Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul - Chapter 18
Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul Chapter 18: Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul Chapter 18. MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
4,496 words
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨ (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)
𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻
*_34_*
........(Mi wannan mutumin ke ƙullawa?). Ta faɗa a zuciya batare data motsa ba. (Keda ke neman kusanci da shi dama miye matsalarki da koma mi yake nufi) wata zuciyarta ta sake ayyana mata. tamkar wadda aka zaburar sunan Arfa da Fariha ya fara amsa kuwwa a zuciyarta har tana jinsa yana tashi bisa sararin samaniya. Kaifafan idanunsa masu nuna tsaurinsa ya zuba mata ganin ta basar da shi itama. Kusan mintuna uku babu alamar zata tankama zancen nasa har ya fara jin haushi. Ta taɓe baki da kauda kanta gefe, cike da dakewa ta furta, “Da gizago na tsorata ƙwarin gwiwata da bazan amincewa shigowa ramin zakin da ɗanyen nama shine abincinsa ba. Karka damu a kaina ranka ya daɗe, dan a wannan gaɓar *_cuta ce ta ɗakko cuta, ɓarawo ya ɗakko akwatin maciji”._* Fuska ya ɗan motsa kamar zaiyi murmushi, sai kuma ya basar. “Bana haɗa ƙwanji da mage duk da kamaninta na yanayi da nawa matsayina na ZAKI har a hallaya. Ki kama kanki dan kina buƙatar rayuwa mai tsaho wajen moran ƙuruciyarki”. Ya faɗa da muryarsa mai zurfi da ƙasaita yana miƙewa ya zagayeta ya wuce abinsa. Shiru bata motsa ba har ta gama jin ɓacewar sautin takunsa a wajen, ta ɗan cije bakinta “Zaki zako ka magantu fiye da haka”. Ta faɗa a fili cike da kwaikwayo salon maganarsa tana sakin wani lallausan murmushi da kai kofin shayi a bakinta, duk da zafinsa ta rumtse ido ta kwankwaɗe abinta sannan ta juya taima hadiman dake tsaye har yanzu kallo ɗaya ta ɗauke kanta batare da damuwar komai ba, dan tasan basuji komai ɗin ba da suka tattauna. A yanda suke maganar ma wani sai ya ɗauka wani zancen soyayya ne ya haɗasu. Komai batacema kowa ba itama ta miƙe tabar wajen, duk suka bita da kallon ƙasan ido kowa da abinda yake ayyanawa a zuciyarsa. A tafiyar tata tana ɗan kalle-kalle taci karo da camara, komai bataji a ranta ba, dan tayi tsammanin hakan tun farko, saboda babu yanda za'ai sashen mutum mai ƙarfin iko kamar Tajwar ace babu wani tsaro makamancin hakan koma fiye da hakan. Da ƙyar ta iya gane ɗakin data kwana. Tana shiga ta zube a kujera da sauke nauyayan numfashi, ɗakin da akaima gyara ɗan gaske tabi da idanu, sai taga ma kamar ba'a cikinsa ta kwana ba, ganin akwatin kayanta kawai ya tabbatar mata da shi ɗin ne. Tunani mai ƙarfin gaske ta faɗa kusan kashi uku zuwa huɗu musamman akan kawota da Malikat Haseena tayi, mi tsohuwar ke nufi da haka bayan su suka sanar mata an rasa matan baya ne a dalilin kawosu turakar Shahan-shan ɗin. Sai kuma akan Tajwar Eshaan ɗin, na farko waccan fuskar data gani a waje kafin shigowarta masarautar matsayin matarsa. Na biyu wannan fuskar ta yanzu da bata da banbanci da waccan ɗin, na uku hanyar da ya kamata ta cigaba da bi domin sanin ainahin wanene Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed a baɗini da zahirin rayuwa. Domin da gasken gaske tana a cikin ruɗani akan fuskokin nan biyu data gani a mabanbanta muhallai. Su ƴan biyu ne? Kokuwa shi ɗinne ke ɓadda kama yana fita?. Abu na uku kuma abinda ya faru a daren jiya da sai a yanzu yake bata matuƙar mamaki, tun a jiyan bawai ta ajiyesa a gefe bane dan bashi da muhimmanci ga haɗarin da tasan ta kawo kanta ciki, kawai dai bata san dalilin da yasa bataji ko ɗar ba a zuciyarta na tsoro, kuma har yanzu batajin tsoron sam, dama kuma tun asali bata da tsoron. Dan Iffah irin mutanen nan ne masu ƙesashiyar zuciya mai iya tunkarar komai koda yanada haɗari a garesu, tanada naci da zama kaifi ɗaya akan zimma da cimma buri duk da ƙarancin shekarunta. Na ƙarshe tattaunawarsu ta yanzu da shi da girman kalaman da yay amfani wajen jifanta da su. Ta ɗan murmusa da cije lips ɗinta tana mai lumshe idanu a hankali......
★★.... ★★.....
Zuwa yanzu tako ina maganar tsallakewar Iffah ce ke kaikawo a cikin masarautar. Kowa ya nutsu wajen tattauna abinda ke bakinsa da abokin maganarsa. Wasu jin daɗine game da hakan, wasu ko baƙin cikine a ransu, dan mutuwar Zawjata-almilk ɗin kamar wani makamine a hannayensu na dukan nasarar Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed ɗin. Tsallakewar Iffah kuma zai kasance kamar damar ƙalubalantarsa da suka riƙe ya kuɓuce musu kenan. Ita kuma yarinyar kimarta da nunawa duniya tafi ƙarfin masu ƙarfin zai yi tasiri a zukatan jama'a.....
★Komai dake faruwa yana isa da shiga a kunnen manyan masu faɗa aji ta bangaren iko da kusanci da Tajwar Eshaan ɗin. Wato Malikat Haseenat da Malikat Bushirat. Sai dai sunyi biris babu alamar zasu tofa nasu akan hakan bayan bayyanar farin cikinsu akan fuskokinsu daya gaza boyuwa ga kowa. Dan a dalilin wannan al'amari Malikat Bushirat har ƴafiya tayi ga wasu firsinoni dake a cikin kurkukun masarautar akan wasu laifuka nasu da basu kai sun kawo ba. A cikin sunne kuma aka sallami harda Diwa a dalilin bincike daya tabbatar da bata da hannu game da abinda ya faru ga Iffah a waccan ranar.
★A ɓangaren Malikat Haseenat kuwa maimakon bama abinda ke zuwama kunenta muhimmanci hankalinta ta maida wajen tantance hadiman da zasu koma aiki a karkashin Iffah ne bisa taimakon Daneen Ammarah da farin cikinta itama yake a bayyane. Dan itama dai har kyaututtuka na musamman yau ta bada ga hadimai tare da sakawa a tattaro mata dukkan malaman masarautar zuwa sashen Iffah da bukatar suyi saukar Alkur'ani mai girma. Ta kuma miƙe da karfin jikinta wajen shirya lunch na musamman ga Tajwar Eshaan da amarya Iffah Zawjata-almilk...
*_★BARRISTER★_*
Abubuwan da suka faru sun sakashi dakatawa a zahirance bisa shawarar Kaka. Sai dai yana cigaba da gudanar da wani binciken sirri dan yayma kansa alƙawarin binciko duk mai hannu akan wannan al'amarin nasu Babiy da ma inda aka ɓoye su. Kamar yau ma tun jijjifin safiya ya fito daga gida. Kai tsaye hanyar jihar Hubab ya nufa inda bincikensa ya tabbatar masa nanne ainahin jihar da matar Abu Moosa ta fito. Jihar Hubab makwafciyar Dahab city ce (Daular ruman kenan) dan haka a cikin ƙanƙanin lokaci ya isa. Bai tsaya sanyaba ya ɗauka hanyar ainahin kauyensu kuma. Kasancewar anan ma hanyace shimfidaɗɗiya a kanƙanin lokaci ya isa. Da farko ya sha wahalar binciken inda gidansu yake, sai da yay dabarar nuna hotonta sannan.
Kusan mintuna goma bayan isar da saƙon tanada baƙo gareta ta fito cikin irin shigarsu. Tayi ɗan tsamm alamar shan jinin jikinta kafin ta ƙaraso a yanayin son basarwa. Barrister shi ya fara gaidata, tare da sanar mata sunansa. Lokaci ɗaya ruɗani ya bayyana akan fuskarta ta shiga waige-waige irin na rashin gaskiya da ƙoƙarin ja baya daga garesa... “Bawan ALLAH ina baka shawara ka taimaki kanka ka bar ƙauyen nan, babu wani abu da zaka iya ji a gareni dan ban san komai ba”. A fusace Barrister yay tsalle gabanta yana huci. “Baki san komai ba amma akaje da ke har gida aka kamasu. Karki sha mamakin bayan sanin inda kike har wasu abubuwa na sani a kanki Mss Farishta. Rashin bani haɗin kai kuma na nufin na tonasu kowa yasan ke ɗin wacece har ma da dalilin auren Dawood, sani kankine wannan babban koma baya ne a gareki kuma harma da zuri'arki”. Yayu ta haɗiya masu kauri tana kallon Barrister, sai kuma ta sake wawwaigawa tabbacin dai akwai abinda take shakka. “Naji Barrister zan baka dukkan bayanan da kake buƙata, amma ina roƙonka kabar wajen nan, idan ma zai yuwu kauyen nan gaba ɗaya nake son ka bari. Wlhy na maka alkawarin zan zo na sameka na kuma faɗa maka komai da kake buƙata harma wanda baka sani ba”. “Miyasa bazan sani ba a yanzu?”. “Saboda zamanka anan yana da matuƙar haɗari”. “Taya zan tabbatar da zaki zo ɗin?”. “Na baka dama kabi duk hanyar da zata bibiyi al'amarina”. Kafaɗarsa ya ɗan ɗage sama da faɗin, “Okay inaga bana bukatar hakan, kije kawai ni na san ta hanyar daya dace na bibiyekin. Amma yaushe ne zamu haɗun?”. “Inasha ALLAH a daren yau ka sameni a ƙauyen Jumna”. “Garin su Abu Hanash da Dawood kenan?”. “Insha ALLAH”.
Tafiya yake zuciyarsa na faman masa kaikawo akan haɗuwar tasa da Farishta (matar Abu Moosa datazo har gida da ƴan sanda aka kama su Babiy. ALLAH yasa kun gane🥱). Duk da yasan zata iya ƙin aikata abinda ta faɗa na haɗuwar tasu a garin Jimna ya zaɓi barinta su haɗun can bisa lumana. A cikin Hubab ya tsaya yaci abinci tare da sallar azhar. Ya fito masallaci idanunsa suka sake sauka akan wata mota da tun fitowarsa ƙauyen su Farishta ya lura da ita tana biye da shi, sai dai duk da ya ganta suna tafiya kafaɗa da kafaɗa bai kawo komai a zuciyarsa ba. Janyewa yay cike da rashin bama abin muhimmanci ya shige motarsa da zummar zai cigaba da tafiya kawai yaga an zagaye motarsa da bindigu.......
★★★.... ★★.... ★...
A firgice ta farka a ɗan barcin daya figeta bayan ta idar da sallar azhar. Ta dafe kanta dake sara mata. Irin mafarkin da tai da dare ne dai babu banbanci. Huci ta furzar da faɗin, “Wace madara ce haka? Tabbas kodaga ina zata fito babu alkairi a cikinta tunda har mafarkin nan ya sake maimaita min kansa. Ya ALLAH”. Ta furta a fili zuciyarta duk babu daɗi, dan zuwa yanzu Iffah ta fahimci wani ɓoyayyen al'amari game da ita, tabbas in har zatai mafarki taita kuma maimaita irinsa sai wani abu ya biyo bayansa mai taɓa zuciya, ta gane hakanne a ɗan zamanta cikin masarautar nan, sai kuma auna abubuwan da suka faru a baya kafin yau ɗin. Sai dai tana ƙoƙarin ƙin gasktama kanta hakan dan kar zuciyarta ta shagala kan abinda zai sakata kaucema umarnin mahaliccinta kuma. Ga kanta jingim kamar yanda yakeyi a duk lokacin datai mafarki makamancin haka, sai zufa data jiƙeta sharkaf tamkar wadda tai wanka. Shigowar saƙo a wayarta da ke gefenta ya sakata tsurama wayar ido na kusan mintuna biyu, kamar wadda aka zaburar wani abu data shafa'a kuma sai ta jawo wayar. Data ta kunna a take tai downloading WhatsApp app..., Bayan ta kammala dai-daita komai tai searching number Sir Fawzan da zuciyarta ke ayyana mata ta fara nema, cikin rashin sa'a taga kusan kwana uku ma baya online ta hanyar lastsin ɗinsa. Duk da hakan bai mata daɗi ba batai wani yunƙurin kiransa ba ta maida akalarta kan number abokinsa Ajmaal. Cikin sa'a shikam dai yana online. Sallama tai masa a taƙaice ta tura, sai dai har kusan mintuna biyu babu reply (yana aiki) zuciyarta ta ayyana mata. Aminta da hakan ya sata cigaba da ajiye masa saƙo kawai a kan duk abinda ya sake faruwa bayan wanda ta tura masa ranar. Daga karshe ta aika masa da roƙon ya bincika mata iyayenta dan har yanzu hankalinta ya kasa kwanciya dangane da su. Ta haɗa masa da adireshin gidansu, da faɗin (In har kaci amanata ko yaudarata na barka da mahaliccin rana da wata yay maka hukunci da alhakin dukkan al'amuran ƙasar ruman da zalincin mulkin wannan shaiɗanin dodo ke tafin hanunsa). Daga haka ta fito shima Sir Fawzan ɗin ta tura masa gajeran saƙo ta goge WhatsApp ɗin gaba ɗayansa ta ajiye wayar. Da ɗan layin nauyin jikin dake tare da ita ta miƙe, tana ƙoƙarin shiga toilet taji kamar an gitta mata ta baya. Idanunta ta ɗan rumtse sai kuma ta waigo. Komai babu dai a zahiri dan haka ta kaɗa kanta kawai ta shige bakinta da addu'a....
Fitowarta kenan bayan ta watsa ruwa alerm ɗin ƙofar yay ƙara alamar ana knocking. Sai da ta zira doguwar rigar abaya data ɗakko cikin kayanta sannan ta ƙarasa ƙofar ta buɗe. Hadimar dake tsaye ta zube ƙasa cikin girmamawa tana kwasar gaisuwa. Amsa mata Iffah tai, zuciyarta babu daɗi akan yanda suke ƙasƙantar da kansu, ta amsa cikin sauƙin muryarta dake a sanyaye sakamakon mafarkin da duk ya sakar mata kasala.. “Wani abu ya faru ne?”. Ta tare hadimar tunkan tace komai. Kai ta gyaɗa mata tana sake rissinar da kanta. “A gafarceni ya Zawjata-almilk. Dama abinci ne aka kawo daga sashen mai Babban ɗaki”. Iffah tai ɗan jim tana hasashen wace kuma mai babban ɗaki? Kamar hadimar ta fahimta tai saurin mata fashin baƙi da “Malikat mai babban ɗaki”. (Malikat Haseenat) shine abinda zuciyarta ta ayyana mata. Ta kaɗa kanta da faɗin, “Okay ba damuwa zan fito”. Daga haka ta maida ƙofar ta rufe. Ciki ta koma, sai dai maimakon zama sai ta koma kaikawo kamar mai Safa da marwa abubuwa masu yawa na faman mata kaikawo. Ta jima a haka sosai kafin ta sake kimtsa jikinta cikin wata tsadadiyar abaya mai adon stones dake ta ƙyalli da ɗaukar idanu. (Wannan yana cikin horon Daneen Ammarah data tabbatar mata koda wasa karta zauna da kazamar shiga ko fitowa da ga ɗaki a raguwar kwalliya. Dolene inhar zata bar cikin ɗakinta ta tabbatar komai na jikinta ya isa a kalleta da shi. A tsarin masarautar hakan ba fariyya bane mutunta kaine ga kowa. A kuma ɗan zaman Iffah cikinsu ta fahimci hakan sarai). A yanzu ma kamar ɗazun turarrukan sa ta baza har ƙamshinsu na rige-rigen fita kafin ita ta fita. Ta fito cikin takunta na nutsuwa da ƙasaita kamar wata budurwar macen ɗawisu (🥱😉lol)..........✍️
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*
*DAUDAR GORA Billyn abdul*
*KI KULANI hafsat xoxo*
*A RUBUCE TAKE Huguma*
*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*
*IDON NERA Mamuh ghee*
_LITTAFI DAYA: 400_ _LITTAFI BIYU: 600_ _LITTAFI UKU: 800_ _LITTAFI HUDU :1000_ _LITTAFI BIYAR: 1200_
_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_
_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
MARYAM SANI ACCESS BANK 0022419171
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
09033181070
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09166221261
*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*
+227 96 09 67 63
Books biyar 1250CFA Books hudu 1050CFA Books uku 850CFA Books biyu 650CFA Bookk daya 450CFA
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨ (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)
𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻
*_35_*
........Hadiman sashin gaba ɗaya kamshin turaren da sukaji ya sakasu tunanin Tajwar Eshaan da bai jima da shigowa ba daga fada ne ya sake fitowa. Sai kuma sukaga saɓanin haka lokacin da Iffah ke ƙarasowa cikin katafaren falon mai ɗauke da duk wani nau'in kayan more rayuwa irin na wanda suka isa. A kujerar da ko ba'a faɗaba tsarin zubinta ya isa tabbatar ma mai kallo Shahan-shan ne kawai ke zamanta ta kai zaune da bismillah a bakinta. Ƙafa ɗaya kan ɗaya ta harɗe fiye da salon sarauniyar Ingila tana kallonsu. Cikin rawar harshe dajin kwarjininta ya cike falon tsaf suka shiga zubewa suna gaisheta. Yatsu biyu ta ɗaga musu cike da ƙasaita batare data amsa ba dan haka kawai yanayin da ta tashi da shi taji bata buƙatar magana. Basu iya sun motsa ba har ta gama zuƙar iska da fesarwa tamkar mai lissafin kaɗawarta sannan ta dubesu, sai kuma ta maida ga tarin abincin da aka shirya yanzu akan wata lallausar darduma saɓanin na ɗazun akan teburin cin abinci. Akan farin tambulan na gilashi mai ɗauke da madara fara ƙal-ƙal ta sauke idanun nata (mafarkina ya zama gaskiya kenan ko saɓaninsa) zuciyarta ta ayyana har lokacin idanunta tsaye akan tambulan ɗin.. Hadiman da basu fahimci ma'anar kallon da takema kayan abincinba cike da girmamawa a gareta ɗaya ke faɗin, “Ya Zawjata-almilk abincine daga saken mai babban ɗaki, an shiryashi ne matsayin liyafa gareki ke da shugaba”. A hankali Iffah ta janye idanunta daga wajen ta maida kan hadimar na tsahon wasu sakkani, acan ƙasan zuciyarta kuwa nanata sunan Malikat Haseenat take tamkar mai bitar karatun hadda. Batare da tace komai ba kuma sai ta kaɗa kanta. Shiru ya sake biyo baya kafin Iffah ta katseshi da duban hadiman da har yanzu dai ke tsaye da alama zaman jiransu sukeyi kenan, dan ta fahimci idan zaici abinci haka suke zagayesa. Kanta ta kauda da faɗin, “Maleek fa?”. Kai tsaye duk suka fahimci wa take nufi, tunda dai duk sun san minene ma'anar kalmar Malik ɗin. Cikin tsantsan da kai ɗaya daga ciki ta amsa mata da “Yanzu ya shigo daga fada”. Bata amsa ba, sai ɗan jimm da tai na tunani akan ambatar fada da hadimar tayi, amma a zahiri ta basar abinta.
★Kasancewar saƙon haɗa liyafar cin abincin na Malikat Haseenat da tai akan iya shi da wadda ake kira matar tasa ya riskesa tunma kafin Iffah, dan kusan shine ma yay sanadin barowarsa fada duk da Aaminsa Miran Jasim (Aami. Kawunsa)ya buƙaci zaman tattaunawa da shi. Badan son ransa ba ya kimtsa ya fito cikin shiga mai sauƙi ta zaman gida. Kamshinsa da takun sawayensa dake tabbatar da girman ikonsa tuni ya iso a kunne da hancin Iffah dama hadiman dake zagaye da ita. Tuni hadiman duk sun zube bisa gwiwunsu kawuna a ƙasa dan kallon shugaban nasu kai tsaye haramunne garesu bisa al'adar masarautar, idanma hakan ta faru gaban Ghazi zaka iya fuskantar tsatstsauran hukunci a dalilin hakan. Akanta dake harɗe kan kujerar da bayan shi babu wani mahaluki daya iya kwatanta zama kanta ya fara sauke ƙasaittun idanunsa. Dai-dai itama ta ɗago nata sakamakon jin takun sawayensa da zubewar hadiman. Cikin ido suka kalla juna, hakan yay matuƙar tsikarar zuciyar Iffah da abinda take faman hasashe da neman tabbaci a kwanakin nan ya tabbata ɗin yau a idanunta. Dan tabbas shigar jikinsa ta yanzu ta sake tabbatar mata da waccan fuskar... Shine ya fara janye nasa kausasan idanun batare data iya tsinto komai a cikinsu ba. Kamewa da gagara fassara abinda ke kan fuskarsa kuma ya taka rawar gani wajen ɓoye ainahinsa. Sai ma kallonsa da ya maida kan ƙaton agogon dake kafe a falon cike da basarwa kai kace bai ganta bane. Ita madai basar da shi ɗin tayi kamar ma bata san da fitowar tasa ba, sai zuciyarta dake faman kai kawo a ƙirjinta cikin sauri-sauri. So take ta gaskata shi ɗinne kota ƙaryata amma zuciyarta taƙi bata haɗin kan karkata akan ko ɗaya a cikinsu. Sai ma neman jefata a ruɗani takeyi......
*_BARRISTER_*
Duk yanda Barrister yaso sanin suwaye su? Mi kuma yay musu basu saurareshi ba suka turasa cikin jibgegiyar baƙar motarsu, yayinda ɗaya daga cikinsu kuma ya shiga motar Barrister ɗin ya fiddo komai na ciki a cikin wata ƙatuwar jakka suka bar wajen.. Suna ɗan matsawa a wajen wani abu mai masifar ƙara ya ziyarci kunnuwan kowa. A take aka fara gudun ceton rai dan duk wanda yasan bomb yasan shine a yanzun ma. “Innalillahi wa inna'illaihirraji'un”. Barrister ya faɗa idonsa nabin motarsa da tai sama ta shiga dawowa pieces ƙasa alamar dai bomb ɗin daga cikinta ya tashi. Duk da ya firgita da mutanen yay jarumtar dubansu fuska a dake. “Ku su waye? Miyasa kuka aikata min haka?”. Babu wanda ya tanka masa a cikinsu, kamarma basu jisa ba sukayi. Hakan sai ya ƙara tada hankalin Barrister, dan ya fahimci ya shiga hannun mugayen mutanen nan kenan. Yunƙurowa yayi da nufin ƙara magana suka jefa masa handkherciff a fuska, daga haka bai sake sanin inda yake ba sai buɗe idanu yay ya gansa a wani ɗaki da bai san inane ba...
Gaba ɗaya jihar Hubab da ƙasar Ruman a rikice ake akan tashin wannan bomb, dan abune da bai taɓa faruwa da su ba. Jami'an tsaro sun iso akan lokaci, sai dai Alhamdullah ba'a samu asarar rai ko ɗaya ba daga mutanen gari, amma ana tunanin harda drivern motar al'amarin ya rutsa saboda babu wanda ya lura da sanda mutanen nan suka ƙwamushe Barrister ɗin kasancewar komai sun yisa ne cikin ƙwarewa... Jami'an tsaro da ƴan jarida tuni sun iso wajen akan lokaci, hakama jama'ar gari masu jarumta sun zagaye wajen domin ganema idanunsu. Babu gawar direban motar a duk iya bincike da jami'an tsaro sukayi, dan basu ga wani alamar sassan jikin mutum ba ko ɗan yatsa, hakan sai ya ɗaure musu kai dan mutanen da abun ya faru a idonsu sun tabbatar sunga lokacin da mai motar ya ajiye ta a wajen ya shiga masallaci, koda aka fito kuma mutane da yawa sun tabbatar sunga lokacin daya nufi motar wasu ma sunce har ya shiga. Wannan zance ya sake ɗaukar hankalin jama'a kowa yana faɗar albarkacin bakinsa akan al'amarin...
Isowar wasu samari wajen kusan dai-dai da tashin bomb ɗin, kallon juna sukai da sakin dariya a tare suna tafawa. Sai da sukai mai isarsu drivern dake jan motar ya ɗauka waya. Nuni yay musu da suyi shiru. Take motar tai tsit kuwa. Ya ɗan rissina cike da girmamawa tamkar yana a gabansa ne yana kwasar gaisuwa, bai damu da a yanda aka amsa masa a daƙile ba ya cigaba da faɗin, “An rufe babinsa ranka ya daɗe”. Murmushi yayi alamar an amsasa da magana mai daɗi daga can. Sai kuma ya sauke wayar da juyawa yana kallon ƴan uwansa ya kashe musu ido. Dariya suka shiga kwasa a yanzun ma, bayan sanyi wadda suka gamsu sun wadata sannan suka fita suma suma shige cikin taron mutanen dake wajen dan jin mi'ake tattaunawa.....
★★★..... MASARAUTA ★.....
Sai da ya kai zaune a inda aka shirya tarin abincin da kusan minti biyu sannan ta motsa itama dalilin maganar da Hadimai sukai mata. Bata musa ba ta miƙe zuwa inda yaken cikin takunta na nutsuwa da wasu ke ɗauka yanga ko makamancin hakan. Zama tai irin nasa na ƙasaita sai dai da alama ita kanta bata fahimci tayi hakan ba ma. Tsaurin idonta ya sakashi dubanta ta gefen ido batare da alamar hakan ta bayyana a yanayinsa ba. Tuni hadiman suka ƙaraso domin shirya abincin garesu. Iffah batai yunƙurin hanasu ba, dan a ganinta dole ta nutsu ta fara fahimtar yanda ake masa komai kafin ta karɓa wannan tsarin shima. Ta ɗan bi madarar da hadimar ta ɗauka, har yanzu zuciyarta na mata wasiwasi akan madarar batare data san dalili ba... “Bar nan”. Ta faɗa dai-dai Hadimar na yunƙurin zuba madarar a ƙaramin cup na glass daya gama haɗuwa. Cikin mamaki hadimar ta sake risinar da kai domin girmamawa ga Iffah tana faɗin, “Ya Zawjata-almilk madara na ɗaya daga cikin abinda shugaba yafi buƙatar amfani da shi a irin wannan lokacin”. Kai tsaye babu ko ɗar tattare da Iffah tace, “Na yau dai bazai sha ba. A ɗaukesa anan”. Tsoro ne ya bayyana sosai a fuskar hadimar, gashi bata da damar ko satar kallon sashin da Tajwar ɗin yake balle ta fahimci karatun tasa fuskar. A ɗan ɗar-ɗar na rashin madafa ta ajiye tambulan ɗin a gefe ta ƙarasa aikinta. Duk da abinda ake yi a gaban Tajwar Eshaan ne, yanaji kuma yana gani. amma tsabar miskilanci da ƙarfin iko irin na masu ƙasa a hannu bai ko motsa ba balle bada wata alama akan abinda Iffah tayi ya bashi mamaki, ko ya ɗimautashi, koya birgesa, koya bashi haushi. Ko ɗaya babu mai iya tsinta a yanayinsa. Iffah ma dai bata yarda ta dubesa ba balle ta tsinta komai a tattare da shi ɗin. Sai ma wani kallon da taima hadiman ya tabbatar musu bata bukatarsu a wajen. Dan haka tuni suka ɓace tamkar ƙyaftawar ido. Ya ɗan ja wasu mintuna zaune batare da ya taɓa komai ba, Iffah ta ɗan laɓe baki, acan ƙasan maƙoshi ta furta “Ranka ya daɗe barka da wannan lokaci”. A hankali ya ɗago ya zuba mata idanunsa, a mamakinsa bashi take kalloba ma. Kuma ya tabbatar itace tai maganar ba wani ba dai. Sake tsukewar fuskarsa mai cike da gizago da motsa hanunsa dake kan spoon ya tilasta Iffah ɗan ɗagowa garesa. Sai kuma ta tsaya cak tare da ɗago birkitattun idanunta da ƙyau. Cikin nasa dake kallonta suka shige tamkar ya tsara hakan da gayya. Muƙut ta haɗiye yawu da ƙoƙarin kame rauninta dake neman bayyana a fili ta kauda kai gefe.. Shima nasan ya janye a ƙasaitance ya fara cakulal abincin kamar mai cin magani batare da ya amsa mata gaisuwar tata ba. Hakan da yay ya sosa zuciyar Iffah, dan haka ta kumbura fuska lips ɗinta suka shiga motsawa alamar akwai magana a bakinta sai dai babu damar faɗa...
★★.... ★....
Tun bayan tabbatar da madarar ta shiga jerin abincin liyafar da aka shiryawa Shahan-shan da Zawjata-almilk ta kasa zaune ta kasa tsaye, bukatarta kawai taji sakamakon da take buƙata ga amintacciyar hadimarta akan lokaci. Sai dai kuma shiru kakeji wai malam yaci shirwa har lokacin da labarin tashin nakiya a jihar Hubab ya iso cikin masarautar. Ba wannan ne a gabanta ba, dan haka cikin jan tsaki ta kashe television ɗin a harzuƙe. Idanunta ta sake maidawa kan agogon falon tanaji kamar tai tsalle ta ganta a sashen Tajwar Eshaan ɗin ayita ta ƙare. Dan yanzu a duniyar nan gani take bata da babban maƙiyya sama da yarinyar nan datai mugun shige mata hanci amma ta gagara fyatota ta huta a dalilin gargaɗin Uwa data kasa gane manufarsa har yanzu. Sai dai yarda da Uwa ɗin ya tilasta mata bin komai ɗin a sannu. Zata iya rantsuwa tunda ta san kanta bata taɓa cin karo da abinda ya kiɗima zuciyarta ba irin saƙon Zawjata-almilk na raye bayan ta kwana a turakar Shahan-shan kuma. Ba ita kawai ba, hatta Uwa hakan ya kiɗimata da sake tabbatar da yaƙine na gaske tsakaninsu da wannan yarinyar kenan. Dan haka batai wani magana mai tsaho da Ta-kurya ba bayan bata umarnin a isar da madarar data bata ga Iffah ta ɓace cikin tsanani ɓacin rai daya ƙara birkita dukkan tunanin Ta-kurya ɗin a yanzu har ta kasa zaune ta kasa tsaye sakamakon hakan........✍️
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*
*DAUDAR GORA Billyn abdul*
*KI KULANI hafsat xoxo*
*A RUBUCE TAKE Huguma*
*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*
*IDON NERA Mamuh ghee*
_LITTAFI DAYA: 400_ _LITTAFI BIYU: 600_ _LITTAFI UKU: 800_ _LITTAFI HUDU :1000_ _LITTAFI BIYAR: 1200_
_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_
_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN