Kenza eBookz

Da'iman complete hausa novel - Chapter 7

Da'iman complete hausa novel - Chapter 7

Da'iman complete hausa novel Chapter 7: Da'iman complete hausa novel Chapter 7. Duk iya yanda ta kama kanta sosai ta danne xuciyarta hakan bata faruba sbd…

3,332 words

Duk iya yanda ta kama kanta sosai ta danne xuciyarta hakan bata faruba sbd muguwar rama tayi sbd tsananin damuwa da tunani dan yanxu kukanma ya daina zuwa saidai idanuwanta su ka'da suyi jajir. Fannah da kanta tasata agaba tace nazli bakida lafiyane ko kinada damuwar zama damune? Kai kawai ta girgixa mata. Kula da abincinsa yana kanta dan tun fara biki fannah take jaddada mata hakan.

Toilet 'dinsa take wankewa cikin cikin tsautsayi bakin taje kunna tab saita kunna shower aiko ruwan sukaxo da qarfi nan take suka jiqata jagab. Dan qaramin tsaki rana kallon yanda ta jiqe gaba 'daya har gashinta. Sanin bayanan bakuma kuma baya dawowa sai maraice yasa ta Xame hijab 'dinta ta shanya a toilet din hakama doguwar rigarta danso take kafin tagama sun 'dansha iska. Bra ce fara qal ajikinta da farin under skirt tsaf dasu kamar sabi sbd sosai fannah ke siya mata duk wani abun buqata.

Zaune yake a sit 'din baya yana sanye da suit black masu red tie sai qamshi yake zubawa driver na tuqasa. Wayarsace tayi qara ya duba saiyaga p.a 'dinsane cikin qasaita ya 'daga wayar. P.a dinsa yace, Sir am sorry walh meeting 'dinnan sun aiko wai sunada babban uxuri an 'daga sai gobe kuma.

Kasa magana yayi sbd haushi sai kawai ya datse kiran ya kashe wayoyinsa gaba 'daya yace driver yamaidashi gida yama fasa xuwa office 'din yau gaba 'daya.

A gate 'din farko yace driver ya ajesa ya aikesa office shikuma ya taka ya 'karasa wanda hakan ya hana sam tasan da yadawo.

Dai dai qofar shigowa palon yaci karo da fannah tana riqeda coke ahannunta tanasha zata fita cikin sauri dan xuwa gidansu meenah sbd yaune suke qunshi.

Gaba 'daya coke 'din ta 6atasa Ya rintse idanu cikin takaici kafin ya wuce da sauri yana ce mata ta tafi kawai tunda yaga she's in hurry.

Yana shiga palonsa yasawa qofar key dan bayason adamesa wanka kawai xaiyi ya huta.

🌕🌕👉mamuh geee 🌕⚜DA'IMAN⚜🌕

Na

MAMUH GEEE

☆dedicated to☆ Husnah bbchoudiallo

171→175

Yana shiga bedroom 'din ya kalli jikinsa yana 'dan yamutsa fuska dan yaso yana dawowa ya kwanta ya huta amma yanxu saiya kuma wani wankan.

Tu6ewa yayi ya 'daura farin towel a qugunsa kyakkyawan jikinsa da lafiyayyar fatarsa sai sheqi suke alamar hutu daya ratsasu.

Kai tsaye ya bude qofar toilet 'din yashiga tareda rufowa.

A firgice ta 'dago daga duqen datake tana canxa ruwan cikin bathtub.

"Ohh my god" ya fa'da yana kare idanuwansa da hannunsa cikin wani irin tsoro da ganin dirinta daya kusan tafiya da numfashinsa dan nan take yaji wata sha'awa ta taso masa.

Gabaki 'daya rikicewa tayi tama rasa yazatayi ta fito dan wani santsi ke janta yana maida ita tama kasa fitowa bare takai gurin kayanta.

Jin tasaka fitowa sai zamewa take yasashi matsowa ya miqa mata hannunsa danshi amatse yake data fice dan ya rikitu sosai ga qamshin turarenta daya cika gurin.

Qaf qaf tafara da idanu tana sake qoqarin fitowa batareda takama hannun nasaba.

Zamewa tasakeyi shisaima tabashi daria ya saka hannuwansa biyu ya 'daukota gaba 'daya aiko bai qarasa fitowa da itaba santsi yajasu gaba 'daya suka fa'da cikin bathtub 'din hannunsa ya bugi shower saiko ta fara sako musu ruwa.

Itace a qasa shine asamanta jikinsu ya ha'de sosai gashi babu me kaya ajiki acikinsu Nan take suka shiga wani yanayi sbd body contact dasuka samu.

Qurawa juna idanu sukayi basako qyaftawa duk da ruwan shower dake xuba akansu.

Hannu yasa ahankali ya matsar da dogon gashinta daya jiqe ya 'dan hawo gefen fuskarta.

Cikin wani salo ya janye da gashin yana kallon tsakiyar idanunta.

Shafo gefen fuskarta yayi har xuwa wuyanta cikin wani salo Taja numfashi ahankali tareda lumshe ido. Kasa bude idonta tayi sbd fuskarsa dataji tana matsowa xuwa tata. Da sauri numfashinta ke fita har qirjinta na 'dagawa yana komawa.

Qirjin ya qurawa ido hankalinsa na qara ficewa daga jikinsa sbd ganinsu farare tas acike tsaye acikin bra 'dinta suna daqawa suna koma sbd numfashinta dake ja.

Hannu yakai ahankali ya shafosu cikin wani salo ai 'dauke huta tayi ta bude baki numfashinta na fita ahankali ya maida kallonsa ga 'dan bakinta bai tsaya komaiba ya shigar da nasa cikin nata 'din.

Ahankali yake kissing 'dinta yana qarajin wata fitinanniyar sha'awa na taso masa.

Zare bra 'dinta yayi yana ya jefar yana qara cusa bakinsa anata.

Sam basusan me sukeba dan kuwa tuni alamari yayi nisa. Qoqarin rabata da pant 'dun jikinta yake ta dawo hayyacinta A furgice ta zame tareda sakin kuka ahankali.

Dafe kansa yayi cikin tsananin kunya da takaici Dan baisan meya hau kansa yatashi aikata hakaba.

Dukkaninsu kasa motsi sukayi sbd rashin kuxari Ita kuwa harda kunyar tashi take yaganta tunda yayi wurgi da bra 'dinta.

Saidaya tattaro 'dan guntun kuzari ya mike ya fito ruwan ya fita Saigashi da jallabiya fara tas ta maza da wani farin towel ya miqa mata ya juya dan idan ba haka yayiba taci gaba da zama gurin xai iyayin komai danko yanxu saidaya yaqi shai'dan sbd baita'ba jin sha'awa kamar yau 'dinba.

Goge jikinta tayi tana rawar jiki kafin ta xura rigar daya bata batareda ta tsaya 'daukar bra dinta ko sauran kayanba ta fito kanta na qasa ta fice da sauri harta tuntu6e.

Tunda take saukowa haj xeenay ta hangota amma ta kasa gasgata abunda idanunwanta suka hango mata. Murza idanuwa tayi taga tabbas rigar tameer ce ajikinta kuma ga kanta a jiqe sharkaf da ruwa.

Wani rikitaccen gumi ta sharce tana jinjina kai har nazli ta shige 'daki.

Lallai nayi sanyi tunda har nayi saken da irin haka tafara faruwa. Wlh babu tsinanniyar macen data isa ta haihu a zuriyar gidan nan tunda ban haihuba ko meenah bazan bari ta haihuba kozanyi yawo tsirara bare wannan shegiyar. zanyi maganin komai Kowama ya huta kona samu nutsuwar zuciya.

Adaren kasa bacci yayi sai juyi yake dan baitaba tunanin shi 'din mai cikakkiyar lafiya bane sai yau dan gabaki 'daya ya birkice buqace yake.

Ita kuwa zuru tayi akwance tana tunani me ciwo ko hawayen takasayi sai radadin zuciya.

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

Tunda wannan abun yafaru tafara 'boye masa. Bata shiga aiki saiya fice hakama abincinsa tun bai dawoba take kaiwa ta aje ta ficewarta dan ta tabbatar da sonda take masa zai iya rinjayarta duk da ita tasan ba haramun bane to shifa? Yazai 'dauki abun?

*********** Yau gidan ba kowa saisu sbd yaune suke bridal night amma fir tameer yaqi xuwa dan sam kamai na auren baya kansa.

Basusan dazai dawoba suka dawo gidan cikin isa da qasaita. Nafisa haj xeenat takira a waya tace tafa'da mata tana neman nazli yanxu.

Fadawa nazli saqon haj xeenat tayi sukayi shiru cikeda tunanin me kuma zaifarune kaba komai yau batajin kanta daidai.

A daidai stairs suka tsaya nafisa tace, Nazli duk abunda zasuyi miki kadaki yadda dasu dan zasuyita amfani dakene suna biyan buqatarsu.

Sawo kai yayi apalon cikin qasaita kuma kunnuwansa sun 'debo mai zancen nafisa na qarshe datace " yadda dasu dan zasuyi amfani dakene gurin biyan buqatarsu"

Komawa nafisa tayi ita kuwa ta haye stairs 'din cikin faduwar gaba.

Tana shiga suka kalleta a wulaqance kafin haj xeenat tace, Ba 'bata lokaci xamuyi ba abunda zamu da'da miki yanxu shine an canxa shara'di. Ma'ana rayuwar fannah itace fansa ga rayuwar masoyinki.

😳😳 ja da baya tayi cikin muguwar ki'dima tana kallon bakin haj xeenat datayi xancen. Haj kareema ta miqe tsaye tace, Bari kada mu barki a duhu.fannah mukeson kisawa guba taci ta mutu idan kuwa ba hakaba to tabbas a daren farkonsa zaisha guba ya mutu.

Qwarai kuwa dan haka kiyi gaggawar xa'ba dan tafiya xamuyi.

Bushewa xuciyarta tayi tafara tunanin yanxu lokaci yayi daya kamata ta ringa tunani irin wanda su basayi sbd ku'butar da masoyanta daga sharrinsu dan tanajin qaunar fannah kaman yanda meer ke qaunarta amma zatayi wasa da tunaninsu dan tsirar dasu fannah.

Hawowa stairs 'din yayi dan xuciyarsa takasa nutsuwa aiko yana riqe handle 'din qofar xai shiga yayi dai dai data fara magana ya tsaya cak yana sauraronta.

ZAN BAWA FANNAH GUBA TASHA TA MUTU NIMA NA HUTA DAN NAGAJI DA WANNAN WAHALALLIYAR RAYUWAR.

Cikeda farin ciki suka miqe suka shige uwar 'daka batareda tunaninsu yabasu plan ne tayiba sbd sun san zatayi komai kan tameer.

Wani wawan jirine ya 'dibesa yayi saurin dafa bango idanunsa suka ka'da sukayi jajir Wata mummunar tsanarta ta rufesa, Qanwarsa dayafi so dakomai ita zata kashe masa da guba.

A fusace ya banka qofar ya shiga. Tsaye take riqeda qullin gubar dasuka bata sai wayarta dake hannunta tana shiein fitowa. Duba palon yayi babu kowa sai ita ka'dai tana waya tana fa'dar kashe fannah xatayi.

Jikinsa har mazari yake ya shaqota xatayi magana ya 'daga hannu ya sharara mata kyakkyawan marin dayasa hancinta 6arewa da jini...

TO FAH.....

🌕🌕👉 mamuh geee [7:39pm, 15/01/2017] Ⓜamuh geee: 🌕⚜DA'IMAN⚜🌕

Na MAMUH GEEE

☆dedicated to☆ Husnah bbchoudiallo

176→180

Damqo hannunta yayi yafara janta zuciyarsa na tafarfasa. Ji yake inama baije kunnuwansa suka jiyo masa itaba.

Jan qarfi yake mata ido jajir saidaya kaita tsakiyar palonsa ya wurgar da ita ta xube a qasa idanuwanta jajir sbd tashin hankali Kukama sam baiga gurin xuwaba dan abun yafi qarfinsa.

Cikin karaji yace, Ke wacece? Me kikeyi anan cikinmu? Meye dalilinki nason kashemun fannah? Waya saki? Wa kikewa aiki? Wa.......

Jikinta rawa ya 'dauka tashin hnkalin da bata ta'ba jiba ya dirar mata ta matso ta xube a qasan kwance ta kama qafarsa a ru'de tafara fadin, Wlh bazan ta6a cutatarda kai ba bare abunda nasan kana tsananin so, Koba dan kai ba vazan iya cutar fannah ba sbd halaccinta gareni, Dan allah kada kayi xargina walh bazan iya cutar......

Cakumota yayi jikinsa har rawa yake tsabar 6acin rai Fuskarnan tayi jajir Ya maqureta abango da qarfi yace, Jst tell me d damn truth who the hell are u before i do sumtin crazy.

Duk tashin hankalin data shiga abaya baikai mata wannan ba dan yau tameer ne dakansa ke... Jijjigata yayi da qarfi kamar qato dan uwansa Sai alokacin wasu hawayen baqin ciki da takaici suka gangaro mata ba abunda takeso sama da mutuwa alokacin.

Sakinta yayi ta xube qasa a zafafe ya bu'de fridge 'din palon ya 'dauko robar swan 'daya ya bu'de ya finciki qullin gubar ya fazge ledar ya juye acikin ruwan jikinsa sai cira yake Ya 'dago hannunta yasa mata tana durqushe jagwaf sai hawaye take cikin baqin cikin kasancewarta araye hartaga wannan baqar rana.

Cikin wata irin tsawa da karaji yace, Kince ba kasheta xakiyiba then prof yourself and drink it.

Qura masa ido tayi hawayenta na qara gudu ga idanun sun ka'da jajir sbd tashin hankali. Cikin tsakiyar idanunsa take kallo gaba 'daya ya juye kamar wani xaki.

Prof me wrong and drink it idan kuwa ba haka walh i wont spare you Hannun police xan miqaki harsai kin fadi abunda yasa kikeson kashe qanwata.

Tabbas rayuwarta batada wani sauran amfani gwara tasha ta mutu kowama ya huta itama ta huta da baqin ciki da wahalar rayuwa.

Kuka ta rushe dashi har tana shi'dewa hannu na rawa ta karbi robar batareda ta 'dagoba dan bata fatar sake ganin fuskarsa.

'Dagawa tayi ta 'dora abaki xatasha aka fixge robar da qarfi

Atare suka kai kallonsu gareta nafisace tsaye cikin tsantsar takaici tamaida kallonta ga nazli datake faman sheshshekar kuka ahankali kamar ranta zai fita Cikin babbar murya tace, Nazli lokaci yayi dazan daina kallon wannan masifar, Me kike tunani xai faru idan kikasha wannan gubar kika mutu?

Me kike tunanin wa inda kikayi shekaru kina wahala sbd su zasuyi da rayuwarsu bayan sun gano ko ke wacece arayuwarsu?

Bakya tunanin ya rayuwar waleed xata kasance bayan kin mutu baki ha'dasa da mahaifinsaba.

Shin nazli meyasa bazaki daina wahala akan wa'inda basusan kinayiba?

Nazli lokaci yayi da sir ta......

Da sauri ta miqe da gudu ta nufi qofa tana wani irin jan numfashi sbd tsabar kukan datake.

Caraf ya riko hannunta batareda yakalletaba idanunsa nakan nafisa dake watso kalaman dasuka kusan tarwatsa masa tunani da qwaqwalwa.

Kukanta ke qara sauti kuma ahakan nafisa taci gaba da zancenta batareda ta tsayaba.

Nazli idan har kinasonsa kinason kare rayuwarsa to tabbas lokaci yayi dazaisan koke wacece.

Fixge hannunta tayi da gudu tana kuka sosai ta fice.

Jiri ya xubar dashi a kujera kansa na juyawa. Qara hargitsewa tunaninsa yayi sbd bai gane komai na xancen nafisa ba amma ya gane abu 'daya shine zancensu nada alaqa dashi.

Duk yanda yaso tashi yabi bayansu jiri hanasa yayi sbd tashin hankali.

Da gudu ta isa 'dakin ta 'dibi kudin albashinta ka'dan ta fice gidan da gudu tana wani irin kuka mai tsima rai.

Tana fita tasamu taxi ta fa'da sai tasha kuma cikin sa'a mutun 'daya ake jira tana shiga suka tashi suka wuce har alokacin kuka take kamar ranta zai fita sbd ta rabu da tameer rabuwa tahar abada.

Tana shiga taga bata 'dakin ta duba toilet bata gantaba. Fitowa tayi tafara dudduba ko ina amma babu nazli Nan take hankalnta ya tashi tuni hawayen takaicin tameer da tausayin nazli ya tsinke mata sbd tana hango tsantsan masifa agaba muddin nazli tace ta tafi kenan kuma itama wallahi tafiyarta xatayi.

A ru'de ya sauko zashi 'dakinsu dan gaba 'daya yau idan basan komaiba komai xai iya faruwa dashi dan wata irin rashin nutsuwa yakeji kamar xaiyi hauka.

A firgice ta fito 'dakin tana hawaye suka ha'de bakin qofar ya wuceta xai shige cikin muryar kuka da takaici tace batanan ta gudu ta tafiyarta sbd kai, Kaine sanadin komai na wahalarta arayuwa, Meyasa ka kasa tsayawa ka fahimceta kayi mata wannan hukuncin harda baraxanar shayar da ita guba, Shin ko kasan sbd kaine xatasha gubar tabar duniya duk dan sbd kai uban 'dan..... Kasa qarasawa tayi sbd kukan dayaci qarfinta tace nima nasan koban tafiba xamana ya qare a gidannan dan haka tafiya xanyi.

Ido rufe ya daka mata wata mahaukaciyar tsawar dabaimasan yayiba ya bu'de ido jajir yace, Har abada bazaki bar gidan nanba harsaikin fadamun abunda yake faruwa sbd xuciyata na gab da tarwatsewa sbd ru'du.

Cikin rashin tsoro tana sharce hawaye tace, Ni 'yar aikice banida dama ko matsayin dazan fadi wani abu amma alh da haj da aminanta sunada dama harmada dr ibrhm.

Tana fadar haka ta shige 'dakinta ta sulale qasa tana kuka amma tasan allah bazai bari su cutatar da itaba tunda qarshen wahalar alamarin ne takawo idan har tameer yasan komai.

A zafafe yake kaida kawo apalon, Banda sarawa ba abunda kansa keyi ga fuskarnan tayi ja abinka ga farin mutum. Zama yayi a 'daya daga cikin kujerun palon yana jiran dawowar kowa daga gurin event 'din dan ayau yakeson jin komai basai gobe ba.

Sallamar dad ne da driver 'dinsa janye da 'yar jakarsa yasashi miqewa tsaye cikin godewa allah da dad 'din ya iso yau kuma a daidai lokacin dayake buqatarsa.

Kallon mamaki dad yake masa sbd ganinsa a yamutse hankali duk atashe idanunsa jajir.

Subhanallah tameer meyene naganka haka hnkli atashe?

Fitowarsu haj xeenat da aminan natane yayi daidai da fa'dar maganar dake bakinsa...

🌕🌕👉mamuh geee [8:55pm, 15/01/2017] Ⓜamuh geee: 🌕⚜DA'IMAN⚜🌕

Na MAMUH GEEE

☆dedicated to☆ Husnah bbchoudiallo

181→185

WACECE NAZLI A RAYUWAR NAN GIDAN?

alokaci 'daya jakunkunan hannuwansu su duka ukun suka kufce musu cikin wani irin mugun tashin hankali.

Kallonsu yayi yakaranto tashin hankalinsu tsaf a fili kafin ya maido kallonsa ga dad 'dinsa dashi kuma mamakine xalla afuskarsa na yanda akayi tameer yasan sunan nazli.

Murya a sanyaye yace, My son ina kaji sunan nan?

'Yar aikin gidan nance me sunan...fannah ta fa'di haka tana shigowa palon dan dawowarta kenan taji abunda ake fada.

Mamakin dad ya qaru muryarsa har rawa take yace, Me aiki anan gidan? Akiramun ita yanxu nan inason ganinta.

Wata wawar murdawa cikin haj xeenat yayi ta diro tsakiyarsu da qarfi tana rawar murya tace, Alh ba nazli 'dinsa bace wannan watace dabam.

😳😳 zaro ido su haj kareema sukayi sbd jin 6arin bakin datayi na cewa nazli 'dinsa.

Gogan kuwa qara 'daukar zafi kansa yayi jin ta danganta nazli dacewa tasa. Fannah kallon rashin fahimtar komai take musu Dad kuwa rashin gaskiya ya hango tsantsa a tattare da haj xeenat wadda ita sai daga baya ta gane ru'du yasa tasaki layi saita fara kame kame amma ina tuni alh zaid ya nufi hanyar kicin da kansa sbd shi ka'dai yasan irin qaunar dayakewa nazli.

Cikin wata wahalalliyar murya yace, dad ta tafiyarta tabar gidan sbd nakamata zata kashe fannah ta hanyar xuba mata guba tasha.

Ai mutanen naku najin haka ko wacce saidata kusan tsirgo fitsari suka fice palon da mugun sauri suka bar gidan dan yau qila rana ta 6atar musu.

Fannah jikin yayan nata ta isa da sauri ta jirgixashi tace, B pls dnt say that nazli baxatayi hakaba i knw her for sum month amma na karanci halayenta she cant d....

Da qarfi yana tureta daga jikinsa yace, Just shut up. I saw her and she......

Shut up. Shima dad ya katsesa da qarfi sbd ganin abunfa da gaskene akwai gagarumar matsala dabai sanda ita a gidansaba.

A fusace yakalli haj xeenat yakalli tameer 'din yace, Weda nazli 'din ce ko kuma wata daban inason tabbas ku nemota sbd koma meyene kune kukasa ta tafi. And as for u dakakeson sanin komai to zan fada maka amma saika nemota duk inda ta tafi.

Fadar halinda yashiga abune mai wuya dan kuwa idanunsa har wasu ruwa suka tara Shima cikin mazewa yace, Nikuma na fasa auren meenah saina san ko wacece nazli.

A razane dukkaninsu suka maida kallonsu kansa dad kuwa hayewa samansa yayi cikin wani irin yanayi.

Da rawar jiki haj xeenat ta juyo xata fara roqonsa ya juya rai abace da sauri ya haywarsa samansa.

Juyowa tayi gurin fannah dake hawayen ganin abundake shirin faruwa dasu yau harb 'dinta na tureta da gudu tabar palon tana kuka tayi 'dakinta ta rufe.

Gumi ta sharce kafin ta ruga 'daki tadauki wayarta jiki na rawa tana qara hada wani gumin takira kareema ta fada mata wata sabuwar masifar fasa auren meenah da tameer yace yayi.

Kaf 'dinsu a daren babu wanda ya rintsa sbd kowa nacikin nasa kalar tashin hankalin bama kamar SIR TAMEER.

Washe gari kowa da damuwa yatashi fal danko breakfast babu wanda yayi.

Haka take agidansu haj kareema dan kuwa aure dai ya fasu sai ranar dayace iya tashin hankali kam suna ciki. Hardai meenah da haj kareema ta zayyane mata komai hankalinta yayi mummunan tashi jin cewar nazli matar tameer ce. Wata muguwar tsanar nazli ta mamayeta nan take ta'dau waya takira megadi mijin sa'adah tace ta koresu maza maza subar gidan ayau basai gobeba.

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

Da asuba suka isa kano Idanunta sun kumbura sunyi jajir ko gani batayi sosai tsabar kuka ga ciwon kai kamar kanta da zuciyarta xasu tarwatse.

Mashin yakaita har qofar gate 'din gidan ta qwanqwasa kofa abu mai gadi mijin sa'adah ya bu'de gate 'din yana ganinta ya saki fara yana mata sannu da hanya duk da fara'ar qarfin halice yakeyi sbd ya lura da yanayinta.

Tana shiga suka ha'da ido da sa'adah data tashi sallar asuba.

Kawai saita saki wani sabon kuka tana shesheka kamar me asma tsabar kukan yacita.

A rude sa'ada ta rungumeta tana lallashinta har suka samu daqyar sukayi sallah.

Har gari ya waye yayi ras suna zaune takasa magana sai kuka takeyi.

Waleed natashi daga bacci yaga antynsa da gudu yafada jikinta ta qanqameshi tanajin maseefar sonsa sbd tayiwa kanta alqawarin ta rabu da tameer da rayuwarsa har abada.

Sunan xaune ne saiga kiran meenah ta koresu nan wani sabon tashin hnkali ya samesu wanda nazli kukanta ta qaru sbd ta dangana hakan da itace sanadi dan haka zata 'dauki 'danta su tafiyarsu.

Nasiha abu yayi mata sisai kafin ta tsaya suka tattara 'yan kayansu sukabar gidan Sai wata babbar unguwar masu ku'di a wani babban gida da aka 'dade da ba abu cigiyar yasamo musu me gadi sai kawai yakai kansa babu 'bata lokaci kuwa aka basu 'dan qaramin boys quaters 'din gidan duk da gidan gidane babba.

Readers Also Read

More by Autar Alheri