Kenza eBookz

Da'iman complete hausa novel - Chapter 2

Da'iman complete hausa novel - Chapter 2

Da'iman complete hausa novel Chapter 2: Da'iman complete hausa novel Chapter 2. Sannu ahankali har dad yasa aka kawo mai koya mata karatu agida tun bata…

3,373 words

Sannu ahankali har dad yasa aka kawo mai koya mata karatu agida tun bata ganewa hartafara ganewa hakama handbag dinta wato tameer duk inda tasa kafa ta dauke yana biye da ita. Lokcin da dad yasiya mata mota yasa aka koya mata bata wani jimaba ta iya shiyasa yanxu har saukarsa take suje yawo sudawo abunsu. Abu daya ta fara fuskanta yanxu akansa shine duk yaga anyi abu idan ya burgesa to sai ya gwada shima. Duk yanda taso gason jin muryarsa bata samuba sbd haryanzu baitaba maganaba saidai taji sautin muryarsa lkc dayake daria idan suna wasa.

⚜⚜⚜⚜⚜

Sanye takeda doguwar riga wani shaking material dayayi masifar yi mata kyau tasanya dan karamin hijab tanata sauri ta gama ta sauka sbd malaminta yazo tun dazu. Xaune ta taddasa a palon yakurawa tv ido yana kallo kamar idanuwansa zasu fado Tasaki murmushi tarafa tafiya cikin san`da sbd tasamu taje ita kadai tunda hnklinsa yatafi a kallo kuma dama kotaje dashi makalkaleta yake ya hanasu karatun yanda yakamata.

Caraf taji anriko hannunta gabanta tayi mummunan faduwa sbd rikon baiyi kamadana tameer ba sbd shi makyalkyaleta yake.

Araxane tajuyo amma ga tarin mamakinta saitaga shine tsaye yarike hannunta din kuma riko mekyau sbd yanda takasa kwace hannnun. Hankalinta bai tashiba saidataji yakai mata wata kyakkyawar runguma datasa numfashinta kusan daukewa sbd a iya saninta ta tameer baya rumgumarta saidai ya cukwuikuyeta. Numfashinta taji yana fita da sauri ta zame da sauri tana dafa bango sai alokacin idonta yasauka akan tv taga wani romance film ne ake a tashar tayi sarin xuwa takashe tadan kallesa saitaga gabaki daya jikinsa amace yake. Sum sum tawuce shikuwa akaro na farko yau baibita wani guriba.

Sam yau bata gane komai akaratunba hakadai aka tashi karatun takoma. Kwance ta taddasa a palon yana ganinta yataso suka shiga bedroom tare ta aje littafanta suka koma palon nan da nan ta sake suka cigaba da wasarsu ta guje guje apalon kamar koyaushe.

🌕🌕🌕👉mamuh geee 🌕⚜DA'IMAN⚜🌕

Na

MAMUH GEEE

☆dedicated to☆ Husnah

31→35

Kashe gas din tayi ta fito kamar me satar hanya takoma daki ta zauna.

Har dare 'kin bari tayi su xauna guri daya. Da daddarema haryayi bacci idonta biyu tana kallonsa dan ganin take idan tayi bacci wani abun kuma xaiti mata.

Da safe ma tun tana gudunsa harta daina sbd shi baimasan metakeyiba tunda ba wani hnkline dashiba. Da maraice bayan sungama komai sun sauka gurin karatu ta lurada duk karatun datake idanuwansa nakan lips 'dinta datake motsawa Duk saita fara rudewa sbd tsoron kada yayi mata kiss agaban malami Aiko bata gama tunaniba taga fuskarsa ta nufo tata fuskar Tayi zambur ta mike jikinta na rawa tana raba idanu. Malamin yakalleta yanason tambayarta amma sai duk yaga a rude take. Kafin yayi wata magana cikin sauri tace, Mlm ina...ina..inajin ciwon kai abari sai gobe. Da sauri ta wuce har 'kafafunta na hardewa. Bin bayanta yayi shima da sauri suka shiga palo takama stairs ta haye. Yanda take haye stairs 'din arude da saurine yasa ta taka ba daidaiba ta zame Tameer dake biye da ita abaya ya ca'beta atsorace shima yana ware ido da le'ka saman yana duba wanda ya turota ta fado "danshi atunaninsa turota akayi. Amma harya haye saman da ita baisaniba yanata ware idanu atsorace.

Kasa 'dauke idanunta tayi akansa tun lokacin daya tarbota harya 'dauketa ya hayo saman da ita. Wani irin masifaffen sonsa takeji yana bin jinin jikinta tana kallon kyakkyawar fuskarsa har suka iso palon batasaniba saidataji yasaketa tim tafadi tsakiyar palon amma sam bataji zafiba saima binsa tayi da kallo tana murmushin dashi baimasan tanayiba.

Saidaya gama le'ke le'kensa kafin yazo gabanta data shagala da kallonsa duk inda ya wulga shima saiya saki murmushi ahankali yana kallon tsakiyar idanunta.

Ahankali ya taka ya isa gabanta har numfashinsu na haduwa sosai Tayi saurin juya masa baya tana murmushi Ya tsurawa bayanta ido yana kallon lafiyayyar fatarta fara tas data bayyana abu'dadden bayan rigarta sbd tuni gyalenta ya zame. Wani kiss ya manna mata atsakiyar baya dayasata numfashinta sha'kewa tajiyo da sauri tana fidda numfashi da sauri da sauri Bai tsaya komaiba ya kai bakinsa cikin nata yana bata wani mahaukacin kiss daya kashe jikinta takasa kwatace saima lafewa datayi ajikin nasa yana cigaba da kissing dinta. Kamar wasa taji yana shafarta harda zura hannu arigarta amma sam takasa kwace kanta dan bakaramin kashe mata jiki yayiba.

Jin suna shirin xubewane yasa ta 'dan tattara 'karfin dabaifi cikin cokaliba ta xame tareda fadawa daki tashige toilet da sauri tana maida numfashi.

Da daddare bayan sunkwantama har bacci yafara 'daukarta taji yanata juyi ta bude idanu dakyar sbd bacci saitagansa ya dafe ciki yanata juye juye cikeda axaba ta tashi zaune da sauri takamosa arude tana kiran sunanta Yana dude idanunsa akanta kawai saiya fixgota tafado jikinsa yana wani irin nishi yafara kissing dinta yana shafa arude takeso tashi amma sai maidata yake da karfi nan take wani irin tsoro yakamata tafara kuka tana kiran sunansa dan tasan tunda ba hankaline dashiba komai xai iya faruwa. 'Yar Rigar baccin dake jikinta ya 'barka da karfi yana lugwui gwuitata tako ina tana rixgar kuka duk karfinta amma sam kamar wani mai cikakkiyar lafiya sbd karfin dataji yanadashi.

Tanaji tana gani yakusanceta adaren Yarabata da budurcinta ta dunkule gefe tana kuka awahalce sbd yanda ya nuna mata rashin tausayi sbd beda hnkali gashi ya kusance a lokacin baisan waye shiba itada taso saiya warke idan ya yadda ya karbeta amatsayin mata tukunna amma yanxu agaba idan yajita ba budurwaba yaki yadda da shine yakusanceta. Duk ta tuno da hakan wani sabon kuka take saki sbd tsoron abunda xai iya faruwa agaba.

Shikuwa wani irin baccine yadaukesa cikin kwanciyar hankali yake sharar abunsa fuskarsa cikeda annuri.....

🌕🌕👉mamuh geee 🌕⚜DA'IMAN⚜🌕

Na

MAMUH GEEE

☆dedicated to☆ Husnah

41→45

Amai taketa she'kawa kaman ranta zai fita sbd babu komai acikin nata Ga rashin 'karfin jiki. Wanko bakinta tayi tana dafa bango radawo 'dakin tazaun 'kasa bakin gadon tana tsiyayar hawaye.

Motsi taga tameer nayi ta yunkura ta tashi ta isa kansa jikinta na rawa takira sunansa

Cikin rashin tsammani taga ya bude idanuwansa awahalce Sbd ciwo dake cinsa

Ahankali kuma taga ya fara jijjiga idanunsa na juyewa

Ihu tasaki tareda dira kansa tana kuka mai karfi tana kiran sunansa.

Jitayi ya Shaketa da karfi Idanuwanta suka firfito tana shure shure amma baida alamar sakinta Shidewa take batunyi taji yasaketa yakoma yaxube kwance yana jijjiga jijiyoyin kansa duk sun fito ya ri'ke kan da hannuwansa yafara buga kan abango da karfi yana ihu..

Kuka tasaki tana tashi Duk da bata gama wartsakewaba daga muguwar sha'kar dayayi mata.

Hankali tashe take kallonsa kukanta na 'karuwa sbd ganin yana buga kan nasa sosai harya fara jiwa kansa Da sauri ta isa ta 'kankameshi tana kiran sunansa cikin kuka

'Kokarin tureta yake daga jikinsa amma ta 'kankameshi ta'ki sakinsa sai kuka take.

Ahankali taji ya daina ya sulale 'kasa xaune idanuwansa arufe. Xamewa tayi itama zaunen agabansa tana ta'ba fuskarsa datayi jajir tana jini tana hawaye tace,

Meer meyake damunka? Meyasa ka chanxa sosai? Pls meer kakoma yanda kake sbd zuciyata da kwakwalwata neman tarwatsewa suke, Bansan yazanyiba.

Bu'de idanuwansa yayi sunyi jajir kamar bashiba ya 'dorasu akanta yana kallonta awahalce.

Tana ganin yabude ido ta mi'ke da sauri ta dauko 'dan 'karamin towel da ruwan 'dumi tafara goge masa jinin fuskarsa tana tanajin ra'da'din ganinsa ahaka.

Idonsa akan fuskarta ko 'kyaftawa bayayi ahaka ta goge fuskar ta mike ta maida kayan tazo tashiga toilet ta ha'da masa ruwan zafi a bathtub ta fito takamasa takaisa har cikin ruwan.

Suna fitowa ta zaunar dashi ta goge masa jiki tasakamai kayan shan iska tazaunar dashi ta fice zuwa 'kasa dan samo masa abinci.

Abincin aikinta takarbo takawo masa dakyar ta lallabasa yaci sbd jikinsa da yayi xafi sosai alamar xaxxabi.

Kwantar dashi tayi ta lullubesa takoma gefe tana kallon sauran abincin tanajin yunwa amma baxataci ba sbd kada yatashi babu abunda zaici duk da darene.

Da wuri ta tashi tayi sallah tana idarwa shima yatashi takaisa toilet sukadawo tasashi yayi sallah yana idarwa wani sabon xaxxabin yataso masa tamayardashi gado ta futa zuwa aiki.

⚜⚜⚜⚜⚜

Gaba 'daya rayuwar ta juye mata Da kuka take yini, Da kuka take kwana, Sbd komai ya lalace mata Tameer gaba 'daya baida lafiya Ga doke doke dayake wani lokacin yayita farfasa kaya Idan kuwa ya damketa saita kusa mutuwa allah ke kubutar da ita. Wani lokacin har falla mata mari yake bakinta yayita jini. Idn kuma haukar ta kwanta to kwana yake cikin matsanancin xaxxabi..

🌕🌕👉mamuh geee 🌕⚜DA'IMAN⚜🌕

Na

MAMUH GEEE

☆dedicated to☆ Husnah bbchoudiallo

46→50

Ta rame sosai tayi wani irin haske wanda takesa ran 'kila jinine babu ajikinta Ta fige,ta hargitse sbd wahala da yunwa ga tashin hnkalin tameer da yanxu gaba 'daya tsoronsa take dan yanda alamun cikar hauka keta bayyana ataredashi.

Shi kansa tameer yayi wata irin muguwar rama sbd yanxu gaba 'daya ko abinci baya iyaci kota basa Rayuwar ta ida birkice masa gabaki 'daya.

Aikin bawa flower ruwa taketa famanyi Sai sauri take tagama sbd mugun jirin datakeji duk da bawani kuzari takedashiba sbd tuni tayi hannun riga da lafiya.

Batayi auneba taji Jiri mai 'karfi ya kwasheta ta xube abun ban ruwan dake hannunta yayi sama yadawo mata ruwan dake cukinsa suka xube ajikinta gaba 'daya.

Sanyin ruwan yashigeta sosai ga muguwar buguwar da kanta yayi.

Goge hawayenta tayi tareda daddafawa ta mi'ke tana kallon kayanta dasuka jike ta nufi babban palon dan xuwa sama ta chanxo kaya.

Tana shiga palon ta du'kar da kai sbd haj xeenat na palon hakimce tana waya.

Hanyar hayewa stair ta nufa tana kakkama jikinta sbd sanyin A.C daya ciki palon gata kuma kayanta ajike.

Wani razanannen ihu taji haj xeenat tasaki ta juyo da sauri har jikinta na mazari.

Nafisa ma dake kicin aguje ta fito hartana zamewa a tiles.

Fizgo nazli tayi da wani irin mugun 'karfi dan yanda tashin hnkali da ki'dima sukasa idanuwanta rufewa Wannu ta 'dora akai tana kallon rigar yadin dake jikin nazli ta kwanta ajikinta sbd ruwa ta nuna cikin nazli jikinta na rawa murya asar'ke tace,

Me..me..mene..ne wannan?

Nazli da nafisa atare suka kai kallonsu ga kallon cikin nazli suka ga ya'dan taso ka'dan

Nafisa data fahimci me haj xeenat ke nufi itama ta waro idanu cikin kidima da tashin hnkali.

Nazli kallon cikinta take tanason taga abunda ya 'daga musu hankali amma bata ganiba bayan cikinta daya kumbura kadan wanda take tunanin yunwace ta kumburar mata dashi dan tuni ta lura da kumburinsa.

Figitaccen marin da haj xeenat tasakar matane yadawo da ita hnklinta kafin ta wartsake marin takuma xabga mata wani wanda ya haddasawa hancinta 'barewa da jini.

Rufeta tayi da duka kamar mahaukaciya cikin tashin hnkli kaman zatayi kuka take fadin,

Wllh kasheki zanyi, Bazan bari wannan abun yafaruba koda zanyi yawo a tsirara, Bazan taba bari haka tafaru ba, Allah ya isa tsakanina dake shegiya munafukar karuwa.

Ganin haj bata hayyacinta gaba 'daya yasa nafisa doka shahada tayi kukan kurar 'kwace nazli tana bawa haj hakuri

Zaman 'yan bori haj xeenat tayi bakinta na kumfar fitina da masifar tashin hnkli.

Dakyar taja jiki ta tashi daga kwancen tana hawaye hancinta da bakinta suna fidda jini Sai kakkarwa jikinta yake dan bakaramin duka haj xeenat tayi mata ba ga mararta dataji ta 'daure nan take ta dafe ciki tana tsiyayar wasu hawayen.

Rarrafe take kokarinyi ta haye sama tsabar wahala

Haj xeenat ta xabura tsaye tayi kanta ta shakurota tajawota kamar kayan wanki ta dawo da ita tsakiyar palon ta wurgar tareda rarumo wayarta jikinta na rawa takira dr tace maza maza yazo yanxu tana son ganinsa..

🌕🌕👉mamuh geee 🌕⚜DA'IMAN⚜🌕

Na

MAMUH GEEE

☆dedicated to☆ Husnah bbchoudiallo

51→55

Kafin dr ya iso kasa zama tayi tafara safa da marwa afalon tana jin xuciyarta kaman xatayi bindiga ta fashe.

Baiwar allah nazli kuwa tuni azaba da zazzabi mai mugun 'karfi ya dirar mata jikinta babu inda baya karkarwa sai hawaye take tsayayarwa dan har alokacin batasan abunda haj xeenat ke nufiba.

Minti goma sha biyar saiga dr yashigo palon Haj xeenat tayo kansa tana nuna nazli da hannu tace, Dr dubamun yarinyarnan dan banason xargina akanta ya tabbata.

Shima cikeda mamaki yakalli nazli 'din dakyau na tsawon lukuta Tabbas amatsayinsa na dr yaga wasu lamomin ciki atattare da ita tunkan ya duba Amma dandai su tabbatar yamatso gabanta ya dukusa yayi mata wasu yan tambayoyi amma ko magana takasayi sbd matsanancin halinda take ciki.

Roba yaba nafeesa yace, Kamata kuje toilet inason fitsarinta yanzu.

Hannu biyu nafisa tasa takamata sukaje toilet 'din 'dakin nafisa dake palon.

Suna dawowa nafisa ta mi'ka masa ya karba da hannuwansa daje cikin hnd gloves ya fiddo da pt strip yasaka cikin fitsarin ya dangwalo ya rike yana kallo dan ganin abunda result zai bayar.

Duk wani numfashin haj xeenat dake fita dakyar to 'daukeda tashin hnkli da tsoro yake fitowa Sai addua take allah yasa kada result 'din ya nuna positive.

Ko 'kyafta idanunta batayi daga kan pt strip 'din yawuma dakyar take hadiyesu.

POSITIVE shine abunda result ya nuna

Kawai sai hawaye suka gani a fuskar haj xeenat ta mike kamar guguwa tayi 'dakinta Ta fito da damin kudi ta xubewa dr tana cewa,

Gasunan idanma basuyiba xan 'karama koma nawane KACIREMUN SHEGEN CIKIN JIKINTA AYAU BASAI GOBEBA.

Nazli dr nafisa atare suka mike tsaye sbd tsoro da bazatar furucinta Hardai nazli da furucin na haj yasa ta fahimci abunda tun farko haj ke nufi harta kira dr kuma ya tabbatar da cikine da ita har takeson axubar.

Bata taba saran zata iya mikewaba sbd axabobin ciwon datakeji acikin jikinta Amma ta zabura ta mike cikin tashin hankaki biyu Dana jin tana 'daukeda ciki dakuma jin xa'a xubar mata dashi.

Magana dr xaiyi ta 'daga masa hannu fuska adaure tace,

Deal ne xakayi kona nemi wani?

Damin Kudaden yakalla yaji bazai iya bari suwucesa suje gurin waniba Koba komai idanma baiyi ya tabbatarda saitayi tunda tayi niyya.

Tattara kudin yayi yana xubawa ajakar kayan aikinsa dayazo da ita yana cewa,

Nafisa kamata kusameni amota muje asibiti yanxu na wankosa waje.

Ajiyar xuciya haj xeenat tasaki tana wani shu'umin murmushi.

Kamar wata rakumi da akala takoma tanajin wani radadi daya danne zuciyarta Takasa bude baki tayi magana sai hawaye dake gudu a fuskarta nafisa tajata suka tafi.

Bushewa xuciyarta tayi dan itama gwara acire mata cikin dan batason ta haifosa yaxo ya tarar da wulakantattar rayuwar dasuke ciki itada mahaifinsa kuma batada tabbacin idan yazo duniya ubansa xai karbesa idan ya warke.

Tunani mai xurfi nafisa tashiga tanajin bazata iya bari axubar da magajin wannan babban familyn me tarin dukiya ba Amma tana tsoron yiwa dr magana yakoma yafadawa haj.

Har suka kai asibitin suka 'dunguma xuwa office 'dinsa suka xauna shikuwa kasa xama yayi yafara kai kawo yana tunanin Tabbas idan yazubar da cikin jikan alh zaid to yaxama cikakken maha'inci kuma butultacce sbd alh xaid ne sanadin duk wani matsayi dayake akai yanxu Afterall yafi kowa sanin alh zaid da tameer suna tsananin bukatar 'da jafin duk ashiga cikin wannan halin na ciwon tameer.

Dakewa nafisa tayi ta mike taje gabansa ta tsaya takallesa cikin ido tace, Idan xuciyarka batason yi kada kayi Kuma ka tuna komai daren dadewa gaskia xata iya bayyana alokacin da baka tunani. Shin me xamu samu idan muka cutatar da rayuwar wa'inda suka taimaki rayukanmu suka kyautata rayuwarmu. Dan allah inason kayi amfani da shawarar da zuciyarka ke baka kadaka cutatar da cikin nan🙏

🌕🌕👉mamuh geee 🌕⚜DA'IMAN⚜🌕

Na

MAMUH GEEE

☆dedicated to☆ Husnah bbchoudiallo

56→60

Kallon nafisa yayi yana nazarin kalamanta kuma sun shigesa sosai ya zauna tareda huro iska Yace, Tabbas bazan iyaba sbd alh da tameer bazan iya cutatar da gudan jinin suba To amma kobanyiba haj bazata zaunaba saita tabbatarda babu cikin nan kuma yanxu bama cikin kadaiba tunda harta gane tameer zai iyayin ciki ayanayin dayake ciki to tabbas zata 'dauki mummunan mataki akan hakan.

Kukan nazli ne ya tsaidasu sbd kukane take rerowa mai ciwo daban tausayi sbd ganin yanda rayuwarta takoma dakuma rayuwar abundake cikinta tun baizo duniyaba. Durkusawa tayi gaban dr tana tsiyayar hawaye tace, Idan har halaccin da daddy yayima kakeson mayarwa to Dan allah kakiramunshi yasan halinda 'dansa yake ciki, Meer yana cikin tsananin halinda yake bukatar taimako Amma babu mai taimaka masa, Dan allah ka taimaka kakirasa koxata shiga.

Duk yanda sukaso su samu daddyn basu samesaba har suka gaji.

Kallonsu yayi bayan yayi scanning 'din cikin yafara musu bayani, Yanzu zan baki maganin karin jini saiku fadawa haj anxubar da cikin Illa dai abu 'daya dazan fada muku shine kushirya tarbon tashin hnklin dazai biyo baya idan cikin ya fito gaba 'daya Dan ni nanda sati mai xuwa zanbar 'kasar zuwa wani aiki.

Babu me cikakkiyar nutsuwa suka dawo gidan sbd gudun kadata gane. Tana ganinsu tasaki murmushin 'keta dajin 'dadi tareda jinjinawa dr. Shikuwa bai tsaya dogan zanceba yatafiyarsa dan gaskia yana shakkar haj zeenat sbd rashin imaninta.

Har 'palonsu nafisa takaita tasauko cikin tunanin bala'in dazai nufatosu nan gaba idan haj xeenat tagano gaskia.

Kwance ta tarar dashi idonsa biyu yabita da kallo da kyawawan idanunsa batasan sanda taje da gudu ta fada jikinsaba tareda sakin 'dan siririn kukan tausayinsu dakuma wani jarababben sonsa datakeji dakuma cikin jikinta daya kasance tsotsonsane.

Shima rungumeta yayi yana lumshe ido akaro na farko taji yace mata, Shihhhhhh.

Cikin farinciki da hawaye ta 'dago tana murmushin datama manta ya ake yinsa ta 'kara 'kankameshi tanajin sonsa.

Wanka sukayo sukayi sallah tare sukaci abincinta na aiki. Mikewa tayi zata fita yayi saurin dawo da ita jikinsa yana kallon 'dan bakinta Batai auneba taji nasa bakin anata yana bata wani irin kiss me dadi.

Sam batayi yunkurin kwacewaba harya fara shafarta yana zura hannuwansa cikin rigarta nandanan yafice hayyacinsa ya sureta sai gado.

Sosai suka raya daren wanda rabonsu da zama ma kusada juna harta manta bare wata soyayya.

Tund safe cikin bacci taji ana 'barin kaya Ta tashi afirgice Idanuwanta suka sauka kan 'dakin Ya fasa komai na 'dakin ya hargitsashi ta hango jini akasa da sauri ta diro gadon jikinta na 'bari ta xari riga tasaka tayi palon a tsorace aiko komai na palon ya fasa duk yajiwa kansa rauni sbd hannuwansa jini suke fitarwa sosai ga 'kafafunsama haka.

Juyowa yayi suna hada ido ta ha'diyi wani yawu da 'kyar sbd gaba daya kamannunsa sun chanxa idanuwansa sun birkice Tafara 'kokarin ja da baya dan ganin ya nufota. Cikin rashin sa'a ta taka kwalba cikin abubuwan daya fasa ta fadi 'kasa aiko nan yahau jibgarta da 'kafa yana taka kanta Tun tana motsi harta daina ta sume agurin.

🌕🌕👉mamuh geee

🌕⚜DA'IMAN⚜🌕

Na

MAMUH GEEE

☆dedicated to☆ Husnah bbchoudiallo

71→75

Tapia suke ta 'kankame hannunsa tana waige waige jikinta sai 'bari yake har lokacin ga mugun zazzabi tanaji Shi kansa tameer ciwone ajikinsa sosai dan layi kawai yakeyi idanuwansa a lumshe.

Tafia kawai suke batareda tasan inda suka dosaba Babban tashin hankalinta baifi dataga dare yafara tsala musuba ga tameer daya fara ficewa hayyacinsa yana 'kokarin xube mataba ga jakar kayansu haka itama ta galabaitu matuka.

Wata motace ta 'dan tsaya gabansu razana tayi tareda ja da baya tana 'kankame tameer.

Wani wurjigegen inyamuri tagani cikin motar yace, Madam do you need a taxi?

Kallonsa tayi cikin tsananin tsoro tana hada gumi Kafin tabasa amsa sukaga tameer ya sulale agurin.

Sakin jakar hannunta tayi aki'dime ta cakumosa tana kwala kiransa. Idansa ya'dan bude awahalce akalleta yamaidasu ya lumshe.

Da sauri ta bude motar tana kokarin tadashi jiki na rawa Direban ganin yanda take kiciniyar kamasa duk a rude takasa ya fito ya kama matashi suka sakashi cikin motar yasaka musu jakarsu tareda shiga motar yace ina zai kaisu? Shiru tayi tana hango tashin hnkalin dazata tadda amma bayanda ta iya dole can xata kodan ganin tun yanxu sun fara yagayyara ga tameer na..... "Kano. Tafada murya na rawa hawaye na silalowa daga idonta ahankali.

Direban kallonta yayi ta mirrow tareda maimaita kano cikin wawuyar hausarsa kafin ya girgixa kai ya tada motar da nufin kaita tasha tunda yasan shidai ba kanon zashiba.

Har aka kai tashar bata hayyacinta sbd hawayen daketa zirarowa daga idanunta tana kallon fuskar tameer dake nuna yana cikin tsantsar ciwo.

Suna isa tashar ya suka fito ya karbi dubu daya yatafiyarsa.

Readers Also Read

More by Autar Alheri