Kenza eBookz

Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul - Chapter 45

Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul - Chapter 45

Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul Chapter 45: Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul Chapter 45. Bayan idar da sallar isha'i koda ya nufi sashensa…

4,282 words

Bayan idar da sallar isha'i koda ya nufi sashensa maimakon ƙarasawa ciki sashen Malikat Haseenat ya nufa ta ɓoyayyar hanya. Tayi sallamar wutiri kawai sai ganinsa tayi. Ba yau ya saba mata irin wannan zuwan ba na sirri, sai dai yafi yinsa a bayan sallar asuba. A nutse take dubansa bayan shafa addu'ar data taƙaita cike da kulawa. Shima sai ya taso a hankali da ga zaman ƙasaitar da yay a bakin gadonta ya dawo inda take kan lallausan carpet ɗin dake fes babu datti sai ma tashin ƙamshi da yake da ɗaukar ido na sabunta. Ga taushi matuƙa da ko'a ido zaka iya fahimtar hakan. “Barka da dare Jadda-ti”. Ya faɗa a can ƙasan maƙoshi ya na kaiwa kwance bisa carpet ɗin ya ɗaura kansa kan cinyarta ya wani lumshe idanunsa da a kallo ɗaya ta fahimci damuwar dake tattare da shi a cikinsu tama ƙaru fiye da ɗazun. Murmushi ta saki mai sanyi a ranta tana faɗin, (Yau kuma ƴan shagwaɓan ne a kusa haka), a zahiri kam hanunnta kawai ta ɗaura kan ƙyaƙyƙyawar baƙar sumar sa siɗik ta fara ɗan tausa masa kan kaɗan-kaɗan. Idanun ya sake lumshewa da ƙyau har yanajin barci-barci na ɗibarsa. Tsahon mintuna kusan uku sannan ta magantu cike da kulawa. “Waya taɓamin kai Niger?”. Shiru bai motsa ba har wasu sakanni. Kafin ya buɗe idanunsa da suka ɗan fara shanyewar barci a hankali. Sai kuma ya ɗan ɓata fuska yana ƙoƙarin kaudawa gefe. Riƙo fuskar tai cikin tafukan hanunnta tana murmushi da faɗin, “Oh oh beautiful Hafidi na faɗamin kaji”. Idanunsa ya ɗan lumshe da jujjuya mata kansa kaɗan ya motsa lips ɗin da ƙyar da maganar nan nasa kamar ta dole, “Kawai ina son jin ɗuminki ne”. “Uhyim, ita kuma Hafida-ti na aka barta ita kaɗai”. Shiru yay kamar bazai tanka ba. Sai kuma ya yamutse fuskar daɗa duniya har cikin zuciyarsa ne ya wani kauda kai gefe, “Tanada hayaniya, gata da surutu”. Mi Malikat Haseenat zatai banda dariya. Cike da nutsuwarta da ƙasaita ta shiga yin abinta. Ta ce, “Wayyo ni kai kuma gashi baka son hayaniya da surutu. Nikam ai ta burgeni, gara ta koya maka hayaniyar tata da surutun ko zamu samu ka dinga amsa mana magana biyar cikin goma. Naji daɗin hakan, dan itace dai-dai da kai”. A yanda take maganar zaka san lallai tana matuƙar jin daɗin. Shima dai acan ƙasan ransa murmushi kawai yake, dan ya sake tabbatar da kakar tasa mafi soyuwa a ransa na matuƙar ƙaunar ƴar hayaniyarsa da gasken gaske. Dama shi baya shakku a kanta, dan duk abinda Malikat Haseenat ta so to da gaske tana sonshi ne har cikin rai, idan kuma ta nuna ƙi to da gaske take ƙin nasa. Kamar tasan abinda yake tattaunawa da zuciyarsa ta cigaba da shafa kansa har yanzu da sauran murmushin dariyar da tai akan fuskarta. “Eshaan da gaske ina son yarinyar nan har cikin raina batare dana san dalili ba nima. Halayyarta kuwa na tuna min wasu abubuwa masu yawa. Yarinyar nada shiga rai, sannan tana da ɓoyayyun abubuwan ban mamaki tattare da ita. Karo na uku kenan ina aikawa nemomin iyayenta batare da kowa ya sani ba amma ana tabbatar min wai basa gidansu, a binciken ƙarshe ne na samu cikakken bayanin dalilin barinsu gidan, nasaka an bibiyar min kakaninta a ƙauyensu da aka tabbatar min su suna nan amma sai suma aka taki rashin sa'a. Na fara jin tsoron kar wani a cikin masarautar nan ne ya shirya cutar da su, dan tabbas abinda ya faru tsakaninka da yarinyar nan aike ne.. Bazaka tabbatar da hakan ba sai ka kusanta kanka da ita, kusanci mafi girma da a yanzu shine babban mafarki na, ina fata kafin na bar duniya naga jininka, a koda yaushe kuma na ayyana hakan zuciyata hoton yarinyar nan take kawo min matsayin uwar ƴaƴanka” Yanda muryarta ke fita da sautin tabbatar da abinda ke zuciyarta ne ya saka shi ɗan buɗe idanu kaɗan yana kallonta, sai kuma ya tashi zaune shima a serious ɗin sa, shiru babu alamar zaice wani abu, ita har ta fidda rai ma da cewar tasa. Sai kuma a hankali taji sassanyar muryarsa ya ce, “Jaddah”. “Yes Niger” Ta amsa masa da kulawa. Kaifafan idanunsa masu nutsuwa da haske mai cika idanu da a yau launinsu ya ɗan surka ya zuba mata. Murya a can ƙasa maƙoshi da kamar an masa tilas ya jefa mata tambayar da ba ita tai tsammanin ji da ga garesa ba. “Tambarin baƙi mai kamar tawadar ALLAH duk wani zuri'ar gidan nan ke da shi ko wasu ne a ciki?”. Yanzu kam kallonsa take da mamaki matuƙa da ya gaza ɓoyuwa har a kan fuskarta. “Ban san miye dalilinka na wannan tambayar ba, ko kake son sani. Faɗamin miya faru?”. Kansa ya girgiza mata alamar babu komai, sai kuma a hankali ya ce, “Ina son sani ne”. Sam zuciyarta bata aminta da haka kawai bane, sai dai bazata matsa da son ji ba dan yana da hujjar ƙin faɗar, idan yaso wataran da kansa zai sanar mata. “In dai daga zuri'ar Aliy Qutb (mahaifin kakanka Abdull-Majeed) ka fito wannan tambarin shike tabbatar da kai. Sai dai bawai haka kawai ake gane kai ɗan zuri'ar bane da'an gansa. Akwai ajiyayyun hujjoji da ke tabbatarwar domin ana haihuwar jariri bayan yanke masa cibiya shine abu na biyu da ake duba masa. Yin wannan tambari a jikin duk wani jinin ahalinku ya samo asaline a dalilin kakanku na huɗu da yake da shi, mahaifin Aliy Qutb kenan, shi kuma Aliy sai yazam bashi da shi lokacin da aka haifesa amma sauran yan uwansa na baya duk sukazo da shi, maƙiya sai suka riƙe wannan hujjar a lokacin da za'a naɗashi sarki suka shigo da wata magana mai ban tashin hankali data girgiza masarautar nan baki ɗaya, har sai da ta kai anbi diddigin jinin Aliy da mahaifinsa. Wannan al'amari shi kuma sai ya riƙesa, bayan hawansa mulki duk wanda aka bincika bashi da tambarin sai an masa da wata alama da ke tabbatar da a cikin masarauta aka masa da hujjojin masu ƙarfi a rubuce. Idan aka haifi jariri kuma bayan yankan cibi shine abu na biyu da ake masa idan har babu shi...” Idanunsa da ya zuba mata tun fara maganar ya ɗan motsa kaɗan zuciyarsa na wani irin bugu da sauri-sauri. Amma a zahiri bazaka taɓa fahimtar a wane yanayi ya ke ba. Murya acan ƙasan maƙoshi ya sake furta, “An cigaba da samun masu tambarin da yawa ne? Ko wanda akai mawa ne suka fi rinjaye bayan farawar?”. Shiru na wasu sakkani Malikat Haseenat batace komai ba, sai kuma taja ajiyar zuciya. “I to ni dai a yanda na samu labari a ɗan binciken tarihi wani lokaci akan samu yawaytar masu shi, wani lokacin kuma sai kaga anata haihuwar marasa shi, al'amarin kamar yana tafiya a ƙarni-ƙarni ne, amma kaga tashi kaga”. Babu musu ya miƙe kamar yanda ta buƙata, da taimakonsa ta hau wheelchair ɗinta, kai tsaye inda ƙaton hoton kakansa Tajwar Abdul-majeed ke manne kamar ka masa magana ya amsa ta nufa. Yatsanta manuniya ta kai a saitin fuskar hoton ta shafa, zuuu ƙaton frame ɗin hoton ya shiga wani naɗe kansa kamar ana naɗe tabarma da ga sama yayo ƙasa. Ƙofa ce ta bayyana, bai wani nuna mamaki ba dan ya riga yasan da kofar nan tun ba yanzu ba, dan shi wannan sashe da Malikat Haseenat ke rayuwa yanzu a ciki asalinsa sashen kakansa ne Tajwar Abdul-majeed, shiyyasa akwai sorrika masu yawa a cikinsa da ita kaɗai tasan da su sai wanda kuma taso ya sani. Da taimakonshi ta shiga yana biye da ita a baya. Ɗakine madaidaici mai ɗauke da tarin littattafai kala-kala. Gurin yayi ƴar ƙura alamar bawani shigarsa ake akai-akai ba. Kekenta ta wulwula zuwa bangaren arewa tana bin jerin manya-manyan littattafan wajen da kallo, shi dai yana tsaye da ga tsakkiyar ɗakin yana binta da kallo a ƙasaitance. Juyowa tai ta yafitoshi da hannu, cikin takun nan nasa na izza da ƙasaita ya nufeta. Littatafai biyu masu girma da tudu sosai-sosai ta nuna masa. “Ciro min su”. Hannu ya kai a hankali yana ɗan yamutse fuska ya cirosu, duk sunyi ƙura, amsa sai ta shiga karkaɗesu, yanda ƙurar ke tashi sama ya sashi ja da baya har sai da ta kammala. Ƙara yafitosa tai da hannu ya sake dawowa gabanta, ta kamo tattausan hanunsa cikin nata ta ɗaura masa littattafan. “Wannan zasu taimaka maka samun duk amsar da kake nema, duk wanda ke cikin zuri'ar nan da aka haifa da tambarin ko akai masa akwai bayaninsa anan. Ka kula da ƙyau suna da muhimmancin da ba kowa yasan inda suke ba a cikin wannan masarautar”. Kai ya jinjina mata yana lumshe idanunsa da buɗewa a kanta......

★★......

Taso share umarninsa na ta samesa bayan sallar isha'in amma zuciyarta taƙi bata haɗin kai. Sai ma ta samu kanta da yin sabon wanka da canja kayan jikinta zuwa wata ƙyaƙyƙyawar abaya mai laushi da santsi kalar fari da akaima adon manyan fulawa da golden mai ɗaukar idanu, ga stones taji farare da duk inda ta motsa sai sunyi ƙyalli kamar wani diamond. Samun kanta tai da nutsuwar naɗa veil ɗin ya zauna ɗam a kanta har wani ɗan gashi siriri data zubo ta gaban goshin na reto a fuskarta. Tayi ƙyau matuƙa, dan ko maƙiyinta sai yaji ta burgesa kasancewar Iffah yarinya ce mai shiga rai, ga ta ƙyaƙyƙyawa komai nata dai-dai da ita. Yau dai har an ɗauki turarurrukansa za'a bulbula sai kuma aka fasa. A cikin wanda tai shopping akai amfani da su, sai kuma aka koma dai aka saka nasan ƙaɗan. Yanda tayi haɗin sai ya bada wani irin ƙamshi mai sirrin da ko shi mai gayya mai aikin da wahala ya iya gane ainahin nasa ƙamshin. Taku take a nutsenta kamar wata ƴar wahainiya. Bedroom ɗin jiya ta nufa dan tafi tunanin samunsa a can duk da bata da tabbas.........✍️

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_ _LITTAFI BIYU: 600_ _LITTAFI UKU: 800_ _LITTAFI HUDU :1000_ _LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI ACCESS BANK 0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 96 09 67 63

Books biyar 1250CFA Books hudu 1050CFA Books uku 850CFA Books biyu 650CFA Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨ (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)

𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (41)

_______________

Lifestyle_Nig for everything that makes your lifestyle complete ..👌 Furnitures Decoration Kitchen items & Boutiques Quality is our watch word at lifestyle shop kano/kaduna Shop no 58 kabuga housing estate janblo kano on the road in between first gate and second gate near kashe magana suya spot Instagram Lifestyle_Nig Facebook Lifestyleng Tik tok Lifestyle_Nig Delivery nation wide 08036414048 Muna tura kaya ko ina cikin aminci da yardar Allah

______________

.........Da ƙyar ta iya danne zuciyarta cikin rumtse idanu ta murɗa handle ɗin ƙofar ta shiga. Kamar jiya ɗakin diff babu yawaitar haske sai wani ni'imtaccen ƙamshi mai saka zuciya nutsuwa da sanyin ac. A hankali ta saki ajiyar zuciya tana mai bin ko'ina da kallo. Babu alamar akwai mutum a ciki kam duk da ita dai tana ji a jikinta yana nan. Tafiya ta cigaba da yi kamar wadda ta shigo sata da sanɗa tana ɗan lalleƙawa. “Bani shayi..” Cak ta tsaya ƙirjinta na wani irin dif-dif, sai kuma ta juyo da sauri domin tabbatarwa. Shi ɗin ne dai zaune cikin ƙyaƙyƙyawar kujerarsa mai ƙyawun gaske da laushi, a yanda yay zaman ƙafa harɗe bayansa kwance a kujerar sai ka ɗauka ma idanunsa a lumshe suke. Sanye yake da ga shi sai bathrobe da tausasan slippers alama wanka ya fito, cikin sauri ta sake juyawa tana rumtse idanu duk ta daburce. Sai da ta ɓata minti guda tsayen kafin tayi dauriyar jan ƙafa da ƙyar zuwa centre table na tsakkiyar kujerun da ke gefe kaɗan inda taga butar shayin. Mita take tayi a zuciyarta harta kammala zubawa ta zabga zuma a cikin ɗan kawai neman magana. Murmushi ta saki na mugunta ta ɗauka cup☕ ɗin da shayi keta turiri ta nufesa. Sai dai idanunta a rissine dan kunyar kallonsa take a haka duk da bawai jikinsa a buɗe bane. Tana ƙoƙarin ajiyewa a ɗan coffee table ɗin gabansa ya miƙa mata hannu alamar ta bashi. Miƙa masan tai har yanzu idanunta a ƙasa. “Thanks”. Ya faɗa a hankali yana kai kofin kan lips ɗinsa. Da sauri ya janye jin zaƙin zuman ya wani ratsa masa harshe zau-zau. Dai-dai kuwa da ɗaga ƙafar Iffah zata bar wajen. A hankali ya riƙo hanunta cikin nashi, ta rumtse ido da ƙarfi batare da ta juyo ba. Matsota yay jikinsa, a bazata ta jita zaune ɗare-ɗare a cinyarsa. Da sauri ta zabura zata miƙe ya maidata ya zaunar. (Ya ALLAHU wannan mutumin yana lafiya kuwa?) ta faɗa a ranta kamar zata saki kuka. “Haka ake haɗa shayi dama?”. Wani irin yamutsawa tsigar jikinta tayi saboda yanda yay maganar a saitin kunnenta da sassanyar muryar nan tasa da a yau gaba ɗaya yinin take jinta a shaƙe. Kasa cewa komai tayi, sai mutsu-mutsun son tashi shiko yaƙi yarda ya bata damar hakan. Sai ma hannunsa da ya saƙalo takan cikinta ya ɗaura kan nata da ke wajen tana ƙanƙame jiki. Tare da sake matsota jikinsa bayanta ya manne da ƙirjinsa. Ɗayan hannun kuwa shayin ya ɗauka ya kawosa bakinta. “Hhaah!”. Ya faɗa babu alamar wasa tattare da shi. A shagwaɓe ta ce, “Ni bance zan sha shayi ba fa”. “Ko?”. Ya faɗa cikin sigar tambaya yana ɗage gira sama. Sai kuma ya shiga yin sama da hannunsa zuwa saman jikinta, kansa kuwa na'a kan kafaɗarta yana wani irin kalan shinshinar ƙamshinta. Daburcewa tai duk da sautin fitar numfashinsa kawai take iya ji a kunnenta veil ɗin data naɗa ya lulluɓe wuyanta. Hannun tai saurin riƙowa ta damƙe, cike da in ina ta furta, “Za..zan sha kayi haƙuri”. Ɗan murmushi ya saki a karo na farko, batare da ya ce komai ba ya sake kai kofin bakinta. Ita kanta sai da ta ɗan rumtse ido jin yanda zaƙin ya ratsa mata harshe. Dan abu mai zaƙi bai cika damun Iffah ba. Baifi kurɓa uku ba tai ƙoƙarin kauda kanta gefe. Hannun ya sake ƙoƙarin kaiwa sama, da sauri ta riƙe kamar zata saki kuka ta ce, “Zan sha fa”. Nan ma ƙin tanka mata yay ya sake kai kofin lips ɗinta. Babu yanda ta iya dole sai da ta shanyeshi tas. “Ai na shanye”. Ta faɗa a marairaice tana ƙoƙarin janye hannunsa da ga jikinta. Amma sam yaƙi bata damar hakan. Sai ma kofin da ya ajiye ɗayan hannun ma ya kawo shi kan ƙugunta sai tin inda taji ciwon ya ɗan murza. Zabura tayi dan wajen har yanzu akwai zafi mai raɗaɗi saboda ya tsuma bata bari an murza ba. Sake maidata yay ya zaunar, yanda zafin ke ratsata sai batama san sanda ta maƙalƙalesa ba har ƙafafunta ta naɗe a jikinsa, hannayenta duka biyu kam ta saƙalosu a wuyansa tare da cusa kanta a ƙirjinsa da bathrobe ce kawai. “Karyani kike son yi ne?”. Yay maganar acan ƙasan maƙoshi kamar mai mura da son danne abinda ke ratsashi. Baki ta ɗan tura gaba tana ƙara cusa fuskarta ta gefen wuyansa, saukar numfashita a wajen gaba ɗaya ya ƙara hargitse masa lissafi har jikinsa na wani irin yamutsawa. Amma sai ya dake kamar yanda ya saba. Sai dai tambaya da ya sake jeho mata da muryarsa dake ƙara shaƙewa. “Kinyi salla?”. “Uhm”. Ta faɗa itama kamar wadda aka shaƙe. “Zaki tayani tawa?”. Ya sake faɗa shima a ƙasan maƙoshin yana ƙoƙarin dai-daita fuskarta da ke a kan kafaɗarsa da tashi. Bata da zaɓin da ya wuce ɗaga masa kai jikinta na tsumar da har yana ji. Tausayi da dariya take bashi, a ransa kam faɗi yake (Stubborn girl matsoraciya). A zahiri kam cak ya miƙe tsaye da ita a hannunsa, sake ɓoye fuskarta tai da cusa kai a ƙirjinsa jinta take kamar ta saki ihu dan kunya. Har cikin bayin ya kaita ya dire gaban tap, yana tsaye a bayanta ya kai hannu ya kunna mata.....

Da kallo ya bita lokacin da suke fitowa ganin tana ɗan ɗingisa ƙafarta. Da alama dai faɗuwar da tai ɗin har yanzu na damunta. Baice komai ba kamar yanda itama taƙi yarda su haɗa ido. “Ina zuwa”. Ya faɗa ƙasa-ƙasa yana raɓata ya wuce, cikin closed room ɗin sa ya nufa, ta bisa da kallo ta gefen ido har sai da ya ɓacema ganinta ta saki ajiyar zuciya da kaiwa zaune a table ɗin gaban gadon mai laushin tsiya. Bata gama dai-daita ba ya sake fitowa cikin jallabiya kalar ash sai ɗaukar idanu take ga wani sirrintaccen ƙamshi. Shi da kansa ya shimfiɗa musu sallaya. “Mi zaki roƙa mana?”. Ya faɗa yana ɗan juyowa shanyayyun idanunsa a kanta. Fuska ta ɗan yamutse batare data kallesa ba kanta tsaye ta furta “Naga iyayena”. “Nifa?”. Ya sake tambaya har yanzu idanun dai na kanta. Sai da ta ɓata fuska da tura baki gaba sannan ta furta, “Kai mi kake buƙata kuma a duniya?”. (Tofa wata sabuwa) ya ayyana a zuciyarsa. A zahiri kam sai ya murmusa kaɗan da ɗan ƙara matsawa kusa da ita gab ya kai yatsunsa biyu kan haɓarta ya ɗago fuskarta da ƙyau. Lumshe idanunta tayi. Bai damu ba ya cigaba da kallonta sosai. “K! Mana”. Idanu ta waro waje da sauri. Sai ya waske, ya cigaba da faɗin, “K! Nake buƙata ki haifamin yara masu kama da ke?”. Baki ta laɓe da kauda kanta gefe ta ce, “Hu'um ALLAH ya kiyaye”. “Sai dai kuma na gaba”. Ya faɗa yana sakin mata fuska ya gyara tsaiwarsa. Itama gyarawar tai tana ƙara takwaf-takwaf da fuska, dan badan tana tsoron karya maimaita mata na jiya ba da tuni ta fece a binta. Sun gabatar da salla raka'a hudu da bibbiyu, ya kwararo addu'oin da suka sata jin nutsuwa a ranta harda ƴan ƙwallarta da bata san na minene ba. Bayan sun idar tana ƙoƙarin miƙewa ya riƙota. Bata da yanda zatai dole ta koma ta zauna a tunaninta wata maganar zai mata. Sai taga ya ɗaura farin hannunsa sol da ke ɗauke da dogayen farce ƙal-ƙal a saman ƙafarta, a hankali ya janyo ƙafar a saman tafin hannunsa ya ɗan riƙe yatsun, ɗayan kuma ya tallafo diddigen ya ɗagota gaba ɗaya ya ɗaura saman ƙafarsa da ya tanƙwashe. Kaɗan ya rage numfashin Iffah ya ɗauke dan mamakinsa, Shiko ko'a jikinsa ya shiga murza ƙafar a hankali cikin salon kulawa. Da sauri ta ɗan ɗaura hanunta a kan nasa tana narai-narai da fuska. “What?”. Ya faɗa yana tsareta da idanunsa da suka wani ƙanƙance sosai a kanta. Kamar zata saki kuka ta ce, “Zafi”. Komai bai sake ce mata ba ya ɗauke kansa cike da basarwa ya cigaba da murza mata ƙafar. Tsahon minti biyu kafin ya ajiye ƙafar ya miƙe. Itama miƙewar tai ƙoƙarin yi taji kawai anyi cak da ita an dire saman gado shima ya kai zaune gefenta. Man zafi ya ɗauka a side drawer ya sake kamo ƙafar ya shafa mata, ita dai tayi kurum yanzu sai binsa kawai take da kallo dan ƙafar ya fara sakin mata. Hannunsa ya janye yana ƙoƙarin rufe kwalban suka haɗa ido. Da sauri ta maida nata ta risinar da faɗin, “Thanks”. Yanzun ma komai baice ba ya miƙe, ita kuma ta zubama ƙafar ido tana sauke ajiyar zuciya. Bayan kamar minti biyu tana kan ƙulla shawarar barin ɗakin ya dawo inda ya tashi hannunsa ɗauke da lap-top da kofin shayi. Laptop ɗin ya ajiye a table ɗin gabansu tare da juya mata fuskanta batare da yace komai ba. Zamansa ya gyara cike da ƙasaita ƙafa ɗaya ƙan ɗaya ya ɗauka cup ɗin shayinsa ya kai baki yana wani ɗan lumshe idanunsa da ke mata kallon nan dai dake hanata sukuni... Itama ta gefen ido take kallonsa yanzu, a zahiri kam tayi wani irin gefe da fuska ita a dole ba kallonsa take ba... “Autah!”. Wata sassanyar murya da ko a cikin tsakkiyar barci ta jita a kunenta bazata taɓa manta mai ita ba. Ƙirjinta ne yay wata irin yankewa ya faɗi, sai kuma ta juyo da sauri jin an sake kiran sunan nata. Idanu huɗu sukai da Ummu, Babiy a gefen damarta, Hanash gefen haggunta. Kamar wadda ta firgita ta miƙe a zabure jikinta na rawa. Sai kuma ta dubi Tajwar Eshaan da ke zaunensa kamar baima san mike faruwa ba. Dan shayinsa yake sha a hankali cike da nutsuwa idanunsan nan a lumshe. Kai ta fara girgizawa, sai kuma ta dubi fuskar laptop ɗin. Still dai Ummu ɗin ta ce, da Hanash da Babiy data gama yarda ta rabu da su har abada. Sai Kaka da Iyyani da suka ƙaru. Sai kawai ta diro a gadon ta durƙushe gaban laptop ɗin ta fashe da kuka. “Dan ALLAH gaskiya ne ko mafarki nake? Gizo kuke mun ko video recording ne aka ɗauka?”. “Live ne auta. Video call ba mafarki kike ba”. Hanash ya faɗa fuskarsa shimfiɗe da murmushi. Yi tai kamar wadda tai suman wucin gadi, sai kuma ta dubi Tajwar Eshaan baki sake. Idonsa shima a kanta suke, ya sakar mata wani shegen murmushin da kanne mata ido ɗaya ya ɗauke kai..........✍️

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_ _LITTAFI BIYU: 600_ _LITTAFI UKU: 800_ _LITTAFI HUDU :1000_ _LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI ACCESS BANK 0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 96 09 67 63

Books biyar 1250CFA Books hudu 1050CFA Books uku 850CFA Books biyu 650CFA Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨ (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)

𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (42)

_____________

Lifestyle_Nig for everything that makes your lifestyle complete ..👌 Furnitures Decoration Kitchen items & Boutiques Quality is our watch word at lifestyle shop kano/kaduna Shop no 58 kabuga housing estate janblo kano on the road in between first gate and second gate near kashe magana suya spot Instagram Lifestyle_Nig Facebook Lifestyleng Tik tok Lifestyle_Nig Delivery nation wide 08036414048 Muna tura kaya ko ina cikin aminci da yardar Allah

______________

.........Zubewa tai a ƙasan lallausan carpet ɗin wajen da ƙyau kamar wadda aka zarema dukkan kuzari. Duk da basu san mita kalla ba tai wannan irin zubewa zaune baki ɗaya duk sai suka saki dariya. Kaka yace “Rigimammiyar yarinya har yanzu ɗin baki yarda ba dai?”. Kuka ta sake fashewa da shi a karon na biyu kamar wadda kaka yay ma allura. Idonta kan Laptop ɗin ƙuri tace, “Kaka! Babiy! Iyyani! Ummu! Hanash Akhi. Dama duk kuna raye? Kuna raye kukai nesa da ni?. Kuna raye nake kuka babu dare babu rana ba mai share mun? Miyisa haka? Why! Why Iyayena? Miyasa akacemin kun mutu har yanda aka kasheku aka nuna min......” Wani irin kuka mai ratsa zuciya ya sake kufce mata. Idanunsa kawai ya lumshe yana ɗan matsesu da ƙarfi, dan har tsakkiyar zuciyarsa yake jin kukan. Ga wani abu na zaburo masa tun daga tsakkiyar kai har yatsan ƙafa. Jin zata ɓallo masa ruwa ya miƙe da ɗan sassarfa. A zahiri kam babu abinda mai kallo zai iya gani sai tarin nutsiwarsa da cikar kamala. Shiko shi kaɗai yasan sirrin dake tattare da baɗininsa. Sirrin da yake adanawa tsayin shekaru duk tsananin bamai iya ganosa akan fuskarsa. Da ga shi sai UBANGIJINSA. Sai amintaccen manomin ganyayyakin shayinsa da yake sha domin cigaba da binne raɗaɗin sirrin nasa. Jikin glass window ɗin ɗakin koma ace bango dan kamar da shi ne gaba ɗaya akai ginin sashen nasa ya ƙarasa. Huci yake faman firzarwa a jajjere, idanunsa da sukai wani irin kaɗawa launinsu ya canja nabin wajen masarautar dake ƙwanyar da haske tako ina da kallo. Babu yawan zirga-zirgan mutane, sai masu tsaro tako ina dake kaikawo kowanne da makami a hanunsa, dan tun abin nan na ƙarshe da ya ƙara faruwa da Iffah aka sake ninka tsaron gidan tako ina.

Readers Also Read