Da'iman complete hausa novel - Chapter 10
Da'iman complete hausa novel Chapter 10: Da'iman complete hausa novel Chapter 10. Ciki suka shiga anty saadah ta hada kaya Fannah da innah suka kama nazli…
3,368 words
Ciki suka shiga anty saadah ta hada kaya Fannah da innah suka kama nazli 'din yana biye dasu abaya ji yake kamar suna ja masa ita da qarfi.
Har sunkai mota yace, Ku bani 3min naje nagano my little soldier.
Arazane suka kallosa duka atare tashin hnkali qarara bayyane afuskarsu amma babu wanda ya iya samun bakin magana.
Ganin da gaske can yayi yasa fannah tayi saurin sakin nazli tareda 'dan sa qafa ta take mata qafa.
Ahhhhhh ta fada da 'dan qarfi aiko kaman yanda ta tsammata a rude ya juyo tareda dawowa yana riqo hannunta.
Ajiyar xuciya fannah tasaki tana riqo nazli 'din cikin damuwa tafara fadin, Oh am really sorry sister inlw bansan ya akayi na takaki ba sorry....
Girgiza mata kai nazli mamakinta na qaruwa da abubuwan datake gani.
Kamar kuwa yanda suka tsammata fasa zuwan yayi ya kama hannunta yashigar da ita motar ya zagaya shima yashiga.
Kallonsu fannah dasuka tsaya yayi fannah tayi saurin sakin fuska tana cewa, No b ku tafi ni zanzo dasu inna amotana.
Innah ya kalla itama ta qaqalo fara'a tana cewa, Eh zamuxo a tata motar tunda dai duka 'dayane.
Murmushi yasaki tareda jan motar sukabar asibitin.
Tuqi yake ahankali yana 'dan satar kallon gefenta jin kansa yake cikin wani irin tsantsar farin ciki mara misaltuwa.
Itadai kanta a qasa yake sbd ita tambayoyine fal aranta.
Suna isa gidan batayi mamakiba dan ganin sbd tasan sunada tarin dukiyar dazasuyi goma irinsa a kanon.
Yanayin parking a harabar gidan ya fito ya zagayo gefenta ya bude qofar. Rintse idanunta tayi sbd ganin abinda yake shirinyi.
'Daukarta yayi cak kamar baby da qafa ya tura qofar motar yayi ciki da ita.
Kallon fuskarta yake yanajin nishadi da shauqinta. Idanunta a rintse suke harya fara hawa stairs da ita ya isa 'dakinsa bai tsaya ko inaba sai a bedroom 'dinsa ya kwantar da ita a lafiyayyen gadonsa.
Saurin kifewa tayi sbd kallon dayake jifarta dashi yana firgitata sbd tasan ma'anar kallon tun awancen lokacin.
Yasoyin wani abu sai ya rarrashi xuciyarsa ya fasa ya fada toilet yana sakin wani shu'umin murmushi.
Ruwan 'dumi sosai ya hada tareda turaren wanka mai sanyin qamshi.
Tun acan ya tu'be ya fito 'daure da towel a qugunsa.
Har alokacin idanunta arufe suke Sai baiyi wani babban motsiba saijin tayi ya 'dagata.
Toilet ya direta tareda zame hijab 'din jikinta yana kallon fuskarta dake qara masa sonta.
Qanqame jikinta tayi hawaye nabin fuskarta sbd jin qoqarinsa nason rabata da kayan jikinta. Jin sautin kukanta yafara fita ahankali yasa ya tsaya da cire mata kayan.
'Dagowa yayi tareda tallabo fiskarta yana kallon hawayen dake gangarowa.
Kan bakinta ya maida kallonsa yana matsar da fuskarsa zuwa nata ahankali.
Jin numfashinsa na matsowa ga fiskarta yasa ta bude idanunta wanda hakan yayi daidai da saukar bakinsa cikin nata.
Kissing 'dinta yake yana lumshe idanu alamar ba qaramin dadin hakan yakejiba.
Jikintane ya mutu gabaki 'daya har qarafunta suka gaza mata Ya tallafota jikinsa yana cigaba da tsotsan bakinta.
Shagalar datayi yasa harya cire mata kaya bata saniba saidaya cirata cak yana sakar mata murmushi ta lura Tsabar kunya kawai saita sakar masa kuka.
Cikin bathtub ya ajeta tayi saurin qanqamesa sbd ganin zai koma seti da ita dan yariqa kallonta dakyau.
Murmushi yasaki yana ra'da mata, Why? Bakyason naga savior 'dina dakyau ne?
Cusa kai tayi a qirjinsa tana qoqarin sakin wani sabon kukan Yayi saurin tallafota yana cewa, No no pls dnt nadaina okey.
Daqyar yasamu sukayo wankan ya na'dota a towel suka fito A kan dressin chair ya ajeta tareda bu'de wardrope ya 'dauko mata wata fitinanniyar sleeping dress ya aje mata. Mai yashafa tareda turare yasaka farar jallabiyarsa ya fice da 'dan sauri sbd sallar isha da aka tayar.
Mai tashafa jiki asanyaye kafin ta 'dan saka turare ta 'daga rigar daya aje mata tasaka Ai da sauri ta duqe duk da ita kadaice adakin. Doguwar hijab 'din sallah daya aje mata ta dauka ta zura ta tada sallah.
Tana gama addua saigasa yashigo yace ta tashi suyi nafila Batada baki ko qarfin musu dan haka saita tashi sukayi nafilarsu suka gama tareda addua.
Kamota jikinsa yayi ya zame hijabinta Wasu yawu ya hade da qyar amma afili saiya miqe tareda miqar da ita yayi palo da ita.
Suna shiga nafisa na aje tray 'din ta juyo. Saurin 6oyewa bayansa nazli tayi sbd rigarta batada maraba da tsirara.
Nafisa na ganin haka itama tayi saurin ficewa tana sinne kai.
Zaunar da ita yayi ya bata gasashen nama dayasa nafisa ta gasa mata mai kyau. Daqyar taci yabata fruit taci kadan suka koma 'daki.
Tsuru tayi bakin gadon dan duk tsoronsa yacikata dan ita sam kunyarsa takeji ba kamar meer 'dinta nadaba da batajin kunyarsa sbd sun saba. Shikuwa kallin sabon mutum take masa.
Ahankali ya jawota jikinsa ya haye tsakiyar gadon da ita yana shinshinarta.
Rungumeta yayi ajikinsa sosai yanason suyi bacci amma tudun qirjinta dayakeji a qirjinsa ya hana hakan.
Wuyanta ya fara lalubowa yana shafawa har xuwa qirjinta Numfashintane yafara gudu da sauri kafin ta ankara ya hayo kanta yana kissing 'din bakinta zuwa qirjinta dasuka tsole masa ido.
Kuka tafara sbd ganin yanda ya fara murzarta tun anan tagane wannan karon zataji maza sbd ga dukkan alama zaiyi jarumta ba kamar meer 'dinta na dah ba.
Yawo take adakinta tana tunanin lallaima ace kowa nacan hnkali tashe sukuma maqiyanta datayi dansu sunacan kwance sunajin dadinsu.
Fitowa tayi ta nufi hanyar xuwa samansa tana cewa, Wlh saina fada muku dan hnkalinku ya tashi ku koma cikin baqar damuwar danakeson ganinku ciki kafin na kashe shegen yaron gaba 'daya kowama ya huta.
MUCH LUV MAMN ABBAH FOR UR CONCERN💋💋💋💋
🌕🌕👉mamuh geee
🌕⚜DA'IMAN⚜🌕
Na MAMUH GEEE
☆dedicated to☆ Husna bbchoudiallo
217→218
Duk yanda taso daurewa saidata dirzi kuka sosai kamar ranta zai fita sbd baqar wuyar data sha a gurinsa.
Tsananin Shauqin sonta ya hana sam yaji tausayinta dan bayama hayyacinsa.
Qanqameta yayi yana sauke numfashi da ajiyar zuciya Ita kuwa kukanta na fita ahankali.
Qwanqwasa qofa sukaji atare gabansu ya dan fadi sbd tunanin ko waye a lokacin.
Jame jikinsa yayi bayan ya manna mata kiss a goshi ya fa'da toilet.
Yana fitowa ya saka kayan baccinsa farare qal ya nufi palo dan har lokacin buga qofar akeyi.
Bude qofar yayi tareda 'dan sake fuska yana mata kallon mamaki.
Bayansa ta 'dan kalla taga nazli bata biyosaba Ba haka taso ba taso suna tare tafada musu kota samu zuciyar 'dayansu ta buga su mutu kota huta.
Ganin ya kafeta da ido yana watsa mata kallon mamaki sai kawai ta fara matso qwalla murya na rawa tafara fadin,
Tameer na kasa bacci sbd banji 'daya daga cikinku yacemin anga koda gawar waleed 'din ne.
Gyara tsayuwa yayi dakyau yana kallonta kafin ya 'dan sauke ajiyar zuciya ya kamo hannunta har tsaiyar palonsa ya zaunar da ita a kujera yace,
Mummy ki daina hawayen haka ya isa sbd ba gaske bane koma meyene yasamu waleed Mafarkine kawai okey? Waleed yanan qlau.
Hararar gefen ido ta jefa masa wata sabuwar tsanarsa da qiyayyarsa na qaruwa a ranta Ta qara share wasu muna fukan hawaye tana cewa, Wlh ba wani mafarki danake tuni alh yakirani yafadamun an rasa waleed 'din kum.....
Dad fa kikace? Yama za'ayi ace 'dana ya 6ata ace bansani ba.
Wayarta dake hannunta ta 'daga ta dannawa alh kira tareda saka handsfree.
Ringin biyu ya 'daga kafin yace kamai ta rigasa da cewa, Alh angansa ni duk hnklina yakasa kwanciya.
Murya a karye yace, Haryanxu ba'a gansaba amma an kira anceman antsinci gawar wani yaro to muna jiran gawar ta iso mugani Ya qarasa zancen nasa muryarsa na qara karyewa kamar yana kuka.
Saurin datse kiran tayi tana miqewa sbd ganin yanda ya zabura ya miqe a cikin wani irin yanayi.
Motsu sukaji daga bayansu suka juya atare Nazli suka gani a tsaye sanyeda farar jallabiyarsa ta sallah hawaye tuni sun mata shabe shabe a fiska.
A ki'dime yayo kanta da sauri duk da shima yana cikin tashin hnklin.
Luuu tayi baya yayi sauri tarota jikinsa yana qoqarin lallashinta amma ina idanunta nakan haj xeenat ta kafeta dasu ko motsawa batayi jikinta har wani rawa yake.
Mutuniyarku na ganin hakan ta fice da sauri har tana tuntube
Saurin datakene jikinta na rawa yasa qafarta 'daya ta juye aikuwa nan tafara gangarowa daga stairs 'din kanta na buguwa tako ina.
Ihunta yasa nafisa fitowa da sauri aiko nan ta tarar da maseefa da tashin hankali dan tana isowa harta gama gangarowa ta iso qasa Da sauri tayo kanta sbd ganin jini a bakin hajiyar.
Itama raxana tayi da ganin jinin dake fita abakin nata tana furzowa suka ga haqoranta uku a qasa Ai a haukace tasaki wani sabon ihun tana miqewa nanma qafa tace batasan xancenba da qurqunta takai 'dakinta ta fada toilet tanata birgima a qasa da ihu.
A cikin daren suka shirya suka fito sai asibitin.
Kai tsaye 'dakin da aka kwantar da waleed 'din suka nufa gabansu na faduwa hnkli tashe.
Zaune suke jigum jigum kowa idanu sun fa'da sbd tashin hnkli sai kukan fannah dake tashe ahankali, Hj nurat ma idadunta harsun kumbura tsabar kukan data sha abinta sbd 6atan jikanta. Inna ma tanan zaunce ta rafka nata tagumi sai dad datafi kowa shiga damuwa Ga securities bakin qofar dakin. Anty saadah kuwa ta tafi gida sbd zazzabi da mijinta ke 'dan fama dashi.
🌕🌕👉mamuh geee 🌕⚜DA'IMAN⚜🌕
Na MAMUH GEEE
☆dedicated to☆ Husnah bbchoudiallo
219~220
A razane dukkansu suka miqe ganin tameer da nazli 'din daidai wannan lokacin. Kallon dad yake kamar zai rusa kuka Dad yayi saurin kamosa jikinsa yana cewa, Im very sorry tameer, I'm sorry i couldnt take gud care an protct my grndson, I.... No dad dnt say dat, Waleed is my son, ur grndson, we will find him insha allah.
Nazli kuwa ganinfa da gaske waleed 'dinta ya 'bata ba wasa akeyiba yasa ta saki wani irin kuka mai qarfi tana kiran sunansa.
Kukanta ya masifar 'daga hnkalinsu dan anyi rarrshin duniya takasa dainawa Muryarta harta shaqe batako fita sbd kukan,
Ummi tajawota jikinta tana rarrshinta amma ina Gabaki 'daya yanxu itama suke tausayi kamar me.
'Dunguma sukayi suka dawo gida A palo suka zauna kamar gidan mutuwa kowa kagani fuska a kumbure.
Ummi,dad da inna suke lallashinta tana jikin ummin sbd kukanta harya daina fita. Ahankli wani wahalallen bacci ya 'dauketa sai alokacin suka 'dan samu nutsuwa kafin ta farka kuma.
A daren nan kuwa tameer nacan tareda jamian tsaro dashi aka je neman waleed 'din.
Sunanan zaune basu ankaraba akayi kiran sallar asuba. Miqewa sukayidan zuwa bada farali su roqi allah saukin alamura Dad ma shigewa yayi dan 'dauro alwala yayi masallacin.
A palo suka barta kwance dan kadasu tadata.
Koda dad yashigo gidan daidai nan tameer yadawo shima suka shiga tare babu wani lbr me 'dadi.
Yana ganinta kwance a palon dukta rame a dare 'daya sbd tashin hnkli.
'Daukarta yayi ya haye sama da ita xuwa 'dakinsu. Akan bed ya ajeta tareda lullu6eta da lallausan bargonsa Ya fa'da toilet yayo wanka ya saka farar shirt da farin wando 3qtr.
Zama yayi bakin gadon cikeda damuwa yafara tunanin inda 'dansa ya shiga kokuma aka sace masa shi.
Bude idanuwa tayi ahankali sbd mugun nauyin dasukayi mata ga kumburi.
Ganinsa yasa ta zabura xaune tareda saukowa gadon taxo gabansa. Fa'dawa qirjinsa tayi tana sakin wani sabon siririn kuka.
Meer waleed 'dina, Waleed 'dina yanacan yana kukan nemana, Meer kayimin alqawarin zaka dawomun da waleed 'dina, Meer waleed 'dina Meer meer waleed Me.....
Girgixata yayi da qarfi tareda rungumeta jikinsa yana qanqameta idanunwansa na tara hawayen tausayinta.
Daqyar ya samu ta 'dan nutsu yakaita toileta yayo mata wanka tayi sallah ya sanya mata doguwar riga blue mara nauyi.
Palo ya sauko hannunsa na riqeda nata.
Dukkanin mutan gidan na palo zaune cikin jimami.
Xaunar da ita yayi bayan sun gaida kowa.
Tea yasa nafisa ta hado mata mai kauri Juyin duniya kowa yayi taqi sha saima sabon kuka data saka musu.
'Dingisawa take kamar gurguwa bakinta ya 'dan kumbura sbd haqoranta dasuka futa.
Palon tashigo tana qarajin wata sabuwar qiyayyarsu sbd sune sanadin data rasa haqoranta.
Kallo kowa kebinta dashi cikeda mamakin abinda yasameta.
Kafin wani yayi magana nazli ta miqe da gudu tayi kanta ta shaqureta cikin kuka tana fadin,
Ina waleed 'dina yake? Kifadamun inda kuka kaimin 'dana. Zan iya yafe muku komai amma bnda 'dana, Wlh kasheku zanyi idan kukayiwa waleed wani abu Ki fadamun inda kikakai waleed Ki......
Tasowa sukayi hankali tashe suna qoqarin 6an6areta daga jikin haj xeenat 'din amma ta riqeta sosai ba alamar zata saketa.
Ihu take tana fadin saita kasheta idan bata kawo mata waleed dintaba.
Tameer ne ya 6an6areta da qarfi ya matseta ajikinsa tanata mutsu mutsun qwacewa Ya qara qanqameta sai kawai ta fashe da kuka tana qara qanqamesa tana cewa, Meer waleed 'dina.
Shafa kanta yayi yana cewa, Jst clmdwn bbynah i promise to bring our son back safe and snd.
Wiqi wiqi haj xeenat tayi tana shafa wuyanta dayaji shaqura dan tayi mamikin yanda yarinya kamar nazli takeda qarfi irin wannan.
Jan qafa tayi takoma 'daki sbd mugun kallon tuhumar da alhaji zaid da haj nuratu suke aika mata ga inna datasan komai akanta itama sai mugun kallon take binta dashi.
Tana shiga 'daki ta dauki wayarta tafara kiran aminan nata.
Ana 'daga wayar tafara magana hnkali tashe
Kareema ranafa ta gama 6aci dan kuwa shegiyar matar mahaukacinan ta dage akan mu mukadaukar mata yaro To tun wuri musan abinyi da yaron kafin afara zargina danko yanxu naga alh na jifana da kallon tuhuma.
Hnkali a'dan tashe haj kareema tace, Ai dama yau kanon nayo sbd nima anan ansamu matsala sbd aikin jikin alhaji ya karye harya dawo da shegiyar matarsa ga meenah taje ta kwaso mana shegen ciki bansandashiba harsai yanxu dayakai wata bakwai.
Tashin hnklintane ya qaru jin zancen da hj kareema take fada. Aje wayar sukayi akan gobe dukansu zasu hadu a kano susan abinyi.
🌕🌕👉mamuh geee 🌕⚜DA'IMAN⚜🌕
Na MAMUH GEEE
☆dedicated to☆ Husnah bbchoudiallo
221~222
Zaune suke a quryar 'dakin haj xeenat suna tattauna matsalolinsu.
Kareema,xeenat ya kuke ganin yanxu za'a kammala aikin nan cikin lokaci mu tattara mubar qasar nan tun asirikanmu basu gama tonuwaba dan ni yanxu haka wanted ce sbd bincike yasa angano ni na kashe tsohon mijina commisioner da hannuwana nakuma kashe matarsa dan haka ni buqace nake da barin qasarnan.
Tabbas bilki tare xamu bar qasarnan tun nima nasan kowane lokaci alh xai iya gano abinda nayi masa tunda yadawo hayyacinsa ga kuma yayansa alh kabiru dana kashe sbd yanamun shishshigi.
Ajiyar zuciya haj zeenat tayi kafin tace, Ku yanxu kunasa ran idan alh da tameer da fannah suka gane ni na kashe nyssa aina da kansu zasu kasheni basai hukuma ta shigoba. Yanxu duka ba wannanba ya zamuyi da yaron nan?
BANI ABUNA ZAKUYI
A gigice suka waiwayo dukkaninsu.
Atare suka saki ajiyar xuciya ganin ita kadaice duk da haka suna cikeda fargaba.
Qarasowa tayi tsakiyar 'dakin ta kallesu a wulaqance tace,
Kun tafka kuskure babba na satar min 'da dan kuwa a shirye nake dana fallasa duka asirinku dake lullube.
Menayi muku arayuwa da kuke fatar ganin bayana. Me mijina,uban mijina da qanwar mijina sukayi muku arayuwa kuke neman ganin bayansu ta ko wane hali. Shin ku bakwada koda 'digon imani ne arayuwarku,
Tabbas ta6a mini 'da zai zama mugun aikinku na qarshe dazakuyi. Akan 'dana jinin meer 'dina zan iya yin komai Dan haka ayau basai gobeba zan tona mugun asirinku kowa yasani.
Juyawa tayi da 'dan gudu zata fice takirawo meer 'dinta yazo yaji komai.
Tsaya kiji me miji me 'da.
Cak ta tsaya batareda ta juyoba.
Har gabanta haj kareema ta xagayo riqe da waya ta danna kira tareda saka handsfree.
Hello haj barka da dare. Barkadai leloh, Gobe da qarfe goma na safe idan bakaji daga 'daya daga cikin mu ukuba to ku kashe yaron nan, Idan kuma munzo to bayan minti biyar da zuwanmu idan nazli batazoba ku kashe yaron.
Angama haj.
Kashe wayar tayi tana kallon nazli da tashin hnklinta da firgicinta ya fito fili ga zufan data hada nan take.
Kinada xa6i nazli tameer zaid omar. Zaki iya xuwa ki tona mana asiri ke kuma abakin ran 'danki. Hakama idan kinso gobe da qarfe goma zaki iya zuwa ki maye gurbinsa saimu tabbatar da son da kikewa tameer gaskia ne ki ceci rayuwar 'dansa ki bamu taki sbd ke kadaice wadda tasan sirrinmu.
Kasa 'daga qafarta tayi jikinta yadau wata irin rawa nan take zazzabi ya cafketa me qarfi.
Daqyar takai kanta 'daki tareda turo qofa ta rushe da wani irin kuka.
********** Wani irin mazari qafafunta keyi dan har fitsari saidaya zubo mata akan tsoro.
Fruit tameer yakirata yace takaiwa nazli ta tabbatarda taci sbd shi tun safe baya gida yana gurin aikin neman.
A tray ta yankosu ta fito daga kicin zata samansu nazli 'din saita hangota ts nufi 'dakin haj xeenat saita aje tray 'din tabita tana kiran sunanta amma batajiba harta shige.
Taso juyawa amma saita tuna da abunda yafaru tsakanin nazlin da xeenat sai kawai tabi bayanta cak ta tatsaya bakin qofar sbd abunda kunnuwanta suka fara 'dauko mata. Duk abinda yafaru tagani ta ji kuma har awayarta ta 'dauka. Jin naxli xata fitone yasata guduwa 'dakinta harta tuntube.
Sharce guminta tayi tana jin yau bazata iya bacci ba saisu dad da b sun dawo ta nuna musu komai sbd ummi da inna na gidan anty saadah mijinta ya rasu jiya da dare.
Qarfe 'dayan dare suka dawo kowanne daki yayi yashige daga dad din har tameer.
🌕🌕👉mamuh geee 🌕⚜DA'IMAN⚜🌕
Na MAMUH GEEE
☆dedicated to☆ Husnah bbchoudiallo
223~224
Ido jajir yashigo palon tana zaune ta cusa kai atsakiyar qafafunta.
Suna hada ido ta taso da gudu ta fada jikinsa ya qanqameta yanajin sonta na barazanar dauke numfashinsa.
'Dago fuskarta yayi zaiyi magana ta jefa bakinta a nasa hawaye na gangarowa daga idanunta.
Mamakine yasashi dan xamewa yana kallonta.
Karaya irinta bankwana ya hango a idanunta sai yaji gabansa ya 'dan buga da qarfi.
Kama hannunsa tayi suka shiga har toilet sukayo wanka. Tea sukasha atare shidai binta yake da kallo tareda wani irin sanyin jiki da faduwar gaba.
Koda suka kwanta lafewa tayi ajikinsa. Shafo fuskarta yayi saiyaji hawaye ya tallafo fuskarta suna fuskantar juna murya can qasa yace, I love you nazli, I love you morethn life itself, I love u morethn enough, Ure my life, Pls promise me you wont leave me, Promise me forever until death do us apart.
Sheshekar kukanta ce ke tashi ahankali sbd kalamansa amma batada yanda zatayi dama tasan haka rayuwa take dole wata rana zata mutu and after all ta sadaukar da rantane sbd tameer 'dinta.
Hankalinta bai tashiba saidataga hawaye nabin fuskarsa da gudu Rungumesa tayi tana cewa, I love you too meer. Kuma zan uyayin komai sbd kai da waleed.
Soyayya suka gurza a daren duk da xuciyoyinsu a dagule suke.
Tun tara da rabi ta gama shirinta ta suri key 'din motar tameer 'daya ta fice.
Bude idanu yayi tareda lalubowa amma bai jiyotaba ya tashi da sauri sai kawai yaga qatuwar paper ta rubuta i love you meer.
A gaggauce yayo wanka ya fito ya shirua ya sauko saigashi yayi karo da fannah xata hawo kafin tayi magana dad yafito yana cewa, Wai ina haj xeenat ne inata nemanta.
Zaro ido fannah tayi tana cewa, B ina sis inlw?
Ita nake nema nima Yafada yana 'dan duba palon.
Ihu mai qarfi fannah tasaki tanacewa, Shikenan zasu kashe min sis inlw, B,dad mummy is behind all... Waya ta fara budewa jikinta na mugun kakkarwa ta nemo video 'din data dauka tana qoqarin nuna musu.
👉 kuyi hkr kadakuga laifina, Masu kira suna cewa kada kowa ya mutu kuyi hkr kawai xance.😭
🌕🌕👉mamuh geee
🌕⚜DA'IMAN⚜🌕
Na MAMUH GEEE
¤dedicated to¤ Husnah bbchoudiallo
225~226
Kallon video din suke hnkali tashe da mugun tsantsar mamakin abinda su haj suke fada sun aikata da kansu.
Cikin wani irin mugun sauri da tsananin baqin ciki tareda fargabar nazli dinsa yayi h yar fita atsiyace haryana qoqarin kifewa
Dad yayi saurin riqosa cikeda tashin hnkli yace, Son pls Kara kaje kbr nakira commissioner sai aje tareda jami'an tsaro sbd mutanen nan kanaji they're very dangerous and.....