Kenza eBookz

Da'iman complete hausa novel - Chapter 3

Da'iman complete hausa novel - Chapter 3

Da'iman complete hausa novel Chapter 3: Da'iman complete hausa novel Chapter 3. Duk da darene amma akwai mutane sosai atashar sunata sha'anin gabansu.…

3,358 words

Duk da darene amma akwai mutane sosai atashar sunata sha'anin gabansu. Rabewa sukayi bakin wata rumfa atsorace take gaba 'daya banda kuka ba abunda take.

Tana kallo ahankali bacci mara da'di ya'dau tameer.ta cusa kanta tsakiyar gwiwowinta tana rero kukan tausayinsa san gwara ita tasaba da wahala amma shi baisan wata wahalar rayuwa ko 'dayaba Gashi yanxu batasan wace irin rayuwa zasuyi ataredasu babah ladingo.

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

NAZLI ADO BUBA TAKAI shine sunanta, Mahaifinta adamu abubakar 'dan asalin takai ne kuma maraya daya taso hannun kakarsa dan yarasa iyayensa tun yana yaro. Yayi karatu dai dai misali dan headmaster ne primary school 'din 'yan 'kauyen. Matarsa 'daya ladidi wadda ake kira da babah ladingo Da 'ya'ya biyu bubah wanda yaci sunan headmaster malam ado,sai idi.

Daga ladingo har 'ya'yanta babu me hali na kirki ko mutunci. Sam su bubah banda sace sace da 'kwaya basusan komaiba wanda ladingo ita ta lalata abunta danko malam bai isa yayi maganaba akansu.

Raihanat budurwar buzayen nijar dasukayi gobara suka rasa dukiyoyinsu da gidajensu ta rasa iyayenta sai aminin mahaifinta 'dan uwan me gari dashima acan yake kuma yayi basa rashin saiyazo da ita tareda matarsa da 'yarsa 'daya asmah ya hadasu ya rike.

Basu wani jimaba agarin ya aurar dasu Ita raihanat ga headmaster ado dake sonta sosai sai ita asmah acan 'kauyen gaba dasu ga wani 'dan dagacin 'kauyen.

Bayan aurensu da wata biyar allah yakarbi ransa me 'dakinsa ta tattara ta tafiyarta garinsu itama.

Raihanat dai takoma batada kowa sai mijinta wanda gaba 'daya rayuwar gidan sam batada da'di ko kwanciyar hankali dan ladingo da 'ya'yanta sun saka gaba da tsangwama ga cuta iri iri gefe 'daya ga aminiyar ladingo wato iya jummai da kullum tana gidan suna cutatar da ita. Iya jummai mijinta ya jima da rasuwa sbd ba'kin cikinta dana 'yayanta iro da karima.

Raihanat nada hakuri da biyayya sosai shiyasa mijinta ke tsananin sonta dan agurintane kawai yakeji sanyi. Ahaka ta haifi 'yarta ta fari nazli mai kama da ita sosai sak buzuwa. Haka 'yarta girma babu ranar dazasuce sunyi farin ciki a rayuwarsu ta gidan sai gashi garin haihuwa ta biyu su ladingo suka rufeta a'daki tana nakuda tayita neman taimako tana rokonsu amma suka 'ki budeta saida suka tabbatar da axaba ya kasheta.

🌕🌕👉mamuh geee 🌕⚜DA'IMAN⚜🌕

Na

MAMUH GEEE

☆dedicated to☆ Husnah bbchoudiallo

66→70

Zaune take bakin gadon dayake kwance tana shafa lallausan gashin kansa dake kan cinyarta ahankali idonta akan fuskarshi tana kallo shima ita yake kallo yana lumshe idanun marasa lpia. Gabanta ke'dan faduwa akai akai dan haka takasa tashi tabar gurinsa.

Hawayene suka gangaro daga idonta ahankali suka sauka akan fuskarsa Ya rintse ido sbd jin afuskarsa suka xuba amma a xuciyarsa yaji zafinsu.

Hannu ya 'dago yana rawa ya shafo fuskarta tareda girgiza mata kai alamar ta daina kuka. 'Karasa rushewa tayi da kukan ahankali tana cewa, Meer inajin wani irin nauyi a xuciyata dana kasa ganewa, Meer idan narasaka bansan ya rayuwata xata komaba, Pls meer kada katafi kabarni, Kabari na rayu dakai dan rasaka daidai yakeda tabarbarewar rayuwata. Meyasa nakeji kamar wata rana xaka barni? Meer pls dnt ever leave me sbd kaine rayuwata da abunda zan haifa.

Yanda take kukan ne tana maganganun yasa ya tashi zaune dakyar tareda jawota jikinsa ya rungume tsam.

Saidata sha kuka sosai har kukan baya fita kafin tafara sauke ajiyar zuciya ahankali har bacci ya 'dauketa.

⚜⚜⚜⚜⚜⚜

Kaida kawo take a tsakiyar makeken 'dakinta. Xuciyarta a cunkushe take ta rasa gasgata abunda xuciyarta da shawarar aminanta suke bata.

Ingizata xuciyarta takeyi akan tayi gaggawar aikatarda 'kudirinta akansu.

Zama tayi bakin gado tareda 'bata fuska tana cewa, To idan nakoresu ai zasu iya dawowa wata rana hardai idan shegen balaraben yaron nan ya warke.

Zabura tayi tana cewa bazai yiyuba.

Wayarta ta 'dauka rai abace ta nemo wata number takira tana huci.

Ringin biyu wayar tayi aka 'dauka Cikin 'kosawa tace, Lilo ya alhajin yake? Lpia klau haj saidai ciwonsa gaba yake. Kyalesa indai kuna basa abinci. Yanxu dai akwai aiki na musamman daxakuyi a daren yau. So nake kuzo da daddare inason ku aika mahaukacin 'dansa barxahu tareda shegiyar aljanar matarsa kuma banaso asamu matsala. Angama haj kawai yanxu naji alert.

'Kokarin sakin tray 'din hannunta take nafisa tayi saurin tarewa tana zare idanu tareda ha'de wani wahalallen yawu tana dam'ko hannun nazli sukabar 'kofar 'dakin sbd datayi 'barin kayan to tabbas data jawo musu masifar datafi wadda sukaji.

Kicin suka koma ko wanne jikinsa na 'bari tsabar tashin hnkl Nazli ta saki wani irin kuka tana sulalewa 'kasa Nafisa ma tsabar rudu kukan take dan iya ka'duwa ta ka'du da abunda sukaji haj na fa'da.

Kuka take mara sauti sosai kamar ranta xai fita Jikinta har karkarwa yake tana sha'kewa.

Cikin tsananin tausayi nafisa ta dafata murya na rawa tace, Na..na..nazli inaga kija sir tameer ku gudu wani guri nesa da inda bazata taba sanin kuna canba, Nazli yanxu kece komaina sir tameer tunda mahaifinsa babu labarinsa, Kodan kasancewarsa UBAN 'DAN DAKE KWANCE ACIKINKI.

'Daki taje da sauri tadawo rikeda kudi masu 'dan afki ta kamo hannun nazli ta dam'ka mata su tana hawaye tace, Ki tafi dashi nazli,i trust you, Nasan ke kadaice xaki kula dashi fiyeda kanki.

Tayar da ita tayi jiri na 'dibarta tana sheshshekar kuka suka hay stairs 'din takaita har 'kofar palonsu ta juya.

Gadon dayake kwance yana bacci ta nufa tana toshe baki sbd kukanta dayake tsananta Ta xube akansa tana sakin kukan gaba 'daya.

Sosai ta risga kuka cikeda tausayin ya rayuwarsu zata koma idan sukabar gidan, Ya zatayi da tameer daba lafiyane dashiba. Ina suka dosa? Yazatayi da kanta,tameer dakuma abunda ke cikinta.

Kiran sallar magrib yasata ta mike tana goge hawayenta tareda fa'dawa toilet tayo alwala tayi sallah Ta tadashi takaisa yayo alwala yayi sallah.

Kayansu ta zuba a akwati 'daya tana danne kukanta ta kama hannunsa tana kallon 'dakin hawaye nabin fuskarta tajasa suka fice gidan batareda kowa yaga fitarsuba danko masu gadi suna cikin masallacin gidan suna sallah..

🌕🌕👉 mamuh geee 🌕⚜DA'IMAN⚜🌕

Na

MAMUH GEEE

☆dedicated to☆ Husnah bbchoudiallo

76→80

Rayuwar nazli ta tagayyare danko wanka ladingo bata iya yi mata sai idan malam da kansa yayi mata dan ya'dauki son duniya ya 'dora ga 'yarsa nazli. Tana isa sakawa makaranta yasakata duk zashi aiki tare suke zuwa su dawo tare ahaka harta girma tasan kanta tanada shekara goma sha 'daya ya rasu yabarta cikin muguwar ukubar ladingo. Ta taso cikin wahala da azaba. Duk wani aikin gidan ita keyinsa, Ga sana'ar abincin ladingo itake 'dorawa duk da aikin yafi 'karfinta kuma idan tayi ba daidaiba a aikin buba ko idi take sawa ko iro 'dan iya jummai su laka'da mata dukan da saita gagara motsa koda 'dan yatsanta.

A mataccen 'dakin mahaifiyarta take zama bayan duk sun kwashe tarkacen kayan 'dakin suka barta da 'yar matacciyar tabarma ga 'kofar 'dakikn sun cire. Ahaka ta rayu ta girma acikinsu har wannan auren 'kaddarar yahau kanta.

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

TAMEER ZAID OMAR Alh zaid omar 'dan asalin jahar maidugurine. Yanada tarin dukiya mai 'dinbin yawa wadda ya gada ga iyayensa dakuma 'karin tashi daya tara takansa. Alh zaid omar su biyu kacal iyayensu suka haifa kafin su rasu shida yayarsa dayafi so fiyeda komai wato HAJ NURATU. Haj nuratu nason 'dan uwanta itama fiyeda komai wanda duk wandake tare da ita zai sheda hakan. Haj nuratu na aure a 'kasar cairo sbd mahaifin mijinta alh kabeer balaraben can ne sai mahaifiyarsa yar maiduguri.

Zamanta acan yasa shima alh zaid yamaida rabin business 'dinsa acan. 'Yayan haj nurat biyu isma'il da ammar.

Ganin da gaske alh zaid baida niyyar aure yasa tasakashi agaba harda hawayenta akan lallai sai yayi aure Hankalinsa ya tashi sosai ganin yayarsa na hawaye Ya lallasheta tareda bata zabin matarda taga ta dace dashi. Farin ciki tayi sosai dan dama akwai 'yar 'kanwar surukinta datayi masa sha'awarta balarabiyar asalin cairo 'din mai suna NYSSA.

Bawani dogon zancen suka amince da juna haka iyayenta basuyi jaba sbd sunason nurat kuma suna yaba halayenta dan haka sunsan 'kaninta xaiyi kirki kamarta.

Aurensu da shekara bakwai nyssa ta haifi 'danta namiji balabe sak ga tsantsar kyawu Aka saka masa suna tameer.

Soyayya da gatan da tameer yake samu ba ka'dan bane sbd takowane 'bangare kowa sonsa yake bama kamar iyayensa da haj nurat dakejinsa fiyeda 'yayanta Ga 'bangaren dangin nyssa masu tashen dukiya mai 'dibbin yawa agarin suma tsananin 'kaunarsa suke. Haka ya girma a sangarce harsaida yayi shekara goma sha biyar kafin mum 'dinsa takara haihuwar mace taci sunan FANNAH.

Tsabar dukiyar alh zaid yasa yayi suna sosai ako ina wanda gidan tashar gatanmu channel dake kaduna nigeria ta aiko da ma'aikatanta na musamman dan samun ganawa dashi.

Ranar daya gana dasu ma'aikatan nakomawa masaukinsu xeenat takasa zama saikai kawo take tanajin wani irin kwa'dayi da son alh zaid yayi mata dirar bomb axuciya wanda daga 'karshe ta 'dau mummunan 'kudiri akansa.

Kodata dawo nigeria gidan aminiyarta haj kareema ta nufa ta fesa mata aiko nan suka 'dunguma gidan abokiyar cin mushensu haj bilki daganan suka 'dunguma gurin boka.

Bayan uwar dukiyar dasuka kashe aikinsu yafaraci dan kuwa tana kiran wayarsa kiran farko daya 'dauka tafara masa bayanin kanta ya datse kiran sai gashi bayan kwana biyu dakansa yakirata.

Sannu sannu aiki yafaraci saiga alh zaid harda zuwa nigeria gurin xeenat inda anan ne sukayi aikinsu na 'karshe akansa wanda baikomaba saida aurenta akansa.

Dukiya da daular daya sakar matane yasa nanda nan ta chanxa tazama hamshakiyar haj dan dama can ba yarinya bace ta'dan kwana biyu.

Dunia tadawo musu sabuwa itada aminanta da mahaifiyarta Haj sabuwa da itama boss ce harkar bin bokayen kafin mijinta ya yarasu.

CAIRO Sannu ahankali suka fara ganin chanji daga alh zaid dan yanxu akai akai yake xuwa nigeria kuma yakan jima acan. Tsananin son dayakewa matarsa da 'dansa harma da 'yar uwarsa bai rageba shiyasa basu kawo komaiba arai sai tunanin kila business dinsane.

🌕🌕👉mamuh geee 🌕⚜DA'IMAN⚜🌕

Na

MAMUH GEEE

☆dedicated to☆ Husnah bbchoudiallo

81→85

Ganin daular da haj xeenat take cikine yasa suka 'kulla 'kullalliyarsu suka aika mijin haj bilki barzahu ta aure mijin 'yayar wata 'kawarsu gurin aiki mai tarin dukiya shima dake abuja bayan sun kore matarsa daga gidan.

Haj kareema ma wani minister ta aura bayan ta tarwatsa matarsa da 'yayansa ya koresu ta haifi 'yarta meenah Wadda sam batada tarbiya ko kadan.

Ganin haryanxu yanason matarsane yasa haj zeenat yanke shawarar xuwa harcan ta tarwatsa zaman tunda anyi aikin har angaji yakasa ciresu aransa koda da minti 'dayane.

Tana isa cairo kai tsaye gidan yayarsa tafara isa cikin iko da takama.

Zaunawa tayi tana murmushin 'keta saiga haj nurat 'din tafito sbd ansanar da ita tanada bakuwa.

Kallon mamaki takebin xeenat dashi kafin tadan saki fuska tana mata sannu suka gaisa aka kawo mata drinks. Ruwan sanyi ta kurba tareda crossing legs tana girgixawa tace, Sunana haj xeenat zaid omar.

Kallonta haj nurat tayi dakyau amma bataga alamun hauka atareda itaba saita 'dan saki murmushin ya'ke tace, Allah sarki wane zaid omar 'din?

Zaid omar 'kaninki Ni matarsane tsawon shekara uku kenan ina zaune a abuja nigeria.

'Kuri tayiwa haj xeenat tanason tayi tunani 'kwakwalwarta takasa dan ita takasa ma tuno me xeenat 'din tace tsabar rudani.

Kafin tace wani abu saiga alh zaid sun shigo shida matarsa dasu tameer Tasaki ajiyar zuciya tana kallonsa dan bakaramin dadin ganinsa tayiba alokacin.

Idanunwansa na sauka kan xeenat ya washe baki duk da ya razana sosai da ganinta.

Ganin yanda yasaki fara'a be yasa suka kalli juna cikeda mamaki. Haj nurat ta'dan ha'de fuska tace, Zauna ka fadama wacece ita.

Zama yayi yana kallon fuskar nyssa dan makaramin so yake mataba Yamaida kallonsa ga yayarsa murya a'dan tsarge yace, Kuyi hakuri naso na bayyana mukune yanda xaku fahinta amma kuma sai abun yazo ahaka Xeenat matata ce, Munyi aure shekara uku yanxu.

Kallonsa suke dakyau ba alamar wasa axancensa bari makamancin hakan.

Iya 'kuluwa sun 'kulu Nyssa ta mike tareda sa'ba fannah akafada ta fice afalon batareda ko gefensa ta sake kalloba. Haj nurat ma mikewa tayi tashigewarta tabarsu.

Mikewa yayi yabi bayanta ta dakata da tafiya ta juyo ba 'bata lkc tace, Tabbas bani bakai idan har kana tareda waccar matar.

Zaro ido haj zeenat tayi dan tana labe tana jinsu.

Lallai zanyi maganin wannan matar tafada tana 'kafa.

Tashin hnkli akayi sosai amma aikin asiri yaki bari yasaketa ga nyssa tuni tafara ciwo sbd mugun 'kullin da haj xeenat tazo dashi ta barbada mata a palo sbd 'karfi da yaji suke zaune gida 'daya.

Tameer bayanan yana paris karatu Kwanciyar hankali ta 'kauracewa familyn dan nyssa ciwo ya munana ga xeenat taki komawa Shikansa alh ya susuce gaba 'daya ganin masoyiyarsa kwance rigis.

Mahaifiyar nyssa ita takarbi fannah tadawo hannunta kafin nyssa ta warke.

Shekara 'daya tana jinya allah yakarbi ranta wanda kuma gurin xuwa gaisuwar munafincine su haj bilki suka zomata da wani mugun aikin daya haddasa fitina gaba 'daya a familyn dan kuwa 'kiyayya mai zafi ta shiga tsakanin dangin nyssa dashi dan gani suke shine sanadi. Hakama 'yar uwarsa haj nurat tayi mummunan fushi dashi tanajin wata irin tsanarsa shima haka yakejin duk tsanarsu dansun tsani matarsa haj zeenat.

Da haka ya tattara yabaro cairo yakoma paris gurin 'dansa dan yanda yakejin tsanarsu ko fannah dake gurinsu bazai iya zuwa ya kar'ba ba.

Rayuwa tayiwa haj xeenat yanda takeso dan tuni tazama haj babba ga hutu da dukiya dasuka mufun ratsata.

Matsalar farko dasuka fara samu itace 'dansa tameer ya girma yazama saurayi yafara 'dorasa adukiyarsa sai abun yafara damunta sbd yanda ta tsani yaron dan ya'dau son duniya dana nyssa ya 'dora masa.

Tameer saurayine bamai wasu shekaruba dan duka duka shekarsa ashirin da biyar xuwa da bakwai, Yarone 'dan gata fiye da tsammani, Balarabene sak dan mum 'dinsa ya 'dauko akomai. Dad 'dinsa baya boye sonsa agaban kowa. Ganin 'kiyayya ta ginu tsakanin haj zeenat da tameer yasa ya tattarata yamaidota nigeria dan yanxu babu wani sauran sonta aransa kawai dai zaman ake hakama 'kiyayyar 'yan uwansa ta ragu aransa.

Barinta 'kasar yasa tameer yakoma cairo dan kula da kamfunan dad 'din nacan wanda wata sabuwar 'kauna da gata yatashi acan dan kuwa dan lelensu yazama wanda hakan ne yasa yake asangarce duk da ya girma amma idan ka gansa a waje ya iya ha'de gira ba wasa.

Zamansa a cairo yasa komai ya cahanxa masu rayuwarsu suke a nutse sai lokaci lokaci yakanje nigeria gurin dad 'dinsa duk da shima bai cika zama a nigeria 'dinba.

Wani zuwane dayayi meenah 'yar haj kareema tagansa tace ita duk duniya shi takeso Shikuwa harya koma baimasan dazamantaba.

Awata dawowar ne suka aikata masa mummunan aikin tunanan yafara 'dan ciwon kai kafin ya tattara yakoma Aiko yana komawa ciwo ya tabbata hauka. Sannu ahankali abu yaki sauki 'Karshe dai dad 'dinsa yazo yadau 'dansa yafara yawon 'kasa 'kasa dashi amma an tabbatar masa da kwakwalwarsa ta juye.

Nijeria ya dawo ya damka kula da 'dansa ga dr sufyan wanda ya budewa babbar asibiti yana sakar masa dukiya.

Ahakane wani malami ya tabbatar musu da sammune. Anyi neman maganin sammun har angaji ba wani sauki ga masu kula dashi sai guduwa suke sbd wahalar kula dashi shinefa karshe akayi masa aure dan asamu akula dashi dakyau kafin ya warke ya za'bi zama da matar ko rabuwa da ita.

TOFAH.....

🌕🌕👉mamuh geee 🌕⚜DA'IMAN⚜🌕

Na

MAMUH GEEE

☆dedicated to☆ Husnah bbchoudiallo

86→90

TASHA...... kiran sallar asuba yasa ta'dan 'dago kanta tana kallon masallacin cikin tashar Bata gani sosai sbd kumburin da idanuwanta sukayi dan tsabar kukan datake sharba har asuba 'din.

Maida kallonta inda tameer ke kwance tayi tana kallon yanda sanyi ke ka'da jikinsa yatakure yana fidda numfashi da sauri da sauri.

Duddubawa tayi taga inda ake diban ruwa taje ta 'debo tadawo tayi alwala ta tada tameer da 'kyar tayi masa alawa sukayi sallah. Gari na'dan fara haske taga anfara gyar motoci zasu fara lodi ta mike tareda kamosa ta'dau jakar kayansu suka nufi motocin. Da sauri wani yayo gurinsu yace ina zasu murya adashe tace kano. Karbar kayansu yayi yasaka a mota suka shiga atsorace sai rabon idanu take sbd kallon da aketa binsu dashi dan ganinsu kamar larabawa ita buxuwa da zuriar hausawa shima larabe da xuriar hausawa.

Tameer gaba 'daya afirgice yake duk da baida lafiya Ganin ana kallonsu saiya 'kankame nazli yana lafewa ajikinta Mutane mezasuyi inba dariyaba ganin 'katon saurayi dashi yana boyewa bayan mace Gashi a fuska kamar jarumi.

Dariya ake musu sosai harda tsokanarsu aka fara tana hawaye tayi saurin jansa suka fada motar suka xauna yana 'kankameta.

Hawaye take sosai har motar tacika suka tashi bayan ankarbi kudin motarsu.

Lafewa tameer yayi ajikinta yana kallon kyakkyawar fuskarta data kumbura Ta'dan kallesa cikeda fargabar abunda zasu tarar atakai dakuma tsoron kada cimar can tayi masa mummunar illah akan wadda yake ciki.

Da rana tsaka suka isa kano ta fito rikeda hannunsa tashin hankalinta na tsananta ganin sun kusa isa kenan.

Motar 'kauyen takai suka shiga daga cikin tashar Ga yunwa da 'kishirwa dake damunsu su duka hardai ita me juna biyu da duk kaganta kasan cikine da ita.

Karfe hudu suka isa takai ana saukesu ta rushe da kuka jikinta na mazari dan tun bata isaba takejin wani irin tsoro na shigarta musamman na cikin jikinta dabatasan yaza'ayiba.

Da 'kafa suka isa 'kofar gidan taja ta tsaya cak shikuwa tameer sai shige mata yake sbd tsoron yaran dake biyarsu tun a hanya suna cewa lah buxaye.

Hawayen idonta suka gangaro ahankali tasaka hannu na rawa ta shafesu tareda doka shahada tashiga tsakar gidan.

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

Zaune suke a tsakar gidan sunacin gyada suna rangada fira itada aminiyarta ta kullum wato iya jummai sai karima 'yar iya jummai dake 'dakin babah ladingo itada bubah suna firar soyayya cewar su babah ladingo amma kuma banda tumurmuxarta ba abunda yake a'dikin kuma sarai suna jiyosu amma sai firarsu suke cikin nishadi.

Ganin larabawa a gidan yasa suka mi'ke atare suna kallonsu Babah ladingo tayi saurin juyawa zata 'dauko tabarma tana fadin, Sannunku ba'ki kushigo. 'Ko'karin shinfida tabarma takeyi iya jummai data 'kurawa nazli dake hawaye ido tana mata kallon 'kurulla ta waro ido da 'karfi tace, NAZLI

Kallon iya jummai tayi murya 'kasa 'kasa tace, Jummai wace nazli kuma salon ki kore manasu 'kila ba'kin arzikine.

Da 'karfi taja bushashshen hannun ladingo takaita gabansu tana duba kigan...... Bata 'karasaba sbd cikin jikin nazlin data gani.

Tattakewa babah ladingo tayi ta zuba ihu tana kiran jamaa suzo su tayata ganin ankoro nazli da cikin shege datayo da aurenta.

A kidime su bubah suka fito yana gyara zaman wandonsa suma a firgice suke kallonta sai alokacin suka lurada balaraben dake bayanta nan take suka rufeta da duka har ita harshi

Ma'kabta suka taru ana kallo tareda yin tir da halin nazli datayo cikin shegen aka korota 'karshema cewa sukayi mai gadin gidanne buzu irinta yayi mata ciki aka korosu tare.

Labari yakai kunnen me gari ya aiko 'dan aike da wuri akan adaina dukansu akawo masasu yanxu yanason ganinsu dan bazasu zauna agarinsaba.

Koda sa'ko ya isa tuni dukkaninsu sun jima da suma tsabar duka.

Ruwa aka kelaya musu suka fara motsi Ta bude idanuwanta dakyar tanajin wani irin ciwo tako ina ajikinta. Cikin wata irin dauriya ta daddafa ta tashi zaune tareda jan jiki ta isa inda yake zube ko yatsa bai iya 'dagawa bakinsa da hancinsa na jini haka itama Kuka tafashe dashi tana kiran sunansa agalabaice.

Ciccibarsa sukayi itama su iya jummai suka jata kawar kaya akayi fadar me gari dan ladingo ta gwammace ta kashesu data zauna dasu.

🌕🌕👉mamuh geee 🌕⚜DA'IMAN⚜🌕

Na

MAMUH GEEE

☆dedicated to☆ Husnah bbchoudiallo

91→95

Gaban me gari aka xubesu kamar kayan wanki ko motsi dakyar sukeyi anyi musu raunika bakyan gani.

Kallonsu yayi saiyaji wani tausayinsu yashigesa hardai na nazli dayasan mahaifinta sosai da mahaifiyarta kuma yana sane da ukubar datake ciki hartayi aure.

Gyara xama yayi yana kallonsu yace, Dukan dakukayi musu bazai bari nayi wani hukunci ayanxuba dan haka abarta ta zauna gidan mahaifinta harta samu sauki sai adawo.

Yana fadar haka ya sallami kowa su babah ladingo kamar zata fashe tsabar ba'kin ciki tana fadin, Ni yaushe wannen 'bakar zuri'ar zasu barni naji da'din rayuwata.

Readers Also Read

More by Autar Alheri