Damuwata complete novel - Chapter 6
Damuwata complete novel Chapter 6: Damuwata complete novel Chapter 6. "Malam Hassan kana da k'arancin sani akan muhimmancin Mahaifiya ga d'iyoyinta, tabbas…
3,367 words
"Malam Hassan kana da k'arancin sani akan muhimmancin Mahaifiya ga d'iyoyinta, tabbas Allah ya S.W.A ya fifita halittar Namiji akan Mace amma a wurin girman matsayi ta fannin biyayya sai ya fifita halittar Mace domin sai da ya ambata da abita sau uku kafin ya ambaci uba kaga kenan ba'aibu ba ne dan na ce zanyi shawara da mahaifiyata, ka san ko masu iya magana sunce ciwon 'ya Mace na 'ya Mace ce."
"Haka ne, kina da hujja mai k'arfi Malama Khadija amma kisani ba kowa ne zaiyi tunanin karatun da kika tunasar dani yanzu ba saboda bayan fitarki k'orafin yarda kike yawan ambaton Mahaifiyarki akan lamuraki sama da Mahaifinki alhali shi d'in jagoran al'umma ne, masanin ilmomin islama abin alfaharin dukkan 'ya'ya a ce shi d'in mahaifinsu ne, wannan dalilin yasa na ce zanyi miki tambaya kuma na gamsu da bayanenki Allah yasa mugama da mahaifanmu lafiya, musanman Uwa."
"Amin."
Na amsa a tak'aice tare da barin wurin cikin jin wani yanayi na rashin jin dad'in cece-kucen da sukayi akaina bayan fitna.
'Dole in bar makarantar nan dan bazan juri gulma ba.'
Cikin zancen zucci na isa bakin gate batare da na nemo inda Beebah ta mak'ale ba.
"Kinganni zaune anan ina dakon fitowarki domin Aliyu ya sanarmin da kin gama darasinki."
Kallon inda ta ke zaune na yi gefen bencin mai saida kayan fruits, da hanzari ta taho ta rik'emin hannu cikin rawar murya ta kuma cewa "Ke da waye Deejah?"
Girgiza mata kai na yi ta motsa hannuna da k'arfi, na kulle ido ina jan hailalah a cikin ruhina.
"Oya tell me! Waya tab'aki? In tafi na ci masa k'aniya."
"Ba kowa Beebah kawai gajiya ne, mutafi gida kada mutane su taru kinsan abin kallo baiyiwa jama'a wahala."
"Ki sanarmin da damuwarki K'awata."
Ta ambata amma cikin rad'a.
Dukan kafad'arta na yi cikin sauke mata murmushin yak'e sabidya yarda ta yi maganar takomamin sak Aminiyata Fanta, mai damuwa da DAMUWATA.
"Jini baya b'uya."
Na furta mata a hankali, ta murta dan ta fahimci inda zancena ya dosa. Hannunta na ja muka isa wurin mai saida fruits, yana ganina yasoma zubawa a leda murmushi ne ya kubcemin ganin abinda keyi wanda faruwan hakan ya tabbatarmin ya gama gane abubuwan da na ke siya duk in na shiga makaranta.
"Gashi Malama."
Amsa nayi tare da bashi kud'insa ya duba ya gyad'a kai, Beebah ta amshi ledar muka nufi bakin titi. Muna cikin Napep Beebah ta cikani da labarin Aliyu Muktar na dubeta kad'an ina k'unshe dariya saboda na san abin da zan fad'a dole yasanya ta barmin kunni ya huta.
"Nafahimci Aliyu ya mallake zuciyar 'yar mutanen Barno."
Aikam d'if ta d'auke zancen na saki siririyar dariya ina kallon idanunta ta had'e rai, sai na juya kaina gefe ina kallon titi domin haka na ke so.
Bayan mun watsa ruwa muka isa farandan Mama ta gabatar mana da abincin, shinkafa mai miya da salad, mukaci sosai tare da korawa da kunun aya mai sanyi. Tashi na yi zuwa d'akina Beebah ta rufamin baya, ina zama gefen katifa ta janyo kujerar kwalliya ta zauna tana wani cin magani dariya na kyalkyale da shi.
"Wato na zame miki mahaukaciyar ko Deejah?"
"No K'awata, kawai nagani ne fushin sam baiyi kyau da kyak-kyawar fuskanki ba."
Murmushi ta saki na jinjina mata hannun ta kama ta rik'e gam tare da cewa "Aliyu Muktar ke yake so ba ni ba."
"So?"
"Eh so tare da k'auna, Aliyu keyi miki kuma na gamsu da halayyansa d'ari bida d'ari dan haka ina baki shawara da ki amshe-shi a matsayin your first love, insha Allah bazakiyi da kin sani ba."
"Yaro ne shi Beebah, bana son b'atawa kaina lokaci."
"Kada ki butulcewa rahman Allah Deejah, domin Allah ne ya amshi rok'onki a yau kika sami wanda ya ambata miki kalman So wanda kike muradin jinsa da jimawa."
"Nagodewa Allah, Allah ya sanya khairan a tarayyanmu."
"Amin ya rabbi, haka ya kamata ki ambata ba wai zancen yarinta ba."
Sosa tsinin gancina na yi tare da gyara zama na ce "Beebah ya akayi Aliyu ya sanar miki da yana So na?"
"Labarin tsarin rayuwarki mukeyi wanda ke burgemu musanman rashin hayaniyarki da gudun abin magana, shi ne ya sanarmin da sirrin ruhinsa akanki wanda ya ce kusan shekara d'aya kenan yake burin ya sanar miki amma kwarjininki na yi masa shamaki sai ya kasa tunk'ararki da zancen, ganina tare da ke ya bashi kwarin guiwar sanarmin."
"Kwarjini kuma?"
"Yes Deejah, kina da kwarjini na ban mamaki wanda shi ne dalilin da ya sanya maza ke shakkar tunk'ararki da kalman So dan ba Aliyu kad'ai ke shakkar furta miki kalman ba hatta da shugaban makarantar tare da mataimakinsa dama wasu malaman duk sun kasa kallon idanunki su ce suna sonki."
"Ikon Allah, to ke wa yasanar miki da wad'annan bayanan?"
"Aliyu, dan ya ce da kunnuwarsa yaji suna tattauna zancen, lamarin da ya sanyashi k'amar jinya amma ganin lokaci ya ja bawanda ya iya tunk'ararki sai ya sami natsuwar ruhi, shi ne yau ya sanarmin domin inyi masa jagora da ki kulashi ko da cikin tsokali ne."
"Uhm to zan kulashi amma dai ina jiyowa ajikina kamar lamarin ba zai d'ore ba."
"Saboda me yasa kike son jifan lamarin da mugun fata?"
"To na yi shiru."
"Hakan ya kamaceki dama."
"Aliyu ya sami 'yar campaign a bulus."
"Eh naji dai kome zaki ce."
Juya kai na yi inajin natsuwar ruhi na ganin a she bana da cutar komi tunda gashi an sami wanda ya furtamin kalman k'auna abin da najima ina tsumayen jinsa a bakin Namiji.
"Aminiyar Fanta ko bakya son Aliyu ne?"
"Ta ya zan iya amsa miki wannan tambayar alhalin ni ban san ya kalman ta ke ba tun tsawon rayuwata."
"Deejah zaki sani da yardan Allah domin na hango tarin k'aunarki mara algus a idanun Aliyu."
"Uhm Allah ya sa hakan ne."
"Amin."
Lumshe ido na yi cikin son yin barci amma sai maganar da mukayi da Malam Hassan ya bijiromin na bud'e ido da sauri Beebah ta sakarmin murmushi cikin cewa "Yanzu bakiji kunya ba da kika ce Aliyu yayi miki yaro?"
Kulle ido na kumayi cikin murmushi batare da nace komi ba.
"Aliyu ba yaro ba ne, ya sanarmin shekarunta talatin da uku, shi ne babba a d'akinsu, yana da k'anni uku mace d'aya maza biyu da kuma wata wacce suke abokan wasa da Hajiyarsu ta rik'e amma ita ta yi aure.
"Tabbas nasan lokacin aurenta, dan naso zuwa Allah bai nufa ba."
"Kinga kenan inda a k'auye ne da yanzu ya kusa ajiye suriki."
Duka na kai mata jin sharrin da ta zabgo. Dariya muka sanya. Zuwa can ta mik'e ta dubeni na d'auke kai.
"Malama ta so muje na gaida Aunty Nafisa kada ta kai k'arata fadar Momy ko Alhaji Babba."
"Sai kindawo amma ni Deejah na gama shiga gidanta insha Allah."
"A she zancen bai wuce ba kenan?"
"Ya wuce amma dai yatsuna har yanzu zugi sukeyimin, kinga ko da ya wuce a raina to a cikin fatana da sauran miki."
"Kina da gaskiya Deejah kuma kin burgene da kika zamo mai fad'ar gaskiyan ruhinki, bari in tafi zuwa dare zan dawo, me kike son in dafo miki?"
"K'awata Fanta da mai da yaji."
Dariya ta kyalkyale da shi ta fice tana dariyar, murmusawa na yi na koma na kwanta na tsirawa ceiling ido, zuwa can na kulle su. Cikin barcin da yasoma d'aukana najiyo sababin Baba na bud'e ido da sauri tare da tashi zaune ina jan hailalah jin muryansa ya nufo k'ofar d'akina. Ina sauke kallona kan bulalan dake hannunsa na daka tsalle sai cikin toilet kafin in kulla ya ritsani ya rizgoni na dawo tsakiyar d'akin, wani tsalla na kuma dakawa na fad'a jikinsa na cukui-kuyeshi.
Gam na ji ya rungumeni har ina jin numfashi nayimin wuyar fita.
"Malam!"
Na tsinkayi muryan Mama cikin tsawa.
Tureni ya yi da sauri tare da daga bulalan zai zubamin Mama ta rik'e cikin wani lakan murya wanda bansanta da shi ba ta ce "Ficemin a gida na barka bari na har abada Malam, sadakinka zan bawa Baba Umaru ya baka kamar yarda ka bashi ya bani. A yau na tsaneka Malam tsana mafi mu...
Kullewa Mama baki na yi jikina na rawa ta ture hannuna abakin nata, kafin ta sake furta kalma na kuma kulle mata baki cikin cewa "Baba shima abin adona ne Mama ki barshi ya hukuntani wata k'ila laifi na yi masa."
"Malam ba abin adon ki ba ne Uwata, Ni ce abin adonki kuna ki barni na kwatar nama 'yancinmu, wallahi na gaji da lamarinsa, daga yau nagama aurensa."
"Mama ki daina fad'ar haka dan girman Allah."
Na ambata cikin matsanancin kuka.
"Na daina, kuma na hak'ura saboda kwanciyar hankalinki Uwata."
Rungume Mama na yi cikin jan hanci ita kuwa ta soma shafan bayana tamkar tana rarrashin yarinya 'yar yaye.
"Nagode Hurera da kalan halaccinki, nagode k'warai."
Muka tsinkayi muryan Baba ya ambata cikin shak'ewar murya. Da kallo muka rakashi har ya fice d'akin.
"Mama me na yi masa ya tsaneni?"
"Zan sanar miki da mafarin komi Uwata, wanda baici ya zama hujja ba ga mutum mai hangen nesa ."
"Ina saurarenki Mamana."
Shafo fuskana ta yi cikin b'oyemin b'acin ranta wanda ni kuma na karantosa amma sai na nuna bangane ba, na sake shigewa jikinta ina sauke numfashi, a haka ina manne a jikinta muka fito daga d'akina zuwa d'akinta.
*TALLA.*
*Ina kuke Mata 'yan kwalisa masu bawa fatarsu 'yancinta musanman babban kadararku wato fuska. To ga dama ta zo muku cikin sauk'i wato samun kayan gyarar fuska da jiki mai inganci na organic wanda aka samar da su da abubuwa masu nagarta. Duk wacce K'uraje, Tabbai, Sunburn, kyafsi suka b'atawa fuska muna da maganin da fuskanta zai dawo fes, sumul, rangad'ad'au. Haka a fannin fatar jiki shima muna da kayan da zaiyi laushi, sulb'i tare da haske mai kyau. Ga kayan kamar haka:*
Sabulu (molato and black soap) Scrub Face cream Oil Body lotion Shower gel Kulachan Humra (White and black) Turaren tsugunon Turaren kaya Turaren wuta na d'aki Garin d'a'a (domin k'an-k'aro martaban aure a turaka)
*Duk za'a samesu a farashi mai rahusa, mai buk'atar d'aya ko sari a tun-tub'emu a wad'annan numbers d'in 08132166848 ko 08147491137. Sai munjiku.* [10/17, 3:35 PM] 💘: DAMUWATA (Sanin abin adona)
By Safiyya (Mrsjmoon)
*Shafin na d'aukakin masoya labarin DAMUWATA ne, Allah ya biya muku bukatunku na alkhairi ya baku yalwan arziki daga cikin tarkokin arzikinsa. Ina sonku har cikin Ruhina.*
07
"Uwata ki k'ara zamowa mai juriya akan lamuran Malam, insha Allah zai zame miki alkhairi."
"To Mamana amma sanar da ni mafarin da Baba ya tsaneni."
"Kibar zancen Uwata wata rana ba sai kin tambayeni ba zan sanar miki."
"Mama dan Allah ki fitar da ni a duhu game da lamurana da Baba."
"Uwata kinsan na sanar miki zan baki labarin kaina ko?"
"Eh Mama."
"To mafarin tare suke da labarina"
Shiru na yi alamun ina son sani na dai k'yale ne kawai saboda bana cikin masu naci akan abu.
"Ina rok'onki Uwata ba dan ni sai dan wanda ya yi halittarmu cikin isa da mulkinsa wato Allah S.A.W da ki bar zancen nan in lokacin ki sani ya yi zansanar miki batare da kin nemi sani ba, ko d'azun natsuwarki na ke son gani shi yasa na ce ki taho kiji amma ba manufata na sanar da ke abin da kike burin sani ba, dafatan zakiyi hak'urin zuwar lokacin dana d'iba?"
"Shikenan Mama abin da kikace shi zanbi kuma zan dakaci zuwan lokacin da yarda Allah."
"Da kyau Uwata alfaharin Mamanta."
Murmushin na yi ganin yarda Mama ta yi maganar ta sigan wayon da ake yiwa yara dan su manta da abu.
Dik yarda ran Mama ya b'aci haka nan ta danne ta soma yimin hira mai sanya nishad'i, nima ganin hakan sai na sake na nuna mata bana tare da damuwar komi sannan wannan damar nabi na sanar da ita abin da ya faru game da buk'atar malamai na son in koma koyarwa kullum amaimakon a sati sau biyu dana ke zuwa.
"Uwata inaga ki sanar da su kin k'ara kwana d'aya akan kwanaki biyun da kikeyi sai ki koma shiga sau uku a sati Asabar, Litini da Laraba."
"Wallahi nima hakan na raya a raina Mama."
"To kingani, dama na hango rashin son hayaniyar da bakiso ne, haka zanso ki huta ba wai ace kullum kina zaryan fita ba."
"Mamana ta kaina, kina son Deejah ta huta alhalin itad'in ba 'yar hutu ba ce."
"Inji wa ya ce miki ke ba 'yar hutu ba ce?"
"Ni na fad'awa kaina."
"To ki sanar da kanki ke 'yar hutu ce domin baki nemi komi kin rasa ba."
"Haka ne Mama, a kullum Ina alfahari da samunki a matsayin mahifiya domin kin gama sharemin hawayen babu akan duk kan komi, wallahi sosai nake sonki Mamana."
"Ina godiya Uwata. Allah ya nunamin aurenki k'asa bai rufe idanuna ba."
Sunkuyar da kaina nayi ina murmushi tare da amsawa da Amin a cikin raina. So na ke na sanar da ita yau wani ya furtamin kalman so amma inajin nauyin ambata.
"Duk ranar da za'a kaiki gidan miji a ranar zan sanar dake abinda ya shige miki duhu Uwata, kada ki saka damuwa akan lamarin ked'in d'iyarmu ce abin alfaharinmu."
"Allah ya kaimu lokacin lafiya Mama, nima ina alfahari da ku."
"Muna godiya da hakan."
"Mamana kiyi hak'uri dan Allah ki sanarmin laifin da nayiwa Baba yau har ya tunzurashi yazo dukana dan in kiyaye sake aita laifin."
"Uhm Uwata bakiyi masa komi ba fad'ar ni da shi ne, to ganin ban kulashi mun raba hali ba shi ne ya d'auko doriga ya huce akanki tunda ni bazan doku masa ba sannan ya tabbatar in ya tab'aki zan kulashi."
"Mama kema kiyi ta hak'uri da lamuran Baba insha Allah watarana sai labari."
"To Uwata Allah ya cigaba da bamu hak'uri."
"Amin."
"Mamana wai meye abin adona?"
"Uwata baki san abin adonki ba?"
Shiru nayi zuwa can na amsa "Na sani kawai ina son k'arin baya ni ne."
"To sanarmin inji in kinsani."
"Ke ce abin adona Mamana domin hakan d'azun na sanarwa da Malam Hassan da ya sanarmin cewa wai Baba ne abin adona sannan naji d'azun kin ce shi ba abin adona ba ne sai na k'ara tabbatarwa da ke d'ince abin adona."
"Eh gaskiya Malam Hassan ya fad'a miki, Uba shi ne abin ado Uwata, daga yau duk wanda ya tambayeki abin adonki ki sanar masa da cewa Mahaifinki shi ne abin adonki, saboda duk tink'ahon 'ya ko d'a to da Uba suke ado domin shi ne haskensu a idanun al'umma ko da aya suke kuwa sune dai tink'ahonsu domin baki tab'a jin ance Mace ta zamo waliyyiya a wurin d'aurin aure ba sannan zancena na d'azun bacin rai ne ya sa na furta hakan amma Babanki shi ne abin adonki ta ko wani fuska."
Idanu na tsira mata ina auna zantukan saman harshenta zuwa cikin ruhinta sai na ji baya rasa nak'asu ganin a yarda ta dage tana mai-maita zantukan tamkar wacce aka tursasa.
"Ki cire shakku Uwata haka zancen ya ke har zu...
"Kina nufin duk takun sak'an dake tsakanina da Baba shi ne abin adona ba ke ba?"
Na katse mata abin da ta yi niyyar ambata.
"Tabbas Malam abin adonki ne Uwata haka nima abin adonki ce."
"Shi kenan Mama na amince zan rik'esa na d'an lokaci zuwa sadda zanyi aure amma ke zan rik'eki na har abada."
"A'a Uwata ki rik'emu abin adonki na har abada kinji."
"Kiyi hak'uri Mamana haka nan kawai na ji zuciyata takasa amincewa da in rik'e Baba na har abada kamar yarda na aminta na rik'eki."
"Lallai zuciyarki ta sanar miki da karatun gaskiya Uwani, kada ki sake ki rik'e ni abin adonki koda na minti daya ne domin bazan rufe miki cinya ba yayin da kika zo d'aura zani."
Idanu na zubawa Baba dake tsaye bakin k'ofar shigowa d'akin barcin Mama. Sai na sami kaina da jin fad'uwar gaba duk da ban gama fahimtar zancensa ba amma na hasko har cikin ruhinsa zancen ya fito. Motsa min kai ya yi alamun tabbatar da kalamansa fuskan nan nasa kamar dare saboda yarda ya d'aureta babu alamun rahma.
"Ki rik'eni ayar zuciyarki ta amince miki Uwani domin bazata sanar dake k'arya ba."
Ya furta cikin halin ko in kula.
Lumshe ido na yi ina hasko Baba a wani muhalli na daban wanda ya haddasa k'arin bugun zuciyana.
"Hurera ina son yau ayita ta k'are tsakanina da ke."
Jin abinda ya furta yasa na bud'e ido da sauri na sauke kan Mama wacce tayi k'asa da kai hakan danagani ya kuma jefa zuciyata cikin rud'ani matsananci.
"Kin amince na baki takardan sakin da kika nema yanzu?"
Da sauri na kalli Baba ya watsomin harara da jajayen idanunsa. Girgiza masa kai na yi cikin zubar hawaye na isa gabansa, ina bud'e baki zanyi magana kuka ya kufcemin sai na kife fuskata a saman k'afafunsa na soma rerawa cikin fitar sauti. Na sami wasu mintoci inayin kukan wanda bai k'areni da komi ba sai janyomin k'arin k'unci a zuciya zuwa can na tsagaita, cikin rawar murya na d'ago na kalli Baba na ce "Ba dan na isa ba sai dan martaban Manzon Allah S.A.W kada ka saki Mamana, ta tuba ga dukkan laifin da ta aikata maka cikin sani da rashinsa kuma bazata sake aikata abinda zai sosa maka raiba insha Allah. Ka hukuntani Baba idan yin hakan zai wanke maka b'acin ran da kake ciki, ka dukeni iya yarda ranka yaso ni d'in abar ikonka ce amma kada ka saki Mamana dan girman Allah."
Tsit d'akin yayi sai sautin kukana kawai ke tashi.
"Kinji abinda Uwani ta rok'a miki ko Hurera? Shin kin amince bazaki sake yimin rashin d'a'a ba tare da nunan iko akanta?"
"Eh na amince amma bisa sharad'in zaka dawonin da dukiyata da ke hannunka kafataninsu."
"Me ye! haka kikeyi Hurera!? Shin soyayyar d'iyarmu har ya kai wannan matakin ban sani ba?"
"Kafi kowa sanin abinda na keyi Malam kuma daga yau zuwa gobe na baka dan ina son ganin dukiyata a kammale tamkar yarda ka amsa domin kwandala ban amince ta yi ciwon kai ba, sannan ka aikata duk abin da kake ganin ruhinka na k'issima maka akan ni da Uwata ban hanaka ba amma ka sani ka tab'amin shaksiyyanta billahil azim sai na yi shari'a da kai wannan a rubuce ya ke bazan d'aga maka k'afa ba a game da dagulawa Nana Khadijatu lissafi, dafatan ka tuna zantukanmu na gaban Baba Umaru?"
Mama na gama ambatar haka ta mik'e ta janyo hijab d'inta ta zira ta fice batare da ta bari idanunmu ya had'u ba gudun kada in hanata aikata k'udirinta.
Kallona na maida kan Baba wanda zufa ke ta tsats-tsafo masa a saman goshi.
"Me ke faruwa Baba? Fitar da ni a duhu dan Allah."
Na jero masa tambayar jikina na rawa.
Abin maamki sai naga Baba ya sunkuyo gabana ya kamo hannuna ya matse gam a cikin nasa, ya yi k'asa da murya cikin cewa "Uwani ki taimaka ki bawa Mamanki baki da tabar maganar dukiyan nan sabida wallahi bani da hanyar samosu."
Shiru na yi ina cigaba kallonsa, sake yin k'asa da murya ya yi ya ce "Idan kika sanya baki nasan zata hak'ura bazata kuma tada zancen ba sannan kin taimaki Mahaifinki ga kub'uta daga tozarcin duniya idan mamanki ta k'wace dukiyanta da ya zamo rufin asirinsa."
"Baba idan na yi hakan zaka dawo yin mu'amala dani mai kyau kuma zaka amince kai d'in abin adona ne?"
"Zan daina hantararki Uwani idan kin cika alk'awari."
"Zamowa abin ado fa?"
"Kada ki damu Uwani aike d'iyata ce, ni dai burina ki tursasa Hurera data ya femin dukiyanta dake kaina yafiya kuma na har abada."
"To zaka janye zancen sakinta har abada kaima?"
"Wannan zancen an barshi Uwani, ni da Hurera aurenmu mutu ka raba takalmin kaza sunarsa da yardan Allah."
"Ina godiya Baba."
"Bakomi Uwani fatana dai ki cika alk'awari."
"To Baba amma shin kud'in ya kai...
"Uwani ke yarinyar kirkice mai hankali gami da natsuwa, Allah yayi miki albarka."
Shiru na yi ganin ya datsemin abinda zan furta da yimin yabo abinda ya zamemin sabon abu daga gareshi.