Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul - Chapter 5
Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul Chapter 5: Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul Chapter 5. ✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨ (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)
4,466 words
✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨ (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)
𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻
*_8_*
..........Zaune takai a kujerar dake duban tasa tana mai kallon agogon hanunanta. Ya saki murmushi cikin kafeta da idanu. “Daga zuwa sai duba agogo?”. “Hakan dolene Sir, domin ko lokacin islamiyya zan cinye anan. Kaga kenan sai da tsantseni”. “Okay”. Ya faɗa yana gyara zamansa. “Ba buƙatar maimaita abinda ya faru baya, na gaba kawai yanzu shine zanyi iya ƙoƙarin ganin na haɗu da abokin nawa koda ta waya ne, kin san aikin nan nasu yana hanasu samun isashen lokaci matuƙa kasancewarsu manya dake tare da babbar kafar yaɗa labarai mai aiki da kamar duniya gaba ɗaya. Ke yanzu a gareki miye shirinki?”. Kafaɗa Iffah ta ɗan ɗage cikin jan iska da hurowa. “Kusan dukan shirina a kammale yake, burina kawai nasamu yin hira da African Aye👁️🗨”. “Indai hakane haɗuwa da abokina kawai ya rage mana, fatana dai bayan ni kar wanda yasan wannan hatta a gidanku, inba hakaba zamu iya shiga haɗarin da har burin rayuwarmu ma bazai cikaba bayan wannan. Nikuma zanyi duk yanda zanyi insha ALLAHU wajen hana wannan sirrin fita daga gareni....” “Shi abokinka ɗin fa?”. “Baki da matsala da shi domin shi aikinsa ne”. Kai ta jinjina masa fuskata cike da murmushi. Sai kuma ta rissinar da idanunta alamar jin kunyarsa saboda kallon daya kafeta da shi. Kunyar nada nasaba da tuna yanda ta dinga wancakalar da shi da manufarsa a sanda yake malaminta. Sai gashi shine na farko data fara tunkara da matsalata a yanzu duk da kuwa tana kallonta a kan matsalar data shafi kowa na ƙasar Ruman ne. Sautin murmushinsa ya sakata ɗagowa ta ɗan kallesa, sai kuma ta sake kauda kanta gefe itama tana murmushin. “Hummm!” Ya faɗa yana miƙewa. Itama miƙewar tayi batare data yarda sun sake haɗa ido ba. “Kije gida zamuyi waya”. “Nagode sir, ALLAH ya tsare gabanka da bayanka”. Jin sautin murmushinsa ya tabbatar mata jin daɗinsa, amma sai tai gaba da sassarfa tunkan ya sake cewa komai........
★__________________★
*_DAULAR RUMAN (MASARAUTA)_*
Katafaren ɗaki mai ɗauke da ƙayatattun kayan more rayuwa, kwance take bisa lafiyayyen gado da dukkan nau'in shimfiɗunsa suka kasance na alfarma. Sautin dariyar dake tashi cikin kunnuwanta tamkar mafarki ya sata buɗe idanu, cikin tsumar jiki ta ture lallausan bargon da take ciki, tamkar walƙiya ta dire ƙasan lafiyayyen kafet ɗin dake malale gaban gadon tai kneel down tamkar mai neman gafara, kanta a risine alamar nuna tsantsar girmamawa..... Tamkar shirin film ko labaran almara tsohuwa tukuf sanye cikin jajayen kaya ta bayyana bisa baƙar kujerar ƙarfe mai ɗauke da adon gold a cikin ɗakin. Baƙace matuƙa mai tsananin muni da jajayen idanu, yanda ta zauna ƙafa a harɗe kai ka ɗauka itace Shahanshan ɗin..... “Lafiya da tsahon rai su ƙara kasancewa a rayuwar *_Uwa_* mai share kukan masu kuka”. Hamshaƙiyar matar ta faɗa cikin tsantsar girmamawa ga tsohuwar dake harɗe saman kujerar tata tamkar sarauniyar ingila. Cike da isa da ƙasaita tsohuwar taja wani kakkauran numfashi da sake faɗaɗa girman ƙofofin hancinta ta hanyar hurashi, ƙara harɗe ƙafafunta tai tana mai motsa yatsun hanunta, idanunta jajaye kafe akan matar. Cike da isa da ƙasaita mai ɗauke da rashin daɗin muryarta ta tsufa ta fara magana. “Ta-ƙurya kin kusa cin nasara wajen cika sharaɗi na biyu akan alƙawarinmu. Na tayaki murna, saura sharaɗinki na ƙarshe, mafi wahala a cikinsu”. Ƙasa ta ƙarayi da kanta cike da girmamawa a gareta, da dukkan ƙarfin zuciyarta ta furta, “Kece madubin nasarata Uwa!, duk inda akaga naje da jagorancinki na isa. Yanda na cika na farko shima na biyu zan cika sa, nayi alƙawarin cika na ƙarshe ma fiye da yanda kike tsammani.....” Jajayen idanunta masu kama da garwashin wutar gidan biredi ta ɗago tana kallon ƙyaƙyƙyawar kuma hamshaƙiyar matar dake gurfane a gabanta. Ta ƙyalƙyale da wata dariya mara daɗin saurare ga kunen kowa, sai kuma ta gimtse tamkar ba ita tayi ba tana zaro manyan jajayen idanunta kamar na dodanni. “Ta-ƙurya nasan zaki iya, sai dai akwai wani babban ƙalubale dake tunkaro cikar nasararki ta biyu, kuma gab yake da cimmawa, idan baki gaggauta datsesa ba, zakiyi biyu babu”. A razane ta ɗago tana kallonta cikeda bushewar zuciya, sai kuma ta maida kanta da sauri ta rissinar “A gafarceni Uwa, a kawar da ko miye mai son yima cikar burina kutse. Na rantse da ALLAH daya halicceni, koda cikin yankin ahalina ne bana buƙatar numfashinsa Uwa!!”. Dariya ta sake ƙyalƙyalewa da shi sai kuma ta gimtse fuska. Kanta ta shiga girgiza mata da dukkan isa. “Ta-ƙurya wannan karon akwai banbanci da koyaushe, dama na taɓa faɗa miki bayan cikar nasararki ta farko akwai ƙalubale dana gani akan cikar ta biyu, sai dai ba'a buɗe mun komaiba a wancan lokacin, alamar haka na nuna ƙarfin taurarin mai yunƙurin, amma a daren jiya dana tsananta bincike akan mafarkinki na gano wani yanki da ƙyar. Ƴar shilar suda na ƙoƙarin yin cara irin ta gawurtattun zakaru a kunnen bututu da taimakon wata zuciya mai son kusantar tata.” “A taimakeni a kawar mun dasu gaba ɗayansu Uwa. Ko a bani damar kawar da su da kaina”. “Hhhhhhh!!!! Ƙaddarar ƴar shilar bata mutuwa bace cikin sauƙi. Tana kuma da ƙarfin taurarin da zata iya cin nasarar dusashe naki”. Bugawar da ƙirjinta yayi ta zata zuciyarta ce zata fito ta bakinta dan tsabar razana. Ta kafeta da idanu cikin wani irin yanayi mai wahalar fassara. Sai kuma tai saurin maida kanta ƙasa ta rissinar tana faɗin, “A gafarceni Uwa”. Wani irin kakkauran numfashi mai cike da gargaɗi tsohuwar taja, cike da ƙasaita tana yamutse mummunar fuskarta ta cigaba da faɗin, “Zamu iya samun mafita sai dai akwai ruɗani a cikinta. Har zuwa yanzu kuma ban samu buɗewar ruɗanin ba kai tsaye. Dan haka kina da zaɓi biyu. Kodai ki ƙara yin duk yanda zakiyi igiya ta ƙullu tsakanin Malik-alMuluk da wannan ƴar shila muyi duk yanda zamuyi tazama cikamakin aikinmu na biyu, ko kuma ki barta ta cimma burinta.......” Idanunta da suka kaɗa jajur tai ƙoƙarin ɗagowa, sai dai ta maidasu da sauri zuwa ƙasa. “Uwa amma kin faɗamin na cinye jarabawa ta biyu da zarar ya aura cika makin matansa shine matakan nasarata, yanzu haka akwai su su biyu da suka rage ɗauke da aurensa a kansu, zasu miƙasu garesa a karshen watannin nan kamar yanda na samu tabbaci. Taya zamu shigo da wata bayan aikin ya cika. A yanzu ya rage kawai samun cikar burina na ƙarshe ne a kansa. Miye dalilin shigowar wannan yarinyar abinda bai shafeta ba? Mizai hana ai mata wani hukuncin daya dace da ita?...” Hannu ta ɗaga mata cikin tarar numfashi da ƴar hasala-hasala, da kakkausar murya tana mai nunata da ɗanyatsa “Amma har yanzu ban sanar dake wadda ta dace ba, kuma damun san cutarwace na umarninmu gareki bazamu ce ta shigo ba”. “Hakane Uwa, a gafarce ni. Sai dai Mahaifiyar Zak.......”. Ta faɗa da alamun shiga tashin hankali mai girma, amma kallon da Uwa ta watso amata ya hanata ƙarasawa. Bata tanka mata ba, sai dai yanayinta ya nuna a hasale take, dan cikin kaushin murya da zunzurutun jin zafi ta kaɗa ƙahon hanunta mai kama da kwarkwaron gidan dodon koɗi. A take haske ya gilma, sai ga farar takarda a hanunta. “Ƴar shila burinta shine ɗaukar fansa, domin biyu a cikin masu ɗakin Malik-alMuluk da suka shuɗe jininta ne. Burinta shine bin kadin jininsu ta hanyar bayyanama duniya ko kawar da shi. Bayyanawar tata kafin cikar burinki faɗuwarki ne, a yanzu haka kuma ta haɗu da mai taimaka matan harma sun gama magana”. Sosai zuciyarta ta ƙara harzuƙowa. Amma sai batace komai ba saboda ganin Uwa a hasale take da ita. Cikin yin ƙara ƙasa da kai tace, “Da ace bayan cikar burina ne kauɗi da ƙudirin ɗaukar fansar wannan yarinya ya shigo haske ne ga cikar burina. Dan zata ƙarasamin aikin ƙarshe da zanyi. Amma tunda ta shigo a tsakkiyar labarina dolene ta fuskanci hukuncin daya dace da ita. Idan ita bazata mutun ba shi a kawar min da shi mana Uwa”. “Hakan mai sauƙi ne, sai dai shima babu buƙatar mutuwarsa, dan zai iya mana amfani a gaba. Sannan shi rabata da shi shine mafi ƙololuwar hukuncinsa. Dan haka daga nan zuwa safiyar kowace juma'a ta ƙarshen shekarar nan ki tabbatar an zarga igiya tsakaninta da Malik-alMuluk, a dakatar da kai masa matan da suka rage a kaita garesa bayan tarewa, dan da ita zamu cigaba da amfani har samuwar cikar burinmu ga kowa!!.” Da sauri ta ɗago kai jin muryar nayin nesa da ita, sai dai kafin ta iya furta wani abu Uwa ta ɓace daga ɗakin tamkar guntun girgijen hadari a tsakkiyar fararen gizagizai. Zumbur ta miƙe tana mai dafe kanta dake sara mata, wani irin tuƙuƙi da ƙaiƙayin mai zafafa ruhi zuciyarta ke mata. Sai dai sanin wacece Uwa ya sata jin ɗan sassauci kaɗan, amma ruɗani mai ɗauke da abubuwa masu matuƙar yawan gaske da fassarasu a ɗauka shekara dubu bisa dubu ba'a kammala ba na neman danne wancan ƙwarin gwiwar. Taya ruhin ƴaƴan sarakunan ƙasar Ruman basu bata matsala ba sai ƴar talakawa ƙasƙantattu? Dolene yarinyar nan ta ɗanɗana kuɗarta na hukuncin shiga gonar daba tata ba ƙwarai da gaske, sai tayi wasa da ita a tsakkiyar titi wasa irin na ɓera a hanun mage, dan ko ita Malikat bata isaba.....
(Tofa masu karatu, ita kuma wannan wacece ita? Iffah fa ta taro match ɗin da babu players. Kumuje zuwa dai muga yaya wasan zai kaya🚴🏼...)
★__________________★
*_IFFAH_*
A ɗan firgice ta buɗe idanunta tare da tura hannu ƙarƙashin filon data tada kai ta sake danne wayar dake faman ɓurari cike da tsoron kar Ummu ta jiyo, dan tasan Babiy da Hanash basa gidan. Ajiyar zuciya ta sauke mai matuƙar ƙarfi da zaro wayar, cikin rawar jiki ta dannata a silent. Tamkar jira kiran ya sake shigowa kuwa. Idanunta masu matuƙar girma da haske ta waro sosai ganin mai kiran, ai batama bari tayi ring na biyu ba taa ɗaga tare da kaiwa kunnenta tana direwa a gadon. “Kina jina?”. Aka faɗa daga can. Kanta ta jinjina masa tamkar tana gabansa dai-dai tana leƙawa tsakar gidansu. Daga can gefen da Babiy ke kiwon tsuntsaye ta hango Ummu, dan haka ta sauke ajiyar numfashi da fara magana cikin raɗa. “Ina jinka Sir! Ta samu ne?”. “Babu lokacin dogon magana Iffah, kiyi ƙoƙari daga nan zuwa awa ɗaya ki sameni, dan kuwa mun tsinta dami a kala Ajmal ya shigo Ruman, kuma a yanzu haka mun gama magana da shi sai dai ban sanar masa ainahin zancen ba, ya kuma buƙaci haɗuwa dake.....” “Ya ALLAH! Alhmdllhi. Naji daɗi matuƙa wlhy Sir. Insha ALLAHU duk yanda zanyi kuwa zan fito ka saurare ni”. “Okay”. Kawai ya faɗa yana mai yanke wayar. Itama shiri ta shiga faman yi a gaggauce, tare da tattare takardun dukkan bayanai data tattara waje ɗaya. Bakinta ɗauke da addu'ar samun nasarar amincewar Ummu abisa ƙaryar data shirya akan fitar ta fito. Daga inda Ummu take tako zubomata ido na alamar tuhuma. Gareta ta ƙarasa cikin danne komai da karsashin data aro. “Ummu kiran gaggawa na samu daga Ikram. Inaga dai abinda muka jima muna jirane ya fito”. “Amma Iffah....” “Ummu dan ALLAH kar kice a'a”. Iffah tai saurin tarar numfashinta cike da marairaicewa. “Ni ba hanaki zanyiba, sai dai wannan yawan fitar taki a kwanakin nan bana zuwa makaranta ba ya fara damuna Iffah. Shin kin manta halin da muka shiga da wanda zamu iya shiga a yanzu? Ina jin tsoro wlhy, matuƙar tsoro a duk sanda kika fita koda makaranta ne”. Sosai tausayin Ummu ya sake mamaye zuciyar Iffah, ta haɗiye hawayen da suka taru mata a ido tana ƙaƙaro murmushi. “Insha ALLAHU Ummu babu abinda zai faru, wanda ya farun ma a baya bazamu taɓa mu yafe ba. Fita ta kuma ta daina baki tsoro, tunda kinga duk sanda zan fitan ina suturta dukkan jikina”. “Shike nan ALLAH ya tsareki, dan ALLAH kiyi maza ki dawo kafin Abbin ku ya dawo gidan nan ko ɗan uwanki”. “Insha ALLAHU Ummuna”. Iffah ta faɗa tana rungumeta. Shafa kanta Ummu tai tana murmushin ƙarfin hali itama, dan ba wani zuciyarta ta samu nutsuwa bane ita dai, ta bartane kawai saboda tace fitar ta shafi karatunta. Amma zata cigaba da rakata da addu'a harta dawo.........✍
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*
*DAUDAR GORA Billyn abdul*
*KI KULANI hafsat xoxo*
*A RUBUCE TAKE Huguma*
*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*
*IDON NERA Mamuh ghee*
_LITTAFI DAYA: 400_ _LITTAFI BIYU: 600_ _LITTAFI UKU: 800_ _LITTAFI HUDU :1000_ _LITTAFI BIYAR: 1200_
_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_
_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
MARYAM SANI ACCESS BANK 0022419171
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
09033181070
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09166221261
*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*
+22 90165991
Books biyar 1250CFA Books hudu 1050CFA Books uku 850CFA Books biyu 650CFA Bookk daya 450CFA
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨ (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)
𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻
*_9_*
...........Kasancewar wajene daba kowa ke shiga ba anyhow yasa sai da Iffah tai kiran Sir Fawzan bayan saukarta a bakin gate. Umarnin bama security ɗin wajen wayar ya bata. Bayan yayi magana da security ɗin suka bata damar shigewa batare data san miya faɗa musu ba. Tafiya take a nutse tana ɗan kallon wajen da tsarinsa. Dan babban garden ne mai cike da ababen kallo da ni'imtattun korayen ciyayi da ƙawatatun filawoyi. Ta taɓa shiga sau biyu a dalilin taron makarantarsu ta Islamiyya da aka gudanar a wajen. Ya riga ya faɗa mata inda zata samesa, dan haka kanta tsaye take nufar wajen ranta fes da nishaɗi tamkar ance mata ga wuƙa ga maƙoshin Tajwar Eshaan ta yanka. Sai da taje kusan ƙarshen garden ɗin ta tsaya, sai kuma ta shiga canki in canka na number wajen daya bata kasancewar akwai rukuni-rukuni na ɓoyayyun wajen hutawa da manyan mutane sukafi tu'ammali da su idan basa buƙatar wata hayaniya. Cikin ɗan ɗage kafaɗa ta nufi na farkon da zuciyarta tafi karkata. Ƙawatuwar wajen takai mai kallo shagala harya iya manta abinda ya kawoshi, kamshin firanni da wani iska mai busawa a hankali kaɗai na dabanne. Jitai kamar da shakku na shigowarta wajen, amma sai ta dannesa a ƙasan zuciya ta cigaba da takawa tamkar mai sanɗa tana leƙe-leƙe. Ta isa kusan tsakkiya zuciyarta ta shiga gargaɗinta ganin babu alamar akwai mutum mai numfashi a wajen, cak ta tsaya tare da ciro wayarta domin neman sir Fawzan. “Ya ALLAHU”. Ta faɗa jin ana sanar mata bata da kati kona sisi a wayar. Kamar zatai kuka ta sauketa daga kunenta tana ɗan ƙara danne-danne da cigaba da takawa a hankali batare data san mike a gabanta ba. Kaɗowar iska da sassanyan ƙamshin turare mai daɗin gaske ya sakata tsayawa cak ƙirjinta na harbawa da ƙarfi. Fararen idanunta ta janye daga kan wayar tare da ɗago kanta gaba ɗaya, a kan mutumin dake kishingiɗe bisa wani lallausan jan darduma daya haɗu da kalar korayen ciyayi ya bada ƙyaƙyƙyawan tsari ta sauke. Rabin jikinsa akan tum-tum yake. Kansa a risine yana kallon lap-top ƙirar kamfanin apple dake akan wani ƙaramin tum-tum ɗin itama. Gefensa kaɗan wani ƙyaƙyƙyawan bowl ne fari na tangaran, sai butar shayi kalar golden akan tray dake tabbatar da set ne dan harda ƙananun cups nashan shayi. Sanye yake da ƙananun kaya farare tas da suka fidda ainahin suffarsa ta masu ta'amalli da ƙarafuna, gashi sun sake fidda ainahin hasken fatarsa da sheƙinta irin na masu jin daɗi. Duk da tana a gab da shi aikinsa yake hankali kwance baiko nuna alamar yasan da zuwanta ba. “Mi kake buƙata?”. Sassaanyar muryarsa mai zurfi da kamewa ta daki kunenta da alamar akwai wanda yay tsammani ba ita ba. Ƙirjinta ne ya sake harbawa har tanaji kamar jininta daya tsinke na neman biyo hudojin gashin fatarta ya fito. Bata da niyyar cewa komai, gata tsaye tamkar an dasata ta gagara ɗaga ko ƙafa ɗaya tabar wajen duk da haka zuciyarta tafi buƙatar da tayi. Jin shiru ba'a amsa masa ba, ga tsaiwar mutum yanaji har yanzu a gabansa ya sashi ɗago lulu idanunsa masu haske da baiwar bakin ƙwayar tsakkiyarsu ya sauke a kanta. Komai tsayawa yay daga garesa, kamar yanda Iffah ma hatta kaɗawar iskar wajen ta tsaya mata cak... Fuskarsa dake a kame da kwarjini ya sake tsumewa yana sassauta girman idanunsa tamkar mai son lumshesu da gayya. A fisge, tamkar an jawo furucin daga bakin Iffah ta yamutsa fuskarta da ƙanƙance manyan fararen idanunta da tun a kallon farko ta kaudasu da ga kansa alamar kunya irin ta mace, “Idan ma kai aljanine wlhy nafi ƙarfinka. Wace irin jaraba ce duk inda nai saina ganka”. Ta ƙare maganar da hura bakinta. Kamar yanda bai motsa daga yanda yake ba haka bai ce mata komai ba, bai kuma janye idanunsa a kanta ba har yanzu. A zuciyar Iffah fa ta fara tsorata dajin tabbacin mutumin nan fa ƙila aljani ne. Amma sai taga idan ta nuna tsoronsa fa zai ma iya kasheta, saboda a yanzu haka ma ƙarfin hali take, tana matuƙar jin kaifi da tasirin idanunsa a dukkan ɓargon jikinta da jijiyoyi da gudanar jini. Amma sai ta dake a ƙasan ranta tana karanto addu'ar neman tsari da aljanu. Kusan tunani iri ɗaya ne a zukatansu. Dan shima dai zuciyarsa ta ƙara yarda wannan abar aljana ce kawai, yana ganin kuma ya kamata yasan miyasa take bibiyarsa ne?. Nisan data fara masa a idonsa ya fahimci tabar wajen, ilai kuwa can ya hangota tana tafiya cikin sassarfa ta nufi ƙofa. Cin karo data kusan yi da mutum ya sata ja gefe da sauri. Ɗaya daga cikin matasan datai masa gani biyu da su ne, cikin nuna alamar mamaki da tsuke fuska yake kallonta. Harara ta balla masa ta ƙyaɓe fuska da raɓashi ta wuce, danji take ƙafafunta tamkar ba'a kansu take takun ba..... “Fareedah!”. Da sauri ta juyo jin muryar Sir Fawzan daya sauke numfashi da dafe kansa na tabbacin ya jima yana nemanta. “Ina kika shigane wai? Tun ɗazun sai faman zagaye garden ɗin nan nake ni da securitys nemanki, ga wayarki ma taƙi shiga sam”. Maimakon ta bashi amsa sai ta zube a kujerar dake a kusa da ita ragwaf. A wahale tace “Sir ka bani ruwa nasha Please”. Sosai yanayinta ya sake neman firgitashi, amma fahimtar ruwan tafi buƙata ba tambaya ba ya sashi barin wajen da ɗan hanzari. Mintuna ƙalilan ya dawo da robar ruwa. Miƙa mata yay bayan ya ɓalle murfin. Tunda ta kafa kai bata koja numfashi ba sai da ta sha fin rabi, ta sauke robar tare da dafe goshinta tana sauke ajiyar zuciya a jajjere. Lokaci ya bata sosai ta samu nutsuwa kafin ya kai zaune a kujerar dake facing ɗinta. “Fareedah miya faru wai? Ina kika shiga? Duk kin tadamin hankali saboda security sun tabbatar min kin shigo”. A hankali ta ɗago manyan idanunta da launin farinsu ya sirka ta zuba masa. Sai kuma ta janye da sauri tana girgiza kanta dan fuskar mutumin nan kawai ta gani a tare da shi saboda ta sakama ranta aljani ne. Idanunta rumtse tare da yakice tunanin ta sake buɗesu akansa. “Sir lokaci ya ƙure ina abokin naka?”. Ya fahimci bata son bashi amsa, sai kawai ya girgiza mata kai. “Rashin ganinki ya sakani a ruɗanin da har ya kira waya ban sani ba, sai daga baya na lura na kirashi shima kuma bai ɗaga ba”. “Ya ALLAH, shike nan itama wannan damar ta kufce min!”. “Bazamuce haka ba sai munji ta bakinsa, a yau ne dai kawai nake ganin bazai yuwu ba gaskiya, kodan ke a karan kanki ma. Kinga saura baifi mintuna arba'in ayi magrib ba. Kije gida, insha ALLAHU zanbi duk hanyar data dace domin ganin kin haɗu da shi”. Kallonsa take kamar zatai kuka. Sai dai saka zantukansa a ma'aunin hankali ya sata kasa cewa komai. “Kiyi haƙuri”. Ya faɗa cikin sake sanyaya murya yana mata wani lallausan kallo. Kauda nata idon tai daga kansa, taja iska ta fesar da jinjina masa kanta kawai. Dan ta tabbatar inhar tai magana kuka ne zai iya ƙwace mata ma.....
*_MASARAUTA_*
Gurfane take a gaban Uwa kamar yanda dokar take ga duk wanda ke binta. Duk da matsayinta da girmanta a cikin daular ruman a gaban uwa ita ba komai bace face mai neman biyan buƙata (Wa'iyazubillah). Kamar ko yaushe tsohuwar da suke kira uwa sanye take cikin jajayen kaya, sai dai saɓanin waccan ranar yau inuwarta kawai ake iya gani a jikin bangon ɗakin. Amma abin mamaki babu tsoro ko wata shakkar hakan a idanun hamshaƙiyar matar. Inuwar uwa ta kece da mumunar dariyarta mara daɗin saurare, kai kace za'a iya jinta a duk faɗin masarautar, sai dai abin mamaki iya ita ɗin kawai take jinta. Sai da tayi mai isarta kafin ta tsagaita tamkar ba'ita tayin ba. “Ta-ƙurya alƙawarina ya cika, zaku iya tunkarar kowa a yanzu da maganar auren Malik-alMuluk babu mai musa miki hatta Malikat da shi a karan kansa balle duk wani mai faɗa masa yaji. Sai dai akwai banbanci a wannan karon da baya. Hhhhhhhh!!”. “Umarninki shine abin jira Uwa mai share kukan mai kuka”. “Hhhhh Ta-ƙurya shiyyasa bana baƙin cikin taimakonki, zan kuma cigaba da taimakonki kiyita na sara keda duk mabiyanki. Ragamar kasancewar gida a hanun wasunki bashine zai sa su zama masu ƙarfin ikoba sama da naki. Ki shiga ki fita a haɗa gagarumin aure na bajinta tsakanin wannan yarinya da Malik-alMuluk. Hakan zaisa su shagaltu da tunanin komai ya canja musamman shafe watanni tara da Zawjata-almilki da suka rage suka kwashe gidan nan batare da ko ciwon kai ba. Ina son ki nuna bajinta irin wadda ko Malikat bazata yiba, Daular ruman zata cigaba da kasancewa a tafin hanunki a baɗini koda a zahiri kinada wanda suke nuna sunfi ƙarfinki. Ranar mako zata zama ranar sa'a Hhhhhhhh!!!”. Sautin dariyar ya cigaba da nesa da kunuwanta har inuwar uwa ta ɓace. Nannauyan numfashi ta sauke tare da murmushi mai nuna tsantsar farin ciki. Ta dubi ƙyaƙyƙyawan farin tafin hanunta da jini keta kaikawo tana sake maimaita kasantuwar daular ruman a tafin hanunta da uwa ta ambata mata. Tabbas ita ɗin mai sa'a ce, sa'ar da zata iya nunata a gaban duk wasu sa'ointa koma wanda suka ɗarata. Fatanta kawai ALLAH ya kaita ranar cikar burinta gaba ɗaya domin tabbatarma kowa dake cikin Ruman ma ba daular ruman kawai ba *Saka ƙwan kaza bashi ke nufin mallakar akurki ita ɗaya ba* sannan zuwan *mai guri bashi ke tabbatarda naɗewar mai tabarma ba*.......
★★_______★
Kwanaki biyu kenan Iffah bata sake neman sir Fawzan ɗinta ba, ta kuma kashe wayarta ta yanda shima koya nemeta bazai sametan ba. Ita tasan dalilin zaɓar yin hakan, duk da yanayinta ya nuna tana da damuwa dan babu walwala tattare da ita sam tun baro garden ɗin da tayi. Yau ma data kasance bazataje makaranta ba kamar yanda ta saba ta tashi taya Ummu aiki, sai dai yanda take komai kamar mara laka a jiki yasa Ummu nutsuwa a nazartar ta.. “Wai lafiyarki kuwa Iffah? Tun dawowar fitar da kikai shekaran jiya duk kin wani canja. Ko jikin naki ne?”. “A'a Ummu, kawai dai kaina na ɗan mun ciwo ne ƙasa-ƙasa. Amma na san barci ne da bai isheni ba”. “Barci kuma? To miya hanaki barcin?”. In'ina ta fara na rashin sanin abinda zata faɗa. Sai kuma tai ƙasa da kanta ganin yanda Ummu ta kafeta da idanu. Ummu mace ce mai yawan tsantseni wajen tarbiyyar ƴaƴanta. Komai tana binsa a sannu babu garaje ko gaggawar akan tafida yaranta tun kafin sukai haka, shiyyasa cikin sauki take iya sanin matsalolinsu da saurin fahimtar sabuwar hanya da suka ɗauka saɓanin wadda ta sansu da shi. Yanzu ma dai ɗauke kai tai ga Iffah ta cigaba da hidimar gabanta batare data sake magana ba. Daga baya ma saita ƙirƙiri jan Iffah da sabuwar hira da bata da alaƙa data farko. Tun Iffah na ɗararewa har ta saki jikinta...
★Washe gari ta ɗan danne kaso sittin cikin dari na damuwarta dan kar Ummu ta hanata zuwa makaranta. Sai dai koda taje makarantar ma dai zaune kawai ta kasance badan ta nutsu a fahimtar komai ba har aka tashi. Kanta tsaye ta fito domin samun abin hawa a bakin gate kamar sauran ɗalibai. Da ƙyar ta samu tare da wasu da suke kusan a anguwarsu, sai dai zasu rigata fara sauka... A hankali wata baƙar mota dake fake ɗan nesa da makarantar tasu ta fara bin bayan mai Mototaxi ɗin da sam shi hankalinsa baima kai ba. Haka suma su Iffah babu wanda ya kula da motar. Da mai motar ya fahimci zasu zargesa sai ya canja salon bin nasu. A haka har aka sauke abokan tafiyarta. Motar ta cigaba da binsu har titin anguwarsu, anan aka dakata har mai Mototaxi ɗin ya shiga ya kai Iffah ya juyo zai fita suka tsaidashi..........✍
_To ke kuma baƙar mota daga ina🙆🏻?._
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*
*DAUDAR GORA Billyn abdul*
*KI KULANI hafsat xoxo*
*A RUBUCE TAKE Huguma*
*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*
*IDON NERA Mamuh ghee*
_LITTAFI DAYA: 400_ _LITTAFI BIYU: 600_ _LITTAFI UKU: 800_ _LITTAFI HUDU :1000_ _LITTAFI BIYAR: 1200_
_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_
_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
MARYAM SANI ACCESS BANK 0022419171
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
09033181070
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09166221261
*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*
+227 90165991
Books biyar 1250CFA Books hudu 1050CFA Books uku 850CFA Books biyu 650CFA Bookk daya 450CFA
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨ (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)
𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻
*_10_*