar mu baki ɗaya, amma in sha Allah, ina sanya ran Allah ba zai wulaƙanta ummi ba, dan Allah kiyi haƙuri mariya, wallahi idan kina kukan nan, sai na ji kamar na bijirewa umarnin iya, na ɗau matakin abun da aka yi wa ummi".
Ta share hawayen ta, ta ce "Kar ka yi haka, aikin gama ya riga ya gama, ko ka ɗau mataki, wannan wani miki ne a zukatanmu da ba zai taɓa warkewa ba".
Yayi shiru ya zubawa mariya ido, shi kansa ya san mariya ba ƙaramin haƙuri take yi ba, zama da shi. Tsakaninta da shi babu wata matsala, amma azabar wahalar da take a gidan, duk ta rame ta yi duhu, soyayar kirki ba sa samun sakewa su nunawa juna, saboda azabar iya.
Ihun Ummi suka ji, hakan ya sanya su yin rige-rigen fita tsakar gida da gudu.
Ummi suka tarar da Alhassan ɗan wurin saminu, ya tattara gashin ummi, ya murɗe shi a hannunsa, jijiyoyin kanta sun mimmiƙe, duk ta gigice.
A guje mariya ta ƙarasa, ta hankaɗe shi, ta ƙwace ummi da ke kuka.
"Alhassan me ummi tayi maka ka murɗe mata gashi haka?"
Cikin fitsara yaron ya ce "Ɗan magenmu take mana wasa da shi"
A fusace mariya ta ce "Kuma saboda zalunci ka rasa me zaka yi mata, sai izaya da gashinta?"
"To waye ya ce ta taɓa mana magenmu, ana ta nemansa?"
Cikin zafin rai, mariya ta ɗauke Alhassan da mari.
Sai da balarabe ya waro ido.
"Tura ta fara kaiwa bango, wane irin zalunci ne haka? Ummi fa ƴa ce ba baiwa ba, wallahi duk wanda ya kuma dokar mini ƴa sai na ci ubansa. Dama a ciki nake da kai, na samu labarin kana ce mata matashiyar buranya, uwarka ce mai kama da buranya ba ita ba"
"Wayyo Allahana iya, a taimake ni ta kashe mini ido" Alhassan ya wage baki yana kwarmato"
Bakomai ya hana balarabe taɓuka komai ba, face sanin idan iya ta fito ba ƙaramar tijara zata yi ba, kuma ƙarshe su zata ɗorawa laifin".
Buje a hannu iya ta fito daga banɗaki tana faɗin "Menene haka? Kashe yaron zaki yi me yayi miki?"
Alhassan ya kwashe ƙarya da gaskiya ya gaya mata.
Ta kuwa hau sababi "Balarabe kana tsaye take neman yin kisan kai, shikenan an taɓa ƴar gwal sai tayi yinƙurin cire masa ido. Duk ɗawainiyar da ubansa yake yi a gidan nan? Wace irin ɗawainiya ce ba yayi da ku, wasu lokutan ba har ciyar da kai yake ba da iyalin naka, da baka ganin kowa da mutunci sai su, saboda zuciyarka ta riga ta mutu, baka da amfani ka kashe zuciyarka ka auri mai ƙashin tsiya, baka da komai sai sokonci da son mace, wadda maganarta ta fi tawa, tun da tana baka abun da bana baka, to kayi ƙoƙari ta kashe masa ɗa, wallahi duk matakin da ya ɗauka a kanku, babu ruwana ko da kuwa wurin hukuma zai kai ku"
Cikin takaici mariya ta ce "Wato iya saboda baban Alhassan yana da kuɗi shi ne ɗa, da idan aka ɗaukar masa mataki ba zaki hana ba, ummi ce da aka ketawa haddi ba ƴa ba? Iya Allah fa" cikin hanzari balarabe ya girgiza mata kai. Cikin ɗacin zuciya ta koma ɗakinta.
"Ai da ka bar ta ta cigaba da gaya mini magana, ta tabbatar mini da bata da tarbiyya, kai ban da ina tsoron Allah da wallahi tuni na saka ka saketa, ko Allah ya sa ƙofar arzkin ka ta buɗe, idan ya so ka auro falla-fallan mata, mu samu ta haifa mana masu kyau, kadara irin arziki"
Bai cewa iya komai ba, ya shiga ɗaki, ya tarar mariya ta rungume ummi, tana aikin kuka. Zai yi magana ta ɗaga masa hannu, ta yi masa alamar ya rabu da ita, haka ya ƙyaleta ya fice.
Har ya tafi kasuwa tunani yake yi? Ko haya zai nema ya tashi ya bar gidan, ya san ba iya ce kaɗai ke da hakki a kan sa ba, iyalansa ma na da hakki a kan sa, kuma suna buƙatar walwala, amma iya ta takura su da yawa, kuma ya san ba zai iya biyan haya ba, kuma duniya zata zage shi, ya kasa zama da matarsa ya fifita iyalansa a kanta, haka yayi ta tunani, ba tare da samun mafita ba.
Mariya ma wuni tayi tunani da zancen zuci, ita kanta ta san bata isa ta tafi gida ba, ta ce tayi yaji saboda takurar uwar miji ba, ba babanta ba yayyenta maza kawai sun ishe ta, babu mai goya mata baya, dan ko hirar take musu, idan ta je ganin gida, sai ace uwa ce a wurinta idan da kara da tarbiyya. Gidansu irin iyayen nan ne masu kashe ƴaƴansu su raya na wani a gidan aure, saboda dattaku dan gidansu gidan malamai ne. Kuma ko kusa ba zata iya gaya musu cewar an yi wa ummi fyaɗe ba, saboda ita kanta da take ta hayagagar rashin bi wa ummi hakkinta, tana yi ne saboda abun yana damunta, mussaman nuna wa da ake yi ƴar kamar ba ta da amfani, saboda babanta ba shi da kuɗi.
"In sha Allah ummi sai ahalin nan sun kwanta a kafaɗarki, Allah ya nesanta ki da talauci, ya baki ikon cin jarrabawar nan da ni da ke baki ɗaya. Allah shi ya san dalilin da ya sanya yayi ki a haka, kuma ya jarrabeki Allah ya baki mai kula da ke, ko bana raye" haka ta wuni cikin kuka da damuwa.
***" Rayuwa ta cigaba da tafiya, umma ta cika shekaru shida a duniya, sai dai bata sauya zani ba, domin kuwa gorin yau daban na gobe daban, haka iya ke yi, a kan cewa balarabe ba ya iya tsinana komai, a gidan komai shi ne koma baya.
Haka zalika balarabe, ya fara tunanin miƙewa ya nemi kuɗi, ko dan samawa iyalin sa farinciki da kwanciyar hankali, mussaman ƴar ƙaramar yarinyar nan, da aka mayar da ita tamkar wata halitta daban.
Yau suna kwance da daddare tare da mariya ya ce "Maman Ummi kin san wani abu?"
Ta ce "A'a"
"Ina ga ƴan kuɗaɗena da nake tarawa, zan je birni in ga abun da zan iya yi, ko Allah ya sa na samo arziki"
Mariya ta kalle shi ta ce "Baban ummi baka yadda da yadda Allah ya ajiye mu ba? Na san babu daɗi abun da iya take yi maka, amma dai ka yi haƙuri da barin garin nan, ka tafi yawon neman kuɗi, raba bawa da arziki sai mutuwa, dan Allah kayi haƙuri"
Ya gyara kwanciyarsa ya ce "Maman ummi, tun da abun nan ya faru da ummi, ji nake tamkar ina kan wuta, gidan galibi duk maza ne tana cikin haɗari, sannan ki duba ki ga yadda ake yi mata a gidan nan, ɗazu fa suna tafe da yarinyar nan da take ɗaukarta ta tafi da ita islamiyya, yara suna tsokanarta baƙar tukunya mai ƙyalli, ba ki ji zuciyata ba, wallahi yanzu haka bani da burin da ya wuce tashi na bar gidan nan. Da nayi tunanin ko kano zan je wurin yaya hashimu idan da wata hanya da zai ɗora ni a kan kasuwanci, to kuma bana son na je na ɗora masa ɗawainiya, kuma kin ga shi ɗan boko ne, iya ta ce sai na bi su Rabiu kudu neman kuɗi, bana son yin nesa da ku, amma na fuskanci idan na cigaba da zama a haka, wahala zamu cigaba da sha".
Mariya ta nisa ta ce "To, ni dai dan ta ni, wallahi baban ummi zan cigaba da haƙuri, komai lokaci ne, amma duk abun da ya shafi umarnin iya, babu ruwana a ciki, Allah ya taimaka ya bayar da sa'a, ummi kam za ta yi gwagwarmaya wadda sai dai mu bata gudunmawa ba zamu iya tare mata ba.
"In sha Allah komai zai zo da sauƙi, kuma zai wuce umminmu zata rayu cikin farinciki"
"Allah ya sa"
Ya amsa mata da "Amin"
Abu kamar wasa, Iya ta din ga yi wa balarabe kwarmato, a kan lallai ta yi magana da Rabi'u maƙwabcin su, lallai ya nemo kuɗi, ya bi shi lagos, ya ɗora shi a kan hanyar neman arziki.
Bashir ba shi da kuɗin da aka ce ya tanada, dan kuwa rabi'u cewa yayi ya tanadi dubu ɗari, harkar fawa yake a lagos, ya je ya koya masa.
Ya ce wa iya ba shi da halin kuɗin nan ta ce "Ai dama ba zaka yi su ba, Allazi babu wanda ya karɓo jakadancin talauci zuwa duniya, ka je ka tambayi ilyasu, ko sagir, ga saminu, ko Yahaya, tun da su masu zuciyar nema ne, kuma ba a rasa nono a riga, su baka aro. Bashir baya son dalilin da zai sanya ya keta billensa ya nemi alfarmar ƴan uwansa, saboda yadda ba sa yi da shi.
Amma bisa ga umarnin iya, ya tambayi sagir aron kuɗi, amma ya kada baki ya ce "In ara maka kuɗi, ka biyani da me? Gaskiya ba zan iya ba, kuɗin nan masu wahalar samuwa, na baka in yi sadakar dole da ba niyya, kayi haƙuri kawai". Ya ji ciwon abun da yayi masa, amma ya dake ya gayawa maman ummi.
Ita kanta mariya abun yayi mata ciwo, abun da iya take musu ya sanya ta tsane ta, duk da ita ta haifi mijinta, tattara samirun ta, har da zobenta da aka saya mata lokacin aure ta sayar, sai ganinta yayi da kuɗi, dan ita kanta wulaƙancin da ake yi masa yana bata haushi.
Ya din ga yi mata faɗa a kan sayar da kayanta da tayi.
Ta ce "Idan har tafiyarka zai sanya iya farinciki, a daina wulaƙanta mu, ka tafi kawai Allah ya tsare"
Ya riƙe hannunta ya ce "Na gode mariya, Ubangiji Allah ya saka miki da alkahirin sa, ya ƙara miki haƙuri, kada Allah ya sa na ci amanarki, ko a yanzu ko a gaba, Ubangiji Allah ya kula mini da ku" haka ya din ga zuba mata addu'a kamar ta yaye masa gaba ɗaya matsalolin sa.
Saura kwana ɗaya ya tafi, da ya shiga ya fita, sai yayi musu addu'a, ya sanya musu albarka da ita ummi.
Da daddare mariya ta shirya masa kayansa a wata jaka, tana ta yi masa addu'a. Ya zura mata ido yana kallon ta.
"Wai wannan kallon fa?"
"Da za ace in nuna matar aljanna a duniya, zan nuna maman ummi"
Tayi murmushi ta ce "Zaka fara ko?"
"Allah ba wasa nake ba amaryata" ta kwashe da dariya ta ce "Ko ba amarya ba, da wannan ƴar tamu nake amaryar, in zo in fara tara kayan ɗakin auren ummi, wai wa ya ganni maman amarya ranar auren ummi ba zama".
Yayi dariya ya ce "Kema ɗin yaushe aka yi naki auren ki ke hango auren ummina, in sha Allah sai ta yi karatu mai zurfi, Allah ya sa kan na tafi ɗin nan akwai rabo a cikin nan, ummi ta samu ɗan uwa"
"Amin ya Allah, ni kaina ina son jariri wallahi"
"To Allah ya bamu mai amfani, ya bani kuɗi na halal na wadata ku, mu rayu cikin farinciki"
"Amin, amma yanzun ma Alhamdilillah, ai kuɗi ba su ne farinciki ba" sosai suka din ga hira, tana ce masa ban da kallon matan yarabawa idan ya tafi lagos, ya din ga yi mata dariya.
Har ta yi barci, amma shi ya kasa bacci, ya tashi daga kan gadon, ya koma shimfiɗar ummi, da ta yi nisa a baccinta sosai.
Ya kunna fitila yana kallonta, sam bai ga munin ƴar sa ba da mutane suke faɗa suna zuzutawa.
Ya din ga shafa gashin ummi, yana kallonta.
Mariya ta yi juyi ta hango shi, ta ce "Baban ummi, ko saka maka ita zan yi a jakar ka ku tafi, wannan ƙauna haka?"
Yayi murmushi ya ce "Ko yara nawa zan haifa ummi ta daban ce a zuciyata, ina ƙaunar yarinyar nan"
Mariya ta ce "To kar dai ummi ta mamaye ko ina a zuciyar, a rage mini wuri"
Yayi murmushi yana cigaba da kallonta.
Juyi ummi ta yi taga hasken fitila, ɗan razana ta yi, saboda haryanzu ba ta manta yadda aka yi mata fyaɗe ba, dan daren da aka yi mata fyaɗe ta tuna, da ƙarfe ta ce "Baba"
Ya ce "Na'am ummina"
"Kai ne" tayi maganar tana shafa fuskarsa.
"Eh Ummina"
Ta ce "To" ta cigaba da lumshe ido zata koma bacci.
"Ina ƙaunar ki ummina, Allah ga ƴa ta da mata ta, Allah ka kula mini da su, ƴar kyakywar ɗiya ta" yayi maganar yana jan kumatunta. Ummi ta ɗora hannunta a kan nasa tana murmushi ta cigaba da bacci.
Washegari da zai tafi har soro suka raka shi, ji yake tamkar kar ya tafi, amma yana fatan idan har tafiyar ta sa zata zama silar walwalar iyalin sa gara ya tafi.