Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul - Chapter 44
Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul Chapter 44: Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul Chapter 44. ★A ɓangaren Iffah data sulale ta gudu tun bayan…
3,917 words
★A ɓangaren Iffah data sulale ta gudu tun bayan shigarsa bayi duk yanda tayi domin ganin ƙamshinsa ya bar jikinta hakan ya gagara. Tayi wanka, ta shafa nau'in turarruka daban-daban sai dai ƙamshin jikinsan na nan daram a cikin hancinta da yaƙi bata damar jin kowane ƙamshi bayan shi. Kamar wadda aka zarema lakar jiki tai sakwat a jikin bango tana lumshe idanu. Ita kanta bata san ainahin mima take ji a kansa ba, abinda kawai ta sani komai kawai ya ƙwace mata, bata da wani ƙarfi a zuciya da jikinta a halin yanzun, abinda ya farun kuma yay mata tsaiwar sojan badakare a ƙahon zuciya babu alamar zai motsa. Hanunnta ta kai ta shafi lips ɗinta, sai kuma tai saurin janye yatsun biyu tana mai girgiza kanta kamar wadda akema magana a kunne. Buɗe idanun nata tai cikin sauri ta sake nufar inda turarrukan suke, ɗaya bayan ɗaya ta dinga binsu tana shafama jikinta, ita dai a dole sai ta daina jin wancan ƙamshi. Abin dariya abin tausai harta gama ƙamshin na nan dai bata daina jinsa a cikin hancin nata ba duk da yanda ɗakin yay wani masifar haukacewa da ƙamshin data baza har ana jinsa waje. Miya rage kawai ta saki kuka ta huta, sai ko tai takwaf-takwaf da fuska kamar zata fashe... Haka taita kai kawonta a ɗakin har mai gyarawa yazo gyara da sanar mata an gama shirya break fast. Da gaske yunwar take ji, amma bazata fita su haɗu da shi ba, dan haka ta bada umarnin kawo mata nan tana mazurai a karo na farko. Cikin ƙanƙanin lokaci aka cika umarnin nata kuwa....
★★.... ★....
A can fada tun kusan awa ɗaya baya ake tsammanin fitowarsa, amma shiru kakeji. Hakan abune da ba faruwa yake ba. Tajwar Eshaan mutum ne da baya saɓa alƙawari. In har yace zaiyi abu to zai yisan komai girman ƙalubale da zai iya fuskanta a yayin yinsa kuwa. Hakama in har yace bazai yiba tofa ko kai waye bazaiyi ɗin ba. Kaifi ɗaya ne shi, mai faɗa da cikawa. Mai gaskiya da son tabbatar da ita a mulkinsa, waɗan nan halayensa ne dake matuƙar sake ƙawatashi da kwarzantashi ga al'ummar sa a bayyane. “Anya kuwa lafiya yau?”. Miran Arshaan daya matsu da ganin fitowar Tajwar Eshaan ɗin ya taso zuwa inda Sayeed Fayzul-haq ke tsaye ya faɗa cike da nuna damuwa. Kai Sayeed Fayzul-haq ɗin ya jinjina masa shima da ƴar damuwar a fuskarsa. “Banajin matsala ce insha ALLAH. Dan ban daɗe da ganawa da shi ba, sai dai kasan mutum mai iyali...” ya ƙare maganar da wani ɗan murmushin su na manya. Kamar Miran Arshaan ya sokama Sayeed Fayzul-haq wuƙa a ƙirji yaji, dan haka kawai maganar iyalin na Tajwar Eshaan ta soki ransa, murmushi Sayeed Fayzul-haq ya ɗanyi yana kauda kai kamar bashi ya takalosa ba, dama kuma ya fadane da biyu....
★★..... ★....
Shikam mai gayya da aikin har akai sallar azhar bai gama samun kansa yanda ya kamata ba, dan haka yay sallarsa a ɗaki cikin ƙarfin hali. Rashin fitowarsa salla ya sa su Sayeed Fayzul-haq suka tabbatar da akwai dalili mai ƙarfi daya hana shi fitowar kam tabbas. Ya cigaba da son ganin ya dawo normal, hakan bata samu ba sai kusan gab da la'asar da ya sake komawa Gym ya maida kansa busy, dan wani irin mahaukacin work out yayi, kafin ya fito sharɓan da zufa idanun nan babu alamar rahama yau kam an tsokalo maza. Tsaf yay shiri cikin ɗan sauran ƙarfin da ke jikinsa, dan gaba ɗaya jinsa yake sai a hankali. Haka dai ya daure ya fito domin zuwa massalaci. Iffah dake sharce ruwan alwala da tayo a fuskarta da wani irin sauri ta buɗe idanunta jin an buɗe ƙofar. Ido huɗu sukai da shi, da wani shegen sauri ta maida nata idanun ta rumtse da juyama ƙofar baya, cikin salon nasa na basarwa da shegen miskilanci da ƙasaitar nan tasa shima sai ya ɗauke kai tamkar bai ganta ba. Ta bayanta ya raɓa ya wuce, wasu takardu da ya ajiye ya ɗauka a kan study table ɗin ɗakin ya sake zuwa zai gittata. Tsaye take har yanzu idanunta a rufen ita a dole bata son su haɗa ido. Ƙirjin Iffah bugawa ya dingayi da sauri-sauri jinsa a kusa da ita, idanun ta buɗe kaɗan dan son tabbatarwa. Shi ɗinne dai a gabanta ya zuba mata idanunsa da ke cikin eyeglasses masu ɗan duhu. (Wayyo ni ALLAH) ta ambata a zuciyarta tana maida idanun ta rumtse a daburce ta ce “Barka da rana”. Idanunsa dake a wani irin yanayin da ya tilasta mishi saka gilashin ya ɗan lumshe yana sake buɗewa a kanta. Cikin dakewar muryarsa dake ɗan shaƙe fiye da koda yaushe data sani kamar wanda akaima tilas acan ƙasan maƙoshi ya furta, “After Isha ki sameni”. Idanunta ta buɗe a firgice, sai dai shi tuni ma har yayi gaba abinsa. Dai-dai yana ƙoƙarin ficewa taji kamar ta fasa kuka, amma sai ta haɗiyesa tana ƙoƙarin aro jarumta. A hankali ta furta, “Zanje na ga Ammie to kafin sannan Please”. Cak ya dakata sai dai bai juyo ba har na wasu sakkani. Kin san dai kina a ƙarƙashin umarnin shari'a ne ko?”. Kanta ta jinjina kamar yana kallonta, kafin ta ce, “Eh na sani, alfarma kawai nake nema. Jiya ranta ya ɓaci, matsayinta na mahaifiyata bai kamata na kwanta cikin nutsuwa ba tana fushi da ni. Ina son naje gareta domin neman afuwa”. Gaba ɗaya jijiyoyin jikinsa ne suka ƙarasa saki, wani sanyi na ratsa masa tun daga kan yatsun ƙafa har tsakkiyar kansa. A sannu ya waiwayo ya zuba mata idanunsa. Kallo yake mata irin na kin mamaye komai da komai ɗin nan, a zahiri kam baka isa tantance komai bai tattare da shi, dan fuskar na'a yanda taken nan tsuke tamau. “Ki jira ni”. Ya faɗa kai tsaye dai-dai yana ficewa. Numfashi ta sauke a hankali da yin ɗan baya kamar maijin jiri ta manne da bango, mamaki takeyi, mamakin kanta da komai ma, ta wani gefen kuma ta fara tsoron abubuwan da ke neman cigaba da wajabta kansu a ƙarƙashin mafarkinta, toso ture wannan amma zuciyarta nata ingizata akai, abu mafi ɗaure kai kamar yanda tai mafarkin ta tambayesa zuwan a mafarkin a zahirin amsar da ya bata acan ne anan ma, mi hakan ke nufi? Tayaya ma kanta zai cigaba da ɗauka, gaba ɗaya sai kewar iyayenta ta sake dawo mata sabuwa a zuciya, ta shiga jan ajiyar zuciya hawaye na ciko mata idanu. Iska ta ƙara fesarwa ta buɗe idanunta tana sakin murmushi, murmushi mai ciwo da ita kaɗai ta barma kanta sani sai ALLAH. Sai kuma ta taɓe baki kaɗan da tuno furucinsa. _Wai ta sameshi, to ta sameshi kamar ya? Itakam wace ƙaddara ce ma ta sata amincewa auren mutumin nan? Jibafa yanda yake wani ɗacin rai da ɗa duniya bashi ya gama murje mata lips da jikinta ɗazun ba, halan ma wai ya manta tsiyar da ya aikata ne. (Ko zaki tambayosa) zuciyarta ta ayyana mata. Zabura tai cikin masifa da tsiwa kamar zuciyar tata mutum ce, sai dai kuma batace komai ba aka dai cuna bakin gaba. (😂Gwara dai kiyi shirun ta gidana)........✍️
______________
Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using mg's batare da kunbukaci wani Mai b🤗nd wnn new soap din💣ne,😯 bama cika Baki kujaraba kugane ma idanku domin ance gani yakoriji Kuma siyan nagari maida kudi gida You can check pic👇for the soap reviews🥰 Soap price:4k maiso yy mgn Whatsapp 08062991549 07046881166 07067210195 Call 08064532391 Instagram:glow_with_mgs Facebook: mg's skincare
Masu bukatar cream Shima munadashi harda ma complete set nagyaranjiki sannan akwai na amare special Wanda inkinyi using baki Kuma bukatar kiyi Wani gyaranjiki domin keda kanki zaki shaida cewa fatar taki ta wanku tarwai😍08062991549
Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free
Be part of the glow team😍karkubari abaku lbr👏
____________________
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*
*DAUDAR GORA Billyn abdul*
*KI KULANI hafsat xoxo*
*A RUBUCE TAKE Huguma*
*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*
*IDON NERA Mamuh ghee*
_LITTAFI DAYA: 400_ _LITTAFI BIYU: 600_ _LITTAFI UKU: 800_ _LITTAFI HUDU :1000_ _LITTAFI BIYAR: 1200_
_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_
_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
MARYAM SANI ACCESS BANK 0022419171
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
09033181070
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09166221261
*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*
+227 96 09 67 63
Books biyar 1250CFA Books hudu 1050CFA Books uku 850CFA Books biyu 650CFA Bookk daya 450CFA
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨ (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)
𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (39)
.........Zuwa yanzu labarin abinda ke faruwa da iyalan Miran Jasim ya gama kewaye cikin masarautar. Hasalima babu wani ka-ce-na-ce dake kai kawo sama da zancen. Musamman da ya kasance Umm Husam na ƙarƙashin kulawar likitoci har yanzu, duk da dai Alhamdullah sun sami nasarar mata ɗorin karayar data samu a cinyarta. Amma taji mummunan ciwo a ƙashin bayanta da bama a saka ran zata iya ƙara cigaba da takawa da ƙafafunta. Malikat Haseenat ta fita dubasu a asibitin har shi Miran Jasim ɗin dan shima dai ya jigatu a hannun Husam ƙwarai da gaske. Lokacin da take fitowa bisa rakkiyar Daneen Ammarah da hadimanta amintattu irin su Banou tawagar Tajwar Eshaan ke gabato Clinic ɗin shima. Malikat Haseenat ta kafeshi da idanu na tsahon lokaci, yanda yake tafiya ɗaɗɗaya cike da ƙasaita da izza, ga wani mayataccen ƙamshinsa da tun kafin ya iso shi ya iso hancinansu. Sai dai fuskar ciɗin-ciɗin fiye da kullum alamar akwai ɓoyayyar damuwa tattare da shi. Idanu ta ɗan lumshe tana ɗan murmushi da jin tarin ƙaunarsa na sake mamaye zuciyarta. Tana ma jikan nan nata so mai ƙarfin gaske da itama bata san adadinsa ba. Zubewar Hadimanta bisa gwiwunsu ya fargar da ita isowarsa gab da su. Itama ƙasa tai da kanta alamar girmamawa garesa. Tun kusantowarsu wajen idanunsa shima na'a kanta, sai dai bashi da damar tsayawa gareta kasancewar a Shahan-shan ɗin sa ya fito ba jikanta ba. Har cikin ransa yana ƙaunar wannan baiwar, ƙauna irin wadda shi kaɗai ya barma zuciyarsa sani. Sai da suka shige sannan ta dubi Daneen Ammarah tana murmushi. Itama murmushin tai mata sai dai batace komai ba suka nufi motar da suka zo Clinic ɗin a ciki.
Fuskar nan a matuƙar tsuke cike da barazanar da ke sake fidda ainahin kwarjininsa yake duban Miran Jasim da gaba ɗaya yake jin ya ruɗe bazai iya ma haɗa ko ido da shi ba. Gaba ɗaya yaron ya sake masa wani kwarjini mai ban mamaki fiye da da. Duk da ya tako zuwa Clinic ɗin ko uffan bai furta ba sai kaifafan idanunsa da ke sakaye a gilashin nan dan ɓoye yanayinsa da ya zuba masa. Sai su Sayeed Fayzul-haq ne ke tambayar lafiyar tasa da yawun Tajwar Eshaan ɗin. Shiko ko sau ɗaya ma bai motsa lips ɗinsa ba a wajen, hasalima shi hankalinsa kamar rabi da rabi ne a tare da su nan kawai. Basu wuce tsaiwar mintuna biyar ba suka nufi ɗakin da Umm Husam take itama. Itako ganin Tajwar Eshaan da kansa yazo dubata sai ta fashe da kuka. Idanunsa ya ɗan lumshe kawai, sai Sayeed Fayzul-haq ne ke bata haƙuri. Nan ɗin ma dai basu wuce mintuna biyar ɗin ba suka fice. Da ga shi sai Miran Arshaan da Sayeed Fayzul-haq suka koma sashensa, sai amintaccen hadiminsa da baya rabo da shi a koda yaushe, jami'an da ke bashi tsaro biye da su kowanne hannu ɗauke da mahaukaciyar bindiga. Tako ina hadimai zubewa suke, sai dai ransu fari tas da ganin sarkinsu duk da ba suna ganin fuskarsa bane. Amma suna jin alfaharin sun taɓa ganinsa, koba komai suna jin shauƙi da sanin fuskarsa sau ɗaya koda bazai sake buɗeta a gare su ba har abada.
Shigarsu da ƴan mintuna shugaban jami'an tsaron ya nema iso. Kasancewar Sayeed Fayzul-haq ya san da zuwansa cike da girmamawa yake sanar da Shahan-shan tare da neman afuwar sanar masa a ƙurarran lokaci. Alama yayi ta abashi izinin shigowar kawai. Takaici ya sake kume Miran Arshaan da ke zaune shima. Ya ballama Sayeed Fayzul-haq hararar gefen ido yana ƙwafa a zuciyarsa. Cikin girmamawa shugaban jami'an tsaron ya miƙa gaisuwa, amintaccensa ya amsa a madadinsa. Zaune ya kai a inda Sayeed yay masa nuni, cikin sake risinar da kai na girmamawa ya miƙa files na hannunsa guda uku. “ALLAH ya ƙarama adalin shugabanmu lafiya da nisan kwana masu albarka. Alhamdullah mun kammala binciken da mukai alƙawarin yi yanda ya kamata, sai dai muna mai neman afuwar jinkirin da aka samu bisa wasu dalilai. Wannan files ɗin na cases ɗin ne duka uku. Alhamdullah mun sami nasarar gano hadimin da ya ɗakko Zawjata-almilk daga kurku ya jefata cikin swimming pool, a yanzu haka kuma yana hanunmu dan a daren ranar litinin muka cafkesa yana shirin guduwa da ga cikin masarautar nan. Mun gano shine ta hanyar zanen yatsun hanunsa da muka samu a jikin ƙofar kurkukun daya kasance ɗaya da ga cikin shaidun mu. Ya tabbatar mana da cewar sakashi akayi sai dai shima bai san wacece ba, amma ta jima tana sakashi ayyuka masu kamanceceniya da wannan tun ba yau ba. File na biyu akan kisan Sayeed Khairul-Bashar ne....” Wani irin bugawa mai azabar ƙarfi ƙirjin Miran Arshaan yayi kamar zuciyarsa zata faso ta faɗo. Shugaban jami'ai da bai san yanayi ba ya cigaba da faɗin, “......shima mun gano an kashesane ta hanyar kaisa ɗakin baya da ke a can wajen tsohon kurkukun can akai masa kisan gilla. A binciken da mukai cikin ɗakin ne muka gano zobensa da ɓalin gilashin jikin eyeglasses ɗin idonsa daya fita, tare da suffar hadimin da ya dinga azabartar da shi har ya mutu a gwajin ƙwayoyin idonsa da muka bibiya. Jinkirinmu ya samo asaline ma a dalilin binciko hadimin kasancewar yana rufe fuskarsa ne a lokacin aikata laifin. Shima dai kamar wancan ya tabbatar mana sakashi akayi, sai dai shi yanada matuƙar taurin kai dan yaƙi faɗar waɗan da suka sashi, da alama kuma shi ya sansu sani na zahiri saɓanin wancan.” Fitsari kawai ya ragema Miran Arshaan ya saki, amma illahirin jikinsa tsuma yake yana ƙoƙarin dannewa. Shugaban jami'ai ya cigaba da faɗin, “File na uku tushen samuwar madarar da aka kai sashen Zawjata-almilk ne.....” (Kun mutu Arshaan) zuciyar Miran Arshaan ta faɗa cikin matsanancin tashin hankali. Da ƙyar ya iya haɗiyar busashen yawu da fisgo numfashisa da ke neman suɓucewa da ga gangar jikinsa. Shugaban jami'ai ya cigaba da faɗin, “...madarar ta fito ne da ga sashen gidajen kuduncin wannan daula, dan an ɗauke ta daga can ne zuwa sashen uwar masu gida saboda yin ɓadda kama. Dan haka suspect ɗin mu dole zai kasance a ɗaya da ga waɗan can gidajen guda shida dake a cikin file ɗin. Domin a daren ranar ɗaya daga cikin jami'an mu ya ga wani a suffar ɓadda kama ya fito ta wata ɓarauniyar hanya da muma bamu san da ita ba a gidan nan. Munbi diddigin masu bin hanyar a tsahon kwanakin nan daya tilasta jinkirinmu, mun samu mutane huɗu sai dai har yanzu bamu tabbatar da fuskokinsu ba kasancewar a shirin ɓadda kama suke fitar. Amma hakan ba matsala bane saboda hanyar tabbatar da su ɗin su waye tana a hanunmu muna kan sake tabbatarwane gudun samun kuskure. Albishir dai da zamu bayar akan shi wannan case ɗin a yanzu haka wanda ya samar da dafin macizan yana hanunmu. An kamosa ne kuma a safiyar yau”. A karan farko Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed ya saki wani malalacin murmushi da ya nema sumar da Miran Arshaan da ke jin kamar ya rumtse ido ya gansa a sashen sa ko clinic wajen Miran Jasim ko ma wajen boka Barbushi shi ma bai san ina yafi so yaga kansa ɗin ba. Sayeed Fayzul-haq kam kansa kawai yake faman jinjinawa ransa na mamakin waɗan nan abubuwa abin kamar wani shirin film. Amintaccen hadimin Tajwar Eshaan kam abun ya masa daɗi, musamman ganin murmushi mafi tsadar gani a fuskar shugabansa adali, sannan koba komai a su kansu ma amintattun hadimansa suna fatan kowaye ɗin kodan wahalar da suka fuskanta ta kusan wata guda a kurkuku. Shi dama ya daɗe daji a ransa Zawjata-almilk bazata iya aikata abin nan ba sai da jagorancin wani sheɗanin da ya fi ƙarfinta. Dan haka kawai yake jin ƙaunarta matuƙa musamman da ya fahimci wani abu ɓoyayye da ke tare da shugabansa game da ita duk da yana ƙoƙarin ganin ya danne. Amma kuma shi a yanzu babu wanda ya kaisa sanin wanene Tajwar Eshaan, koba komai barci ne kawai ke rabasu sai ko idan ya shiga ciki ko ya yini bai fito a bedroom ba. Kuma ko'a hakan tabbas tabbas sai ya gansa a yinin sama da sau biyar. Zai iya cewar da ga matarsa a yanzu sai shi ko a mafi ƙololuwar ganin Tajwar Eshaan ɗin. Wani irin kirari ya shiga jeroma shugaban jami'ai, tare da jinjinar ban girma na ƙoƙarin sa da yawun Shahan-shan da bayan murmushi babu alamar zaice wani abu. Magana da ga bakin amintaccen Tajwar Eshaan tamkar kai tsaye ne da ga bakin sa, dan yana cewa ne da say ɗin sa bawai raɗin kansa ba. Sannan koba komai shima a idanunsa Tajwar Eshaan ɗin ya saki murmushin nan da zai iya rantsuwa bai fi a karo na ƙalilan kenan ya taɓa gani ba. Hakan na nufin da gaske Shahan-shan ɗin ya yaba da ƙwazon jami'an tsaron gidan koda bai furta ɗin ba.
Jiƙewa iya jiƙewa jikin Miran Arshaan ya gama yi da zufa. Ga wani irin hajijiya da idanunsa suka fara gani. Kaɗan ya saci duban Tajwar Eshaan da babu alamar hankalinsa a kansa yake, hakama Sayeed Fayzul-haq. Yawu ya haɗe masu kaurin da har yanajin suna kamar ɗaɗa masa maƙoshi. Da ƙyar ya iya jarumtar cigaba da zama har shugaban jami'an tsaro ya gama ya fice. Babu alamar Tajwar Eshaan zai sake cewa wani abu akan batun, hakan yasa shima Sayeed Fayzul-haq haɗiyewa ya ɗakko zancen Miran Jasim da iyalansa, sai ɗansa dake a sashen Malikat Haseenat har yanzu. Ba ƙaramin dauriyar danne tashin hankalinsa yay wajen saka musu baki ba gudun kar Tajwar Eshaan ya harbo jirginsa. Dan ya mugu-mugun sanin hatsabibancin yaron nan, babu abinda ya baro a halin ubansa sai ma finsa taurin kai da yayi. Tattaunawar ta ɗan jasu wani lokaci dan har gab da magrib sannan suka tashi..........✍️
______________
Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using mg's batare da kunbukaci wani Mai b🤗nd wnn new soap din💣ne,😯 bama cika Baki kujaraba kugane ma idanku domin ance gani yakoriji Kuma siyan nagari maida kudi gida You can check pic👇for the soap reviews🥰 Soap price:4k maiso yy mgn Whatsapp 08062991549 07046881166 07067210195 Call 08064532391 Instagram:glow_with_mgs Facebook: mg's skincare
Masu bukatar cream Shima munadashi harda ma complete set nagyaranjiki sannan akwai na amare special Wanda inkinyi using baki Kuma bukatar kiyi Wani gyaranjiki domin keda kanki zaki shaida cewa fatar taki ta wanku tarwai😍08062991549
Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free
Be part of the glow team😍karkubari abaku lbr👏
__________________
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*
*DAUDAR GORA Billyn abdul*
*KI KULANI hafsat xoxo*
*A RUBUCE TAKE Huguma*
*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*
*IDON NERA Mamuh ghee*
_LITTAFI DAYA: 400_ _LITTAFI BIYU: 600_ _LITTAFI UKU: 800_ _LITTAFI HUDU :1000_ _LITTAFI BIYAR: 1200_
_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_
_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
MARYAM SANI ACCESS BANK 0022419171
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
09033181070
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09166221261
*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*
+227 96 09 67 63
Books biyar 1250CFA Books hudu 1050CFA Books uku 850CFA Books biyu 650CFA Bookk daya 450CFA
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨ (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)
𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (40)
______________
Lifestyle_Nig for everything that makes your lifestyle complete ..👌 Furnitures Decoration Kitchen items & Boutiques Quality is our watch word at lifestyle shop kano/kaduna Shop no 58 kabuga housing estate janblo kano on the road in between first gate and second gate near kashe magana suya spot Instagram Lifestyle_Nig Facebook Lifestyleng Tik tok Lifestyle_Nig Delivery nation wide 08036414048 Muna tura kaya ko ina cikin aminci da yardar Allah
_______________
..........A bala'i bala'in matsanancin tashin hankali Miran Arshaan ya nufi clinic, yaji daɗin samun Miran Jasim da ke tambayarsa lafiya ganinsa a firgice shi kaɗai. Maimakon amsa masa sai ca yay, “Kasa a sallameka da ga clinic ɗin nan a daren nan”. Cikin kallo mamaki Miran Jasim ya ce, “Kamar ya nasa a sallameni, kai bakaga yanda shegen yaron nan nawa ya fasan kai ba. Ga wuyana tsabar yanda ya nema karyashi sai da aka samun wannan abun”. Ya kare maganar da nuni da abin wuyansa. Tsaki Miran Arshaan yayi yana ji kamar ya sake shaƙesa shima. “Shaƙar da Husam ya maka ba komai bace akan wacce ke tunkaro rayuwarka”. Ya ɗan ƙara waw-wai-gawa alamar gudun kar wani ya jisu. Cikin sake ƙasa da murya ya cigaba da faɗin, “Idan ka bari ka sake awa biyu anan nadamace ta har abada zata zama abokiyar rayuwarka in har ma matsiyacin yaron nan ya Barka da ran naka kenan”. Yana ƙare faɗa ya ficewarsa da ƴar sassarfa dan dama yay amfani da lokacin shiga sallar magrib da akayi ne......
★.... ★....