Damuwata complete novel - Chapter 7
Damuwata complete novel Chapter 7: Damuwata complete novel Chapter 7. "Uwani ke haske ce a rayuwarmu ni da Hurera dan haka ki kuma zamowa haske wanda bai…
3,372 words
"Uwani ke haske ce a rayuwarmu ni da Hurera dan haka ki kuma zamowa haske wanda bai yankewa a gareni ta hanyar yimin wannan alfarman."
"To Baba amma ka amsa...
"A'a Uwani kada ki yimin tambaya wanda samo amsarta zai zamemin babban aiki."
"Shikenan Baba na bar tambayar, insha Allah Mama zata mallaka maka."
"Da kyau Uwani, Allah ya rayaki rayuwa mai albarka."
"Amin ya rabbi Baba."
"Zan tafi amma dan Allah kada ki muna mata ni na tursasaki da ki rok'armin yafiyanta, kawai ki nuna mata ra'ayinki ne aikata hakan."
"Zan kiyaye baiyanar sunarka Baba."
"Madallah d'iyar arziki."
Da kallo na rakashi har ya fice, cikin tutani na shiga sai kuma na murmusa cikin jin natsuwar ruhi.
"A yau ranace da bazan manta da ita ba, Aliyu ya aikomin da sak'on yana so na, Baba yayimin magana cikin lumana har da sanyamin albarka, tabbas gobe zan tashi da azumi domin nuna godiyata ga Allah akan wannan rana da ya nufeni da ji tare da ganinsa"
Da sauri na tashi na soma gyara d'akin Mama duk da baya da datti. Ina gamawa na fito waje nanma na gyarasa tsaf sannan na shiga kitchen na d'ora girkin dare. Ina kammala zuba a bincin a kula na tsinkayi sallaman Fanta cikin karad'inta na fama, da sauri na fito muka rungume juna cike da murna, idanu muka had'a da Beebah na saki Fanta da sauri na nufeta ina doka murmushi.
"Ke dai tafi ku gama ganin juna da aminiyarki tunda abin 'yar wariya ce."
"Affuwan my Beebah."
Na furta cikin rungumota.
"Uhm ni sakeni ki tafi wurin Fanta ta baki sak'on farko daga Uncle wanda ya ce tukuici ne kafin ni kuma na baki ta biyu wacce tafi na farkon muhinmanci."
Kallon Fanta na yi ta zira hannu cikin hand bag ta fiddo leda fara sol ta mik'omin amsa na yi batare da na fidda abinda ke cikin ledar ba.
"Ciro da bissmillah Aminiyata domin mallakinki ne."
Fanta ta Umurceni.
"Tura hannu na yi na ciro abin da ke ciki d'auke da basmallah, ware ido na yi suka sanya dariya, bud'e kwalin dana ciro nasomayi jikina na rawa na cikaro da dalleliyar waya k'iran sumsung, takardan da ke d'auke da kudin wayar na kalla sai na ajiye wayar a k'asa ina kallon su Beebah idanu waje hannayena dafe a k'irjina.
"Ba'a maida hannun kyauta baya, ki amsa tare da godiya domin mallakan waya mai daraja irin wannan rabonki ne ya tsaga."
"Amma Fanta wayar sama da dubu d'ari tafi k'arfina."
"Idan ta million ce batafi k'arfinki ba Deejah domin na tabbata in kika ce kina so Mama zata siya miki dan haka ina had'aki da Allah ki amshi kyautar nan tare da yiwa Uncle godiya, ya tabbatar min ke tamkar ni ya d'aukeki kinga kenan shi yasa ya siyo mana wayoyi iri d'aya illa bambancin kala."
"To Fanta nagode sosai kuma a mik'amin godiya a garesa kafin inzo da kaina."
"Masha Allah, zaiji K'awata."
"Uhm!."
Beebah tayi gyaran murya, muka maida hankalin gareta, ta rausayar sa kai cikin kashe min ido d'aya sannan ta ce "Sak'on Uncle na biyu ita ce samun wuri na musanman a ruhinki."
"Banfahinceki ba."
"Zanyi miki dala-dala k'awar Fanta, ke dai bini a sannu kawai.
Zama na yi suma suka zauna, sallaman Mama ya dakatar da zancen sa Beebah ke shirin sanar da ji, mukayi mata sannu da zuwa ta amsa a hankali tare da shigewa cikin d'aki.
"Mama bata da lafiya ce?"
"Eh "
Na amsawa Fanta domin bana da amsar da tafi wannan."
"Allah ya bata lafiya."
"Amin."
Bari mu tafi zuwa anjima zan dawo sai muyi maganar amma kafin nan zan turo miki sak'o domin ki soma shirin burge Uncle d'inmu."
Tagumi na zabga saboda zantukan sun jefani cikin tunani, aikam a tare suka kyalkyale da dariya ganin yarda na yi tamkar mara lafiya, harara na cilla musu suka sake kwashewa da dariya tare da nufar hanyar fita gidan, ina kallonsu suka tafi na tashi jikina a mace na shiga kitchen na d'auko abincin, ina fitowa Mama na sanyo kai kitchen d'in sai na koma da baya ta shigo ta kama kafad'una ta rik'e gam, na rintse ido ina karanto addu'an samun kariya daga musiba sabida yarda naga idanun Mama ya tsoratani.
"Uwata kiyi hak'uri da rayuwa domin kowa da kika gani da abinda ya zame masa k'alubale duk kuwa muk'aminsa ko sarautarsa."
"Haka ne Mama shi yasa Annabi S.A.W ya umurcemu da mu zamo masu yarda da k'addara ta khairan ko kishiyarta."
Rungumeni Mama ta yi tana sauke ajiyar zuciya, mun jima a haka kafin da sakeni tare da rik'o hannuna muka fito na ajiye kulan abincin, zama mukayi a shinfid'ar da na yi domin cin abinci, sai lokacin idanunta ya sauka kan kwalin waya tare da wayar da suke a jiye gefe.
"Wa ya baki?"
"Uncle Muhseen ya aiko su Fanta su kawomin wai tukuicin dafawa abokansa abinci da na yi ranar Dana k'one."
"Allah ya biyasa da dubun alkhairori."
"Amin."
"A she abinda zai siya miki kenan d'azun ya shigo neman izini."
"Ya shigo wurinki Mama?"
"Eh ya zo shida Fanta ya sake bani hak'uri akan abinda ya faru sadda zai tafi sai ya ce yana neman izinin da in bashi dama ya rik'a kula da lamuranki kamar yarda yakeyiwa Fanta, na kuma bashi dama saboda na hango gaskiya a tare da shi gami da uwa uba natsuwa."
"Ikon Allah Uncle na da abin mamaki, a da fa ko na gaisheshi bai amsawa sai yaga dama amma daga jiya zuwa yau ya sanjamin matuk'a."
"Uwata hoo, to kika sani ko yana ciki ne?"
"Cikin me Mama?"
"Manema aurenki mana."
"Innalillahi! Bana fatan faruwan hakan Mama, dan Allah ki daina zancen nan bana so, wallahi bazan iya zama da matarsa ba."
"Uwata natsu dan Allah, nifa hasashe na ke yi ba zahiri ba ne da zaki rud'e haka kamar zaki zauna da mala'ikan d'aukan rai."
Mik'ewa na yi nufin yi dan gujewa zancen, Mama ta maidani na koma zaune ba shiri, cikin tsare gira ta dubeni na sunkuyar da kai.
*TALLA.*
*Ina kuke Mata 'yan kwalisa masu bawa fatarsu 'yancinta musanman babban kadararku wato fuska. To ga dama ta zo muku cikin sauk'i wato samun kayan gyarar fuska da jiki mai inganci na organic wanda aka samar da su da abubuwa masu nagarta. Duk wacce K'uraje, Tabbai, Sunburn, kyafsi suka b'atawa fuska muna da maganin da fuskanta zai dawo fes, sumul, rangad'ad'au. Haka a fannin fatar jiki shima muna da kayan da zaiyi laushi, sulb'i tare da haske mai kyau. Ga kayan kamar haka:*
Sabulu (molato and black soap) Scrub Face cream Oil Body lotion Shower gel Kulachan Humra (White and black) Turaren tsugunon Turaren kaya Turaren wuta na d'aki Garin d'a'a (domin k'an-k'aro martaban aure a turaka)
*Duk za'a samesu a farashi mai rahusa, mai buk'atar d'aya ko sari a tun-tub'emu a wad'annan numbers d'in 08132166848 ko 08147491137. Sai munjiku.* [10/19, 4:58 PM] 💘: DAMUWATA (Sanin abin adona) By Mrsjmoon
E.W.F
*Shafin na ku ne 'yan uwa rabin jikina, Yaya Sadiya (Mmn Ihsan) tare da Yaya Amina (Mmn Ganar) Alkhairori marasa iyaka su dawwama a gareku bi jahiy Nabiy S A W. Amin.*
Page 08.
"Uwata me ke damunki? Da kike son maida wata d'abi'a mara kyau ya zamo naki. Ni ce fa na ke yi miki magana amma kikayi nufin tashi ki bani wuri, innalillahi wa Inna ilaihin raji'un, yau wacce kalan rana ce tazo gareni ni Hurera."
"Rabbi igfirli. Na tuba Mamana kiyi hak'uri bazan sake aikata makamancin haka gareki ba."
Na ambata cikin rawar murya.
"Uwa banyi fushi da ke ba kuma da yardan Allah bazan tab'ayi ba."
Fad'awa jikinta na yi ta rungume ni, a hankali take shafan suman kaina zuwa bayana, nayi lamo ina jan hailalah domin samun nutsuwar ruhi.
"Uwata."
"Na'am Mama."
"Shi me ya kamata kiyi a daren wannan ranar wanda kika tsinci kanki da d'a namiji ya aiko miki da kyau mai matuk'ar amfani?"
"Zan rayata da nafilfili sannan na wayi gari da Azimi domin nunawa Allah godiyata akan faruwar hakan."
"Masha Allah, Uwata tafi na kowa hangen nesa."
Murmusawa na yi tare da sark'e tafin hannunta cikin nawa na ce ,"Mamana a yau abubuwa uku sun riskeni kuma dik a kusan lokaci d'aya, dan haka kema ki tayani nuna farin cikin ta hanyar raya daren da salloli tare da tashi da Azimin nafila."
"Wannan a rubuce ya ke Uwata amma zanso sannin ragowar abubuwa biyun dan nasan na farkon dai kyautar waya ce daga makwafcin arziki."
"A'a kyautar waya ita ce cikon na ukun."
"To ina saurarenki Uwata kuma Aminiyar Mamanta."
Manna jikina na sake na yi da nata sannan na sunkuyar da kai domin ina jin kunyar zancen farko, a hankali na ce "Mama a yau abokin karatuna ya aikomin da sak'on yana sona ta bakin Beebah haka a yau Baba ya... Hamdalah da Mama ta sanya mai k'arfi ya sanya na dakata da zancen na kamo hannunta na kife fuskata a kai ina dariya k'asa-k'asa.
"Uwata insha Allah sai kin tara masoya masu yawa, kin zab'a kin darje, ina fatan ki samu nagari maiyi miki k'auna ta hak'ik'a,."
"Allah ya nufa hakan Mamana."
"Amin, ai ina jiyo jinkirin nan naki alkhairi ne."
Ina kallon idanunta na cigaba da cewa "Mamana abu na biyu shi ne Baba ya sanya min albarka ya sanarmin ni d'in yarinyar arziki ce kuma haskenku ce ni, ya amince shi abin adona ne, ya tabbatar min bazai sake hantarata ba, mu'amalar arziki zai kasance tsakaninmu."
Kallon da Mama ke bina dashi yasa jikina ya yi sanyi sai na kamo hannunta na rik'e gam na ce "Dan Allah Mama ki yafe masa du...
"Uwata tashi muyi haraman sallah idan mun idar ina son yin magana dake sannan ina tayaki murnan abinda Malam ya ambata miki na albarka, ina addu'ar yasa har cikin ransa haka zancen yake ba don cikar wani buri nasa ya sanya shi yin furucin ba."
Kasa amsawa na yi da Amin sabida yarda jikina ya yi lakwas jin Mama ta harbo jirgin.
"Uwata ko har yanzu yatsun suna yi miki ciwo ne naga fuskanki ya sanja?"
Kallon yatsun k'afata na yi sannan na girgiza kai. "Sun k'ame banjin ciwo sosai sai abinda ba'arasa ba kamar k'ai-k'ayi na warkewa."
"Hakan na ke son ji, maza tashi muyi sallah a cikin lokacinta."
Mik'ewa na yi na shige d'akina. Saida na saka sabuwar wayata a chargy sannan na fad'a toilet. Ko da na idar da sallah sai na koma na yi suddaja na rok'awa Uncle Muhseen rahamar Allah tare da neman alkhairi a lamarina da Aliyu a k'arshe na rok'i Allah ya sanyawa Mama sanyi da ta yafewa Baba dukiyanta kamar yarda ya ke buri.
Bayan mun sallaci isha'i muka fito baranda muka zauna, abinci Mama ta umurta da mu soma ci bayan mun gama sai muyi zancen. Kamar ko da yaushe ban wani ci abin kirki ba sai kunun Aya dana cika cikina da shi. Bayan na wanke kayan da muka b'ata na dawo na zauna na tsirawa Mama ido murmushi ta sakarmin tare da tashi ta nufi zaure ba jimawa ta dawo.
"Na kulle gidan ne sabida na fahimci yanzu Malam ya koma yimana lab'e."
Kauda kai gefe na yi batare da na ce komi ba.
"Uwata kinajin haushina akan lamarinmu da Malam ko?"
"A'a Mama kawai dai raina baya son tanki in tanka da kukeyi ne akaina."
"Uwata bana iya jure ganin Malam na tab'amin ke ce."
"Shi d'in mahaifina ne Mama ki barshi ya rik'a hukuntani kamar yarda yakeyiwa d'iyoyinsa idan sunyi masa ba dai-dai ba."
"Ke kina da bambanci da su domin bakya k'yetare umurninsa kamar yarda sauran sukeyi masa, sam ba kyayi masa laifin da zai hukuntaki dan haka bazan bari ya zakunceki ba."
"Zalinci kuma Mama?"
"Eh."
"Shifa Uba yake gareni, abin ikonsa ce ni."
"Nasan da haka amma ki sani akwai hakkin d'iyoyi akan mahaifansu dan haka yi miki hukunci batare da kin aikata laifin komi ba wannan zalinci ne kuma ba zan tab'a lamunta ba."
"Nidai Mama ki koyi hak'uri akan duk wanda ya tab'ani domin wata rana sai labari, ko ance su tab'ani bazasu iya ba."
"Allah ya kaimu wannan lokacin Uwata k'asa bai rufe idanuna ba."
"Amin Mama."
"Uwata natsu da kyau ki saurari maganar da zan sanar miki."
"To Mama ina saurarenki."
"D'azun dana fita gidan Baba Umaru naje, mun gama magana akan aurena da Malam, zan bashi sadakinsa shi kuma zai bani takardata tare da dukiyata."
"Innalillahi wa Inna ilaihin, Mama dan girman Allah ki bar maganar rabuwa da Baba domin yin hakan tamkar kin maidani marainiya ce dan na tabbata Baba ba zai barni na zauna tare da ke ba, zai gwadamiki karfin ikon da mazaje ke gwadawa matayensu da zarar sun rabu da su."
"Ki rubuta zamanmu dake aure ne kawai zai rabumu amma ba k'arfin ikon Malam ba saboda ke d'iyata ce da na ke da iko ita ko ta wani fuska."
"Mama nidai ki janye maganar rabuwan nan dan girman Allah."
"Uwata in kinga na janye sai Malam ya bani dukiyata dama Baba Umaru ya ce idan ya dank'amin hakkina in janye maganar saki idan kuma shi ya bani takardana kamar yarda yake shiri to shi kenan ba kare bin damo."
"K'alu innalillahi wa Inna ilaihin yanzu aina Baba zai samo miki kudinki alhalin kinfi kowa sanin baya da hanyarsu."
"Yana da shi Uwata, mugunta ce irin tashi ya ke son dannemin gadon da mahaifina ya barmin wanda yasha wuya wurin tarasu."
"Mama nikam ina rok'on da ki yafe masa dan girman Allah da Manzon sa."
"Uwata Malam ne ya rok'eki da ki nema masa affuwana kika amince shi ne ya ke saka miki albarka tare da yi miki alk'awarin daina hantararki."
Shiru na yi domin idan na amsa da eh, na karya alk'awarin da nayiwa Baba akan bazan bari sunarsa ya fito ba in kuma na ce a'a nayi k'arya, shirun danayi shi ne mafita."
"Uhm Uwata kenan har yanzu baki gama sanin duniya ba to bazan bar masa ba wallahi tallahi kinji na rantse to ko baya sallah sai ya biyani hak'k'ina."
Tsirawa Mama ido na yi cike da ruwan hawaye.
"Uwata kada ki sakawa kanki damuwa, zamu warware da Malam saboda yana da gidan gona wanda ya bunk'asashi da dukiyana. Kuma kema kin san sagonsa na saida kayan hatsi, yana kuma da filaye kinga kenan yana da hanyar biyana dukiyata kuma ba da jimawa ba zakiga hakan domin Baba Umaru tsohon alk'ali ne zai amsarmin kayana kamar yarda ya amsa a hannuna ya mik'a masa bisa shaidun lauya da wasu dattawa."
"Nidai Allah yasa kada kuyi rikici a binda ke tadamin da hankali kenan."
"Bazamuyi ba Uwata dan haka ki kwantar da hankalinki idan ya tambayeki yarda mukayi kice masa kin sanarmin ban amsa miki ba."
"To Mama."
"Gobe da safe zamu shiga muyiwa Alhaji Muhseen godiya."
"Tare da ke Mama?"
"Eh domin nafiki jin dad'in kyautar nan."
"Uhm Mama kenan, Allah ni kad'ai zanje in yaso idan kun had'u kyayi masa."
"Nima na ambata ne dan naji na bakinki Uwata."
Murmushi na yi ganin Mama na son maidani yarinya k'arama.
"Uwata wallahi ina farin ciki da tarayyanku da Alhaji Muhseen sama da yaron nan Aliyu da kika sanarmin."
"Mama shifa Uncle bai furta yana sona ba kawai hasa-shenki ne abinda bana fatar ya tabbata."
"To shikenan Uwata Allah ya zab'a miki mafi alkhairi cikinsu."
"Wayyo Mama shin wai da wanda ya furta da wanda bai furta ba wanne ne dahir?"
"Wanda ya furta."
"To Mama Aliyu shi ne dahir d'ina."
Kallon da Mama ke yimin yasa na tashi da gudu na fad'a d'akina. Bayana ta biyo ta zauna gefen katifa ni kuma na koma k'asa na zauna kaina sunkuye.
"Uwata dik abinda kike so shi na ke so amma ki sani ke d'in allurar cikin ruwa ce mai rabo ka d'auka dan haka na ke baki shawara idan Alhaji Muhseen ya furta miki kalman so da ki amince kada ki duba kina da Aliyu, kinji ko?"
Gyad'a kai na yi alamun amsawa amma a k'asan raina addu'ar kada Allah ya bashi damar furtamin na ke yi.
"Uwata kada kiga ina ta ambatar Alhaji Muhseen kiga kamar dan yana da kud'i ne na ke kwadayin da ki aureshi sam ba haka bane ina dai duba natsuwarsa ne tare da sanin darajar makwataka da uwa uba ilimin addini da ta zamani da ya mallaka sannan ke shaidace yana aiki da iliminsa yarda ya dace."
"Haka ne Mama."
"Da kyau sannan shi managarcin namiji ne wanda duk kan uwa ta gari zata so d'iyarta ta zamo k'ark'ashin ikonsa wato ta aureshi a game da kyautatawa iyali kuwa wannan ke ce zaki bada shaidan shi d'in jarimi ne ta kowani fuska ga iya mu'amala da mutane da sanin hak'k'in makwaftaka, kinga ko dan wad'an nan abu-buwa zanso ace ya zamo surikina, Uwata ta sami kwanciyar hankalin da na ke yi mata addu'ar samu."
"Mama dan Allah kiyi shiru haka nan wallahi kina yin maganar k'irjina na harbawa sam bana son maganar."
"Shi kenan Uwata na yi shiru amma zan cigaba da yi miki addu'ar samun miji na gari ko da kuwa ba Alhaji Muhseen ba ne ko Aliyu."
"Nagode Mamana ta kaina."
"Uwata abin alfaharin Mamanta, za'a soma soyayya."
Tura fuskata na yi tsakanin cinyoyina, ina jin ta mik'e tare da shafo kaina sannan tafice. Tashi tsaye na yi na soma kai kawo domin magan-ganun Mama sun tsayamin a rai.
"Tabbas Uncle mijin aure ne amma matarsa abar tsoro ce."
Na furta a hankali cikin jan karan hancina. Hangowa wayata na haske yasa na isa na d'auka tare da sallama muryan Aliyu Muktar ya doki kunnuwata sai na daburce domin ban saba waya da maza ba in ba Kawu Habibu ba. Dariyar da najiyo yanayi k'asa-k'asa yasa na saita kaina har da wani tsare gira tamkar yana gabana na amsa sallaman tare da tambayar shi lafiyarsa.
"Lafiyalau, alhamdulillah matar Ali."
Ware idonu na yi jin sunar da ya rad'amin, dariyarsa na kuma jiyowa amma irin mai fitowa cikin iska d'in nan.
"Ina son Nana Khadijatu ainun shi yasa na kirata da Matana kai tsaye dan inaji ajikina ke d'in mallakina ne, uwar 'ya-'yana."
"Uhm, ya su Mama da sisters."
Na samu kaina da ambatar haka duk kuwa da naji dad'in kalamansa.
"Suna lafiyalau, Salma ta ce agaisheki kafin ta zo gida."
"Wacece ita?"
"K'anwarmu ce yanzu ta shiga S S 1."
"Masha Allah ina amsawa, sai tazo ina zuba ido."
"Ai tare zamuzo gobe da hantsi insha Allah."
"Gobe!"
"Eh ko bakya nan ne?"
"Ina nan sai kunzo."
"Insha Allah kafin mu taho zan sanar miki."
"To."
Mukayi jim zuwa can ya kira sunana cikin wani siga, ban amsa ba sai gyaran murya da na yi, murshinsa najiyo nima sai na murmusa.
"Yimin hirar k'auna dan bazan tambayeki amincewa da k'auna ta ba saboda tunda kika d'auki wayar najiyo amon amincewarki na amsa kuwwa a kunnuwana da tsokar zuciyata."
Dariya ce ta kufcemin ba shiri. Shima dariyar ya sanya daga nan yasoma yimin kalaman k'auna wanda bansan da su ba a rayuwata, ni dai iyakata da shi eh, a'a, uhm domin bansan taya zan maida masa da martanin ba. Muna tsaka da wayar Beebah ta shigo da sallama yana jin na amsa sallama sai yayimin sallama, na ajiye wayar ina kallon cikin idanunta.
"Soyayya da dad'i, wata yarinya ta fad'a a cikinsa."
"Baki da dama Beebah."
"Ina da ita fa sai dai inayin dana sanin yiwa Aliyu jagora zuwa gareki."
"Ban fahimceki ba."
"Zaki fahimta tunda gida bai k'oshi ba, ba za'a bawa dawa ba."
"Matsalata da ke kenan iya salon magana wanda bancika fahimta ba."
"Kina Bahaushiya amma d'iyar Kanuri tafiki jin Hausa."
"To ya zanyi?."
"Ki koma School ki yo degree a fannin Husa."
"Aiki ja, ban iyawa kam."
Dariya muka sanya.
"Ina wayarki?"
Nuna mata na yi da yatsa, ta iso ta cirota a chargy ta sanya layukan MTN da GLO ta soma latse-latse tun ina kallonta har na gaji na kwanta barci ya d'aukeni dama shi na ke ji sosai.
Washe gari ina kammala azkar na fito waje da Baba na yi arba zaune a baranda yana jan tsarbi, gabansa na isa na gaisheshi ya amsa cikin gyaran murya na koma d'akina batare da na shiga d'akin Mama ba.