Kenza eBookz

Cutarwa complete by ayshercool - Chapter 34

Cutarwa complete by ayshercool - Chapter 34

Cutarwa complete by ayshercool Chapter 34: Cutarwa complete by ayshercool Chapter 34. Ta riƙe ɗan kwalin rigar a hannunta, ta zubawa mudubin ido, ta tafi…

3,316 words

Ta riƙe ɗan kwalin rigar a hannunta, ta zubawa mudubin ido, ta tafi tunani, ta zubawa mudubin ido, tana hango rayuwarta ta baya a ciki, cike da tozarci da ƙasƙanci, da rashin galihu kamar mara amfani, shigowar raihan rayuwarta ya bata lokacinsa, duk hankalinsa saboda kawai ya sakaya farinciki. A ranta take addu'a 'Allah idan ina da rabon yin aure a duniya, Allah ka kawo mini miji na yi aure, kar na yi aure na kasa rabuwa da raihan' saboda sosai take jin sa a jikinta.

Ummi bata san adadin daɗewar da ta yi a tsaye ba, saboda gaba ɗaya ta bar cikin hayyacinta.

Raihan gajiya yayi da zaman jiran ummi, kawai ya ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin amma shiru, kawai ya tura ƙofar da sallama.

Kamar gunki ya ganta a tsaye hannunta riƙe da ɗan kwalin rigar, hawaye ya wanke mata fuska.

Sandarewa yayi a tsaye, ta saka siririn ribbon ta ɗaure gashin, ta sake shi har tsakiyar bayanta.

Ganin raihan ta cikin mudubi daf da ita ne, ya sanya ta dawo hayyacinta a razane, kokowar rufe kanta ta fara yi.

A hankali ya saka hannu ya ɗaure zaren rigar ta baya.

Ya saka hannu ya kamo gashin da ya sauka a bayanta, tsigar jikinta ce ta tashi, ta waiwayo da sauri, ƙare mata kallo yake yi. Rigar ta yi cif a jikinta, dirarriyar mace ce ta gaske, baƙar fatarta kawai mutane suke kallo, amma daga ƙirjinta zuwa ƙugunta komai dai-dai jikinta, kasa daina kallonta yayi, karo na farko kuma da yau ta kalli raihan a wani abu daban ba ƙaninta da take yawan faɗa ba.

(Team a bamu daga farko, ku yi Allah ku din ga dubawa a watpad Please 🙏)

Ayshercool 08081012143 What's app only *CUTARWA!*

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

P28

FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK.

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

Masu neman free books ɗina, da free pages duk akwai a kan watpad account ɗina. Irinsu Abduljalal Wata kissar sai mata Wuta a masaƙa Cutarwa Ƙanwar maza Gaba da gabanta Aƙidata Ruɗin ƙuruciya

Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata. 08081012143.

And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link. https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ayshercool.

PAID ADVERT!.

Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi. Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku

Oll types of Turaran wuta Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra Kulakcha Dilke da kalta Kayan Garan jiki Muna turara Kaya Kujerar garan jiki Kannada Madarorin turare masu kamshi Man garan gashi Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921

*TALLA!TALLA!TALLA!* *INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*. *BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU* *MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA*

BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.

28

Ajiyar zuciya ya sauke, ya sanya hannunsa a aljihunsa, ya ciro wayarsa.

Ya shammaceta ya fara ɗaukar ta hoto ta cikin mudubi.

Haɗe rai ta yi ta ce "Meyasa zaka shigo mini ba izini? Ni ka fita"

"Na yi knocking, na kuma yi sallama, duk baki amsa ba, kin bar ni a tsaye ina ta jiranki, kin shigo kina kuka, idan ma dan in bar miki rigir ne ki ke kuka, ba zan baki ba, fito mu tafi"

Ba tare da ta saki fuska ba, ta ce "Ni ka fita na cire rigar"

Ya basar ya ce "Ki batta a jikinki, ki zo mu tafi".

"Dan Allah ka fita na cire" tayi maganar a raunane tana ɓoye jikinta.

A hankali ya taka ya nufi hanyar fita, ya sake waiwayo wa, tana tsaye jiran ya fita ta canza kayan.

Ya fita ya koma reception.

Ba ƙaramar kunya ce ta kama ta ba, ganin da yayi mata a haka, gashi dai doguwar riga ce, amma ta kasa manta irin kallon da yayi mata, da ya sanya ta shiga wani yanayi da ba ta san menene ba, gaba ɗaya sai ya canza mata, kamar ba raihan ɗin da ta sani ba.

Ta mayar da hijjabinta, ta fito da rigar a hannunta, matar ta kallesu ta ce "Rigar ta yi?"

Ya ce "Eh, bamu wasu kalolin a haɗa da wannan, su zama biyar sai takalmi uku da zai shiga da kowacce" komai da ummi aka gwada, kuma ba ta kawo komai a ranta ba.

Ɗan nazarinta ya din ga yi, ko fushi take yi da shi, amma ya lura kawai ta tsorata ne, ta kasa sakin jiki ma tayi masa magana, dan abu ne mawuyaci ka ga ummi ta yi fushi, dan zai iya cewa bai taɓa ganin tayi ba, idan ma abu bai yi mata daɗi ba, sai dai ta yi shiru.

Suna tafe a hanya ya cigaba da yi mata hira, kamar bai ga komai ba, yana koɗa kyan da kayan suka yi.

Sai dai gaba ɗaya shima jikinsa yayi sanyi, basarwa kawai yake yi.

Wani restaurant suka je, yayi reserving VIP, aka kawo musu abinci kala-kala, amma ummi ta ce ba za ta ci ba, ya gama kawai su tafi ita hankalinta yayi gida.

"Amma mussman saboda baki je walimar nan ba na shirya mana wannan"

"Sai ka ce wani film, ni ka yi sauri mu tafi, kar na je gida na kasa kare kaina".

"Da na san zaki watsa mini ƙasa a ido, da ban kashe kuɗina ba, i did all this because of you"

Ta ɗan kalleshi ta ce "Ni ban taɓa cin abinci a waje ba, dan Allah ka yi haƙuri"

Raihan ya ce "Zan fita na baki wuri ki ci, amma idan ki ka yi mini haka ba zan ji daɗi ba".

Ƙarshe dan kar ya ji haushi, da ƙyar ta cakala ta ci, suka tafi gida.

A hanya yake ta ce mata tayi ƙoƙarin rarraba CV ɗin ta, ko Allah zai sanya ta samu wani aikin da ya fi wanda take yi. Ta ce masa zata jarraba yin hakan.

Raihan ya dage sai ya mayar da ummi ƴar gayu, ta hanyar kaita wurare da zasu ɗebe mata kewa, ba tare da ƙetare iyakar addini ba.

A ɗan fitar nan da ummi suke yi, take ganin mata kala-kala, masu dressing kala-kala, ba ta sani ba ko rashin shiga cikin mutane ne ya sanya ita duk ba ta iya wannan abubuwan ba, hatta ɗaurin ɗan kwalin da ta kan gani a kan mata yana burgeta, amma ita ba yi take yi ba, daga aikin gida sai makaranta ba ta da wani hope balle tayi tunanin wata kwalliya.

Da Raihan yaje gida ya duba ledar da ummi ta bashi, sabon agogo ne kar, da links sai littafin azkar babba, da carbi counter.

Ta yi rubutu kamar haka "Allah ya taya riƙo mai girma MD, wannan ce gudunmuwata, ban san me kake buƙata ba, amma ina fatan ba zaka raina kyautar yayarka ba, Ummi"

Ya yi murmushi a hankali ya ce 'Kin rama kenan, a taƙaice kin dawo mini da kuɗina'

Ya kirata a waya, sai dai wayar a kashe.

Ya kashingiɗa yana tuno ummin, mussaman ɗazu da ta saka doguwar rigar abaya, tayi wani irin kwwarjini da kyau, daga cikin abun da ya ɗau hankalinsa dogon gashin ta har tsakiyar bayanta, ya fara tunanin anya ummi ba ta haɗa dangi da wani ahali na yankin ƙasashen ƙetare ba? Idonta da gashinta, sun nuna hakan.

"You are beautiful fa ummi" ya faɗa a fili ba tare da ya shirya yin hakan ba.

Dubu talatin ɗin nan da ya bata, dubu biyu ce tayi saura, dan sai da ta saya wa kawunta turare, ta saya wa Abdul, sai ƴar ɗakinta wato noor, har da su farida, amma kausar ta yatsuna fuska ta ce Allah ya kiyaye ta shafa wannan abun kamar ƴar bori, suka bar ta da abun ta.

Duk da abun da suka yi mata, ummi ta ji daɗin murna da addu'a da dr. Yayi mata, hakazalika Abdul ma yayi mata addu'a sosai, mutuniyarta kuwa kasa zama wuri ɗaya tayi, dan ƴar tsana ta saya mata.

Ummi ta yi mamakin yadda aka yi kuɗin ma suka isheta, ba ta taɓa tunanin haka yi wa mutum kyauta yake da daɗi ba, ayi ta yi maka addu'a.

Kwanaki biyu da fitar su ita da raihan, tana ɗakinta tana tilawa Abdul yayi sallama, ta kaste karatun tare da amsa masa. Ya miƙa mata ledar hannunsa, ta karɓa tana kallonsa bakinta fal tambaya. Kan tayi masa tambayar ya ce "Wani guy ne muka haɗu a waje ya ce na baki, wani ɗan dogo mai haske" gaban ummi ya faɗi, ta san ba wani bane face raihan. Abdul bai sake yi mata wani bayanin ba, ya fita daga ɗakin. Jikinta na rawa ta hau duba kayan, dogwayen riguna nan ne da suka sayo, har takalman da komai.

Da sauri ta tashi ta leƙa ƙofar ɗakin, ta tabattar babu kowa, me raihan yake nufi ne? Wannan kayan idan aka tanbayeta ta ce a ina ta samu?

Layinsa ta fara kira, ya ɗaga a nutsensa tare da amsa sallamar da tayi masa.

"Raihan, shine ka bawa Yaya Abdul wannan kayan ya kawo mini, idan aka tuhume ni a ina na samu me zance? Kar ka janyo mini matsala fa"

"Kar ki ji komai ki ce ni na saya miki, saboda na fuskanci kina so, budurwa ce ke ba tsohuwa ba, dan haka mace sai da kwalliya, ni ina da yayye da ƙanne mata, duk in da mace take tana buƙatar kulawa, a kan buƙatunta na yau da kullum, kar ki ji komai yayata, ki yi kwalliyarki dai-dai da addinin musulunci, Allah ya kawo mana abokin rayuwa na gari" maganar sa ta ƙarshe, da yayi addu'ar sai ya ji wani abu mara daɗi a ƙasan zuciyarsa.

Ya kashe wayarsa, ummi ta bi kayan da kallo, ina ma zata iya amfani da kayan nan, ta tashi ta kulle ƙofar ɗakin, ta ɗauki kayan tana gwadawa ɗaya bayan ɗaya, karo na farko da ta ɗauki jambakin da yasa mata wancan karon, ta ƙara tisa shi a kan jajayen laɓɓanta, ta saka kwalli a idonta.

Ta ƙurawa kanta ido a gaban mudubin, ta din ga juyi a tsakiyar ɗakin, wai yau ita ce ta saka wannan kayan masu tsada, ta kalli takalmin ƙafarta mai tsini, ta din ga kaiwa tana komowa a ɗakin.

"Allah ya ƙaro maka arziki mara yankewa, ya yalwata maka duniya da lahira" hakanan ta ji ina ma ya ga kayan a jikinta, har da janbaki ta saka yau, abun da yake so ya mayar da ita ƴar gayu.

***

Gaba ɗaya farida ta kasa sukuni, tun da mijin inteesar ya ce zai ƙara aure, suke yawon neman asiri, amma babu abun da ya sauya, ga azabar takura daga dangin miji, da gori na cewa ita juya ce. Da ya ce kan ya ƙara auren zai canza mata gida da furnitures, amma babarsa ta ce bata yadda ba, da wanne zai ji, kuɗin da zai kashe yayi wani auren, ko kuma wanda zai kashewa juya, da ma tana haihuwa ne da sauƙi. Gefe ga kausar dr. Ya ƙara hura mata wuta, a kan lallai ko tayi karatu, ko sai ta fitar da miji. Farida kuma ta yi alwashin, sai ummi ta koma ƙauye ta bar mata gida, ko kuma ta fitar da miji itama, dan ba zai yiwu ya takura wa ƴar ta ita kaɗai ba.

Ga noor wani irin rashin ji take yi, ba ta shakkar farida ko kaɗan, tsagera ce ta gaske, ummi ce kawai sai dr. Suke iya tanƙwarata, dan ko Abdul sai ta ga dama take jin maganar sa, dan ta ce faridan ba ta sonta, su inteesar kawai take so, ita kanta ummi tsagerancin da noor take yi da ƙanan shekarun nan, yana bata tsoro, amma babu yadda ta iya, tana yi mata addu'a, tare da yi mata fatan shiriya.

Gashi farida ta ɗora laifin hakan a kan ummi, wai ita take zigata, take hurewa ƴar ta kunne.

Kamar a baya da duk abun da za ayi ummin ba magana take yi ba, haka yanzun ma, ba wani abun take cewa ba, duk abun da za ayi sai dai tayi shiru.

Babban abun da ya ɗaga mata hankali, bai wuce kawu Yahaya da ya je gagarawa, ya dawo da katin bikin Yaya magaji ba, kuma ya tabbatar mata da ita za su je bikin nan, kuma a yadda yayi maganar umarni ne kawai ba wai neman yardarta ba.

Ta amsa masa da to, amma ƙasan zuciyarta wani irin lugude take yi da fargaba, da fatan Allah yasa ba da sun je za a baro ta a can ba, dan kuwa farida ta ƙara matsa lamba sosai da sosai, ta addabi ummi da gorin rashin aure da kuma ƙara tabattar mata da barin gidan.

Gefe guda kuma, abokin shawarar ta ta, ya zama very busy, wataran sai su wuni ma basu yi waya ba, ga tafiye-tafiye da suka sako shi a gaba, saboda importing na kayansu, nan da nan kuwa ya fara rama, duk ranar da zai dawo gari, sai ya yi wa ummi waya tayi masa abinci, ya aika a karɓo masa ba zai ci na gida ba.

Alhaji Tahir ya sha suka da caccaka, a kan yadda ya ɗauki ragamar babban kasuwanci kamar wannan, ya danƙawa raiha, a matsayinsa na ƙaramin yaro, Alhaji Tahir ya toshe kunnensa, dan kuwa bai ji zai canza ra'ayi ba.

Abunka da mata da miji, mami tayi ta lallaɓa Alhaji, har ya amince da maganarta a kan raihan yayi aure, amma ya ce ba ruwansa da zaɓa wa raihan ɗin matar aure, balle auren yaƙi daɗi ace laifinsa ne.

Shima Alhajin yayi iya ƙoƙarin sa wurin fahimtar da raihan muhimmancin ace yana da iyali yanzu, tun da ya samu matsayi.

Raihan ya ce "Wai Alhaji da wanne zan ji?, tsufa zan yi da wuri, ka manta nauyin da ka ɗora mini?"

Alhaji ya ce "Ni meyasa ban tsufa da wurin ba?akwai riba a cikin yin aure da wurin babban mutum, aure ba takura bane ba, kwanciyar hankali ne da nutsuwar zuciya ka yi tunani a kai".

Raihan ya ce "To Alhaji zan yi, zan yi shawara da hajiya"

Alhaji ya ce "Ba maminka ba?".

"A'a Hajiya"

"Ɗan gidan Hajiya, ni ba zan bayar da shawara ba sai Hajiya kenan? Ai shikenan babban mutum".

Gidansu ummi kuwa yau gaba ɗaya jikinta babu daɗi, ta gaji sosai da sosai, dan farida baƙi tayi, kan ummi sai ciwo yake yi, kamar za ta yi zazzaɓi da ƙyar ta lallaɓa ta yi aikace-aikace.

Sai da ta jera kwana biyu ba ta zuwa aiki, ta sanarwa manager ba ta da lafiya ne, haka islamiyya ma, kwana biyu zazzaɓi ya sakata a gaba da matsanancin ciwon kai da na ciki.

Dama Ummi ba ta saka ran wani ya bata kulawa ba, ita da noor kawai suke jinyar, noor ta yi wanke-wanke da abun da zata iya, a daddafe ummi take aikin gidan, farida ta lura da hakan, amma ko a jikinta dama da dr. Yana nan ne ya fuskanta zai kaita asibiti.

Raihan kuma ba sa iya waya, sai ta what's app, dan kuwa baya ƙasar gaba ɗaya, dan haka bai san halin da take ciki ba.

Tun ƙarfe shida ummi ta ga farida sun ɗauki mota da ita da kausar sun fice, Abdul kuwa aiki yaƙi samuwa, dan haka a wani kamfanin sarrafa taki, dr. Ya samar masa aiki, shima farida ta din ga kushewa, da nuna ɗanta ya fi ƙarfin wannan, amma Abdul ya ce yana so zai yi.

Ganin da noor tayi ummi babu lafiya sosai, ya sanya ta karya da buredi ta tafi tahfeez, ummi ta din ga burgima a ɗakin ta, ga amai kuma cikin ta babu komai.

Wayarta tayi vibrating ya fi sau shida, da ƙyar ta ɗaga ta yi sallama.

"Baccin safe ki ke yau kenan, ko islamiyyar baki je ba? Na shigo gari jiya da daddare, abincinki nake son ci, kuma in ganki".

Cikin ƙarfin hali ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri, bana jin daɗi amma zuwa yamma in sha Allah idan na gama zan kira ka".

Bai san lokacin da ya tashi tsaye ba ya ce "Ummi kamar fa haki ki ke yi, kina Asibiti ne?".

"A'a ina gida ne, zan warware in sha Allah" tayi maganar da ƙyar kanta na sarawa.

"Bani 20minutes gani nan" kan ta sake magana ya kaste kiran, ya fita da sauri.

Ummi ba ta sake sanin in da kanta yake ba ma, sai da ta ji ana buga ƙofar ɗakinta.

A hankali ta ce "Waye?".

"Mai gadi ne, kin yi baƙo ne, yana sallama"

Ummi ta ce "To" maimakon ta tashi, sai ta cigaba da bacci na rashin lafiya, a ƙalla maigadin ya zo sau uku, kan ta iya fitowa.

Hankalin raihan ba ƙaramin tashi yayi ba, da ya ga ummi, idanuwanta duk sun yi waje. Tana ƙarasawa ta nemi wuri zata zauna a ƙasa, ya hanata hakan ya saka ta shiga motar. Tun da ya ja motar yake faɗa a kan wasa da lafiyarta, oho ba ta ma san takamaiman zahiri ne ko mafarki ba saboda zafin zazzaɓi.

Ba a samo kan ummi ba, sai bayan ta sha ruwa roba biyu, sai dai a halin da take ciki, hankalinta yana gida, kar wani ya dawo a tarar ba ta yi girkin rana ba.

Likita ya din ga yi mata tambayoyi cikin harshen Ingilishi, dan ba ya jin hausa, da ƙyar take iya amsawa saboda ciwo, kuma hankalinta yayi gida.

Ya ce "Akwai ciki ne?" Sai da ummi ta kalli likitan, amma ta kasa magana.

Raihan ya ce "Babu".

"Ka tabattar? When last ta yi period?"

Maimakon raihan ya ce ba ta da aure, sai ya kalleta ya ce "Yana tambayar ki".

Likitan ya ce "Kai baka sani ba ne? Are you not couples? Na ji ka ce babu ciki"

Raihan ya wani gyara tsayuwa ya ce "Ai da yake bana gari, shiyasa ban riƙe ba, ummi ki gaya masa" ta sunkuyar da kai ta yi shiru, kamar ta buɗe ido ta ga ta ɓace, raihan ya gama da ita gaba ɗaya.

Raihan ya ce "She can't recall, but she's not pregnant"

Aka yi wa ummi teses, malaria da typhoid sun yi mata mummunan kamu.

Likita ya ce a bari ta kwana ɗaya a asibitin, ummi ta ce ba ta san zance ba, ta sha faɗa a wurin raihan kan rashin kula da lafiyar ta, tare da yi mata kashedin saura ta je gidan a sakata aiki tayi. Ji yake tamkar ya samu wani kauwamammen wuri, ya ajiye ummi ya din ga kula da ita, kulawa ta musamman.

Ta so ace zata iya abun da raihan ya ce, taƙi yin aikin gidan, dan a galabaice take, amma da cin mutuncin da za ayi mata, gara aikin gidan.

Tayi ta yi wa Allah godiya, har suka dawo bayan azahar su farida ba su dawo ba, dama noor sai la'asar zata dawo.

Haka ta lallaɓa take aikin, lokaci-lokaci sai raihan ya kira ummi, ya tambaye ta ya take ji a jikinta, gaba ɗaya ya kasa nutsuwa hankalinsa ya ƙi kwanciya, dan babban fatansa ace a kwance take ko ruwa za ta sha, a ɗaukko a bata.

Readers Also Read