Kenza eBookz

Cutarwa complete by ayshercool - Chapter 4

Cutarwa complete by ayshercool - Chapter 4

Cutarwa complete by ayshercool Chapter 4: Cutarwa complete by ayshercool Chapter 4. Sai da iya ta fara maganganunta na rashin mutunci, a gaban mutane tana…

3,366 words

Sai da iya ta fara maganganunta na rashin mutunci, a gaban mutane tana neman yi musu tijara, sannan suka rabu ya tafi.

Kwanaki uku da tafiyar baban ummi, kewa duk ta ishi ummi da mariya, sai dai tafiyar ta sa bata sanya sun samu sassaucin jaraba da masifar iya ba da gore-gore, gashi a lokacin waya bata yawaita ba, dan haka ba wanda ya san halin da wani yake ciki.

Bai fi sati biyu ba da tafiyar sa, abun da ya bar musu duk ya ƙare, gashi abu kamar wasa, muraran yara ke cigaba da cin zalin ummi, ga farmaki da Idris yake cigaba da kai mata, loka-lokaci da wasu daga samarin gidan, dan ma yanzu ta yi wayo sosai da sosai, da ta gansu sai gudu.

Cin zali a wurin ƴan samarin yaran nan maza, tamkar sun samu sa'ar su, saboda tana mace, abu kaɗan sai a kai mata duka, ko ayi mata wata izayar ko a gida ko a makaranta, saboda ana ganin ummin tamkar sokuwa, kuma babu mai tare mata, da mariya tayi magana iya tayi kanta da tijara.

Ɗan abun da ya rage a hannunta, ta fara fanken sayarwa, saboda ta samu abun juyawa, amma sai da iya ta cinye jarin da cin bashi, tare da tula mata ayyukan da zasu hanata sana'ar.

Abubuwa fa suka fara yi wa mariya da ummi yawa, duka ko ta ko ina, wani ta iya karewa, wani ta kasa sai dai tayi kuka ta gaya wa Allah.

Tana tsakar gida tana wanke-wanke, ta samu da ƙyar ta jiƙawa ummi garrin kwaki, bayan ta dawo daga makaranta tana sha, ta ji hayaniya ta yi yawa a waje. Bata damu ba ta cigaba da aikinta.

Da gudu Alhassan ya shigo ya ce "Babar ummi Albishirinki?"

Ta kalleshi ta ce "Albishirina kuma? Menene?"

"Wai baban ummi ƴan fashi suka kashe a hanya, zasu taho gida daga ikko!!!"

Ayshercool 08081012143 *CUTARWA!*

Watpad ayshercool7724 Arewabooks ayshercool7724 YouTube https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels What's app 08081012143

BRIGHT PENS (FREE BATCH)

P4

Wani irin jifa mariya tayi da kwanon hannunta, ta miƙe a gigice jikinta na wata irin tsuma, zuciyarta na bugawa da saurin gaske amma ta kasa magana.

Miƙewa ummi ta yi ita ma, tana bin su da kallo.

Iya ta fito a gigice ta ƙundumawa Alhassan ashariya ya ce "Uban wa ye ya gaya maka haka? In ji wani ɗan iskan".

Ilyas da saminu ne suka shigo, fuskokin su babu walwala.

"Ku gyara wurin da za a shigo da balarabe, Allah ya yi masa rasuwa, tun safe muka tafi ɗaukko gawarsa"

A gigice iya ta ce "Ƙarya ne ban yarda ba, ya za ayi ace ya mutu? Balaraben ne ya rasu? Waye ya kashe shi, ya aka yi aka kashe shi?"

Sagir yayi sallama tare da idris, ya ce "A ina za a kwantar da shi idan an shigo ne? Ana jira fa"

Mariya ji take abun kamar mafarki, addu'a take Ubangiji Allah ya sanya mafarki ne, Allah ya sa ba mijinta ne ya mutu ba, Allah ya sa ba baban umminta ne ya mutu ba".

Magaji ya shigo da tabarma, ya shimfiɗa, aka yi sallama tare da ƴan sanda, da rabi'u da suka tafi tare, aka shigo da gawar bashir, tana ta ɗigar da jini.

Nan da nan gida ya cika da jama'a, Iya sai ihu take tana kururuwa tana kuka, kai da gani ka san jahilci ya samu gidin zama a wurin iya, saboda yadda take ihun ta shiga uku ta lalace.

Jiki na rawa mariya ta saka hannu ta buɗe mayafin da aka rufe gawar bashir, fuskar nan fayau kamar yana bacci, kamar wanda yayi wanka ya fito haka gawar take, ga ƙirjinsa in da aka harbe shi, jini yana ta zuba.

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un" shi ne abun da mariya ke ta nanatawa, tare da fatan Allah ya saukar mata da nutsuwa da dangana.

Ummi ta shafa fuskar sa tana faɗin "Baba ka tashi, baba ka tashi daga bacci mama tana kuka" cikin haɗe rai sagir ya yi wa ummi tsawa ya ce ta tashi.

Sa'adatu ta ce "Haba baban auwwalu, ka tausaya musu mana".

Mutane suka cika gidan danƙam, saboda mutane sun san bashir sosai, mutum ne na mutane mai matuƙar haƙuri da girmama mutane.

Sai ajiyar zuciya kawai mariya take yi, tana rungume da ummi, aka shiga da shi ɗakin Iya, aka yi masa sutura, sannan aka ce su je su yi sallama da shi.

Har a lokacin mariya ta gaza zubar da hawaye, sai wata irin ƙuna da zuciyarta ke yi mata, abu kamar wasa bashir shikenan an yi an gama, rayuwar ta ƙare.

Duk da yarinta ta ummi, amma ta san idan an mutu ba a dawowa, tayi kuka idonta duk ya kumbura, ta dinga taɓa shi tana "Baba ka tashi, ka ce zaka sai mini ƴar tsana in yi addu'a ka samu kuɗi, kullum ina yi maka addu'a"

Mariya kam zubawa gawar ido kawai tayi, tana kallon ikon Allah, wai bashir ya mutu.

Sa'adatu ta ce "Mariya ki riƙe yarinyar nan, za a shigo a ɗauki gawar"

Mariya kamar sokuwa, dan kamar ma ba ta iya gane me ake cewa.

Aka zo aka ɗauki gawar bashir, ana ta iface-iface, ummi ta riƙe ƙafar Saminu wan mahaifinta, da suka ɗaga gawar, tana wani irin kuka, amma babu tausayi ko imani, ya angije ta ƙasa suka yi waje.

Allah sarki, ba ta karaya ba ta sake bin su, tana faɗin "Ku dawo da baban, zai tashi fa, bacci yake yi"

Surayya, wadda take ƴar autar su bashir, ta riƙo hannun ummi tana kuka, ta rungume ta, tana ta rarrashinta.

Gida ya cika da jama'a ana gaisuwa, mariya kuwa ta samu gindin bishiyar da ke tsakar gidan ta rakuɓe, tayi shiru ba ta cewa komai, ita kaɗai ta san azabar da zuciyarta take yi mata.

Bata san hawa ba, ba ta san sauka ba, ta ji muryar iya na bala'i a cikin mutane "Dama ya za ayi mutuwar ta dame ta, ai dama ba dan Allah take zaune da shi ba, kalleta a ƙeƙashe ko kuka ba ta yi ba, alhalin ita ta takura lallai ya tafi neman abun duniya, ya zo ya wahalta mata, wallahi ban yafe miki ba"

Daram! Gaban mariya ya faɗi, jin abun da iya ta faɗa na ƙarshe.

Mutane suka shiga salallami, surayya ta ce "Haba iya, haba iya, baki san kukan zuci yafi kowanne ƙuna ba, gara ke kin yi kukan, ita kaɗai ta san me take ji a zuciyarta, da can ba ta ce ya tafi neman kuɗi ba, sai yanzu, dama Allah ya yi ajalinsa a can za same shi".

Ai nan ta mayar da faɗan kan surayya, wanda hakan ya tilasta mata yin shiru, wasu suka goyi bayan iya saboda makira ce, wasu kuma suka goyi bayan mariya, kowa ya san kusan halinta ɗaya da mijinta, ba sawa ba fitarwa, akwai haƙuri da juriya, mussman a zamanta da iya.

Yadda ta ga rana haka taga dare, abu goma da ashirin, ga raɗaɗin mutuwar mijinta, ga sharrin da iya ta ƙulla mata, wai ita ce silar mutuwar sa, ita ta hura masa wuta ya tafi neman kuɗi.

Ta rasa me ta tsarewa iya, take yi mata wannan azababbiyar ƙiyayyar, saboda kawai tana auren ɗan ta, abun da ba haka take yi wa sauran sirikanta ba, kuma dukkansu babu wanda yake yi mata biyayyar da take yi mata, kawai ta camfata cewar ita ce mai farar ƙafar da ta toshe masa hanyar arzikin sa, ya kasa gaba ya kasa baya, gashi ya ɗauki son duniya ya ɗorawa mariya, yana matuƙar son ta da ƙaunarta.

Ko fuskanta Iya tayi sun yi mu'amalar aure, ta ga sun yi wanka, to wunin ranar, haka zata wuni cikin ɓacin rai da tashin hankali, a wurin iya ta din ga ƙirƙirar mata laifi kenan tana ci mata mutunci, ta rasa wannan masifar, ga uwa uba ummi sunan kishiyar ta ne da ita, wanda hakan ya sa ta ƙara tsanar ummi, ga ƴaƴanta sun riƙe ta uwa, abun da ta dama suke sha, amma tana masifar kishi da uwar su.

Washegari da azahar, dangin mariya suka dira a jigawa, suka zo gaisuwa, haka zalika Yahaya, yayan bashir da yake birni, shi ma ya zo ta'aziyya, ya ji mutuwar bashir ba kaɗan ba, abun ya girgiza shi, dan kaf cikin ƴan uwansa, ko wanda suke ciki ɗaya, basa shirin da suke yi da bashir, saboda biyayyar sa, yana matuƙar girmama shi.

Yana son ummi, kasancewar sunan mahaifiyarsu ne shi ma da ita, marigayiyya uwar gidan malam hashimu.

Ya tarar ana ta fama da ummi, ba ta ci abinci ba, sa'adatu da ba wani shiri suke yi da mariya ba, amma mutuwar bashir, da abubuwan da iya ke ta yi, ya sanya wani irin tausayin su ya kamata.

Yahaya ya ga yadda ake fama da ummi, tana kwance a jikin mariya, ba wanda ya iya cin abinci a cikinsu.

Duk da tana tsoron maza sosai da sosai, kuma shi baya yawan zuwa gidan, amma ta gane shi, dan yana kama da babanta sosai, kuma yana bata tsaraba idan ya zo.

Ya ƙarasa ya ɗauketa, ya saka hannunsa a nata, ya ce "Mamana, ki din ga yi wa babanki addu'a, kuma ki din ga cin abinci, kuka ba zai yi magani ba"

"Baba ba zai dawo ba ko, ya mutu wai?" Tayi maganar hawaye na zubo mata, kamar an kunna famfo.

"Ba zai dawo ba ummi, amma zai ji daɗi idan kina yi masa addu'a"

Cikin kuka ta ce "Na fi son ya dawo" ya din ga share mata hawaye, cike da tausayawa.

Sai dai yayi mamakin yadda iya ke ta hantarar mariya, tana cikin alhinin mutuwar mijinta, ga ƴan uwanta a gida, amma iya na ta masifa da nanata ta kashe mata ɗa.

Ya dubi Iya ya ce "Haba iya, haba iya da wanne za ta ji? Ya za ayi ta yi sanadiyyar mutuwar mijinta, mijin da suka yi auren soyayya, shekara bakwai tare, ko sulhu ba a taɓa yi musu ba, ki ce ita ta kashe shi, ga ƴan uwanta a gida ai babu daɗi"

"Yahaya, ni fa nake zaune da yarinyar nan, ni na san abubuwan da take aikatawa, azabar son zuciyarta ya sanya ta hura masa wuta ya tafi neman kuɗi, gashi nan ya mutu a banza, yaron nan haƙurin zama yake yi da ita"

Yahaya ya ce "A'a iya, idan na zo fa muna hira da bashir, a bar kaza cikin gashinta kawai banda tone-tone, amma batun ace mariya ce ta kashe mijinta bai taso ba, dan Allah ki bari ta ji da alhinin da take ciki"

Kasancewar yana da abun duniya, domin kuwa lecturer ne shi a kano, kuma albashinsa da tsoka, dan haka yana yi wa iya sha tara ta arziki, a dole ta ja bakinta ta yi shiru.

Wasa² magana har waje wurin maza, iya ta tubure tana cin mutuncin sirikarta, wai ita ta kashe mata ɗa.

Yayan mariya har cikin gidan ya shiga, ya yi wa mariya wankin babban bargo. "Irin tarbiyyar da aka baki kenan dama mariya? Irin zaman da ki ka yi da mijinki kenan, ki kasa zama da shi a yadda yake, ki hura masa wuta ya tafi ajali ya riske shi, kuma gashi an ɗora miki, an ce ke ce sila. Mariya kin ɓata wayonki, wannan ba tarbiyyar gidanmu ba ce ba, kuma ahalinsa ba zasu taɓa mantawa da abun da ki ka yi ba". Kasancewar yana cikin manyan yayyenta, kuma tana bala'in tsoronsa, dan haka ba ta iya kare kanta ba sai kuka, ga shi a gaban mutane ya din ga yi mata faɗa, mariya ta rasa da wanne za ta ji.

Iya kuwa ta samu damar cigaba da ƙullawa mariya sharri a wurin yayanta.

Yahaya ya tsawatar, saboda shi ɗan boko ne, ya ce ba zai yiwu a saka mariya a gaba ace ita take aikata duk wannan laifukan ba. Idan ma haka ne tana matsa masa kan ya rasu yanzu yana ina? Kuma ai mijinta ne, tana da right na ya yi mata abun da take so.

Ɗakinta ta shiga ta zauna, tayi kuka, tayi kuka, har zuciyarta ta fara raya mata ko kashe kanta zata yi ta huta da wannan azabar.

Ummi ta zo tana kuka ita ma, dan tun ana yi mata faɗan nan ummi take tayata kukan, ta din ga share mata hawayen tana cewa "Mama ki yi haƙuri, ki daina kuka" ita kanta yayar mariya, ta san mariya ba za ta aikata haka ba, yadda iya ke yi wa mariya a gaban su, ba ƙaramin ƙular da ita yayi ba. Sai dai su al'adar gidan su, muddin ak kawo ƙararka daga waje, ba a taɓa goya maka baya, balle kuma a gidan aure, idan miji gutsurar namanki yake yana ci, sai ace ki je ki cigaba da haƙuri, wataran sai labari, kowa haƙuri yake yi.

Maryam ta tambayeta ina samirunya, ta ga duk babu? Mariya taƙi gaya mata, ta shashantar da zancen.

Bayan kwanaki uku da share zaman makoki, ƴan nesa suka watse, sai masu shigowa jefi-jefi gaisuwa, yayar ta ta zauna da ita, ta ɗan din ga ɗebe mata kewa, zuwa kwana arba'in, aga meye abun yi.

Gaba ɗaya mariya ta gama fita daga hayyacinta, kai daka ganta ka san tana cikin alhini, ko abincin kirki ba ta iya ci. Salla kawai take iya yi, wanka kansa sai ta yi da gaske take iya yi. Daga kwanciya sai kuka, amma hakan bai sanya ta tsira daga tashin hankalin Iya ba, ga kyarar ummi da take yi kamar ba jininta ba, wanda hakan ya fara tunzura yayar mariya maryam.

Kwanan bashir goma sha huɗu da rasuwa, rabi'u ya zo yayi sallama, suka amsa ya sake yi musu gaisuwa.

Ya ce wa iya "Ina mariya, ina son zan yi magana da ku ne"

Iya ta ce "Dole ne sai ta nan? In dai abun da ya shafi ɗa na ne, gaya mini kawai ina jinka"

"Wane irin a gaya miki kawai? Ai tana da hakkin sanin menene ita ma, tun da mijinta ne" yaya maryam tayi maganar a zuciye kamar ta kife iya da mari, saboda a zamanta ɗin nan ta gane lallai mariya tayi zaman haƙuri.

"Rashin kunya zaki yi mini?"

"Ba wani rashin kunya, maganar gaskiya ce ai. Ke mariya fito za ayi magana"

Jiki a sanyaye mariya ta fito cikin hijjabi, ta zo ta samu wuri ta zauna.

Suka sake gaisawa da mariya, yayi mata gaisuwa, Sagir yayi sallama ya shigo suka amsa masa, shima ya samu wuri ya zauna.

Rabi'u ya ce "Yauwwa, dama ni na yi masa magana tun da yana gida na ce masa ya shigo, Iya kamar yadda ki ka roƙi na tafi da bashir lagos, ya nemo arziki, to mun sauka Lagos lafiya".

Maryam ta ce "Amma ki ka ce mariya ce ta ce lallai sai ya tafi neman kuɗi"

Iya a fusace ta ce "Wai wace irin mara tarbiyya ce, ƙarya nake yi kenan, matsin da take yi masa ya sanya na yi masa magana, ya tafi da shi"

Maryam ta ce "Amma ai ba haka ki faɗa ba, ki ka saka yayanmu ya din ga ci mata mutunci a gaban mutane, wallahi ki ji tsoron Allah"

Rabi'u ya ce "Dan Allah ku yi haƙuri, ku saurare ni ku ji, bayan zuwanmu Lagos, mun fara sana'ar fawa da balarabe, kasancewar ba shi da account, yake tarawa a account ɗina, ya ce mini mariya ta sayar da kayanta, ta bashi kuɗin, amma shi a bashi ya karɓa, zai mayar mata da kuɗinta, dan haka ba laifi ya tara kuɗi, riba kawai kusan dubu sittin, uwar kuɗin sa da ribarsa da komai, kusan dubu ɗari biyu, basussuka da sauran su, duk na biya masa dubu ɗari da arba'in ne suka rage, mun taho gida da niyyar idan mun zo na cire kuɗin na bashi.

A hanya ƴan fashi suka tare mu, suka ƙwace mana kaya, da kayan tsarabar sa, har sun yi gaba ya tashi kan su ƙarasa barin wurin, shi ne suka harbe shi a ƙirjin sa, kan ya rasu ya ce: kar a raba gado, sai an biya mariya kuɗinta na kayanta, da sauran kuɗin da take bin sa" Ya kalli ummi da ke zaune tana bin su da kallo, sannan ya kalli mariya ya ce "Ya ce; ki kula masa da ummi, sannan ki yafe masa" yana faɗar haka mariya ta sanya tafukan hannunta ta sake fashewa da kuka.

"Ni bai ce maka komai a kai na ba?" Iya tayi maganar tana kallon rabi'u.

"Yana cikin maganar yayi kalmar shahada, ummin dai ya fi nanatawa"

Ta share hawayen da ke shirin zubo mata sannan ta ce "Ba wani zancen tana bin sa kuɗi, ni ban yi wannan maganar da shi ba, dan haka ka je ka ɗebo kuɗi ka kawo mini"

Maryam ta ce "A kawo miki kuɗi kiyi me da su? Ai kuɗi na magada ne, kuma sai mariya ta gama idda za a raba gado, saboda a tabattar da babu ciki".

"Ba dai ciki ba, shekara nawa rabonta da haihuwa, tun daga wannan mummunar yarinyar fuska kamar turotso, ba ta sake haihuwa ba, ba haihuwa take ba, dan haka ba ta da wani ciki. Wa ya sani ma ko balaraben baya haihuwa"

"To me ki ke nufi, ummin ba ƴar ku ba ce ba? Wai ke matar nan anya musulma ce ke? Kin yi imani da Allah kuwa?"

Sagir ya ce "Ke malama kar ki sake ki zagar mana uwa, na gaya miki" miƙewa maryam ta yi ta ce "Na zageta ɗin, ka yi abun da zaka yi. Azzalumar tsohuwa mara imani da tausayi, ashe ke ki ka ingiza ɗanki ya tafi neman kuɗi, amma kin saka yarinya a gaba, kina ta yi mata sharri, to wallahi dan kanki, ummi kuma idan ba ƴar ku ba ce, sai ki fita neman ubanta" nan da nan hayaniya ta ɓarke.

Mariya ta tashi ta ce "Dan Allah yaya maryam ki yi haƙuri, in dai kuɗi ne, ni babu bashi tsakanina da baban ummi, na rasa mijina balle abun duniya? Tumunin takabar ma na yafe, a bawa ummi hakkinta, in ɗau ƴa ta in koma in da na fito dan Allah" tayi maganar cikin matsanancin kuka, tare da jan hannun ummi ta tafi ɗaki.

Shi kansa rabi'u yayi mamakin rashin arzikin Iya, kawai ta ɗorawa mariya karan tsana. Ta sake jaddawa rabi'u ya kwaso kuɗi ya kawo mata, me balaraben ya mutu ya bari, da za a tsaya wani rabe-raben gado.

Maryam kuwa da kanta ta tafi tasha, ya bayar da saƙo zuwa gida, a kan lallai a cewa yayansu ya zo, akwai matsala.

Ko abinci ba a basu, maryam ita ta din ga cefane tana ciyar su.

Yayan su mariya ya dira a garin, Iya sai da ta yi mamakin ganinsa, maryam ta ja shi, ta ce masa akwai matsala cigaba da zaman mariya a gidan nan, tana kallon irin zaman da mariya take yi a gidan, nan ta kwashe komai ta gaya masa. Abun ba ƙaramin ɓata masa rai yayi ba, wani irin tausayin mariya ya kama shi, karon farko da ya ji zai goyi bayan ƙanwarsa, dan haka ya yanke cewa kawai zasu ɗauki mariya da ummi su tafi.

Dan haka ya je ya samu iya ya ce mata, washegari da safe zasu yi sammako su tafi Maiduguri, yaso su zauna su cigaba da gaisuwa, tayi takaba a ɗakin mijinta, amma wasu dalilai ya sanya sun yanke shawarar su tafi da ita gida kawai.

Iya ta ce "Shikenan babu laifi"

Mariya ta wani fannin ta ji daɗi zasu koma gida, wani ɓangaren wata irin kewar ɗakinta da mai ɗakik wato baban ummi, ta sake mamaye mata zuciya, har take jin anya ba za ta ce a bar ta a ɗakin nan ba, za ta cigaba da haƙuri da ita, kawai dan ya din ga gurbin da bashir yake dabdala.

A daren Maryam ta taimaka mata, ta harhaɗa kayanta, abun da zasu buƙata, Maryam ta ce daga baya azo a sayar da sauran kayanta, dan ba zasu iya dakon kaya zuwa Maiduguri ba.

Da sassafe maryam ta yi wa ummi wanka, suka yi wanka suka karya, ummi tana murna zasu tafi su bar gidan nan, tana fatan Allah ya sa idan sun je can babu yara masu tsokanar ta, ko dukanta.

Readers Also Read