Kenza eBookz

Da'iman complete hausa novel - Chapter 11

Da'iman complete hausa novel - Chapter 11

Da'iman complete hausa novel Chapter 11: Da'iman complete hausa novel Chapter 11. No dad, Bazan iya tsayawaba, My wife is out dia sacrificing her life for…

3,375 words

No dad, Bazan iya tsayawaba, My wife is out dia sacrificing her life for me and my son and for u all Hw can i jst sit and wait for wasu jami'an tsaro.

Ficewa yayi da gudu ya fada mota a tsiyace ya fice zuwa gurin address din dasukace tasamesu.

Gudu yake sheqawa kamar zai tashi sama ji yake xuciyarsa na harbawa da sauri kamar zata tarwatse dan kuwa tabbas idan wani abu yasami nazli dinsa bayajin zai iya handling kansa sbd tabbas yasan haukarsa zaikoma harma wadda tafi tada.

********

Tsaye take idanunta sunyi jajir banda fuskar tameer 'dinta ba abinda take gani.

Rintse ido tayi wani ra'dadi na cin zuciyarta ta budesu ahankali ta 'dora akansu.

Da qarfin hali ta fara fadin, Kada kuyi murna bayan mutuwata sbd sadaukarwata bazata taba zama iska ba, Meer bazai ta6a hutawaba sai ya gano wanda ya kashe masa nazli dinsa And trust me bazai kalli matsayinki na matar daddynsa zai aikaki inda nake Sbd yanamin.....

Tsawa ta daka mata sbd zancen yana shigarta fiyeda yanda nazli ke tsammani sbd tabbas tasan son da tameer 'din kewa nazli to ko fannah ta kashe masa ita to tsaf xai aikata lahira bare ita.

Kallansu haj balki tayi tana share zufa tareda 'daga musu kai alamar ayi agama.

Leloh hj bilki ta kalla tareda cewa, 'Dauko yaron.

Riqeda hannunsa leloh yafito daga wani 'daki cikin palon. Yana ganinta yayo kanta da gudu yafada jikinta tareda sakin kuka Yana kiran, Ummanah.

Qanqamesa tayi tareda rintse ido zuciyarta na karyewa da tsananin son 'danta da tausayinsa sbd sunan daya kirata dashi akaro na farko yakirata da ummansa.

Leloh ne ya janyesa daga jikinta tareda miqawa yaronsa 'daya yace ka kaisa gida yanxu.

Kasa miqewa tayi daga durqushen sai alokacin hawaye suka gangaro mata masu ciwo.

Tananan durqushe haj xeenat ta kira fannah tareda saka hnsfree A fusace fannah ta 'daga kafin tayi mgna sai ganin waleed tayi yashigo palon da gudu yana kiran, Daddy, daddy.

Waleed ta fada da qarfi tareda cillar da wayar tayi kansa.

Kashe wayar haj xeent tayi tana cewa, Kinji 'danki yana gida hnnun auntynsa so muyi abinda yakawomu.

Cup din juice leloh ya aje gabanta yana aika mata da wani irin kallon shaqiyanci da kwadayi yana warware qullin hannunsa ya zuba garin gubar gaba 'daya.

Girgixawa yayi ya miqa mata yana kashe mata ido tareda 'daga mata gira.

🌕🌕👉mamuh geee 🌕⚜DA'IMAN⚜🌕

Na MAMUH GEEE

I dedicated this page to👉 😘Fa'in💋💋😍, Sis Rahamat nalele(samareen bana👯), Xinniee💋, Maman khalid💋. Thnk you all for ur concern.

227~228

Kallonsu take idanunta na tsiyayar hawayen baqin ciki da tausayin kanta.

Sigari yayiwa wani wawan ja ya fesar da hayaqin ya kur6i giya kafin yace, Haj nifa nagani kuma raina ya biya dan haka kawai abari na rage xafi kafin ta wuce garin daba'a dawowa.

Wani shu'umin murmushi dukkansu suka saki atare cikin farin ciki dan tabbas sunason ganin ta wulaqanta a rayuwarta.

Cikeda farin ciki hj xeenat tace, Leloh ka cire kwadayinka saika tabbatar da kaciresa duka.

Shewa yayi a 'dan buge yana wurgar da sigarinsa ya nufi gurinta yana wani qanqance ido.

Xabura tayi Dasauri tayi baya.

Tunkarota yakeyi yana wani karkace kai tsabar buguwa da yayi. Kuka take harda shesheka tanaja da baya.

Damqota yayi yana sunsunarta Ta turesa da qarfi yayi baya sbd rashin karfin jikinsa dake buge.

Qara kamota yayi yana janta xuwa 'daki taga da gaske nakasta mata rayuwa xaiyi taji wani zafin rai ta fincike da qarfi ta dawo baya ta 'dau cup 'din gubar tanajin gwara ta mutu data bari yayi mata fyade.

'daga cup din tayi da sauri takai bakinta sbd ganin ya dosota.

Da qarfi aka fixge cup 'din danhar ruwan yafara shiga bakinta.

Cikin xafin nama leloh ya damqeta yaja baya da ita tareda xaro bindiga ya 'dora saitin kanta batareda yace qalaba.

Suma dukkansu a kidime suka miqe cikeda tsoro da mamakin ganinsa. Hardai haj xeenat da jikinta yadau rawa nan take a rude cikin tsawa tace,

Leloh harbeta ka harbesa duka su mutu mu huta tunda yakawo kansa ya sauqaqa mana aikinmu.

Wurgi da cup 'din yayi yayo kan leloh ido arufe da bacin rai.

Leloh na ganin haka yayi saurin sakinta zai gudu tameer ya bisa da gudu suka fito harabar gida kowa na neman guduwa.

Ganin tameer yakusa kamasa yasa ya juyo yana gudu ba wani 6ata lokaci yasakar masa bullet biyu daidai lokacin haj xeenat da haj kareema sun danne nazli suna qoqarin dura mata sauran gubar cikin rashin sa'a harbin ya sauka kansu Haj xeenat ta tsakiyar idonta yabi ya 6ulla bayan kanta, Haj kareema kuwa ta tsakiyar wuyanta yashiga.

Atare suka zube agurin sunata shure shure jini na tartsi ba kyan gani harsuka daina alamun rai yafita.

Ihu haj balki tasa tana ja da baya fitsari nabin qafafunta a gigice dan ta fita hnklinta nan take.

Damqarsa yayi daidai xai bude gate din gidan yafice Ya haukace yake dukansa Nandanan ya hada masa jini da majina amma yakasa sakinsa sbd har lokacin yana ganin nazli 'dinsa a hannunsa harda kara mata bindiga akai.

Yaron leloh ta hango ya 'daga bindiga saitin bayan meer zai harba

Gudu take tana kiran sunansa da qarfi amma yayi nisa da muguwar xuciya sai dukan leloh yake.

Tana kaiwa ta janyesa da qarfi daidai nan shikuma yayo harbin kuma nan tameer yaga abinda ke shirin faruwa sbd bullet 'din direct kan nazli yayi Da qarfi ya tureta gefe daidai nan bullet 'din yashiga qirjinsa

Wata mahaukaciyar qara tasaki tareda kiran sunansa da qarfi daidai nan ya sulale qasa idanunsa na lumshe zasu rufe.

Da zafin nama tayi kansa tana kiran sunansa jiki na 'bari

Hannu yasa cikin qarfin hali ya fixgota fuskarsu ta hade ahanki ya furta I LUV U tareda hade bakinsu yana tsotsa ahankali numfashinsa na 'dan daukewa kafin taji tsit.

Tanajin shiru batasamu qarfin yin wani motsiba a jikinsa ta sume.

Daidai nan su dad da fannah da haj nurat da innah harmada anty saadah da rundunar 'yan sanda da sojoji suka iso.

Ihun fannah ya razana kowa sai alokacin kallansu yakai kansu nazli dake kwance cikin jinin tameer 'din.

Umminsa na gani wani wawan jiri ya 'debeta saida anty saadah ta riqeta sbd hawan jininta yariga yatashi nan take.

Inna da fanna suka dauki nazli dad kuwa kwa6e bbar rigarsa yayi ya cincimi tameer wasu police suka bisu a haukace akayi asibiti dasu

Sauran kuwa haj bilki da leloh da yaransa uku aka kama tareda kwasar gawarsu xeenat.

Emergency aka shiga dasu hnkali tashe sbd duba idan da sauran rai ataredasu.

🌕🌕👉mamuh geee

👉👉ina miqa godiyata sosai ga masoyana dasukayi ta aiko saqon adduar samun lpiata dakuma wainda suka kira, Ngd sosai allah yabar qauna😍😍😍😍💋💋💋💋💋💋💋💋

Mamuh geee

[2/4, 9:25 PM] ‪+234 703 962 5239‬: 🌕⚜DA'IMAN⚜🌕

Na MAMUH GEEE

¤dedicated to¤ Husnah bbchoudiallo

233~234

Kwana biyar tameer bai farfadoba A kwana biyar dinnan duk wanda yakalli nazli ita zai tausayawa sbd yanayin datake ciki. Sam bata iyaci bare sha sai aikin kuka.

Yau su kadaine adakin itada fannah Fannah na lallabata akan ta daure ta 'danci fruit salat din data hado mata.

Knocking door akayi ahankali Fannah ta aje cup din hannunta ta miqe zuwa qofar ta bude.

Gabanta saida ya fadi da ganinsa amma tuno abinda yayiwa b akan nazli saita hade fuska tana turo qofar zata rufe.

Saurin riqewa yayi tareda cewa, I love you fannah.

Cak ta tsaya gabanta na tsananta faduwa sbd xancen yazo mata abaxata.

Ta jima atsaye tana jin faduwar gaba kafin ta juyo tana dan 6ata fuska takallesa ta dauke kai tace,

Sorry dan banajin zaka sami karbuwa anan bayan hakama meka dauki kanka bayan abinda kayiwa b kana tunanin ni fannah zan iya tsayawa na saurareka harna iya soyayya dakai Sorry. Tura qofar tayi tadawo ta zauna kusada nazli data qurawa meer ido ta fada duniyar tunani.

Itama tunanin tafada sbd tabbas tasan tanasan hameed to amma abinda yayiwa b fa. Miqewa tayi ta fice dakin sbd tana buqatar air.

Tana fita nazli ta miqe ahankali jiri na dan dibarta ta nufi gadon dayake kwance.

Shafo fiskarsa tayi tanajin sonsa da kewarsa na dawainiya da ita.

Hawa gadon tayi ahankali tareda shigewa cikin jikinsa tana kiran sunansa ahankali hawaye na xubowa daga idanunta. Ta jima ahaka zuwa can bacci yayi awon gaba da ita bata saniba.

Cikin bacci taji motsinsa batareda ta gasgataba ta bude idanu ahankali daidai lkcin shima ya bude nasa idanun. Tsaf idanunsu suka shiga cikin na juna Wata irin qanqama tayi masa da qarfi tana sakin kukan farin ciki.

Hannunsa ya daga ahankali ya dago fuskarta yana kallo tareda lumshe idanu.

My my savior are u okey? Daga mai kai tayi da sauri tana hawaye tareda rungumesa tana cewa,

Meer kadaka sake kwanciya kabarni. Meer kaine rayuwata, Meer....

Shihhhh Ya isa haka kwantar da hnklinki bazan qaraba insha allah.

Fannah ce ta turo qofar tana ganinsa idanu abude ta murza idanu taga tabbas shi dinne sai kawai itama ta saki siririn kuka

Hannunsa daya ya miqa mata yana dan murmushi tazo da gudu ya rungumeta.

Daqyar suka sakesa yatashi zaune fannah taje da gudu takira dr daidai nan su dad da ummi dasu inna suka iso.

Nan take kowa farin cikinsa ya kasa boyuwa dad rungume dansa yayi yanajin farin ciki sbd shi kadai yasan halinda yakeciki game da ciwon tameer din.

Ummi ma hawaye tasaka masa saidaya jawota jikinsa yana share mata.

Inna da anty saadah ma sunyi masa barka da arzikin tashi Itadai mutuniyar tana maqale kusadashi taqi tashi dan ita tama manta da wata aba kunya Can sai su kalli juna su sakarwa juna murmushi harda wani kashe mata ido yakeyi itakuma tana murmushi.

Dr ne bayan yagama dubasa yaga babu matsalar komai yaso riqesa har bayan kwana biyu amma sam tameer yadage akan a sallamesa sbd jin wani mayen son matarsa dayake.

Haka aka sallamesa suka dunguma zuwa gida hannunsu cikin na juna dan lurada hakan yasa kowa yafara dan baya baya dasu sbd gane ga dukkan alamu masoyan mantawa sukeda kowa. Ko amota su kadai suka shiga daya fannah tajasu Duk da itama saidata ringa jin kunya.

Suna isa gida suna fitowa daga motoci nafisa ta fito riqeda hannun waleed yana ganin mamarsa da babansa ya yanko da gudu tameer ya daukesa yana rungume yanajin son dansa na qara shigarsa.

A palo ummi takalli waleed tace,

Waleed zo muje 'dakina nabaka choculate din danasa akasiyo maka.

Gyara zama yayi ajikin daddynsa kafin yace, Aa ki riqe daddyna yadawo zai siyamun.

Dad yace, To ni zo muje ka rakani dakina muyi kallon news ko.

Shima maqe kafada yayi. Inna ma tayi nata yaqi, Anty saadah ma haka.

Fannah tace, My boy ka tuna abinda nace xankaika nasiyama.

Eh aunty yanxu xamuje? Gurinta yayi da gudu ya 'dale jikinta.

Ummi takalli nazli tace, Nazli kuje son dina yayi wanka ya huta nafisa nacan takai abinci can samanku din.

Miqewa sukayi bako kunya hannunsa na riqe da nata harsuka haye.

🌕🌕👉mamuh geee [2/4, 9:25 PM] ‪+234 703 962 5239‬: 🌕⚜DA'IMAN⚜🌕

Na MAMUH GEEE

¤dedicated to¤ Husnah bbchoudiallo

235~236

Suna shiga palon yasakawa qofar key tareda jawota jikinsa yana jifanta da wani shu'umin kallo daya sakata sadda kai tana murmushi.

Gani baida shirin motsawa yasa takamo hannunsa suka nufi bedroom ta dauko towel ta miqa masa yaqi kaba yakuma qi dauke kallonsa akanta.

Da kanta ta tubesa tajasa toilet ta hada ruwan dumi a bathtub zata juya ya jawota jikinsa yana qoqarin tubeta ta qwace da sauri ta fice tana dariya.

Murmushi yasaki tareda daukar brush.

Ko ina nafisa ta gyare sai qamshe da sanyin ac ke tashi dan haka babu abinda zatayi sai kawai ta fitar masa da kayan shan iska takoma palo tazauna tareda qurawa tv ido murmushi da zallar farin ciki na fita a fuskarta.

Yana fitowa wanka ya shafa mai tareda saka kayan data fidda masa ya fesa turarukansa masu tsada yafara gabatar da sallolinsa.

Tashi tayi tayi dayan bedroom din wanda na waleed ne tayi wanka cikeda farin ciki dan yau sam bakinta yakasa rufuwa.

Tana fitowa 'daureda towel sai ganinsa tayi a dakin ta tsaya tana kallonsa shima ita yake kallo jiki amace Dan duk ta kallesa jikinsa mutuwa yake.

Ficewa tayi tashige dayan dakin ta xauna gaban mirrow tana murmushi. Riga da skirt tasa na supa red me kwalliyar black dinkin ya xauna daram a jikinta.

Daure gashin kanta tayi a tsakar kai da red band me yar kwalliya ta fesa turare yashigo dakin ya jawota jikinsa yana shinshinata.

Qwacewa takesonyi ya dago fuskarta yana kallon tsakiyar idanunta aikuwa nan take ya kashe jikinta ta rasa duk wani kuxarinta.

Murmushi yayi tareda hade fuskrsu guri daya yana ha'de yawu kafin ya isa cikin bakin nata.

Atare suka saki ajiar xuciya yafara kissing dinta cikin sanyi. Yanda suke kissing din ne zai tabbatar da yanda suke tsananin son junansu sbd cikin nutsuwa sukeyi yana shafarta.

Hannu yasa ya zuge zip din rigarta tayi sauri juyawa tana fidda numfashi Yajawota ta baya bayan ya xame rigar ya jefar ya birkitota tareda daukarta tayi saurin rintse idanu tana tura kanta a qirjinsa.

A gado ya kwantar da ita tareda hawayewa yana aika mata da tsimin son dayake mata.

Basu sauko palon qasaba sai lokacin cin abincin dare suka taru duka gidan akaci dinner cikin farin ciki Waleed kuwa kasa taqamaiman me basa abinci akayi sbd kowa basa yakeyi tun daga dad ummi fannah da daddynsa nazli dasu inna iyakacinsu murmushi.

Kwanansu biyar suka tattara suka koma abj bayan antura haj bilki gidan yari daurin rai da rai.

Sun koma abuja da sati daya suka tattara gabaki dayansu suka wuce cairo inna da nafisa da abdl da ahmd 'yayan saadah kawai aka bari dan har ita saadah aka tafi sbd wani irin janta ajiki da ummin keyi.

Ranar dasuka isa cairo taga qauna da gata agurin dangin uwar mijinta marigayiya nyssa. Waleed kuwa sam ita batamasan inda yakeba bare waleed din akwai rashin ji shiyasa yakeda saurin sabo.

Duk yanda tameer yaso qin barinta akayi ta kwana gurinsa tanayi masa dariya ya wuce yanajin wani zazzabin dole daya saukar masa.

Wasa wasa saida suka share sati tana 'dakin tsohuwa amma ganin da gaske suke ya shirya musu tafiya zuwa greece da uk gurin aminisa EMRAAN da matarsa AYEESHA.

Ba yanda sukaso haka yadau matarsa suka tafiyarsu.

🌕🌕👉mamuh geee [2/4, 9:25 PM] ‪+234 703 962 5239‬: 🌕⚜DA'IMAN⚜🌕

Na MAMUH GEEE

¤dedicated to¤ Husnah bbchoudiallo

237~238

Sabon babin rayuwa suka bude a qasar dan tuni sun manta da nigeria sai luv sukeci abinsu, Sun canza sunyi jajir dasu kullum suna manne da juna dan wani irin so sukewa junansu mai wuyar fassarawa.

Dad da fannah da anty saadah sun koma dan waleed dai anbarwa ummi shi a cairo zai zauna.

A nigeria dai aure ya tabbata tsakanin dad da anty sa'adah dan andaura inna kuwa qin zama tayi agidan saidai takoma gidansu na kano aka zuba mata yan aikinta qauye dai kuma sai lbr.

Duk yanda taso yakice alamarin hameed abin ya gagara sbd ya nace yakoma kalar tausayi dole ta sauke komai ta bada kai bori yahau dan dama tanason abinta.

Ba 6ata lokaci suma suka fara zuba luv dinsu danma ta hanasa turowa sai b dinta yadawo.

*********** Kwance take tana bacci cikin kwanciyar hnkali tayi wani irin haske ta ciko.

Tsayawa yayi akant yana kallonta cikin yar rigar data sa me kama da babu tana baccinta. Komai takeyi kyau take masa hardai yanxu data qara cikowa.

Zama yayi bakin gadon tareda shafo fuskarta tayi wani irin juyi tana rungumo hannunsa. Murmushi yayi kafin ya sunkuya daidai kunnanta yace, Missty zamuyi missing flight fa.

Bude idanu tayi tana turo baki cikin shagwaba tace, Bacci fa nakeji sosai my meer.

Hawa gadon yayi tareda jawota jikinsa yana kallon 'dan bakinta yace,

Missty tashi kifadamun wannan sleeping sickness na menene.

Kallon fuskarsa tayi sonsa na qara hudata ta shafo fuskarsa tareda kai bakinta cikin nasa.

Saidaya kuma wani wankan dan wancan tuni yabi ruwa. Tare sukayi wanka suka shirya tana jikinsa har airport.

Suna isa uk emran da kansa tareda ayeesharsa sukaxo daukarsu daga airport din.

Kallon juna suke kowacce na maqale jikin mijinta tana tunani to acikinsu wayafi son mijinsa suma mazan tunaninsu kenan na wayafison matarsa acikinsu.

Babban hotel din garin suka sauka sbd tameer yaqi yadda su sauka gidan emran din.

Abu kamar wasa nazli ta langabe masa gaba daya duk inda zasu tana langabe aikinsa ga yawan bacci da shagwaba. Ba yanda ya iya banda yabiye mata yayita lallaba abarsa.

Nanma saida suka share sati biyu suna shiririta kafin suka dawo cairo.

Tunda suka dawo yaga yanda umminsa da amma na kula da ita sai okacin yagane cikine da missty dinsa. Nan wata sabuwar rayuwa ta tashi dan qara dauketa yayi sukayi tafiya.

Basu dawoba saida cikinta yakai wata biyar harya dan fito kafin suka wuce nigeria sbd takurawar da hameed yayi masa awaya akan fannah taqi bari ayi komai saisun dawo.

🌕🌕👉mamuh geee [2/4, 9:26 PM] ‪+234 703 962 5239‬: 🌕⚜DA'IMAN⚜🌕

Na MAMUH GEEE

¤dedicated to¤ Husnah bbchoudiallo

239~240

Lokacin da suka iso fannah naganin cikin nazli rungumeta tayi tana murna hameed yadan duqo kunnenta cikin rada yace,

Dakin yarda anyi komai da yanxu namiki irin wannan din. Hararar luv ta aika masa tana murmushi.

A gidama dai dad da anty sa'adah data canza takoma wata babbar haj murna sukeyi sosai.

********** Tunda suka dawo saiya lallabata take bacci sbd cikin wata muguwar shagwaba yasakar mata da son jiki Jikinma nasa Shikuwa haka yafiso dama.

Duk wanda ke gidan lalla6ata yakeyi abu kuwa idan tace shi takeso to anty sa'adah da fannah da nafisa suke taruwa a kicin ayi mata shikuwa boss din shine me bata abaki dan aikin office ma dad ganin haka yabasa hutu har missty din 'dan nasa ta haihu danko yaje yasan ba abinda zaiyi.

Rayuwa dai allah ya canzawa nazli ita sbd kaf gidan har cairo itace abinson kowa dukiya kuwa dad yabata kadarori sunfi a qirga sbd itace farin cikin iyalinsa da nasa.

******* Gadan gadan aka fara bikin fannah da hameed wanda sam tameer kasa barin missty dinsa yayi ta sake sosai sbd bbynsa sakuma rashinta da baya iyawa. Ahadai har akayi daurin aure amarya ta tare a gidanta.

Kwance take cikin jikinsa yana bata fruitshake abaki tana sha yace,

Missty, Yes my meer.

I love you. I love u too my meer.

Tell me sumtin missty do u....

Washhh ta fada kafin yaqarasa zancensa.

A rude ya aje cup din yana tallafota jikinsa.

********* 5yrs later.

Missty kinga waccar tanata kallona harda murmushi take aikomin.

Ha'de fuska tayi har zatayi maganasaita fasa tasaki murmushin daya qara fiddo da kyawunta aikuwa sai gogan ya ha'de rai yana kallonta Tace, Ya akayine my meer?

Missty yazaayi kiyi murmushi agurin nan tunda kinga akwai maza. Dariya tayi tace, Eyya my meer ainayi ne sbd tunowa danayi babu filin ko wace mace azuciyar meer dina.

Kamota yayi jikinsa tareda miqewa yana cewa, Muje gida kawai mungama bikin kuma.

Miqewa tayi suka fice daga babban qayataccen hall din dake cikin babban hotel na qasar australia dasukazo bikin auren 'dan kanwar mahaifiyarsa nyssa.

Mota suka shiga yana tsokanarta tun bata kulasa harta 'bata fuska kamar zata fashe.

Suna isowa gidansu na qasar ta fito motar da sauri tayi cikin yayi saurin riqo hannunta yana kiran sunayen 'yayansu dake 'daki tareda nanny dinsu.

Da gudu suka fito su biyu suka fada jikinsa suna cewa, We miss u daddy.

Kiss yabasu a kumatu yana cewa, I miss u too my angels.

Kallon nazli yayi yace musu, Abrar and nyssa oya kuzo kubawa mummy hakuri dad yayi mata laifi.

Shida su suka kama kunnuwansu tareda cewa, Sorry mummy.

Dariya tasaki tareda rungumosu hardashi suna dariya..

ALHAMDULILLAH.

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

Nagode allah daya nunamin nagama wannan novel din lpia.

Sannan ina miqa godiyata ga masoyana dasuka ringa tayani da addua,

Godiya ta musamman ga members na grp din,

Mamuh geee fans 1

Mamuh geee fans 2

Sauyin lamari fans

Masoyan mamuh geee

Novels only

Taurarin mamuh geee

Da duk masoyana tared writers yan uwana.

Wannan takuce ta musamman👉

Husnah bbchoudiallo Maryam matasa Subee umar Zee gummy Fammah gummy Jameela gummy Sis rahamat na lele Amina jaji Xinnie Maman khalid Fain Sis jamila muhd ali Maryam aliya Da duk sauranma daban xayyanoba.

Readers Also Read

More by Autar Alheri