Da'iman complete hausa novel - Chapter 6
Da'iman complete hausa novel Chapter 6: Da'iman complete hausa novel Chapter 6. Sam su haj karima da haj bilki babu wanda yagane nazli ko kusa sbd muguwar…
3,343 words
Sam su haj karima da haj bilki babu wanda yagane nazli ko kusa sbd muguwar canxawar datayi sannan kuma dama can ba wani cika ganinta sukayiba tunda kullum tana sama.
Sun fara hidimar bikin daya kawosu dan gobene xaa daura aure amarya ta tare kowa ya watse.
Sosai fannah ta fara yabawa da halin nazli sbd yarinyar akwai nutsuwa da tsafta ga wani irin class datake dashi duk da tana 'yar aiki dan bata shiga lamarin kowa saina ita data 'dauketa aiki. Murmushi tayi tana cewa, B nasan zakaji dadin wannan abun danayi mana tunda nasan sarai kana bu'katar mai kulada tsaftar part 'dinka dan nafisat aikin yayi mata yawa da bazata iyayinsa yanda kakesoba.
Ranar dazasu wuce kuka take wiwi akan rabuwa da waleed amma haka tayi masa wayo suka fice.
Aharabar gidan ta tarar dasu sun fito suka shiga mota akayi airport dasu.
Jirgi suka shiga babu bata lokaci suka 'daga xuwa abuja.
Da maraice suka isa motar gidan haj bilki tazo 'daukarta Itama haj karima direbanta yazo 'daukarta. Suma motarce tameer ya aiko 'daukarta airport.
Suna isa gidan kai tsaye 'dakinta ta wuce nazli na biye da ita sbd babu kowa a gidan Dad baya 'kasar yayi tafiya, Tameer ma bayanan yaje lagos meeting hakama mum tana cikin gari sai dare zata dawo.
Akwatinta da nazli ta jawo mata tayi mata nuni data shigar dashi bedroom. Kaiwa tayi tadawo ta tsaya gefe atsaye bakomai hannunta dan fannah tace kada tadauko kayanta zata siya mata kaya idan sunzo nan 'din dan idan b 'dinta yaganta a yamutse zai iya cewa bayason aikinta dan bayason 'kazanta ko ka'dan.
Nafisa fannah takira da landline 'din palonta tace tazo yanxu tana nemanta.
MUCH LOVE😍😍😍😍😍😘😘😘😘😘
🌕🌕👉mamuh geee 🌕⚜DA'IMAN⚜🌕
Na
MAMUH GEEE
☆dedicated to☆ Husnah bbchoudiallo
146→150
Turo 'kofar palon fannah 'din tayi tareda sallama ta 'karaso kusada nazli ta tsaya tareda cewa, Gani.
Hankalinta nakan wayarta Tana 'kakarin kiran b 'dinta tace, Nafisa wannan wadda zata ringa kula da tsaftar dakina da palona dana b ce kuma ni takewa aiki ba kowa ba atakaice komai nawa dana b Is her responsibility ta kula dashi. Daidai nan tameer yadau wayar ta mike tayi 'daki tana waya dashi.
Atsanake suka juyo dan gaisawa da juna Lokaci 'daya kamar wa inda wutar lantarki taja kowanne yaja baya da sauri cikin mugun tsananin ki'dima.
Nafisa ce tayi 'karfin halin 'daga hannu tana nunin nazli 'din tana cewa, Nazli kece? Ko kuwa idanuna ne?
Nazli datafi firgita sosai dan nan take tafara tunanin kaddai fannah 'yar uwar tameer ce takawota gidan aiki? Idan kuwa hakane kiketa zasuyi saita kaisu gurin tameer Tameer 'din dabatasan inda yakeba Yanacan 'kilama cikin mugun garari.
Girgixata nafisa tayi da 'karfi jikinta na rawa ganin sai zubar hawaye take ba magana.
Murya na rawa cikeda damuwa da tsoro tace,
Nafisa inane nan? Ina haj xeenat? Wacece wannan fannah 'din? Wane gidane nan?
Duk arude take watsowa nafisa tambayoyin Itama nafisar arude take Kawai saita damki hannun nazli tajata sukabar palon.
'Dakinta dake gurin 'kofar kicin tajata ciki ta dannawa 'kofar key har alokacin duka hankalinsu atashe yake su duka.
Jiyowa nafisa tayi a kidime take cewa,
Nazli nan ba gidan kowa bane face gidan alh zaid da iyalansa,
Haj zeenat nanan acikin gidan,
Sun baro can gidan sun dawo nan ne tun bayan da alh zaid yadawo yatarar da 'bacewarku yakasa zama awancen gidan,
Fannah 'kanwar sir tameer ce daya dawo da ita nan tun bayan dawowarsa daya samu lapiya.
Tunda nafisa tafara koro mata bayanan hankalinta da nutsuwarta suka fara barin jikinta amma Kalmar nafisa ta 'karshe ita tafi dukan zuciyarta ta razanar da ita fiyeda tunani.
Kamar bebiya tafara nuni da hannu tana cewa, Meer...meer...a..a...ina Meer...ya...ya...
Ganin takasa 'karasawa dan a birkice take yasa nafisa ta gya'da kai tace, Tabbas nazli sir tameer ya warke yanzu yana cikin cikiakkiyar nutsuwarsa. Dr ibrhm yakira alhaji yace ya bugesa da mota can hanyar wani 'kauye a kano Akayi kasar waje dashi kuma yana farfadowa cikin hankalinsa yatashi wanda kowa yayi mamakin hakan.
Nazli babban abun ba'kin cikin dazan fada miki yanxu shine SIR TAMEER BAISAN KOMAI DAYA FARU LOKACIN RASHIN LAFIYARSA BA ma'ana BAISAN DAKEBA BAZAI TINAKI BA.
Sulalewa tayi 'kasa tana neman shi'dewa komai na duniyar na juya mata Jitake kamar zuciyarta zata buga Gaba 'daya zantukan nafisa sun hargitsata batamasan wane tunani zatayi ba.
Sai alokacin wani irin kuka mai ciwo yazo mata ta 'kankame jikinta tanayi abunta sosai. Yanda take kukan ne ya masifar kashe jikin nafisa dan tana tunanin akwai abunda yafaru akan rabuwarsu.
Zama tayi kusada ita tanason ta rarrasheta amma yanda nazli ke kukan tana bukatar abarta tayi abunta kodan samun saukin radadin zuciya sbd kalar kukanta ya bayyana zuciyarta tana cikin wani mugun hali.
Tsoro nafisa tafaraji ganin nazli na neman sha'kewa ahalinda take ciki Ta dafata cikin tausayi tana shirin yin magana nazli ta gwalo mata manyan idanunta dasukayi jajir sbd kuka. Girgixa kai tayi murya ashake tace, Dan allah ki fitar dani agidan nan yanxu, Banason bayanke dakika ganni wani yaganni musamman haj xeenat Bakuma zan iya jurar ganin meer 'dina yaganni amma baisanniba, Bai tunaniba, 'Karshema yanamun kallon 'yar aiki Baxan iya jure wannan ba Gwara natafi nakoma nayi jinyar xuciyata dazata rayu da tsananin sonsa da damuwar rashinsa 'karshe ta mutu da sonsa.
Nazli kece wadda duk masoyan alh da 'yayansa ke adduar su samu sbd nagani nakuma ji ajikina kece zaki kubutar dasu daga sharrin hajiya.
Mikewa tayi tana nufar 'kofa nafisa tayi saurin shan gabanta tace, Nazli ina cikin jikinki dakika tafi dashi?
Cikin kuka tace, Babushi ya xube.
Garin yaya yazube? Bansaniba nima
Tun yaushe? Bazan iya tunawaba
Bazai yiyu ba sbd kinason tameer nasani fiyeda kanki dan haka joda cikinsa dake jikinki ya zube nasan bazaki taba manta ranar ba. Dan haka tun yaushe ne cikin ya zube?
Shekara hudu. Tafada da 'karfi tana kuka dan duk tambayoyin na nafisa a jere take matasu duk sun rudata dan dama aruden take.
Ja baya nafisa tayi tareda sakin ajiyar zuciya tace, Shekarar abunda kika haifa hudu kenan nazli Dan banyarda da cikin yafitaba.
Rintse idanu tayi tana jingina da bango hawayenta naci gaba da ambaliya. Gidan takeson bari danji take makar zata 'kone tsabar ciwon zuciya.
Cikin hawaye da sanyin murya tafadawa nafisa komai tun bayan barinsu gidan 'karshe ta 'dora da fadin, Rayuwata ba 'daya daga cikinsu wato meer ko waleed to tabbas batada amfani agareni. Inasonsu fiyeda kaina, Inason meer tun bansan soba, Inason duk wani abu daya dangaci meer 'dina shiyasa nakeson waleed fiyeda numfashi sbd duk nakallesa fuskar meer da jinin meee nake gani yana yawo ajikinsa. Inason meer 'dina, Inason meer 'dina kuma meer 'dina yana sona kaman yanda nake sonsa Amma wannan na yanzu ba meer 'dina bane sbd meer 'dina bazai mantani ba, Bazai daina sonaba, Meer 'dina ya mutu ya barni daga yanzu zanyi takabar meer 'dina Nida waleed 'dina munzama marayu mun rasa meer 'dinmu wannan tameer ne yafi 'karfinmu.
Kukan tausayinta nafisa keyi tana lallashinta.
🌕🌕👉mamuh gee 🌕⚜DA'IMAN⚜🌕
Na
MAMUH GEEE
☆dedicated to☆ Husnah bbchoudiallo
151→155
Kiranta fannah tayi ta hanyar landline 'din 'dakin nafisa Nafisa tafada mata suka mike gaba 'daya zuwa can 'din.
Kaya dake gibge kan kujera ta nuna mata tareda cewa, Ki 'dauka ga kayanan zan siya miki wasuma sbd inaso ki ringa wanka biyu ayini tareda canza kaya dan ki kasance atsaftace koyaushe. Na yaba da tsaftarki amma inaso ki 'kara dan kiyaye duk abunda zai 'bata ran b 'dina.
Ki gyara 'dakina yanzu bari ni nashiga wanka. Bedroom tashige tana tubewa tashige toilet.
Nafisa ta kwasar mata kayan sta fice itakuma ta gyare gurin cikin sanyin jiki. Tana gamawa ta fito kenan yayi daidai dashigowar haj xeenata dasu haj karima harsun samu fitowa daga dawowarsu dan bata rahoton gurin boka dasukaje can kanon.
Zabura tayi da 'karfi taja baya tana nuna nazli tareda ha'de wasu wahalallun miyau.
Kallon rashin fahimta suke mata haj bilki takalli nazli tamaido da kallonta ga haj xeenat tace, Me aikin da fannah ce datasa aka samo mata tun akano fa.
Afirgice takallesu tace, Kun kuwasan me kukayi barin wannan tsinanniyar tazo mana da wannan Ta nuna nazli a rude.
Haj karima tace, Xeenatu kiyi mana gwari gwari mana munkasa gane me kike nufi.
Karima nazli ce fa matar shegen tsinannen yaron nan. Meyasa kuka bari tazo da ita? Na shiga uku ni zeenatu meyasa abubuwa ke neman tabarbaremun ne?
A kidime suke kallon nazli datati 'kasa da kai tana adduar allah yasa su koreta yanzu basai gobeba tabar gidan dan tabbas bazata iya rayuwa agida 'daya da tameer ba.
Wata wawuyar dam'ka haj xeenat takai mata ta shaqota tana fadin, Zo tsinanniya munafuka kibar gidannan yanxu tun wani daga cikin alh ko tameer basu gankiba duk da nasan yanxu baisankiba ko kukuwa wlh nayi miki mummunar kisa.
Janta tafara tanajin wata irin tsanarta kamar ta shaqeta ta mutu ta huta.
Riqeta haj bilki tayi da sauri tana ha'da zufa tace, Aa wannan ba itace mafitaba agaremuba dan taga inda suke yanxu zata iya dawowa ta baya ta tona asirin komai ta gudu kuma kunga basanin inda takeba zamuyi bare mu 'dau fansa ko mataki akanta.
A ru'de haj xeenat tace, To meye abinyi dan namatsu tun kafin shegiyar can ta fito taganmu ahaka tayi zargin wani abin.
Haj kareema tace, Mafita 'dayace mu barta anan muna ganin duk wani motsinta da abunda takeyi duk ranar data gudu ko ta tona mana asiri wallahi saimun bashi guba ya mutu tunda shine abunda tafi so fiyeda komai tunda allah ma yasa babu shegen cikinta dayanzu masifar dazamu shiga saitafi haka.
Jinjina kai sukayi cikin gamsuwa da bayaninta haj xeenat ta 'dora da fa'din, Kuma duk rintsi kadaki bari alh yaganki kuma kadaki bari tsautsayi yasa ki nuna kinta'ba ganinmu arayuwarki dan kuwa da kaina zan dama guba na basa kina kallo yasha, Bake bashi, Ki tsaya amatsayinki na me aikinsa da tsinanniyar qanwarsa. Idan kikayi ganganci to kisani da rayuwarsa kike wasa dan yanzu tana hannunki.
Ficewa sukayi batareda sun tattauna abunda yakawosuba.
Kukandata risga adaren bai fa'duwa sbd abun yazo mata ba yanda tasoba. Meyasa koyaushe tameer ne abunda kowa ke amfani dashi gurin quntatar da ita? Meyasa tameer yazama wanda zata iyayin komai akansa har ayanzu dasuka zama duniya daban daban? Tameer shine farin cikinta, Shine baqin cikinta, Shine damuwarta, Shine buqatarta. Kuma shine weak point 'dinta. Yanzu gashi once again zatayi rayuwar wulakanci acikinsu akansa duk da baimasan tanayiba. Amma koba komai zata zauna tayi gadin Koda garin haka zata rasa rantane.
Koda garin ya waye fuskarta ta kumbura suntum ko gani sosai batayi amna haka taje tayi gyaran dakin fannah tsaf.
******** Sannu ahankali ta 'dan saba da fannah sbd tana janta ajiki sosai tana kula da ita kamarba 'yar aiki ba. Wasu lokutan kiranta take su zauna tana janta fira duk da ita bata sakewa sosai.
Abunda ta lura dashi shine tana tsananin son yayanta sbd takanas ta 'dauketa takaita shago tayo mata siyayyar turaka masu kyau da qamshi da kaya sosai duk dan sbd kada yayanta shaki wari ko tsami idan tana masa aiki.
Itadai damuwarta duk kayan yawancinsu dogayen rigunan kantine masu kyau da 'dan kama jiki. Amma haka take sakawa atakure tana aikin.
'Bangarensu haj xeenat kuwa ido sosai suka saka akanta.
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Duk inda nutsuwarta take bata jikinta yau dan yau tameer zai dawo Tun safe aka bu'de mata sashensa amma takasa shiga ta gyara saida nafisa takama hannunta suka hau saman har cikin tsakiyar palonsa kafin ta juya ta fita.
Lumshe idanu tayi tana tsiyayar hawaye. Komai na palon tsaf yake sai 'kamshi dake tashi duk da 'dakin ya kwana biyu bakowa.
Daqyar ta lalla'ba kanta ta gyara palon da bedroom ta fesheshi da airfreshner masu da'di ta kukkuna ac ta rufo qofar ta fice.
Girki na musamman sukayi hadda fannah 'din sai farin ciki take ga aminiyarta meenah tuni ta iso taci wani irin ado dan tarbar tavin ranta.
Suna gamawa suka jere a dining fannah tayi gurin wanka bayan ta umarceta da itama taje tayi wankan dan driver yaje 'daukarsa daga airport.
🌕🌕👉mamuh geee 🌕⚜DA'IMAN⚜🌕
Na
MAMUH GEEE
☆dedicated to☆ Husnah bbchoudiallo
161→165
Cikin rashin bawa xancen mahimmanci yace, Tunda kunaso zan duba nagani.
Mikewa yayi yabar gurin yana xuba hannuwa a aljihun wandonsa.
Dai dai xai shiga 'dakin ita kuma ta fito 'daukeda glass cup din fresh milk sukayi wani wawan karo Fresh milk 'din tazube ajikinsu gaba 'daya tayi baya da qarfi cikin tsoro aikuwa ta taka wadda ta xuba a qasa santsin tiles yayi mata mummunan ja ta tafi da qarfi zata xube Wata fixga yay mata ta fado masa da qarfi saikuma suka zube gaba 'daya.
Fannah dake tsaye ta dariya ta kufce mata dan tun qarar faduwar cup 'din ta taso dan dubawa komai akan idonta yafaru.
Dariya take sosai kamar 'yar bby sbd ganin yayanta kwance cikin madara har a fuskarsa ga nazli itama duk ta 6aci da madarar sai suka koma kamar wasu yara.
Saurin tashi tayi daga jikinsa ta bar gurin da sauri idonta na qoqarin kawo ruwa dan haduwar jikinsu ya zaburo mata da tsimin sonsa datake neman dannewa.
Mikewa yayi yana ha'de fuska yayi hanyar stairs dinsa. Gaban madubin bedroom 'dinsa ya tsaya sai kwai yasaki murmushi dan komawa yayi kamar yaron da yayi 'banna.
Wanka yayi yayi sallar magrib yazauna palon yakira fannah.
Da sallama tashigo palon itama ta canxa kaya tana 'daukeda tray 'din farfesun kifi da akayi masa fannah na bayanta. Ajewa tayi tana mikewa fannah tace, Nazli ki xuba masa saiki 'dauko ruwa da drinks ki kawo masa.
Riko hannunsa tayi tace, B pls get married, I really want to see you happy kuma inason naga 'yan babys sun fara kirana aunt. B pls do dis for me qnd marry my friend meenah. Na yaba maka da ita and you knw i always choose wats best for you. She's very nice, Kind and gud..bayan wannan she really loves you.
Kallon tv yake yana saurarenta jin muryarta ta fara rawa kaman xatayi kuka yasa ya juyo aikuwa hawayen take Jawota yayi jikinsa yana cewa, Little youre askin for sumtin dat i dnt really tink i can do for you. Marriage is not a joke or sumtin simple. Its abt my future,my happiness my.....
Daz y i want you to get married b bcos i want to see u live a happy life.. Pls pls b do this for me, Do this for ur little sister.
Zanyi tunani little but for now pls kibar xancen okey? Kai ta 'daga cikin tana murmushi.
Miqewa tayi xuciyarta na bugawa da qarfi kamar zata fashe. Kishinsa takeji yana kona zuciyarta ta fice da sauri tabar palon ko ruwanma bata 'dauko masaba sai dai fannah ta kawo masa.
Sosai ya lura da yanayin data shiga amma ya basar sbd baisan dalilin shigarta halinba.
Kuka ta la6e ta risga a 'daki har saida taji kanta na sarawa kafin ta lallashi kanta ta fito.
Da daddare harta kwanta fannah takira wayarta data siya mata dan irin haka.
Nazli pls ki kaiwa b hot coffee yanxu yanacan yana jira.
Kicin ta nufa ta 'dora yanayi ta juye tadauka ta nufi 'dakinsa.
Apalo ta tarar dashi zaune da farar singlet da farin dogon wandon bacci mai taushi yana aiki da laptop.
Duqawa tayi ta aje tray 'din akan center table 'din dake gabansa, Qamshin turarenta ya daki hancinsa ya lumshe ido batareda yakalli gefen datake ba.
Mikewa tayi zata fice saitaji tanason kallon fuskarsa ta juyo ahankali idonta tab da hawaye. Juyowarta tayi daidai da 'dagowarsa idanunsu suka shiga cikin na juna.
Qurawa juna idanu sukayi Tsantsar damuwa yake hangowa a idanunta yayinda ita kuma take hango rayuwarta a idanunsa.
Hawayene suka gangaro mata ta juya da gudu ta fice tana toshe bakinta sbd kukan dayazo mata.
Qofar yabi da ido cikeda mamaki Dan iya tunaninsa magana bata taba shiga tsakaninsu ba amma yanayin yanda ta kallesa kamar tasanshi yayi mata wani laifi.
Shafo fuskarsa yayi yana ayyanawa aransa akwai wata damuwa atare da ita.
********** Bayan 'dan lokaci ya amince da maganar auren meenah badan yana sonta ba sai dan yanda fannah ta damu sosai akan zancen dan shi sam beyi wani tunanin xai iya samun lokacin kula mace bare soyayya ayyukan gabansa ma kawai sun ishesa arayuwa.
Meenah,haj xeenat,haj kareema,haj bilki da fannah ji suke kamar su taka kan jariri sbd farin ciki, tuni aka fara shirin biki sbd har dad yazo ankai qarshen komai. meenah tuni ta dawo gudan da xama dan idan ba ita ta nemesaba baya bi takan zancenta saiya xama itake zuwa fira 'dakinsa.
🌕🌕👉mamuh geee 🌕⚜DA'IMAN⚜🌕
Na
MAMUH GEEE
☆dedicated to☆ Husnah bbchoudiallo
166→170
Zaune suke a garden 'din gidan yana waya dasu ammah akan sha'anin bikin yace suyi zamansu basai sunxo ba bayan bikin zasuzo tareda meenah 'din.
Meenah dake zaune taredashi tasaki wani murmushin farin cikin samun cikar burinta dan yanda takeji ko kisa xata iya akan tasamu tameer.
Miqewa yayi sbd umminsa haj nurat data karbi wayar zasuyi magana kasancewar yasan batason auren da meenah yasa yatashi ya zagaya yana wayar 'dayan hannunsa na sanye cikin aljihun 3quater jins blue dake jikinsa da farar body hug.
Yana cikin yin wayarne yaringa jiyo sheshshekar kuka natashi ahankali. Ignoring yayi yana cigaba da wayarsa.
Sautin kukan yafara yawo a kunnuwansa har baya iya fahimtar me umminsa ke cewa, Ya rintse idanunsa yanason kukan yadaina damunsa amma ina saima qara shigarsa yake haryana dukan zuciyarsa.
Bayan flowers 'din gurin ya nufa sbd daga can kukan ke fitowa.
Duqe take tasaka kai atsakiyar qafafunta tana rero kukan. Bayanta ya kalla ya gane 'yar aikin nance. Juyawa yayi yana 'bata fuska yana jin haushinta aransa na yanda takeda damuwa takasa fa'da ataimaka mata tunda tasan fannah zata iya taimaka mata da koma nawane.
Cak ya tsaya xuciyarsa na tantama sbd sunansa dayaji ta fa'da cikin kuka.
Tameer,meer meyasa rayuwata take wahala haryanxu akanka? Meyasa zan zauna dan ganin wannan baqar rana agareni duk dakai farin cikine agurinka. Waleed 'dina zai tabbata a maraya kenan shima baqar rayuwar danayi ita xaiyi sbd rashin mahai.... Bata qarasaba kukanta yaci qarfinta duk da bata bari sautinsa yafuta ba.
Xuru yayi qwaqwalwarsa a cunkushe dan baisan tunanin dazaiyiba. Baimasan me zancen nata yake nufiba, To amma meyasa sunansa yashiga zancen nata? Kodai bashi tameer 'din ba. And waleed? Who is that waleed she's talkin abt? Is he her hus...
Juyawa yayi yabar gurin dan tuni kansa ya fara sara masa. Baikoma takan meenah ba yawuce 'daki kai tsaye.
Da daddare data kawo masa fresh milk ko kallonta baiyiba sbd bayason yaringa damun kansa da abubuwan daba serious ba.
Juyawa tayi ta fice jiki asanyaye kamar mara lafiya.
Bayan ta fita saiyaji yana buqatar coffee sai bai nemi fannah ta turo masa ita ya miqe yasauko dakansa dan yasa nafisa tayi masa sbd ita 'din ya lura kaman tana cikin tough time.
Ba kowa apalon dan haka ya nufi qofar 'dakin dan qwanqwasawa Hannu ya 'daga zai buga maganar nafisa ta daki kunnansa,
Nazli pls kadaki bari ayi wannan auren ki fito ki fa'da komai Ki bayyana musu waleed da gaskia sbd da anyi wannan auren babu wata mafita dan kuwa burinsu yagama cika akansu. Kuma dolene sir yasan gaskia wata rana dan haka gwara ki sanar ma......
Cikin tsananin kuka tace, Nafisa babu gurina arayuwarsa yanxu, Yana cikin farin cikinsa bazan katse masashiba dan tarayyata dashi ba abunda yaja masa sai wahalar rayuwa da qasqantacciyar wahala.
Kasa sauraron sauran yayi yajuya yabar qofar 'Daki yakoma yakasa zama ya kasa tsayuwa so yake ya gano me suke nufi amma bai ganoba qarshema ciwo kansa yafara saiya kwanta kawai.
Tundaga lokacin yafara saka ido akanta sbd hankalinsa ya kasa kwanciya akan xancensu duk da yanada tabbacin wani tameer ne suke magana akai.
************** An fara shagalin biki sosai dan dukiya alh zaida da tameer suka sake musu anata shagali duk da dad bai dawoba sai saura kwana 'daya 'daura auren.
Shagali sukeyi sosai duk da angon baida lokacinsu saisu ka'dai suke bidirinsu sudai suga an 'daura auren.