Kenza eBookz

Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul - Chapter 11

Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul - Chapter 11

Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul Chapter 11: Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul Chapter 11. _TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE,…

4,208 words

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI ACCESS BANK 0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 90165991

Books biyar 1250CFA Books hudu 1050CFA Books uku 850CFA Books biyu 650CFA Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨ (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)

𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻

*_21_*

________________________

_Innalillahi wa-inna ilaihirraji'un. A madadin ɗaukacin ɗalibai na G.G.A.S.S D/Z. Muna miƙa saƙon ta'aziyyar ga ƴan uwanmu da iyayenmu da yayyenmu na rasa Uwa abin alfaharin duk wani ɗa na gari da mukai *Hajiya Ai'sha Ahmad Tukur* tsohuwar principal ɗinmu. Ya rabbi ka gafarta mata, ka yafe mata kurakuranta. Ka bama iyalanta da mu haƙurin rashinta. Mu data bama tarbiyya a wani bigire na rayuwa, ALLAH yasa muyi koyi da ƙyawawan halayenta managarta. Dan ita ɗin abin alfaharinmu ce da bazamu taɓa iya mantawa ba😭, zamu tunata, zamu cigaba da tunawa da ita, zakuma mu tunatar dana bayanmu kyawawan halayenta da alkairinta. (ALLAH ya gafarta mata.😭🙏🏻)_

________________________

...........“Ina kan ƙoƙarin yin hakan yawaitar kiranyanki ya katse ni, amma tabbas wanda ya aikata yana a cikin wannan daula ne, yana kuma da babban shirin daya kamata mu sani tun a yanzu. Ina kuma ji a jikina babban yaƙine da kema ya shafeki, kuma za'a cigaba da amfani da yarinyar ne wajen tabbatar da shi in har tana cikin masarautar nan”. “Shiyyasa tun farko nace a kawar da ita Uwa, dan babu wani amfani da wannan yarinyar zatamin face cigaba da ɗagamin hankali, gashi kuma har tana neman zama tafinta a al'amurana dake gab da kammala bayan gumurzun yaƙin da naci na tsahon shekaru a baya kafin zuwa lokacin tattara ganima”. “Abinda kike ƙoƙarin yi shine mafi girman kuskure da zai rusa dukkan nasarorinki Ta-kurya. Domin yunƙurin kashe wannan ƴar shilar da kike tamkar kashe rayuwarki ne baki ɗaya. Tun farko na faɗa miki kasheta kai tsaye bashine mafitar ba, ba kuma shine ƙarshen daƙile yunƙurinta ba ita a karan kanta. Hasalima a yanzu rayuwarta mukafi buƙata, zamu jefata ne matsayin dutse ɗaya dazai wargaza tsuntsaye biyu. An wargaza mana shirin mu na farko a kanta, dan haka zamu tafi na biyu. Yaƙinki a yanzu shine kiyi duk yanda zaki ta baro wancan sashen daga nan zuwa cikar kwanaki bakwai. Zakiyi yanka na baƙar babbar dabba a daren goma sha uku, zakuma ki dawo da rigar data sanya. Kiyi duk wani ƙoƙarin da zai hana kusancinta da Ajlaan a turaka. Dan maganar kaita turakarsa ta rushe kuma zamu sake sabon salo ne domin kama tsuntsu mai wayo.......” “An gama Uwa mai share kukan masu kuka. Sai dai dawo da rigar nan zai zama abu mai wahala kasancewar tana a hanun Mamma (Malikat Haseena) ne a yanzu haka”. “Wannan umarni ne Ta-ƙurya”. “Zanyi iya ƙoƙarina Uwa. Sai kuma maganar mutuwar Hadiman can, Shahanshan da kansa ya saka kwamitin bincike masu tsauri da basu taɓa ƙetare nasarar cika umarnin da'aka basu ba. Kinga akwai matsala kenan tunda waɗan can sun laɓe ne a jikin aikinmu suka zartar da nasu, sannan suka kashe hadiman tamkar yanda muka shirya kafin mu mu aiwatar da hakan”. Wata irin mahaukaciyar dariya mai amsa kuwwa Uwa ta shiga ƙyalkyalawa, sai da ta ɗauka tsahon lokaci tanayi kafin ta tsagaita ta tsuke fuska tamkar ba itace tayin ba. Har ta ƙurya ta fidda ran samun amsa sai kuma Uwa ta sake ƙyalkyalewa da dariya tana ambaton “Ajlan! Ajlan!! Ajlan!!!” ta ƙara kwashewa da dariya tana mai disashewa a idanun Ta-kurya da zuciyarta ta kasa fassara ma'ana ko dalilin dariyar ta uwa...

🤔Ko miye naku tunanin a wannan gaɓar kuma masu karatu???.

★... ★.★.★ ★...

*_GIDAN BABIY_*

Sun dawo har yanzu da ɗan sauran mutane maƙwafta da aketa ɗan ƙus-ƙus akan lamarin. Cikin ƙanƙanin lokaci aka baibaye motar, waɗanda suka shige gidaje suka fara fitowa. A yanayin da aka fidda Ummu mafi yawansu sunma ɗauka dai bata da rai, dan kuwa da gaske babu alamar rai tare da itan. Kuka da salatin da mafi yawan mutane suka ɗauka na tunanin ta mutun ne yasa Abu Zainab saurin dakatar da su. “Dan ALLAH kowa ya kwantar da hankalinsa. Umm-Arfa ba mutuwa tai ba”. Badan hankalin su ya kwantaba sukai shiru, sai dai dama kukan na wasu na munafurci ne dai. Matane suka kamata aka shiga da ita, a tabarmar da suka samu tsakar gida suka shimfiɗeta. Cikin sa'a Abu Zainab yaci karo da wayar Babiy dake yashe a ƙasa. Da alama sanda jami'an nan zasu fita da shine ta faɗi. Jikinsa har tsuma yake a duba contact ɗin wayar, cikin sa'a ya samo number da akai saving da Baba. Baya raba ɗayan biyu mai sunan nada babban matsayin baban a wajen Babiy ɗin, dan haka ya danna masa kira kai tsaye, sai dai harta tsinke ba'a ɗaga ba. Sake kiran yay yana addu'ar dacewa sai ko gashi an ɗaga...

★A lokacin da kiran Abu Zainab ya riski su kaka ta hanyar wayar Babiy ba'a ƙaramin tashin hankali suka tsinci kansu ba shi da Iyyani. Duk da kasancewar yamma tayi kuma yasan a yau dole ne sai ya dangana da daular ruman dole ya bazama neman wani yaro mai mota a ƙauyen nasu dake jigila a ko yaushe, cikin sa'a ya samesa ya dawo kenan ma ko gida bai shiga ba. Amma saboda mutuncinsa da ake gani yana masa bayani babu musu ya amsa masa suka ɗauka hanya harda Iyyani daketa faman sharar hawayen da suka kasa tsaya mata. Ana sallar isha'i suka iso cikin daular ruman. Basu sami mutane ba a gidan kamar ɗazun, sai Umm Yazeed da matar Abu Zainab dake dai tare da ita har yanzun. Zuwa yanzu Ummu ta farfaɗo, sai dai taƙi magana da kowa sai hawaye da taketa faman zirarwa ta gefen ido, ga numfashinta baya fita normal kamar na kowa, tana fitar da shine da fisgosa a wahale sannan a fiffisge. Kuka Iyyani ta sake fashe da shi da rungume Ummu a jikinta tana kiran sunanta. Kaka kam tsaye yay kawai zuciyarsa na harbawa da ƙuna. Suna a haka Abu Zainab ya dawo, dama sallar isha'i yaje. Cikin girmamawa ya gaida kaka, shima ya amsa masa da kulawa da godiya. Ya ɗan murmusa kansa a risine. “Ai ba komai baba yiwa kai ne. Sannan mun zama ɗaya ai mu da Abu Hanash. Ko mu irin haka ta faru da mu zai tsaya tsayin dakane a kan komai. Ruɗanin halin da Umm Arfa ke ciki yasa su bamu bibiyesu musan miya faru ba har yanzu gaskiya. Dan munata yawo a asibitoci amma sunƙi amsarta, ga jikin nata kuma yana buƙatar a duba mata shi, shiyyasa yanzu dana idar da sallar magrib naje na samo ɗan uwana dake aikin asibiti gashi muna tare, sai dai ba wani babban likita bane dai....” Kai kawai Kaka ya jinjina masa da faɗin, “ALLAH ya saka muku da alkairi, haka ake fatan zaman makwaftaka, domin ita makwaftaka tanada ƙarfin da zata iya fin ƴan uwantaka muhimmanci ma a wani ɓangaren. Yanzu gashi abu ya samesu, kafin mu muzo kun basu ɗauki, da bakwa zaman lafiya kuma hakan bazai yuwuba. Dan haka duk wani mutum na ƙwarai daya san kansa ya dace ya rayu da maƙwafcinsa lafiya da ƙaunar juna”. “Hakane Baba, ALLAH ya saka da alkairi. Bara na shigo da shi”. Murmushi Kaka yayi da jinjina masa kai. Koda suka shigo tare da ɗan uwan nasa shima ya gaida Kaka da girmamawa, hakama Iyyani da har yanzu ke faman sharar hawaye tana tofama Ummu addu'a. Damar duba Ummun Kaka ya bashi dan haka ya shiga aikinsa. Ya tabbatar musu jinin Ummu ya hau matuƙa, amma zai mata allurar barci ta samu nutsuwa dan barinta a ido biyu akwai haɗari komai zai iya faruwa. Sai da suka maida Ummu ɗaki sannan ya saka mata ruwa da allurai aciki, cikin sa'a kuwa babu jimawa barci yay awan gaba da ita. Sosai Kaka yay musu godiya da sanya albarka, dan ko sisi ɗan uwan nasa bai amsaba ma.......

★★.... ★.... ★★.....

An wayi gari da samun canji sosai a yanayin Iffah, dan zuwa yau kam Alhmdllh. Sai dai jikinta dake wani irin saɓa saikace wata macijiya. Sai kuma rauni data tsinci kanta a ciki sakamakon mummunan mafarkin datai akan su Babiy daya haddasa mata matsanancin faɗuwar gaba da akai-akai. Gata dai iya gata tana gani wajen tsohuwa Malikat Haseena duk da bata da lafiyar ƙafa sai a wheelchair take komai. Hakama Daneen Ammarah tsaye take kan Iffah, yanda take kula da ita yasa Iffah jin ƙaunarta batare data san dalili ba, ganinta take tamkar Ummu. Yanda ake tsaye kanta da gata da kulawa yasa ko damar yin ƙwaƙwaran tunani bata da shi, dan da tayi shiru Daneen Ammarah zata nuna damuwa taita jera mata tambayar mike damunta? Ko tamanin wani abu ne a jikinta har yanzu?. Dole take sassauta damuwarta, sai dai tayi matuƙar dagewa wajen ambaton UBANGIJI kamar yanda Babiy da Ummu suka dinga jaddada mata a nasiharsu ta ƙarshe gareta. Labarin mutuwar hadiman da suka kai mata rigar nan ta saka yazo kunenta itama, sai dai jin sanadin mutuwar tasu ya tsaya mata a rai matuƙa, harma ta rasa yaya zata fassara al'amarin... Bayan idar da sallar isha'i tana zaune tayi tagumi gaba ɗaya hankalinta ya tattara ga tunanin iyayenta da mummunan mafarkin daren jiya a kansu Daneen Ammarah ta shigo hadimai uku biye da ita. A bakin gadon takai zaune tare da kai hannu ta janye tagumin da Iffah tai. Nannauyan nunfashi ta sauke da ɗan ɗagowa ta kalla Daneen Ammarah ɗin, sai kuma ta maida kanta ta risinar da mata sannu da zuwa. Daneen Ammarah dake kallonta cikin damuwa taja numfashi ta fesar batare data amsa ba. Dai-dai nan Hadiman da suke tare suka zube gaban Iffah bayan sun ajiye kayan hanunsu. Gaisheta suke da tsantsar girmamawar da ko iya ɗaga kawunansu basayi su dubi sashen da take. Sam Iffah batajin daɗin yanda suke matan saboda bata sababa, a ranta gani take kamar ƙasƙancine. Hannu Daneen Ammarah ta kaɗa musu alamar suje, zumut suka miƙe tamkar ƙyaftawar ido suka fice. Iffah ta bisu da kallo cike da jin raɗaɗi a zuciyarta. “Ibnati!”. “Na'am Mamy!”. Iffah ta amsa cike da girmamawa ga Daneen Ammarah. Sosai sunan da Iffah ke kiranta da shi ke raunanata da sake jin ƙaunar yarinyar, dan a bakin mutum ɗaya tak take jinsa kafin ita. Taja numfashi da haɗiye hawayen da suka cika mata ido ta maye gurbinsu da murmushi. “Ibnati bana son cigaba da ganin damuwar nan a fuskarki, ki kwantar da hankalinki insha ALLAHU babu abinda zai sake samunki. Wanda ma ya sameki ki ɗauka kaddararkice kinji, amma inaji a jikina insha ALLAH kece mabuɗin nasararmu, ke ce hasken da zata haska mana duhun da muke a ciki a Daular nan kinji”. Kai Iffah ta jinjina a hankali, haka kawai take jin matuƙar nutsuwar kasancewa da wannan baiwar ALLAH, sam batajin irin zafi da tsanar da takema duk wani mai alaƙa da masarauta a kanta. Kallonta take tamkar wata katanga ta wani babban al'amari dake tunkarota. “Mamy bana tare da damuwa in har kina a kusa dani, duk abinda ya sameni kuma dama ALLAH ya ƙaddara sai ya sameni koda banzo nan ba. Ina tunanin su Ummu ne da jin tsananin kewarsu saboda mummunan mafarkin danai akansu jiya, ina tsoron kar wani abu ya samesu ne suma?”. Cike da jin tausayita Daneen Ammarah ta shafa kanta, “Duk ɗa na gari dolene ya kasance cikin kewa a lokacin da yay nesa da ahalinsa, da ace inada dama da a yau sai na kaiki kinga su Ummunki. Amma dokar masarauta ce Zawjata-almilki tana fitane kawai bisa ƙwaƙwaran dalili, zuwa gidansu kuwa tana yinsa ne sau biyu tak a shekara, ɗaya a sirrance, ɗaya a bayyane tare da rakkiyar hadimai. Shiko mafarki ai na gaskiya bane Ibnati, MANZANNI ne kawai idan suka yisa yake gaskiya a garesu, amma mu namu yakanzo da wasu sigogi ciki harda sheɗanu”. A hankali hawaye suka silalo a kumatun Iffah, bawai lokacin ziyarar bane yay mata nisa, rashin tabbacin kaiwa lokacin ziyararne ya sata zubar hawaye. Ita dake zaman jiran ƙaddarar mutuwarta taya zatai tunanin zuwan waɗan can damarmaki guda biyu na ganin su Babiy, maganar mafarki kam ta san gaskiya Mamyn ta faɗa, itama kuma ba tana dangantashi da zama tabbaci bane, kawai tana matuƙar jin tsoron faruwar wani abu ne a dalilin mafarkanta na baya.... Ganin hawayen Iffah ya matuƙar tada hankalin Daneen Ammarah, a rikice ta shiga tambayarta kamar yanda ta saba in har ta ganta a makamancin damuwar nan. Hannu Iffah tasa ta share hawayen nata da ƙirƙiro murmushi. “Mamy ki kwantar da hankalinki hawayen sunzo ne kawai da kansu babu dalili”. “Haba Ibnati, dama ana kuka babu dalili ne? Ko baki faɗaba nasan kinada dalilan yin kuka, amma idan kika zama mai haƙuri da juriya wataran ke zakiyi dariya a gaban waɗanda suka cancanta suyi kuka.” (ALLAH ya tabbatar da wannan ranar) Iffah ta faɗa a zuciyarta, a zahiri kam sai ta goge hawayen tana murmushi. Hakan yasa Daneen Ammarah yin murmushin itama, kafin kuma ta mike tsaye da kama Iffah suka koma kan dardumar da aka shirya abinci acan gefe na ɗakin, dan ɗakine ƙaton gaske mai dauke da komai na jin daɗin duniya. Tare sukaci abincin, Daneen Ammarah har tana bama Iffah wani lokacin a baki, jitake inama Iffah ɗiyartace, dan da'ace tana gidan aurenta har yanzu ɗiyarta ta fari zata iya kasancewa dai-dai da shekarun Iffah ne. Kulawar Daneen Ammarah ta sake saka sassauci a zuciyar Iffah harta ɗan saki jikinta. Bayan sun kammala ta sakata shiga bayi tai wankan maganin da take amfani da shi, data fitoma da kanta tai mata hayaƙin turare. Iffah ta hau gado ta zauna, Daneen Ammarah a gefenta da littafin tarihin annabawa acewarta zata dinga karantama Iffah har sai taga tayi barci domin ɗebe mata kewa. “Yauwa Ibnati kin shirya dai ko?”. Fuskar Iffah da ɗan murmushi tace, “Eh Mamy na” “Masha ALLAHU ashe dai Habibty na tare dani”. Hannu Iffah tasa ta rufe fuska tana murmushi, itama dai Daneen Ammarah murmushin take. Ta fara buɗe littafin. Iffah dake kallonta tai dauriyar finciko ɗaya daga ɗunmbin tabayoyin dake cin ranta ganin zata fara karatun... “Mamy dan ALLAH na tambayeki wani abu?”. “Oh Ibnati tambayeni mana kanki ma tsaye kuwa.” Iffah ta jinjina kanta da sauke ajiyar zuciya..........✍️

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_ _LITTAFI BIYU: 600_ _LITTAFI UKU: 800_ _LITTAFI HUDU :1000_ _LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI ACCESS BANK 0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 90165991

Books biyar 1250CFA Books hudu 1050CFA Books uku 850CFA Books biyu 650CFA Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨ (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)

𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻

*_22_*

.......Iffah ta jinjina kanta da sauke ajiyar zuciya, “Immm Mamy dama...” sai kuma tai shiru dalilin gargaɗin da zuciyarta ke mata tunda har yanzu fa Bama wai tasan matsayin Daneen Ammarah ɗin bane a masarautar. “Dama mi? Kinga karkiji komai kimin duk tambayar da kike buƙata, insha ALLAH zan kasance mai baki amsa, idan kuma bata dace ba zan baki shawara kodan nan gaba”. Kai Iffah ta jinjina “Dama dan ALLAH zance ne yanzu mutuwar su hadiman can shikenan ta tafi a banza baza'ai wani bincike a gano ba?”. Kallo na kusan sakan biyar Daneen Ammarah taima Iffah da har tama ɗauka tai laifi, amma sai taji taja numfashi da maida kanta kan littafin hanunta. “Mutuwarsu bazai tafi a banza ba saboda dalili mai ƙarfi Ibnati. Dan duk wanda ya kashesu yana gudun tonuwar asirinsa ne akan cutar da ke da akai yunkurin yi. A yanzu haka Shahanshan ya saka kwamitin bincike, muna fatan kuma ta wannan hanyar za'a gano koma wanene ya saka ki a halin da kika tsinci kanki. Kuma dama kema ana jiran ƙara samun lafiyarki ne aji ko akwai wani abu da kika sani, ko kuma bayan su ukun can da ɗayar da aka samu nasarar ceto ranta ko akwai wasu..” Da sauri Iffah ta dubeta. “Mamy akwai wadda bata mutu ba dama?”. “Eh akwai amintacciyar hadimar Umm-Jasrah (haka take kiran Malikat Bushirat) mai suna Diwa. Ita an kaita asibiti kafin gubar da suka sha ta karasa katsa ƴan hanjinta. Alhmdllh kuma an dace dan yanzu haka tana kan shan magani, tana kuma zagaye da tsatstsauran tsaro” “ALLAH ya ƙara bata lafiya, sai dai kuma banajin tanada hannu a cikin al'amarin Mamy, dan da ganinta mutiniyar kirki ce”. “Gane mutanen kirki ba'a ido yake ba Ibnati musamman a wannan masarautar da kowa kansa kawai ya sani, a mafi yawan lokuta ma ba'a gane maƙiyi da halayya. Akwai rikitattun abubuwa dake a matuƙar cuɗe a wannan Daular da gani da ido bazai wadaci mai kallo ba, dan haka nakeso ki nutsu kisa hankalinki waje ɗaya kafin ki koma sashenki ki koyi abubuwa da yawa na salon mulki da tsarin matsayinki na Zawjata-almilki. Saboda kunada matuƙar tasiri da girma a tsarin ƙarfin iko na masarauta da kaikawon talakawan ƙasan ruman. Fatana kuma kece Malikat a cikin Zawjata-almilki insha ALLAHU”. Sam Iffah bata fahimci komai ba ga kalaman Daneen Ammarah, amma sai bata sake cewa komai ba dan a ganinta tana buƙatar samun lokacin yin nazari na musamman a kansu kafin ta fahimcesu dallah-dallah.......

★★... ★... ★★....

Ana idar da sallar asuba drivern daya kawo su Kaka jiya dan hanashi komawa yay saboda dare ya ɗauka Iyyani da Ummu suka wuce. Kaka da Abu Zainab kuma sukai shirin fara neman inda zasu samo Babiy da Hanash. Dai-dai suna shiga mota kaka ya dubi Abu Zainab da ɗan murmushin ƙarfin hali a fuskarsa, “To Zakariyya kai ne ɗan gari, yanzu ta ina zamu fara kenan?”. Numfashi Abu Zainab ya furzar, tare da yin ɗan jimm alamar tunani, “E to Baba banace ba dai, dan al'amari nada wuya, saboda bamu da tabbacin waɗan nan jami'ai daga wane station suke. Amma ni yanzu a nawa shawaran ina ganin kamar mu nema gidan shi marigayi ɗin, tunda matarsa ita ta kawo jami'an tasan daga ina suke”. “Hakane, wannan ma shawara ce mai kyau, sai dai inda gizo ke saƙar kai koka san ina gidan Dawood ɗin yake? Dan ni dai rabona da shi ma kusan shekara biyar kenan tun suna tare da Muhammad Zayyan”. “Ito baba banace ba, dan kusan nima hakan dai take, amma bayan tashinsa daga anguwarmu nasan inda ya koma, sai dai bani da tabbacin ko har yanzu acan ɗin yake zaune tunda ba wani huɗɗa muke ba gaskiya, dama dalilin Abu Hanash ɗinne ake gaisawa sai kuma idan wani zama na anguwa ya haɗa kafin ya tashi kenan. Amma yanzu dai bara mu tafi can ɗin kawai rana ma nayi”.

Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso anguwar, kasancewar ma ta cika ba kamar da ba da kyar suka iya samo gidan. Duk da jikinsu ya ɗanyi sanyi ganin ƙofar gidan babu alamar anyi wani abu daya shafi mutuwa Abu Zainab yay sallama har sau uku. Ana huɗun wani mutum ya fito. Cikin binsu da kallon rashin sani ya basu hannu suka gaisa. Abu Zainab da shima dai jikinsa yay sanyi ya ce, “Kayi haƙuri nasan baka sammu ba. Muma dai munzo nan ɗinne neman wani bawan ALLAH daya zauna anan shekara kusan huɗu haka baya. Sunansa Dawood, amma ana masa alkunya da Abu Moosa. Matarsa ɗaya bashi kuma da yaro ko ɗaya”. “ALLAH sarki, gaskiya ban sanshi ba, dan nima dai ban wuce shekara biyu da tarewa anan ɗin ba. Na kuma sayi gidanne a hanun wani mutum Ibrahim Askari”. Abu Zainab zai sake magana Kaka ya girgiza masa kai alamar kar yace komai. Godiya sukai masa da sallama suka wuce.

“Baba ban san miyasa ka dakatar dani ba. Dama zan tambayesa ne ko zai faɗa mana inda zamu samu shi Ibrahim Askari ɗinne”. Numfashi Kaka yaja ya fesar, “Dalilin da yasa na dakatar da kai kenan. Kasan shi al'amari irin wannan yana buƙatar kasan dawa zakai maganar abu na gaba. Inaji a jikina waɗanda suka haddasa tushen wannan matsalar dole suma zasu kasance suna bin bayanmu domin toshe duk wata hanyar da zamu iya bi. Dalili kuwa shine ina kallon lauje ne cikin naɗi akan al'amarin”. “Eh gaskiya hakane kuma Baba. To amma in har hakane mizai hana mu nema lauya, sai nake ganin cikin sauƙi shi zai iya binciko mana inda suke ma, kuma koma minene sai yazo cikin sauƙi tunda ana magana ne akan abinda ya shafi shari'a ko kuwa?”. “Itama wannan babbar shawara ce a mahangar hankali Zakariyya, sai dai shi lauyan ne matsala musanma irin mu wanda muke bukata. Mai gaskiya da amana”. “In dai dan wannan ne babu damuwa insha ALLAHU, akwai yayan matata data rasu, kwararren lauyane kuma mai nagarta da nasan zakaso aikinsa kuma zai taimakemu kasancewarsa babba. A yanzu dai nasan bazamu samesa a gidansa ba. Bara kawai muje ofishinsa”...

★★..... ★... ★★.....

Kamar yanda Iffan ta nema alfarma a wajen Daneen Ammarah akan ɗakko mata akwatinta da aka kawo ta gidan dashi ya iso gareta. Taji matuƙar sanyi a ranta da farin ciki. Hadimar data kawo na fita ta buɗe akwatin ta shiga dubawa. Alhamdullah komai yana nan yanda yake, hatta takardar da malam Fawzan ya bata ɗinnan itama tana a inda ta ɓoye ta. Tana idar da sallar azhar littafin data sako a kayan nata kawai ta ɗauka da biro ta fara rubutu. Anutse take rubuta komai daya faru daki-daki tun daga barowarta gida har zuwa shigowarta cikin masarautar, abinda ya faru da ita dama wanda ke kan faruwa bayan warkewarta. Da zarar taji motsi koda ma Daneen Ammarah ne sai ta boye, a haka ta kwashe kaf yinin har zuwa dare tana abu ɗaya. Da daddare bayan kammala shirin barci maimakon kwanciya zaman karatun Alkur'ani tayi, koda Daneen Ammarah ta shigo ta sameta a hakan bata katseta ba. Tasa Hadimar dake biye da ita ajiye mata madarar da suka shigo da ita. Daga haka ta fice taja mata ƙofar da nufin ta dawo zuwa anjima, dan yanzu tana son zuwa ta duba Malikat Haseena ne da yai batajin daɗi. Iffah na ganin ta fice ta sauke ajiyar zuciya, addu'a tai ta rufe Alkur'anin ta mike, kofar taje ta sanyama key bayan ta leƙa babu kowa a corridor ɗin. Ta ɗan jingina da ƙofar tana mai ambaton “Alhamdullah” da sakin ɓoyayyen murmushi. Cikin sassarfa tabar jikin ƙofar zuwa ga akwatinta, ta buɗe tare da ɗakko wayar Arfa da takardar da Malam Fawzan ya bata. Number da aka rubuta ta kwashe a wayar, ta haye tsakkiyar gadon ta kwanta tare da jan lallausan bargon ta shige ciki har kanta sannan tai dailing number. Gaba ɗaya a kage take da zumuɗin a ɗauka. Dan haka take bin sautin shigar kiran da zuciyarta. Sai dai harta yanke ba'a ɗaga ɗin ba. Kira ta sake yi, nan ma dai shiru, bata gajiya ba ta cigaba da kira har fin sau goma kafin a ɗaga a karo kusan na goma sha biyar. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tamkar wadda aka tsamo daga cikin ƙanƙara. Sai kuma tai saurin faɗin, “Assalamu alaikum”. “Wa'ake nema?”. Aka faɗa daga can maimakon amsa sallamar tata. Da lafiya lafiya ne sai tayi mitar ƙin amsa sallamar, amma sai tai saurin faɗin, “Sir Ajmaal”. “Wa'ake nema?”. Aka sake maimaita mata tambayar. Zuciyarta ta ɗan fara zabura amma sai ta danne ta sake maimaitawa itama. “Sir Ajmaal”. “Wa'ake nema?”. Still aka sake faɗa kamar dai ba'ama jita ba. Wayar ta janye a kunenta ta tashi zaune ta ɗauka takardar, number dai dake a jikice dai-dai batai mistake ba. Sake maida wayar tai kunne aranta tana faɗin (bara naga ƙarshen ku dai) ta sake amsawa da “Sir Ajmaal”. “Kin saɓa lamba”. Aka bata amsa da yanke wayar lokaci guda batare da anjira cewar ta ba......

★★..... ★... ★★.....

Chapter notes and social links

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

Readers Also Read