Kenza eBookz

Cutarwa complete by ayshercool - Chapter 35

Cutarwa complete by ayshercool - Chapter 35

Cutarwa complete by ayshercool Chapter 35: Cutarwa complete by ayshercool Chapter 35. Babban abun da ya bawa ummi mamaki, bai wuce yadda headmastern…

3,303 words

Babban abun da ya bawa ummi mamaki, bai wuce yadda headmastern makarantar islamiyyar su ya zo dubata ba, har da kawo kayan dubiya, headmaster yana daga cikin mutanen da su kan hantari ummi, mussman idan ta je a makare, gashi ita kuɗin makaranta take biya, wurin ɗaukar nata karatun, ita kuma koyarwar da take yi, ko sisi basa bata, dan raihan har mita yake yi, a kan hakan ya ce yakamata ko ba yawa a din ga biyanta.

Amma ga mamakinta sai ga headmastern ya zo dubata, ba ta kawo komai a ranta ba, tayi masa godiya ya tafi.

Saboda rigimar raihan, ummi ta lallaɓa ta koma aiki, dan kuwa idan ba ta yi wasa ba, a sintirin da yake yi, sai an san da alaƙarsu, alaƙar da ba ta san ta yaya za ta yi bayaninta ba.

Har wurin aikin yake bin ta, ya tabbattar ta ci abinci ta sha magani.

Ta sanar masa da batun zuwa gagarawa, da yadda take cikin damuwar hakan, kar idan ta je a riƙeta a can.

Raihan ya ce "Ki kwantar da hankalinki, babu abun da zai faru sai ikon Allah, kuma babu wanda zai rabaki da garin nan, abun da nake so da ke, ki yi iya ƙoƙarinki ki sake samo information a kan mama idan kin je, zan san ƙoƙarin da zan yi a kan hakan, da wallahi suka riƙe ki a garin nan, ba abun da zai hana ni binki"

Ɗan buɗe baki ta yi tana kallon sa, da gaske har cikin zuciyarsa yayi maganar.

"Raihan wai ranar da na yi aure, yaya zaka yi ne?"

"Yaya zamu yi dai? A ƴan uwanmu zan samo miki miji nagari, ni kin san kuwa mami ta sakani a gaba, wai tun da Alhaji ya bani ragamar kasuwancin nan, wai sai na yi aure"

Ummi tayi dariya ta ce "Daɗina da mami hangen nesa, wallahi kuma da gaskiyarta"

Ya girgiza kai ya ce "Ba zaki gane bane yanzu haka kawai ganina ki ke yi, bana son yawan takura miki, amma sai kin tayani da addu'a, akwai ƙalubale sosai a harkar kasuwancin nan, kuma kamar yadda ki ka faɗa, akwai buƙatar yadda ki ka gaya mini, ina buƙatar mace ta gari to assist me, wallahi ummi ban taɓa budurwa ba, kuma bana son auren haɗi, ni ba zan auri matar da bana so ba"

Ummi ta yi dariya ta ce "Za a sha ƙiriniya, amaryar ka za ta sha fama da ƙuruciya"

Kallonta yayi ya ce "Kin rainani da yawa fa, idan na fita kin ga yadda nake tsare gida kuwa a waje, a man of 24yrs, ki ke cewa za a sha ƙuruciya"

Ummi ta waro masa idanunta ta ce "24 kuma, ka ji tsoron Allah raihan, yaushe ka kai 24yrs kuma?"

Ya ce "Wallahi na cika 24yrs"

Da suka yi lissafi, watanni goma sha huɗu ummi ta bashi.

Ya ce "Da na san ba wani girmata ki ka yi ba, ba zan bari ki raina ni ba, ashe ma sa'ata ce na ma fa fiki girma ummi, daga yanzu ma ni ne yayanki yaya zaki din ga ce mini"

Ummi ta ce "To meye a ciki Han? Ai duk in da namiji yake jagora ne, mai girma MD, sai dai ba a canzawa tuwo suna, ni yayarka ce"

Yayi dariya yana shafa sajensa, ya na bin ta da kallo, ya kasa gane a wane bugire ma ya ajiye ummin ne a yanzu.

"Me ka ke kallo ne?"

"Your eyes, masha Allah i like them, ina son idanunki"

Ummi ta rausayar da kai ta ce "Idan ka faɗi haka kana tuna mini da babana, idan na ce masa baba wai idona irin na akuya ne da mage? Sai ya ce A'a, idonki mai kyau ne, ina son idonki ummina"

Raihan ya ce "Allah sarki, Allah ya jiƙan baba da rahama"

"Amin Yaya Han, ina godiya sosai da sosai"

Yayi murmushi ya ce "Han sai ka ce sunan ƴan china, amma duk yadda ki ka faɗa zan amsa, ki kula da kanki sosai a garin idan kin je, zamu din ga waya har ku dawo"

Ummi ta ce "To, in sha Allah"

Ummi na son nunawa raihan hotunan da ta yi da rigunan nan a wayarta, amma ta kasa, shi kuma bai takurata da tambayar bai taɓa ganin ta saka kayan da ya bata ba.

Ummi ta lura kamar babu jituwa tsakanin dr. Da farida tun wancan karon da ya koma aiki, har wannan dawowar tasa, sai dai kasancewar ummi ba huruminta bane ba, ya sanya ta cigaba da sabgoginta.

Ranar tafiyarsu gagarawa na ƙaratowa, adadin tashin hankalinta, da fargaba na ƙaruwa, sai dai ta na ta addu'a a kan Allah ya kare faruwar dukkan wani abun ƙi.

Ta ɗauki ɗaya daga cikin dogwayen rigunan wurin raihan, da abun da ba a rasa ba, ta haɗa kayan da zata yi tafiyar da su.

Dr. Ya ce har da noor zasu tafi, noor ta din ga murna, tana jin daɗi.

Suna tafe a hanya, adadin fargaba da tashin hankalinta, yana ƙaruwa, tana tuna irin azabar da ta sha a gagarawa, ta din ga fatan ina ma har ta je ta dawo, ba zata haɗu da wasu mutanen ba, dan ko ambatar sunansu na sanyata cikin damuwa.

Kwantsin yaran gidan ne suka firfito, suna shelar ga kawu Yahaya ya zo, yaran da galibi duk ba ta san su ba, dan da yawansu bayan ta baro garin aka haife su.

Kallon gidan ummi take, zata iya cewa wannan gidan shi ne kurku mafi azaba a tarihin rayuwarta.

Da yawa yaran basu san ummi ba, dan haka suka din ga bin ta da kallo.

A tsakar gida sashen iya, mata nata hada-hadar shirin biki, sallamarta ce ta janyo hankalin matan.

Wanda suka santa, suka din ga zuzuta girman da tayi, ta ɗaga kai ta kalli ɗakinsu, ɗakin mai ɗauke da ɗumbin tarihi, alamu ya nuna akwai mutane a ɗakin, amma ba ta san suwaye a ɗakin ba.

Ɗakin Iya ta nufa, ta tarar da Iya zaune a tsakar ɗakin ta, tana ta bayar da umarni.

Saroro ta bi ummi da kallo, cikin ƙarfin hali ummi tayi murmushi tana gaida Iya.

"Yau Allah ya kawo ki wurin mayu kenan, wanda za su cinyeki?" Ummi ta yi shiru tana sunkuyar da kai.

Noor dai ta kame tana kallon kowa ɗaya bayan ɗaya.

Dr. Ya shigo shima yana ta gaisawa da mutane, da ya isa ɗakin iya, ko gaisawa ba su yi ba, ta fara masifar ya bar ummi ta balage ba aure, kodayeke dama ya za ayi ta auru, ai dama tun da tun farko taƙi amincewa da rufin asirin aure, ya goya mata baya, haka zata riƙe a gida ba aure.

Aikuwa kawu yahaya ya haɗe rai ya ce "Iya dan Allah ya isa haka, haba ummin guda nawa take? Ke ba ki yi farincikin ganinta tayi ilimi, a nutse a kame ba, ni na zaci wannan abubuwan duk sun wuce tun a baya?".

Ummi ta sha mamakin yadda Iya ba ta canza ba, tsawon wannan lokacin.

Tun a daren yaya magaji ya zo wurin ummi, sun daɗe suna hira, tare da murnar ganin sauyin da ummi ta samu, ya din ga gaya mata irin yadda abubuwa suke ta kwaɓewa a cikin dangin nasu.

Abubuwan duk babu daɗin ji, mussaman gidan Idris, yarinyar su ta gaba da alfatiha, ƙalubalen da take fuskanta ya sanya ta fara fanɗarewa ita ma.

Al'amarin bai yi wa ummi daɗi ba, wanda jahilci ke taka muhimmiyar rawa a rayuwar mutanen gidan.

Washegari ɗaurin aure, bayan ummi da noor sun yi wanka sun shirya, ta ja noor suka fita gidansu na'ima, amma ta tarar maman na'ima ta rasu, ƙannenta duk sun yi aure.

Doguwar riga ummi ta saka ta wurin raihan, sai dai tana jin ta kamar ba ita ba, saboda jin ta take a takure a cikin kayan, dan ma rigar isashiya ce, sai dai fa ta zama a bar kallo a cikin gidan, duk in da tabi sai a kalleta.

Iya ta din ga nuna wa mutane ummi, ga ƴar wurin bashir, da Idiris ya aura taƙi zama, ta bi kawu yahaya gashi haryanzu ta gama balagewa ta riƙa ba aure shi yanzu yana da yara biyar.

Idiris kuwa tun da ya ga ummi kamar maye, saboda azabar kallo, sai dai ga mamakinsa ummi tayi masa kwarjinin da ko magana ya kasa yi mata, gashi dai ba wani abun ta canza ba, kamaninta suna nan, sai dai ta girma ta cika, kai ba ka ce tana fuskantar ƙalubale a in da take ba.

Ko in da Idris yake bata kalla ba, balle ya sanya ran za ta gaishe shi.

Su Alhassan ma duk sun girma, da su auwwalu, sai dai babu wani cigaba su ma, dan kuwa auwwalu ma ya zama ɗan shaye-shaye sosai da sosai, dan har prison yayi, babu sana'ar kirki ya zama criminal.

Alhassan ma babu sana'ar kirki, sai kamasho da ƴan buge-buge.

Raihan kuwa yana ta kiran ummi a waya, da jin ko komai lafiya ƙalau.

Ana dawowa daga ɗaurin aure, kawu yahaya ya ce zasu koma gida, sai dai ummi ta sha surutun mutanen gidan na rashin aure.

Suna tafe kawu yahaya yana yi wa ummi nasiha, a kan ta kwantar da hankalinta a kan rashin aure, saboda lokaci ne, shi aure ba gaggawa ba samun nagartaccen miji da gidan aure mai cike da farinciki shi ne abun fata.

Ita dai ummi ganin sun taho daga gagarawa ya fi komai faranta mata rai.

Tashin hankali ba a saka masa rana, bayan su ummi sun sauka a kano gida, ummi ta tarar da ɗakinta a garƙame an saka masa mukulli.

Falo ummi ta tafi, ta samu Farida ta ce "Anty ke ki ka kulle ɗakina?"

"Eh ni na kulle, saboda ba gidan ubanki bane ba? Dan mun riga mun yi da shi ba zaki dawo mini gida ba"

Saroro ummi ta yi tana kallon fareeda, dr. Ya fito yana faɗin "Wai farida bamu gama wannan maganar ba? To wallahi idan ki ka cigaba da matsawa, sai dai ke ki bar gidan, kema ki koma naku gidan"

Farida ta duba wajen dining, ta ɗaukko kaya ta watso su tsakar falon ta ce "Sai ka tambayeta a ina ta samu wannan kayan? Wallahi dole ta bar mini gida, kan ta lalace ta lalata mini yara"

Ummi tabi kayan da kallo, kayan mayukanta ne, na wurin raihan da kayan sawa.

"Wannan kayan sun fi ƙarfin na dubu ɗari, sai ka tuhumeta a ina ta samu, kuma gidanka ba zan bar shi ba, dan na ci gida".....

Ayshercool 08081012143 [4/20, 7:20 PM] Authoresses: *CUTARWA!*

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

P29

FOLLOW ME ON WATPAD VIA THIS LINK.

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

Masu neman free books ɗina, da free pages duk akwai a kan watpad account ɗina. Irinsu Abduljalal Wata kissar sai mata Wuta a masaƙa Cutarwa Ƙanwar maza Gaba da gabanta Aƙidata Ruɗin ƙuruciya

Zaku iya samun paid pages ɗin a Arewabooks @ayshercool7724. Ko ku tuntuɓe ni kai tsaye ta lambar wayata. 08081012143.

And also don't forget to subscribe my YouTube channel via this link. https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ayshercool.

PAID ADVERT!.

Ina uwargida, amare, har ma da ƴan mata masu burin zama gaba gaba, wurin yin amfani da turarruka na kece raini, masu daɗi da ƙamshi. Mafaka gidan ƙamshi da ke, Ring Rord western bypass kanawa park sun kawo muku

Oll types of Turaran wuta Sandal Halut Irik Difur Gab Gab Kajiji Habil Nabak Humra Kulakcha Dilke da kalta Kayan Garan jiki Muna turara Kaya Kujerar garan jiki Kannada Madarorin turare masu kamshi Man garan gashi Indai kamshine kuzo MAFAKA GIDAN KHAMSHI karshene Sai Sai kin zamo abin kwatanche Ku nememu a wan nan no 08065728702 08025453921

*TALLA!TALLA!TALLA!* *INA MANYAN MATA, UWARGIDA DA AMARE KAI HAR DA ƳAN MATA MASU SON KECE RAINI, DA SHIGA TA ALFARMA, MUN SHIRYA TSAF DOMIN KUWA MUN TANADAR MUKU LAGOS LACE MANYA DA ƘANANA, DAIDAI ALJIHUNNKU BA TARE DA TSAUWALAWA BA* *HAKAZALIKA INA MASU SON ƘAWATA GIDAJENSU DA HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN, UNIQUE DA SAI AN KALLA AN SAKE KALLO, MUN TANADAR MUKU HAƊAƊƊUN KAYAN KITCHEN NA ALFARMA NA GIDA DA NA WAJE*. *BAMU TSAYA IYA NAN BA, DOMIN KUWA MUNA SAYAR HAƊAƊƊUN SUPPLEMENT NA GYARAN JIKI, MAYAR DA TSOHUWA YARINYA, GYARAN JIKI DOMIN DAUWWAMAR DA HASKEN TAURARUWARKU A WURIN MAZAJEN KU, TARE DA KECE RAINI A CIKIN SA'ANINKU* *MUN SHIRYA TSAF DOMIN SHARE MUKU HAWAYNKU, DOMIN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU A KAN LAMBAR WAYARMU 08166117985, SAYEN NA GARI MAYAR DA KUƊI GIDA*

BRIGHT PENS A SHIRYE MUKE, WURIN KARƁAR TALLACE TALLACENKU CIKIN FARASHI MAI SAUƘI.

29

Wata irin tsuma jikin ummi ya fara yi, dan ba ta san ta ina zata fara bayani ba, bata taɓa tunanin farida za ta shiga ɗakinta, tayi mata bincike ba.

Dr. Ya bi kayan ɗaya bayan ɗaya da kallo.

Cikin haƙilo farida ta ce "Sai ta yi maka bayanin in da take samun wannan kayan, idan ba wani mugun abun take aikatawa na rashin gaskiya ba"

Tsulum noor ta tsoma baki ta ce "Kai, yaya raihan ne fa ya saya ya bata, ko yaya ummi?"

Kamar gunki ummi ta sake sandarewa, dan ba ta san ta aka yi noor ta riƙe sunan raihan haka ba ma.

Dr. Ya durƙusa ya tsince kayan, ya mayar cikin ledarsu, ya miƙe tsaye ya kalli farida ya ce "Bani mukullin da ki ka rufe mata ɗaki"

"Ban gane ba, me ka ke nufi?"

"Abun da ki ka gani, ba budurwa ba ce ba? Ke abubuwan da ake kawowa kausar cikin gidan nan zama ki ke ki tuhume ta?"

"Amma tsakani da Allah ka taɓa ganin wani yayi sallama da ita da sunan yana sonta, da zai saya mata wannan kayan masu tsada?"

Ya wuce ɗakin farida, tabi bayansa tana cigaba da masifa, ya ɗaukko mukullaye, ya dubi ummi ya ce "Mu je"

Tabi bayansa hawaye na zuba daga idonta, ya buɗe ɗakin nata, duk an hargitsa shi.

Ya ajiye mata kayan, ya kalleta ya ce "Mamana, na yarda da ke ɗari bisa ɗari, na san ba zaki aikata wani abu na Allah wadai ko a bayan idona ba, goya miki baya baya nufin, ki aikata abun da bai dace ba, ba zan matsaki a kan lallai sai na san me ki ke ciki ba, ni uba ne, kuma malamin makaranta, na san yadda zan tafiyar da tarbiyar yarana. Kin mai munzalin da bin diddigin rayuwarki, ba shi ne mafita ba, amma dai ina sake yi miki tuni, da ki ji tsoron Allah, ki kuma kare mutuncinki, amma har ga Allah ni bana zargin ki, ki goge hawayenki ki samu ki huta, ni ban gaji da zamanki da mu a gidan nan ba, saniya ba ta taɓa gazawa da ƙahonta, dan haka ki kwantar da hankalinki komai mai wucewa ne, kuma in sha Allah zaki sha mamakin abokin rayuwar da Allah zai zaɓa miki, ke dai ki cigaba da tsare mutuncinki"

Ummi ta jinjina masa kai, ya fita daga ɗakin, ta zauna a hankali tana kallon kayan, tayi shiru tana nazari, idan har zargi zai shiga zuciyar dr. Game da ita, gara ta nemi duk mai yiwuwa ta rabu da raihan. Tabbas kaya ne masu tsada da ta cancanci a tuhumeta a kansu, da kawu ya matsa ta ina zata fara yi masa bayanin wannan alaƙar ta su, da ba kowane mai hankali ne zai sanyata a gurbi mai ma'ana ba.

Ya zama dole ta nesanta kanta da raihan, duk da abu ne mai wahala a wurinta, daga haɗuwarsu zuwa yanzu, ya gina wani tarihi da ba zai rushe ba a rayuwarta, raihan na daga cikin mutane masu muhimmanci da ba zata taɓa mantawa da su ba, zuciyarta ta saba sa shi, ta shaƙu da shi, ya bata ƙarfin gwiwa daban-daban, ya sanya ta jin ita cikakkiyar mace ce ɗan Adam da zata iya gogayya da kowa, tabbas raihan ya cancanci a kira shi ƙaraminsu babbansu, domin kuwa a manyan ba kowa ne za a samu da irin qualities ɗin sa ba.

A hankali ta tattare kayan, ta gyara ɗakinta, ta rama sallolin da suka tsere mata, ta cigaba da tunani.

Ta ɗaukko wayarta ta duba, missed call ɗin sa duk a wayar, har da saƙo yana tambayarta meyafaru ba ta ɗaga wayarsa?. Ta kashe wayar gaba ɗaya ta ajiye, tana son fara koyawa kanta janye wa raihan.

Ta yinƙura ta fito daga ɗakinta, amma ta jiyo hayaniyar kawu da farida, kuma duk a kanta, jiki a sanyaye ta koma ɗakinta, da tana da wurin zuwa da zata bar wa farida gidanta, ko kawu ya samu sassauci daga wulaƙancin da farida ke yi masa.

*** Anty Rakiya ta cigaba da matsa lamba, da ƙarfafa mami, a kan lallai a haɗa auren nan na zumunci, ita kuma mami ta cigaba da matsawa raihan, tare da ziga Alhaji a kan lallai a takura raihan yayi aure.

Abun ya fara damun raihan, dan haka ya samu hajiya da maganar, Hajiya ta ce "Babban mutum, menene a ciki dan ka yi aure, gaskiyar maminka ne shi ne cikar kamalarka ai".

"To hajiya sai in yi aure su yaya ba su yi ba, kuma nema ake fa a sakani na auri wadda ba na so, ni bana son yarinyar nan"

"Raihan, dan ka riga su Salim aure babu laifi a ciki, bujirewa umarnin mahaifiyarka ba shi da fa'ida, ko ba ka auri wadda take so ba, ka yi ƙoƙari kai ka kawo musu wadda ka ke so"

Yayi shiru yana nazari, sannan ya kalli hajiya ya ce "Shikenan hajiya na gode sosai da sosai"

Ya tashi ya fita, yana nazarin maganar Hajiya.

Gefe guda kuma yana mamakin kasa samun ummi a waya, har ta what's app, ya fara tunanin ko dai wani abun ya sameta ne.

Yaje wurin aikinsu Ummi, ya tambayi mai yi musu shara, ya ce masa ba ta je ba.

Ita ma ummi a lokacin da take ƙoƙarin ƙauracewa kiran raihan, headmastern su ya kunno kai, sai ya din ga kiranta a waya, wai su gaisa, wannan satin har da bata dubu biyu wai ta hau mota, saboda ɗawainiya da take yi da ɗalibansu.

Hankalinta ba a kan wannan yake ba, kamar ta fi raihan azabtuwa da ƙauracewar da ta yi masa, gashi pressure cikin gidansu, ta ƙara yawa, dan kuwa farida kullum cikin masifa da tashin hankali take a cikin gidan nan.

Babu tsammani dr. Ya samu ummi ya ce mata "Mamana, wani mutum ya zo wurina, ya ce mini yana sonki, kuma babu daɗewa yake son ayi auren, na bashi damar ya zo ku gana, sai dai ba ina nufin lallai sai kin aure shi bane ba, bana son yi masa karambani, ganin babban mutum ne, amma duk yadda ku ka yi sai ki gaya mini"

Ummi ta amsa masa da to ne, amma ta shiga cikin fargaba da zullumi, tare da tunanin, waye wannan? Kai tsaye ya tafi wurin dr.?

Abun yayi ta bata mamaki, sai dai sam ba ta ɗokin abun, domin kuwa bayan saka wayarta a flight mode, sai ta koma tana duba messages ɗin raihan.

Gaba ɗaya ummi ta manta da dr. Ya ce za ta yi baƙo, saƙon raihan na ƙarshe ya tsaye mata a rai.

"Ummi na bincika kina lafiya, amma you are avoiding me, ban sani ba ko nayi miki laifi ne, idan na yi miki laifi ne dan Allah ki yi haƙuri ki yafe mini, ina cikin damuwa sosai wallaahi, ban zaci shaƙuwarmu ta kai in shiga damuwa haka ba, dan Allah ki yi mini reply ummi, zan tafi italy gobe in Allah ya kaimu da asuba, dan Allah ki yi mini magana" Ajiye wayar ummi tayi, idonta na cika da hawaye, "Ban kyauta maka ba raihan, amma yanzu ko na yi maka bayani ba zaka gane ba, buyagi zaka yi mini" tayi maganar a hankali, tana sake kallon wayarta.

"Yaya ummi, wai baƙonki ya zo" noor tayi maganar ba tare da ko sallama ta yi ba.

Readers Also Read