Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul - Chapter 25
Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul Chapter 25: Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul Chapter 25. KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN…
4,498 words
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨ (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)
𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻
*_47_*
.........Kamar yanda Iffah tai tunani labarin zuwanta sashen Sayeed Khairul-Bashar ta'aziyya har ya isa kunnen surukarta dama na jikin Tajwar Eshaan irinsu malikat Haseenat da su Daneen Ammarah. Dan tana fitowa kiran Daneen Ammarah ya shigo wayarta. Bata ɗaga ba, aka kuma sake kira nan ma dai ta share kamar bataji ba. Sai da ta koma sashenta da kusan mintuna goma sannan tai kiran Daneen Ammarah ɗin back. A bugu biyu ta ɗaga, Iffah ta taɓe baki cikin rashin damuwa tai sallama da fara gaishe ta. Da kulawa Daneen Ammarah ta amsa. Iffah na jiran jin ta mata batun fitarta sai Daneen Ammarah ta jeho mata tambayar da bata da alaƙa ma da fitar. “Ibnati na kiraki ne akan Abni, shirunsa na tadamin hankali matuƙa, gashi yana ƙara harzuƙa mutane ƙasa, kinga dai yanda ƙasar nan ke sake rikicewa. Mu dukanmu mun nemesa a waya amma bamata shiga, na fara zargin anya ma yana cikin masarautar nan?”. Murmushin takaici Iffah tayi, amma a zahiri sai ta danne ta fara magana cikin kwantar da murya. “Wannan shine tunani na nima Mamy, sai dai ban san yanda zanyi ba ganin ku manya bakuce komai ba.” “Shirun na dole ne Ibnati, bazaki gane babbar sarƙaƙiyar dake cikin masarautar nan ba ne. Amma tabbas akwai matsala, akwai kuma gagarumin al'amarin dake ɓoye amma yana son bayyana kansa a wannan gaɓar.....” Cikin zumuɗi Iffah tace, “Mamy minene shi dan ALLAH?”. “Humm Fareedah kinyi ƙarama da yawa ba yanzu ba. Ke dai kawai abinda nake so da ke shine ki taimaka ki bincika min idan Abni yana a gidan nan...” “To Mamy, amma dai zaiyi wuya tunda kunce idan yana cikin damuwa kulle kansa yakeyi baya kuma sauraren kowa. Sai nake ganin ni taya zai saurare ni”. Murmushi Daneen Ammarah tayi mai sauti. “Rashin saurarenmu bashi ke nufin kema bazai saurareki ba Ibnati. Ke dai gwada sa'arki mu gani”. Iffah dai ta jita ne kawai, amma sai bata sake musawa ba sukai sallama.....
★★.... ★.....
Miran Jasim ya sauke wayar dake a kunnensa bayan gama sauraren abokin wayar tasa, yanda fuskarsa ta canja daga farin cikin dake shimfiɗe a kanta kafin wayar yasa Miran Arshaan sake maida hankalinsa garesa. “Wani abu ya sake faruwa ne?”. “Zai dai faru”. Cewar Miran Jasim ɗin a fusace yana miƙewa. Miran Arshaan da maganar ta dakesa ya miƙe zumbur shima. “Ban gane mi kake son cewa ba Jasim Akh?”. Kamar bazai tanka masa ba sai kuma yaja kakkauran tsaki. “Harun Al-rashid ne dai akan waccan maganar banzar ta ranar, duk yabi ya tashi hankalinsa yana cigaba da damuna nima, tun abin bai tasiri a raina ba har ya fara, wai Barrister da suka bama aikin can kan ɗan iskan can ne ke cigaba da musu bayani dai kan Barrister Abdallah bai mutu ba dai da gaske.” “Wai suna nufin shi ya tabbatar da hakan kenan?”. “Abinda ke cazamun kai kenan, na rasa wane shirme ne kuma hakan? Taya wanda bomb ya tashi da shi ace bai mutu ba?”. “To amma fa kuma maganarsu fa abin a duba ce Jasim Akh. Dan koni naji shakku a randa bomb ɗin nan ya tashi amma jami'an tsaro suka tabbatar babu wani alamar an rasa rai......” “Amma shine kai shiru?!”. Miran Jasim ya katsesa a zafafe. “Mi kake so nayi bayan wanda nayi to? ina son ka tuna tun a ranar na kawo maka wannan zancen amma ka nuna min cewar zata iya yuwuwa ƙarfin tashin nakiyar ya cillashi wani waje ne shiyyasa basu gansa ba. A kuma shekaran jiya da suka kawo maganar na kuma ƙoƙarin maka nuni ka kalli zancensu a shirme”. Shima Miran Arshaan ɗin ya karɓa masa a nasa zafin. Shiru Miran Jasim yayi da dafe kansa yana murza goshinsa dan ya tuna tabbas anyi hakan. Amma wannan aikin na cikin gida da rashin sanin mi Tajwar Eshaan ke ciki ya ɗauke hankalinsa bai nutsu yayi nazari kan batunba kasancewar akwai abubuwa da yawa da bawai yana buɗema Miran Arshaan ɗin bane, kamar yanda shima Miran Arshaan ɗin ba komai yake yarda ya buɗe ma Miran Jasim ɗin ba. Sai dai a yanzu dukansu sun fahimci yin kuskure, dan haka kowanne ya ajiye ɓoyayyar manufarsa suka fuskanci juna. “Ni ina ganin in har an yarda da aikin Barrister ɗin nan shawararsa ba abar yardawa bace. Sannan dole ne fa mu gaggauta ganawa da yarinyar can in ba hakaba aikinmu zai iya buɗewa. Dan idan ya kasance Barrister Aas na raye bazai samu ɗaki bane ya kulle kansa domin hutu kaima ka sani”. Miran Jasim ya gyaɗa kai da faɗin, “Hakane maganarka na kan gaskiya. Yanzu minene abinyi?”. “Abinyi ɗaya ne bama Barrister Akeem damar shigewa gaba kafin kwana biyun nan na cikar aikinmu abar ƙasar nan da mutanen. Bayan ka haye karagar mulki shi kuma shegen duk inda yake zamu nemishi ne ya ɗan-ɗana kuɗarsa”. “Ina sake godema ALLAH da kasancewar ka kusa da ni, dan kana farkar da ni a duk sanda kaina ya shiga duhuwa ɗan uwana”. Murmushi Miran Arshaan ya saki a zahiri, a zuciya kam faɗi yake, (Banza ka gama cusamin ƙayar a rumbu na rufeta da ɗan boto ina daga kwance). Ɗaukar wayar Miran Jasim dai-dai da kammala wayar Iffah da Daneen Ammarah daga can......
★★.....
Tana ajiye wayar wani kiran ya sake shigowa, kamar zata share dan bata san number ɗin ba sai kuma dai ta ɗauka da tunanin ko Sir Ajmaal ne kasancewar a saƙonta na ƙarshe ta roƙesa idan ya gani ya kirata. Daga can aka amsa sallamarta kai tsaye, hakan ya sata Ciro wayar a kunenta ta kalla tamkar mai son gano muryar. Miran Jasim da kamar yana ganinta yay gyaran murya, hakan ya sata sake maida wayar. “Kina magana da Jasim Ibn Abdull-Majeed Aliy”. Kai tsaye Iffah ta ganesa, dan haka ta fara gaidashi da girmamawa. Hakan ya masa daɗi, dan yanda yake amsa mata da kulawa zai baka tabbaci. Shiru ne ya ɗan biyo bayan gaisuwar, kafin ya katsesa da faɗin, “Ibnati inata zaman jiran ji daga gareki amma shiru. Ko baki amince da abinda kika gani bane ba dai?”. Iffah da ke jin an taɓo mata inda ke mata ƙaiƙayi hawaye suka shiga rige-rigen sakko mata. Hannu tasa ta sharesu da ɗan jan hanci. “Ba yarda ne banyiba ranka ya daɗe, kawai dai zuciyata na kaikawo ne na son sanin dalilinka na yin hakan a gareni. Idan ban manta ba kai fa Ammi ne garesa, mizaisa ka zaɓeni sama da shi? A barshi ma zaka iya hakan kasancewar ka mai gaskiya ko ƙyamar abinda yake. Amma miyasa su na baya da aka rasa bakuyi wani yunƙuri ba sai ni a kaina bayan akwai ƴaƴan Tajwar mafi rinjaye a cikin wanda ya halaka?”. (Kaga ibilishiyar yarinya) ya ayyana a zuciyarsa. A zahiri kam sai yay gyaran murya cike da dattako yana kallon Miran Arshaan da shima ke sauraren komai. “Wato Ibnati duk yanda zan miki bayani a wayar nan ba lallai ki fahimta ba. Amma zan tura miki lokaci da adireshi mu haɗu zai fi”. Jimmm Iffah tayi kamar mai shakku, sai kuma ta nisa cikin gyaɗa kai tace, “Okay babu damuwa ina jira”. Daga haka sukai sallama kowa ransa na masa kaikawo...
★★....
Cikin ƴar dariya Miran Arshaan yace, “Amma shegiyar yarinyar nan fa da zata samu dama a masarautar nan ba ƙaramin hatsabibiya za'ai ba. Kaji murya cauy-cauy bata ko tsallaken kalma ga shegen wayo”. “Shiyyasa dolene tana kammala aikin nan a kaudata kawai, ai tunda har tana da ƙarfin halin shigowa masarautar nan da ƙudiri irin na kashe Shahan-shan dama nasan zamuga fiye da hakan tattare da ita. Irin waɗan nan yaran masu taurin zuciya a cikin mata basu da yawa, amma kuma kasancewar su mata ga mai mulki ba karamin ƙara samun power bane. Badan-badan ba babu abinda zai hanani tabbatar da ita abokiyar tafiyata. Dama yarinyar ga shegen ƙyau da ƙira tamkar ita ta zana kanta...” Ƙaramar dariya Miran Arshaan yay idonsa akan ɗan uwan nasa. “Wato dai Jasim Akh har yanzu bazaka canja ba, na ɗauka tuni ka jingine batun son matan nan naka kodan kujerar da ke gab da zama taka”. “Bazaka gane bane Arshaan Akh”. Miran Jasim ya faɗa yana tasa ƴar dariyar shima da komawa jikin kujera ya lafe ƙyaƙyƙyawar surar Iffah da bata wuce sa'ar autarsa ba na masa kaikawo. Shima dai Miran Arshaan ɗin hakance a ransa, dan tun randa suka haɗu da Iffah a wajen wasan takobi da Tajwar Eshaan yarinyar ta kasa barin ransa. Duk da dai shi yanzu kam ya ɗan rage bin mata tun aurensa da Jasrah. Humm masu karatu Bara na ɗan tsakura muku wata gulma dai karna wuce. (A baya ƙiyayyar ƴan ɗakin su Miran Jasim da Miran Arshaan a bayyane take fiye data ƴan ɗakinsu Tajwar Haysam (mahaifin Tajwar Eshaan kenan) amma a wasu shekaru bayan hawa mulkin Tajwar Haysam sai aka wayi gari sun ɗinke, ƙiyayyar da sukema juna ta koma ta ƙarƙashin ƙasa. Wannan haɗin kai nasu kuwa ya samo asaline a dalilin kasancewar halinsu da yazo ɗaya. Awani lokacin bikin al'ada kamar yanda duk suka saba sun baza yaransu samo musu yara matasan ƴammata masu jini a jika da basu gaza sha bakwai zuwa ashirin ba. Karku ɗauka da yardar yaran wai ake kai musu su, ko ɗaya, ta karfin tsiya za'a ɗaukeki bayan an shaƙa miki abu ko an yaudareki, bazaki tashi tsintar kanki ba sai a ɓoyayyen gurin da in zaki kwana dubu ihu babu mai jinki. Idan sun gama lalata rayuwar yaran kuma a jefar da su. Alokacin da labarin yaje ga Tajwar Haysam hankalinsa ya tashi, dan a shekarar an samu gawar yara ƴammata kusan biyar da waɗan da aka jikata, iya bincike kuma na jami'an tsaro ba'a sami komai ba. Da shekara ta dawo kuwa yasa tsatstsauran tsaro akan kaikawon mata fiye da maza, aka kuma sake sabon tsarin yanda bikin al'ada zai kasance. Ransu Miran Jasim ya ɓaci matuƙa, dan ƙarshe sai a yaran masarauta suka huce haushinsu ƴaƴan talakawa sun gagara ɗauka. Duk da ba tare suke aikatawa ba sai shirunsu yazo ɗaya a lokacin, har ya kasance yaransu dake sato musu ƴammatan sunyi haɗaka akan yarinya rigima ta kaure, kowanne ya sanarma ogansa, a zafafe Miran Jasim da Miran Jasim suka buƙaci sanin juna kowanne da tunanin shike da ƙarfin iko, sunko haɗun a yanayin da hantar kowanne ta kaɗu dan mamaki, amma ƙwallafa rai da kowannensu yayi akan yarinyar ya sasu amincewa juna yin tarayya da ita a tare Wa'iyazubillah 😭🤦. Haka suka haɗu suka lalata rayuwar yarinyar daga ƙarshe ta rasa ranta, a cikin masarautar suka bizneta har a yau kuma babu wanda ya san hakan sai ɗauka da ake yarinyar ta ɓata ne a taron bikin al'ada. Wannan shine sanadin zamowarsu inuwa ɗaya dan wannan ya basu ƙofar dinga kawoma juna mata, sai dai Miran Jasim yafi Miran Arshaan ƙwarewa a harkar, dan shi har order mata yomasa ake daga wasu ƙasashen ma🤦). Wanda ya gane na tayasa murna, wanda bai ganeba ya tsallake kawai😂🥱.
★★ BARRISTER ★★
Kamar yanda su Barrister ke zaman tsammani a yau sai ga kira daga Sayeed Harun Al-rashid, sun tattauna sosai ciki harda yarjewar fita da su Babiy zuwa wata ƙasa da kuma tsananta bincike wajen gani maɓoyar Barrister Abdallah Aas kamar yanda Barrister suka tsara musu. Abu mafi saka Barrister a ƙololuwar farin ciki shine damƙa fita da su Babiy ɗin a hannunsa, amma a zahiri sai ya nuna hakan ba aikinsa bane, shifa ya bada shawara ne kawai. A ɓangaren su sun nuna masa sufa sun yarda da shine, bayan shi kuma bazasu iya bama wani aikin ba gudun abinda zai je ya dawo. Bayan dai ɗan cigaba da tirjewa da ga ƙarshe Barrister ya amsa. Hakan ya musu daɗi suma, dan a nasu ɓangaren sun bashi aikinne domin ƙullama rayuwarsa, acewarsu koda ta tashi salin alin zasu zare hanunsu su barsa a ciki. Barrister da ya gama fahimtar su da ƙudirinsu duk da basu fito sun faɗa ba yay murmushi yana mai girgiza kansa da mamakin mutanen wannan duniya mai cike da rikici. “Son kai shine tushen rugujewar kawunan mu a wannan duniyar. Mai mulki kansa kawai ya sani. Mai arziƙi kansa kawai ya sani. Talaka kansa kawai ya sani. Mai ilimi kansa kawai ya sani. Jahili kansa kawai ya sani. Iyaye kansu kawai suka sani. Matasa kansu kawai suka sani. Yaro kansa kawai ya sani. Kowa akan buƙatarsa kansa kawai yake iya kallo. Duk shaƙuwa irin ta ma'aurata akan son kansu kowanne zai iya aikata komai. Duk shaƙuwa irin ta ɗa da iyaye akan son kansu zasu iya komai. A wannan duniyar yanzu samun cikakken amini sai an tona, ka gama yarda da mutum amma akan son kansa zai iya komai. Son kai dai! Son kai dai ya rabbi. Ƴan uwa son kai fa na kawo abubuwa da yawan gaske. Yana gina hassada a zuciya, ƙyashi, zalunci, raunana imani, ƙarya, munafunci, kai komai ma wlhy, hatta shirka tana iya shiga a cikin son kai batare da mun sani ba. Ya rabbi ka ganar damu gaskiya tun kan ta nisanta a kunnuwanmu da idanunmu.......✍️
(Wannan zance haka yake Barrister, ALLAH dai ka shiryar damu🤦).
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*
*DAUDAR GORA Billyn abdul*
*KI KULANI hafsat xoxo*
*A RUBUCE TAKE Huguma*
*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*
*IDON NERA Mamuh ghee*
_LITTAFI DAYA: 400_ _LITTAFI BIYU: 600_ _LITTAFI UKU: 800_ _LITTAFI HUDU :1000_ _LITTAFI BIYAR: 1200_
_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_
_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
MARYAM SANI ACCESS BANK 0022419171
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
09033181070
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09166221261
*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*
+227 96 09 67 63
Books biyar 1250CFA Books hudu 1050CFA Books uku 850CFA Books biyu 650CFA Bookk daya 450CFA
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨ (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)
𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻
*_48_*
...........Babu kwanciyar hankali gasu Kaka, dan har yanzu basu sami bakin zaren jin komai ba game da wadda aka rasa a cikin matan Shahan-shan. Ga tashin hankalin ɓatan Barrister dan sun je har gidansa amma a rufe alamar iyalansa ma dai basa nan. Acewar makwafta kuma dai anzo an kwashesune a cikin dare, yau kusan kwanaki takwas kenan. A lissafinsu kuma ya kama randa Barrister ya ɓata kenan. Zuciyar kaka ingizashi take kan abubuwa masu yawan gaske amma yana gocewa, dan duk tsanani yayi alƙawarin dogaro ga ALLAH majiɓincin al'amuran bayi a kowane tsanani da sauƙi. Kwanansa ɗaya ya juya ƙauyen Jumna, dan yasan ya baro su Iyyani a tashin hankali.
Ilai kuwa koda ya koma sai ya samesu a birkice, dan suma dai zuwa yanzu labarin halin da ƙasar ke ciki ya isa har kunnuwansu. Ummu tayi kuka har hawaye sun daina zuba. Ta gama sadakarwa ta rasa autarta itama. Dama ta jima da fidda rai ga su Babiy tuni. Kaka rasa ma mizai ce da su yayi, dan shima dai nasa kan a zafafe yake. Sai kawai ya shige ɗakinsa ya rufe kansa yana mai safa da marwa.......
★★..... BARRISTER ★★......
Da taimakon masu tsaronsa bisa umarnin ogansu da tun a ganin farko da yay masa bai sake ganinsa ba sai ta waya tun a yammacin ranar suka fara tattara abubuwan da zai basu kariya wajen fita da su Babiy duk da basu zo hanunsu ba har yanzu. Sai dai a daren ranar su Sayeed Harun Al-rashid sukai alkawarin danƙasu hannun Barrister, duk da ya nuna musu shifa yana jin tsoro su bari komai ya kammala sannan suka nuna masa suna tare da shi da kuma tsaro na musamman duk da kuwa ƙarya ne a baɗini. Zancen kam nasu ya tabbata, dan a daren ranar ƙarfe kusan tara na dare aka damƙa Babiy da Hanash a hannun Barrister Abdallah Aas matsayin Barrister Akeem da zukatansu su suka ɗauka. Daga gani kasan sun jigata matuƙa, sun rame sosai sunyi duhu. Ga rashin ƙarfin jiki da zaman waje ɗaya harma da ƙarancin abinci dana iska mai ƙyau. Hankalin Barrister ya tashi matuƙa, ya dinga share hawayen tausayinsu. Ya sake tabbatar da mutanen nan da suka kamashi mutanen kirki ne a yau, dan ana iso da su Babiy hanunsu sai ga likitoci, dan-da-nan suka duƙufa kansu da kulawa kai kace dama a shirye suke da hakan.......
★★..... MASARAUTA ★★.....
Duk da ƙarancin shekarunta ALLAH ya bata basira irinta masu hangen nesa. Tun bayan gama wayarta da Miran Jasim zuciyarta bata aminta da yarda su gana fuska da fuska ba. Dan haka ana idar da sallar magrib ta tura masa saƙo kamar haka duk da ita ba sallar zatai ba tana fashi. _Na amince mu tattauna, sai dai bata haɗuwa ba, muyi magana ta video call._ Miran Jasim ya karanta saƙon yafi sau ashirin, takaici kam ba'a magana ga ɗunbin mamakin basirar ƴar ficikar yarinyar. A take ransa duk ya jagule, ga boka Barbushi ya tabbatar masa haɗuwa da yarinyar fuska da fuska yafi fa'ida. Dan kwarjininsa da suddabaran da ya basu zai sakamata tsoronsa mai tsanani ya dinga yanda yaso da ita har zuwa sanda itama zasu ɓaddata bayan ta cika musu aikinsu. Gashi yanzu guri ya ƙure, bazai yiwu masa ba zuwa ga Barbushi ɗin dan zai iya rasa wannan damar da bokan nasu ya tabbatar musu itace ranarsu mafi Sa'a akan yarinyar kasancewar tana fashin salla, tana kuma cikin ruɗanin da ba komai yake iya banbancewa yanda ya kamata ba zasu iya sarrafata a duk yanda sukaso musamman akan Shahan-shan. Duk da sallar isha'i data gama gabatowa haka ya miƙe ya fice a masallacin bayan yayma Miran Arshaan alama da ido. Bai jima da fita ba kuwa yabi bayansa....
“ALLAH yasa dai lafiya na ganka duk a wani birkice?”. Miran Jasim ya sauke idonsa akan Miran Arshaan mai maganar yana mai jan tsaki. “Wane kwanciyar hankaline da ni inba gani nai komai ya daidaita ba Arshaan. Yanzu ma ƴar iskar yarinyar nan ce wai fa ta turamin text message bata yarda mu haɗu fuska da fuska ba sai dai video call”. “What! Waini wace irin hatsabibiyar yarinya ce wannan? Nama fahimci kallon sa'aninta take mana”. “Ka barta karka damu, zata yabama aya zaƙinta ta dai gama mana aikinmu. Anan zata gane ko wanda ya ajiyeta a gidan bai isa ba balle ita karamar halitta. Ni yanzu damuwata ma shine Barbushi ya tabbar mana da wannan ranar ta sa'a, haɗuwarmu kuma fuska da fuska wani babban cigabane garemu.” “Komai ya kwaɓe kam, sai dai ni a wannan gaɓar ina masa kallon mai sauƙi. Kaga dai a yanzu bamu da isashen lokacin komawa wajen Barbushi, na biyu barin wannan damar ta wuce a garemu kuskure ne. Dan haka kawai mubita a yanda take so ɗin, da sassafe mu nufi Barbushi”. Ajiyar zuciya mai nauyi Miran Jasim ya sauke domin gamsuwa da zancen Miran Arshaan ɗin, daga haka basu koma masallacin ba sukai zaman kulla yanda zasu tunkari Iffah bayan sun tura mata saƙon amincewa ayi video call ɗin.
*_10:30pm_*
Ƙarfe goma da rabi na dare agogon ƙasar Iffah zaune gaban laptop ɗin ta, sanye take cikin suturar ta mai sirrinta jiki, iya zagayen ƙyaƙykywar fuskarta kawai ake iya gani. Tayi fayau ga mai kallo baka iya ganin komai sai damuwa da tsantsar ƙuruciyarta. Cikin girmamawa ta gaida dattijan guda biyu dake a fuskar lap-top ɗin tata. Miran Jasim da Miran Arshaan suka amsa mata da kulawa da nuna tausayawa tsantsa a fuskokinsu. Ita dai idanunta a rissine, dan tun kallo ɗaya datai musu bata sake yarda ta ƙara ba. Miran Jasim yay ƴar gyaran murya da fara magana bayan gaisuwar tasu. “Ibnati mu mun sauke nauyin dake kammu naki, abinda kika yanke kawai muke buƙatar ji domin tsallakar da rayuwarki data ƴan baya. Dan a yanzu mun shirya tsaf ba tsafi ba ko bataliyar ifiritai Eshaan zai sauke a kammu domin danne cewarmu bazamu taɓa yin shiru ba”. Iffah ta jinjina kai a hankali da faɗin, “Uncles naji daɗin hakan, kuma tun farko dama haka ya kamata ku kasance, duk da dai nasan bai zama lallai kuji irin zafin da iyayenmu sukaji ba. Amma a yanzu daya fara taɓaku gashi kun zaburo. Duk da haka bazamu ƙi karɓar taimakonku ba, dan a yanzu bani da wani abu dana tsana sama da shi, a shirye nake kuma na zama ajalinsa koda nima zan rasa nawa ranne. Sai dai ina son dan ALLAH uncle ka faɗamin gaskiya taya ka samu wannan videon? Ta ya kuma kasan na cikin videon nada alaƙa da ni ne? Miyasa kuke son taimaka mini? Miyasa duk da kun san yana kan rashin dai-dai baku taɓa wani yunƙuri ba a baya sai yanzu?”. Kallon juna Miran Arshaan da Miran Jasim sukai kowanne ransa na susa da mamakin tsaurin idon wannan yarinya da sukema kallon hatsabibiya. Amma a zahiri sai Miran Jasim yaja ajiyar zuciya ya fesar cikin ƙoƙarin danne razanin da tambayoyinta suke neman jefasa. “Ibnati duk wannan ai na abin mamaki bane da har zai saka miki shakku, amma tunda kina son sani yanzu zakiji komai. Wannan video ɗin da kike gani na samosa ne a system ɗin Eshaan, bakuna shi kaɗai bane ba. Akwai ire-irensa da yawa harma dana yanda aka hallaka matansa na baya. Ina haɗasu ne domin miƙasa kotu a kwatarma masu hakki hakkinsu duk da ina fargabar ƙarfin iko irin na Shahan-shan bazai bari a hukunta shin ba kasancewar komai sai da say ɗinsa ke gudana a ƙasar ruman baki ɗaya. Sanin alaƙarki da wannan video kuwa ta samune duk a dalilin bibiyar tasa, sai dai bamu tabbatar ke bace ba sai a ranar da kika samesa tare da Arshaan Akh suna wasan takkubba. Sannan kasa tunkararsa a baya Ibnati bazaki gane ba, ƙarfin ikon Shahan-shan fa bana wasa bane ga kowa....” “Tabbas hakane” Miran Arshaan ya amshe zancen. Batare daya jira cewar Iffah ba ya cigaba da faɗin, “Idan baki manta ba bayan kin basa shayi ya koma gefene yana kallo cikin masarauta, nima kina bani kuma na koma kusa da shi ina mai yabama tarbiyyarki da tabbatar masa yayi dace mace tagari data dace da shi a yanzu. Buɗar bakinsa sai ya sake tsaki da faɗin, “Tukunna dai, ai shi har yanzu matar da zai rayu da ita bata iso ba. Naji mamaki harna tambayesa ba'asin hakan amma sai bai tankani ba kin sanshi da girman kai. Zancen ya tsaya min a rai nazo na sami Jasim Akh da maganar, shine fa ya duƙufa bincike harya samu ganawa da kakanki da ke a ƙauyen Jumna”. Sosai Iffah ta zabura da jin sun gana da kaka harta ɗago ido ta na kallonsu. Tabbas sihiri gaskiya ne, kuma yakanci kowama tunda har yaci ma'aikin ALLAH. A take wani abu mai sanyi ya dinga shiga jikin Iffah tamkar ana kwararashi cikin jininta. Hawaye ne suka silalo a idonta ta buɗe baki a hankali ta furta “Tabbas zan kashesa da hannuna, zan kashesa da dafin maciji na gaskiya kamar yanda yake halaka mutane dana tsafi. Nayi alkawarin yanda ya wargaza min ahali nima sai na wargaza rayuwarsa..” Miran Arshaan da Miran Jasim suka kalli juna sukai murmushi. “Zako mu baki dukkan gudunmawar da kike buƙata Ibnati. Tare da kariya ta musamman ga duk wanda zai iya kawo miki hari, balle ma a yanzu abinda zakiyi sai dai ya ƙara kawo miki ɗaukaka dan irinki ƙasar ruman ke nema. Mi kike buƙata a yanzu?”. Kai tsaye ta amsa da cewar, “Dafin maciji mai matuƙar haɗari”. “Zako ki sami na macizai ma ba maciji kawai ba. Ki saurari saƙo zuwa safiyar gobe. Mun barki lafiya”.
Wani irin kuka mai taɓa zuciya Iffah ta saki, a hankali ta zame takai kwance kanta da yay mata nauyi na sara mata. Gaba ɗaya duniyar tai mata dummm bata gane komai, burinta kawai shine ta ɓatar da Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed. Gawarsa kawai tafi bukatar gani kwance a ƙasa fiye da komai. So take taga ahalinsa na kuka fiye da wanda sukai a dalilin rasa ƴan uwansu saboda son kansa. Haka ta kwana a wani irin bahagon yanayin da bazata iya koda tunawa ba. Ita bamai barci ba ita ba ido biyu ba, ita ba matacciya ba ita ba mai rai ba gadai tanan. Duk da tana fashin salla ana kiran salla ta miƙe, bayi ta shiga ta tsaftace jikinta duk da babu wani ƙazanta tattare da ita, tana ƙoƙarin naɗe gashinta daya ɗan warware takeji kamar magana a ƙofar ɗakin nata. Cikin shakku ta gyara rigar wankar jikinta ta nufi ƙofa ta buɗe. Da mamaki take kallon amintacciyar hadimarta mai suna Abal dake a durƙushe hanunta ɗauke da ƙyakywan bowl. Da sauri Abal takai ƙasa tana gaidata. Batare da Iffah ta amsa ba ta ɗaga bakinta da yay mata nauyi da ƙyar tace, “Lafiya.....?” “Lafiya Lau ya Zawjata-almilk. Saƙone daga sashen mai Babban ɗaki”. Hakan ya ɗan saka Iffah a shakku da mamaki, amma sai bakinta yay mata nauyi bata iya ta sake cewa komai ba ta amshi tambulan ɗin mai ɗauke da sabuwar madara fara ƙal. Idanu Iffah ta tsurama madarar wani shawa'ar shanta na fusgarta. Amma sai ta dake ta ajiye ta da nufin sai ta gama kimtsawa tasha ko kaɗanne kaffin ta sake komawa barci. Harta nufi kayan data fiddo zata saka kira ya shigo wayarta. Ruɗewa tai dan abune da bai taɓa faruwa da ita ba, kofa sallar asubahi ba ayi ba. Kamar wadda ake ingizawa da remote ta ɗauka wayar, ganin Miran Jasim ta amsa da tsumar jiki tana gaisheshi kai kace yana a gabanta ne. Bai amsata ba, sai ma umarni daya bata cikin kakkausar murya saɓanin wadda yake mata magana da ita a baya. “Wannan madara ce mai ɗauke da dafin macizai masu haɗarin gaske har guda biyar, daga yanzu zuwa ƙarfe takwas na safiya ina buƙatar jin kukan mutuwa. Kukan mutuwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed nake buƙatar ji har gadon barci na ta dalilinki”. “An gama ranka ya daɗe”. Iffah ta amsa da rawar murya hawaye na ciko mata ido ga girmamawa har tana rissinawa kamar tana a gabamsa.........✍️
*_🤦ALLAH sarki Iffah baki shike yanka wuya. Kin ɗauka niyya badan zuciyarki zata iya ba a zahiri, gashi masu babban burin sharri zasuyi jifa da hannayenki batare da kin san illar hakan ba a gareki._*
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*