Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul - Chapter 35
Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul Chapter 35: Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul Chapter 35. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*
4,319 words
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨ (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)
𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (18)
.........A haka idanun nata suka kai garesa, zuba masa su tai a yanayin kallo na ƙasan ido, har ranta take jin bugun zuciyarta na harbawa da sauri-sauri. Ba yau ta fara ganinsa cikin ƙananan kaya ba idan yana sashensa a keɓe, amma sai taga yau ɗin kamar special ne. Baƙaƙen kayan sun masa ƙyau matuƙa da sake bayyana haskensa da ƙuruciyarsa kamar wani matashin saurayin da bai taɓa mallakar ko budurwa ba. Tsantsar ƙasaita da izzar mulki dake yawo a jininsa na ƙara masa wani irin kwarjini mai cika ido da barazana. A hankali ta ƙara ƙasa da kanta jin kamar yana nufota. Gareta ɗin ko ya iso fuskar nan ɗam-ɗam babu alamar yasan minene murmushi ma balle a kai ga dariya. Mug ɗin hanunsa da keta faman tururi da tashin ƙamshin haɗaɗɗen shayi na musamman ya ajiye a side drawer ɗin batare da yayi magana ba. Shayin ta ɗan kalla da sake maida kallonta gareshi cike da mamaki, dan ya ajiye baice komai ba ya bar wajen, bathroom ya shige, ta ɗan lumshe idanu batare data iya cewa komai ba. Babu abinda take buƙata sama da shayin a yanzu, dan haka ta ɗauka ta fara sha lokaci-lokaci tana atshawa ɗin a wahalce da duban hanyar bathroom ɗin. Tsahon mintuna biyar sai gashi ya fito yana faman sake tsuke face. Da sauri ta ɗauke idonta kamar bata gansaba itama, ta ajiye mug ɗin hanunta data kammala shanye shayin da ya zuba matan tana yaye duvet ɗin da take a ciki jin zufa na karyo mata tako ina a jikinta. Yunkurin sakkowa take a gadon dai-dai yana isowa gab da ita, hakan yasa ta dakata da miƙewar ta ɗan dubesa ta kauda kai. Idanu ya tsura mata kamar mai tunanin ta yanda zaice wani abu, kusan minti ɗaya ya ɗan yamutsa fuska cikin motsa lips da ƙyar yace, “ki shiga ruwa a bath....” ya haɗiye sauran a maƙoshi batare da ya ƙarasa ba. Sake ɗago ido tai ta kallesa, ganin nasa idanun a kanta sai ta tura baki kawai ta kauda fuska gefe sai kace wata ƴar yarinya. (Taɓara) ya ayyana a zuciyarsa shima yana ɓata fuskar. Ƴan jin kanne yau a kusa, wanda dama ita su ta sani a zahiri. Bama ta taɓa kallonsa a jerin mutane masu sauƙi ba. Batare da sake cewa uffan ba kawai taji ya ɗan duƙo kanta, zabura tai baya, sai dai kafin tai wani yunƙuri ya ɗagata cak kamar wata ƴar baby. Yo akansa micece wata Iffah. Tsayayyen namiji ne fa ingarma da duban damtsen hannunsa kawai ya iya saka mai tsoro zawayi a wando. Baka gane hakan sai yana sanye da ƙananun kaya. Gaba ɗaya ta waro idanunta sai cikin nasa, da sauri taso kauda natan ya hana hakan ta hanyar sarƙesu. Sai kawai taji zafin zazzaɓinta na ƙaruwa ma... “Ni dai ka daina kallona”. Furucin ya fito cikin suɓutar baki tana laɓe fuska kamar zatai kuka, dan da gaske idanun nan nasa tsoro suke bata. Ta ɗan so bashi dariya, sai dai a zahirinsa babu ko alamar hakan sai ma sake tsuke face ɗin da yay bai kuma janye idanun nasa ba. Sai ma tafiya da ya farayi da ita a hankali. Rumtse nata ta samu nasarar yi da ƙarfi dan gaba ɗaya jikinta yamutsawa yake har zuciyarta na zallo a cikin ƙirji. Zabura tai da buɗe idanun nata a lokaci guda jinta cikin ruwa mai ɗumi sosai. Taja ajiyar zuciya da faɗin, “Wayyo Ummuna”. Bai kulata ba ya ida ajiyeta a ruwan dake ta faman tashin ƙamshi na masifa, ga wani ɗumi mai ratsa ƙashi da ɓargo. Fuska a ƙwaɓe take duban kanta da yanda ya sakata ita da kayan gaba ɗaya cikin ruwan. Sai taji kamarma ta saki kuka kawai ta huta. Wannan wane irin kalar walaƙanci ne. Idan yace mata taje tai wanka kawai ai ya wadatar, amma yanzu gashi ya jiƙa mata kaya duka al'halin bata da yaƙinin wasu dan ta fahimci a sashensa take. Bai dai san tanai ba, dan tuni ma shi ya fice abinsa. Haka ta cire kayan a jiƙe ta ajiye a gefe, nutsa kanta ta sakeyi a ruwan tana mai lushe idanu kamshin ruwan da ɗuminsa na ratsata, ga yanda kumfar tai a sama ful-ful na wani irin ƙayatar da ita.....
★Ta jima a bayin kafin ta fito, sam batai tunanin samunsa a ɗakin ba. Dan haka ta fito kanta tsaye a zatonta ai zai fita ya bata waje tunda ya san wanka ta shiga. Sai da tazo tsakkiyar ɗakin tana ƙoƙarin sharce ruwan dake sakkowa daga jiƙaƙƙen kanta data wanke zuwa kan fuska ta tsaya turus. Da sauri ta juya bayanta kamar zata fasa ihu. ALLAH ma ya sota bathrobe ta sanyo ba towel ba. Ai da yau taji ƙarshen kunya a duniya. Babu alamar zai motsa a zaman ƙasaitar da yay cikin haɗaɗɗiyar kujerar da yake duk da yaji fitowar tata. Sai da ya mula dan kansa ya ɗan ɗago idanunsa ya dubeta kaɗan ya kauda kai. (Bata tausayama kamata) ya ayyana a zuciyarsa yana jan sirrin tsaki a can ƙasan maƙoshi. System ɗin dake a cinyarsa ya ajiye saman ɗan coffee table ɗin gabansa ya miƙe fuska a daƙile, ta gabanta ya raɓa ya wuce kamar bai ganta ba. Jitai kamar tasa ihu dan takaicinsa, sai dai kuma ta kasa motsawa da ga tsaiwar har ya sake dawowa. A bazata yanzun ma taji tattausan hanunsa kan dogon gashinta data naɗe dan ya tsane da wuri kasancewar ta jiƙesa lungu da saƙo dan wanki ta masa mai ƙyau. Warwaresa yay sannan ya ɗaura karamin towel ɗin hanunsa baby pink a kanta ya fara tsane mata ruwan. A yanzu kam ba mamaki ne ya kashe Iffah kawai ba har da suman wucin gadi tai na ɗunbin mamakinsa. Ita Iffah, ɗiyar Babiy da Ummu ne tsaye Shahan-shan ke mata hidima, Shahan-shan fa ba wai hadimin daular ruman ba. Shahan-shan gaba ɗaya, wanda ke amsa shugaban na ƙasarta baki ɗaya, shugaban kuma al'ummar ƙasar ruman baki ɗaya. Sarkin da duniya ke shakka da tsoron nunama koda ƙasarsa yatsa. Ɗan gata da iyayensa suka haifa shi ɗaya ƙwallin ƙwal a duniya. Shi ɗin nan dai da duniya ke kallo matsayin wani babban tauraro mai girman gaske. “Kai ya ALLAH anya ba mafarki nake ba?” (Idonki biyu) zuciyarta ta bata amsa da tabbatar da abinda takewa kokwanto. Ai kanta bai nema kwancewa ba sai da ya kama igiyar bathrobe ɗin jikinta ya kwance. A ɗan zabure ta riƙe hannunsa caraf cikin nata tana waro idanu. “Mi zakayi...?” kalmar ta fito a suɓuce daga bakinta. Wata irin dariya ce ta nema kufce masa ya danneta da ƙyar. Cikin ƙara kame fuska ya tsareta da idanun nan nasa masu kaifin tsiya, hanun nata ya ture zai ƙarasa kwancewa abinsa. Sai kawai ta daka uban tsalle ta faɗa masa a jiki “Ni wlhy ba ƴar iska bace, babu fa komai a c....” ta kasa ƙarasawa tana ƙara cikuykuyesa da ƙyau. Jikinsa rawa ya neman farayi saboda yanda ta ƙanƙamesa, tunda yake a rayuwarsa bayajin ya taɓa rungumar mace kamar haka. Gaba ɗaya abinda ya ɗauka tsahon shekaru yana dakon dannewa ya nema yunƙurowa. Ƙoƙarin janyeta yake tana sake ƙadandanesa a tunaninta so yake ya cire matan koda tsiya. (Ya arrahaman zata halakani) ya faɗa a zuciya yana mai rumtse idanunsa da masifar ƙarfi a zahiri. Cikin zafin nama ya finciketa da sauri yana ƙoƙarin riƙe rawar da jikin nasa ya fara. Cikin wata ƴar sassarfar da bata hana takunsa na ƙasaita fita a yanda yake ba ya bar wajen, a kujerar da ya tashi ya koma ya zube. Faɗi yake (shike nan ta buɗe aiki, Fitinanniyar yarinya zata halakani). Oho Fareedatu batama san yanai ba, dan tana samu ya jayetan daga jikinsa ta kwasa da gudu sai saman katafaren gadon da aka gyara tsaf kamar ba yanzu ta sauka akansa ba. Bata da nutsuwar tunanin yanda akai aka gyara ɗin ko wanda ya gyara taja lafiyayyen duvet ɗin ta naɗe jikinta dake faman kakkarwa. Dan jinta take kamar wadda ta jonu da lantarki. Shiru ɗakin kowa yay ɗif a cikinsu. Babu ko motsin ac dan bai kunna ba saboda ita, duk da yana buƙatarsa, sai dai ya kashe na'urar ɗúmama ɗakin dake aiki tun ɗazun saboda itan. Sai da ya ɗan saita kansa kaɗan kafin ya miƙe, batare da ya dubeta ba ya nufi hanyar fita. Ƙasa-ƙasa ta bishi da kallo, ganin ya tsaya tai saurin kauda kanta. Bai juyo ba sai dai yaji a jikinsa ana kallonsa, murya a shaƙe can ƙasan maƙoshi ya motsa lips ɗinsa kaɗan. “Ki canja wannan rigan”. Jitai kamar ana narkama jikinta ƙanƙara, ta wani lumshe idanunta dake faman yin mar-mar, sai kuma ta sauke ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya dai-dai da rufe ƙofar da yay bayan ya fice. Jitai gaba ɗaya kanta yama tushe, ta gagara tunanin komai kamar yanda take buƙata, kamar wadda aka zabura ta miƙe, idanunta ne suka sauka kan wata ƙyaƙyƙyawar abaya mai ɗaukar idanu. Karasawa tai ta daga rigar, sai kuma ta ɗan waro idanu ganin b&p a ƙasa, “Kam babbar buta, duk shi ya ajiye wannan ma? OMG! Wannan Shahan-shan ɗin daular ruman ɗin ko”. Ta ƙare faɗa kamar zata fashe da kuka. Dan ji take duk ta daburce tsabar wata kunya da take ji na ratsata tamkar tana a gabansa.........✍️
_🥱🏇🏇🏇🏇Babu abun faɗa yau kam, nayi nan kar ace kuma..... To bara dai nai shiru kawai._
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*
*DAUDAR GORA Billyn abdul*
*KI KULANI hafsat xoxo*
*A RUBUCE TAKE Huguma*
*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*
*IDON NERA Mamuh ghee*
_LITTAFI DAYA: 400_ _LITTAFI BIYU: 600_ _LITTAFI UKU: 800_ _LITTAFI HUDU :1000_ _LITTAFI BIYAR: 1200_
_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_
_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
MARYAM SANI ACCESS BANK 0022419171
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
09033181070
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09166221261
*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*
+227 96 09 67 63
Books biyar 1250CFA Books hudu 1050CFA Books uku 850CFA Books biyu 650CFA Bookk daya 450CFA
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨ (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)
𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (19)
.......<<★★ TA-ƘURYA ★★>>
_(Itace muke buƙata ta zama uwar Miran mai jiran gado, ki gaggauta, ki gaggauta tabbatar da ita cikin masarautar nan matsayin Zawjata-almilk daga nan zuwa mako huɗu. Inba haka ba kiyi kuka da kanki ta-ƙurya hahaha!!! hahaha! hhhhh!!!!)_ Zumbur ta miƙe daga ɗan barcin daya figeta, firgitattun kalaman uwa da tayi mata su a zahiri ne waccan ranar ke maimaita kansu yanzu a barcinta matsayin mafarki. Hannu takai ta yarce uban gumin da ya jiƙe mata goshi har yana zirarowa akan fuskarta. Tana a tsaka mai wuya, irin tsakan da bata taɓa shigaba a duk umarnin da uwa ta bata a baya. Maganar ƙulla auren nan bazai kasance ƙarami ba gareta a wannan karon, sakamakon zaman babu wanda ya yarda da ɗan uwansa da akeyi yanzu a masarautar ta ruman. Gaba ɗaya ta rasa ta inda zata ɓullowa al'amarin nan. Ji take komai ya sukurkurce mata, sai dai kuma bazata iya yarda da barin cikar burinta ba na tsawon shekaru da take ganin tazo gab da cimmawa. Dolene ma tai wani abu, sai dai salon zai banbanta dana baya koda kaɗanne, zatai irin ɓadda kamar data saba wajen ganin wannan auren ya ɗauru, dan ko zatai yawo tsirara bazata taɓa yarda Iffah ta zama Malikat ba, mai haihuwar magajin Shahan-shan never for ever hakan ta faru tana numfashi a doron duniya....
🥱To ta-ƙurya bara mu gani ko zaki iya, mudai ƴan kallo ne😉.
★★... ★.....
A hankali ta matse fuska sai kuma takai hannu kan shafaffen cikinta dake mata zafin yunwa. Rabonta da abinci tun yammacin jiya, dan ƙin cin abincin da aka kai mata da dare tai a kurkuku. Zamewa tai a hankali ta kwanta a gadon tana cigaba da matse fuska. Dubanta ta kai a karo na biyu kan kofin shayin da ya bata ta ɓalla masa harara kamar shi ya hanata abincin, sai kuma tai juyi ta maida fuskarta ɗayan side ɗin tana ƙara cure jikinta waje guda hanunnta na kan cikinta..
A hankali ya tura ƙofar ya shiga idanunsa da hankalinsa gaba ɗaya na kan wayar hanunsa mai shegen ƙyau da ɗaukar ido kamar wani glass. Ciki-ciki yay sallama a ƙasan maƙoshi, batare da nuna alamar tuna yabar wani a ɗakin ba ya nufi ƙyaƙyƙywar kujerar zamansa ta musamman ya kai zaune a ƙasaitance. Wani kalan zaman isa da izzar mulki yay har lokacin idonsa akan wayar da alamar serious abu yake yi. Sassanyan ƙamshin turarensa dake ratsa mata ƙofifin hanci ya sata buɗe idanunta sannu a hankali. Har sun canja kala alamar barci ya fara ɗaukarta. Juyowa tai sannu a hankali batare da tunanin shi ɗin bane da gaske, dan indai ƙamshin sa ne ya riga ya gama kama duk bedrooms ɗin da yake amfani da su tsabar yanda yake wanka da turare kamar ruwa. Akan ƙyaƙyƙyawar farar fuskarsa da hasken wayan ya ɗan haska baƙin sajen siɗik ɗin gashinsa na ƙyalli ta sauke, yanda akai masa gyaran fuskar da wani irin haɗaɗɗen style yay matuƙar ƙara masa ƙyau. Sai taji tana buƙatar cigaba da kallonsa kawai, wani abu data kasa banbancewa na tsikarar ƙasan zuciyarta. A jikinsa yaji ana kallonsa, dan haka ya tsaya cak da ga sarrafa wayar da yake faman yi cike da ƙwarewa. Sai dai bai ɗago ba har tsawon kusan minti ɗaya. Sai da yay bala'in shammatarta a bazata ya ɗago nasa kaifafan idanun sai cikin nata dake tsaye ƙyam a kansa. Da wani irin sauri ta fisge kanta gefe cike da pretending ta riƙe ciki tana murƙususu ita a dole bata da lafiya ma. Idanun nasa ya kaɗa kamar wani mai zuƙota ta cikinsu, sai kuma ya yamutse fuska da sake tsuketa ya ɗauke kansa shima. Ci gaba yay da sarrafa wayarsa batare da ya sake kallonta ba, hakan ya bata damar sake satan kallonsa ta ƙasan ido tana sake ƙaƙaro kukan ƙaryanta. lips ɗinsa ya ɗan ciza kaɗan batare da ya bar abinda yake ba a hankali can ƙasan maƙoshi ya furta, “What happend?”. Baki ta tura gaba kamar bazatace komai ba. Sai kuma cikin kuka-kuka da kai tsaye za'a kirashi na shagwaɓa tace, “Ni dai kayan cikina zasu naɗe, yunwa nakeji ga headache, ga ciwo jikina namun ko'ina da ina”. Ta ƙare maganar tana ƙara tura baki. (Yarinyar nan ko...) Ya faɗa a cikin ransa idanunsa na wani binta da kallon slowly kamar mai zooming ɗin ta a cikinsu. Dan can ƙasa-ƙasa yake mata kallon da ita sam ta ɗauka hankalinsa na kan wayar ne baya ganinta saboda ganin yanda yake cigaba da sarrafa wayarsa bai dakata ba. Babu alamar zai sake tanka mata har tsawon kusan mintuna huɗu data cika tai fam da haushinsa. Tsabar son ƙular da shi sai ta fashe da sabon kuka ta shiga wani murƙususun tana kiran “Wayyo cikina Ummu yunwa zata halaka miki ni, nima kasheni zaiyi kamar yanda ya kashe ku. Abbiy ka shirya tarbana gani nan a hanya inda kuke. Ni wlhy garama a kasheni da wannan azaba da akemun, wayyo wo wo wo!!”. Tamkar wani gunki haka ya cigaba da zuba mata ido yana kallon ikon God, shi kam bai taɓa ganin Fitinanniyar yarinya irin yarinyar nan ba a rayuwanshi. Sam batajin magana, ga shegen tsiwa kamar wata babyn roba mai battery. Da ƙyar ya iya ɗaga ƙafa inda take ganin bata da alamar barin kunensa ya huta, yay tsaye a kanta kamar wanda aka dasa, sai wani binta yake da kallon ƙasaita. “Mike ciyon?” ya faɗa a fisge kamar ba shine ya tambayeta yanzun nan ta bashi amsa ba. Ɗan zabura tai da jinsa gab da ita dan batai zato ba, ta yunƙura da sauri zata tashi ya maidata. Sai kuma ya kai zaune gefenta har jinkinsu na gogar juna. Sake zaburar taso yi ya sake maidata yana tsatstsareta da mayun idanunsa masu kaifi. “Ni dai ya warke barshi” ta faɗa da sauri tana ƙoƙarin ture hannunsa dake jikinta. Ko gezau baiyi ba, sai ma ɗorasa da yay saman kanta ya zare towel ɗin da ya naɗa mata tun ɗazun. Dogon gashinta mai alamar lema har yanzu dake faman ƙyalli ne ya bayyana, ya ɗan tsirama gashin ido na wasu sakkani kamar mai nazari, sai kuma ya janye yayo ƙasa da su kan fuskarta. Da sauri tai ƙoƙarin kauda fuskar, sai dai ya hana hakan ta hanyar taro fuskar tata cikin tafin hannunsa ya sarƙe idanunsa cikin idanunta ta ƙarfin tsiya. Wani irin tashi tsigar jikinta ta farayi, cikin rawar lips kamar zata saki kuka ta ce, “Nifa na warke nace”. Idanunsa ya lumshe da sake buɗewa a kanta yana kusanta fuskarsu gab-gab da juna. “Ban yarda ba”. Ya faɗa cikin raɗa-raɗa yana hura mata iskar bakinsa mai ƙamshin banana akan fuskar. Zuƙa tai ta lumshe idanun tana kame jikinta da ke son fara rawa. Da ɗan rawar lips ɗin ta sake furta, “Da gaske nake ciwon ya daina”. Yanda tai maganar a hankali cikin rauni kaɗan ya hana Shahan-shan sakin ihu, amma ya kanne cike da son nuna jarumta yana haɗe tsinin hancinsu waje guda. “Ni ban yarda ba, ki nuna na tausa miki bada zafi ba fa”. Da ƙarfi numfashin Iffah ya fisga tsabar shiga ruɗani, sai da ƙyar ta jawoshi ya koma ƙirjinta, sai dai rawar jikinta ta fara bayyana kanta. Jin saukar tattausan hannunsa bisa lallausar fatan gefen cikinta zuwa ƙugu da ya matsa ya sata furta “Wayyo Ummuna”. “Nima wayyo Ammie-na”. Ya faɗa cikin kwaikwayon ƴar muryarta yana sake tura hanun saman shafaffen cikinta. Da sauri tasa hannu biyu ta riƙe hannun tana tura baki, hakan ya bama lips ɗinsu damar haɗewa, sai tai azamar son kauda fuskar amma ya hana hakan. A bazata taji saukar lips ɗin nasa kan nata. A tare suka buɗe idanun da suka lumshe, sai dai ita zazzaro nata tayi saɓanin shi da ya tsareta da nasa cikin kallon data kasa bama fassara. Da wani salo ya kaɗa nasa alamar ta rufe natan, kamar wata gaula ko wadda yake juyawa da remote kuwa ta rufesu ruf jinin jikinta na hautsina mata. Dole ta ƙanƙame hannunsa dake kan cikinta har yanzu da masifar ƙarfi dan bata da zaɓin daya wuce haka bayan shi. Sai da yaso dan kansa ya janye lips ɗinsa suna mai sauke numfashi a jajjere kamar wanda sukai gudun gasa a ƙaton fili, cikin matuƙar dauriya ya kame nasa yanayin sai dai yaƙi yarda su haɗa ido sam. Itama ɗin dai ba kallon nasa take ba, hasalima bata da burin da ya wuce ta samu wajen ɓuya ko zata samu sassaucin halin da ya jefata na rashin tabbas. Tsahon wasu ƴan mintuna ɗakin ya cigaba da zama shiru, kafin shi ya katse hakan ta hanyar ɗagota gaba ɗayanta ya zaunar a kan gadon, hannunsa ya tura cikin gashinta, tai azamar rumtse idanunta da ƙarfi. Har yanzu akwai damshin da yake gudar mata shiga halin muran. A nutse ya miƙe tare da miƙar da ita, hannunta riƙe a cikin nasa suka isa gaban wadrub ɗin glass ɗin ɗakin nasa dake cike da kayan barci kawai. Ya ɗan danna wani maɓalli sai gata ta zuge ƙofa ta bayyana kanta. Saurin dubansa tai mamaki na barazanar halakata, shiko yay fuska abinsa kamarma bai ganta ba, sai ma janta da yay suka ƙarasa shiga. Ashe anan abun mamakin yake ba can ba, dan kuwa ɗakine babba zagaye da irin waccan wadrube na glass ɗin, kai kace wani shagon saida kaya ne mai zaman kansa. Duk wani nau'in sutura da kayan ado da yake sakama jikinsa ne anan, hatta da takalma sunada nasu sashen, agoguna masu ƙyau na diamond dasu azurfa dana manyan companys ne gasu nan ba'a magana. Bataji a ranta hakan mafarki bane ko bazai yiwu ba kasancewar sanin matsayinsa, Shahan-shan fa, ai ko abinda yafi haka ka gani bakayi mamaki ba. Shi dai ya fuske abinsa tamkar bai fahimceta ba, ya ƙarasa da ita gaban ƙaton mirror ɗin da ke ɗauke da nau'in kayan gyaran gashi kala-kala, ko mace albarka, saukar iskar ɗumin hair dryer ne ya maidota hayyacinta ta sauke nannauyan numfashi da ɗago idanunta ta dubi madubin.........✍️
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*
*DAUDAR GORA Billyn abdul*
*KI KULANI hafsat xoxo*
*A RUBUCE TAKE Huguma*
*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*
*IDON NERA Mamuh ghee*
_LITTAFI DAYA: 400_ _LITTAFI BIYU: 600_ _LITTAFI UKU: 800_ _LITTAFI HUDU :1000_ _LITTAFI BIYAR: 1200_
_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_
_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
MARYAM SANI ACCESS BANK 0022419171
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
09033181070
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09166221261
*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*
+227 96 09 67 63
Books biyar 1250CFA Books hudu 1050CFA Books uku 850CFA Books biyu 650CFA Bookk daya 450CFA
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨ (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)
𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (20)
.........Tar-tar take kallonsu a ciki yana busar mata da gashi a nutse fuskar kuma babu fara'a kota sisin kwabo. Kauda nata tai jikinta gaba ɗaya yay sanyi da al'amarinsa. Sotake tayi tunanin akansa dan ya gama birkita duk ginin da take kallonsa da shi a baya yau baki ɗaya, kaikawo kawai zuciyarta keyi. Ada zahirinsa take tunanin kallo, ashe ba haka bane, dan a yau ta kasa iya banbance zahirinsa na gaskiya. Ya rikita komai a lokacin daya kamata ace ta fahimci komai ɗin. Itafa gaskiya man kanta kawai ma ya tsiyaye tas..
_(Nima dai nawa ya tsiyaye ƴar koran taki Iffah. Shahan-shan yazo da babbar bidi'a fa gaskiya🥱🤣)._
★★ MALIKAT BUSHIRAT ★★
Tun fara faruwar al'amuran nan yau ne zuciyarta ta ɗan fara mata wasi-wasi, a karan kanta sai take ji tana son sanin wanene ya shugabanci yarinyar domin halaka mata gudan jininta. Dan tabbas akwai ƙamashin gaskiyar lauje cikin naɗi. Ba komai ya sata farga ba a yau sai kallon zancen ido data ga yana gudana tsakanin Malikat Ashwaq da Ameera Haifah a ɗazun sanda aka wuce da Iffah. Sai kuma kallon da taga shi kansa Tajwar Eshaan ɗin ya musu su dukansu kasancewar suna tsaye duk a waje guda ne. Ita ta haifesa, duk da bata rayu da shi na tsawon lokaci a zaman kwana da yini ba, tasan halin ɗanta ciki da bai, ta masa sanin da ko da ido yay magana tana fahimtarsa. Lallai kallon yana da manufa, manufa irin wadda ya kamata ace ta sani. Manufa irin wadda ya kamata ace ta farka daga nannauyan barcin dake neman tasiri a idanunta. Ta jima tana zargin Malikat Ashwaq a duk abinda ke faruwa ga tilon ɗanta, sai dai a yau zuciyarta na gaya mata akwai wasu bayan itan, a wasun kuwa har Mamma (Malikat Haseenat) bata cire a ciki ba, dan akwanakin nan take-taken tsohuwar na rikita mata yardar data mata a baya. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, gaba ɗaya ji take komai ya cinkushe mata, dole ne ma tana buƙatar yin nazari mai faɗi, ya kamata kuma ta gana da shi....
★ Zaune yake harɗe a ɗaya daga cikin lafiyayyun kujerun falon. Tun dawowarsa da ga sallar la'asar ya yada zango anan. Laptop ce a coffee table ɗin gaban kujerar da yake yana sarrafata sannu a hankali. Sai mug na shayi dake ta faman tururi ƙamshinsa mai daɗi daya gauraya dana turarensa na tashi sannu a hankali. Sosai siririn farin gilashin idonsa ya sake masa ƙyau. A yanda gaba ɗaya ya tattara hankalinsa ga screen ɗin computer ɗin zai tabbatar maka abu mai matukar muhimmanci yake yi. Dan sai lokaci-lokaci ya kan ɗan ɗauka mug ɗin ya kai bakinsa ya maida ya ajiye duk hankalinsa na kan abinda yake yin. Sayeed Fayzul-haq dake shigowa ya sake maimaita sallamarsa cikin nutsuwarsa, a hankali ya motsa lips ɗinsa ya amsa batare da ya ɗago ba. Sayeed ya ɗan ranƙwafa yana kai gaisuwa duk da basu jima da rabuwa ba. Kansa kawai ya jinjina masa alamar amsawar kenan. “ALLAH ya ƙara maka lafiya da nisan kwana. Malikat ke neman izinin ganinka idan bata shiga lokacin da bai dace da ita ba”. Shiru ya ɗan tsaya daga sarrafa system ɗin, sai dai kuma bai dagoba har shurewar wasu sakanni da suka zama mintoci biyu. Maida yatsunsa yay kan keyboard ɗin kamar bazai ce komai ba sai kuma ya motsa lips ɗin kamar an masa dole ya furta, “Zata iya shigowa”. “Malikat na godiya, ALLAH ya cigaba da kare mana kai adalin shugabanmu. ALLAH ya gafartama magabata”. Duk da addu'ar ƙarshe ta masa daɗi a cikin rai bai motsa ba balle ya amsa. Har cikin ransa yana masifar jin maɗaukakin daɗi a duk lokacin da wani yay ma mahaifansa da suka kwanta dama addu'a..