Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul - Chapter 34
Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul Chapter 34: Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul Chapter 34. Ya kai mintuna goma yana kallon yanda masu tsaron…
4,498 words
Ya kai mintuna goma yana kallon yanda masu tsaron kurkukun ke kaiwa da komowa, kowanne kuma da makami tare da shi. Ga haske ƙal tamkar rana dan ko allura ka yar ka duka ka ɗauka abinka batare da ka nema ba. Bugawar ƙaton agogon masarautar da ake iya gani tako wace kusurwar daular ta ruman ya sashi jan numfashi a sarƙe. Karfe uku dai-dai kenan, awa ɗaya garesa kacal na kammala wannan aikin. Dan huɗu nayi zaka fara jin motsin hadimai na tashi domin fara ayyukansu, musamman masu share-share da goge-goge. Zaman ɗammarar ƙugunsa ya gyara da ƙyau, hakama hular kansa kalar kayan jikinsa na ainahin amintattun jami'an dake cikin sashen Tajwar Eshaan. Ya ƙara saita kansa da ƙyau cikin dakewa ya tunkaresu hannunsa ɗauke da babbar jaka. Duk da sanin matsayin masu waɗan nan kayan a gidan gaba ɗaya sukai masa ca. Bai nuna razana ba duk da zuciyarsa na faman dukan dari-ɗari ne. Cikin sake matse kansa ya sara musu alamar girmamawa yana mai miƙa musu I'd card ɗinsa. “Umarnine da ga shugaba, zan sada kayan nan ga Zawjata-almilk domin sakasu a gobe idan zata fita, na kwashe na dattin dake tare da ita”. Kallonsa suke kawai suna sake kallon katin domin tantance shi ɗinne a hoton kokuwa. Sai dai hoton ya ɗanyi duhu, duk da kuma hasken wajen dai rana bazata taɓa zama ɗaya da hasken lantarki ba. A dake ya sake faɗin, “Ba tantancewar kaɗai ake buƙata ba. Ya kamata ku kira sashen shugaba domin tabbatarwa, wannan shine cikar aikin masu tsaro”. Kalamansa sun ɗanyi tasiri garesu, sai dai duk da haka wani ya tubure akan sai ya fara zuwa ya tabbatar bawai kiran waya ba. Dan ko ƙuda an tabbatar musu su kasance masu himma wajen hanashi gittawa zuwa inda Iffah take sai da ƙwaƙwƙwaran dalili. Tsabar ƙarfin hali na hadimin nan, babu ko nuna gezau ya bada goyon baya. Hakan ya ƙara saka sauran jin sun yarda da shi, sai dai wancan ɗin babu alamar hakan. Sai ma tabbatar musu da yay su cigaba da tsaresa zaije ya dawo”. Tsahon mintuna goma da tafiyarsa sai gashi ya dawo, batare da yace komai ba yay masa nuni da ya shiga. Wata irin wawuyar ajiyar zuciya ya saki da ɗan kashe ido wa jami'in da a yanzu yake ta faman sinne kai kamar wani munafuki. Sauran basu damuba dan su dama sun aminta tun dazun, dan haka ya wuce hankali kwance.
Tana tsaka da ɓarawon barcin da ya sace ta bayan ta idar da sallar da take tsaiwar yi duk dare domin miƙa kukanta ga UBANGIJI taji kamar numfashinta na fita a fisge, firgigit ta farka da ƙoƙarin kai hannunta saman hancinta, sai dai aikin gama ya gama dan ya riga ya shaƙa mata abinda ke cikin handkherciff ɗin. Duk yanda taso sake yunƙurawa hakan ya gagara sai ma jikinta dake saki baki ɗaya. Daga haka bata sake sanin inda kanta yake ba. Jikinsa na ɗan ɓari ya sakata a babbar jakar hanun nasa tare da zuge zip ɗin. Bai tsaya ɓata lokaci ba ya saɓeta kasancewarsa ƙaƙƙarfan mutum babu alamar da zai tabbatar maka mutum ya ɗakko. Gashi dama Iffah ta rame sosai duk da dama ba wata mai jiki bace can. Sai dai kuma duk da hakan ƙarfin haline kawai irin na masu busashshiyar zuciya dan sumar da itan da yay jikinta duk ya saki ta sake nauyi. Sai da yay musu sallama da sanar da su ya kwaso kayan dattin wajenta ne bisa umarnin Tajwar Eshaan sannan ya wuce.........✍️
Hummm
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*
*DAUDAR GORA Billyn abdul*
*KI KULANI hafsat xoxo*
*A RUBUCE TAKE Huguma*
*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*
*IDON NERA Mamuh ghee*
_LITTAFI DAYA: 400_ _LITTAFI BIYU: 600_ _LITTAFI UKU: 800_ _LITTAFI HUDU :1000_ _LITTAFI BIYAR: 1200_
_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_
_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
MARYAM SANI ACCESS BANK 0022419171
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
09033181070
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09166221261
*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*
+227 96 09 67 63
Books biyar 1250CFA Books hudu 1050CFA Books uku 850CFA Books biyu 650CFA Bookk daya 450CFA
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨ (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)
𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (16)
........Kamar yanda al'adar take duk wani hadimi da karfe huɗu tayi zai fara gudanar da aikinsa in har yana cikin hadimai masu kula da tsaftar masarautar. Musamman ma masu shara da tsaftace irinsu garden barga da sauransu. Yauma hakance ta kasance, hadiman duk sun tashi domin kama ayyukansu, kowa ƙoƙarinsa ya kammala kafin sallar asubahi. Swimming pool ɗin garden ɗin gabashi dake kamar ta bayan sashen Shahan-shan gab, babban swimming ne da masu aikin tsaftace ruwan cikinsa suka kasance har su huɗu, kowace kusurwa da mai gyarawa. Sukan saka raga domin tace duk wani datti daya shiga ciki, tare da sake ingantashi ya fita fes yana bada kalar blue mai ɗaukar ido ko daga nesa. Aikinsu suka fara a nutse, tare da yima juna magana jefi-jefi, can wanda ke a bangon yamma ya zabura tare da ƙwala ƙarar da tai amsa kuwwa zuwa kunnen duk hadiman dake aikinsu suma gab da wajen. A take ƴan uwansa sukayi kansa suna tambayar lafiya. Jikinsa na rawar karkarwa yay musu nuni da cikin swimming pool, kallonsu suka maida wajen zukatansu na dukan tara-tara, dan basu mance tsautsayin da ya taɓa faruwa ba da har yay sanadin rasa ran Miran Nayyar (ƙani ga Marigayi Tajwar Haysam). A tare suma suka zabura jikkunansu na sake shiga mazarin rawa. “Tabbas mutum ne mun shiga uku!!”. Wani ya faɗa a cikin sauran hadiman da ihun wancan ya jawo hankalinsu. Sake daburcewa duk sukayi, an rasa wanda zai yi hoɓɓosan kai agaji ko neman agajin, gashi motsin da suke gani anayi a cikin ruwan ya fara lafawa alamar wanda ke cikin yana sake ƙasa. Wani da yazo kusan a ƙarshe-ƙarshe ne ya zabura zai afka, da sauri wani ya rikoshi yana girgiza kansa. “Wannan bashine mafita ba, ayi azamar sanar da jami'ai gudun kar mu aikata kuskure tunda bamu san wanene ba. Duk wanda ya kai shekara arba'in da biyar baya anan yasan miya faru a dalilin irin wannan kuskuran”. Sun gamsu da jawabinsa, duk da wasu labari kawai sukaji dan sannan girmansu bai kai ba, wasu ma ba'a haifesu ba.
Cikin ƙanƙanin lokaci jami'ai suka iso wajen, hakama mazan masarautar dake ƙoƙarin tafiya masallaci sallar asubahi. Rashin sanin wanene a ciki yasa shugaban jami'an ya hana a shiga kai tsaye, sai dai tuni an gama dasa na'urorin da zasu iya fiddo koma wanene. (Dan tun rasa Miran Nayyar da masarautar tayi Tajwar Abdul-majeed ya tanadar da na'urorin domin tsaro). Tayi ƙasa sosai ga swimming pool ɗin da girma sosai, cikinsa kuma anyi style kamar wani sashe-sashe da suffar ado. Hakan yasa akaja lokaci mai tsawo kafin a samu nasarar samota, zuwa lokacin har an idar da sallar asuba. Kasancewar tsirarun mutane da Tajwar Eshaan ne kawai suka sami damar yin sallar asubahin ya bada mamaki har Tajwar Eshaan ɗin yasa akai tambayar ko wani abu na faruwa ne haka?. Waɗanda suke a masallacin duk basu sani ba, dan haka suka tabbatar da babu komai, sai dai ko makarace ta kawo hakan. Baiji ya gamsu ba, amma sai bai musa ba ya miƙe ya fito Sayeed Fayzul-haq da ya zama kamar amintaccensa yanzu biye da shi. A falo Sayeed ya dakata, shi kuma ya nufi bedroom domin shiryawa ya shiga grm. Dai-dai nan kiran waya ya shigo ta landline. Tsayawa yay cak, dan duk kiran da zai iya shiga a wannan wayar direct dole mai muhimmanci ne da shi ya shafa, kuma kai tsaye ake bukatar magana da shi. Tana gab da tsinkewa ya juyo, idanunsa ya sauke akan sayeed, cike da ƙasaita yay masa nuni da wayar alamar ya ɗaga. Cikin bin umarni sayeed ya ɗaga wayar, shiru kusan na minti ɗaya ya janye a ɗan zabure yana kife wayar. “ALLAH ya ƙarama shugaban sarakuna da al'ummar ƙasar ruman baki ɗaya lafiya da tsohon rai mai albarka. Kirane da ga shugaban jami'an tsaro. An samu accident ne a cikin swimming pool ɗin babban garden, mace ce kuma, ana kyautata zaton bata cikin hadimai, gashi tana buƙatar taimakon gaggawa da basu da hurumin taɓata su”. Ƙirjinsa ne yay wata irin mummunar bugawa, mafarkinsa na gabanin asubahi da har yasa shi ƴar makara ya shiga maimaita kansa a kwanyarsa. Ƙoƙarin basarwa yay kamar yanda ya saba, sai dai zuciyarsa taƙi bashi goyon bayan bada umarnin waninsa yaje. Har ya daga ƙafarsa da niyyar cigaba da tafiya hakan ya gagara, idonsa ya rumtse da ɗan ƙarfi ya buɗe, batare da yace uffan ba ya nufi ɓoyayyar hanyar da zata sadashi da babban garden ɗin. Sosai mamaki ya kama Sayeed Fayzul-haq, sai dai bashi da hurumin tambaya dan haka ya take masa baya da sassarfa...
★Cikin rawar jiki hadiman wajen suka shiga zubewa bisa gwiwunsu ganin mai ruman ɗin ne fa da kansa. Yayinda jami'an suma duk suka risinar da kawuna. Taku yake a nutse cike da ƙasaitar da ke tabbatar da kasancewarsa bajimin namiji da ko a cikin jaruman gwarazo ne. A ƙirjinsa bugu yake kamar zai hantsilo waje, a zahirinsa kuwa babu mai iya fahimtar komai koda daga fuskarsa ne. A hankali matan da ke zagaye da ita suka dare, dan sune suka sanar cewar Zawjata-almilk ce, shugaban jami'ai ya faɗa a rufe ne saboda shakkar isar da saƙon kai tsaye ga Shahan-shan ɗin. Suma kawunansu duk a rissine suke, cikin rawar murya ɗaya daga cikin matan data kasance amintacciyar hadima mai ƴanci dake da alhakin kaiwa da komowar duk wani abinda ya shafi Shahan-shan da matansa ko makusancinsa (kamar jakadiya a ƙasar hausa) ta ƙarasa zubewa cikin gurfana, “ALLAH ya huci zuciyar shugaban sarakunan ƙasar ruman da al'ummar cikinta. Umarninka muke jira domin taɓa Zawjata-almilk, dan rayuwarta zata iya salwanta.....” Idanunsa da ke ma Iffah kallon ƙasa-ƙasa ya ɗan lumshe, cikin jarumtar son danne zillon da zuciyar ke masa ya ɗaga ƙafarsa da ƙyar yay taku ɗaya biyu da ya sake saka matan darewa cikin rawar jiki mamaki na neman halakasu ganin gadan-gadan Iffah ya nufa. Dai-dai yana ƙarasawa ɗaya da ga cikin jami'an wajen da yay wata irin zabura ya sunkuto ɗaya daga kujerun dake a wajen ya dire masa, da sauri aka ɗaura hiramin sayeed Fayzul-haq daya fincike a kansa. A hankali ya kai zaune shanyayyun idanunsa na sake tar-tar a kanta cikin ɗan hasken da garin ya fara. An lulluɓe jikinta da mayafi kasanwar kayanta dake jiƙe zai iya bayyana ainahinta, kallon kusan sakanni biyar yaja numfashi ya fesar yana mai kai yatsunsa biyu saman hancinta, babu alamar numfashi, ɗaukewa yay ya maida a jijiyar wuyanta, nan ma bata harbawa, cikin jarumta da zaburo da sanyin da ke sauka a jijiyoyin jikinsa ya ɗan ɗaga mayafin ya ciro hanunta. A kan tattausan nasa ya ɗaura yana mai ɗaura yatsansa akan jijiyar tsintsiyar hannun ya lumshe ido. Da sauri ya buɗe sai dai ga mai kallo bazai taɓa fahimta ba. Dan a nitse yake sarrafa hannunsa dake motsi kawai a jikin nasa. Shugaban jami'ai da Sayeed Fayzul-haq dake ɗan satar kallonsa kasancewar duk wani hadimi da sauran jami'an tun zamansa a kujerar duk sun juya bayansu suka ɗan waro ido ganin ya kusanta ƙyaƙyƙyawar fuskarsa da ta Iffah har hancinansu na gogar juna. Ya lumshe idanu tare da sauke tausasan lips ɗinsa kan nata, ai dole suma suka sake rissinar da kawunansu duk da sun san bawani abu zai yi ba illa bata taimakon gaggawa. Shiko da bai ma san sunayi ba da harshensa yay nasarar raba lips ɗinta da haƙoranta dage datse cikin na juna ya turashi cikin bakin nata, sai kuma ya kai yatsunsa biyu kan hancinta ya matse. Iskar bakinsa mai ƙarfi ya hura mata cike da salon ƙwarewarsa akan iya ruwa da ceton duk wanda ya samu accident a dalilinsa. Da wani irin ƙarfi ta zaburo ƙirjinta na ballaƙowa sai ruwan bakinta bulla a kan fuskarsa. Idanu ya lumshe a hankali yana mai sauke wata irin nannauyar ajiyar zuciya daga cikin maƙoshinsa da ɗan jan fuskarsa data wanke da ruwan bakinta. Cikin sauri Ama. Ta miƙama Sayeed ƙaramin towel cikin wanda ke hanunta, amsa yay ya matsa kusa da Tajwar Eshaan kansa a rissine ya miƙa masa. Bai motsa ba idonsa a kanta tana cigaba da amayo ruwan saboda ɗan danna ƙirjinta da ya cigaba dayi har tsawon kusan mintuna biyu, kafin ya miƙama sayeed hannu batare da ya juyi ba ya amsa. Kan fuskarsa ya kai ya tsane ruwan da tuni yama gangagare har wuyansa har ya ɗan jiƙa jallabiyar jikinsa mai tsananin ƙyau da ɗaukar idanun kai kallo. “Duvet”. Ya faɗa a hankali ganin jikinta ya fara karkarwa har ɗan gadon agajin gaggawar da aka daurata na ɗan jijigawa. A cikin ƙanƙanin lokaci aka kawo, yanzu ma da kansa ya rufa mata. Sannan ya miƙe gaba ɗayansa yana ɗan duban Sayeed. “A maidata gareni”. Ya faɗa can ƙasan maƙoshi tamkar bashine yay maganar ba yana ƙoƙarin barin wajen. Sai yanzu ya lura da cikar garden ɗin da duk masu faɗa ajin masarautar a wajen. Idonsa ne ya sauka kan Malikat Bushirat da Malikat Haseenat da ke kusan tare da juna. Dan Daneen Ammarah da Malikat Ashwaq ne suka ɗan shiga tsakaninsu. Ɗauke idanun nasa yay ya cigaba da takunsa na bajimta. Dan kowa a wajen kansa a rissine yake har su Malikat Bushirat ɗin kansu domin tabbatar da girman da ALLAH ya bashi na shugabanci.... A gaban idon kowa aka wuce da Iffah sashen Tajwar Eshaan ɗin tare da Doctor da zata sake bata taimakon gaggawa, a hankali ƙus-ƙus ya fara tashi a wajen kowa na jimanta al'amarin da jinjina faruwarsa kasancewar duk wanda ya kwana ya tashi a gidan yasan Iffah na kurkuku ne, kuma a yau za'ai zaman shari'a ta biyu, hakama abinda ta faɗa a zaman waccan shari'ar kowa ya jisa. Sai dalilin faruwar al'amarin yau ya saka zukata fara rarrabuwa a kan al'amarin ta, masu ganin a wancan zaman shari'ar ta faɗi waɗan can kalamanne danta kuɓutar da kanta ko sharri, sai a yanzu suke ganinfa akwai ƙamshin gaskiya tunda a karo na biyu kenan ana yunƙurin kasheta. Idan babu rami to miya kawo rami? Wannan shine tambayarsu...........✍️
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*
*DAUDAR GORA Billyn abdul*
*KI KULANI hafsat xoxo*
*A RUBUCE TAKE Huguma*
*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*
*IDON NERA Mamuh ghee*
_LITTAFI DAYA: 400_ _LITTAFI BIYU: 600_ _LITTAFI UKU: 800_ _LITTAFI HUDU :1000_ _LITTAFI BIYAR: 1200_
_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_
_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
MARYAM SANI ACCESS BANK 0022419171
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
09033181070
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09166221261
*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*
+227 96 09 67 63
Books biyar 1250CFA Books hudu 1050CFA Books uku 850CFA Books biyu 650CFA Bookk daya 450CFA
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨ (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)
𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (17)
........Samun gawar ɗaya daga cikin jami'an dake tsare da Iffah, da ɗaya daga cikin na sashen Tajwar Eshaan ya sake tabbatar da akwai ƙullalliya. Dan alamomi na bayyane sun nuna an fara kashe jam'in sashen Tajwar Eshaan ɗin ne akai amfani da kayansa zuwa kurkuku, sai kuma gawar jami'in dake cikin masu tsaron Iffah da bayanin sauran jami'an ya tabbatar da koma miye a lokacin da yace zaije ya binciko gaskiyar zuwan jami'in da yace yazo kawoma Zawjata-almilk kaya ne. Sarƙa-sarƙar ta ɗaure kan mutane matuƙa da yanda tama faru, sai dai jami'an sun tabbatar da sai sun gano koma wanene anan kusa cike kuma da alwashi.....
★★.... ★....
Tunda akace ta farfaɗo hankalin duk masu hannu akan al'amarin ke'a tashe musamman ta-ƙurya da hadimin da yay aikin. Tashin hankalin ta-ƙurya rashin mutuwar Iffah ne, dan tanada hanyoyin da zatabi na ɓatar da hadimin cikin sauƙi, kai koda ta barsa da rayuwarsa ma bai san ita wacece ba. Amma kasancewar cigaba da rayuwar Iffah na nufin MATSALARTA na nan har yau da gobe dama ranar da bata san iyaka ba. Idan har tace kuma zata sake wani yinƙuri a yanzu akwai matsala, mafitarta ɗaya ce sake komawa ga UWA ɗin da take hangen ta gaza a baya. Wasu irin zafafan hawaye ne masu raɗaɗi suka shiga bin kumatunta, ɗuminsu kawai taji batare da tasan ta farasu ba. Hakan ya ƙara ƙona ranta dan akan ƴar yarinyar data raina hawayenta na zuba a karo na babu adadi, abinda bai taɓa faruwa da ita ba kasancewarta mai nasara ga duk abinda ta sanya gaba. Shawarar da zuciyarta ta bata akan sake kiranyen uwa ya sata miƙewa. Surkullen jiya ta shiga fara maimaitawa. Tsahon lokaci har ta fidda rai a yanzu ma sautin mummunar dariyar uwa ta fara karaɗe ɗakin. Dariya ta tsaho lokaci babu alamar za'a daina kafin uwa ta bayyana a gabanta. “Ashe k! ƙaramar mara kunyace ta-ƙurya. Ashe baki shirya yaƙin ba kika yanki filin yinsa ba! Ashe b......” “Tuba nake Uwa mai share kukan masu kuka. Nayi kuskure a gafarceni bazan sake ba. Ni mai biyayyace ga umarninki a koda yaushe. Wannan ma saɓanin fahimta aka samu”. Shiru kamar uwa bazata tanka ba, sai kuma ta hura mummunan hancinta dayin ƙwafa. “Dalilai biyu zasu sa na miki afuwa ta-ƙurya. Baki taɓa saɓama umarninmu ba sai a wannan karon. Na biyu darajar wannan masarautar da kike ci. Kije ki kalmashe bakin zaren aikinmu na ƙarshe, dan aikinki na gab da buɗewa. Ki kuma kiyayi kaima yarinyar nan hari kai tsaye, dan duk yanda kike tunanin zaki iya a kanta ta waɗan nan hanyoyin al'amarinta ya fi ƙarfin nan. A yanzu haka Ajlaan ya fara shinshinar ta. Kuma komai zai iya faruwa, dan muna a gaɓar da zai iya kashe ƙishinsa kanta a yanzun, babu makawa magajin kujerar daular ruman na kusanto duniya kenan.....” Zabura ta-ƙurya tai jikinta na matuƙar rawa, sai wani irin rawa da lips ɗin ta keyi suma tama gagara furta abinda ke bakinta tsabar shiga tashin hankali. Uwa ta miƙa mata hoto cikin bada umarni. “Itace muke buƙata ta zama uwar Miran mai jiran gado, ki gaggauta, ki gaggauta tabbatar da ita cikin masarautar nan matsayin Zawjata-almilk daga nan zuwa ƙanƙanin lokaci. Inba haka ba kiyi kuka da kanki ta-ƙurya! Kuyi kuka da kanki!! hahaha!! hahahah!! hhhhhh!!!!!”. Ta ɓace ɓat sautin mummunar dariyarta na amsa kuwwa cikin ɗakin kai kace duk masarautar za'a iya jinta...
★★....
“Wannan na sake tabbatar mana da ƙamshin gaskiya akan yarinyar nan Mammah”. Daneen Ammarah ta faɗa cikin sanyin murya da jimamin abinda ya faru ya haddasa mata. Numfashi mai nauyi Malikat Haseenat ta sauke, kamar bazatace komai ba sai kuma ta dubi ɗiyar tata. “Akwai al'amarin dake tare da yarinyar mai girma da ko iyayenta bana jin sun san da shi tattare da ita ba. Inaji a jikina a dalilinta komai na gab da buɗewa a wannan masarautar”. Cikin nuna mamaki Daneen Ammarah ta ce, “Babban al'amari kuma Mammah? Kamar wane iri kenan?”. A karo na farko Malikat Haseenat ta saki murmushi mai ƙayatarwa, batare da tace komai ba ta danna kekenta yay gaba. Da kallo Daneen Ammarah ta bita baki sake, ita kam wani lokacin Mammah na hargitsa mata tunani da sakata a wasiwasi gaskiya.....
★★....
“Idan har ya kasance bakai bane kamar yanda ka faɗa to wanene kenan? Dama da gaske kamar yanda muke zargi bayan mu akwai masu harar rayuwar yarinyar nan kenan akwai ɗin?”. “Ga alamun hakan ka gani. Sai ma nakega su ɗin sun fimu shiri. Sai dai abinda ke ɗauren kai su kuma miye nasu dalilin? Dan na hanga na hango a duk cikin wanda zasu iya aikata hakan burinsu zai kasance irin namu ne amma basu da hujjar yin hakan. Idan a matan mahaifinsa ne miye ribarsu tunda ba wasu ƴaƴane da su ba balle ace suna yaƙi irin namu ne? Anya kuwa ba iyalan Sayeed Khairul-Bashar bane ke son ɗaukar fansa?”. “Idan kuma zasu ɗauki fansa sai su ɗauka akan wadda ba'ita ta musu laifin ba?. Idan har sune rayuwarsa zasu hara bata matarsa ba. Kuma ai tun farkon shigowarta masarautar nan aka fara wannan wasan. Akwai dai wata a ƙasa daya kama mu sani mu kuma san mai wannan shirin dan dalilinsa mai ƙarfi ne.” Cikin gamsuwa Miran Jasim ke gyaɗama Miran Arshaan kai fuskarsa ɗauke da murmushi, dan koda basu suka aikata ba abinda ya farun ya musu daɗi har cikin rai yake jin farin ciki da nishaɗi..
★.....
Tunda Doctor ta gama dubata ta fice ya cigaba da tsaiwa akan ƙafafunsa lumsassun idanunsa da suka canja kala kaɗan na ɓacin rai ƙyam a kanta. Kallonta yake tamkar wata sabuwar halitta a rayuwarsa. Kallonta yake zuciyarsa na harbawa da sauri-sauri. Kallo yake mata irin na miyasa kika zaɓi shigowa rayuwata a haka?, bayan ba haka na so ki kasance ba. Ƙanƙance idanun ya sakeyi a kanta yana mai datse lips ɗinsa da haƙori har yanajin raɗaɗin hakan a karan kansa. Sannu a hankali ya fara kai kawo a ɗakin hannayensa duk biyu goye da bayansa. Sosai a wannan gaɓar fuskarsa ta nuna matsanancin fushi. Zuciyarsa ta fara kaiwa maƙura akan abubuwan dake faruwa a masarautar, ya fara jin bazai iya cigaba da jurewa akai gaɓar da yake buƙata ba tun farko. Kalaman wasiyyar mahaifinsa ne suka shiga dawo masa ɗaya bayan ɗaya. A yanzu kam idanun ya rumtse tare da kaiwa zaune cikin kujera. Zuciyarsa na gudu da sauri-sauri. Sosai yake jin ɗaci mai sosa zuciya. Hawayene suka cika masa ido domin shima mutum ne kamar kowa, zuciyarsa irin ta kowa ce, yanajin zafi, yanajin farin ciki. Sosai yake buƙatar son jinsa a jikin wani. Mahaifiya ko mata. Sai dai yasan hakan shine abu mafi wahala a gareshi bayan abubuwa masu yawa da ALLAH ya azurtashi da su. Yanada tarin dukiya daya nema da guminsa, mahaifinsa ya bar masa tarin dukiya da shi kansa bai san iyakarta ba. ALLAH ya bashi mulki, mulki mafi daraja sama da kowane shugaba da ke a ƙasar ruman. Ya azurtashi da ƙyawu irin wanda ko'a cikin ƙyawawa yasan zai zama abin kallo. Ya azurtashi da ilimi na boko dana addini da babu abinda zaice sai Alhamdullah. Sai dai ya tawaya ta ɓangaren mace, shi mutum ne mabuƙaci, ya daɗe da fahimtar hakan, amma ƙaddarorimsa sun nisanta shi da samun cikamakin waɗan nan ni'imomin da UBANGIJI ya mallaka masa. A hankali ya sauke lumsassun idanunsa kan Iffah zuciyarsa na kaikawo. (Abbie miyasa kace na kasance haka?) Ya ambata a zuciya cike da ƙunar da take masa mai raɗaɗi..
★★......
Jigum-jigum aka yini a masarautar cike da jimamin abinda ya faru. Al'amarin ya fara ɗaure zuciyar kowa a yanayin da yake da wahalar fassara. Sai dai a zahiri babu mai iya cewa komai sai ƴar ƙus-ƙus kai da abokin maganarka. Har yamma Tajwar Eshaan na tare da Iffah, duk da damunsa da na'urar ɗumama ɗakin da aka kunna saboda ita keyi haka ya cigaba da zama a ɗakin. Hatta da fada da akai zaman fadanci da tunanin zai fito yace wani abu akan abinda ya faru bai fitan ba. Sallama a ɗakin yayi ta yau. Hakan ya fara ankarar da mutanen masarautar kenan duk lokacin daya killace kansa yaƙi fita yana fushi ne ko cikin damuwa. Dan yau dai kusan kowa a haka ya fassara rashin fitowar tasa. Su dai ke kiɗansu suna rawarsu, dan shi dai bai ce ba babu kuma alamar zai ce ɗin har yammaci. A hankali ta fara motsi dai-dai lokacin da yake zaune yana raira karatun Alkur'ani mai girma da wata irin sassanyar murya mai tsaushi da ratsa zuciyar mai saurare. A duk lokacin da ya samu kansa a irin wannan yanayi na damuwa mai ƙuna yafi buƙatar zama yayta karatun Alkur'ani sai ya samu nutsuwa. Da atshawa ta fara a jere har guda huɗu, hakan ya ankarar da shi farkawar tata. Amma tsabar ƙasaita da miskilanci baiko motsa ba ya cigaba da karatunsa har inda yaji zai tsaya dan kansa. Koda ya ajiye Alkur'anin ma bai juyo ɗin ba kai tsaye duk da atishawar da ta cigaba da jerawa a wahalce kuma a jajjere. A nutse ya miƙe babu alamar gaggawa ko garaje tattare da shi, sannu-sannu ya sauke manyan ƙyawawan fararen idanunsa kanta dai-dai ta sake yago tissue dake gefenta a bed side drawer ta toshe bakinta domin tare atshawan da ya sake taho mata. Kusan uku ta sake jerawa kafin ta ajiye tissue ɗin inda ta tara sauran cikin ƙanƙanin lokaci. Numfashi take saukewa a ɗan wahale kumburarrun idanunta na lumshewa da buɗewa.........✍️
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*
*DAUDAR GORA Billyn abdul*
*KI KULANI hafsat xoxo*
*A RUBUCE TAKE Huguma*
*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*
*IDON NERA Mamuh ghee*
_LITTAFI DAYA: 400_ _LITTAFI BIYU: 600_ _LITTAFI UKU: 800_ _LITTAFI HUDU :1000_ _LITTAFI BIYAR: 1200_
_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_
_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
MARYAM SANI ACCESS BANK 0022419171
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
09033181070
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09166221261
*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*
+227 96 09 67 63
Books biyar 1250CFA Books hudu 1050CFA Books uku 850CFA Books biyu 650CFA Bookk daya 450CFA
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.