Kenza eBookz

Damuwata complete novel - Chapter 22

Damuwata complete novel - Chapter 22

Damuwata complete novel Chapter 22: Damuwata complete novel Chapter 22. Zillo zuciyana ta yi na bud'e ido da sauri na kafeshi da su.

1,238 words

Zillo zuciyana ta yi na bud'e ido da sauri na kafeshi da su.

Dariya ya kyalkyale da shi tare da dukan steering, na yi kwal-kwal da ido zan fashe da kukan dama na ke cikinsa, ya yi saurin kunna wayarsa karatun Qur'ani ya bayya cikin sural Ankabut. Lum na yi ina bin karatun cikin raina ina maijin natsuwa na rab'ata.

Sautin fitar murmushinsa yasa na kalleshi ya motsamin kai "Duk kan damuwa maganinsa na cikin sauraren zancen Allah ko tilawarsa dan haka kada ki sake damuwa ya yi sanadin rayuwarki abanza batare da kin cikawa Mamanki burinta ba na yiwa 'ya'yanki tawai."

"Nagode Kawu da kayi sanadin natsuwa ya nashe ruhina."

Jinjina kai ya yi tare da yin parking a k'ofar gidan sannan ya maido hankalinshi kaina ya ce "Ba Hajiya Inna ta ce in daukoki ba ni da kaina naga zuwarki tare da komawarki shi yasa na dawo da ke domin inji dalilin zuwarki sannan kika koma batare da kin shiga cikin gida ba."

"Kawu yawan bincike haramun ne to ka barshi a sirri ne."

"Shi kenan Dije na bar kaza cikin hashinta domin kada in figeta na gano kwarangwal ce."

Murmushi na yi jin yarda ya yi zancen cike da tsokanar da ya saba.

"Yanzu taho muje ki gaida su sai in maidaki gida."

"Hajiya Inna zata tambayi inda muka had'u kuma kasan ban iya k'arya ba."

"Haka ne shi yasa na ke k'aunarki tamakar rai da ajali."

"Kawu dan Allah ka bari wallahi zanyi maka kuka."

"Oya maza kiyimin kukan tsun-tsu Kanari ni kuma na shagala da saurarenki na yi ta dilalan yamu tamkar dolo."

Da sauri na bud'e k'ofar na fice ina murmushi ya biyo bayana yana dariya muka jera ya yi k'asa da murya "Kada kiyi magana ko ta tambayeki daga inda muke, ni zan amsa domin na iya girba k'arya tamkar kud'in duba, right?."

Ware ido na yi ya kauda kai gefe cikin cewa "Zanyi Istiggifari da dare kinsan Allah gafurilul rahimun ne."

Ban tanka ba ya mintsili fatar wuyana na kwabe fuska ya kyalkyale da dariya domin shi mutum ne wanda dariya baya yi masa wuya ga tarin tsokana duk da ina jin kunyarsa amma haka nan ke takuramin da tsokana duk in mun had'u.

"Wa na ke gani da darenan kamar Mariliya?"

"Ita ce fa Inna gata nan Gawa tak'i rami ba, na tsinto miki ita a gaban tukuban mai tsire wai kwad'ayin cin nama ta ji ta fito batare da Yaya Hurera ta sani ba, bata ko jin tsoron 'yan iskan gari suyi wuf da ita mu shiga gararin nemanta har birnin sin."

"Amsa naka Habibu wai meyasa ka maidamin da Takwara abokiyar wasarka ce?"

"To Inna ai kyawun Uba ya sake da d'iyoyinsa ba yawan sababi ba, dake janyo tsana a tsakani."

"Kawu ka bar cimin fuska dan Allah, shima Baba zai daina sababin insha Allah."

"Kingani ko Inna? To na kame bakina mai Baba sarkin sababi har da na sari."

Duka na kawo masa ya gofce Hajiya Inna ta nuna masa k'ofar fita ya taho kamar zai fad'a jikinta ta rafka salati ya dawo da baya ya zauna saman Cushing yana kyal-kyalan dariya, nima dariya lamarin ya bani na murmusa.

Gaisar da Hajiya Inna na yi ta amsa cikin wal-wala tare da tambayata lafiyar Mama.

"Alhamdulillah."

"To masha Allah."

Abinci ta kawomin tuwon shinkafa da miyar yauk'i sai farfesun k'ashin Akuya mai taushi sai k'amshin kayan k'amshi ya ke fitarwa.

Tare da Kawu Habibu mukaci tuwon a kwano d'aya saboda ina cikin ci ya tsoma hannu duk maganar da Hajiya Inna keyi masa bai kulata ba, sosai lamarin nasu ya burgeni sai naga tamkar ni da Mama masu fahimtar juna.

Gyaran muryan Baba Umaru ya ratso kunnuwaemu, duk muka natsu tare da zubawa hanyar idanu.

"Habibullah Kawun kawai, to maza taso inbaka sak'on Malam Isuhu kada in manta."

"To Baba dama ina son magana da kai domin na yi Mata kuma mai hanani aurenta sai mutuwa ka zamo shaida tamkar yarda na sanar maka a garin Kwara."

"To Habibullah, Allah yasa abokiyar arzikinka ce dan nafi kowa farin ciki da lamarin."

Sark'ewa na yi Hajiya Inna ta mik'omin ruwa na sha, ta rufe Kawu da fad'a shi kuwa ya soma zabgomin harara fuska a had'e, Baba kam girgiza kai ya yi tare da barin k'ofar ganin haka sai na rufa masa baya da hanzari ina cewa "Muje in gaisar da tsohon arziki Uban Mamana."

Kawu Habibu ya tashi tsaye zai biyo bayana Hajiya Inna ta daka masa tsawa ya koma ya zauna cike da ladabi ya tsira mata ido ba k'iftawa lamarin da ya razanata domin ta hango gaskiyan kalamansa cikin idanunshi.

Alhamdulillah anan muka kawo k'arshen free pages. Kamar yarda na sanar daku zaku sami ruwan kyautar pages to gasu nan da fatan sun sanyaku nishad'i fiye da zato na.

*Mun soma dai jin tsokacin labarin DAMUWATA to gundarin labarin na nan tafe cikin cigabansa sai dai babban DAMUWARMU shi ne sanin waye mijin Deejah. Aliyu, Uncle ko Habibu ne? Uhm ba zance komi ba domin Deejah allura cikin ruwa ce mai rabo ka d'auka sannan mai rabon zai bada mamaki. Tambayar a nan shi ne ta ya hakan zai faru? Shin me ye sirrin da Mama ke adawa da fitowarsa fili? Ina labarin k'azamin nufin su Hinde da Asabe? Ina k'udirin Nafisa na b'atawa Deejah fusaka? Shin addu'ar Aliyu na tab'a Zainab kuwa?Duban tambayoyi gami da amsoshinsu masu tarin yawa duk muna dakon jinsu abakin Mama da ma wasu jama'ar da bamu kai ga jiyo sunayensu ba. Labarin DAMUWATA ba damuwar Deejah kad'ai ke d'auke da shi ba, damuwoyin mutane masu yawa ne masu halayyar mabam-banta tare da soyayya mai tafiya cikin salo na daban da sauran da kuka sani.*

*Duk mai son cigaban labarin pay #300 to 0468069082 Haruna Safiyya GTbank or MTN card. Send the evidence via 08132166848. Update ba delay da yardan Allah S.W.A. Thank you fans, ina girmamaku iya girmamawa domin da bazarku na ke taka rawa. On 13 insha Allah zamu cigaba da posting ba kama hannun yaro. Bissalam sai mun had'u a paid group 😍* [11/7, 2:09 PM] 💘: DAMUWATA (Sanin abin adona) BY Safiyya (MRSJMOON)

Labarin DAMUWATA: Labari ne mai nisan zango domin komi da mafarinsa dan haka warwaransa zai zamo mai fad'i ne. K'aunar uwa da 'yar ba kara zube ya ke ba da mafarinsa wanda ya kasance fansa ce ga wata rai mai tasiri a jiki da ruhi.

(Ba'asan ta inda aka hau ba balle saukan) Kalma ce mai buk'atar li'irabi, gamsas-shiyar amsarta yana cikin Labarin DAMUWATA.

Labarin DAMUWATA ba damuwar Deejah kad'ai ke d'auke da shi ba, damuwoyin mutane masu yawa ne kana masu halayyar mabam-banta kuma da soyayya mai tafiya cikin salo na daban da sauran da kuka ji da gani.

Labarin DAMUWATA: Akwai wani zanen k'addara wanda ya ke tabbatacce daga Allah.

Labarin DAMUWATA: Ya k'unshi abubuwa masu ban al'ajabi, takaici da nishad'i. Salon labarin na dabanne, tafiyar k'uran na cike da fikrah, kudai ku garzayo ku samu damar kantashi cikin 'yanci.

Kada dai ku manta marubuciyar ta goge wurin warware zare da abawa tamkar dai a yarda ta saba tubka kuma ta war-wareshi tsaf a cikin littafanta kamar su: Rabi'atul Addawiyya Rashin jituwa Mutunci Madara ne Bak'on lamari Rumasa'u Mabrukha Dr. Laylah da sauransu masu matuk'ar fad'akarwa gami da nishad'antarwa.

Pay #300 to 0468069082 Haruna Safiyya GTbank or MTN card. Send the evidence via 08132166848. Update no dealy on 13 insha Allah.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull