Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul - Chapter 36
Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul Chapter 36: Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul Chapter 36. ★Kallo yake mata irin na kewa da lumsassun idanunsa.…
3,793 words
★Kallo yake mata irin na kewa da lumsassun idanunsa. Sai dai a zahirinsa baka isa fahimtar hakan ba kai tsaye. A hankali ya ɗan kauda idanunsa da ke binta da kallo yana rissinar da kansa dai-dai tana zama. Itama fuskarta da murmushi take dubansa saɓanin shi da tashi babu walwalar sosai. Sai dai ya motsa lips ɗinsa a hankali ya furta, “Barka da yamma Ammie.” Murmushi ta sake saki da ke sake fidda ƙyawun da ALLAH ya mata. “Ina fatan kana lafiya Niger?”. Maimakon amsa gajeren murmushin da ita kawai keda lasisin ganinsa ya ɗan saki yana kauda kansa, sai kuma ya sake maidowa yana mai zuba mata idanunsan nan masu kaifi. Dan ita kanta data haifesa a duk sanda ya tsareta da su tana jin tasirinsu sosai tattare da ita. Nata ta janye cike da ƙasaita ta furta, “Ya jikin Ibnati?”. Kamar bazaice komai ba sai kuma a fisge ya amsata. “Alhamdullah”. “Thanks God. ALLAH ya ƙara lafiya”. A zuciyarsa ya amsa amin ɗin. Bata damu ba ta cigaba da faɗin, “Abubuwa da yawa da ke faruwa suna sake rikitamun kai, sai dai basu ne suka kawoni ba a yanzu. Yaya maganar shari'ar da aka fara?”. “Tana nan Ammie, za kuma a ƙarasata”. Ya faɗa a hankali cikin taushin harshe. Ajiyar zuciya ta ɗan sauke sai kuma ta ambaci sunansa. Dara-daran idanunsa ya sake saukewa a kanta da ƙyau. Itama kallonsa take cike da so da ƙauna. “Ina son tattaunawa da kai mai muhimmanci, sai dai ba'a nan ba Bin Haysam Abdul-majeed”. Idanunsa ya lumshe ya buɗe a hankali, sunan data kirasa na ratsashi matuƙa, cike da girmamawa a gareta ya furta, “Ki yanke duk lokacin da kike buƙata ni mai jiran umarninki ne a koda yaushe”. Ƙasaitaccen murmushi ta saki ƙaunarsa na sake ratsata. Cikin gyaɗa kai ta furta, “ALLAH ya cigaba da karemun kai, ya lulluɓeka da tarin albarka da rahamominsa marasa yankewa. Duk sanda na yanke zaka jini na barka lafiya”. Kansa ya ɗan rissinar alamar girmamawa, kafin ya furta, “A huta lafiya”.
★★..... ★....
Bayan sallar magrib duk wani mai alaƙa da shari'ar ya kimtsa kansa a katafaren falon da akai wancan zaman farkon. Shine ƙarshen shigowa kamar a wancan zaman. Kan kowa rissine har ya zauna a inda aka tanada masa, tuni ƙamshinsa ya gama danne duk wani turare mai ƙarfi a wajen. Sai da ya gama binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya ta ƙasan ido na tsawon wasu mintuna kafin ya mula dan kansa yay gyaran murya. Dake nutsuwa kowa yay da maida hankalinsa garesa. Nan ma ya sake jan wasu mintuna biyun kafin ya ɗaura da faɗin, “Naso yanke hukunci a zaman ƙarshe na Shari'ar nan a yau, sai dai masu hannu a al'amarin sun nuna mana su basa buƙatar hakan. Bazan tambayi dan mi akai yunƙurin kasheta ba a karo na biyu, sai dai zan sanar da duk wanda ya aikata ya sake shiri akan wanda yake da a baya. Kamar yanda kuka kawo ƙarar neman hakkin yunƙurin kisan jininku da tayi, nima zan shigar da ƙarar neman hakkin kashe min mata da akayi. Kamar yanda nai alƙawarin nema muku haƙƙinku matsayina na shugaba, itama zan nema mata nata hakkin Insha ALLAHU a matsayina na shugaba bayan ta samu lafiya”. Kan babbar buta kenan, ai ba wanda suka shigar da ƙarar ba hatta masu goyon bayan Iffah kalaman Tajwar Eshaan ɗin sai da sukai musu tsawar saukar aradu na wucin gadi. A hankali Malikat Haseenat ta saki wani ƙayataccen ɓoyayyen murmushi, a zahiri kam ta katse suman zaunen da jama'ar wajen sukai ta hanyar faɗin, “Hukuncinka adalcine ga kowa koda son zuciya ta rufe idanun kowa. ALLAH ya ƙarama Zawjata-almilk lafiya, ya tona asirin wanda sukai mata wannan aikin koda a cikinmu ne”. “Shugaba ya amsa tare da godiya ga Uwar masu gida abin al'faharin ƴaƴan ƙwarai. ALLAH ya ƙara miki lafiya da tsohon rai mai albarka baya goya marayu”. Wannan kalamai sun fito ne da ga bakin Sayeed Fayzul-haq mai yawun faɗa da yawun Tajwar Eshaan kasancewar yanzu tamkar amintaccensa yake. Babu dai wanda ya motsa a zahiri, dan tamkar duk sun tafi suman wucin gadi ne, hakan yasa ya cigaba da faɗin, “Wannan kotu mai adalci ta bada umarnin sakin Zawjata-almilk da alƙawarin bata kariya har zuwa sanda za'a yanke mata hukuncin daya dace da ita. Ta kuma saki amintattun hadiman da har yanzu bata kama da laifin komai ba, zakuma su cigaba da aikinsu da ga yau. Ta bada dama ga duk mai ƙorafi akan wannan hukunci ya faɗa a zama na gaba”. Tabbas sun gama yarda cewar Tajwar Eshaan tsohon makirin kansa ne. Sannan hatsabibancin da suke jifansa da shi fa sun tabbatar da shi ɗin a tattare da shi yau. Rai ɓace kusan kowa ya fita a falon bayan fitarsa, kowa bakinsa fal da magana sai dai babu damar yinta anan kuma gudun abinda zaije ya dawo...
★★......
Sam Iffah bata san wainar da ake toyawa ba, dan tun fita sallar la'asar da yay a ɗakin bayan ya tsareta ta ɗanci abincin da aka kawo bata sake ganinsa ba. Sai ma wani wahalallen zazzaɓi ne ya rufeta ruf. Da ƙyar ta iya tashi sallar magrib. Tayi ta a daddafe ta sake komawa saman gadon ta kwanta dan rawar sanyi jikinta ke mata. Bata iya tashi sallar isha'i ba tana cikin bargo. Sosai jikin nata ya ɗauka matsanancin zafi ga ciwon kai ga sanyi tana ji. Tun bata damu da ƙin shigowar tasa ba har ta fara addu'ar hakan, a haka wani wahalallen barci ya ɗauketa.........✍️
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*
*DAUDAR GORA Billyn abdul*
*KI KULANI hafsat xoxo*
*A RUBUCE TAKE Huguma*
*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*
*IDON NERA Mamuh ghee*
_LITTAFI DAYA: 400_ _LITTAFI BIYU: 600_ _LITTAFI UKU: 800_ _LITTAFI HUDU :1000_ _LITTAFI BIYAR: 1200_
_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_
_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
MARYAM SANI ACCESS BANK 0022419171
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
09033181070
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09166221261
*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*
+227 96 09 67 63
Books biyar 1250CFA Books hudu 1050CFA Books uku 850CFA Books biyu 650CFA Bookk daya 450CFA
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨ (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)
𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (21)
........Har ya kammala shirin barcinsa zai kwanta zuciyarsa taƙi bashi haɗin kan hakan. Fuska ya ɗan yamutse kai kace bashi da ra'ayin abinda zuciyar tasa ke so. Sai dai a kallo ɗaya zaka fahimci tsabar miskilanci ke cinsa da ƙasaitar mulki. Cike da izzar dake bayyana takunsa a matsayinsa ya nufi ɗakin. A hankali ya tura ƙofan ya shiga bakinsa da sallama ƙasa-ƙasa. Kallon mamaki yake mata ganinta naɗe a cikin bargo, ga alamar ɗan rawa-rawa da jikinta ke mata da yake gani. Hannu ya kai ya ɗan janye bargon daga saman fuskarta. Aiko ta wani zabura, caraf ta damƙe hannunsa idanunta rufe ruf da alamar tana cikin mayen barcin dai bakinta na motsi cikin faɗa-faɗa take faɗin abinda baya ji. (Fitinatu har a cikin barcin ma ba'a kadata) ya faɗa a zuciyarsa yana lumshe ido da riƙota ganin da gaske fa faɗan take ga zafin hanunta dake kan nasa na ratsa fatar shi. Jikinta rawa yake sosai, dan mafarkin da tai ya matuƙar firgitata, ta daɗe batai irin mafarkan nan ba. Da farko mamakin yanda take ɗinne ya shiga, sai dai ganin abinfa na gaske ne sai hankalinsa ya tashi. Amma bazaka taɓa tantancewa ba a face ɗin sa. Kaɗan ya girgizata muryarsa a ƙasan maƙoshi ya furta “K!”. Ina batama san yanai ba, sai ƙoƙarin fisge jikinta da take kamar dai yanayin da takan shiga a duk lokacin da tai irin mafarkan. Jikinsa ya jawota sosai yana ɗan bubbuga fuskarta kaɗan-kaɗan, sai kuma ya sake faɗin, “Open your eyes. Iffah k!”. Karan farko daya taɓa ambatar sunanta, duk da bata a hayyacinta sai da taji fitar sautin sunan. Buɗe idanun tai a hankali jikinta na ɗan tsuma ta sauke a kansa, sai kuma taja nannauyan numfashi tana ɗan ƙara warosu domin tabbatar da shi ɗinne a zahiri ko har yanzu a mafarkin ne dai. A hankali ya mannata da ƙirjinsa ya rungume. Wani ajiyar zuciya ta sake ja mai ƴar shashshekar data saka tsigar jikinsa tashi. Sai kuma ta maida idanunta ta lumshe sannu a hankali ganin yanda ya tsareta da kaifafan nasa idanun. Lafewa tai a jikin nasa kamar wata mage, dan kanta ciwo yake matuƙa. Ba ƙaramin dauriya yay ba na zamanta jikinsa har tsahon mintuna uku, cikin son danne yanayin da ke neman halaka shi ya buɗe idanunsa da suka canja kala akan ƙyaƙyƙyawar fuskarta. Wani irin kallo yake binta da shi tun daga fuskarta har zuwa ƙafafunta, gaba ɗayanta naɗe take a jikinsa. Yanda ta naɗe ɗin ya bama abayarta mai sanyi damar lafewa a jikin nata ya fidda mata suranta da ƙyau. A kasalance ya lumshe idanunsa yana kauda kansa jin numfashinsa na wata rawa-rawa. Ga ɗumin jikinta na matuƙar ratsa nasa jikin. “What happend?”. Ya faɗa a cikin kunenta da wata irin shaƙaƙƙiyar murya da bata taɓa ji da ga garesa ba, gata acan ƙasan maƙoshi matuƙa. Yanda sautin ya ratsa kunenta har cikin ɓargonta da ƙwaƙwalwar ta ya sata rumtse idanunta da masifar ƙarfi tana wani ƙanƙamesa. Ihu kawai ya rage ya sakar mata ko zata gane a wane riski ta jefashi, amma sai ya danne cike da jarumta ya furzar da boyayyan huci. Cikin sigar tambaya ya sake faɗin, “Uhhuyim?”. Nan ma kamar bazata amsa ba sai kuma ta nisa tana sauke ajiyar zuciya. Kanta ta ɗan girgiza a hankali ta ce, “Mafarki”. “Mafarki?”. Ya maimaita akan lips ɗinsa yana ƙoƙarin saka idanunsa cikin nata kasancewar ta ɗago da ga jikin nasa. Kanta ta gyaɗa masa tana ɗan kauda idonta, dan tun abinda ya faru ɗazu a tsakaninsu sai ta tsinci kanta da jin matsananciyar kunyarsa. Yanzun ma dan kawai tana a firgice ne. Kamar zai ƙara magana sai kuma ya share, murya a shaƙe mai tabbatar da ya gaji da magana ya motsa lips ɗinsa a nutse kamar a fisge, “Kinyi salla?”. Kanta ta ke girgiza masa batare da ta yarda ta kallesan ba yanzu ma. Komai bai sake cewa ba ya miƙe kawai, kamar wanda ke'a yanayin sanyi jiki ya nufi hanyar bathroom. Da kallo ta bisa ƙasa-ƙasa, mummunan mafarkin da tayi a kansa na dawo mata. (Mafarki ba gaskiya ba ne) zuciyarta ta ayyana mata, hakan ya sata sauke ajiyar zuciya ta zame ta kwanta jin sanyi na ratsa mata gaɓoɓi. Bai wani jima sosai ba ya fito, bargon data rufa ya kama ya yaye, tai saurin riƙowa tana ɓata fuska da turo masa baki. “Ni dai sanyi nake ji”. Ido kawai ya tsirama lips ɗin nata batare da ya iya cewa komai ba, kafin ya ranƙwafa a kanta slowly ya ɗauke ta cak ɗinta cikin hannayensa. Ba ƙaramin waro masa manyan idanunta tai ba. Ya ɗan harareta yana kauda nasa. Itama kauda natan tai tana kumbura bakin gaba sosai. (Stubborn girl) ya faɗa a ransa, a zahiri kam fuskar ya sake tsukewa da kyau kai kace da ɗa duniya bai san miye murmushi ba. Yana direta yay fitowansa abinsa. Binsa tai da kallo, abubuwa masu yawa na mata yawo a zuciya game da shi....
Da ƙyar ta iya bin bango ta fito bayan idar da alwalar, yana zaune a cikin kujerar idonsa kan television ɗin ɗakin. Kaɗan ya ɗaga idanunsa ya kalleta ta ƙasa-ƙasa. Duk da yaga yanda take layi tsabar baƙin hali da ƙasaitar mulki ya hanashi tashi ya sake taimaka mata. Harta ƙaraso inda ya shimfiɗa sallayar kamar bai ma san da fitowarta ba. Kallonsa ta sata ta kauda kanta, sai kuma hakan da yay mata ya ƙona mata rai. Cikin jin haushi-haushinsa ta ɗan ƙarfafa kanta, gyalen daya ajiye mata ta ɗauka ta naɗa a kanta, kasancewar abayar jikinta babu ta inda ta tawaya ta kabbara sallarta cike da nutsuwar da ke tabbatar da ta samu wadataccen ilimin addini. Shi kansa yanda take sallar a nutsu duk da wani lokacin jiri kanyi kamar zai kadata sai yaji wata nutsuwa ta ratsashi. Wani kimar iyayenta da sake ganin darajarsu na mamaye sa. A zahiri kam bama zaka taɓa ɗauka hankalinsa a kanta yake ba. Fuskar nan tai ciɗin-ciɗin ko ɗan yankar kanun mutane sai haka😏. Tana idarwa ta zame a wajen ta kwanta hanunta dafe da kanta dake matsanancin sara mata, zuwa can kamar wadda aka zabura ta miƙe zumbur hanunta a baki, sai kuma ta nufi bathroom da ɗan gudu-gudu alamar amai. “OMG!”. Ya faɗa a hankali ƙasan maƙoshinsa jin tana kakarin amai. Bai motsa ba duk da yanda zuciyarsa ke bugawa da sauri-sauri, kusan mintuna biyu da wasu sakanni sai gata ta sake fitowa tana layi. Ga hawaye shaɓe-shaɓe a fuskar gwanin ban tausayi. Yanzu kam miƙewa yay da ƙyar ya nufeta, kamar jira dai-dai yana isowa gab da ita tai wani luuuu zatai baya ya tareta cikin zafin nama ta faɗo cikin hannunsa.. A hankali ta dinga jan ajiyar zuciya jin bata faɗin ba. Sai dai ta kasa buɗe idanunta da ke rufe ruf duk da tanajin alamun nasa kamar na binta da kallo. Kallon nata kuwa yake cike da kasala, sai kuma ya ɗan lumshe nasa idanun shima yana sake rungumota da ƙyau har yana jin saukar numfashinta a jikinsa. Yanda nunfashinta ke saukar masa a jiki sai yake jin tamkar shima hajijiyar na neman kwasarsa, gudun kar ai abin kunya ya ɗagata cak ya ajiye a saman gadon. Kafin ya zauna a kusa da ita yana mai tsura mata fararen idanunsa. Sun kai kusan mintuna biyu a haka, kafin ya katse shirun ɗakin ta hanyar motsa lips ɗinsa a hankali ya furta, “What again?”. Kanta ta nuna masa da gyar ta furta. “Kaina kamar zai fashe”. Sai ga hawaye sharr. Ita kanta bata san miyasa take jin karaya ba a gabansa ko ma shagwaɓa ne oho. Idanunsa ya zuba mata kawai yana bin hawayen da ke bin ƙyaƙyƙyawar fuskarta da gudu-gudu da kallo. Haka kawai sai yaji murmushi na suɓuce masa. Kansa ya kauda gefe yay murmushin sannan ya ɗan sake matsawa kusa da kan nata sosai. Numfashi ta ɗan ja a sanyaye jin saukar lallausan tafin hannunsa saman goshinta. Shi kansa yanda zafin kan ya ratsa hanun nasa sai da ya ɗan lumshe ido. Murya can ƙasan maƙoshi ya ce, “Ta nan ne?”. Kanta ta ɗan jinjina masa, sai kuma ta ɗaura nata hannun saman nasa ta ɗan matsar zuwa gefen kunenta idanunta na sake kawo ƙwalla ta ce, “Harda nan da ma duka”. A yanda tai maganar cikin shagwaɓa kamar wata ƴar baby yaji tsigar jikinsa na wani yamutsawa. Amma jarumin naku sai yay ƙoƙarin basarwa har da yamutsa fuska kaɗan ya furta, “K raguwa ne ko? Just ciwon kai ki ke ma kuka?”. Kamar ya tunzurata ta sake turo masa baki da son ture hannunsa da ke kanta. Ko gezau, dan haka tai yunƙurin juyawa. Nan ma sai da ya nema sakin murmushi amma ya fuske. Cikin wata murya da mai lura zai iya fahimtar shauƙin da yanayin da suke cikin ke bashi ya ɗan matso da jikinsa gab-gab da nata yana faɗin, “Kin cika ragwantaka ne ai. Na miki addu'a?”. Kamar zata sakar masa kuka ta ɗaga kan dan da gaske kan na mata ciwo ne sosai. Shiru bai sake magana ba ya kamota, kan nata ya ɗaura saman jikinsa. Sannan ya sake maida hanunsa saman goshin yana ɗan murza mata sannu a hankali yana mata addu'an. Idanun ta dinga lumshewa sannu-sannu itama, batare data farga ba barci mai nauyi yay awon gaba da ita. Bai daina addu'an da murza mata goshin ba, sai ma wani mayataccen kallo da yake mata idanunsa a shanye. Ya kwashe tsahon lokacin da bai fargaba a wajen zaune, dan tun kan da zafi har ya fara hucewa. Inda wani yace masa hakan zata faru tsakaninsa da wata ɗiya mace zai ƙaryata. Sai dai shi lissafin ƙaddara bai damu da wanda zai lissafa maka ba komai taka tsantsan ɗin ka akan nisanta kai ga abu.........✍️
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*
*DAUDAR GORA Billyn abdul*
*KI KULANI hafsat xoxo*
*A RUBUCE TAKE Huguma*
*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*
*IDON NERA Mamuh ghee*
_LITTAFI DAYA: 400_ _LITTAFI BIYU: 600_ _LITTAFI UKU: 800_ _LITTAFI HUDU :1000_ _LITTAFI BIYAR: 1200_
_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_
_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
MARYAM SANI ACCESS BANK 0022419171
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
09033181070
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09166221261
*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*
+227 96 09 67 63
Books biyar 1250CFA Books hudu 1050CFA Books uku 850CFA Books biyu 650CFA Bookk daya 450CFA
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨ (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)
𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (22)
........Komai ya ƙara kwaɓema ta-ƙurya, ta rasa wace hanya ya kamata tabi dan ganin wannan aure ya ƙullu tsakanin Shahan-shan da yarinyar da sai a yau ta saka amintaccen bawanta bincike a kanta. A ɗan gefen ga jami'an gidan sun mugun duƙufa domin gano wanda yay tsaurin idon ɗaukar Zawjata-almilk daga kurkuku zuwa cikin pool har da kashe jami'an dake tsaronta. Da zafi-zafi suke aiki a wannan yini dan Tajwar Eshaan ya basu kwana biyu ne kacal. Sunko duƙufan matuƙa, domin umarnin mai gayya mai aiki ba abin wasa bane a garesu. Tasan amintaccen hadimin nata shi a karan kansa bai san ita ɗin wacece ba, dan bayan muryar da take masa magana da ita a duk sanda zata sakashi aiki babu abinda ya sani tattare da ita kuma. To ko muryar ma ai bada tata ta ainahi take masa maganar ba. Sai dai duk da wannan tsaron data tabbatar tana da shi bata kasa jin wani ɓurɓushin damuwa ba a ƙasan ranta game da tsananta binciken. Ga Uwa tai mata alƙawarin bazata taimaketa da komai ba a wannan gaɓar, acewarta shine hukuncinta. Ta tsani yarinyar nan, tsana irin wanda batajin ta taɓa yima wani mahaluki irinta a rayuwa. Bata taɓa fuskantar tangarɗa a aikinta ba sai da yarinyar ta shigo rayuwarta. Matsala bata taɓa shiga a aikinta ba sai da yarinyar ta shigo masarautar. Tabi hanyoyi da yawa domin ganin bayanta amma ko gezau. Ta rasa wane kalar shegen taurin kai yarinyar ke da shi. Ita zuciyarta ta fara bata ma anya yarinyar ba shugabar wata ƙungiyar asiri bace mai zaman kanta? Dan abubuwan da ke faruwa a kanta sun fara bata tsoro. Sai dai taci alwashin kota halin ƙaƙa ne sai ta shafe babin rayuwar yarinyar da kaf zuri'arta a duniya nan bada jimawa ba. Wannan alkawarin ta ne......
(Ni dai nace hummmm).
★★.... ★★....
Fuska cike da murmushi yake duban kayan surkullen da boka Barbushi ya basu. Cikin ƴar dariya-dariya ya dubi Miran Arshaan da shima a kallo ɗaya zaka fahimci nasa nishaɗin. “Idan ya isa shi hatsabibi ne a wannan karon ya tsallake mana, ai idan yasan wata bai san wata ba damu yake labarin da ga shi har ƴar iskar yarinyar tashi”. Ƴar dariyar shima Miran Arshaan ɗin yayi, cike da nishaɗi ya ce, “Sai dai uwarsa Bushirat kuwa ta haifi wani amma ba madadinsa ba. Tunda taƙamarsa taurin rai sai mu bisa ta hanyar da zai laushi ta dolen dole da ƙaniyarsa. Shegen yaro kamar jinin aljanu da ga shi har ƴar ƙaniyar yarinyar”. “Kona ifiritai ne wannan karon dai tasu ta ƙare. Dan haka a daren nan na yau zamu saka komai a inda ya dace kamar yanda Barbushi ya bada umarni. Dan ubansu badai sunƙi mutuwa ta sauƙi ba, to ga rayuwar yayita sai dai a cikin ƙunci da baƙin ciki da ga shi har duk wani mai iya jin zai bashi kariyar.” Dariya suka sheƙe da ita har da tafawa kamar wasu abokai. Kafin su miƙe cikin ɓadda kamar da suka gama shiryawa suka nufi fada yanda boka Barbushi ya basu umarni.....
★★... ★★....
Kamar yanda ta saba farkawa akan lokaci domin gudanar da sallar asubahi yau ma bata makara ba. Sai dai saɓanin ko yaushe yau a firgice ta farka. Da sauri-sauri ta ke karanto addu'ar tashi da ga barci tana faman waige-waige a ɗakin mummunan mafarkin da tai a daren jiya da ya sake maimaita kansa gareta yanzu na sake dawo mata. Sosai take jin zuciyarta na tsitstsinkewa, dole taja jikinta ta maƙure kanta a fuskar gadon tana mai naɗe jikinta da son riƙe rawar da yake yi bakinta na ambaton sunan ALLAH kamar yanda kaka ya horeta da daina ihu a duk sanda tai mafarki makamantan hakan saɓanin da da take ihun. Ta ɗauka tsahon mintuna shida kafin ta ɗan samu nutsuwa. Sai ajiyar zuciya da take faman saki a jajjere. Da alama ita ɗaya ta kwana a ɗakin batare da tasan sanda ya fice ba. Hanunta ta kai saman goshinta da zuwa yanzu Alhamdullah babu matsanancin ciwon kan nan data kwanta da shi. Sai ma ɗan sanyi-sanyi da damshin zufar data haɗa ya haddasa mata. Janyewa ta sake yi tana mai lumshe idanunta, haka kawai take jinta wata daban a yau kamar ba Iffahn Babiy da Ummu ba. Ko miye dalilin jin hakan bata sani ba. Kabbara salla da aka farayi ya sata miƙewa zumbur tana ture komai gefe. Gaba ɗaya jikinta babu ƙarfi, ga mafarkin da tai ya sake nunar mata da gaɓɓan jikin baki ɗaya. Haka dai ta ɗan watsa ruwa mai ɗumi ko zai saki sannan tayo alwala ta fito. Bayan ta gabatar da salla maimakon ta koma ta kwanta sai tai zaman karatun Alkur'ani ko zata samu nauyin da zuciyarta ta mata na kwana biyu ya ɗan rage...