Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul - Chapter 16
Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul Chapter 16: Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul Chapter 16. Masarauta da jama'ar cikinta zance ya yaɗu yau za'a…
4,491 words
Masarauta da jama'ar cikinta zance ya yaɗu yau za'a maida Zawjata-almilk sabon sashenta tunda ta samu sauƙi. Shaidar haka kuma nada nasaba da walimar da Malikat Haseena suka shirya, acewarsu ta aure ce da ba'aiba sanadin abinda ya faru za'ayi yanzu. Shirya wannan walima ya kawo ƙananun magana matuƙa, dan kuɗi aka kashe tamkar za'a sake wani sabon auren. Abin mamaki sauran mata biyu kafin Iffah ga Tajwar Eshaan sai al'amarin ya sosa musu zuciya duk da har yanzu zaune suke batare da ko Tajwar ɗin sun san kalarsa ba. Sam Iffah bata san da wani taron walima ba, sai da aka kammala mata shiri cikin wasu ƙawatattun kaya masu tsananin ɗaukar ido da tabbatar da ita amarya ta gaskiya mai amsa sunan Zawjata-almilk kanta ya fara ɗaurewa. A ganinta in har shigace ta iya rakata sashenta baici ace ta ƙawatu har haka ba kodan kasancewar dare ne ma. Kai mutanen nan fa sun fara caja mata ƙwaƙwalwa, ta faraji a ƙasan ranta akwai manufa. Amma dai koma minene zata jure har zuwa lokacin samun ƴancin kanta na komawa sashen nata dan ta shiryawa kowa talalarsa. A kwanakin baya ta kwantar da kai ne ga kowa domin fahimtar manufar wasu koda kalilanne a cikinsu. Alhamdullah kuma ta dace, dan koba komai ta gama samun yardar Daneen Ammarah da masu gayya da aiki Malikat Haseena da Malikat Bushirat. Duk da dai tasan kada mage ba yankata bane. Amma koba komai raina allura yakan sa ta zama garma ga wanda yay sakaci ai. Taji ba daɗi da barin ɗakin data rayu tsahon kwanaki cike da kewa. Koba komai bazata manta da rayuwar kusan sati uku da tayi a cikinsa ba. Ta koyi ilimi da yawa, harma da darasi data ɓoye matsayin sirrinta. Da wannan tunanin a ranta har aka iso babban ɗakin taro na cikin masarautar, wanda ya ƙunshi duk wani babba mai faɗa aji. Al'ajab ya kama Iffah, amma ta dake zuciyarta na sake tauri na nan dalilin ɓoye mata wannan zaman da akai. Amma a zahiri rashin ƙarfin cewa yasata yin luff kamar yanda ta kasance a kwanakin da suka gabata na samun lafiyarta. Daneen Ammarah data kasance mata ƴar jagora kasancewar fuskarta a sakaye take ta kaita har mazaunin da aka tanada dan ita a cikin ƙaton falon bisa tattausar dardumar da aka shirya walimar. Kamar yanda al'adar take, abinci aka fara ci yayinda Iffah ta gagara kai ko ruwan madara bakinta. Yanda tayi ɗin ya sake burge su Malikat Bushirat, suna ji a ransu sun dace da irin surukar da suke fata. Bayan anci ansha kowa ya nutsu. An fara buɗe taron da addu'a, tare da saƙon maraba ga sabuwar Zawjata-almilk, harma da fatan kasancewar ta abinda kowa ke fata. Kowa dai ya amsa da amin a zahiri, a baɗini kam sanin sirrin wasu sai ALLAH. A mataki na biyu shine zagayawa da Zawjata-almilk takai gaisuwa ga duk wanda ke wajen, kasancewar kakanni ne makusanta da iyaye, da yayye. A yanzu dai kam da taimakon Jasrah ta motsa, bayan ta janye hular rigar alkyabbar jikinta data hana kowa kallon ainahinta a tun farko. Duk da Iffah taji ta takura, hakan wata damace a gareta na sanin dukkan masu faɗa ajin, zai kuma zama jagoran abinda zai taimakawa nata ƙudirin. Idanunta suka cika da hawaye, a lokacin da take durƙushe gaban Malikat Haseena matsayin bankwana. Tanajin tsohuwar a ranta, ta kuma samu wani kebantaccen ilimin zamantakewa da ita. Ta saka mata albarka tare da yaba ƙyawawan halayenta da jinjinama iyayenta tarbiyyar da sukai mata. Ta ƙare da fatan alkairi da samun zuri'a mai albarka tsakaninta da Shahan-shan. Waɗan nan zantika sun zama abin kaiwa da komawa a zukatan manyan masarauta. Dan kowa na ganin kamar wata isharace Malikat Haseena ta isar cewar ta karɓi Iffah ɗari bisa ɗari matsayin Zawjata-almilk fiye dana baya da suka gabata. Iffah a karan kanta taji tausayin tsohuwar bisa ƙudirinta na shigowa daular ruman data tabbatar yasha banban da fatan da Malikat Haseena tayi gareta a yau gaban duk wanda ya isa a ƙasar ruman ma ba daular ruman ɗin kawai ba. Har yanzu har gobe da jibi tana akan bakanta na ɗaukar fansar rasa ƴan uwanta. Abin harinta kuma ɗaya ne tal shine Tajwar Eshaan, inma da wanda zasu biyo bayansa sai ta gama da babban dodon nasu. Ta samu ƙwarin gwiwar hakanne da tabbacin jin sai an kai matan turakarsa ake fiddosu babu rai. Sai kuma bincike da shaƙiƙansa guda huɗu sukai yunƙurin ɗaurata a yanzu haka. Kenan babu buƙatar wasi-wasi koma minene shike ƙullasa... Malikat Bushirat ma tayi irin makamancin addu'ar Malikat Haseena ne ga surukar tata. Ta ƙara da faɗin ita ɗiya takejin ta samu ba Suruka kawai ba, tana kuma fatan ta kasance kibiyar ajali ga masu ƙudirin sharri a ciki da wajen daular ruman. Tabbas maganar Malikat Bushirat tafi ta Malikat Haseena ɗumama zukatan wasu, yayinda mugun ƙudirinsu akan Iffah ya ƙara hauhawar farashi a zukatansu, amma duk sai suka ɓoye suma sukai mata irin tarbar data ɓoye dukkan ainahinsu. Dan Miran Jasim ma da akazo kansa har ƙyauta ta musamman ya gabatar ga Zawjata-almilk. Iffah data kasance cikin ladabi da ƙawata harshenta gaban kowa yayin miƙa gaisuwarta duk da ƙarancin shekarunta kaifin basirarta da wayonta ya bata damar nazari da adana cewar kowa a wajen da fuskar daya tarbeta ta hanyar kallonsu a ƙyalkyalin jikin rigarta datai matuƙar taimaka mata harta ambata godiya ga Malikat Haseena data zaɓa mata rigar domin sakawa a yanzun. Ba kalaman kawai ta riƙe ba da fuskokinsu da suka fita tartar bisa taimakon hasken kwayayen wutar lantarki. Harda sunayensu sun kasance kamar wani zane akan dutse cikin ƙwaƙwalwarta da zuciyarta. Ƙarfe goma da kusan mintuna talatin taron ya tashi na dare, aka fara fita da Zawjata-almilk da kowa ke tunanin sashenta za'a kaita kai tsaye. Sai kuma hakan ya bambanta da tunaninsu a lokacin da Malikat Haseena tabi bayansu akan wheelchair ɗinta matsayin maiyin wannan rakkiya. Abu ne da ba'a taɓa gani ba a masarautar. Dan hatta Malikat Bushirat da Daneen Ammarah sun sake jinjina wannan soyayya mai ƙarfi data shiga tsakanin Malikat Haseena da Iffah. Sai dai hakan ya musu daɗi, musamman Malikat Bushirat da take ganin hakan matsayin ƙarin sanin wanene Shahan-shan a zuciyar Malikat Haseena ga maƙiyanta. A lokacin da kowa ke fitowa daga falon da walimar ta gudana bayan gama sallamar sai da safe gagarumin labari da ɗumi-ɗuminsa shine cin karo da motar data ɗauka Malikat Haseena da Iffah a ciki ƙofar sashen Shahan-shan. A wannan karo hatta da Malikat Bushirat da Daneen Ammarah sai da sukai turus dan shirine da sam basu san da shi ba. A take suka koma ƴar kallo a tsakaninsu, cikin tambayar juna yaya akai haka kuma? Da idanu. Rashin amsa da mai basu amsar ya sasu shanye komai......
★★.... ★... ★★.....
Komai ya tsaya cak a ɓangaren su Kaka a kwanakin nan da suka gabata dangane da neman inda su Babiy suke. Barrister ya sake bin duk hanyar da yake da yaƙinin samu koda na ƙarfin iko ne amma sai ya risketa a toshe. Zuwa yanzu kam su duka ukun sun fahimci komai shiri ne bisa la'akari da labarin da suka bama juna na gargaɗin da akai musu. Sai dai abu mafi ɗaure kai da ban mamaki, wanene mai shirin? A wane dalili yay shirin kuma? Miyasa zaiyi shirin akansu Babiy ɗin?. Waɗan nan tambayoyi sune suka zama abun tattaunawa tsakanin Kaka da Barrister dama Abu Zainab daya saudaukar da dukkan lokacinsa domin ganin komai ya daidaita. Bisa shawarar Barrister Kaka yay shirin komawa Jimna, dan a cewarsa suna buƙatar bada ƙafa kodan harar rayukansu da aka farayi suma. Saboda a kwanaki biyun da suka gabata da ƙyar Barrister yasha a hanun wasu tankunan mai da suka sakashi tsakkiya bisa titi lokacin da yake tashi aiki. Haka yaron Abu Zainab a jiya anyi wuff da shi daga hanyarsu ta zuwa makaranta a cikin ƴan uwansa. Ba kuma a sakesa ba sai a daren jiya bayan sallar isha'i lokacin kowa ya gama jigata da nema da hasashen inda ya shiga. Rubutacciyar wasiƙar da aka haɗosa da shi yayin maidosa ya basu tabbacin daga inda tsiyar take. Kaka ya kammala kulle ko'ina na gidan sannan yay sammala da su Abu Zainab tare da godiya ya ɗauki hanyar inda zai samu motar ƙauyen Jumna. Harya sauka a mototaxi aka dakatar da shi, da mamaki yake duban mai mototaxi ɗin dake miƙa masa ƙaramar jakkar hannunsa. “Baba kayi mantuwa, ALLAH yasa na farga da wuri”. Kafin Kaka ya samu damar cewa wani abu saurayin ya ajiye jakkar gabansa ya koma cikin mototaxi ɗin da baiko waiwayo ya dubi Kaka dake yunƙurin dakatar da shi ba. “Kar kai jayayya tsoho, ka ɗauka dan naka ne”. Aka faɗa ta bayansa dai-dai yana kaiwa duƙe zai ajiye jakar. Ɗagowa kaka yayi, sai dai bayan mutumin kawai ya gani sai ƙurar motarsa. Ran Kaka ya sosu, har fuskarsa ta nuna haka. Alamar ƙosawa da wasan kwaikwayon waɗan nan mutane ya fara tunzura kawaicinsa da son bin doka a yanda tazo. Amma ya fuskanci burinsu kawai su kaisa maƙurar da sai ya gwada ƙwanjinsa akansu. Yay ƙwafa tare da ɗaukar jakar.......
★ “Boss ya ɗauka fa”. Wani matashin saurayi siriri dake zaune cikin taxi nesa kaɗan da Kaka ya faɗa yana ɗan kai hannu a kunensa ya dafe bluetooth ɗin dake manne a ciki. “Tabbas akwai alamar ɓacin rai tattare da shi a yau, dan fuskarsa harta kasa ɓoyewa”. Saurayin ya sake faɗa da alamar amsawa wanda ya kira da Boss ɗin a farko idonsa ƙyam akan Kaka da har yanzu ke tsaye jikin wata mota. Kai ya gyaɗa alamar an sake masa magana daga wayar, sai kuma ya gyara baƙar facing cap ɗin kansa da faɗin, “Eh da alama bai samu motar garin nasu bane. Amma gani ina tunkararsa, komi kenan zan cigaba da riƙe wayar dan kaji komai”. Kaka na shirin ɗaukar jakar da mai mototaxi ya barsa da ita zai bar wajen saurayin ya katsesa ta hanyar masa sallama. A ɗan daƙile ya amsa dan ransa babu daɗi har yanzun. A yanda ya kafe saurayin da idanunsa masu kaifi duk sai yaji ya tsargu. Ya haɗiye yawu da ƙyar cikin ɗan harɗewar harshe yace, “Baba tafiya ne?”. Kaka dake nazartarsa ya ƙyabe baki cikin masa kallon sama da ƙasa yace, “Kaima nasun ne?”. Sai da gaban saurayin ya faɗi, amma yay jarumtar ƙwaɓe fuska da faɗin, “Nasuwa kuma Baba? Ni fa mai taxi ne, na hangokane kawai na iso”. Kaka ya cigaba da masa kallon nazari, sai kuma ya furzar da isaka da kauda kansa yana kallon mutanen daketa faman kai kawo a titin cikin son watsar da lamarin saurayin... “Bar wajen kamar kayi fushi”. Aka faɗa daga cikin bluetooth ɗin dake manne a kunensa........✍️
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*
*DAUDAR GORA Billyn abdul*
*KI KULANI hafsat xoxo*
*A RUBUCE TAKE Huguma*
*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*
*IDON NERA Mamuh ghee*
_LITTAFI DAYA: 400_ _LITTAFI BIYU: 600_ _LITTAFI UKU: 800_ _LITTAFI HUDU :1000_ _LITTAFI BIYAR: 1200_
_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_
_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
MARYAM SANI ACCESS BANK 0022419171
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
09033181070
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09166221261
*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*
+227 96 09 67 63
Books biyar 1250CFA Books hudu 1050CFA Books uku 850CFA Books biyu 650CFA Bookk daya 450CFA
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨ (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)
𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻
*_31_*
.......Takun da baifi uku ba Kaka ya juyo ya bisa da kallo, kamar a bazata saurayin ya tsinkayi muryarsa na faɗin, “Jumna zanje”. Yi yay tamkar bai jisa ba. Hakan yasa Kaka sake ɗaga murya amma ya cigaba da sharesa shima. Yana ƙoƙarin shiga motarsa Kaka daya biyosa a baya yace, “Haba ɗan nan baka jini bane?”. “Sarai na jika Baba. Na fahimci ba tafiyar zakai ba, ba kuma hurimina bane tilastaka”. A karan farko kaka ya saki murmushi. “ALLAH sarki, to ayima tsoho haƙuri ɗana”. “Baba kamin laifin komai ba ALLAH, ai aikina ne. Dama naji kana sanarma wancan ne ni kuma hanyatace shiyyasa ma naje gareka. Zanje ƙauyen Yamanu ne dama”. “A Alhamdullah, lallai hanyarmu ɗaya Bara na ɗakko kayana.”
Mutum biyu kawai saurayin ya ƙara ɗauka bayan kaka suka ɗauki hanya. Hakan baisa kaka ya ji wani zargi game da shi ba. Sai ma hira da suka dingayi kai kace sun san juna. Bayan sauke mutum biyun daya ɗakko har ƙofar gida ya kai Kaka. Yaji matuƙar jin daɗin wannan karamci dan haka yay masa tayin shiga ciki yasha ruwa. Saurayin ya ɗan nuna tirjewa amma Kaka ya janye ra'ayinsa a dole ya bisa suka shiga, sai dai dama a ransa hakan yake fata. Ummu na zaune a tsakar gida ita da Iyyani, ta rame matuƙa tayi duhu irin na wanda ya shiga damuwa. Tamkar an sare gwiyawun Kaka ya ƙarasa shiga idanunsa akan Ummu data tsurama bayansa ido. Iyyani ma jiki a sanyaye ta miƙe dan tasan komai tunda kullum sai sunyi waya da Kaka. Itace tai ƙarfin halin masa sannu da zuwa. Ya amsa a sanyaye yana waiga bayansa. “Yaro shigo mana”. Kaka ya faɗa domin samawa Ummu nutsuwa. Da sallama saurayin ya shiga. Ummu tai ƙasa da kanta a hankali.
Bayan sun gama zama a tabarmar da Iyyani ta shimfiɗa musu saurayin ya fara gaishe da Ummu. Bata amsa ba, hakan ya sakashi shan jinin jikinsa yay shiru a sanyaye. Iyyani data sake kawo musu ruwa ce ta amsa masa da “Bata magana yaro”. “ALLAH sarki” ya faɗa cikin sauke ajiyar zuciya ita ya gaisheta. Da kulawa ta amsa masa dukkan hankalinta a kan Kaka dake kallon Ummu tamkar ya samu television. Ummu da hawaye suka cikama ido ta miƙe a hankali, ɗaki ta shige duk suka bita da kallo. Kaka baice komai ba hakama Iyyani data zarce kitchen sai gata da kwanon abinci.......
★★... ★★★ ....★
Tamkar raƙumi da akala haka Iffah ke tafiya bisa jagorancin Malikat Haseenat. Kasancewar dare ne babu yawaitar hadimai masu hidima. Sai dai masu tsaro tako ina kai kace zasu iya kare ran wanda suke tsaye a dalilinsa daga ziyartar mutuwa. Tsirarun hadiman da suka samu nata zubewa kwasar gaisuwa, Malikat Haseenat ce kawai ke iya jinsu da ganinsu. Iffah dake ta faman sauke ajiyar zuciya da al'ajabin dukiyar dake narke a wannan gini ji take komai ya ƙwace mata. Ta kasa fasalta komai ta kasa auna komai a ma'aunin rinjayen aikin zuciya dana ƙwaƙwalwa.... “Bismillah”. Malikat Haseenat ta katse mata ɗimuwar da take ciki ta hanyar nuna mata ɗaya daga cikin kujerun katafaren falon mai cike da abubuwan da bazasu lissafu ba. Da gaske Iffah bazata ma iya tantance yanda akai ƙafarta tazo nan ɗin ba. Komai Malikat Haseenat batace ba, dan ta gama karance ɗimuwar dake jagorantar fitar numfashin Iffah. Amintattun Hadiman dake a falon na uku suka zube gaban Malikat Haseenat kawunansu a ƙasa. Hannu kawai ta iya ɗaga musu. Babu buƙatar sai ta faɗa abinda tazo dan shi, shugaban hadiman dake a wannan falon ya miƙe zuwa ga landline domin isar da saƙon zuwanta... “Tsahon rai da lafiya su tabbata ga Uwa a garemu, shugaban na tsumayen isarku a falon sama”. Shiru malikat Haseenat batace komai ba. Yayinda Iffah da zuciyarta ke luguden ke saurarensu cikin juyewar tunaninta da har yanzu bai dawo dai-dai ba. Kusan mintuna uku Malikat Haseenat taima Iffah nuni data miƙe, ita kuma ta birka wheelchair ɗinta suka shiga lifter. Mintuna biyu ne kacal suka iso da su katafaren falon da yafi kowane falo ƙawatuwa a kaf daular ma da sashen kawai ba. Iffah tai ƙoƙarin danne harbawar ƙirjinta sakamakon tozali da wanda ke zaune a falon cikin zama na ƙasaita da izzar masu mulki. Tafiya take tamkar hawainiya saboda tsabar kasala da sanyin gaɓɓai. Zuwa yanzu wannan fuskar bata aljani take fassarata ba, neman ƙarin bayani take a kanta a dalilin ganinta a waje biyu da basu da alaƙa da juna a zahirin rayuwa... Tajwar Eshaan da ke kishingiɗe bisa ƙayataccen kujera mai kama da wani madaidaicin gado gabansa butar shayi ce da ƙaramin kofin da alamu suka nuna yasha ko zai sha, idanunsa ya janye daga kan television da yake kallo ya ɗan waigo garesu. Akan Iffah dake tafiya tamkar hawainiya ya fara saukewa, fuskarta a sakaye take, hanunta dake riƙe da rigar jikinta ne ta ƙasa kawai a bayyane. Janye wa yay ya maida ga Malikat Haseenat. Ta ɗan hararesa da salon kulawa da nuna damuwa. Idanun ya janye a sannu daga kanta itama yana sakin kasaitaccen murmushi.... Harya gama gaisawa da kakar tasa a yanda yake kishingiɗe batare da ya motsa ba Iffah na tsaye ƙyam tamkar an dasata. Malikat Haseenat ta maida kallonta gareta tare da ambatar sunanta. A dake Iffah ta amsa dan tayi alƙawari ma kanta bazata taɓa barin rauninta sake bayyana ga kowa ba a yanzun. Kafinma Malikat ta sake cewa wani abu tai ƙasa a hankali, cikin rashin ƙwarin jiki ta zube ƙasan lallausan carpet ɗin da ko jikin zomo bazai nuna masa laushi ba. Ƙamshi ko ba'a magana dan ko'anan ake shukashi iyaka kenan. “Amincin ALLAH ya tabbata a gareka”. Ta faɗa badan har zuciyarta abinda take son faɗar kenan ba. Sai dai kwarjininsa daya mamaye falon da duk girmansa take jinta a matse yaƙi bata damar fitar jin zafinsa dake a ƙasan zuciyarta a zahiri. Kamar a waccan ranar yau ma bai amsa ba, babu ma alamar yajita tattare da shi. Daga cikin hular alkyabbar jikinta ta cije lips ɗinta da masifar ƙarfi tamkar zata hudasu da haƙori..... “Ai ma Zawjata-almilk rakkiya ɗakin da Tajwar zaiyi barci a yau”. Furucin Malikat Haseenat ga hadiman dake rakuɓe gefe zube a ƙasa kawunansu rissine tun shugowarsu ya nema sarƙe numfashin Iffah da Tajwar Eshaan a lokaci guda. Babu wanda Malikat Haseenat ta kalla a cikinsu sai ɗaya daga cikin Hadiman ce da suke girki ta miƙe da rawar jiki zuwa inda Iffah take. Dole ta mike dan a furucin Malikat Haseenat babu wasa ko ɗaukar turjiya ga kowannensu.... Shiru falon babu wanda ya sake ƙwaƙwƙwaran motsi har hadimar data raka Iffah iyakar ƙofar ɗakin ta dawo Malikat Haseenat ta sallamesu. Da ga shi sai ita suka rage, dan haka ya kafeta da idanunsa. Kai Malikat Haseenat ta ɗauke gefe tamkar bata gansa ba ko fahimtar kallon. “Anan zata zauna, sai ka zaɓi inda kake buƙatar ta kasance har tsahon sati ɗaya, dan zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu masu mata hidima zasu kasance tare da ita. Na damƙa amanarta a hannunka, ina kuma fatan ta kasance ƙarƙashin kariyar UBANGIJI. Fatan alkairi da shiga sabuwar rayuwa, tare da tayaka murnar sabon aure. Na barku cikin amincin ALLAH”. Da alama gushewar numfashi da rikicin wannan tsohuwa ya gama daskarar da jinin Shahan-shan. Dan harta fice a falon ko gashin idonsa bai ƙyafta ba, kai kace wani butun butumine aka dasa a wajen domin tarihi.......
(🤔Tsohuwar nan kuwa na lafiya? Zata kai mana Iffah har ƙuryar Dodon Mayu🥱🤦).
★★... ★★....
Duk da dare ne gaba ɗaya masarautar ta ɗauki ɗumi bisa wannan bahagon hukunci na Malikat Haseenat. Basu da al'amarin yazoma a bazata ba, hatta Malikat Bushirat da Daneen Ammarah da Jasrah da akai zaman da su komai ya musu cak. Abinda suka sani kawai komawar Iffah sashenta, bawai kaita turakar Shahan-shan ba. Miyasa Malikat Haseenat ta canja lissafin a kan kansu suma?. Wannan itace tambayar daketa musu kaikawo su duka.
“Ni kam dai a wannan gaɓar na kasa gane komai wlhy Akia. Shin minene dalilin Mamma nayin haka? Miyasa lissafin ya canja daga yanda muka tsara gaba ɗaya?”. Kamar malikat Bushirat bazata tanka har ta kai ta kawo kusan sau uku kafin ta dubi Jasrah mai maganar. “Kaina ya kulle Jasrah”. Ta faɗa a takaice da kaiwa zaune bakin gadon ta dafe kanta. “Ya ALLAH! Wlhy zuciyata ta fara kai ni ga hasashen wani abu daban?”. Jasrah ta sake faɗa tana dafe nata kan itama.
★
A ɓangaren Daneen Ammarah ma dai a rikicen take. Sai dai ita nata lissafin yasha banban da nasu Malikat Haseenat. Daga ɗakin taro bedroom ɗin Malikat Haseenat ta wuce zaman jiranta. A zaman da bai wuce mintuna arba'in ba kuwa sai gata. Kallo ɗaya taimata ta ɗauke kai. Hadimar dake biye da ita ta ajiye madarar hanunta da zubewa ƙasa tana gaida Daneen Ammarah. Hannu kawai ta ɗaga mata.... “Na matuƙar gajiya, kwanciya kawai nafi buƙata”. Malikat Haseenat ta faɗa tana wulla kekenta hanyar bathroom ɗinta batare data sake kallon Daneen Ammarah ba. Da kallo ta bita cikin shakku da shan jinin jiki. Dan duk da a dunƙule tai magana tana nufin bata bukatarta a ɗakin kenan. Jiki a sanyaye ta miƙe ta fice zuciyarta na faman tsalle-tsalle...
Duk yanda taso kwanciya ta kasa hakan, fargaba da tausayin Iffah ne ke matukar ɗawainiya da ita. Har cikin zuciya bata son rasa yarinyar dan ta matuƙar shiga ranta. Soyayya take mata irin ta ƴa da uwa. Ita kanta har takanyi mamakin yanda takejin Iffah a rai matuƙa, amma tasan wannan ƙaunar daga ALLAH ne kawai. Wayar dake a hannunta ta ƙara rumtsewa, ta gwada kiran Iffah ya kai sau huɗu kenan amma tana fasawa, so take taji lafiyarta ko zata samu ƴar nutsuwa, amma wata zuciya na gargaɗarta da kalmar rashin dacewa....
★★.....
“Mi wannan tsohuwar ke nufi wai shin? Ko itace abin neman mu kamar yanda barbushi ya sanar mana?”. Miran Arshaan yaja numfashi ya fesar, kamar bazaice komai ba sai kuma ya kafe Miran Jasim da kallo yana girgiza kai. “Wlhy kaina ya kwance Jasim Akhi. Na kasa gane komai a wannan gaɓar, abinda na sani kawai shine mutuwar yarinyar nan a wannan gaɓar tamkar mutuwar cikar birinmu ce, dan na gama ɗora dukkan hope ɗinmu a kantane. Bai kamata ta mutu a yanzu ba har sai ta ƙarasa mana aikin da muka kwashi tsahon shekaru muna ginawa”. “Miye mafita?”. Cewar Miran Jasim a firgice, dan zantukan Arshaan ɗin kamar sun zaburar da shi ne abinda ke gabansu. Kai tsaye Miran Arshaan yace, “Ziyartar Barbushi a wannan daren, kafin waccan sankaran matar da ban san amfaninta a tafiyarmu ba tazo ta ishemu da tsarin banza”. “Hakan yayi mun, babu amfanin ɓata lokaci kaje kayi shiri”. Kai Miran Arshaan ya gyaɗa masa, tare da mikewa ya fice. Da banzan kallo Miran Jasim ya bisa, cikin ƙanƙance idanu da wani shu'umin murmushi a fuskarsa “Ba matar can bace kawai abin banza a cikinmu, har da kai Arshaan, daka gama mun amfani zan kawar da kai, dan ni kaɗai nake son mulkar daular ruman batare da ɗan uba ko ɗaya ba da zai zame min abokin gaba, nasan idan har na barka kaima zaka zamemin maƙiyi dan burinka wannan kujerar ne na sani shashasha”...
(🥱Waɗan nan mutane dai to bara nayi shiru dai🤫)
*_ZAWJATA-ALMILK_*
Duk da akwai wani ɗan ɓurɓushin tsoro a ƙasan zuciyar Iffah ta matuƙar dakewa da addu'a ta shiga ɗakin bayan ta gama ƙarema bangon dogon corridor ɗin da suka biyo kallo, ta jinjina kai cikin jin matuƙar ƙuna da tausayin talakawan ƙasan ruman baki ɗaya. Tayi imanin akwai dubbunan mutane dake barci akan titi cikin yinwa da ƙishirwa da yawa. Amma abin mamaki yau ga bangon ɗakin barcin Shahan-shan yasha ado da zinari matsayin fenti, “Taya ma imani zai zauna a zuciyar mutanen nan har su ɗauka rai wani abun mai daraja?” ta faɗa a zahiri idanunta na cika da ƙwallar baƙin ciki da ƙara jin tsanar Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed..........✍️
(😭Hikenan Iffahr mu an shigo ɗakin mutuwa😱🙆).
Ko miye dalilin Malikat Haseenat na kai Iffah turakar Shahan-shan kai tsaye haka? Miye dalilinta na canja abinda suka tattauna da su Malikat Bushirat? Shin ko dai malikat Haseenat ce T....😱🤫🤭?.
Yaya zata kasance tsakanin Iffah da Shahan-shan ne? Ta wani ɓangaren abinda ke kashe Zawjata-almilk kuna ganin zai ƙyale rayuwar Iffah a wannan dare kuwa?.
Gadai wasu ɓoyayyun maƙiya na sake fitowa. Irinsu Miran Arshaan (mijin Jasrah kuma ƙani ga Tajwar Haysam) da Miran Jasim (shima ƙani ga Tajwar Haysam). Shin wacece wai matar nan da suketa a ambata batare da sunanta ba?.
Hhhh tabbas yanzu ne wasan zai fara. Sai ku shirya ku sake shiri dan sai a yanzu ne muka kalmashe bakin shimfiɗar labarin dake cikin littafin DAUƊAR GORA... Wasan na asali yanzu ne filin yinsa ya kammala. Masoya sai mu antaya kawai😉🥱🏇🏇🏇🏇.
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*
*DAUDAR GORA Billyn abdul*
*KI KULANI hafsat xoxo*
*A RUBUCE TAKE Huguma*
*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*
*IDON NERA Mamuh ghee*
_LITTAFI DAYA: 400_ _LITTAFI BIYU: 600_ _LITTAFI UKU: 800_ _LITTAFI HUDU :1000_ _LITTAFI BIYAR: 1200_
_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_
_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
MARYAM SANI ACCESS BANK 0022419171
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
09033181070
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09166221261
*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*
+227 96 09 67 63
Books biyar 1250CFA Books hudu 1050CFA Books uku 850CFA Books biyu 650CFA Bookk daya 450CFA
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽
_𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨ (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)
𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻
*_32_*
........Ni'imtaccen ƙamshin dake tashi a katafaren ɗakin ta zuƙa ta fesar da cigaba da bin komai daki-daki. Ɗaki kam ya cika a kirasa ɗaki ga masu arziƙin dake ɗaukar duniya gidan zama. Sai dai ta gama ayyanawa a ranta babu wani ƙyale-ƙyale da zatai sakacin da zai ruɗeta har ya dakatar mata da ƙudirinta data fara taka tsanin nasararsa a yau insha ALLAH. Ta saki kasaitaccen murmushi da ware hannayenta iskar na'urar ac ta busota tare da ƙamshi, idanunta ta lumshe ta buɗe tare da tsuke fuska. Cikin wani kakkausan sauti daya bambanta da nata na baya ta furta. “Yanzu ne za'a fara wasan na gaskiya. Dodon matsafa MATAN ƘWARAI bisa kanka!!”...
(🥱 Iffahn mu irin wannan alwashi haka🤔 kinfa fara bani tsoro😱🏇).
★★...