Kenza eBookz

Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul - Chapter 17

Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul - Chapter 17

Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul Chapter 17: Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul Chapter 17. Tun wucewar Malikat Haseenat ya bar falon shima.…

4,493 words

Tun wucewar Malikat Haseenat ya bar falon shima. Tsaye yake jikin windown ƙaramin falonsa na hutawa da babu mai shigarsa sai shi ɗaya tak da amintacen hadiminsa mai gyarasa. Dan a doka ma hatta matarsa bata da hurumin shiga wannan falon a tsari da ƙa'idar masarautar. Hasken daya ƙawata cikin masarautar ya bashi damar iya ganin abubuwan dake kusa daga inda yake, sai dai kuma a zahiri idanun nasa ne kawai ke kallon zuciyarsa sam ba'a nan take ba. Ya kwashe tsahon lokaci a wajen kafin ya warware hannayensa dake goye a bayansa ya furzar da numfashi. Ƙofar ɗakin barci ƙwaya ɗaya dake a falon ya nufa. Shima tsaf yake tamkar anan yake zaman din-din-din. A maimakon kwanciya anan ɗin ma zaune yakai cikin kujerar dake ajiye a gefe domin hutawa kawai. Tun agogon ɗakin na juya sakanni da mintuna har ya koma awanni yana zaune idanunsa lumshe, ya kwantar da bayansa a makarin kujerar dake ɗan juyawa a hankali. A kallon fuska baka isa gane yanayinsa ba balle ka samu damar masa fassara. Bugawar agogon ɗakin mai nuni da cikar ƙarfe biyu dai-dai ta sakashi buɗe idanunsa da ƙarancin hasken ɗakin ya hana damar iya tantance launinsu a yanzu. Agogon ya tsurama ido tamkar mai lissafa daƙiƙun da suka cigaba da motsawa.....

A ɓangaren Iffah wannan lokaci na dai-dai da kai goshinta ƙasa domin yima UBANGIJI suduja a karo na babu adadi. Tun bayan kammala lissafe-lissafenta da ƙidaye-ƙidaye ta zanzare rigar jikinta, ƙaramin akwatinta ta buɗe babu alamar damuwa tattare da ita ta sauya kayanta zuwa abaya. Daga haka ta nufi bayi bakinta ƙunshe da tarin addu'oin da taketa yi tun shigowarta ɗakin. A karan farko data buɗe fanfo da nufin yin alwala saɓanin zubar ruwa sai taci karo da jan abu tamkar jini. Tabbas taji firgici, amma sai tai yaƙi da rauninta wajen cigaba da addu'a da son daidaita harbawar da zuciyarta keyi da sauri-sauri. Tamkar almara kalar jan ya ɓace a idanunta ainahin ruwa ya maye gurbinsa. Numfashi taja ta fesar zuciyarta na tabbatar mata ta ƙara dakewa. Tsaf ta ɗaura alwalarta kuwa ta miƙe, tana ƙoƙarin gyara ɗan kwalinta taji tamkar an gitta ta bayanta. Anan ɗinma dai zuciyarta ta tsinke, amma sai ta cigaba da ambaton sunan ALLAH ta basar. Bata damu da nan wanin abin salla ba, dan tsaftar dardumar da aka ƙawata ɗakin da ita ya gamsar da ita. Mayafinta ta naɗa tai nagartacciyar tsayuwar salla domin fuskantar UBANGIJIN talikai mai jin kukan wanda ma basu fara kukan ba, mai bada kariya ga wanda ya yarda babu abin dogaro sama da shi... Taja tsahon lokaci a sujidar tana mai zubda hawaye da ƙaskantar da kai ga mai gani a duk inda ka ɓuya. Bayan ta sallame tai zaman karatun Alkur'ani a cikin wayarta dan batajin zata samu Alkur'ani a wannan ɗakin da ƙyaleƙyalen cikinsa ya tabbatar mata zamowa fadar aljanu ba komai bane. Sai da ta gama karance baƙara har zuwa inda suka tsaya a makaranta sannan tai addu'a mai tsawo itama. Sosai taji wata iriyar nutsuwa na ratsa dukkan jikinta, ta sauke ajiyar zuciya da miƙewa. Hankalinta kwance ta haye katafaren lafiyayyen gadon da Shahan-shan ne kawai ya taɓa hawansa a tarihi. Nanma zama tai tai addu'ar barci ya shafe jikinta ta gyara lausasan filos ɗin da aka ƙawata adon gadon da su ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya. Barci mai daɗi ya fara fisgar idanunta a sannu-sannu sai gata tana sauke numfashi.......

★★...... ★★..... ★★.......

Bayan wucewar saurayin da Kaka ya shimfiɗama sha tara na arziƙi gidan yay shiru. Kamar yanda bai cema Iyyani komai ba itama batace ba, tsahon wasu mintuna sannan ya miƙe ya shiga ɗakinsa. Tashi Iyyani tai ta bisa, dan ta fahimci maganarce baya buƙatar ayi sam.. A ɗakin ma baice mata komai ba har tsahon wani lokaci, ganin haka ta katse shirun da faɗin, “A haɗa maka ruwan wanka?”. Batare da ya bar abinda yake ba ya jinjina mata kai. Fita tai jiki a sanyaye, babu jimawa ta koma ta sanar masa an haɗa. “ALLAH yay miki albarka”. Ya faɗa kamar yanda ya saba. Ta ɗan ji sanyi a ranta, dan haka ta amsa da “Amin tare da kai” cikin sauke ajiyar zuciya....

“Ai bakaci wani abincin kirki ba”. Iyyani ta faɗa idonta akan kwanikan gaban Kaka da ya gama cin abincin data kawo masa bayan fitowarsa wanka. Kai ya jinjina mata da sakin murmushi a karan farko tun bayan shigowarsa gidan. “Alhamdulillahi wanda naci ya wadatar dani”. Kai kawai ta jinjina masa jikinta na ƙara sanyaya. Duk wanda zai sam mijinta a bayanta yake, ta san murmushin sa ba yana nufin farin ciki bane na tsantsar damuwa ce..... “Yaya jikinta?”. Ya katse tunaninta da abinda taketa zumuɗin san ji a bakinsa. “Alhamdulillahi da sauƙi”. “ALLAH ya ƙara afuwa. Bara na ganta”.

Ummu na zaune shiru ta tsurama waje ɗaya idanu suka shiga. Har suka kai zaune gefenta babu alamar tana san da zuwan nasu. Kaka ya kafa mata idanu na wasu sakanni sai kuma ya kauda kai. Taɓata Iyyani tayi, ta kawo nannauyan numfashi da ɗan zabura na ganinsu a ɗakin dan da gaske bata san da shigowar tasu ba. Kaka ta kalla idanunta na cikowa da ƙwalla, sai kuma ta duƙar da kai ta fara gaishesa. A hankali ya nisa kafin ya amsa a taƙaice kamar yanda tai gaisuwar. “Jumaimah!”. Ya kira ainahin sunanta. “Na'am Baba”. Ta amsa akan laɓɓanta. “Damuwa ko ƙuntata kai bata sauya ƙaddarar bawa. Juriya da tsantsar jarumta baya hana ƙaddarar zuwa. Haƙilo ko nuna ƙarfin iko baya ture ta a lokacin da aka so. Rauni ko rashin tawwakali bazai dawo maka da abinda dama can ba naka bane ba. Haƙuri shike samar da komai koda kuwa a zahiri yafi ƙarfin ƙarfinka”. “Hakane Baba”. Ta faɗa cikin rawar murya. Murmushi ya saki da matsawa kusa da ita sosai. Ɗa a gaban iyayensa baya girma koda ace yayi furfura a saman kai. Kaka ya riƙo hanun Ummu cikin nasa, ɗayan kuma ya shafa kanta. “ALLAH yayi miki albarka. Yasa ƙaddarar su ta zama kaffara a garemu baki ɗaya.” “Baba mun rasa su suma ko?”. Ummu dake dubansa idanu cike da ƙwalla ta faɗa. Murmushin ya sake sakar mata. Sai kuma ya girgiza kansa da kwanto da kanta bisa kafaɗarsa. “Bamu rasa su ba, ba kuma mu fidda rai da samunsu ba”. A hankali hawayen da suka kasa fita a idonta tsahon kwanaki suka fara sauka a kafaɗarsa.......

★★.... ★★.... ★★.....

Mummunan mafarkin da ALLAH ya bata ikon cin galaba a cikinsa ta farka a zabure, cikin amincin UBANGIJI harshenta ya ambato addu'ar tashi daga barci kamar yanda musulinci ya ɗoramu akai. Ajiyar zuciya ta sauke da saka gefen bargon data lulluɓa ta yarce gumin da yay ma goshinta jalab, sai kuma ta sake lumshe idanu jin sautin kiran salla da take ƙyautata zaton a masallacin cikin masarautar ne. Hasken ɗakin ta kai hannu ta ƙara, ta bi ko'ina na cikinsa da kallo tamkar zataga munanan halittun data gani a cikinsa a mafarki. Rashin ganin komai a zahiri ya bata ƙarin gwiwar sakkowa a gadon ta nufi toilet. Bata damu da rashin ganin Tajwar Eshaan a ɗakin ba duk da taji Malikat Haseenat ta ambata nan ɗin matsayin ɗakin barcinsa na daren jiya. Ƙarancin shekarunta da wautarta yasa bata ɗauki tsallakewar komai ba. Abinda kawai zuciyarta ke mata kaikawo a rai shine ta tsallake daren na jiya dai koma yaya ne, ta tsallake tarihin mutuwa a daren kwana turakar dodon matsafa. Dalilin tsallakewar, ko barinta da yay da ranta ne bata sani ba, ba kuma tasan tayaya ya kamata ta sani ba. Abinda kawai take da damar yi shine buɗe kunne da idanuwa taga mizai biyo baya ga kowa da kowa. A yanzu ɗin ma tayi zaton ganin jinin kamar jiya dai, sai dai babu alamar hakan har ta kammala uzirinta tayo alwala ta fito. Tana idar da salla wani irin nannauyan barci ya dinga fisgar idanunta. Dakewa tai cikin dauriya tai zaman yin azkar, da ƙyar ta iya kammalawa barci yay mata baban fisga a wajen dole takai kwance tana ambaton sunan ALLAH. A hankali ta fara sauke numfashi alamar barcin nata mai nauyi ne....

★★.... ★★.....

A cikin masarauta tako ina an gama baza kunnuwan jin fito da gawar Zawjata-almilk. Hatta da Malikat Haseena bata tare da nutsuwarta gaba ɗaya. Tun ana ƙirga sakanni a bayan sallar asubahi har aka koma mintuna, mintuna suka koma awanni babu wani labari. A take aka koma ƴar ƙus-ƙus tun daga kan hadimai har manyan masu faɗa ajin masarautar. Yayinda suma Hadiman sashen Shahan-shan suke zaune jigum-jigum na jiran tsumayen abinda kowa keda tabbacin zai kasance. bakunansu cike yake taf da abubuwan faɗa akan abinda suka wayi gari da shi mai matuƙar rikitarwa da zai maimaita faruwa bayan ya faru ga duk wata Zawjata-almilk data kwana ta tashi a wannan sashen. Duk ɗunbin yawan abin cewar iyakarsa zukatansu dan ko'a tsakaninsu bai faɗuwa balle gulmantawa a waje saboda tako ina camara ce zagaye da su.....

*_★MALIKAT BUSHIRAT★_*

Ba'a safiyar yau ba, ita tun ma a daren jiya tai hanun riga da nutsuwa. Gaba ɗaya a daren ko sau ɗaya bata iya ta rintsa ba. A maimakon barci ma idanunta akan sashen Shahan-shan da kowa ke iya gani daga nasa sashen a cikin masarautar suka kwashe mafi yawan awannin daren na jiya. Tayi yunƙurin kiransa amma wayar a kashe, hakanne ya sake ɗaga mata hankali da jin zafin wannan hukunci na Malikat Haseenat a karo na farko. A ganinta ganganci ne miƙa nagartacciyar yariya irin Iffah hannun gudan jinin nata bayan Mamma tasan minene makomar yin hakan ga rayuwar yarinyar. Duk jarumtarta a duk sanda ta tuna zuwa safiya gawar yarinyar ce zata fito takanji ƙwalla sun cika idonta. Amma takan danne ta hanasu fitowa har garin ALLAH ya kammala wayewa... Tun idar da sallar asubahi bata iya ta motsa ba, ƙirjinta ne ke matuƙar bugawa da jiran tsammanin mummunan labari.....

*_★DANEEN AMMARAH★_*

A ɓangaren Daneen Ammarah itama a kwatankwacin irin halin da Malikat Bushirat ta kwana ta tashi take ciki. Dan ita kwana tayi ma tana hawaye. Har ƙarƙashin zuciya takejin matsanancin ƙaunar Iffah. Tana jin yarinyar a matsayin cikon wani gurbi data rasa irin na kowace uwa mai shekarunta. Sai gashi Mamma da ta fara bata tsoro a daren jiya ta rusashi da maye gurbinsa da fargaba mai matuƙar tsanani da razani. Wani mutum saɓanin jininta bai taɓa mamaye zuciyarta da ƙauna mai ƙarfin haka ba kamar yanda yarinyar tayi mata. Sosai take jinta a rai da jinin jikinta. Itama dai tun daga sallar asuba bata sake iya kataɓus ba tai zaman jiran tsammani irin na duk wanda ya kwana ya tashi a cikin masarautar.......

★★... ★★.... ★★....

Harya gota ɗakin cikin shiga ta blue ɗin jallabiya mai tsananin ƙyau da ƙyalli mai ɗaukar ido da nuna taushinta a zahiri dake nuna daga masallaci yake ya tsaya cak. Kamar bazai motsa ba sai kuma ya juya kansa a sannu yana kallon ɗakin. Kallon kusan minti ɗaya da wasu sakanni ya motsa gaɓɓansa cikin takunsa na izza da kame kai ya tura kai ciki. Da farko rashin lura da ita ya sakashi yin tsamm, sai dai fuskarsa ta nuna dakewa kamar koyaushe. Ya ɗaga ƙafa da niyyar juyawa ya fita idanunsa suka sauka a kanta. Yay tsai yana kallonta na tsahon mintuna kusan huɗu tamkar mai rarrabe ita ɗin ce ko wata? Dan a kallo ɗaya zaka fahimci salla ta idar a wajen barci yay awon gaba da ita. Ya ɗan furzar da numfashi da kauda kansa gefe ya sake bin ɗakin da kallo kai kace baƙonsa ne har ya sake direwa akan fuskar Iffah dake ta barcinta numfashinta na fita a hankali.........✍️

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_ _LITTAFI BIYU: 600_ _LITTAFI UKU: 800_ _LITTAFI HUDU :1000_ _LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI ACCESS BANK 0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 96 09 67 63

Books biyar 1250CFA Books hudu 1050CFA Books uku 850CFA Books biyu 650CFA Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨ (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)

𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻

*_33_*

.........Ƙarfe takwas da rabi dai-dai agogon ƙasar ɗaya daga cikin amintattun Hadiman dake gyara ɗakunan barcin na Tajwar ta iso cikin faɗuwar gaba hanunta ɗauke da akwati da aka kawo yanzun nan daga sashen Malikat Haseenat matsayin kayan da Iffah zatai amfani da shi. Zuciyarta har wani zallo take na fargabar abinda take da tabbacin tozali da shi kamar yanda sukayi a baya ga sauran Zawjata-almilk da suka shuɗe. Ta tura ƙofar cikin sanɗa tana mai ambaton sallama da rawar harshe badan tana tunanin samun amsa ba. Ganin Iffah kwance a saman gado, lulluɓe da lallausan bargo baisa taji ƙwarin gwiwa ba. Tai yunƙurin ajiye akwatin hanunta, cak ta tsaya dukkanin idanunta na fitowa waje dan firgici ko sumar tsaye sakamakon juyi da Iffah tai alamar gyara kwanciya. Akwatin ta saki ƙasa ta shiga jan jikinta dake ɓari baya-baya harta dangane da ƙofa gab..... Iffah dake ƙoƙarin gyara bargo idanunta rufe ta buɗesu da sauri saboda jin ƙarar bigewar hadimar. Da mamakin jinta kamar a gado ya sata shashshafa hannunta. (Tabbas gadonne) ta ayyana a zuciyarta tana sake buɗe idanunta da ƙyau tana mai yunƙurin tashi zaune. Tuni hadimar nan ta sake firgicewa, da lalube ta murɗa handle ɗin ƙofar ta fita a guje. Kallon ƙofar Iffah tayi, sai dai hadimar ta gama ficewa bayanta kawai ta ɗan gani kaɗan da wulgawar mayafinta. da sauri ta yaye bargon da bata san ya akai yazo jikinta ba. Ta dire ƙasa mamakin duniya na cigaba da dabaibaye ta. “Wacece wadda ta fita? Mi tazo yi? Wai ta yaya ma na dawo saman gadon nan bayan a ƙasa na kwanta?”. Ta shiga jerama kanta tambayoyin da bata san inda zata samu amsarsu ba. Sai kuma ta ɗan kamo rigar jikinta ta kai hancinta. “Ya ALLAH, da gaske fa wannan mayataccen ƙamshin a jikina ne?”. Ta sake faɗa a fili tana sake shinshinar rigar......

A ɓangaren jama'ar masarauta dake a zaman jigum-jigum kam fitar hadimar nan ya isar da saƙon Zawjata-almilk na raye. Da farko duk wanda zancen yaje kunensa ɗaukewar numfashi na wucin gadi ne ke riskarsa, sai kuma rashin gaskatawa a zahiri ya biyo baya. Hatta da Malikat Bushirat da Daneen Ammarah yanayi da ruɗanin jin hakan bai tsallakesu ba suma. A kusan tare suka ɗauka wayoyinsu domin neman Iffah ko zasu samu jin gaskiyar zance. Cikin Sa'a kuwa ta Daneen Ammarah ta fara shiga....

Iffah na zaune har yanzu cikin ɗaurewar kai akan wanda ya maidata saman gado da wulƙawar fitar wadda bata sani ba wayarta ta katseta. Numfashi taja ta fesar da ɗan ƙarfi tana kai hannu akan wayar. *_Mamy_* ta gani rubuce ɓaro-ɓaro. Ganin zata katse tai ƙarfin halin ɗagawa ta kai kunne tana faɗin, “Assalamu alaikum. Amincin UBANGIJI da rahamar sa su yalwatu a gareki Mamy barka da safiya”. A matuƙar razani da motsuwar zuciya Daneen Ammarah taja numfashin dake neman ƙwace mata. “Ibnati!”. Ta ambata cikin son tabbatarwa. “Na'am Mamy”. Iffah ta amsa kanta tsaye babu alamar irin fargabar dake harshen Daneen Ammarah ɗin a tattare da ita. Dan ita wanda ya ɗauketa daga ƙasa ya maida saman gado da fitar macen data ganine kawai damuwarta a yanzu. Daneen Ammarah da taji al'amarin tamkar a mafarki ta lumshe ido hawaye na silalo mata saman ƙyakykywar fuskarta a hankali. Ƙasa takai durƙushe tana mai godema UBANGIJI ta hayar kai goshinta ƙasa tai sujjadar shukur...

Iffah da mamaki ta cigaba da ambaton “Hallo Mamy! Mamy kina jina kuwa?”. Shiru babu alamar za'a amsa. Yanke wayar tai da yunƙurin sake kira a zatonta matsalar network ce sai ga kiran Malikat Bushirat ya shigo shima. Ɗan jimm tai tana kallon wayar, sai kuma ta ɗaga takai kunne da sallama nan ma. Malikat Bushirat da idanunta ke cikowa da ƙwalla sakamakon jin muryar Iffah tar-tar a kunenta ta kai zaune tana ambaton sunan ALLAH. Iffah na son tambaya tana jin nauyi, sai kawai tai shiru tana sauraren kalmomin godiya ga ALLAH da Malikat Bushirat ɗin ke ambata daga can. (Ya rabbi! Wai mike faruwa ne haka?) Ta ayyana a zuciyarta da al'ajabi. Knocking ƙofa da akai ta hanyar danna alerm a dai-dai lokacin ya katse tunanin nata. Ta kai dubanta ga kofar babu alamar zata tanka har aka sake danna alerm ɗin sannan tai ƙarfin halin amsawa da bada umarnin shigowa tana gyara mayafin data yanama kanta.. Hadimar ɗazun ce dai ta shigo ɗauke da ƙaramin tray mai ɗauke da butar shayi. Kanta a ƙasa ta ajiye a inda ya dace tana mai zubewa ƙasa durkushe. “Amincin ALLAH da tsahon rai mai albarka su kasance tare da Zawjata-almilk Barka da safiya”. Iffah da ke kallonta ta amsa cikin motsa lips ɗinta kaɗan. Sabo da hakan yasa hadimar bata damu da rashin amsawar Iffah ba. Cikin sake rissinar da kai tace, “Ya Zawjata-almilk yanzu lokacin wankanki ne, bayan nan karin kummalo na jiranki tare da Shugabana”. Yanzu ɗin ma kamar Iffah bazata amsa ba sai kuma ta jinjina kanta. “Kije abinki zan fito”. “Umarninki shine abin jirana. Amma a gafarceni zan haɗa ruwan”. “Kije abinki zan yi komai da kaina”. Babu yanda hafimar ta iya dole ta miƙe domin bin umarni shine kawai huruminsu. Da kallo iffah ta bita abubuwa masu yawan gaske na son fara mata kutse a ƙwaƙwalwa da zuciya. Ƙwarin gwiwar da take bama kanta akan turesu ya sata miƙewa ta nufin toilet tana mai ambaton addu'ai a bakinta saboda tuna abinda taci karo da shi a daren jiya a toilet ɗin. Ko'ina tsaf, kuma cikin ƙamshi irin na daren jiya. Sai da ta ƙarema komai kallo fiye da jiya kafin ta ɗage kafaɗa irin na koma miye ta shirya masa. Tsabagen rigima da wuce wuri ko tsageranci za'ace ta haɗa ruwanta mai ɗumi da zuba duk wani nau'in turaren wanka da aka jera domin Shahan-shan ta shige cikin kwamin wankan tai luf. Sai da taji ko'ina nata ya miƙe yanda take buƙata sannan ta fita a ruwan domin fara wanka...

Tsaf ta kammala shirinta cikin doguwar rigar material sky blue da akaima ɗinkin daya fidda ainahin halittarta tamkar ƴar tsanar roba. Rigar ta zauna mata ɗas, siririn mayafin da aka haɗa rigar da shi ta naɗa tamkar yanda larabawa keyi, ta ɗakko after dress shara-shara mai kamar alƙyabba ta ɗora a sama kalar blue sosai. Ta ɗanji babu daɗi na rashin turarurrukanta tare da ita, dan ko waɗan nan kayan ganinsu kawai tai, cikin ɗan taɓe baki da ɗage kafaɗa a zahiri ta dinga kwasar turarrukan da taci karo da su a ɗakin cikin wani ƙyaƙykyawan glass dake kusa da mirror ta dinga zazzagama jikinta har sai da ta gamsu ƙarfin kamshin zai kai duk inda mai rai ke numfashi a sashen sannan ta haƙura. Idanunta ƙyam a mirrorn ta saki ƙayataccen murmushi da kanne ido ɗaya a fili ta furta “Irin wannan haɗuwa haka autar Ummu”. Tai salute ɗin kanta....

Sautin ƙarar takun takalman ƙafarta da mayataccen ƙamshin tiraren da shi kaɗai aka sani da shi ya sashi tsayawa cak daga ƙoƙarin kai hannu a abincin da aka gama haɗawa gabansa. Fararen idanunsa tar-tar tamkar madara ya ɗago ya sauke a kanta. Hakama hadiman dake a tsaye ta gefe da gefensa kawunansu a ƙasa cikin yanayin mutuwar tsaye data rikesu suka zube ƙasa kan gwiyawunsu illahirin jikkunansu na ƙyarma akan dalilai guda biyu. Na farko ganin tabbatar da wadda suka gama fidda rai da jiran tsammanin ganin an shigo fidda gawarta tamkar Zawjata-almilk na baya dai na raye ɗin kamar yanda Hadimar ta gano. Na biyu ƙamshin turaren jikinta da ga mutum ɗaya tak ake iya jinsa a duk faɗin ƙasar ruman ma bawai a daular ruman ba... Tamkar Iffah bata fahimci halin da suke a ciki ba ta ƙaraso cikin katafaren falon batare data dubi ko ɗaya a cikinsu ba balle mai gayya mai aikin. Cikin sauri ɗaya daga cikin hadiman ya miƙe ya gyara mata kujera, zaune ta kai tana mai dubansa a karo na farko. Tuni shi kuma ya maida kansa ga abinda yake yi tamkar bai san da zuwan tan ba. Ta taɓe baki da juya idanunta ta maida ga hadimar dake ƙoƙarin fara haɗa mata abincin. Nunin abinda take buƙata tai mata da ɗan yatsa. Hadimar na kammalawa ta koma cikin ƴan uwanta ta tsaya itama kanta a rirrine. Gaba ɗaya jinta take a takure, kwarjininsa ya cika ko'ina a falon. Cikin dakewa da kaucewa gizago sa ta ɗan ɗago ta ɗan saci kallonsa da nufin gaishesa idanunta suka shige cikin nasa da ya ɗago da nufin kallon nata... “Who are you?” Ya fara faɗa cikin basarwa yana kaɗa idanusa da har yanzu ke cikin nata tamkar bashi yay maganar ba. Badan a idanunta tausasan lips ɗinsa suka motsa wajen ambaton wacece itan ba zata iya gaddamar hakan. Kaifin idanunsa sun neman sage duk wani ƙwarin gwiwarta. Ƙoƙarin fara sassauta nata idanun tai yunƙurin yi cikin ƙanƙance su sannu a hankali. Shima sai ya kankance nasa kamar yanda takeyi, fuskarsa na sake tsukewa babu alamar sassauci tattare da ita. Nata ta fisga da ƙarfi ta lumshe su, sai kuma ta buɗe a kansa tana mai sake tsuke tata fuskar itama, bazata iya jure salon nasa ba dake neman ƙone ƙudirinta, dan haka ta kauda kanta gefe babu alamar zata bashi amsar da yay yunƙurin ji daga garetan.. “Barka da safiya”. Ta faɗa a ƙoƙarinta na basar da tambayarsa ta farko. Bai motsa ba, babu alamar kuma zai amsa ta. Hakan sai ya sake sukar zuciyarta harta ɗan saci kallonsa, da sauri ta kauda idanunta, dan da gaske fuskarsa ruguza mata lissafi take, da gasken gaske shi ƙyaƙyƙyawa ne, irin ƙyawun dako a cikin ƙasar tasu ake yabawa da shi, koda yake batai mamakin hakan ba, dan Malikat Bushirat ba'a magana, duk da girma ya fara zuwa gareta tsantsar ƙyawunta a bayyane yake. Hakama Malikat Haseena dake matsayin kakarsa data haifi babansa tunda ita dai bataga baban nasaba ko'a hoto har yanzun, amma zubin Malikat Haseena dana Daneen Ammarah ya tabbatar mata shima ɗin dai zai kasance ƙyaƙyƙywan ne...... “What is your goal in life?”. Kalmomi guda shida suka katse mata tunani a bazata. Ta kallesa tana ƙoƙarin danne mamakinta kan waɗan nan tambayoyi da yake faman yanko mata kai tsaye. Ganin yanda ya zuba mata ƙasaitattun idanunsa masu firgita mara gaskiya ta janye nata tana yamutse fuska. (Damarki ce wannan) wata zuciya ta ayyana mata. Cike da gamsuwa ta sake kauda kai gefe dan har yanzu tanajin kaifin idanunsa a kanta. “Ni ban kasance kowa ba sai talakar dake a ƙarƙashin mulkinka ranka ya daɗe. Abinda nake son cimmawa kuwa a rayuwata irin abinda shugaba ke fatan cimmawa ga talakawan ƙasarsa ta hanyar mulkarsu da fuska biyu ne”. Yanda tai maganar kanta tsaye babu ko ɗar ya sashi jin mamakinta. (Tabbas wannan abar ba mutum bace) zuciyarsa ta tabbatar masa. A zahiri sai ya ɗauke kansa cike da basarwa. Shiru babu alamar zai sake tankawa har Iffah tama fidda rai ta cigaba da tsakurar abincinta kamar yanda yakeyi shima. “Wasa da rayuwarki kuskurene ga ƙarfin halinki, ƙin kasancewar ki tarihi a wannan safiyar bashi ke tabbatar miki nasarar tsallakewa ba”. A yanzun kam zantukansa sun zama masu matuƙar tasiri a fitarsu da saurarensu gareta, jin bazata iya dannewa ba ta amsa batare data ɗago ta kallesa ba, “Hakane shugabana, sai dai fa _Fate is some thing undeniable”_ Ya basar babu alamar yanzu ma zai amsa, shayin sa ya kai baki cike da ƙasaita. Itama sai bata sake cewa komai ba ta cigaba da cin abincin tana mai kallonsa ta gefen ido, sannu-sannu tabi sautin motsa plate ɗin gabansa da kallo har kan lallausan farar fatan hanunsa masu ɗauke da tsaftatattun fararen dogayen farce, baya tai ƙoƙarin jan jikinta batare data yarda idanunta sun wuce kallon hanun nasa ba. Yanda ya basar da ita ɗin kuma sai yay matuƙar sukar zuciyarta, dan bata buƙatar tattaunawar tasu ta tsaya iya haka. Amma sai bata yarda fuskarta ta nunaba. Sai ma mamakin ƙasaita da tsantsar izzar wannan bawa da zuciyarta ke faman yi. A wani ɓangaren ita kanta dakewa kawai take, amma kwarjininsa da gizago na firgita ta matuƙa. Tana ƙara tsarkake sunan ALLAH akan yarda da jinin mulki gaskiya ne. Duk da ta shigo daular ruman da wani ƙudiri a ranta hakan bazai hanata girmamashi ba, koda ace tayima yunƙurin hakan kwarjinsa bazai bata damar yin saɓanin girmamawar da kowa ke masan ba. So take taji tsanarsa a ranta kamar yanda takeji kafin ganin wannan fuskar matsayin shi amma zuciyarta taƙi bata haɗin kai. Numfashi taja a hankali ta fesar a ƙasan maƙoshinta. “Kokawa da ƙaddara a fuskar iyawa na nufin faɗuwa! Kinga ko what you get is, what you have?”. Ya faɗa cikin katse mata tunani dai-dai yana ɗagowa.......✍️

“Fareedatu kibar danginmu su tsinkayi yini da kwana cikin sallama, Banda taro dutsen zuma inake ina kace nace da dodon may...🥱🏇”.

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_ _LITTAFI BIYU: 600_ _LITTAFI UKU: 800_ _LITTAFI HUDU :1000_ _LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI ACCESS BANK 0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 96 09 67 63

Books biyar 1250CFA Books hudu 1050CFA Books uku 850CFA Books biyu 650CFA Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

Readers Also Read