Cutarwa complete by ayshercool - Chapter 33
Cutarwa complete by ayshercool Chapter 33: Cutarwa complete by ayshercool Chapter 33. Bin mami kawai yake yi da kallo, ta haƙiƙance ta din ga yi masa faɗa,…
3,345 words
Bin mami kawai yake yi da kallo, ta haƙiƙance ta din ga yi masa faɗa, shi dai yayi shiru bai ce mata komai ba, babban abun da ya bashi mamaki, irin huɗubar tsiyar da ta din ga yi masa, har ta yi ta gama bai ce mata komai ba, ya tashi ya tafi, yana mamakin halin mami da tunanin yaushe zata sauya. Ta kafa wa Hajiya ƙahon zuƙa, gashi dai hajiya ta tarar a gidan, amma tun tasowarsu mami ta kanainaye komai, gashi kishi take da hajiya kamar abokiyar gabarta, ta haɗe kai da yaranta mata duk sun saka Hajiya a gaba, dan ma duk an yi musu aure saura Nihal da ke karatu a ABU zariya, ba ta fiye zama a gidan ba, shikaɗai ne a ƴan ɗakinsu suke shiri da hajiya, dan shi har ga Allah bai ga aibun matar ba.
Ummi kuwa daga ita sai noor suka san da kayan nan, ummi ta ɓoye su a cikin kayanta, tuni ta yi wanka ta fara shafawa, sai dai fa kayan kwalliyar ne ba sa gabanta, ita turarukan da mayukan sun fi ɗaukar hankalinta.
Tayi ta kiran Raihan, daga baya tana ta shiga amma baya ɗagawa, tayi wankanta ta shafa mayukanta da turare, tana sake kiran wayarsa farida ta shigo ɗakin.
Gabanta ne ya ɗan faɗi, ummin na zaune a kan katifa, babu hijjabin nata na gado, ta saka skirt kawai da vest ga hijjabin a gefe, fatarta tana ta ƙyallin man da ta shafa, ga ƙamshi da ɗakin yake yi, ta saki gashin kanta ta sunkuyar da kai tana danna waya.
"Ke!" Ta daka mata tsawa, ummi ta ɗago da sauri, ta ja hijjabi ta saka.
"Dalla ki tashi ki wuce ki ɗora mana abincin dare" kallonta ummi take da mamaki, ɗazu taje tayi girkin ta koreta ta ce ba ta buƙata, yanzu kuma ta ce wai sai ta taso ta yi.
Da "To" ta amsa, ta tashi ta tafi kitchen.
Ga alamar an yi girki, amma duk an jibgeshi an ƙi ci, ta duba tukunya wata jallof aka yi ta shinkafa ta yi jagab kamar da shinkafar tuwo aka yi ta, ta kai bakinta ta ɗanɗana, da sauri ta fuzar an zabga uban gishiri da attaruhu, ga mai male-male a kai.
Hakan ba aikin kowa bane sai kausar, dan farida ta ce ummi ba zata sake shigar mata kitchen ba, ta ƙuduri aniyar ƙuntata mata, kausar ta yi girki ya ƙi ciyuwa.
A daren ta tuƙa tuwon semovita, ta sallami kowa sannan ta koma ɗaki.
Missed calls ɗin raihan ta tarar, da message "Call me when you are available"
Ba ɓata lokaci ta kira shi, ya ɗaga da sallama, ta amsa masa sannan ta ce "Ka kyauta raihan".
"Da na yi me?"
"Ka fi kowa sanin me ka yi mini ai, sannan ka kashe wayarka, daga baya ka ƙi ɗaga wayata, mun yi da kai muje mu yi sayayya, in saya maka abu sai ka sai abun da ya fi ƙarfin kuɗina, kuma ka dawo mini da kuɗina har da ƙari, kafi ƙarfin abun hannuna ko?"
"A'a ba haka bane ba, dan Allah kar ki yi mini wata fassara daban".
"Haka ne mana, ni bani da abun da zan baka ko? To ka zo ka karɓi kuɗin nan and am serious"
Ya gyara kwanciyarsa ya ce "Ni fa a cikin damuwa nake, kaina har ciwo yake yi, zaki ƙara mini damuwa"
Sai kuma ta nutsu "Wace irin damuwa kuma?"
"Ba maganar waya bace ummi, zan zo in sameki"
Ummi ta ce "Amma dai komai lafiya ko? Kar ka sa hankalina ya tashi fa, ka fara gaya mini"
"A'a ba abun tashin hankali bane ba, ki kwantar da hankalinki gobe in sha Allah zan zo"
"To Allah ya kawo ka lafiya, ko menene ka fawwala wa Allah ka ji?".
"In sha Allah, sai da safe" suka yi sallama, ta gyara shimfiɗarta, ta kwanta tana jin ta kamar wata ta daban, ƙamshin da yake tashi a jikinta sai nishaɗi take yi.
*** "Anty Rakiya, ai in gaya miki da ƙyar na yi barci daren jiya, tun da Alhaji ya faɗi wannan sanarwar da ƙyar na yi barci saboda murna, shi ɗan naki da yake ba kan gado ya cika ba, ya je ya samu uban wai ba ya so"
Rakiya ta ce "Kin ga raihan da rigima, Allah ya kawo dama yayi fatali da ita, kar ki kuskura ki yarda, ai ke lalacewar ƴaƴan can gaba ta kai ki Bilki".
Mami ta ce "Can gaba ma, kuma ƙoƙari zan yi duk mai yiwuwa in saka masa ido, dan tun a jiyan na kirawo shi na ƙare masa ta tas, yanzu abun da ya rage zan yi, dole in jajirce kar ruɗin kuɗi ya sanya shima ya fara biye-biye in yi biyu babu, shima ya lalace aure zan yi masa yaya, ai zai iya riƙewa"
Yaya rakiya ta ce "Ke bilki"
"Wallahi yaya rakiya, kar in je ya lalace mini in shiga uku, idan na yi masa aure, sai ma yafi mayar da hankali a kan kasuwancin uban, ya san yana da nauyi a kansa, duk da ba ma'abocin kula mata bane ba, amma kin san kuɗi, yadda ya samu wannan babban matsayin yakamata ace yana da cikar kamala ta aure kuma"
"Wannan gaskiya ne, to da mai zai hana ki haɗa shi da Safiyya, ayi ƴar gida kawai"
Mami ta ce "Wallahi kuwa, tuwona naina sai dai kin san shi, ba a iya masa, zan tuntuɓe shi da zancen idan har ya amince bani da matsala, amma dolensa yayi aure, hakan zai ƙara sanya ma'aikatan su girmama shi"
Suka cigaba da hira, Anty rakiya na ƙara ziga mami, da yadda za ta ɓullowa lamarin hajiya, ta kankane komai, da kuma muhimmancin aurar da raihan, mussman idan suka haɗa shi da Safiyya, dan ƙarafafa zumunci.
*** Ƙurii raihan ya yi wa ummi da ido, yadda take ta yi masa dariya.
"Ni ko? Ni zan gaya miki damuwata ki saka ni a gaba kina dariya, wasu abubuwan duk shawararki na bi, ƙarshe na rufta kuma kin zo kina dariya"
"To ai kai ɗin ne, yadda duk ka tashi hankalinka dole ka bawa mutum dariya. Ni da na zata wani abun da ba a so ne, da farko dai congratulations mai girma MD" hararta yayi yana kallon wayarsa.
"Attention" tayi maganar tana kallon sa.
Ya juyo yana kallonta shi ma "Ka saurareni, mu ajiye wasa da komai a gefe, zan yi magana a matsayina na yayarka ne" ya haɗa hannyensa biyu ya yi tagumi ya zuba mata ido.
Ummi ta ce "Ba bakina zaka kalla ba, ka saurareni da kyau, a matsyinka na mutum mai muhimmanci da ba zan manta da shi ba, ina fatan Allah ya haɗa ni da kai a aljanna a majalisar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam, kuma duk mai son ya tashi da annabi Sallallahu alaihi Wasallam sai ya kiyaye cin hakkin mutane. Kai mutumin kirki ne raihan, kar ka bari kuɗi da shugabanci su yi wasa da imaninka, ka ji tsoron Allah, ka ji tsoron Allah ka riƙe gaskiya da amana, kar ka cuci kowa kar ka ƙasƙantar da kowa, yayyenka ƙannenka ma'aikatanka da duk wani na ƙarƙshinka, ka kula da su bisa amana, kar ka yi son zuciya, kuma kar ka saka a ranka lallai sai kowa ya soka, kawai ka yi dan Allah. Abu na gaba, dole ka rage wannan jin kaɗe-kaɗen, ka mayar da hankali a kan azkar, da addu'a Ubangiji ya dafa maka yayi maka jagora, ya rabaka da dukkanin abun ƙi. Sannan idan Allah ya sa ka tashi yin aure, a yanzu ko a gaba, ka samo mace ta gari, wadda abun da ka ke da shi, ba zai rufe mata ido, ta ja ka ga hallaka ba, danmu mata mutane ne masu kanmu da yawa, tsaf sai wata ta yi yinƙurin mallakarka da dukiyarka ta rabaka da kowa, kar ka auri mace dan kai kana sonta kawai, ka duba makomar zuriyarka da ahalinka, kai mutumin kirki ne zaka iya babban mutum, ka yawaita saurara tarihin salihan bayi da yadda suka gudanar da rayuwarsu mussaman ta fuskar shugabanci, hakan zai ƙara sanya maka tsoron Allah, Allah ya tayaka riƙo Muhammad Raihan"
Jikinsa gaba ɗaya yayi sanyi, kalaman ummi maimakon su kwantar masa da hankali, tayar masa da hankali suka sake yi, tare da jin tamkar ta sake ɗaure shi da jijiyoyin jikinsa.
"Ummi wallahi an scared, ba zan iya ba, jagoranci abu ne mai wahala"
"Haba madubina, kai kake ƙoƙarin koya mini jajircewa, kai kuma in ga gazawarka? A'a kar ka watsawa Alhaji ƙasa a ido, zaka iya ka ji"
Yayi shiru bai ce komai ba.
Ta ce "Ka ce to mana"
"Ba zaki gane a yanayin da nake ba ne".
Ummi ta ce "Eh ba zan gane ba kam, karɓi kuɗinka" tayi maganar tana ajiye masa envelope ɗin da ya saka mata kuɗi a kan tebur.
"Ɗauke tun kan ki fusata ni, na yi miki rashin mutunci a gaban mutane"
Da mamaki ta kalleshi ta ce "Amma raihan idan ka yi mini haka ba ka kyauta mini ba, kuma ba zan ji daɗi ba" tayi maganar muryarta na rawa, dan tuno shi tayi ranar da suka je office ɗin su, da ya burkice sai da ya bata tsoro.
Ya tashi tsaye ya ce "Bari na ƙarasa office, idan na samu kaina zan zo mu tafi gida, idan kuma aiki yayi mini yawa zamu yi waya" ko amsarta bai jira ba, yayi waje ya barta da kuɗin.
Sai da ya fita manager ya ce "Ummi, me aka yi wa mutumin ne na ga yana cika yana batsewa?"
Ummi ta ce "Rigima kawai yake ji"
"Ai nima na ga alama, shiyasa ban kula shi ba".
Abu kamar wasa, aka yi ta shirin yi wa raihan liyafa, ya so ummi ta je, amma ta ce ba zata ba. Abokan hulɗar Alhaji Tahir wasu sun ga wautarsa, na bawa raihan jagoranci babban business irin wannan, matashi mai shekaru 23 dan ma yana da siffar kwarjini da girman jiki, amma kallo ɗaya zaka yi masa ka san yaro ne. Sai dai ko a kalamansa na godiya, da na kama aiki, sun tabattar wa da mutane ƙaraminsu babbansu ne, kamar yadda Alhaji Tahir yake faɗa, wanda wasu maganganun ummi ce ta gaya masa abun da zai ce, dan Alhaji Tahir ya sanar masa ya shirya kalaman da zai faɗa ranar liyafa.
Aka yi taro aka watse, ya turawa ummi hotunan abun da aka yi, ta ɗauki hotonsa guda ɗaya ya sha coat, ƙuruciyarsa ta fito sosai, sai dai ya tsare gida babu fara'a, ta saka shi a status da caption na "Allah ya tayaka riƙo ƙanina, MD Muhammad Raihan"
Ta kai awanni biyu da yin status ɗin, da ta buɗe what's app ta tarar da saƙonni, na tambayar waye shi, ciki har da yaya magaji, babban wanda ya fi bata mamaki shi ne message ɗin maryam, tun da raihan ya haɗa su, suka yi magana maryam ba ta sake kulata ba, idan ta yi mata magana ma, sai ta ga tana shareta, dan haka ita ma ta daina kulata, sai yanzu taga message ɗin ta, wai ya aka yi ki ka sani?.
Ummi ta yi mata reply da "Shi ya gaya mini".
Maryam ta ce "A ina ku ka haɗu ya gaya miki?"
"Muna gaisawa idan zai wuce ta wurin da muke aiki ne".
Ta yi reply da "Dan Allah ki cire shi, ba kowa ya sani ba, kar azo hakan ya bashi matsala" Ummi ta daɗe tana jujjuya message ɗin, ita mutum nawa ne ma a what's app ɗin nata. Ta ga ita kanta maryam ɗin, ta saka hotunan sun fi goma, kodayeke wata kusan ta fi wata, dan haka ummi ta goge.
Tamkar jira yake ta goge, ya ce "Meyasa ki ka goge status ɗinki?"
"Bakomai".
"Akwai dalili mana, saboda Maryam ko?".
Abun ya bata mamaki, kan ta yi magana ya sake turo wani saƙon ya ce "Muna tare take nuna wa mami status ɗin naki ai, ita take saka miki data da zata ce ki cire abu kuma ki cire? Ina ruwanta, ko haifarki tayi da zata bani umarni ki bi? Akwai mutane a wurin ne ya san na ƙyale maganar, ƙarewa gobe in Allah ya kaimu hira za ayi da ni a wani gidan jarida. Dan Allah ki daina bari ana raina mini ke bana so"
Karanta saƙon nasa ta din ga yi, tana ƙoƙarin bawa saƙon damar yin tasiri a zuciyarta, amma ta kasa.
"Dan Allah ki sake duba wani hoton, ki ɗora ni ki yi mini addu'a, tun da ba ki je taron ba Please".
"Yanzu ka gama cewa a daina sani abu in yi, ai ba kai ka saka mini data ba" ta tura masa tana dariya.
Emojin dariya ya tura mata ya ce "Ta kaina zaki fara kenan? Ni ki ka raina ko?"
"Kai ka mayar da ni haka ai, ina salihata ka koya mini surutu".
"Dama can kin iya abinki"
"To na ji, sai da safe bacci nake ji"
" ya kaimu" ya rufe data ya ajiye wayar, ya lumshe ido yana tuno moments ɗin su tare, ba zaka taɓa cewa ummi na magana ba, dama ce kawai ba ta samu ba, amma tana da baki sosai".
*** Alhaji Tahir kallon mami yake yi, bayan ta gama kora masa bayanin abun da take so.
Ta kalleshi ta ce "Wai ya ka yi shiru kana kallona ne?"
"To ai abun ne na ji shi banbarakwai, guda nawa raihan ɗin nawa yake zaki ce ayi masa aure yanzu? Daga ɗora masa wannan ɗawainiyar sai kuma ki ce ayi masa aure?".
"To ai shine cikar kamalarsa, ya samu matsayi ya zamana yana da iyali, dole zai nutsu ya mayar da hankalinsa, ko so ka ke na saki jiki shima ya lalace? Ni dai dan Allah ka taimaka ka amince"
Alhaji ya ce "Ai ni bani da damuwa, in dai ya amince yana so shikenan, Allah ya sanya alkhairi"
"Yauwwa, dan Allah ka tayani shawo kansa, ka san ko budurwa ba shi da ita, ko zancen na yi masa sai ya sha kunu, dan Allah ka tayani lallaɓa shi, ko da Safiyyar Anty rakiya a haɗa shi"
Ya kashingiɗa ya ce "Wannan ba hurumina bane, kin san takura wa ɗa ba ya cikin tsarina, ku tattauna kawai"
Tayi ajiyar zuciya ta jinjina kai.
Mami ta din ga fargabar tunkarar raihan da maganar, haka nan ta dake da safe ya shiga gaisheta zai fita office, ta ɗaukko masa zancen, aikuwa ya haɗe rai, ya ce "Dan mami ki daina wannan zancen, abokaina kowa ba wanda yayi aure sai ni, kawai na tsufa da wuri, kuma matar ma ki rasa wa zaki zaɓar mini sai wannan marar kunyar, ni ba zan auri matar da ba zan iya tanƙwarata ba, yarinyar da bata da kunya, ni bana so".
"Raihan, cikar kamalar mutum iyali, ace kana da wannan matsayin baka da aure, ai sai a rainaka, kuma ganin kai baka da ko budurwa ya sanya na zaɓa maka, aure yana ƙarawa mutum kamala"
Ya ce "To mami na ji, amma dan Allah ki ƙyaleni, idan lokaci yayi zan yi miki magana zan yi auren, amma ni yanzu wallahi ban yi niyyar yin auren ba, kuma da kaina zan samo budurwa da zan aura, ummi ta ce in nutsu in samo mace ta gari".
Cikin mamaki mami ta ce "Wacece ummi kuma?"
Ya miƙe tsaye ya ce "Kar ki damu mami, ni dai ki bar wannan maganar"
"Wallahi ba zan barta ba, dole ka yi aure dan ba zan zuba ido ka lalace a banza ba, ko wata ta lallaɓa ta lalataka ba, wato ni nake yi maka kallon salihi, har mai baka shawara ce da kai a waje?".
"You should thank God, shawarar kirki take bani, ita ta saita ni a hanyar da na ci jarrabawar Alhaji" daga haka ya fice ya bar falon.
Abu kamar wasa, raihan har ba ya son shiga sashin mami, dan ta fara hura masa wuta, shi ko zancen ba ya so.
Yanzu Ummi haɗuwa da raihan yana bata wahala, saboda yadda aiki ya saka shi a gaba, ba shi da cikakken lokacin kansa. Yau ya kirata a waya ya ce mata zasu fita, zai zo ya ɗau excuse a wurin manager.
Da azahar ya zo ya sameta, lokacin ta gama aiki, tana ta tsokanarsa MD, yayi mata shiru yana hararta.
Ta bashi wayarta ta ce "Raihan, dan Allah ka buɗe mini Instagram"
"Me zaki yi da shi?"
Ta ce "Kallon abubuwa zan din ga yi"
"Wai wannan wayar taki, da ke da ita waye ya girmi wani? kalli yadda ta ci ƙaniyarta"
"To sai ka bani taka ai" tayi maganar tana hararsa.
Ya ce "Kin samu, ciro mini layukana ki ɗauka"
"Ni da wasa nake yi, ka buɗe mini dan Allah na kasa buɗewa".
Raihan ya ce "Ke Instagram ba zai hau wannan dattijuwar wayar taki ba, ai na ce ki ɗau tawa, ba abun da zaki ce na baki na hanaki"
"Da wasa nake yi maka, ka buɗe mini" tayi maganar tana miƙa masa wayar tana ɓata fuska kamar ƴar yaye.
"Da gaske na bar miki wayata ummi, kawo wayar taki mu yi exchange na layukan".
"So kake ace na fara sata ko? Me nake sayarwa da zan mallaki wannan wayar?"
Ya ce "Sai ki ce ke ƙawar MD ce"
"A'a nice ma MDn, tun da ba zaka buɗe mini ba shikenan" ya karɓi wayar ta ta yana dubawa, ya ce.
"Tashi muje mu dawo da wuri"
"Ina zamu je?"
"Budurwata zan sai wa wasu kaya, mu je ki tayani saya, za ta yi ki a jiki, bana son na sai mata wanda zai yi mata yawa".
Ta harare shi ta ce "Kuma saboda ka raina ni, da ni zaka gwada? Daga baka muƙami ka fara kule-kule, guda nawa ka ke da ka fara yin ƴan mata" wani irin kallo yayi mata, tayi shiru, ta zata maganar da tayi ne, ta ɓata masa rai.
Shi kuwa hoton da ya gani ne ya bashi mamaki, hotonta da noor, gashin kanta kamar aljana.
Sai dai yayi tunanin ko sakawa tayi, amma ina ummi take da wata wayewar saka gashi.
"Tashi mu je" ta tashi tabi bayansa, a ranta tana fatan Allah ya sa ba haushi ya ji ba.
Ita kanta mamakin kanta take yi, yadda take bin raihan duk in da ya ce suje, ba tare da musu ba, yanzu ta daina fargabar shiga motarsa, kodayeke zuciya na son mai kyautata mata, kuma bai taɓa yi mata wani abu na rashin ɗa'a ba.
Suna tafe a motar, ta ciro leda a jakarta ta ce "Gashi, dama ina ta jira mu haɗu, kuma saura ka ce baka so, sai ka je gida zaka duba"
Ya amsa mata da "To babbar yaya"
Wani ƙaton shagon sayar da kayan sawa suka je, suka shiga raihan suka gaisa da matar da ke shagon.
Ya nuna mata ummi ya ce "Yauwwa hajjaju, ban san size ɗin da take sakawa ba, amma ga wata mun zo tare da ita, ki bata ta gwada, idan dai ta yi mata dai-dai, ita ma za ta yi mata.
Matar ta ce "Masha Allah, bisimillah, muje to ka zaɓa sai ta gwada".
Tarin abaya ne a wurin da suka je, kala-kala na kece raini.
Ya kalli ummi ya ce "Zaɓo ɗaya wadda za ta yi mata kyau sosai".
"To ai ban san ya take ba, ko wanda ta fi so ba, fara ce ko baƙa?"
"Ina ruwanki da kalarta? to black beauty ce"
Ta tsaya ta kalleshi ta riƙe ƙugu ta ce "Daga baka office, ka fara kashewa ƴan mata kuɗi ko? Alhaji ya sani?"
Raihan shima ya riƙe ƙugu ya ce "Yau nake ganin ikon Allah, ke ina ruwanki ne? Wai ce miki aka yi ɗan zaman banza ne ni? Ɗauki muje akwai in da zamu je".
Wata blueblack ta ɗaukko mai matuƙar kyau, matar ta nunawa ummi in da zata shiga ta gwada rigar.
Tsayawa ta yi a gaban mudubin ɗakin, tana ƙarewa kanta kallo sanye da rigar, yau dai sau ɗaya a tarihin rayuwarta, ta saka doguwar rigar abaya da take matuƙar burgeta.