Da'iman complete hausa novel - Chapter 8
Da'iman complete hausa novel Chapter 8: Da'iman complete hausa novel Chapter 8. *** Duk yanda kowa ya tsammaci abun yawuce nan dan sosai gidan yakoma kamar…
3,374 words
********** Duk yanda kowa ya tsammaci abun yawuce nan dan sosai gidan yakoma kamar gidan mutuwa sbd kowa nacikin muguwar damuwa bama kamarsa da tunani da damuwa sufara yi masa yawa har ciwo nason yashigo ciki. Ku'di yasakarwa p'a 'dinsa sosai ana nemanta amma ba wani lbr.
Kwance yake apalonsa idanuwansa a lumshe yayi nisa cikin tunani.
'Dayar wayarsace tayi ringin ya bu'de idanu ahankali sai yaga p.a ne akasalance ya 'daga wayar sai yaji yace, Sir dama alh ne yasani 'dauko masa wasu takardunsa acan tsohon gida gashi yanxu nakawo amma bayanan ya fita kuma naga takardun nada mahimmancin da bazan iyaba kowaba saikai.
Siririn tsaki yaja tareda kashe wayar ya miqe yasauka palon qasa saiyaga takardun da 'dan yawa ya watsawa p.a kallon wane irin takardune wa'inan.
Yayi saurin cewa, Eh dama takardun gidan yace mu 'dauko ta sai muka samesu da wasu sauran takardun daban sai kawai na kwaso masa gaba 'daya.
Hannu yasa ya kar6ba tareda hayewa saman.
Fannah dake tsaye qofar 'dakinta tana kallon yayanta taga muguwar damuwa tattare dashi ta share hawayen dasuka gangaro mata takira nafisa tace taje takaiwa tameer abinci yanxu ita xata yanka masa fruit tazo dasu.
Yana shiga palon yayi wurgi da takardun a kujera suka watse kansa na sarawa yajuya zai shige 'daki ya tsaya cak tareda juyowa da mugun qarfi sbd hotunan dasuka watse daga cikin takardun. Raruma yakaiwa hotunan nan take jikinsa ya 'dau rawa sakamon kansa daya gani tareda wata kyakkawar yarinya kamar balaraba daya sake dubawa saiyaga tabbas nazli ce.
Hotunane birjik duk suna dariya da wasa ta daukesu hotunan ga tsantsar so da qaunar junansu dayake bayyane afuskarsu
Hotunane datake daukarsu awaya lokacin tana turawa dad sune yasa aka wanko masa tun da dadewa.
Baraxanar 'daukewa numfashinsa yayi lokacin daya 'dago hoto na qarshe wanda ashe ba hoto bane katin 'daurin aurene na TAMEER ZAID OMAR DA NAZLI ADO TAKAI. Da akayi shekaru biyar dasuka gabata.
A haukace ya 'daga takardar qarshe ta gidace da dad yasaka sunan nazli yabata gidansa dasuka taso.
Qoqarin xubewa yake nafisa tashigo tayi saurin aje tray tayo kansa da sauri..
TO FAH YANXU AKE.
🌕🌕👉mamuh geee 🌕⚜DA'IMAN⚜🌕
Na MAMUH GEEE
☆dedicated to☆ Husnah bbchoudiallo
186→190
Da gudu ta iso gurinsa tana kiran sunansa. A kujerar ya zube yana dafe kansa dake neman bugawa, Hotunan da katin ya qanqame cikin tashin hnkli yanajin zuciyarsa na wata irin bugawa da qarfi.
Manyan idanuwansa dasuka koma jajir ya warowa nafisa saidatayi saurin ja da baya cikin tsananin tsoro sbd gaba 'daya ya birkice yakoma kamar wani jan xaki.
Jada baya tafara ganin ya miqe yana jefa mata wani mugun kallo da jajayen idanunsa.
Cak ta tsaya tana ha'de yawu a dan tsorace.
Gabanta ya tsaya yana mata kallon dayake qara razanata.
Hotunan hannunsa da katin 'daurin auren ya 'daga da qarfi ya watsa mata da qarfi jikinsa har rawa yake yace,
Waye nazli aguna? Wannan auren, Wannan hotunan, Da wannan.... Just tell me everytin now I want to know every single thing akan auren nan.
Zufa ya fara fesowa nafisa tako ina jikinta na 'dan rawa.
Wata mahaukaciyar tsawa ya daka mata data mugun razanata batasan sanda tace,
KANA CIKIN HAUKA AKAYI AUREN.
hawayen dake cikin idanunsa na 6acin rai suka gangaro ya qura mata ido kamar bai fahimci mai tace ba sbd qwaqwalwarsa ta gaza 'daukar xancen.
Hauka? Ni? Nayi hauka? Har akayimin aure Dakuma harkar?
Sanyi muryarsa tayi sosai kamar yaro yafara roqonta kamar itace boss 'din.
Nafisa pls am begging you ki fadamun abunda nakeson ji kada kiyi wasa da tunani ki fadamun gaskia.
Ka kamu da lalurar ciwon juyewar qwaqwalwa shekara biyar dasuka wuce,
A farkon ciwon alh yayita yawo dakai a qasashe amma babu Wani cigaba saima tsanani da abun yake,
Bayan andawo dakai nan ne akayita 'daukar masu kula dakai amma dasun zauna kwana biyu saisu gudu daga qarshe aka kira malami yazo ya tabbatarda aikin sihirine malam yabada shawarar ayi maka aure dan zakafi samun kulawa daga matar datasan kai mijintane.
Nazli marainiyace bata uwa batada uba ita aka auro maka. Fa'dar irin baqar wuyar datasha kafi gurin kula dakai zaiyi wuya, Ahaka ta samu.....
Shiru tayi tana ha'de wasu yawu sbd tsoron fa'da.
Jikinsa ya mutu iya mutuwa saiya bude baki daqyar yace, Kada kiji tsoro fadamun komai pls.
Naz....naz..nazli ta...ta samu ci.. Ciki alokacin.
Saurin dafa bango yayi sbd wawan jirin daya kwashesa.
Sannu ahankali tafara fayyace masa komai na irin baqar wuyar da naxli tasha akansa harda rayuwarsu a takai da kuma gidan innah asmah da waleed da aka haifa masa. Komai bata 6oyeba saidata bayyana masa illah abu 'daya shine mugayen ayyukan da haj xeenat ke aikatawa....
🌕⚜AM REALLY SORRY FANS DAJINA SHIRU DA KUKAYI TWO DAYS I WAS VERY BUSY NE AMMA INSHA ALLAH YANXU XAKU RIQA JINA. 🌕⚜ LUV U ALL😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘
🌕🌕👉mamuh geee 🌕⚜DA'IMAN⚜🌕
Na MAMUH GEEE
☆dedicated to☆ Husnah bbchoudiallo
191→195
Luu ya tafi xai kife fannah dake tsaye bayansu tana wasu irin axababbin hawaye sbd tun fara zancensu tazo kuma taji komai.
Wurgi tayi da tray 'din hannunta tayi kansa da mugun gudu yana ganinta ya sulale zaune itama ta zauna yayi saurin fa'dawa jikinta tareda sakin wani irin kuka mai ciwo kamar qaramin yaro.
Rungumesa tayi tana gargiza masa kai tana cewa, No b pls dnt cry Kada kayi kuka, Ure breaking my heart.
Cikin kuka yake fadin, Fannah i have a son Who is out there yana wulaqantacciyar rayuwa, And she's my wife,my sons mother but babu wanda yadamu da afadamun qarshema a me aiki take acikin gidanta gidan mijinta. Meyasa aka bari matata tazama me aiki anan gidan aftr knowing d fact shes my wife the mother of my son. Why why. I even try to kill her wit my own hands ta hanyar bata poison tasha. Fannah i wnt to see her i wnt to see my son I wnt them both.... Fan fannah i..i..i.....
Toshe masa baki tayi tana kuka mai tsanani sbd tsananin tausayin halinda yake ciki dan kuka yake sosai yana sambatun kamar ma ciwon nasa na haukane yataso.
Nafisa duqe take agefe tana nata kukan ahankali sbd ganin yanda tameer 'din ya birkice sai sambatu yake cikin kuka fanna na jawasa jiknta tana goge masa hawaye amma sam kamar zugasa sukeyi.
Abu kamar wasa tameer ya birkice sosai fannah tun tana kuka kamar ranta zai fita tadawo itama kamar wata zararra gurin lallashinsa amma sam shi ba abunda yakeso sai ganin matarsa da 'dansa.
Nafisa tadataga abin yayi tsanani saita 'daga wayar fannah jiki na qyarma takira dad.
Yana 'dauka cikin tsabar ru'dewa sai kawai tace masa Daddy sir tameer ya qara hauka..... Bata qarasa fadaba yayi wurgi da wayarsa yayo saman tameer 'din dan yadawo ko minti goma baiyiba da dawowarba saiga kiran.
A gigice yashigo palon saiya tsaya turus ciwon xuciyarsa na neman tashi sbd ganin 'ya'yansa zaune a qasa tameer na risgar kuka fannah ta rungume kansa itama kukan tausayin 'dan uwanta take duk sunyi wani iri dasu.
Fannah na ganin dad ta 'dan rage kukanta Ya qaraso cikin fargabar idan da gaske 'dan nasa ya qara haukacewa.
A tsorace yace, Fannah fadamun abinda yasamu 'dana tun ciwona bai tashiba.
Saidata 'dan goge hawayen fuskarta Tace, Dad nazli da ciki ta tafi and..... Kuka yaxo mata
Dad ma baisan sanda yajawo tameer jikinsaba yana fadin, Kufadamun ta haihu kadaku cemun na rasa rasa grandson.
Lafewa tameer yayi jikin dad murya a dashe yace, Dad ta haifamun 'dana Ur grandson, And natashi da 'dana tun yana jariri, Nayi wasa da 'dana infact he was my friend alokacin, We played as frnds Dad inason ganina tareda shi da nazli, Dad do sumtin I wnt to see them now pls. My heart is beatin faster dad ta6a kaji i cnt breath pls dad i want to see th..... Bai qarasaba yafara wani irin tari Ai nan suka qara rikicewa dad yakira dr da sauri.
Dr ibrhm nazuwa yaga halinda yake ciki bai tsaya wata wataba yayi masa allura nan take ya xube yana baccin wahala.
'Daki dad da dr suka kaisa suka kwantar fannah ta lullubesa tana hawaye tareda shafa gashin kansa da ku'din gyaransa dabanne amma yau tashin hankali yasa duk ya hargitse.
Bayan fitar dr da dad ta qura masa idanu tana tunano fuskar nazli. 'Dan naxli dataxo dashi suna kano kafin sudawo was her own son amma rashin sani yasa batamayi tunanin dasukazo tace tanason ganinsaba qilama datun anan zata ga wani alamar cewa shi'din jininsune. Allah sarki my b yanada 'da, Ni aunt ce bansaniba.
Wani mugun son yaron yashigeta tun bata gansaba tana tunanin irin gatan dazai samu daga gareta kawai kafinsu dad da ubansa gaba 'daya wato b 'dinta sbd ta hango wani irin tsananin son nazli atake dayayiwa b muguwar shiga LOVE AT FIRST SIGHT, To bare abunda ta haifamasa,jininsa,me sunan dad 'dinsu.
Data tuno irin baqar wuyar da akace sunsha sai hawaye suka sake 'balle mata.
********* Bai farkaba sai washe gari da allurar data sakesa Kowa gidan cikin tashin hnkali yake banda haj xeenat da itama sam saura ka'dan ta haukace sbd jin nazli ta haihu kuma namiji. Yanda tashin hankalunta yafito filine yasa dad qura mata ido amma sai baice komaiba. Qarshe dai itama allurar akayi mata sbd jininta daya hau lokaci 'daya.
Qarfe tara ya farka amma da tashin hnkali dan kuwa wani irin jijjiga yakeyi datasa akayi asibiti dashi hankali tashe.
Kwantar dashi akayi asibitin sbd dr ya tabbatar musuda zancen daki xuciyar sosai wanda yaso taba qwaqwalwarsa amma bai ta6a 'din ba saidai kuma fa dole anemo masa matarsa da 'dan nasa.
shiru sukayi cikin damuwa hardai fannah da kullum saita kira wayar data siyawa nazli amma batashiga abunda bata saniba shine agidan nazli tabar wayar yashe akashe tun lokacin da tameer ya damqeta da guba ahannu.
Kano suka shirya ta jirgi sukaje amma cikin rashin sa'a koda sukaje babusu sa'adah a gidan an koresu.
Hankalinsu bai tashiba saida suka kwana biyu akano ana xagayen nemansu harda hotunan nazli ake nunawa a gidan talabijin dakuma kyautar maqudan kudi amma babu wani alamun za'a samesu.
Komawa sukayi jiki asalube da damuwa.
Sannu ahankali ciwo ke cinsa amma sbd yanason yaje nemansu da kansa yasa ya nuna ya warke dan yanda yakeji aransa idan babusu arayuwarsa xuciyarsa bugawa zatayi ya mutu dan ko ayanxu 'din daurewa kawai yake amma yana cikin tsananin tafasar xuciya.
Tunda yadawo gida da hotonta yake kwana wanda fannah tasaka masa a 'dan frame ta dora masa kan bedside drower dake gefen gadonsa.
Duk iya yanda yaso sakewa kasawa yayi dan gabaki 'daya farin ciki yabar gidan kowa cijin damuwa yake sbd damuwar son aga su nazli 'din dakuma uwar damuwar da tameer 'din yake ciki.
Abinci ma dainaci yayi sai ruwan lipton kawai yakesha shima kullum sai fannah tayi masa kuka tace "B nazli 'dinka babu abinda takeso kaman tameer 'dinta dan haka duk inda take xataji ajikinta meer 'dinta yaqi cin abinci so zata shiga damu... Bata qarasawa yake shanyewa ya miqa mata cup.
🌕🌕👉mamuh geee 🌕⚜DA'IMAN⚜🌕
Na MAMUH GEEE
☆dedicated to☆ Husnah bbchoudiallo
196→200
Haj xeenat al'amura sun tsananta gareta sbd tana cikin tsananintashin hnkli na neman nazli da 'danta da akeyi kullum sai dukiya alh zaid ke sakarwa jamian tsaro gashi ta fara samun matsala da haj kareema sbd auren meenah da tameer 'din da'aka fasa kuma haj bilki bayan kareema tabi abun yana ca6e musu.
Hankalinta bai qara tashiba saida taji alh zaid yace angama zuba komai a katafaren gidansa na kano daya maida sunan waleed akan takardun gidan zasu koma kano harsai yaga surukarsa da grandson 'dinsa da tuni an maida sunansa ga wasu daga cikin takardun dukiyarsa.
********* KANO Yau sun tare a gidansu na kanon wansa yake babba sosai shima kuma tsarinsa 'daya dana abj dan haka kamar abj kowa irin 'dakinsa nacan ya 'dauka.
Tunda suka iso bai zaunaba kullum yana tareda manyan jami'an tsaron gari ana masa bayani akan binciken.
Yau tun safe yayi order 'din masu gyara sukazo 'dakinsa 'daya dake cikin palonsa aka cire komai aka zuna kayan wasan yara kamar hauka da gado da komai na 'dakin na yara ne gar stickers 'din bango na spiders da ben10 komaidai mota,mashin da sauran tarkace. Wardrop 'din 'dakin kuwa kayan da aka xuba sunfi kala hamsin duka masu shegiyar tsada hatta takalmi saidana gaji da qirgawa. Duk na waleed ne his own son and his bst friend.kaman yanda take cewa kenan.
A 'dakinsa ma abun haka yake domin kaya na fitar hankali ya siya yacika wardrope 'dinsa dasu duk na nazli 'dinsa dayake cewa she is his savior.
Duk abunda yake su dad na lure dashi sbd mugun tausayinsa sukeji dan gaba 'daya kamar a 'dan xauce yake ga ciwo dayake dannewa tsabar qarfin hali.
******** Satin su uku agarin ya 'daga hankalin dad akan saiya kaisa gurin wa'inda aka nemi auran nazli tun farko.
Sai alokacin dad yama tuna dasu suka kwasa sukaje su duka har haj xeenat daketa shiryeshiryen cimma burinta dan tayi alqawarin kobata aikasu duka lahiraba ta wlh saita aika koda 'daya tsakanin TAMEER,NAZLI,WALEED,FANNAH KO DAD.(readers wa kuke tsammanin xata kashe batareda xuciyoyinmu sun karayaba )
Koda suka isa gidan haj salamatu tana ganin haj xeenat tahau rawar jiki ba 6ata tym sukace gidansu nazli na takai sukeson akaisu.
Mijin haj salamatu yanajin haka yasan kudi zasu samu yace aiba matsala haj salamatu ta tashi suje.
Suna isa qofar gidansu nazli na takai nan take guri yacika ana kallonsu sbd anga larabawa.
Qofar gidan ya qurawa ido xuciyarsa na harbawa sbd muguwar tausayin wainda ke rayuwa acikin gidan. Savior 'dina anan tayi rayuwa taredani cikin so harta haifi bbynah anan.hw i wish zanganki my savior dazan xa6i rayuwa a inda yafinan muni idan har tareda kene. Hw i wish kin haifamun babys da yawa ba waleed ka'daiba.
Fannah ta katse tunaninsa ta hanyar dafasa sbd ta lurada yayi nisa tunani.
Su haj xeenat ne suka fito tareda ladingo da jummai sai wani rawar jiki suke har qasa suka xube kamar zasu kwanta suka gaida alhaji zaid.
Tameer kuwa kallonsu yake kamar wasu halittu sbd a koma'de suke sai tsami ke tashi tunda suka fito.
Suma kallonsa suke ko qyaftawa basayi sbd tunanin kamarsa da shegen mahaukacin nan mijin nazli.
Haj xeenat ta katse musu tunaninsu ta hanyar miqa musu bandir 'din dubu ashirin tace su wuce an gode.
Kallon rashin fahimta suka aika mata tace, Alh sunce nazli tun 'danta na jinjiri tabar garin tareda tameer kuma basusan qauyen da innah asma take bare su fada.
Cikin 6acin rai tameer yace, Dad zai iya yiyuwa qarya suke tunda basa santa ni xan saka police su kamaminsu ayita horonsu saisun fadamin inda my savior take.
Da sauri dad ya dafasa yana fadin, Calm down son bazasuyi qaryaba sbd sunga kudi dan dasun san inda take dasun fada sbd kudi. Muje my son ka qara hkr ankusa ganinsu.
Jiki asanyaye suka koma kano bayan sun sallami haj salamatu da 'dubu hamsin.
********** CAIRO lokacin da dad yayi waya da haj nurat ya zyyane mata komai itama kukan tasa masa tana fadin a kashe konawa xa'a kashe koma duka dukiyarne a nemo mata nazli da jikanta 'dan tameer 'dinta.
Su ammah ma dasukaji 'yar tsohuwar rikice musu tayi jin cewar harda 'da a alamarin kuma ba abunda takeson gani kamar yarinyar dataso tameer 'dinsu alokacin hauka lkcn da bashida kowa. Saurin dangi kuwa banda waleed ba abunda sukeson gani daji. Qarshe dai haj nurat kasa xama tayi ta tarraro tayo nigeria dan sam hnklinta yakasa kwanciya idan basu aka ganiba.
Lokacin data iso taga yanda tameer 'dinta yakoma rungumesa tayi tana hawaye shima lafewa yayi ajikin umminsa yanajin wani sabon radadin rashin matarsa da magajinsa.
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
NAZLI(mai fans da yawa😃)
Rayuwa a sabon gidan da mijin anty sa'adah take aiki ba laifi saidai kam ita tuni tayi bankwana da farin ciki sbd rashin meer 'dinta ba qaramar illace ba. Ciwon datake fama dashi a zuciyarta shiya tabbatar mata da ciwon xuciyane yakamata sbd azaba takeji sosai amma haka take rayuwarta sbd bata tunanin akwai ciwon dayakai mata rayuwa babu meer 'dinta.
Waleed kuwa ya sake suna zuwa wata makarantar gwamnati dake 'dan kusa dasu kullum mijin sa'adah ke kaisu da qafa yadawo.
Ta rame sosai kullum cikin yimata nasiha anty saadah take harta gaji ta bari ta zura mata ido saidai addua.
******* Wayarsace tayi qara yana kwance 'dakin umminsa kansa nakan qafarta tana shafawa ahankali alamar rarrashi kamar shine waleed 'din😡.
Ganin yaqi ko kallon wayar yasa haj nurat kallonsa cikin muryar lallashi tace, My boy ka 'daga wayar mana tunda kasan a nema muke zai iya zama cikin masu neman ne wani yagan..... Bata qarasaba ya 'daga da sauri kamar ance masa nazli 'din ce.
Hey mr tameer ne kuwa?
Yes,yes nine.
Hahhhhhhh tameer hameed lamido ne.
Duk da yana cikin damuwa hakan bai hanasa farin cikiba sbd jin babban aminsa 'dan govnr din kano dasuka 'dibi shekaru basu haduba sbd kasancewarsu basa zama su duka.
Hameed yace 'dazu naga p.a 'dinka a bank yacemun kuna kano ku duka dasu dad.
Ajiyar xuciya yasaki tareda cewa Hameed matana da only son 'din sun 6ata anan kano.
Wat. Hameed yafada da qarfi cikin shock
Tameer ur wife and ur son? To mekayi akan hakan kaga muhadu yanxu kawai dan nima ina kanon.
Ok hameed send me ur address xanxo yanxu. Bayan hameed ya turo masa address din ya miqe yafita dan xuwa.
Dakansa yake tuqin fannah data biyosa tanagefensa xaune tana waya ammah tana kwantar mata da hankali.
Sun shigo anguwar gidan hameed 'din dai dai saura qadan su isa qofar gida wani yaro yafito aguje da 'yar ball 'dinsa kadin tameer yayi wani motsi tuni ya ka'desa.
A gigice suka fito motar basu tsaya wata wataba suka 'daukesa sai asibiti.
Kunasn waye fans? WALEED NE.
🌕🌕👉mamuh geee 🌕⚜DA'IMAN⚜🌕
Na MAMUH GEEE
☆dedicated to☆ Husnah bbchoudiallo
203→204
No dad i'm feeling sumtin abt him, I jst have this feeling dat hes my waleed my boy my little me.
Dafasa umminsa tayi sbd ganin yana neman rikice musu tace, My boy kwantar da hankalinka dr zaiyi mana dna test 'din just relax okey?
Kallon dr dad yayi yace yayi musu test 'din.
Zama sukayi cikin dan tsurewa dan hakanan suke fargabar jin result 'din badan komai ba sai dan gudun ace ba waleed 'dinsu bane ba tameer ya birkice musu dan yanxu yakoma kamar yaro.
Fannah ce zaune bakin gadon tana qure kallonta ga waleed tanajin maseefar sonsa tun kafin ace shine.
Dad da haj nurat a xaune suke a kujerun 'dakin
Yayinda shikuwa yakasa koda zama jinsa yake cikin wani sabon tashin hankali haryaje aka 'dibi jininsa ya dawo.
Zaman shiru sukayi nakusan rabin awa Kamar a mafarki saiga yaron yafara motsi ahankali harya bu'de idanunsa ya saukesu kan fannah dake kusa dashi.
Qura mata ido yayi sbd ganin kamar yasanta sbd fuskarta da kamanninta.
Ita quri tayi masa gabanta na tsananta bugawa sbd qwayar idanunsa zak na tameer sbd sun 'dan fita manyan ido kadan.
Tashi yayi da sauri sbd tsoro daya kamasa lokaci 'daya ganin kansa a inda yake 'din.
Saurin miqewa tayi taja da baya ganin ya firgita sai alokacin kowa ya lura da abinda ke faruwa. Hankalinsune ya qara tashi ganin qarin kamannin dasuka bayyana.
Shikuwa da kallon tsoro yake binsu 'daya bayan 'daya har idanunsa suka sauka kan tameer dayayi wujiga wujiga tsabar tashin hankali.
Qara kallonsa yake dakyau ya murza ido ya sake kallonsa
Duk sukayi tsit suna kallon ikon allah Ai basu gama tunaniba Waleed ya diro gadon da wani irin qarfi ya fa'da jikin tameer ya qanqamesa sai kawai yasaki kuka yana cewa, Abbanah, Abbanah ka tafi ka barni nayita kuka anty ma tayita kuka harda inna tayi kuka, Ka tafi ka barni a makaranta su abdul suna fadawa 'yan ajinmu banida baba, Abbah kadaka tafi ka barni kuma ka tafi dani mu ringa wasanmu na doki, Kada ka tafi anty kullum kuka takeyi ka tafi.
Ai sai kawai sukaga tameer ya fashe da wani irin kuka yana qanqame waleed kamar zai maidasa cikin cikinsa.
Da gudu fannah ta fada kansu tana sakin nata kuka itama.
Haj nurat na hawayen take gogewa Dad qarfin hali kawai yayi shima sbd ba qaramin dukan xuciyoyinsu xancen waleed yayiba.