Kenza eBookz

Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul - Chapter 10

Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul - Chapter 10

Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul Chapter 10: Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul Chapter 10. (Tofa! Tajwar......🤔 bara dai nai shiru🤫).

4,498 words

(Tofa! Tajwar......🤔 bara dai nai shiru🤫).

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_ _LITTAFI BIYU: 600_ _LITTAFI UKU: 800_ _LITTAFI HUDU :1000_ _LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI ACCESS BANK 0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 90165991

Books biyar 1250CFA Books hudu 1050CFA Books uku 850CFA Books biyu 650CFA Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨ (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)

𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻

*_19_*

..........Shigar Malikat Bushirat sashen Tajwar da yanayin data fito ya sake zama wasu ƙananun maganganu a masarautar, musamman ga masu ikon faɗa aji. Dan ta ko'ina suna da masu leƙen asiri a cikin hadimai da masu tsaron gidan kamar yanda itama Malikat ɗin ke dasu a kowanne sashe. Ga hadimai dai babu damar yin faɗa da kuwwa sai ƴar ƙus-ƙus, ƙus-ƙus ɗin ma sai ka samu wanda kafi yarda da shi kuɗan zanta gudun karka faɗa tarko.

★★......

Tun barowarta sashen Tajwar ta kasa zaune ta kasa tsaye. Abubuwane birjik ke faman mata kaikawo a zuciya. A karo na farko kenan da zuciyarta ta fara rawa akan al'amarin dake faruwa tun daga randa aka ɗora tilon ɗanta karagar mulkin kujerar Shahan-shan. Anya kuwa ba'akwai lauje cikin naɗi ba a wannan al'amarin?. Sannan ba zaton wuta a maƙera sukema komai ba alhalin yana a masaƙa?. Ta rumtse idanunta da sukai matuƙar ja da ƙarfi, saboda zuciyarta ke hasaso abun, amma ƙirjinta ne keci da wutar ƙunar dangantashi da abinda tafi so fiye da komai a duniya. Sai dai ya zatai, hakan kamar dole ne a gareta kodan rashin samun wani bakin zare har yanzu.... Kalmar bakin zare data faɗo a tunaninta ce ta sata buɗe idanu da sauri, sai kuma ta jawo ɗaya daga cikin wayoyinta da dan tsumar jiki tana gyara zama. Danne-danne tai tare da kaiwa kunnemta. Daga can akai sallama tun kafin ita tayi. A taƙaice ta amsa da faɗin, “Jasrah ina buƙatar hadiman nan yanzun nan”. “An gama Akia”. Jasrah ta amsa mata da girmamawa. Mikewa tai itama ta hau shirin fita fadarta. Sai dai komai tana yinsa ne a tsanake amma yanayinta tattare da matsananciyar damuwa. Fitowarta dai-dai da shigowar Ghazi, ya zube ƙasa yana mai miƙa gaisuwa a gareta. Hannu kawai ta daga masa bayan ta kai zaune. Jasrah ma dake zaman jiran fitowar tata tai mata sannu da fitowa. Kai ta jinjina mata da maida hankalinta ga Ghazi dake gurfane kansa a risine. Itama Jasrah hankalinta ta maida kansa. “Ghazi ya naganka kai ɗaya?”. “Ranki ya daɗe an samu matsala ne”. “Matsala kuma? Kamar ya kenan?”. Ɗan jimm yay na jimamin faɗar abinda ke bakinsa. Sanin Malikat Bushirat bata buƙatar kawane-kwane a magana ya sashi girgiza kansa idanunsa na canja kala zuwa ja sosai. “Ranki ya daɗe gawar uku daga cikinsu kawai muka samu, tare da hadiman dake tsaron inda aka killace sun su duka biyun. Diwa da ta rage ma bana zaton zata kai labari, kuma da alama yanzu-yanzu aka aikata ta hanyar madarar da aka basu matsayin abincin rana. Ba ƙaramar zabura Jasrah tai ba, yayinda Malikat ta rumtse idanu da sauri ƙirjinta yay wata irin harbawa da ƙarfi tamkar zai buɗe dan firgici. Amma a zahiri miskilancinta da ƙasaitar mulki bazai taɓa haska maka komai ba daga yanayin nata.....

★Kamar yanda labarin mutuwar hadiman nan ya isa kunnen Malikat Bushirat haka ya karaɗe kunen kowa a masarautar. Yayinda likitoci suka rufu akan Diwa da itama gab take da rasa tata rayuwar. Wasu kuma sun duƙufa ne akan binciken madarar da suka sha ta ƙarshe duk da kowa ya san daga cikinta ne akama zuba musu ko minene.......

*_ZAWJATA-ALMILKI_*

Yayinda ake tsaka da jimamin rasa hadiman da sukai sanadin shigar Iffah a mawuyacin halin da take ciki, ita kuma waraka ALLAH ya saukar a gareta bayan duƙufar Baba yaro akanta da maganin da aka amso a wajen Kaka. Tun a mata hayaƙin farko jinin dake fita a jikinta ya tsaya. Hakan ya basu hope ɗin cigaba da bin dokokin da kaka ya kafa na maganin daki-daki har ALLAH yasa aka dace ta kawo wani nannauyan numfashi da ambaton sunan ALLAH. “Ruwa!”. Shine abinda ta ambata na biyu. Cikin sauri Daneen Ammarah ƙanwa ta biyu ga marigayi Tajwar Haysam da ayanzu ke tare da ita ta zabura da kanta ta ɗauka ɗaya daga cikin bottle water dake a ɗakin ta ɓalle murfin ta kafa mata a baki. Cikin mawuyacin hali Iffah take zuƙar ruwar, sai dai kasancewar shine abinda tafi buƙata a ƙanƙanin lokaci ta shanye sa tas. Yumma da itama dai uwa ce gasu Daneen Ammarah ɗin, sannan matsayin Kaka ga Tajwar Eshaan dan ƙanwace ga Malikat Haseena ta sake ɓalle wani ta zuba a hanunta ta shafa a goshin Iffah dake jiƙe sharkaf da gumi. Ajiyar zuciya ta sake ja a hankali tare da buɗe idanunta da sukai mata matuƙar nauyi. Kaɗan ta buɗe ta maida ta rufe. Alhmdllh suka shiga ambata da mata sannu, yayinda Daneen Ammarah cike da zumuɗi tai kiran Malikat Bushirat. Ita ta fara sanar mawa kafin mahaifiyarsu Malikat Haseena duk da tana cikin halin ciwon ƙafa da bata iya ko miƙewa sai da taimakon wheelchair dama ga tsufa..... Cikin abinda baifi mintuna goma ba ɗakin da Iffah ke kwance ya cika da wasu a manyan masarauta. A fuska dai suna nuna farin cikin farkawar tata ne, amma a ƙasan zuciya mafi yawansu kowa da irin tasa manufar. Malikat Bushirat kuwa harda hawayen farin cikinta, farkawar yarinyar da a kallon farko ta gama shiga ranta ya goge mata sauran damuwar abinda ya faru game da kashe Hadiman da aka aika suka aikata sherin daya jawo komai. A take Malikat Bushirat ta bada ƙyauta mai tsoka ga Baba yaro. Hakama wasu a cikin manyan sun masa ƙyautar. Daneen Ammara ce ta biyu, itama kuma ta bada mai tsoka daya bama kowa mamaki. Ana ƙoƙari daukar Iffah zuwa sashen Malikat Bushirat kamar yanda ta buƙata sai ga saƙo da ga Malikat Haseena cewar akai Zawjata-almilki sashenta. Take fuskokin mutane da yawa ya canja a wajen, saɓanin ta Malikat Bushirat data nuna tsantsar farin ciki da jin ƙaunar surukar tata. Dan dama zuciyarta cike take da fargabar sake kasancewar Iffah babu tsaro. Duk da sashenta ma bazai iya zama kanwar lasa ba ga wani mahaluki a zahiri, sai dai yaƙin sunƙuru. To amma idan ta danganta da abinda zuciyarta ke rawa a kai komawar Iffah sashenta kamar an gudu ba'a tsira bane. Sashen Malikat Haseena kuwa sunyi imanin ko ifiritu da kansa zaiji tsoron gittawa kai tsaye balle wani shiryayye dake a masarautar.... Rashin ƙarfin jiki da rashin dai-daiton tunani yasa Iffah ba fahimtar komai take ba, hasalima tun yunƙurin farko bata sake gwada buɗe idanunta ba suna a lumshe. Sai dai tana jin komai dake gudana har ɗaukarta da akai akan keken asibitin zuwa waje. A mota a ka sakata Daneen Ammarah tare da ita. Sai Malikat Bushirat da tabi bayansu a tata motar da ake tuƙata. Ganin haka sauran ƴan son ganin ƙwaf suma duk suka bisu can dan babu mai fatar yin laifi ga Malikat Haseena.......

*_GIDAN BABIY_*

Tun bayan barin Iffah gidan ɗan sauran kakkaɓin farin ciki da ƙwarin gwiwar da su Fareeha suka barsu da shi ya ida kakkaɓewa. Ummu bata da aiki sai kuka. A kwana uku kawai duk ta rame saboda ko abinci bata ci yanda ya kamata. Hanash kam ba'a magana dan makamancin irin ciwon Iffah na damuwa ne ke neman bugarsa (Depression). Shi kansa Babiy dake dauriya duk ya zuƙe a tsaye wani lokaci har yi yake kamar zai faɗi. Komai ya tsaya musu cak, kunnuwansu ne kawai a buɗe na jiran kiran jana'izar tilon ƴarsu mace data rage. Dan gushewar kwana uku bai sa sun saka ran ta tsallake ba. Suna tsaka da wannan zaman jigum-jigum akai sallama da Babiy ƙofar gida. Kamar bazai fita ba sai kuma ya miƙe cikin ƙarfin hali ya zura takalma ya fita. Ɗan turus yayi idanunsa kafe akan wanda yay sallamar da shi... Abu Moosa da shima ke kallonsa ya iso gabansa da ƙyar yana tangaɗi. Riƙesa Babiy yay da sauri da faɗin, “Subahanallahi Abu Moosa!”. Bai iya ya amsa masa ba saboda halin da yake ciki. Riƙesa da ƙyau Babiy yay suka shiga ciki yana jera masa sannu. Zai zaunar da shi a soro ya girgiza masa kai cike da ƙarfin hali. “Kamin alfarma mu shiga ciki”. Ya faɗa da ƙyar tamkar numfashinsa zai rabu da gangar jikinsa. Cikin sauri Babiy ya cigaba da riƙesa suka shiga cikin gidan, shigowarsu yasa Ummu miƙewa da sauri ta ɗakko tabarma ta shimfiɗa a ƙasan bishiyar dake tsakar gidan... “Ku bani ruwa dan ALLAH”. Abu Moosa Ya sake faɗa da ƙyar yana fisgar numfashi. Ruwan Ummu ta kawo masa, dai-dai da fitowar Hanash daga ɗaki saboda jin maganganu na tashi a gidan nasu. Da ƙyar ya iya maƙwarwa uku saboda numfashinsa fisga yake. Babiy ya ajiye ruwan da sake tallafosa jikinsa. “Abu Moosa mike faruwa ne haka? Daga ina kake?”. Da ƙyar ya iya ɗaga idanunsa dake zubar da hawaye ya kalla Babiy. Sai kuma ya girgiza kan yana jan numfashi da shashsheka. “Abu Hanash ka gafarceni dan ALLAH, nasan wannan yana cikin numfashin bankwana da nakeyi”. “Babu abinda kamun nikam, dan ALLAH kuma ka daina faɗar wannan magana bara mu kaika asibiti”. Riƙo hanun Babiy dake yunƙurin tashi yay yana girgiza masa kai da ƙyar. “Babu buƙatar hakan, domin ban cancanci kwatankwacin wannan adalcin daga gareka ba, kayi haƙuri ka zauna ka saurari abinda zan faɗa maka da yafi kaini asibiti muhimmanci, nasan kuma insha ALLAHU zai maka amfani da kuɓutar da yarinyarka dama sauran yaran da zasu iya biyo baya a makamancin halin data tsinci kanta”. Numfashin dake neman kufce masa yaja da ƙyar kafin ya cigaba da faɗin, “Abu Hanash ka gafarce ni nine nai sanadin shigar ƴaƴanka wannan halin, dan nine nai shunensu ga masarauta”. Da ga Babiy har Ummu da Hanash wani irin zabura sukai mai bugawa da bugun ƙirji. Ya cigaba da faɗin, “Nayi hakane dan son zuciya da shegen son abin duniya. Sai hassadarka data daɗe a zuciyata saboda sana'armu ta kasance iri ɗaya, ada tare ake amsar zumar mu a masarauta amma daga baya aka koma amsar taka kawai saboda gaskiyarka da rashin algus. Maimakon na gyara nima na zama mutumin kirki kamarka sai na kasa hakan, shaiɗan ya dinga tunzurani akan kayi sammu ne shiyyasa. Tun daga wancan lokaci naketa ƙulla hanyoyin ganin bayanka a matsayin ɗaukar fansa, sai dai duk wadda na ƙulla sai ALLAH ya kuɓutar da kai, hakan ya cigaba da ƙaramin tsanarka, dan haka na cigaba da kutsa kaina cikin masarauta dan kawai naga na ɓataka an wulaƙantaka, nan ma banci nasara ba dai. Kwatsam sai aka samu canji gwamnati, ni kuma nai amfani da wannan dama wajen sake cusa kaina cikin tsakkiyar masarauta harna samu nasarar amsuwa, nasan komai game da mutuwar Zawjata-almilki, dan ina gaba-gaba a hadiman da ke aiki ga masu aikatawar”. Yaja numfashinsa da ke fisga da ƙyar. “Lokacin da aka sakamu aikin binciken yara mata guda biyu masu hankali dan a aurama Tajwar naji a raina lokacin nasarata a kanka ya yi, dan haka na bada sunanka da adireshin gidanka. An ɗauka tsahon kwanaki ana bibiyar yaranka da kai kanka kafin azo gareka. Ko bayan mutuwar ta farko ni na ƙara ƙulla aka sake dawowa ta biyu dan burina kawai naga na durƙusar da kai ƙasa. Ka gafarceni Abu Hanash dan nayi nasara, sai dai ramin muguntar dana gina daga ƙarshe ni na afka ciki......” Babiy da hawaye suka gama wanke masa fuska ya share yana duban Abu Moosa “Kenan kai ne ka ƙulla na uku ma?”. “Wlhy a'a bani da alaƙa da wannan, hasalima ban san ƴar wajenka bace sai ranar da aka kawo kuɗin aure”. “Waye ya kashe min ƴaƴa? Kai kuma miya faru da kai?”.......✍

🤔Ikon ALLAH, wannan duniya ina zaki kaimu, baka damu da kowa ba amma kana barcine da rashin barcin wasu, kana ci ne da rashin cin abincin wasu. Kana numfashi ne da burin ƙaruwar na wasu. Kana farin ciki da gushewar farin cikin wasu. Kana shiga tarkon wahala da dariyar bakunan wasu. Ya ALLAHU ka ɗoramu akan maƙiyammu, ka hanemu yin hassada da zaluntar wani koda ace shi ɗin ya zaluncemu. ALLAH sarki Babiy namu🤦🏻

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_ _LITTAFI BIYU: 600_ _LITTAFI UKU: 800_ _LITTAFI HUDU :1000_ _LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI ACCESS BANK 0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 90165991

Books biyar 1250CFA Books hudu 1050CFA Books uku 850CFA Books biyu 650CFA Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨ (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)

𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻

*_20_*

........Abu Moosa dake sonyin magana ya dafe ƙirjinsa da numfashi ke kokawar kufcewa, tari ne ya suɓuce masa sai ga jini. Hankalin Babiy da Ummu ya tashi, amma Hanash ko'a jikinsa. Da ƙyar tarin ya lafa, Babiy dake riƙe da shi yace, “Kayi haƙuri muje asibiti, aman jini fa kake yi”. Murmushi yay mai ciwo da kaɗa ma Babiy kansa da ƙyar. “Abu Hanash zuwa asibiti bazai canja komai ba, dan gubar da aka shayar da ni bata da makari a ko'ina sai a wajensu.” “Ya ALLAH! Guba kuma?” “Wannan shine hukuncin daya dace da masu irin halina ai karka damu, kai dai kawai ka saurareni zan gaya maka ta hanyar da zaka kuɓutar da yarinyarka, ina fatan hakan ya zamar min aikin alkairin dazan samu sassauci a kabarina”. Babiy zai yi magana ya dakatar da shi. “Ka saurareni kawa Ab.....” ya kasa ƙarasawa saboda sabon tarin daya sake sarƙesa. Sosai Babiy ya rikice ya shiga ƙwala kiran Hanash duk da yana a kusa da shi. Hanash dake jin tamkar yasa wuƙa ya ƙarasa numfashin wanan shegen tsoho ya amsa da ƙyar. “Kaga kamashi maza muje asibiti”. “K...k...karku wahal da kan.. Ku. ka saurareni kawai”. Abu Moosa ya tari numfashinsu da ƙyar yana dafe ƙircinsa da tari ke yunƙurowa. Babiy ya buɗe baki zai yi magana cikin taresa shima sai kawai sukaga yarab alamar rai yayi halinsa. Salati suka ɗauka a tare, wanda yay dai-dai da shigowar jami'an tsaro dake na ƴan sanda a ƙasar, bayansu wata mata ce ke rusar kuka... “Ranka ya daɗe dama na faɗa muku, na faɗa muku mutumin nan baya ƙaunar mijina, yanzu kun gani da idonku gashi nan ya kashe mini shi, dama kullum yana faɗa min neman rayuwarsa yake yi, ashe dai shine ɗin zai zama ajalinsa.....” ta zube ƙasa tana cigaba da kuka harda kururuwa.......

Hankali tashe su Babiy ke kallon wannan mata da jami'an tsaron, ba shigowarce ta tada hankalinsu ba da farko, dan tunaninsu ya basu duk wanda ya bama Abu Moosa guba shine yasa suka biyo sa. Furicin wannan mata da kai tsaye Babiy ya gane matar Abu Moosa ce ya firgitar dasu. Cikin ƙarfin hali Babiy yace, “Yallaɓai taya daga taimako kuma zan zama mai kisa? Abu Moosa abokina ne tun ƙuruciya kowa ya sani, ban kashesa a da da muke tare ba sai yanzu da a ƙalla nama kai shekara biyar kenan ban sakashi a idona ba sai yanzu dana gansa ayam cikin gidana babu zato.....” “......Shiyyasa akaga gawarsa a cikin gidanka yanzu daka samu damar ganin nasa ko?”. Jami'in ya tari numfashin Babiy da sauri yana wani makirin murmushin ƙeta... “Allahumma ajirni fi musibati wa'akhlifni khairin minha” Babiy ya faɗa a zahiri gumi na karyo masa. Duban jami'in yay zaiyi magana matar ta taresa tana cigaba da kukanta mai cike da bori.... “Ƙarya yake wlhy yallaɓai, shekaran jiya jiyan nan sai da yaje har gidanmu ya faffaɗa masa magana mara daɗi da tabbatar masa shine ajalinsa, idan ya ƙaryata ai munada shaidar hakan”. Hanash da zuciyarsa tazo ta tokare maƙoshi a hasale yayo kan matar, wata shegiyar shaƙa yakai mata saiga idanunta tamkar zasu fito waje. “K! baƙar matsiyaciya, dan kawai anga gawar mutum a waje sai ya tabbatar masu wajen suka kashe shi!!”. Idanuta ta rumtse da ƙarfi jikinta na ɓari, ta fara kakarin azaba dan da gaske ta shaƙu. Tuni jami'an tsaron duk sukai kansu da ƙoƙarin ɓanɓare hanun Hanash a wuyanta amma sun kasa. Ummu kuka ta sanya, yayinda Babiy keta kiran sunan Hanash da faɗin ya saketa amma sam babu alamar yana ma jinsa. Da ƙyar aka iya ɓanɓare Hanash, ta zube gefe tana sauke nunfashi da ƙyar hanunta riƙe da wuyanta. Sai da suka bata ruwan da suka fita suka ɗakko a mota da sauri tasha ta samu dai-daiton numfashi. Cike da gadara ogan tawagar ya bama yaransa umarnin kama Babiy da Hanash. Sosai Ummu ke kuka da roƙonsu amma babu wanda ya saurareta, har ƙofar gidansu daya cika da mutane tun isowar jami'an tsaron ta biyosu amma kamarma basu san tanayi ba. Haka aka saka Babiy da Hanash a mota, sai gawar Abu Moosa a Ambulance da sukazo da ita (Alamar akwai dai lauje cikin naɗi kenan. Inba hakaba miye na zuwa da Ambulance ɗin?🤔). Matan anguwar ne suka rufu kan Ummu data yanke jiki ta faɗi bayan wucewar motocin. Amma koda suka zuba mata ruwa bata farfaɗo ba. Hankalinsu ne ya sake tashi, makwafcinsu ya bada umarnin a sakata a motarsa a kaita asibiti. Da taimakon matan aka sakata a mota, matarsa da wata mata dake anguwar itama mijinta ya rasu suka shiga. Sai lokacinne mutane suka samu bakin magana. Wasu na nuna tausayawa ga wannan ahali, wasu na jin farin ciki badan sun taɓa musu komaiba, sai dan kawai dalilin hassada na rashin dalili. A asibiti kam har an amshesu za'a fara dubata sai sukaga Doctor ɗin ya dakata sakamakon kiran wayarsa da akayi. Kansa ya girgiza musu ya nufi barin ɗakin yana sanar musu yanada uziri. Hankali tashe makwafcin nan nasu da ake kira Abu Zainab ya shiga roƙonsa amma bai sauraresu ba. Sun fara neman taikon Nurses suma sai zuƙewa suke saboda gargaɗin da Doctor yay musu. Al'amarin kamar wasa anƙi taɓa Ummu, dole suka ɗauketa suka bar asibitin zuwa wani, sai dai acan ɗin ma har an amshesu aka koresu. Basu gajiyaba suna kuka suka nufi privet ko acan za'a dace tunda aikin kuɗine. Anan sun amsheta, amma sun sara musu maƙudan kuɗaɗe kafin su taɓata, acewarsu dokarsu kenan. Matar nan da mijinta ya rasu ta fashe da kuka tana girgiza kai. “Suma basa son su amshemu ne kawai, shiyyasa suke mana kora da hali. Inba kora da hali ba ai banajin Abu Hanash ya mallaki koda kwatar waɗan nan kuɗaɗen da suka ambata inba dai kaddararsa zai saida ba”. “Hakane Umm Yazeed maganarki nakan gaskiya, kuma tabbas na fara ji a jikina akwai lauje cikin naɗi a wannan lamarin, da alama hanasu amsarmu akeyi”. Abu Zainab ya faɗa ransa a ɓace. Matar Abu Zainab dake share hawayen itama ta ce, “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un. Wannan wace irin masiface haka? Mi bayin ALLAH nan suka tarema wani da zafi haka?”. “Sanin gaibu sai ALLAH, inaga inada mafita ɗaya, mu ɗauketa mu maidata gida sai a sanar da ƴan uwansu ko? Tunda mudai munyi iya ƙoƙarin mu...” “Da hakan kukai tun farko da baku wahal da kanku ba”. Wata murya ta faɗa a bayansu. Da sauri suka juya su duka, sai dai bayan mutumin kawai suka iya gani. Da gudu Abu Zainab ya bisa, amma kafin yaƙarasa garesan harya shige mota sai ƙura ya bulesa da shi.......

(🤔????)

*_MASARAUTA_*

Babban ɗaki na musamman aka warema Iffah a sashen Malikat Haseena. Tare da amintattun hadimai biyar da zasu dinga mata hidima. Sai Ghazi biyar suma da zasu dinga bata tsaro duk da dama sashen zagaye yake da masu tsaron, amma an ware biyar ɗinne na musamman domin kula da duk wani motsin shiga da fitar mutane da zai shafi Iffah. Hakan ya sake saka Malikat Bushirat a farin ciki matuƙa. Yayinda sabanin haka ya bayyana a fuskokin munafukai, sai dai wasu sunyi jarumtar dannewa baƙin cikin nacin zukatansu tamkar wutar daji. Malikat Haseena data zartar da hukuncin batama nuna tasan sunai ba. Ita kuwa Daneen Ammarah damar nutsuwar nazartarsu ta samu ɗaya bayan ɗaya dalilin wani ɓoyayyen al'amari dake ajiye a zuciyarta tsahon shekaru.

Daneen Ammarah ta kasance ɗaya daga cikin ƴaƴan Malikat Haseena da Tajwar Abdul-majeed Ibn Aliy. Su huɗu suka haifa. Tajwar Haysam shine babba, (sarkin daya shuɗe kuma mahaifin sarkin yanzun). Sai Daneen Waheeda tana auren wani babban sarki a yankin larabawa. Sai Daneen Ammarah, itama tayi aure sai dai auren bai jimaba sakamakon wani ɓoyayyen al'amari dake tattare da ita, wannan ne sanadin dawowarta gida take zaune kusan shekara goma sha tara kenan bata kuma sake wani auren ba. Ƴar uwarta da mahaifiyarsu Malikat Haseena da marigayi Tajwar Haysam da mahaifinsu daya bar duniya da tabon damuwar ƙaddarar ɗiyar tasa ne kawai sukasan wannan sirrin, al'amarin ya sameta tun tana ƙarama dan bata wuce shekara 14 ba, shiyyasa ta jima batayi aure ba, bayan ta samu tai auren kuma bata jimaba suka rabu da mijin dan auren baifi wata takwas ba ma. Manyan masarauta sunta ƙananan magana akan hakan da fassara al'amarin na Daneen Ammarah ta siga daban-daban amma su Malikat Haseena sukai biris dasu. Sai auta Miran Nayyar nada shekara bakwai ALLAH yay masa rasuwa.

Bazamuce Iffah tayi garau ba kam a wannan yini. Dan har yanzu ko idanunta bata iya ɗagawa ta kalla kowa. Sai dai daidaituwar fitar numfashinta ya saka nutsuwa a zuciyar kowa. Koba komai dai an samu sassauci ai. Daneen Ammarah itace da kanta ta gogema Iffah jiki ta canja mata kaya, itace kuma da kanta tai zaman bata abinci daya kasance mai ruwa-ruwa. Daga haka aka ƙara bata magungunan da duk suka dace da gyara mata kwanciya a lafiyayyen gadon da yaji shimfiɗu na alfarma. Wani irin barcine mai daɗi yay awon gaba da ita, cikin ƙanƙanin lokaci ta fara sauke numfashi. Daneen Ammarah dake kallonta cike da tausayawa da jin wani ɓoyayyen al'amari akan yarinyar ta sauke numfashi ahankali da mata addu'ar samun lafiya da fatan ya zama kaffara a gareta.......

★★.... ★.... ★★.....

Duk wani nau'in kiranye ga uwa ta yisa tun lokacin da labarin abinda ya faru da yarinyar can sakamakon saka riga ya risketa, tabbas sune suka bada riga, amma abinda ya faru da yarinyar bashine ya kamata ya faru ba akan rigar, dan shirinsu sam bashi da alaƙa da halin da take a ciki yanzun. Hakan na nufin kenan bayansu akwai wasu masu shiri akan yarinyar kenan?. In dai har hakane kuwa to su ɗin su wanene? Minene tasu manufar kuma?. Wannan amsar take buƙatar ji a wajen Uwa, sai dai har zuwa duhun dare babu alamar zata ziyarce ta. Tun zuciyarta na raya mata ta jira har ta fara jin ita taje gareta mana kawai. Amma tuna zuwa ga Uwa babban al'amari ne mai wahalar yiwuwa gareta yasa ta kasa iya cigaba da tabuka komai har dare ya cigaba da tsalawa masarautar ta ɗauki shiru tamkar babu wani mahaluki mai sauran numfashi. Ta cigaba da kaikawo a cikin wannan shiru, tare da ƙara gwada dabaru kala-kala na kiranye ga Uwa. Dai-dai lokacin da take sarewa, gaɓɓanta ke nuna gajiyawa mummunan sautin dariyar Uwa mara daɗin saurare a kunnuwa ta fara mata kaikawo tamkar tana yawo cikin iska. Ƙasa ta zube akan gwuyawunta tana mai jan nannauyan numfashi dajin sanyi a ranta. Tarwai Uwa ta bayyana a gabanta, akan kujerar baƙin karfenta mai adon gwal sanye cikin jajayen kaya kamar koyaushe. Mummunar fuskarta a matuƙar tsuke take babu alamar itace ta gama dariyar dataita amsa kuwa a mintocin da suka shuɗe..... “Barka da isowa Uwa mai share kukan masu kuka. Uwa ina cikin matuƙar ruɗani, dan aikinmu yasha banban da wanda ya bayyana ga ƴar shilar suda. Kamar yanda na riski yinin jiya a cikin ruɗani, haka na kasance a duhun dare batare da na rintsa ba, na kuma sake wayar gari da ƙishirwar ganinki a yinin yau har zuwa iyanzu da daren ke ƙoƙarin zama dare biyu da faruwar komai?. Shin kuskuren daga garemu ne? Kokuwa kece kika canja aikin ya koma hakan? Ko akwai wasu masu irin shirinmu ne a wannan daula batare da mun san dasu ba? Minene manufarsu su? Wane buri kuma suke da shirin cimmawa?. Uwa ki taimakeni nasan wannan amsoshi in ba hakaba zuciyata na gab da tarwatsewa ne”. “Bazan gaji da tuna miki akwai ƙalubale zagaye da cikar matakin aykinki na biyu ba, kuma wannan ƴar shila na tare da kaddarar ƙalubalenne, sai dai na miki alkawarin tsayuwar daka akan hana faruwar nasarar da zatazo in har bataki bace ba. Tabbas aikin ba namu bane, kuma rigar da aka kai mata ta sanya ba tamu bace itama. Na gano hakane a daren jiya bayan mutuwar waɗan can hadiman da kuma samun lafiyar ƴar shilar.. Hakane ya sani duƙufa bincike tuƙuru domin gano daga ina matsalar take?, wanene ya shirya aikin laɓewa bayan namu? Har yaci nasarar kuɓutar da ita da tarkon makircin sa cikin sauƙi haka?......” “Uwa kin gano kenan?”. Ta-kurya ta tari numfashinta cike da zalamar son jin amsa........✍️

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_ _LITTAFI BIYU: 600_ _LITTAFI UKU: 800_ _LITTAFI HUDU :1000_ _LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

Readers Also Read