Kenza eBookz

Da'iman complete hausa novel - Chapter 4

Da'iman complete hausa novel - Chapter 4

Da'iman complete hausa novel Chapter 4: Da'iman complete hausa novel Chapter 4. Da taimako suka iso gidan ladingo naxabga musu harara kamar idonta zasu…

3,336 words

Da taimako suka iso gidan ladingo naxabga musu harara kamar idonta zasu fado Zuciyarta na tafarfasa kaman ta 'kone jitake kamar ya sha'kesu su mutu ta huta Ta shige 'daki da 'karfi tana huci tareda mukarabanta.

Da bin bango ta isa kofar tsohon 'dakinta daya tsufa ya mutu duk ramukan cinnaku da 'beraye yacikashi sbd dama ba siminti ne dashiba.

Jiri na 'dibarta ta share 'dakin ta fidda zaninta 'daya ta shimfida a'kasa takoma takamosa ta kwantar dashi akai itama ta sulale 'kasa ko shimfida babu Nan take suka fice hayyacinsu sbd zazzafan zazzabin dayayi musu mummunan kamu sbd azaba.

Ruwan randa me sanyin aka antaya musu bokiti guda

A firgice ta tashi zaune duk da ba 'karfi ajikinta ko kadan Shikuwa idanu kawai ya iya budewa awahalce dan ko motsi baya iyayi sbd arayuwarsa baisan wahalaba, Jikinsa banda hutu da gyara ba abunda yasani shiyasa yake cikin azaba sosai.

Baba ladingo ce tsaye karima agefenta rikeda bokiti.

Cikeda ba'kin cikinta takalli shegen buzun ta 'karbi bokitin 'karfen hannun karima xata buga masa akai Nazli tayi surin fadawa jikinsa bokitin yasameta a goshi tuni jini ya 'balle amma hakanan ta daure tana share hawaye.

Shewa ladingo tayi tana cewa lallai naga alamar akan wannnan ko'dadden zaki 'dau komai to muzuba nidake dan wallh su buba da iro da idi zansa su jibgarmun shege kekuma ni zanji dake. Tashi nafasa korarku agidana aikin bauta zakuyimun koba komai nasamu bayi Tashi maza wanki zakimun yanxu.

A ki'dime ta 'dago sbd tsakar darene gata tana cikin wani hali na ciwo da yunwa ina taga 'karfin wanki.

Kan tameer tayi da bokitin a fusace zata rafka masa cikin sauri ta mike tana cewa xanyi wankin.

Wata dariyar 'keta suka saki suna kallon wani sabon ikon allah.

Tana kallo yana rawar sanyi kamar zai shide sbd sanyi ake ga ruwan da aka zuba musu ga 'dakin ko 'kofa baida Tana kallonsa ahaka ta fice tana hawayen ba'kin ciki.

Wankine kamar sunyi shekara basuyi dan harda kayan iya jummai danasu buba dana karimar dana ita ladingo hardana iro da idi.

Jikinta na rawa ta fara wankin ko gani batayi sosai ga hankalinta duk yanakan meer dake can kwance cikin ruwa da sanyi.

🌕🌕👉mamuh geee. 🌕⚜DA'IMAN⚜🌕

Na

MAMUH GEEE

☆dedicated to☆ Husnah bbchoudiallo

96→100

Wankine mai yawan gaske na dukkaninsu hardana iya jummai da 'danta iro, Gana buba da idi hardana karima da ladingo.

A wahalce take wankin jikinta na mazari sbd zazzabin datake ciki ga sanyi dake kadawa sosai Duk radadin datake ciki Gaba 'daya hankalinta nakan tameer data baro 'dakin kwance yana rawar sanyi cikin ruwa ga sanyi da ciwo.

Saida gari yayi haske sosai ta gama wankin dakyar ta mi'ke a duddu'ke tana tafiya dan bazata iya mikewaba.

'Dakin ta nufa tana hawaye dakuma fargabar halinda zata samesa.

Kukane tareda farin ciki sukaxo mata lokaci 'daya sbd a zaune tasamesa jingine da bango yana bude idanu dakyar sbd azaba.

Da gudu ta fada jikinsa tareda sakin wani irin kuka mai ratsa zuciyar mai sauraro.

Saidata sha kukanta kafin ta mike tareda kamasa tana shirin canza masa kaya sbd ajike yake har alokacin. Jakar kayansu ta duba bataga komaiba. Ta sake dubawa da kyau ba kala ko 'daya aciki

Hayaniya tajiyo a tsakar gidan tana saurarawa saita jiyo rabon kayane suke Da sauri ta fita tsakar gidan aiko kayansu kaf

Su idi,da bubah, da iro suka rabe kayan tameer Nawa kuwa kaf karima aka ba.

Ahankali hawayenta suka cigaba da gangarowa ta juya takoma 'dakin tareda zama kusada shi ta cusa kanta a tsakiyar gwiwowinta tana rero kuka sbd.

Kiran tashin hankali ladingo tafara yo mata ta mike ahankali taje fuskarta duk ta kumbura sbd kuka.

Aikin gidan tasata harda 'diban ruwa tana gamawa taje tasiyo tameer koko Tana basa yafara kelayo mata amai. Hankali tashe take kallonsa harya gama Ta goge masa jiki tareda gyare gurin.

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

Rayuwa ta zame musu u'kuba a 'kauyen Tun suna jiran kiran me gari harta daina dan yayi watsi da zancen.

Ladingo kuwa duniya tadawo musu sabuwa dan tasamu bayi yanda takeso duk da itake duk aikin dazasu saka tameer 'din kasancewar yanxu agarin kowa yasan lalurarsa ta juyewar hankali.

Itake aikin gidan kaf Tayi wankinsu kaf Tayi 'dibar ruwa da abincin saidawar ladingo komai yawansa duk da aikin yafi 'karfinta.

Tun yana mata rakin cizon cinnaku harya daina yasaba

Yunwa kuwa tasamu kyakkyawan mazauni ajikinsu dan sunyi wata muguwar rama. Fatarsu ta dafe ta lalace sbd sunma manta da wani sabulu ake wanka Sunyi wani furi furi dasu.

Tameer yadaina ciwo sosai saidai haukarsa data fito muraran dan yanda idan zasu 'dibar ruwa suna tafiya yana tsince tsince Hakama idan sukaje rafi cewa yake saiya fada ruwan yayi wanka Ga yara da suke bibiyarsa suna masa wakar mahaukaci. Abun nadamunta amma ba yanda ta iya.

Tun ana zaginsu da kyararsu har andaina anfara tausaya musu sbd ukubar dasuke ciki sosai. Suturar sawama basuda ita dan kayansu sun ko'de harsun fara yayyagewa.

Ahaka Cikinta ya tsufa sosai kuma hakan take duk wahalar Ta bushe bayan kashi ba komai.

Soyayyarta da kulawarta kullum akan tameer 'dinta suke, shi kadai ke kawo murmushi afiskarta dan duk takallesa takanyi murmushi hardai idan tana aiki yana damunta da shirmensa.

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

Zaune take tana wanke wanke cikin sanyin jiki sbd tun daren jiya takejin ciwo ahankali amma take daurewa dan kota nuna ba me taimakonta.

Tana kallonsa yana wasa da ruwan wanke wanken amma takasa hanasa hartasamu ta gama dakyar.

Gyare gurin tayi ta'dau bokiti tana rintse idanu suka fice zuwa 'dibar ruwa.

Shike rikeda bokitin itakuma tana tafiya ahankali sbd ciwonta yafara tsananta.

Wata mata data shigo 'kauyen rikeda 'yar ledarta harta giftasu saita 'dan dawo tana kallon nazli tace,

Yarinya gidan malam adamu headmaster nake nema dan ya'dan 'bacemun.

Lumshe idanu tayi ta budesu dakyar cikin 'dan kannewa tace, Ya rasu tunda dadewa.

Salati matar tasaki cikin rawar murya tace, 'Yarsa fa tanan? Dan allah nunamun gidan.

Cikin ciwonta daya fara fin karfinta tace, Ni..ni nice 'yarsa.

'Kara dam'ke hannun tameer tayi duk da tana cikin ciwo dan zai iyayi wani gurin.

Akidime ta 'kurawa fuskar nazli ido Sai alokacin matar ta lura da halinda nazli take ciki

🌕🌕👉mamuh geee 🌕⚜DA'IMAN⚜🌕

Na

MAMUH GEEE

☆dedicated to☆ Husnah bbchoudiallo

101→105

Kamota tayi tana kiran sunanta dan 'kokarin durkushewa take kuma har lkcin takasa sakin hannunsa

Matar takalli tameer dakeson kwace hannunsa ya hango kara yanason yaje ya 'dauko. Kamata tace masa tana kamo nazli 'din Kallonta yayi yana son boyewa bayan nazli. Cikin azaba tace bashida lafiyar hnkli.

Kamata tayi suka koma gidan dakyar Kai tsaye 'dakinsu suka shiga zuwa lkcn ciwo take sosai.

Bakowa agidan dan basanan sunje wani 'kauye bikin suna. Kwantar da ita matar tayi dan dama itake karbar haihuwa garinsu.

Cikin ikon allah babu 'bata lokaci ta haihu lafiya 'kalau.

Ruwa matar ta 'dora tayiwa yaron data kirada balarabe sbd tsantsar kyawunsa data gani wanka. Kama nazli tayi tayi mata wanka tas kuma allah yasa bayau su ladingo zasu dawoba.

Nade yaron sukayi axanin bakuwar dan babu kayan daza'a saka masa.

Ido ta 'kurawa yaron tana hawaye dan tasan bazai samu rayuwar jin da'di kamar yanda taso masaba.

Kuka take rerowa harda shesheka matar nakallonta harta gama ta matso kusada ita tace, Sunana INNAH ASMAH Tareda mahaifiyarki nataso akayi mana aure tare Tun rasuwar baffana data mahaifiyarki ban 'kara xuwa garinnanba sai yanxu naxo sbd na duba 'yar rahane ashe har malam yarasu an miki aure.

Hakanan ta kwashe komai kaf tafada mata tana kuka sosai.

Ita kanta innah asmah hawaye take tana sharce majina kafin ta mike tana cewa Nazli wahalarki insha allah takare dan bazan barkiba dake xan tafi.

Mikewa tayi tafice afusace tana sharce hawaye.

Sai alokacin tameer yashigo 'dakin kayansa sharkaf da ruwa dan tunda suka shigo yanacan tsakar gidan yana 'bata ruwan ladingo allah ma yasa basanan.

Da sauri yazo kusa da ita yazauna yana kallon 'dan jaririn dake hannunta yana keta kuka ta rasa yazatayi sai kukan take itama.

Washe hakora yayi yana 'kokarin tabashi saiga innah asmah tayi saurin karbar yaron tareda saka masa kayan dataje tasiyo yanxu.

Duk wani abun bukata tayi musu dan kwananta biyu kafin su ladingo suka dawo sunyi mamakin ganin na haihu amma ganin innah asmah yasa sukayi biris damu dan tace sai bayan sati zata koma.

Tameer kuwa wawa yakoma kan yaron dan rigima yakeyi sosai sai anbashi jaririn Tun innah asmah najin tsoro harta daina dan sosai yake nuna son yaron.

Sati nayi suka radawa yaron suna ZAID Nazli nakiransa da WALEED

Sun 'dan walwale cikin 'yan kwanakin sbd samun cima mai 'dan kyawu da kula da innah asmah ke musu.

Kwananta goma cif ta ha'da kayanta zata tafi da niyyar zata dawo ta tafi dasu wani satin.

Hawaye nazli keyi sosai bayan tafiyar innah dan tasan zasu komama wahalane Amma idan ta tuna daxata dawo ta tafi dasu saitaji wani sanyi aranta.

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

Ahankali dai sai gasu sunkomawa wahalarsu ladingo ga nauyi daya 'karar mata na waleed allah ma yasa tameer takebawashi su zauna 'daki tayita aikinta.

Tun tana lissafin dawowar innah harta daina sbd fiyeda wata uku kenan amma babu ita.

Wahalarsu ta yanzu hartafi tada dan tuni suka 'karmaje dukkansu hardai ita dake shayarwa. Kullum dare kwana take kuka, Ko aiki take hawaye takeyi sbd tausayin rayuwarsu.

Kamannin waleed sun fito sosai da tameer dan kuwa kamar tasu hartayi yawa. Ga wata irin shakuwa dake tsakaninsu danko ita wani xubin yafison tameer da ita.

Muguntar dasu bubah kewa waleed yasa bata bari suna fitowa tsakar gidan kullum suna 'kunshe adaki.

Akwai ranar da waleed yayiwa ladingo 'barin gari aiko buba yayi ball dashi Ladingo kuwa ruwan talginta ta zuba masa ahannuwa harda sumewa yayi Ranar basuyi bacciba kwana sukayi zaune suka kuka harda tameer 'din sbd yanda yaron hannuwansa suka sale ga wani irin kuka dayake sbd zazzabi da azaba.

Komai ya ida jagule musu wuya tayi wuya Ga waleed yagirma sosai harya iya magana Sunkoma suturama saida fadar mai gari taji tausayinsu aka basu kala biyu biyu wanda daga gani kayan sun jima da mutuwa amma haka suka karba suna sawa.

Babbar damuwarta baifi waleed da bayajiba gasu sukuma sukamasa suyi masa dukan tsiya kamar wani 'kato 'dan uwansu.

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

Zaune take tana bawa tameer ruwa sbd ciwo dayake fama dashi tun daren jiya. Waleed ya shigo 'dakin da gudu yana haki yace, Anty kinga wata tana nemanki gatanan xuwa. Zaunar dashi tayi tana cewa, Waleed bana hanaka yawoba. Allah anty banje yawoba ina 'kofar gidafa.

Sallamar innah asmah ya hanata yin magana ta mike da gudu ta rungumeta tareda fashewa da kuka.

🌕🌕👉mamuh geee 🌕⚜DA'IMAN⚜🌕

Na

MAMUH GEEE

☆dedicated to☆ Husnah bbchoudiallo

111→115

Wani wawan haushin kare yaji daga nesa baisan sanda ya juyo da gudu ya fa'da gonar wani wawan jiri da sarawar kai ya ziyarcesa amma baitsayaba saidaya kai tsakiyar titin wanda yayi daidai dakawowar wata mota aguje tayi sama dashi ya zube cikin jin.

Akidime nacikin motar yafito yayo kansa yana salati sbd ganinsa cikin jini Juyosa yayi da sauri dan 'daukarsa yakaisa asibiti tunda shi likitane abun zaixo da sauki insha allah.

Zabura yayi da 'karfi ya ware murya yace TAMEER

Jikinsa har rawa yake yadaukesa yasa amotar ya figeta da wani irin speed sai kano. Asibiti ya wuce dashi kai tsaye aka shige dashi emrgency.

Waya dr ibraheem ahmad ya fiddo wayarsa jiki na rawa ya lalubo wata number ya danna kira.

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

ABUJA

Zaune yake cikin tangamemen palonsa Idanunsa sanyeda farin medicated glass Yayi xurfi cikin tunani da damuwa

Yau tsawon wata shida kenan da allah yabasa sa'ar kubutowa daga 'yan ta'addan dasuka sacesa suka rufe Tunda yadawo yasamu bayanin 'bacewar 'dansa da nazli abakin matarsa datayita kukan munafuncin cewar ba'asan inda sukayiba anyi nema har angaji.

Wannan mugun labarin saidaya haddasa masa kwanciya asibiti tsawon wata biyu a newyork kafin yadawo aka baza bincike tako ina.

Wayarsace tayi ringin harta katse bai dubi inda takeba.

Haj xeenat data shigo palon cikin ado tana she'ka 'kamshi takalli wayar dan ansake kira tamaida kallonta garesa tana zama kusa dashi tareda 'daukar wayar sbd sunan dr ibrhm data gani dan sam tana kasa nutsuwa a duk lkcn dataji yakira alh zaid sbd tsoron yafada masa komai gameda abunda yafaru.

Arikece yake fadin, Alh...alh tameer....gashi nnan asibiti

Wat ta fa'da da 'karfi tana mikewa cikin wani irin tashin hankali Jikinta nan take ya'dau rawa.

Alh zaid kuwa wayar ya warta da 'karfi yana sauraron bayanin dr ibrhm aibai tsaya jin sauranba yafice palon baikobi takan haj xeenat dake daskare agurin tana aman xufa.

Motoci uku na alh zaid da securites suka 'dau hanyar airport adaren dan xuwa kano.

Wuraren asuba suka sauka kano kai tsaye asibitin suka wuce Alh zaid naganin yanda tilon 'dansa yakoma ya yanke jiki yafadi.

Yana farfadowa ba'a tsaya komaiba ya ha'da 'dansa da dr ibrhm suka bar 'kasar zuwa germany.

******** Jinyarsa ake ana kula dashi sosai a garmany 'din dan tuni su haj nurat suka isa germany 'din suma.

Watansa 'daya akwance kuma anasa ran farfa'dowarsa ko wane lokaci.

Haj nurat ce da fannah zaune a'dakin. Haj nurat waya takeda ammah mahaifiyar nyssa tana fada mata yanayin jikin nasa Fannah kuwa chattin takeyi da tsadaddiyar wayarta.

Ahankali yafara bu'de idanunwansa dasukayi masa nauyi sosai yana gani dishi dishi harsuka bu'de.

UMMEE ya fa'da muryarsa bata fita amma cikin sa'a kuwa haj nurat taji hakama fannah.

Rige rigen isa gurinsa suke cikin tsananin farin ciki wanda yayi daidai dashigowar alh zaid

Farin cikin dasuke ciki baya misaltuwa dan kuwa tameer ya warke ras yadawo cikin cikakken hankalinsa kamar kowa.

An sanar da 'yan cairo dabasu sabu xuwa kowa murna yakeyi anata farin cikin.

HMMMMMNN WATA SABUWA KENAN.

🌕🌕👉mamuh geee 🌕⚜DA'IMAN⚜🌕

Na

MAMUH GEEE

☆dedicated to☆ Husnah bbchoudiallo

106→110

Zaunawa sukayi tana lallashinta tace, Nazli kiyi hkr rashin lafiya nayi sosai kuma maigidana ya rasu shiyasa ban dawoba amma yanxu gani nazo kuma ayau zamu wuce basai gobeba.

Sharce hawaye tayi gabanta na faduwa hakanan taji gabanta yafa'di da tafiyar.

Kallon tameer tayi kafin tamaida kallonta ga inna tace, Inna meer bashida lafiya yazamu iya tafiya dashi.

Kadaki damu tunda zai iya tafiya muje damun shiga mota zai aishikenan.

Ha'da 'yan tsummansu tayi tana share hawaye dan sam ta rasa nutsuwa batasan dalili ba.

Kamo tameer tayi inna ta riko hannun waleed dake murnar zasuje yawo. A tsakar gida suka samu ladingo da iya jummai suna she'ka firarsu Suna ganinmu suka 'daure fuska suna harare harare. Inna ce tayi musu bayanin xata tafi damu har xuwa samun saukin tameer.

Harara iya jummai ta watsowa inna tana fadin, Dan wa'innan dangin buxayen masu kama da figaggun kaji to tafi dasu ko aminiyata da 'yayanta sa huta da ba'kin iri. Ladingo kuwa ko kallo basu isheta ba sai ka'da kafarta take.

Ficewa sukayi jiki asanyaye. Dakyar suka samu motar 'kauyensu inna. Tunda suka baro gida takasa tsaida hawayenta tana tunanin yaushene zata samu kyakkyawar rayuwa? Itakenan kullum garari yanxuma batasan wace rayuwa zasuyi acanba.

Da maraice suka isa 'kauyen da 'kafa suka isa gidan inna. 'Dan 'karamin gidan 'kasane mai tsakar gida da 'dakuna biyu sai 'dan 'karamin ban'daki atsakar gidan.

'Daki 'daya tabasu suka share tsaf tabasu tabarma suka shimfida tareda aje 'yan kayansu.

Sanwar abinci inna ta 'dora musu tana gamawa tabasu sukaci suka 'koshi nan waleed yafara wasarsa itakuwa share gidan tayi tas Ana kiran sallah sukayi sallarsu har lkcn kwanciya yayi suka kwanta. Washe garima da kanta ta gyare gidan tayi duk aikin gidan inna na yaba mata sosai sbd tayi 'kokari.

Chanjin rayuwa yazo musu sosai sbd yanxu harsuna dariya su 'kyakyata Ga yunwa tuni ta gudu ajikinsu Sunyi 'danyi kyawun gani dan yanzuma kamannin tameer da waleed ke 'kara fita abun har tsoro yake bata Ga muguwar sha'kuwar dake tsakaninsu sbd waleed yasan tameer shine babansa. Hankalinsu yanxu akwance yake basuda matsala sbd inna asmah nada rufin asiri sosai sbd tanada dabbobi da yawa ga sanaar saida kayan 'kulle 'kulle datakeyi.

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

4 month later

Tun jiya takejin jikinta asanyaye da faduwar gaba har saida inna ta tambayeta lafiyarta 'kalau kuwa Tace lafiyarta 'kalau.

Zaune suke tsakar gidan inna na 'daura kuka datake saidawa nikuma ina wanke wanke.

Waleed da tameer ke wasarsu suna dariya sai waleed ya 'dale bayan tameer ya goyasa yazagaya tsakar gidan dashi ya saukesa saiya juya waleed yana 'kokarin shima wai waleed 'din ya goyasa.

Daria muka saki duk mu duka waleed ya gudo bayan inna yana cewa, Inna dubi wai saina goyasa babba dashi fa.

Daria inna tayi tana cewa, Aini bana shiga tsakaninka da babanka nazo naji kunya anjima dan nasan shiryawa zakuyi.

Da gudu waleed yabar bayan inna yana daria shima tameer dariyar yake Nazli ta 'kura masa ido sbd kyawun dataga yayi mata sosai wanda rabon datayi masa irin kallon harta manta Wani sabon sonsa takeji yana sake tsima azuciyarta.

Waje sukayi dukkansu suna daria itakuwa taci gaba da aikinta inna ma hankali ta mayar anata aikin.

'Boyewa waleed yayi bayan bishiyar 'kofar gidan tameer yawucesa batareda yagansa ba Shikuwa yana ganin ya wuce fito ya zauna 'kafar gida yana wasar 'kasarsa.

Tafiya yaketa famanyi shi ala dole saiya kamo waleed haryayi nisa sosai. 'Karyen 'kauyen yakai ammai bai tsayaba sai kawai yaci gaba da tafiya tun yana gani har duhun mangariba yasawo kai nan take tsoro yafara kamasa Yafara waiwaye yana tafiya da sauri sauri.

Har duhu yayi sosai gudu yake ketawa adajin kamar ba mutumba.

Daidai wata gona yakai ya tsaya cak kamar an tsaidashi.

Gonar wani bawan allah ce dayayiwa wani kyakkyawan asiri sbd 'barayi duk wanda yashiga gonar indai yanada asiri ajikinsa to zai karye ko wane irine.

Soyake ya keta gonar ya wuce yakasa dan tsananin tsoro sbd titin daya hanga motoci na wucewa da mugun gudu dazarar ka wuce gonar.

Juyawa yayi da sauri dan komawa inda yafito.

🌕🌕👉mamuh geee 🌕⚜DA'IMAN⚜🌕

Na

MAMUH GEEE

☆dedicated to☆ Husnah bbchoudiallo

116→120

Gab da magrib ta le'ka 'kofar gidan taga waleed ka'dai tace, Waleed kudawo gida lkcn sallah yayi Ina meer 'din yake?

Kwaso kayansa wasansa yayi yana cewa, Tun tuni fa yatafiyarsa yawo nika'dai nake wasana.

Dam. Gabanta ya buga tareda ha'de wani yawu da'kyar tafito wajen gaba 'daya ko hijab babu ta riko waleed ta jijjigasa da 'karfi tace,

Waleed ina yatafi? Kuma tun yaushe?

Anty tunda muka fito baiko tsayaba fa yawuce yabi can. Yayi mata nuni da hanyarda tameer 'din yabi.

Cikin gidan takoma a ki'dime jikinta na zuba wani irin 'bari tajawo hijab tasaka a birkice tana 'kokarin ficewa inna tayi saurin kiranta tana cewa, Lafiyarki kuwa inata tambayarki kina 'kokarin ficewa hijab ajuye?

Hawaye suka tsinke mata cikin rudewa tace, Inna meer bayanan wai wai baya 'kofar gida ya..ya..y sai kawai ta juya ta fice da sauri Hijab inna tasaka tabi bayanta da sauri sukabi inda waleed yake nuna musu yabi.

Yawon nemansa suka fara suna tambayar duk wanda suka hadu dashi har akayi magrib babu wata alamar ganinsa.

Kuka take wanda ya gagara tsayawa jikinta Sai mazari yake saida inna ta ri'keta sbd ganin yanda take neman xubewa dan gaba 'daya a ki'dime take Waleed ma dayaga halinda antyn tasa take ciki saiya fara kuka.

Har 'karfe goman dare suna yawo saida suka zagaye 'kauyen tas amma babu alamarsa.

Da'kyar inna takamota dajan 'kafa suka dawo gidan suna shiga ta sulale 'kasa tareda sakin kuka da 'karfi tana kiran sunansa.

Kuka sosai take tana kiran sunansa cikin wani irin ra'da'di da ciwo a xuciya,

Yanda take kukan ne kamar ranta xai fita cikin wani irin hali yasa hawaye tsinkewa inna na tausayinta dakuma tunanin wane hali tameer 'din yake.

Kamata inna tayi tana 'kokarin tadata sai kawai taga ta zube idanuwanta arufe.

Salati tasaki tana yayyafa mata ruwa cikin ru'dewa dan yanda take ganin wani irin tashin hankali daga nazli 'din dan tasan tameer ya 'bata amma tasan nazli zata shiga mummunan halinda yafi wanda zaije yashiga sbd ganin idonta taga yanda naxli ke masifar sonsa fiyeda komai.

Tana farfadowa tasaki siririn kuka ahankali inna takaita 'daki tana bata 'karin gwiwar zaa gansa insha allah.

Readers Also Read

More by Autar Alheri