Kenza eBookz

Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul - Chapter 24

Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul - Chapter 24

Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul Chapter 24: Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul Chapter 24. KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN…

4,487 words

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨ (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)

𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻

*_45_*

........Daneen Ammarah dake tunanin yanayin ma Iffah tashin hankaline kawai sai ta shiga rarrashinta. Dole Iffah ta cigaba da pretending da matsawa a sallameta taji sauƙi. Daneen Ammarah na rakata sashen ta wuce dan jikin Malikat Haseena ma dai babu daɗi sam. Dama Daneen Ammarah ɗin ta zauna da Iffah ne domin saka ido kar wani ya cuta mata itama. Hakan yama Iffah daɗi, dan ya bata damar nutsuwa a kallon videon data ɗauka ɗazun. Sosai tai zooming gawar Zawjata-almilk tana kai bin jikinta ta inda yake a waje daki-daki. Wata irin zabura tai ganin abinda take ma ɗin kuwa a saitin wuyan gawar ta gefen kunenta na haggu. Wato alamar ɗigon sarin maciji har biyu. Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un take ambata wata irin zufan na keto mata, dan kuwa tabbas zancen mutumin can ya zama gaskiya. Amma duk da haka tana buƙatar sake tabbatar wa. Cikin rawar da jikinta ke mata ta shiga laluben number ɗin Sir Fawzan. Bugu ɗaya kuwa ya amsa kasancewar dama a jirace yake da kiran, dan ya nemeta amma bai samu ba. Yaci kuka har ya godema ALLAH dan zatonsa ma ita suka rasa. Cikin rawar murya ya ambaci sunanta duk da yaji muryarta. Amsawa tai da kuka, bata jira cewarsa ba tace, “Sir kaji tsoron ALLAH ka sanarmin gaskiya akan iyayena. Na rokeka karka ɓoyemun komai”. Zufa ce ta shiga karyo masa tako ina, dan baiyi tunanin jin wannan tambayar bazatanba a bakinta. Shirunsa ya sake tada hankalin Iffah, ta cigaba da masa magiyar da dole ya faɗa mata gaskiyar data buƙata. “Tabbas na ɓoye miki Iffah, amma tun bayan barinki gida baifi da kwanaki ba aka rasa ɗan uwanki da Babiy sakamakon......” Ya zayyane mata labari tiryan-tiryan kamar yanda ya bincika. Babu kuma banbanci da abinda ta gani a wancan video ɗin na farko. Ya kare da faɗin, “Wlhy har yanzu akan binciken inda aka kaisu ake amma babu labarinsu. Nima kuma a yanzu haka ina yin nawa ta ƙarƙashin ƙasa amma har yanzu ban samu wani bakin zaren ba....” Kukan data fashe masa da shi ne ya katsesa daga jawabin nasa. “Ba zaku gansu ba, ba zamu ƙara ganinsu ba, sun rabani da su kamar yanda suka rabamu da ƴan uwana. Wlhy nima sai na kasheshi kamar yanda ya kashesu. Na rantse bazan barsa ba, bazan taɓa barinsa ba. Yanda ya halakasu da macijin tsafi sai na halakashi da dafin maciji na gaskiya. Shima sai ya ɗanɗa......” kuka ya sarƙeta ta kasa cigaba da magana... Cikin tashin hankali daga can Sir Fawzan ke faɗin, “Iffah ban gane ba. Dan ALLAH ki daina kuka kimun bayani, kaina ya kulle dan ALLAH kiyi shiru kinji, wlhy na miki alkawarin taimaka miki akan koma minene, koda kuwa nima zan rasa rayuwata ne.....”. “Babu wannan lokacin sir, bani da shi. Kai dai kawai ina zan samu dafin maciji mai haɗarin gaske?”. “Ya ALLAHU! dan ALLAH ki faɗamin mike faruwa? a yanda zan fahimceki”. “Idan bazaka samamin abinda nake buƙata ba na Barka lafiya”. Yana hello-hello bata sauraresa ba ta yanke wayar, koda ya sake kira bata ɗauka ba, da taga zai dameta ma sai ta jefa shi a black list. Kaikawo ta cigaba dayi a ɗakin tana kuka. Komai ya cakuɗe mata, zuciyarta ta gama ƙeƙashewa da bushewa. Ta sallama duk wani ɗan sauran rangwamenta. Abinda kawai idonta da zuciyarta ke gani gawa huɗu ta ahalinta kwance duk a dalilin mutum ɗaya tak, lokaci yayi da zatai abinda ya kawota itama dan bai cancanci cigaba da rayuwa ba mutumin nan sam, tayi alkawarin tare zasu mutu, amma sai ta kasheshi ta kuma bayyanama duniya wanene shi. Yanda taci kuka ta fita hayyacinta dole ta bama duk wani tausayi, da ƙyar ta iya zaman rubuta komai da ya rage, ta tattare ga Ajmaal, a ganinta ta gama tattare dukan abinda ya dace ta tattare masa. Hatta ƙudirinta na kawar da Shahan-shan ta hanyar dafin maciji bata ɓoye masa ba. Ta kwashe videos ɗin dake wayar zuwa wayarta ta turama Ajmaal ɗin, takumayi gajeren video da kalaman masu girgiza zuciya har biyu. Ɗaya na Ummu da su Kaka ta roƙa ya bamawa, ɗaya kuma na al'ummar ƙasar ruman ne baki ɗaya. Shima tai masa godiya da fatan alheri da nasara har ƙarshen rayuwa.......

★★..... BARRISTER ★★.....

Barrister dake jin kamar ya ƙwaɗa wayar da ƙasa ya rumtseta a hannunsa da masifar ƙarfi, a karo na farko wasu zafafan hawaye suke silalo masa. Jarumar zuciyarsa zugasa take kada ya yarda ya amince koda zai rasa rayuwarsa, yayinda wani ɓangaren kuma ke haska masa iyalansa da yafi so fiye da komai a duniya a halin yanzun. Wannan shine tashin hankalin mafi ƙololuwar girma daya taɓa cin karo da shi a rayuwarsa....

Washe gari da safe wujiga-wujiga ya wayi gari, amma hakan bai saka ko gezau ga mutanen ba. Sai ma duk wani details daya shafi case ɗin da suka dire masa. Mamaki da tsoronsu ya sake mamayesa ganin duk wani abinda ke hannunsa ne. Kuma ya adanasu ne a mabanbanta wajeje. Akwai wanda a gidansa suke, akwai wanda a office suke, akwai na mota ma. Amma abin mamaki gasu duk a gabansa sun tattaro sun kawo masa. Tabbas ya sadaƙar, dan mutanen nan hatsabibaine na innanaha. In har zasu iya hakan a kankanin lokaci bayaji idan ya bijire musu iyalansa zasu tsira kuwa.... “Barrister baka da lokacin dogon tunani, ka shirya dan a yau oga ke son ka tattaro masa duk bayanin da yake buƙata a wajen mutanen can. Ciki har da sanin su wanene ainahin masu aikin, da inda suka ɓoye Abu Hanash da ɗansa”. Karan farko Barrister ya dubeshi a razane, har ƙoƙarin taune harshe yake wajen faɗin, “Kana nufin dama baku bane ke riƙe da su Abu Hanash ɗin...?” Saurayin yay ɗan waige-waige alamar baya son wani yaji, cikin raɗa-raɗa yace, “Bamu bane Barrister. Muma kuɓutar da su muke son yi har ma da kai kanka. Sai dai ban san miyasa oga bai son ka sani ba ya zaɓi baka aikin a kife”. Ba ƙaramin zabura Barrister yay ba jikinsa har rawa yake ya matsa gab da saurayin. “Dan ALLAH kada ka yaudareni ka faɗa min gaskiya”. Da sauri saurayin ke masa nuni da yay ƙasa da murya kar wani yaji, “Barrister wlhy kaji na rantse maka abinda na faɗa maka shine gaskiya. Na kuma sanar maka ne saboda ka bani tausayi. Amma iyalanka kansu suna zagaye da tsaro ta yanda wani bazai taɓa iya samun damar cutar da su ba, kai kanka kusan sati uku fa muna tare da kai batare daka sani ba. Oga ba azzalumi bane ba, amma ban san miyasa bai son kasan taimakonku zaiyi ba. ya kamata kaima ai ka gane hakan tun farko musamman aikin daya baka ɗin, taya wanda zai cutar da kai zai kuɓutar da kai?, taya wanda zai cutar da kai zai ɗauraka akan hanyar abinda kake nema ya baka bakin zarensa haka cikin sauƙi?”. “Hakane wlhy ɗan uwa hakane. Kaina ne ya kulle a ruɗani nake gaba ɗaya. Nagode nagode yanzu kam ka bani ƙwarin gwiwa, insha ALLAHU kuma sai na bada mamaki. Dan a wannan gaɓar sai su Abu Hanash sun fita da izinin UBANGIJI, zan kuma gano koma wanene da hannu a kan ɓoyesu”. “ALLAH ya baka nasara. Ni bara naje kar wani ya fahimci ina anan har yanzu”. Kai kawai Barrister ya ɗaga masa yana murmushi. Wannan tattaunawa ce ta bama Barrister duk wani ƙarfi da sabuwar himma na musamman, a yanzu kama baka iya ganin komai sai murmushi tare da shi, lokacin da aka kawo masa abincin rana ya buƙaci takarda da abin rubutu. Takardu aka kawo masa bama takarda ba, hakan ko ya masa daɗi, dan ya kwashe sauran wannan yinin da dare wajen tsara duk abinda ya dace. Washe gari har ya fisu zumuɗin son fita ma, sauran da basu san miya faru ba canjawar Barrister ɗin taita basu mamaki.....

★★... KAUYEN JUMNA ★★....

Tun kammala bayanin Abu Zainab ga su Kaka jikkunansu duk yay sanyi, Ummu ma hawaye takeyi, Barrister shine hope ɗin su a yanzu bayan UBANGIJI masanin abinda ke fili da ɓoye. Gashi a dalilinsu an rasashi. Idan har aka cutar da shi ta dalilinsu bazasu yafema kawunansu ba. Kaka dai jinjina kai kawai yake amma komai ya kasa cewa, sai Iyyani ce cikin ƙarfin hali da sharar ƙwalla ta dubi Abu Zainab da damuwa ke shimfiɗe a fuskarsa. “Zakariyya kuyi haƙuri dan ALLAH, mun jefa rayuwarku a haɗari, ya ALLAH ka bayyana Abdullahi da gaggawa”. Ɗan murmushin yaƙe Abu Zainab yayi, cikin danne abinda ke masa kaikawo yace, “A'a mama ai mutum baya taɓa wuce ƙaddararsa, kuma har yanzu bamu tabbatar ba ko akan wannan case ɗin bane muka rasa shin, dan Barrister da kike ganinsa nan shima hatsabibin kansa ne, gaskiyarsa da tsayuwa akan ganin tabbatar da ita yasa yanada maƙiya da yawa akan cases daban-daban hatta a cikin abokan aikinsa ma. Kinga kuwa zama ta iya yiwuwa ba'akan wannan ɗin bane.....” “Dole ya zama akan wannan ne” Kaka ya faɗa cikin katse Abu Zainab. Duk kallonsu suka maida a kansa. Ya jinjina kai batare da ya kallesu ba. “Ban san gaibu ba, amma inaji a jikina akan su Muhammad Zayyanu ne, sai dai kuma tabbas koma a ina yake har yanzu yana raye insha ALLAHU. Inajin wannan ƙwarin gwiwar ne a zuciyata”. Ba ƙaramin mamaki kalaman kakan suka basu ba, sai dai kowa ya gagara cewa komai sun dai zuba masa ido. Kusan mintuna biyu gidan shiru kafin kaka ya miƙe, babu jimawa ya dawo da jakka a hanunsa. Su dai duk suna kallonsa kawai. Takardar daya zaro ya miƙama Abu Zainab. “Ungo duba wannan”. Da sauri Abu Zainab ya amsa ya fara karantawa. Bakinsa cike da magana ya ɗago yana duban kaka da ke kallonsa. “Baba wannan kuma fa?”. Murmushi Kaka yayi da kauda kansa kamar bazaice komai ba. Sai kuma ya ɗan taɓe baki da fara basu labarin yanda duk a kai a randa zai dawo. Ya ɗora da faɗin, “Saurayin daya kawoni gidan nan zuciyata ta bani ba haka nan ya kawoni ba....” “Amma baba shine ka amince harma da nuna masa gida?”. Kaka yay ƴar dariyarsu ta manya. “Zakariyya kenan, to idan baka iya kama ɓarawo ba ai shi sai ya kamaka. Ka ganni nan barni kawai inda ka ganni. Idan na nuna nasan yanada manufa a kaina tun farko kamar yanda naso nuna masa a tasha ai bazan san sirrin zuciyarsa ba. Amma dana bashi dama fa? Yanzu a tafin hannuna yake, kuma jirace nake da zuwansa dan na tabbatar zai dawo, na masa talalar da tabbas sai ya dawo da izinin UBANGIJI”. Abu Zainab kam a yau Kaka ya fara bashi tsoro. Sai dai ya danne bai yarda ya nuna ba. Kaka ma ya fahimci haka amma ya kanne, sai jakkar ya tura ma Abu Zainab yana faɗin, “Wannan sune kuɗin dake tare da takardar”. Nan ma dai da mamaki Abu Zainab ke kallon kuɗin, kuɗine masu yawa sabbi ƙal sai ƙamshi suke na sabunta. “Baba waɗan nan mutanen kuwa anya....” Kaka yay murmushi mai bayyana haƙora. Sai kuma ya ɗan kalli sashen da Ummu ke zaune. Tuni ta tashi batare da sun farga ba har Iyyani..........✍️

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_ _LITTAFI BIYU: 600_ _LITTAFI UKU: 800_ _LITTAFI HUDU :1000_ _LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI ACCESS BANK 0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 96 09 67 63

Books biyar 1250CFA Books hudu 1050CFA Books uku 850CFA Books biyu 650CFA Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨ (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)

𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻

*_46_*

..........Lokacin da kaka yayi ma Abu Zainab rakkiya sukejin halin da ƙasar ke ciki, dan shima Abu Zainab kasancewar fitowar sassafe yayi sannan komai bai fasu ba. Hankalinsu yayi matuƙar tashi dan basu san wacece a cikin matan sarkin ta rasu ba. “Zakariyya zama bai ganni ba, dole ne mu wuce tare kenan, kayi haƙuri kaɗan jirani anan ina zuwa”. Kaka bai jira cewar Abu Zainab ba ya koma gida da sauri, koda su Iyyani sukaga a yanayin da ya shigo suma hankalinsu ya tashi, amma tambayar duniya yaƙi ce musu komai kan abinda ya farun, sai cemusu da yay shima zaije Daular ruman ne.”. jin wannan furucin nasa yasa jikin Ummu fara rawa, a hankali ta zube ƙasa dan zuciyarta ta gama bata kodai ta rasa Iffah ko su Babiy. Dama yau kusan gabbanin asuba tayi mafarkin Iffah na kuka da kiranta tazo ta ceceta, sai kawai ma zuciyarta tafi karkata akan Uffan..

Su Kaka sun iso daular ruman a harmutse, dan ƴan zanga-zanga nata da ɗa karuwa harma abin na bama mutane mamaki. Yayinda jami'an tsaro tuni sun fito ta kowane titi na masarauta sun tare. Da ƙyar suka samu ƙarasawa gida, kasancewar ana aikowa gidan domin halartar jana'iza yasa Kaka yay tunanin wannan ma indai Iffahr ce zasu aiko. Dan haka suka shiga tambayar ƴan anguwa amma kowa na tabbatar musu babu wanda yazo. Hankalin Kaka ya tashi fiye da farko, dan kuwa dai bayan wannan hanyar babu wata mai sauƙi da zai iya ji sai abokinsa dogon yaro da ke cikin masarauta. A yanda kuma garin yake hakan abune mai wahala a garesa kenan......

★ BARRISTER ★

Yanayin da aka wayi gari a ƙasar bai hana su Barrister fitowa ba, sai ma lokacin shi yasan abinda ke faruwar, al'amarin ya taɓa masa zuciya, dan ta wani fannin case ɗinsa tamkar kacokal yanada alaƙa mai ƙarfi ne da abinda ke faruwar. Har yaji yana tsoron ace yarinyar ce ma ta rasa ran nata. Dan dole dai ya daure ya isa inda ya nufa. A yau dai bai samu Sayyid Faizul-Anwar a falon ba, sai dai kasancewar an san da zuwansa ya samu tarbar data dace. Bayan zaman kusan mintuna arba'in Sayeed ya fito cikin shigar jallabiya, cikin girmamawa Barrister ya gaidashi, ya amsa masa da kulawa shima yana masa barka da zuwa. Suna tsaka da gaisuwar cikin yaran Sayeed ya shigo ya isar da saƙon zuwan wasu baƙin. Damar shigo da su ya bada dan yasan da zuwansu, daga haka ya maida hankalinsa kan Barrister. Barrister yayi matuƙar mamakin ganin baƙin, sai dai ya danne hakan dalilin kallon da suke masa matsayin Barrister Akeem. Gaisuwa sukai ta mutunta juna, har suna tsokanarsa da cewa shine idonsu na gari. Murmushi yayi yana rissinar da kai alamar girmamawa. “Kar kuji komai ranka ya daɗe, a komai muna tare da ku kuma zamu kare mutuncin ku”. Sosai suka nuna jin daɗi da zancensa. Nan suka shiga kwarzantashi. Shi dai nasa murmushi ne a zahiri, a kasan rai kuma yana matuƙar mamakin abokinsa da ɓoyayyun ayyukansa. Dan bai taɓa tunanin Barrister Akeem zai iya irin waɗan nan ayyuka ba..... “Barriter ina alkawarin mu?”. Sayeed Faizul-Anwar ya katse masa tunani. Ajiyar zuciya yaja a ɓoye, sai kuma ya muskuta yana murmushi da taɓa bag ɗin daya shigo da ita. “Ranka ya daɗe komai yazo hannu fiye ma da yanda kuke buƙata. Sai dai kafin mukai ga nan ina son nace wani abu saboda wasu dalilai”. “Faɗi kanka tsaye Barrister baka da damuwa akan hakan”. “Nagode ranka ya daɗe. Bawani abu bane mai girma akan dai shi wannan case ɗinne. Komai dai gashi na gani anan kuma na tattaro, sai dai yanda aka bani aikin a dunƙule ina ganin ya kamata nace wani abu duk da dai naga komai a kansa, amma saboda nasan inda duk ya kamata na toshe a ramukan da zasu iya yunƙurin buɗewa koma su buɗe ɗin yasa nake son bada shawara bisa wani hangena”. Shiru kamar bazasu ce komaiba. Sai dai sun maida dubansu ga Sayeed Faizul-Anwar, kai ya gyaɗa musu alamar tabbatar da babu matsala, dan haka kusan a tare suka sauke numfashi, kafin ɗaya a ciki ya shiga faɗin. “Barrister mun yarda da kai, sai dai ka sani koda baka san komai akan case ɗin nan ba bazamu taɓa bari wani rami a buɗe mana ba koya buɗe maka, zamu kasance a bayanka a kowanne lungu da saƙo na ƙasar nan.” “Nagode da wannan karamci”. Barrister ya faɗa da girmamawa. “Baka da damuwa Barrister ka cancanta ne.” Murmushi ya sake saki tare da mikewa ya kai jakar gabansu, cike da farin ciki suka buɗe suna mai fiddo duk takardun ciki. Bayan sun ɗan dudduba su suka ɗago fuskoki cike da murmushi suna yabama Barrister namijin ƙoƙarin sa. Shi dai nashi murmushi ne kawai. Ɗaya daga cikin baƙin da ake kira da Sayeed Harun Al-rashid, babban mutum ne a ƙasar ta ruman, dan riƙƙaƙen ɗan kasuwa ne na gwal da kowa ya sani kasancewar sunansa yayi matuƙar shura a wannan harkar data zama babban tattalin arzikin su na ƙasar, dan Ruman kam bata san iya arziƙin gwal da ALLAH yay mata ba, shiyyasa duk wani riƙƙaƙen ɗan kasuwa zaka samu gwal ɗin ne mafi rinjayen makaminsa kamar dai Sayeed Harun Al-rashid. Ta wani gefen kuma yana riƙe da sarauta sai dai yafi bama kasuwancin muhimmanci matuƙa. Zamansa ya gyara sosai yana fuskantar Barrister. “Barrister yanzu mi kake son ka sani?”. “Ranka ya daɗe ba komai bane dama sai akan waɗan da naga case ɗin ya karkata. Na duba dukkan bayanan Barrister Abdallah Aas, sai dai a yanda na fahimta kamar ya gano inda su mutanen dake hannun naku suke, dan kafin ma ya rasa ransa kamar ya fito da ga ƙauyen Lufana ne wajen matar marigayin, abinda nake son cewa anan ina tsoron yazam bayan Barrister ɗin akwai wanda yasan wannan sirrin. In kuwa hakan ta kasance zaman mutanen a station ɗin dana fahimci kun ɓoyesu zai zama barazana ke nan koda anan gaba”. Kusan a tare sukai murmushi, Sayeed Harun Al-rashid ya muskuta zamansa cikin nuna damuwa da zancen Barrister. “Maganar ka nakan hanya Barrister shiyyasa tun kafin yau muka gama maganin duk abinda kake gudun. Tun daga farkon wannan case ɗin idanunmu akan komai suke, dan haka ka kwantar da hankalinka. Su kuma tuni basa a police station ɗin, dama mun kai ajiyar su ne domin ɓadda kama bayan kwanaki kuma muka ɗauke su, amma kai a yanzu mi kake son cewa?”. Anzo dai-dai gaɓar da Barrister keson azo, dan haka ya ɗan murmusa yana mai ƙara bama kansa nutsuwa. “Alhmdullh kun fahimci inda nake buƙatar akai ranka ya daɗe. Abinda nake son cewa kai tsaye shine ayi duk yanda za'ai cikin kwanaki biyun nan abar ƙasar ruman da mutanen gaba ɗaya”. “Eh maganarka abin dubawa ce kam, amma kuma mizai hana kawai a ɓaddasu a wuce wajen, dan abinda ya zama dalilin zuwansu hanunmun ma an sameshi cikin sauƙi yanzu haka”. Barrister yay ɗan jimm dan bai fahimta ba, amma sai ya dake bai sake musu wata tambaya ba gudun karsu zargi wani abu. Sai dai ya cigaba da faɗin, “Ɓaddasu bashine mafitaba ranka ya daɗe, dan a ɗan bincike da nayifa akwai babbar matsala game da mutuwar Barrister Aas”. Babu wanda zancen bai daka ba a acikinsu, Sayeed Faizul-Anwar daya kafe Barrister da ido yay saurin faɗin, “Barrister bamu fahimce ka ba, mi kake son cewa?” “Ranka ya daɗe yanzu zan fahimtar da ku. Idan har kun saurari dukkan labaran dake yawo har yanzu babu wani tabbaci na samun alamar sassan mutum a cikin motar Abdallah, wannan shine yaja hankalina tun a ranar farko bayan nabar nan na fara nazari da bincike. Tabbas Abdallah na raye, sai dai ya ɓoye kansa domin bada ƙafa. Na sanshi nasan mizai iya fiye da tunaninku. Shiyyasa nake ganin kashe mutanen a yanzu bashine mafita ba, muyi nesa da su da ƙasar nan ta yanda babu inda zasuji ɗuriyarmu, sai kuma mu samo wasu a madadinsu a buɗe shari'ar ta yanda zamu ƙona Barrister Abdallah Aas da ransa batare daya farga ba”. Dukansu gumi suke na tashin hanakali, sai dai babu wanda ya iya cewa komai har zuwa wani tsahon lokaci. Sayeed Harun Al-rashid ya nisa yana mai share ɗan gumin daya taru masa a goshi. Ƙyaƙyƙyawar fuskarsa fara tas gaba ɗaya ta ƙwaɓe alamar rashin damuwa. “Zartar da hukunci bazai yuwu yanzu ba Barrister, amma kaje zuwa anjima zakaji komai ta waya”. “Babu damuwa ranka ya daɗe”. Barrister ya faɗa cikin jimami shima, sai dai acan ƙasan ransa dariya yakeyi, yayinda wani gefe na zuciyarsa ke tabbatar masa akwai wani babba mai alaƙa da case ɗin bayan su, shiyyasa bazasu iya zartar da hukuncin ba kai tsaye. Yau ma dai an rakosa da kuɗi masu yawa har mota.......

★★... BAYAN KWANA BIYU ★★....

A kwanaki biyun nan abubuwa da yawa sun faru tako wane ɓangare, sai dai marasa daɗi sunfi masu daɗin rinjaye. Zuwa yanzu dai da gaske ƙasar ruman da jama'arta suke basa buƙatar Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed matsayin Shahan-shan. Dan tun tsirarun mutane na zanga-zanga a wasu jahohi takai yanzu ƙasar ma gaba ɗaya ta ɗauka. Abu mafi ban mamaki harda wasu a manyan ƙasar na nuna goyon baya ga talakawa, ciki kuwa harda wasu Tajwar na jihohi. Yayinda ta wani gefen kuma hankalin wasu manyan ƙasashen duniya ya fara dawowa kan zanga-zangar dama dalilin yinta. Babban abinda ke tunzura jama'a shine biris daga Shahan-shan, yayinda kuma a cikin gida hankalin ƴan majalissar sa ya rabu kaso biyu, wasu na goyen bayan ya saukan wasu na buƙatar karya sauka dan shine kawai ya cancanta da kujerar a ganinsu. A talakawan ma bai rasa tsirarun masoya ba, sai dai basu da ƙarfin ja da masu boren shiyyasa suka koma gefe sukai shiru matsayin masu kallo da ido.

*_IFFAH!_*

A kwanaki biyun nan yanda Daular ruman ke a hargitse haka Iffah ke a hargitse. Kuka kam idanunta har sun daina fidda ruwan hawaye. Cikin ƙanƙanin lokaci tayi wata irin rama mai ban tausayi. Haukan da iyalan Sayeed Khairul-Bashar keyi a masarautar da wanda jama'a keyi a waje sai ta ɗaukesa wasan yara. Idan su da suka rasa uba kawai zasu harmutsa masarautar haka ina ga ita data rasa ahalinta duka, a ganinta ita ya cancanci ta hargitse ƙasar ruman baki ɗaya ma ai. Sai dai yanda ƴan zanga-zanga ke daɗa ƙaruwa na saka mata farin ciki, dan abin ban mamaki har wasu a cikin Tajwar na jihohi suma sun ƙara tunzura wuta da bada goyon baya akan saukar Shahan-shan ɗin, hankalin ƙasashe kuma ya fara dawowa ƙasar ruman, da alama dai dama a jirace kowa yake da wannan damar. Hakan na sake tunzura ƙwarin gwiwar ƙudirinta. Wutar wannan al'amari na ƙara ruruwane dalilin shirun Tajwar Eshaan. Babu shi babu cewarsa, harma wasu sun fara tunanin anya kuwa yana cikin masarautar ma ko?.... Duk wannan bai damu Iffah ba a yanzu, hankalinta gaba ɗaya ya tattara ne akan ta ina zata samo dafin maciji. Bata da wani amintacce a cikin masarautar, a waje kam sir Fawzan ne kawai, shima kuma zuwa yanzu ta fara shakku akansa saboda tana ganin ya ɓoye mata abinda ya faru da su Babiy ne bisa wata manufa. Idan tace zata fita a sulale daga masarautar taya kuma zata dawo cikinta? Wannan ƙalubalen keta faman mata kaikawo harya gagara samun mafita a kwanaki biyun nan. Tana a bangarenta bata ganin kowa kowa baya ganinta, waɗan da zasu iya ganinta hankalinsu a tashe yake dan kai tsaye su abin ya shafa, shirunsu kuma sai ya bama Iffah damar fassarashi da abinda zuciyarta ta gama tabbatar mata, dan haka itama a yanzu ta haƙƙaƙe bata da lokacinsu.

Kamar yanda ta tsara bayan sallar la'asar ta shirya tsaf cikin abaya data amshi jikinta, dan ma ta rame ga idanunta da suka ɗan kuklumburo amalar taci kuka bana wasa ba. Duk da masarautar a harmutse take haka ta keta cikinta hadimanta na take mata baya har sashen marigayi Sayeed Khairul-Bashar. Tayi matuƙar mamakin tarbar data samu dan batai zaton irinta ba, sai dai abinda bata sani ba shine su kallon tausayi suke mata da tabbatar da itama bawai ta tsira bane a hannun azzalumin. Dan malamin duba da matar Sayeed Khairul-Bashar ɗin ta ziyarta tun lokacin daya ɓata kafin aga gawarsa ya tabbatar mata akwai ƙulli mai girma da Shahan-shan keyi game da rayuwar Iffah shiyyasa itama bata mutu ba a sanda aka kaita sashenshi. A ranar bata ɓoyema ƴaƴanta komai akan zancen nan data jiyo ba, sun kuma yi niyyar samun Iffah har sashenta da batun washe gari aka tashi da wannan tashin hankali. Wannan shine dalilinsu na mata tarbar data bata mamaki. Ita kuma kasancewar zuciyarta a kusa take tana musu ta'aziyya tana share hawaye da handkherciff. Sai hakan ya ƙara mata kima a idon iyalansa. Yayinda ƴan uwansu kuma da basu san komai na ke jin zafin ganin Iffahr da fassarashi matsayin leƙen wani asiri dan a yanzu wasu a cikin ahalin masarautar su kuma suna ma Iffah kallon wata ƴar kaɗafin Tajwar Eshaan ce tunda har ta tsira daga kisan gillarsa..........✍️

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_ _LITTAFI BIYU: 600_ _LITTAFI UKU: 800_ _LITTAFI HUDU :1000_ _LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI ACCESS BANK 0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 96 09 67 63

Books biyar 1250CFA Books hudu 1050CFA Books uku 850CFA Books biyu 650CFA Bookk daya 450CFA

Readers Also Read