Kenza eBookz

Damuwata complete novel - Chapter 5

Damuwata complete novel - Chapter 5

Damuwata complete novel Chapter 5: Damuwata complete novel Chapter 5. Lokacin dana fahimci Fanta nayimin k'auna wanda na rasa abaya wato k'awa na shiga…

3,346 words

Lokacin dana fahimci Fanta nayimin k'auna wanda na rasa abaya wato k'awa na shiga nishad'i ainun, wanda a dalilin hakan yasa na sanar da Mama dukkan DAMUWATA tun daga lokacin dana soma fuskantan rashin abokan mu'alama a waje da makaranta sai dai abin da na ke gudu shi yafaru domin Mama tashiga damuwa inda ta d'auki kwanaki tana maganar lamarin wanda na yi danasanin sanar da ita domin ban cika son mai-maita zance ba, idan abu ya wuce to ya wuce kenan a gareni.

K'aunata da Mamana na daban ne wanda zance banga wata d'iya da Mahaifiyarta ke jiyo DAMUWATA ko farin cikinta ba kamar yarda Mamana ke jiyo nawa. Lokuta da dama na kan zauna ina nazarin faruwar hakan amma a k'arshe sai na d'inauce na rasa gano dalilin. Hak'ik'a nima ina son Mamana domin ita ta koyar dani k'aunarta tun bansan kaina ba tamkar yarda ta zamo ita ce malamata na farko a fannin ilimin addini."

"Masha Allah da samun managarciyar uwa kamar Mama."

Beebah ta ambata cikin murmushi.

"Godiya nake sister."

"Mention not dear cigaba ina saurarenki."

Gyaran murya nayi na d'ora "K'awancenmu da Fanta hak'ik'a ina alfahari da shi domin a lokacin na gano samun abokin hira sa'anka na sanya natsuwa sama da komi.

A haka na cigaba da rayuwa cikin godiyan Allah domin a yanzu bana tare da Damuwar rashin abokin tattauna lamurana tunda na samu Fanta dik da ba komi na ke iya sanar da ita ba makar yarda bana iya sanar da Mamana dik kan DAMUWATA har kwanar gobe lamarin da ta ke kan yimin fad'a da in daina domin bai da kyau sam.

A yanzu haka na kammala Jami'a inda na samu Degree d'ina akan harshen turanci haka na yi bautar k'asa na kammala cikin nasara sannan na yi saukan Al'qur,ani mai girma tare da haddarsa da kuma wasu littafai na addini wanda Mamana ta jagoranci karantar da ni tun ina k'arama daga bisani na k'ara gogewa a gaban malamai. Mamana nada ilimin addini sosai da na boko daidai misali, shi yasa muke rayuwa cike da wayewa. Baba kuwa na addini gareshi domin shi malamin zaure ne wanda bai barin d'iyoyinsa yin karatun boko mai zurfi dan Mata daga Primary suke tsayawa Maza kuwa daga secondary domin suna kallamawa suke kama sa'anar hannu dan ba wanda yanemi gadar Baba a fannin malumta sai babban yayanmu Auwalu. Ni ce kad'ai na samu yin karatun Boko mai zurfi har zuwa matakin Jami'a, wanda bansan dalilin faruwar hakan akaina ba sai dai wani lokacin ina danganta rashin jituwana da Babana na da nasaba da zurfin karatuna tunda kaf d'iyoyinsa ba mai ilimina maza da matan, ba alfahari ba har zuwa na addini ba wanda ya kaini domin ni ce kad'ai na haddace Al'qur,ani cikinsu amma Mazan unyi sauka a gabansa Matan kam ko saukan basa samun damar yi ya keyi musu aure.

"Ikon Allah amma kin more kam Allah yayiwa iliminki albarka."

"Amin tare da naki."

Na amsawa Beebha cikin murmushi.

"Amma sai dai ban gane Rashin jituwar dake tsakaninki da Mahaifinki ba?"

Shiru na yi ina lalibo amsan da zan bata domin ciki ba anyisa dan cin abinci bane kad'ai har da ma'adanar ajiye sirruka.

"Ok just ignore it."

Na yi Beebah ta ambata a hankali.

Ajiyar zuciya na sauke cikin jan hamdala a ruhina dan ko Fanta da ta ke ganin komi a idanun ta ban tab'a yin maganar da ita ba haka itama bata tab'a tambayar dalilin faruwan hakan ba.

"Uhm Nana Khadijatu fad'in Uncle Muhseen."

Na kuma tsinakayar muryanta daf da kunnina murmusawa na yi tare da cigaba da cewa "Na yi training a catering school inda na samu kwarewa a fannin girkin zamani da had'a snacks dan na gargajiya wannan Mamana itace malamata tun inayi bai nuna har na zamo gwana."

"Masha Allah, a fannin aiki fa?"

"Nasoma karantarwa a wani Privet Shool amma yanzu na bari, sakamakon 'yar tsaman da mukeyi da yaron mai makarantar yasa na ajiye masu aikinsu. Haka nan mutumin ya d'uaki karan tsana ya d'oramin domin ko magana bai had'amu amma a kullum zak'ulo laifina ya keyi yana tozartani a bainar jama'a, gani da saurin kuka, da girmana na yi ta zubda hawaye d'alibai nayimin dariya akan haka Mama ta maramin baya na bar musu aikinsu. Kuma tunda na bar makarantar ba wanda ya waiwayeni da ban hak'uri akan haka naji banson sake yin wani aiki ko wani iri ne duk da ina da takardu masu kyau, idan nace zan nema bazan rasa ba.

Yanzu dai ina koyar da karatun Hadda a makarantar Tahfiz da na yi bisa tursa-sawan Mama wai wannan ta addini ne zan sami lada tunda Malaman suka biyoni gida to in je. Ba dan nasoba na soma zuwa, shi bana fuskanta matsala illa ta kallon nan da maza keyimin tamkar mai d'auke da lalura sannan muna hira da malamai jefi jefi, abu d'aya ke damuna a makarantar yawan hayaniyar yara domin abinda na tsana na farko kenan hayaniya dan na sakamin ciwon kai mai zafi, haka zalika kallon banza da mata keyimin duk in na shiga taro ko had'uwa da su a wani sabgar bai sanja ba, ako da yaushe DAMUWATA shi ne sanin dalilin faruwan lamuran biyu da suka kewayeni wato kallon da Maza keyimin na k'urulla da kallon da Mata keyimin na wulak'anta, shi yasa sadda ku ka shigo gidanmu na hango kulawanku gareni nashiga nishad'i ainun sannan gashi yanzu kin kuma tabbatarmin da hakan ta hanyar nunan k'auna tamkar yarda Fanta ta nunamin a baya."

"Ikon Allah hak'ik'a rayuwarki Deejah da a baben mamaki cikinsa sannan ina hasko lauje cikin nad'i amma ko meye shi ina rok'on Allah yasa khairan ne domin ba kyau danganta lamari da wani abu daban wanda ba khairan ba ne sabida wani abin daga Allah ne."

"Ina godiya da addu'a tare da nasiha akan yarda da k'addara mai kyau ko kishiyarta."

"Bakomi sister, Allah ya shige mana gaba."

"Amin."

Munyi shiru na wasu mintoci sannan Beebah ta kuma cewa "Deejah kin gama bani labarinki a tak'aice amma har kika kammala banji kin ambaci Saurayinki ba."

Idanu waje nake kallonta ta kyalkyale da dariya na yi hanzarin kulle mata baki ina kallon agogo cikin cewa "Sister dare fa ya yi."

Motsa kai ta yi cikin murmusawa ta ce "Ina saurarenki."

"Wai Beebah ke yar jarida ce ko marubuciya?"

"Babu ko d'aya."

"To in haka ne dan Allah ki rabu dani da wannan tanbayoyin naki, kuma wannan uban surutun da kika sakani na yi shi ne kike kira da tak'aitaccen tarihi."

"Eh mana domi in nasoma baki nawa sai mun kwana munyini ban gama ba."

Sa ke ware idanu na yi ta kawo yatsarta kamar zata sakamin a cikin ido na kulle da sauri, mukasaki murmushi a tare.

"To bani naki ina saurarenki."

"Wasa na keyi miki ni bani da labarin komi sabida komi na ke muradi na sameshi abokai maza da mata, 'yan uwa na gari tare da iyaye masu k'aunar farin cikinmu. A ittifak'i Aunty Nafisa ce kawai ta fita zakka a zuri'armu dan ita ta taso da fad'a tare da kyashi, hakan nan ita mai...

D'aga mata hannu na yi da sauri ta dakata tana kallona, juya kai gefe na yi "Dan girman Allah kada ki sake yimin maganar Aunty Nafisa saboda a duniya itace ta biyu da naji banson ko jin muryanta balle sunarta."

"Waye na farkon?"

"Sirri na ne dear Beebah."

Na ambata cikin dafa kafad'arta.

"Ok nadaina sonji kuwa."

"Godiya na ke da hakan."

"Uhm da wayau dai kin kori zancen Saurayinki ko Deejah?"

"Bani da shi kuma ban tab'a yinsa ba."

"Ban yarda ba kawai kina b'oyemin ne domin Fanta ta sanarmin bakya da sabo haka kina da zurfin ciki wanda har Mama kina yiwa."

"Eh na amince duk abin da kika ambata halina ne amma ki sani ke banyi miki ko d'aya ba, in baki yarda ba gobe ki tambayi Fanta idan na tab'a sanar da ita wad'an nan labaran duk dad'ewarmu da ita."

"No basai na tambayeta ba, na yarda kin bani matsayi na daban a rayuwarki kamar yarda nima na baki dan hak'ik'a ina k'aunarki Deejah k'auna irin ta tsakani da Allah."

Rungumeta na yi da sauri ina jan siririyar dariya, itama dariyar ta keyi. Mun raba dare da Beebah muna shan hira, barcin dake damuna tuni ya tafi kam dole.

Bayan ta idar da Sallar subahi domin ni ina fashin sallah, na dubeta cikin hasken da baiwadaci d'akin ba na ce "Sister sanar dani abinda kika hasko jiya wanda ya saka Aunty Nafisa ta k'onani."

Tasowa tayi daga saman sallayar ta dawo kan katifa ta rik'o hannuna ta ce "Na hasko Uncle Muhseen na sonki shi ne dali...

"So! Kuma? Wacce irin so?"

Na katseta da sauri idanu waje.

"It's may be na au...

"Dan girman Allah Beebah mubar maganar, rik'e abinda kika hasko a ranki na fasa jinsa."

Ina ambatar haka na zame na kwanta tare da juya mata baya, k'irjina kuwa sai harbawa ya keyi.

"Tabd'i jan kishi da Aunty Nafisa, ai abinda ma ba zai yiwu ba ne, ya Allah ka tsareni ji da ganinsa."

"Ba amin ba."

Jin maganar Beebah yasa na gano zancen da na keyi a zucci ya fito fili kenan. Shiru na yi tamkar mai barci alhalin idanuna biyu. Saukan hannun Beebah a bayana yasa na sauke numfashi ta rik'e arm d'ina ta soma magana cike da natsuwa yarda ko banso dole su shiga kunnuwana.

"Khadija wallahi Allah na hango k'aunarki a idanun Uncle Muhseen, kuma na yi murna sosai domin na sha jin Momy na addu'a akan Allah ya shirya mata Nafisa tare da bawa mijinta mafita akan bak'in cikin da yake kwasa akanta, nima danaji haka sai na soma tayata addu'a saboda na tsani mugun hakinta na rashin jituwa da dangin mijinta. Wannan dalilin ya sanya tun jiya dana hango kin fito daga motarsa tare da yarda fuskan Aunty Nafisa ya koma na amincewa ruhina kece mafitarsa kuma addu'ar mu ta karb'u."

Na juyo zanyi magana ta d'agamin hannu tare da cigaba da cewa "Ina mai baki shawara da ki amince da zarar ya ambata miki asirin ruhinsa, sannan idan har Allah ya nufa kika zamo matarsa wallahi kinyi miji na kere sa'a son dukkan d'iya mace ta sameshi a matsayin bokin rayuwar duniya har da lahira saboda yarin nagartansa a fili suke, na tabbata kema kin sansu."

Lumshe ido na yi ina jin tsigan jikina na tashi, abin mamaki sai naji tamkar in bud'e ido na yi arba da Uncle a zaune gabana kamar yarda Beebah ta ke yanzu.

"Deejah kince baki son sanin labarin Aunty Nafisa da na baki labarin fitinarta wanda ya kai mutanen gida basa murnan zuwanta ziyara itama hakan da ta lura da shi yasanya bata zuwa sai bayan shekara-shekara amma kinga Uncle yana zuwa dik k'arshen wata ko sati biyu sabida harkan kasuwancinsa yana da k'arfi a Maiduguri, haka yana kawo yaransa su Hafiz ganinmu duk in an sami hutun makaranta, yana da kyaky-kyawan fahimta da danginmu sama da jininmu Nafisa. Na ji kakarmu Hajiya Babba na cewa Aunty Nafisa irin mutanen ne da Allah ya halitta tsiya na ganiyar shed'ancinta dole muyi hak'urin zama da ita a haka."

Ban san sadda na kyalkyale da dariya ba jin abinda Hajiya Babba ta ambatawa Aunty Nafisa. Ita ma Beebah dariyar kyalkyale da shi

"Madallah da wannan safiya mai cike ni'ima."

Muka tsinkayi muryan Mama daga bakin k'ofa, cikin murya mai cike da nishad'i na ce "Amincin Allah ya tabbata ga Mamana, abin alfaharina."

"Amin Uwata farin cikin Hureratu."

Sakkowa na yi na yaye labulen na rungume Mama wacce ke tsaye a bakin k'ofa tana jiran fitowana domin lokuta da dama haka takeyimin, ta kance koyarwar Ma'aikin Allah S.A.W ta ke bi na neman izini shiga wuri kafin bayyana.

"Ina kwana Mama?"

"Muntashi lafiya Habeebah?"

"Lafiyalau Mama."

"Masha Allah, ya kuma gajiyar hiran jiya? Dan najiyo Uwata batayi barci da wuri ba."

Kulle baki Beebah tayi tana dariya k'asa-k'asa.

"Uwata ya k'afafun?"

"Sunyi sauk'i sosai Mama."

"Masha Allah, nagode Habeebah da taimako."

"Kai Mama ai Deejah tamuce tunda masoyiyar Fanta ce."

"Haka ne, Allah ya biyaku da khairan ita kuma Nafisa Allah ya shiryata."

"Amin."

Beebah ta amsa yayin da ni kuma na jefowa Mata tambayar

"Mama wa ya sanar miki da itace ta k'onani?"

"Mijinta kuma darajarsa taci wallahi da sai na koya mata hankali, ina da hak'uri amma akanki ban san kalmar ba, gidanta dai kingama shiga insha Allahu."

"Ayi hak'uri Mama kada Aunty Nafisa ta raba zumuncin nan tasu da Fanta."

"Wannan ne kam bata isa ba Habeebah, Allah da ya had'asu shi ya isa ya rabasu ba ita ba."

"Yawwa Mamanmu haka na ke son ji."

Murmushi Mama ta yi tare da ficewa, muka biyo bayanta ta shige kitchen ni kuma na soma gyara gida Beebah na tayani, muna gamawa muka koma kitchen muka amshi Mama aikin had'a abin k'aryawa. Kafin bakwai da rabi mun gama komi, mukayi wanka, na bawa Beebah kayana sabbi ta saka sannan muka zauna karyawa inda ruwan tea kawai nasha saboda ban son karyawa da sas-safe ya yin da Beebah ta baje ta cika tumbinta ba wani bak'unta.

Sake yimin dressing d'in ciwon Beebah tayi tare da matsamin nasha magani dan cewa na yi tunda ya soma k'ak'ewa ba zan sha ba.

Misalin k'arfe tara saura kwata na shirya dan zuwa makarantar Tahfiz inda na ke koyarwa, Mama taso hanani dubi da ciwona na nuna zan iya zuwa, Beebah ta biyoni muka fito muna hira cike na natsuwa. Kafin mukai Bintu ta kirata ta sanar mata da cewa sun wuce Kano ta yi musu fatar dawowa lafiya ta bani wayar nima nayi musu addu'a.

Muna shiga makarantar abokin koyarwana kuma classmate d'ina dan tare mukayi karatun hadda amma ya girmeni sosai wato Aliyu Muktar, shi ne ya dubeni cikin murmushi ya ce "Malama Deejah yau da bak'uwa kika zo mana?"

Kallon shi na yi kamar zan amsa masa sai na sami bakina da yin nauyi, jin haka sai na wuce na bar Beebah tsaye da shi.

*TALLA.*

*Ina kuke Mata 'yan kwalisa masu bawa fatarsu 'yancinta musanman babban kadararku wato fuska. To ga dama ta zo muku cikin sauk'i wato samun kayan gyarar fuska da jiki mai inganci na organic wanda aka samar da su da abubuwa masu nagarta. Duk wacce K'uraje, Tabbai, Sunburn, kyafsi suka b'atawa fuska muna da maganin da fuskanta zai dawo fes, sumul, rangad'ad'au. Haka a fannin fatar jiki shima muna da kayan da zaiyi laushi, sulb'i tare da haske mai kyau. Ga kayan kamar haka:*

Sabulu (molato and black soap) Scrub Face cream Oil Body lotion Shower gel Kulachan Humra (White and black) Turaren tsugunon Turaren kaya Turaren wuta na d'aki Garin d'a'a (domin k'an-k'aro martaban aure a turaka)

*Duk za'a samesu a farashi mai rahusa, mai buk'atar d'aya ko sari a tun-tub'emu a wad'annan numbers d'in 08132166848 ko 08147491137. Sai munjiku.* [10/16, 11:08 PM] 💘: DAMUWATA (Sanin abin adona) Mrsjmoon

EWF.

*Shafin na my Billy Galadanci ne, Allah ya bar zumunci tare da yalwatuwar nasara agareki mara iyaka, Amin*

Page 06.

"Kayi hak'uri haka Deejah ta ke sam bata da sabo musanman ga Maza."

"Ni ne shaida akan wannan halin na Khadija, tsawon shekaru da muka shafe muna karatu a cikin aji d'aya amma bamu tab'a maganar da ta wuce na mintoci biyu ba sai ko in karatu ne ya had'amu shima sai wurin muraji'a ko amsarwa juna hadda."

"Lallai kai ne ya dace ka sanar da mutane rashin sabonta ba wai asanar da kai ba."

"Uhm k'awar malama Khadija na tsareki da surutu, gashi har ta b'ace miki."

"No bakomi, dama rakiya nayo yanzu dai ka bani wurin zaman da zan dakaci fitowarta."

"Ok muje daga can in ban takuraki ba na tayaki hira kafin lokacin shiga darasina ya yi."

"Aikam ina godiya da karamcin nan, abokin Deejah."

"Aboki kuma?"

"Eh."

"Ina, ai ban isa na zamo abokin Malama Khadija ba saboda ita d'in kayan manya ne irin Sarakuna d'in nan masu fad'a abi dole ko da rai bai so ba."

"Kai Abokin Deejah, duk ita kad'ai."

"Allah kuwa Khadija ta da bance, samun irinta cikin Dubban Mata sai antona domin sauraren kalaman da suke fitowa daga bakinta kawai zai bawa mutum amsar cewa ita d'in ba sa'ar zancen yara irinmu ba ce ko manyanma sai wanda Allah yayiwa gamdakatar."

Dariya sosai Beebah ta sanya wanda hakan ya janyo hankali wasu malamai tare da d'alibai.

"K'awar Malama muk'arasa wurin kada nasamu kira daga hukumar makaranta ace ina zance cikin tsakiyar makaranta."

Motsa kai ta yi tana d'auke dariyar, suka jera cike da wayewa. Aliyu ya dubeta kad'an ya ce "Sunana Aliyu Muktar."

"Masha Allah, ni kuma Habeebah."

"Wow my Aunty, domin sunar babban yayarmu ce wacce muke Baba d'aya.

"A she ina tare da k'anina"

Motsa kai ya yi batare da ya furta kalma

A k'asar bishiyar magoro ya yi musu masauki saman kujerun roba, ganyen bishiyar na kad'awa cikin fitar da iska mai gamsarwa, hira suka cigaba da yi cike da sakewa tamkar sun jima da sanin juna.

*** Misalin k'arfe shabiyu saura mintoci goma na kammala koyar da aju-juwan danake shiga, na fito ina raba ido dan neman inda zan hango Beebah.

"Malama, Malam Auwal yana kiranki."

Idanu na zubawa matashiyar yarinyar tamkar ban gane abinda ta fad'a ba.

"Malam Auwal ne ya ce in kira masa ke, yana office d'insa tare da su Malam Bashir."

Motsa kai na yi, yarinyar ta bar wurin, najima tsaye batare da na motsa ba.

"A'a Malama Khadija kina lafiya kuwa?"

Saida nayi gaba kad'an sannan ta amsa "Ina lafiyalau Malam Hassan, dafatan kaima haka?"

"Alhamdulillah"

Ya amsa cikin nufar office d'in shugaban makarantar tamkar badani yake maganar ba alhalin shi ya soma.kulani, tsaki na ja a cikin raina tare da nufar office d'in nima ina k'issima dalilin kiran da a keyi min.

Office d'in cike da malamai na samu domin malamai shida ke ciki gami da shugaban makarantar bakwai, na zauna tare da gaisar da su a jam'i suka amsa, shiru ya ratso wurin zuwa can na tsinkayi muryan mataimakin shugaba Malam ishaq ya kira sunana, ban amsa ba illa idanu da na d'ago na zuba masa gabana na fad'uwa. Sake kiran sunana ya yi alamun yana buk'atar amsawana, amsawar na yi a hankali, ya yi gyaran murya tare da cewa "Shugaba Malam Auwal ya kiraki ne domin ya nemi alfarman da ki cigaba da koyarwa regular saboda wasu daga cikin malamanmu sun sami takardan cigaba da karatu a k'asar misra, idan sun tafi zamu fusakanci karancin Malamai shi yasa mukaga dacewar ki dawo koyarwa full, dafatan zaki amsa k'ok'on bararmu da hannu biyu?."

Wani dim na ji saboda burina na bar koyarwan baki d'aya sai ga wani batu sabo.

"Dan Allah Malama Khadija ki amince sabidya muna da bukatarki ainun, d'alibanmu na gane koyarwanki haka iyayensu na alfahari da hakan makarantarmu na samun d'auka ta wannan fannin, dan Allah kada ki watsa mana kasaya idanu."

Shiru na yi ina sauraren magan-ganun Malaman wanda duk kaninsu saida suka tofa albarkacin bakinsu ta hanyar rok'on amincewana a k'arshe suka tsuke bakunnansu suna dakacen amsana. Na d'auki mintoci kusan uku kafin na ce "Zanyi shawara da mahaifiyata."

"Allah yasa muji alkhairi."

Shugaba Malam Auwal ya furta cikin saukemin kallon k'urillah wanda na tsana.

"Amin."

Duk suka amsa.

Sallama na yi musu na fito sai dai ban ga Beebah a inda na barta d'azun ba, tsayawa na yi ina nazarin inda ta shiga, maganar Malam Hassan ya sa na juyo ina nemo amsan da zan bashi akan tambayar da ya yi min.

'Me yasa bakya alfahari da abin adonki Malama Khadija?' Tambayar nasa na sake maimaitawa a raina ina son sanin ma'anar kalman ABIN ADO daya ambata. Tamkar kuwa ya shiga raina najiyo yana yimin fashin bak'in manufarsa

"Manufata shi ne me yasa ba kya danganta kanki da Mahaifinki sai dai a koyaushe Mahaifiyarki kike ambata a muhallin Mahaifinki alhalin ita d'in k'asa ta ke da shi ta kowani fuska tun daga halitta har zuwa girman matsayi wanda Allah ya bashi akan sama da nata dan mace bata tab'a jagorancin d'iyoyintaba sai da tsayayyen namiji."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull