Kenza eBookz

Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul - Chapter 6

Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul - Chapter 6

Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul Chapter 6: Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul Chapter 6. ........Kamar wasa Iffah na shigowa gida ta zube kwance…

4,484 words

........Kamar wasa Iffah na shigowa gida ta zube kwance tana rawar sanyi, ga jikinta ya ɗauka matsanancin zafi. Ummu bata kawo komai a ranta ba game da ciwon Iffah sai tunanin ranar da ake ƙwallawa ce ta washeta. Da ƙyar ta tilastata tai wanka, taci abinci kaɗan ta ajiye. Maganin zazzaɓi Ummu ta bata tasha, daga haka ta koma ta kwanta ranar ko Islamiyya bataje ba. Da dare firgita data dingayi saboda munanan mafarkai ya sa kusan kowa bai rintsa ba a gidan sai gab da asuba. Da barci yaɗan figeta saita tashi a firgice har sai sun rufeta da addu'oi take samun nutsuwa ta sake komawa barci. Al'amarin ya tsayama kowa a rai, sai dai ganin ta tashi ragal da asuba tai salla sai sukaita mamaki. Dan bazaka taɓa tsammanin itace a daren jiya ba. Da safe koda tace zataje makaranta hanata Babiy yayi, acewarsa ma asibiti zasuje da Hanash. Kasancewar Iffah da rashin son asibiti sai ta turje akan itafa ta warke, dama jiyan rana ce (ta fake da abinda Ummu tace). Ganin harda ƴan kwallanta Babiy yace to inhar zazzaɓi ya sake dawowa a yinin yau dole suje asibitin nan. Da sauri tace ta yarda. Bayan wucewar Babiy tai ta ɗan ƙarfafa kanta harda taya Ummu aiki, duk da yanda takejin yanayinta babu daɗi haka tai ƙudirin shirin Islamiyya idan lokaci yayi, tana ɗaki kwance bayan idar da sallar azhar sai ga kiran malaminta Fawzan, wayar kawai ta tsurama ido tamkar bazata ɗauka ba harta katse, wani kiran ya sake shigowa shima harya katse bata ɗaga ba. Duk da zumuɗin son ganin kiran nashi da take ciki a kusan kwanaki uku sai taji hanunta ya mata nauyin ɗagawa a yanzu daya kira... Shigowar saƙo ya katse mata tunani, ta kai hannu kan wayar ta ɗauka kamar mai tsoro... _“Fareedah ga dama ta biyu ta sake samuwa, Idan kinga saƙona kiyi ƙoƙarin fitowa kafin Four”._ A zabure ta miƙe jikinta na tsuma ta hau shirin Islamiyya, tare da tattare dukkan takardun bayanan da take ta faman adanawa harma da waɗanda ta ƙara haɗawa a kwanaki ukun nan. “Ummu zan wuce Islamiyya”. Ta faɗa lokacin da take ƙoƙarin saka takalmi a ƙafarta Ummu na tsakar gida tana alwalar sallar la'asar. “Ke da baki da lafiya auta”. “Ummu naji sauƙi wlhy, kinga saukarmu ya kusa babu buƙatar na fara wasa ai. Malam nata mana gargaɗin hak......” Sauran maganar ya maƙale a harshenta sakamakon tashin sautin busa mai nuni da isowar jama'ar masarautar Daular Ruman. Tamkar an daki kan Iffah da guduma haka taji wani dummm! A cikin kunnenta har suka ƙarasa shigowa cikin gidansu jinta bai dawo ba. (Shin tsoro ne? Ko firgici?) bata san wanene ya risketa ba...... Taɓata da Ummu tayine ya sata jan kakkauran numfashi tare da kallonta. Jikin Ummu ne ke rawa, idanunta kam tuni sun tara ƙwalla. Iffah ta shiga girgiza mata kai alamar kar tai kuka, ta sake damƙe hanunta cikin nata tare da maida kallonta garesu rai ɓace, dan ta ɗauka alwashin a wannan karon komi sukazo da shi sun tara sun samu, sai dai a kasheta... “Mi kukazo yimana a gida kuma? Ko kun dawo muma ku idasa kashemu tamkar yanda kuka halaka min ƴan uwana da tsafink......” Da sauri Ummu ta danne mata baki da tafin hannunta tun kan ta ƙarasa faɗa. Kai take girgizamata cikin rawar jiki. Da ace ba Ummu bace babu abinda zai hanata ta ture hanunta ta ƙarasa abinda ta fara faɗa ko zata samu salama a ranta. Sai dai kuma bazata iya ba, dan haka ta shiga yima Ummu alamar roƙo da magiyar ta barta amma taƙi yin hakan... Basamuden nan ne na kullum mai riƙe da bulala ya daka mata tsawa. Da sauri Ummu ta sakemata baki, sai dai ta jawota jikinta ta ƙanƙame. Iffah jitai zuciyata ta ƙara hautsunowa, a matuƙar zabure ta sake buɗe baki zatayi magana ya dakatar da ita... “Ke ƴar talakawa lura da inda kike. Bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane. Idan taƙamarki tsageranci tamkar ƙiftawar ido za'a sauke miki shi, a kuma shafe babinku daga ke har iyayen naki a doron ƙasa”. Hasala iya hasala Iffah tayi, Kukan da Ummu ta fashe da shi ya hanata cewa komai ta juya gareta jikinta na rawar shiga tsananin ɓacin rai, kanta take juyamata alamar karntace komai..... “Umm....” “A'a Iffah! Ina umartarki karki ce komai”. “Kibarta tace ɗinma yanzu harshenta ya zama datsatstse a gabanki.” Kafin Ummu dake girgiza kai tace komai Babiy ya shigo tamkar an jehoshi, da alama dai wanine ya sanar masa da zuwan jama'ar masarauta gidan nasa. Ko sau ɗaya basu bashi damar cewa komaiba suka isar masa da saƙon kira daga daular ruman. “Innalillahi.....” Iffah ta shiga ambata ita da Ummu, dan sunaji a ransu tarihine dai yake ƙoƙarin maimaita kansa, hawaye masu tsananin ƙuna da ɗaci na gangarowa bisa ƙyaƙyƙyawar fuskata Babiy da shima dai yasan labarin gizo bazai wuce ƙoƙi ba. A gaban idonsu aka wuce da Babiy Daular Ruman a karo na uku, tare da barin wasu dakaru a ƙofar gida ta hanyar hana duk wani mai yunƙurin fita daga gidan. Haɗe kai kawai Iffah da Ummu sukai suna kuka, dan shi kaɗai suke da damar yi ɗin..

★Bayan cikar awanni biyu da tafiyar Babiy sai gashi ya dawo, dawowa irin wadda ya saba a duk lokacin da makamancin kira irin wannan ya samesa daga daular Ruman. Yanda ya kafe Iffah da idanunsa dake zubda hawaye ya saka Ummu zubewa ƙasa cikin kuka. “Abu Hanash itama zamu rasata ko? Itama ka ɗaura mata aure da Tajwar.....?” Hawayene masu ɗumi da ƙuna suka ziraro a idanun Babiy, ya girgizama Ummu kansa a hankali alamar a'a, tare da girgiza kan nasa kuma alamar tayi shiru. Hawayen nata ta share kamar yanda ya buƙata, sai dai jikinta bai bar tsuma ba. Kamar yanda Iffah data kafesa da idanu bata iya ko ƙyaftawa ba. Ummu ta sake gyara zamanta da fuskantar Babiy da ƙyau.... “Idan ba abinda muke tunani bane to minene ya faru?”. “Ki kwantar da hankalinki babu komai f.....” “Bazan taɓa yarda babu komai ba. Sai dai idan kana so ka rufeni ne. Hakan kuma shine mafi ƙololuwar kuskuren da banajin zan iya yin afuwa gareka a kanshi. Dan inaji a jikina zuwanka masarauta nada nasaba da rayuwar yarinyata data rage min, idan har zuciyarka ta iya ɓoyewa ƙwayoyin idanunka basu lulluɓe komai ba, garama ka sanar min”. Babiy ya fahimci idon Ummu ya rufe ta manta Iffah na wajen, dan haka ya cigaba da ƙoƙarin ganin ya kufcema faɗar abinda yazo da shi har sai sun keɓe amma ta dage akan itafa ya faɗa mata a yanzu. So yake ya buɗe ido amma bashi da sauran ƙarfin zuciya a yanzu, dan haka a sanyaye ya rumtse idanunsa da launinsu yay matuƙar komawa ja. “Ba'a ɗaura mata aure da shi ba. Sai dai....” ya kasa ƙarasawa. “......Sai dai me? Dan ALLAH ka faɗa min”. Ummu ta faɗa tana mai sake fashe masa da kuka mai matuƙar sake ɗaga masa hankali. Miƙewa yay yunƙurin yi tai saurin riƙe masa ƙafa. Babiy ji yake shima kamar ya fashe da kuka ya huta kawai. Ya dawo ya durƙusa gaban Ummu tare da riƙo mata hannu, “Akan abinda suka faɗa munada mafita tunda yasha ban-ban dana baya Jumaima. Dan haka na gama yanke shawarar zamu bar garin nan dama ƙasar gaba ɗaya a daren yau insha ALLAH. Dan sun buƙaci izinin neman auren Iffah ne a gareni, sun kuma bani damar zuwa nai shawara daga nan har zuwa ƙarshen makon nan”. Kafin Ummu ta samu damar cewa wani abu sulalewa da faɗuwar Iffah a lokaci guda ta riski kunnuwansu. A tare suka zabura kanta jikunansu na matuƙar rawa da tsuma. Ummu ta fashe da kuka dai-dai tana ɗago Iffah dake wanwar a ƙasa taga ta koma yaraf alamar babu rai a tare da ita.....

.....Sosai kukan Iffah ya sake ɗaga hankalin Babiy. Dan tunda aka zuba mata ruwa ta farfaɗo ta haɗe kai da gwiwa. Suma idanu kawai suka zuba mata suna hawayen zuci, rikicin yana a kantane kawai, amma sune suka fita jin raɗaɗin a zuciya saboda ita akwai ƙuruciya tare da ita. A ganinsu bai zama lallai ma tana hange irin wanda su suke matane ba. Kusan mintuna talatin suna a haka, kafin Babiy yay ƙarfin halin miƙewa suma yay musu umarnin su tashi su koma ciki. Sai da taimakon Ummu Iffah ta iya miƙewa, har sun kusa shiga ɗakin ta tsaya, ɗagowa tai ta dubi Ummu ta juya ta dubi Baby hawaye na sauka da gudu bisa ƙyaƙyƙyawar fuskarta. “Bazamu gudu ba Babiy, zan aure shi....” Kaɗan ya rage Babiy yaci uban tuntuɓe saboda firgitaccen furicin Iffah mai kamanceceniya da gawurtaciyar sautin saukar aradu cikin tsakkiyar duhuwar dare. Ummu ma dai da taima Iffah sakin bazata ƙirji ta dafe dukanin idanunta na firfitowa..... Iffah ta share hawayenta da sakin murmushi a karo na farko. “Ummu! Babiy! ku kwantar da hankalinku, kar kuma ku ɗauka ba'a cikin hayyacina nake ba. Nasan burinku shine ku kuɓutar dani daga mutuwa, sai dai kuma a duk inda zanje ku sani tana tare da nine. Wannan azzalumin ba guje masa ya kamata ayi ba, tunkararsa ya kamata ayi. Kamar yanda kaka ya faɗa, a wasu lokutan gujema ƙaddara ba mafita bace sake kirawowa kai halaka ne. Amma tunkararta gaba da gaba ƙarfafa imani ne sannan jarumtace. Shin idan mun gudu kunada tabbacin zamu iya tsere musu bayan ƙasar a hanunsu take? Sannan idan mun tafi ina zamuje bayan babu inda muka sani sama da ƙasar Ruman. Fir'auna ma da yay nasa zamanin mulkin da ko kama kafarsa wannan shaiɗanin baiyiba UBANGIJI maida ANNABI MUSA (A.S) yay cikin gidansa ya rayu bisa ƙudirarsa da tabbatar masa shine mai iko akan kowa da komai. Azzalumin nan ba gudun masa ya kamata ayi ba, daƙilesa ya kamata ayi, domin idan ni kun kuɓutar dani, su sauran iyayen da zasu iya fuskantar makamancin halin da kuke ciki fa bayanku?. Babiy zanyi biyayya kamar yanda ƴan uwana sukayi, kuma ku sani da iznin ALLAH nice zan kashes........” Cikin rawar jiki Ummu ta zaburo tare da toshe bakin Iffah. Sai faman waigen bayansu take domin sanin dakarun Daular Ruman na ƙofa gidan har su biyar. Babiy ma gaba ɗaya kalaman Iffah sun sake rikitashi. Sai dai kafin wani cikinsu ya samu damar cewa wani abu ta shige cikin ɗakin. Idanu suka tsirama juna shi da Ummu harna tsahon mintina biyu, kafin Babiy yay ƙarfin halin janyewa yana mai jan nannauyan numfashi da barin wajen ya shige ɗakinsa. Da ƙyar itama Ummu ta sauke numfashin, har zatabi bayan Iffah sai kuma ta fasa ta nufi ɗakin Babiy ɗin itama.

Shigowarta dai-dai dayin sallamarsa waya manne a kunensa. Zaune takai a bakin gadon dake ɗakin dan inba haka ba zata iya zubewa ƙasa saboda yamutsawa da jininta ke mata. Jin sunan Baba da Babiy ya ambatane ya sata maida hankali garesa itama. Komai sai da Babiy ya zayyanema Kaka kafin yay shiru alanar saurarensa. Daga can Baba yaja nannauyan numfashi bayan gama sauraren surukin nasa mijin ƴarsa tilo data rage masa a raye. Sai kuma yay murmushin ƙarfin hali mai sautin daya isa har cikin kunnen Babiy. “Ni ma ina goyon bayan maganar Fareedatu. Da ace wani rai nada ikon hana tabbatuwar wasu daƙiƙu na gaban rayuwarsa masu tafe da ƙaddara da mutane da yawa sunyi rigakafi kafin cikar adadin waɗan nan daƙiƙu Muhammadu Zayyanu. Amma inaso ku tuna muɗin talakawansu ne, masu rayuwa a ƙarƙashin mulkinsu, bamu da wani ƙarfin iko akan hukuncinsu garemu ko kan ƴaƴanmu. Dan haka ku bita da addu'a kawai itama.” Tamkar yana gabansa ya jinjina masa kansa, tare da ƙoƙarin danne hawayen da yake na zuciya da ƙunarsu gara ace a zahiri suke zuba bisa ƙyaƙyƙyawar fuskarsa. “Shikenan Baba, amma furucin Iffah ya girgizani, ina tsoron kar zuciya ta ingizata tai yunƙurin aikatawa. Kisa fa! Koda bata aikata ba fitar wannan furucin zuwa kunen wani bayan mu ba ƙaramar magana bace” “Kar komai ya dameka Muhammad Zayyan. Ta faɗane kawai saboda raɗaɗi da takeji da kuma ƙuruciya, kai dai ka sanar dasu ka amsa daga nan zuwa kwanaki uku. Zan zo a amsa kuɗin auren da ni dama wasu a cikin zuri'an ka insha ALLAHU.........✍

ALLAH sarki Iffah kin bani tausayi🥲

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_ _LITTAFI BIYU: 600_ _LITTAFI UKU: 800_ _LITTAFI HUDU :1000_ _LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI ACCESS BANK 0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 90165991

Books biyar 1250CFA Books hudu 1050CFA Books uku 850CFA Books biyu 650CFA Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨ (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)

𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻

*_11_*

..........Iffah taci kuka matuƙa da ko maƙiyinta ya dubeta sai ya tausaya mata. Sai dai kuma iya juyawa su Babiy sun mata akan su gudu ta kafe akan itafa ta yarda zata aura *_Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdull-Majeed_*. Sosai hankalinsu yake ƙara tashi da tirjewarta. Gashi gaba ɗaya ta bikice musu ko isashen lafiya babu a tare da ita. A cikin wannan halin Babiy ya sake samun saƙon kira daga masarauta. Yana shirin tafiya sai ga Kaka. Duk sunyi matuƙar mamakin zuwan nasa, dan abune mai wahalar gaske a garesa zuwa inba da wani dalili ba. Sun tarbesa kamar yanda suka saba matsayinsa na uba. Bayan gama gaisawa ya kai dubansa ga Iffah dake kwance cikin bargo duk ta rame ta sake komawa fayau da ita, dama tun rasa ƴan uwanta ɗan jikinta ya zube, dan sam ba siririya bace. Iffah nada jiki murjajje daba za'ace mata siririya ba kuma babu mai sakata a sahun masu ƙiba. Duk da shekarunta har yanzu sunada ƙaranci ALLAH ya bata jiki na manyan mata da'a yanzu komanta yake ciff dai-dai da halittarta. Kaka ya ɗauke idanunsa a hankali tare da maidasu ga Babiy. “Muhammadu Zayyanu ka sakama ranka nutsuwa ka cire batun barin gidan dan bashine mafita ba. Hasalima tun randa ka amsa kiran masarauta wannan gidan zagaye yake da dakarun daular ruman harta inda baka zata ba. Ko'a tunaninka zasu tunkareka da wannan maganar su baka damar kanka sannan su koma gefe da tunanin kai bazakayi wani yunƙuri ba”. Daga Babiy har Ummu da Hanash kallon tsoro da mamaki sukema Kaka. Ya ɗan jinjina kansa alamar tabbatarwa. “Karku damu da yanda akai nasan wannan, kai dai kawai kaje ga kiran da sukai maka. Karka kuma nuna wani ja'inja kace ka amince musu suzo neman auren”. Kuka Ummu ta fashe da shi tana kallon mahaifin nata. Yay ɗan murmushi da ɗauke kansa tamkar bai fahimci mitake nufi ba. Ganin haka Hanash da idanunsa sukai jajur cikin cinkushewar harshe yace, “Amma kaka miyasa ka zaɓa itama mu sake rasata? Wlhy nayi alƙawarin in har itama ta salwanta sai na salwantar da ran Shahan-shan da wannan hanun nawa wajen ɗaukar fansa koda nima za ai gunduwa gunduwa da naman jikina!!”. “Ba kai ne zaka salwantar da ruhinsa ba, ni nan Fareedah bint Zayyan nice zan karya ƙarfin ikon azzalumi da hannuna, zan masa shaƙa irin wadda har sai ya mutu yana mai kallon tsakkiyar cikin ƙwayar idanuna Hanash Akhi”. Su duka zuba mata idanu sukayi, dan a yanda take maganar babu alamar tana a cikin hayyacinta. Babiy zaiyi magana Kaka ya girgiza masa kai alamar kar yace komai yaje kawai....

★Kamar yanda Kaka ya umarci Babiy ya amsa kiran masarauta kasancewar a wannan karon an bashi damar zuwa ne shi kaɗai batare da dakaru sun taho da shi ba. A yanda ya samu tarba zai tabbatar maka dama a jirace ake da zuwansa. Kamar ko yaushe a wannan karon ma baiga Tajwar ba, amma dai a karon farko na tarihin rayuwarsa an kaisa har cikin fadar Shahan-shan. Inda yaga tsantsar dukiya da ainahin karagar mulki ta Shahan-shan da akayita da zallar zinare. Hakan ba'abin mamaki bane ba, saboda girman Shahan-shan koda da diamonds akai kujerar mulkinsa bazai zama wani babban al'amari ba, sannan zinare arziƙin ƙasar su ta ruman ne da bare ma kanzo ya ci balle su ƴan ƙasa musamman Shahan-shan. Karo na farko da Babiy yaga karramawa daga dattijan daular ƙasar ruman. Waɗan da ko'a mafarki bai taɓa tunanin gani ba dan su ɗin ma ba'abune mai sauƙi ga duk wani talaka ganinsu ba kai tsaye haka. Duk da a birkicen da yake ALLAH sai ya saka masa nutsuwar yi musu bayani babu ko rawar harshe a tare da shi. Sun masa godiya da tabbacin a gobe idan ALLAH ya kaimu masu neman aure zasu zo. Karramawar da sukai masa ta matuƙar basa mamaki da tsayawa a ransa, sai dai ta wani gefe na zuciya ya tabbatar da sabuwar hanyar yaudarace kawai. Cikin danƙareriyar mota aka maidasa har gida badan yaso haka ba, yayi shiru ne kawai domin bin unarnin mahaifin matarsa, dan duk da bai taɓa ambatawa ba ga kowa ya jima da tsanar duk wani abu daya shafi masarautar daular ruman..

★A wannan dare Babiy yayi zaman kuka irin wanda ake kira kuka a zahiri da baɗinin rayuwa. Har yanaji bazai iya cigaba da yima kaka biyayya ba shikam, zai ɗauke Iffah su gudu daga ruman koda daga shi sai ita ne. Sai dai wani ɓangare na zuciyarsa na tunatar da shi maganar Kaka, yasan gaskiya ya faɗa, dan daular ruman bazata zuba ido na barinsa sakakai ba. Ajiyayyun dakarun dake a ƙofar gidansa ma kawai tabbaci ne.... A ɓangaren Ummu ma bata runtsa ba, sai dai saɓanin Babiy ita kwana tai tsaye tana gayama UBANGIJI damuwarsu da roƙonsa kariya da kuɓuta ga yarinyarta. Shi kuwa Hanash kwana yay ƙulla ta yanda zai halaka Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdul-majeed da kansa. Hakama Iffah nata shirin nada alaƙa dana Hanash. Ta gama yankema kanta koda zata mutu itama sai dai su mutu tare da Tajwar Eshaan. In yaso a binne gawarta a tsakiyyar ruman matsayin tarihin da za'a dinga tunawa.......

*_WASHE GARI_*

Washe gari data kasance safiyar laraba da misalin ƙarfe biyar na yamma sai ga manyan baƙi daga masarauta ruman. Baƙi masu ban mamaki, dan kuwa wasu manya ne a cikin dattijai masu faɗa aji a daular ruman. Sannan iyaye ga Shahan-shan ta ɓangaren jini makusanta sosai ga mahaifinsa. Tamburan masarauta da ɗunbin tawagar hadimai da jibga-jibgan motoci da suka ƙoshi ne suka tabbatarma da jama'ar anguwa dama maƙwaftan anguwar wace tawagace. Tuni mutane suka fara ƴar rige-rigen fitowa daga gidajensu bama idanunsu abinci. Sun tarbesu bisa jagoranci Kaka daya tsara komai tare da shimfiɗa kakkauran gargaɗi ga su Babiy. Bayan an musu masauki a cikin lambun Babiy ta ɓangaren garden ɗin da yayi domin farin ciki ga iyalansa aka cika musu gabansu da ƴaƴan itatuwa duk da babu tunanin ko zasu ci. Babiy, Kaka, da wasu dattijai biyu, ɗaya ta ɓangaren Babiy, ɗaya ta ɓangaren Ummu ɗan uwa ga kaka kenan suka zauna da su. Sun miƙa gaisuwa a garesu cikin mutuntawa da nuna tabbacin su ɗin masu ƙarfin iko ne a garesu talakawan ƙasan ruman. Hakan yayima dattijan matuƙar daɗi da yabama su Kaka. Dan haka suma suka nuna mutuntawa a garesu da basu ƙarfi matsayin waɗanda sukazo neman iri wajensu. Hakan ya ɗan bama su kaka mamaki amma sai babu wanda ya nuna. Sun gabatar da buƙatarsu, tare da bada duk wani abu na al'adar aure da ƙasar ruman ta tanada ninki wanda akanyi sau goma. Hakan sai ya ƙara firgita Babiy da bashi tabbacin yanda za'a salwantar da rayuwar ƴarsa ɗaya tilo data rage masa zai zama ƙololuwar girma fiye da ƴan uwanta kenan. To inbaice hakaba mizaice, dan dukiyar da suka kawo kawai tamafi ƙarfin ma sayen Iffah idan sayarwar zaiyi. Bai samu damar cewa wani abu ba, yadai cigaba da kukan zucinsa yabar su Kaka dayin abinda ya dace. A wannan zama aka ƙarƙare komai har ranar ɗaurin aure dama inda za'a ɗaura auren. Daga haka sukai addu'a suka tafi bayan an shigo da tarin kayayyakin da sukazo da shi. Daga Babiy har Ummu tagumi kawai sukai suna kallon kayan da aka baza a tsakar gida. Hakama Hanash da dattijan nan guda biyu da sai gobe zasu koma tare da kaka. Kaka kuwa na gefe zaune abinsa tamkar baima san mike faruwa ba a gidan. Yayinda Iffah ke can ƙuryar ɗakin Ummu kwance cikin zazzaɓi data yini da shi..... Washe gari su kaka suka wuce batare daya sake cewa uffan ga su Babiy ba akan komai. Yadai gargaɗi Babiy akan karya kuskura yace zai yi wani yunƙuri. Ya kuma sakasu killace dukkan kayan da aka kawo daga masarauta.....

★★★_______★

Tamkar da gayya cikin kanƙanin lokaci gari ya ɗauka Shahan-shan zai yi aure, alamu kuma sun nuna ana shiryama auren da shiri na musamman duk da amaryar bata kasance ƴar kowa ba. Hasalima ahalinta nada tabon Shahan-shan a dalilin salwantar ƴaƴansu biyu kafin ita. Dukkanin waɗan nan ƙananun magana na faruwane a bakunan mutane da ƙaramar murya, yayinda a kafafen ƴaɗa labarai da fejikan yaɗa zumunta babu mai iya ɗaga murya yayin faɗa sai fatan alkairi kawai. Mutane sun sake samun tabbacin wannan aure na musammne daya sha banban dana baya sakamakon fara shelarsa a kafafen yaɗa labarai domin gayyatar manya-manyan ƙasar kamar kowane Tajwar da jama'ar majalissarsa da talakawan garinsa. Da yanda ake wasu ƴan gyare-gyare a daular ruman wai duk na tarbar zuwan ranar ɗaurin aure ne. Humm abin faɗa taf bakunan mutane sai dai babu damar faɗar. Idan kuma suke ganin zasu sami wani ƙarin bayani an toshesa dan babu mai ikon shiga gidan Babiy a halin yanzu kasancewar zagaye yake da dakaru tako ina, acewarsu suna bama *_Zawjata-almilki_* tsaro ne. A cikin gidan kuma babu mai fita hatta da Hanash dake zuwa babbar makaranta... A haka kwanakin biki da suka rage suka cigaba da shurawa batare da wadda ake iƙirarin zama amaryar ta sake tada kai ta dubi wani abu daya shafi auren nata ba koda da kallo. Ta dake matuƙa tamkar ba itaba, hatta da ciwon dake cinta a tsaitsaye taki bada damar da su Ummu zasu fahimta. Ta ƙeƙashe idanunta ƙam ta hana hawaye zuba daga cikinsu. Ta tattare gaba ɗaya hankalinta ta maida ga rubuce-rubuce da babu wanda ya fahimci na minene a gidan, dan bata bari kowa ya duba mata shi. Sai dai ga duk mai hankali a duba ɗaya da zai mata zai fahimci tana cikin matsananciyar damuwa, mai busar da zuciyar mai ita da zai iya aikata komai da zai iya zama komai akan komai.. Kamar ko yaushe yau ma bayan ta kammala ayyukan gidan da take taimakawa Ummu da su ɗaki ta koma tana kukan zuci daya zame mata abokin rayuwa. A idaniyarta kam babu alamar ɗigon hawaye, sai dai raɗaɗin wanda ke kwaranya a zuciya ya maida launin idanunta sirkin ja har kana iya ganin jijiyoyi a cikinsa. Duƙufe take akan littafinta tanata rubutu da sakin ajiyar zuciya akai-akai. Ummu data shigo ɗakin takai zaune a kusa da ita tana mai tsurawa rubutun idanu na wasu sakanni. “Ibnati!”. Karan farko Iffah ta ɗago ta kalla Ummu duk da tun shigowarta ta jita sarai. Wani irin miskilin murmushi ta saki tare da maida kanta a hankali ta duƙar.. “Kina ganin laifinmu ko?”. Cak ta tsaya da rubutun data cigaba, sai kuma ta saki murmushi. Tsahon sakkani uku kafin ta ɗago ta dubi Ummu. Ta ɗan girgiza kanta da ajiye biron hanunta. “Ummuna idan har zanyi zargin wani akan wannan al'amarin to kaina ya dace na zarga. Ku ɗin nagartattun iyayene abin alfaharin kowane irin ɗa. Ni ya dace nazo muku da wannan maganar, domin nice na saka zukatanku a damuwa da ɗunbin fargaba. Na tabbata a kowane sakan, a kowane minti, a kowane awa, a kowane kwana na waɗan nan kwanakin kunayinsa ne cike da fargabar shuɗewarsu da gabatowar su. Kuyi haƙuri ku ƙara haƙuri ku gafarceni. Koda baku faɗamin ba, baku faɗama duniya ba nasan irin raɗaɗin da kukeji a zukatanku domin nima makamancinsa nakeji. Sai dai ina muku albishir Ummuna, koda zakuyi kuka a wannan gaɓar bazakuyi irin na baya ba. Na muku alƙawarin kukan ku zai kasance tare da dariyarkune a lokaci guda. Dan ruhina sai ya amso muku diyyar su Nina Arfa kafin yabar gangar jikina. A duk randa saƙon mutuwata zai riskeku insha ALLAHU zai riskekune tare da na mutuwar azzalumai. Dan haka ina roƙonku kar kuyi baƙin ciki a wannan karon, zaku sadaukar da ruhin da zaije muku yaƙin neman ƴancin kai ne ku da al'ummar ƙasar ruman.....” Kai Ummu ta shiga jujjuyawa hawaye na kwaranya a idanunta, “Ibnat...” “Na roƙeki kar kice komai Ummuna, albarkarki itace mafi ƙololuwar buƙata ga ruhin daya daɗe da zama cikin tahin gawa. Ƙaddarata rubutacciya ce tun daga alƙalamin da idan yay rubutu babu wani duster dake iya gogesa”...........✍

ALLAH sarki Iffah, ALLAH ya baki damar yaƙi irin wanda ya dace da fatanki na alkairi🙏🏻😭

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_ _LITTAFI BIYU: 600_ _LITTAFI UKU: 800_ _LITTAFI HUDU :1000_ _LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI ACCESS BANK 0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 90165991

Books biyar 1250CFA Books hudu 1050CFA Books uku 850CFA Books biyu 650CFA Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨ (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)

𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻

*_12_*

Readers Also Read