Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul - Chapter 53
Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul Chapter 53: Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul Chapter 53. Shiru baice komai ba, dan zuciyarsa tafasar kishi…
4,132 words
Shiru baice komai ba, dan zuciyarsa tafasar kishi take har yanzu akan wanna kalmar, tafi komai tsaya masa a zuciya fiye da abinda Miran Jasim din ya aikata masa dan ya jima da sanin dama suna farautar rayuwarsa. Sai maganar rashin fitowar sunan Miran Arshaan shima na masa kaikawo, kamar zai mata magana akan hakan sai kuma dai ya hadiye kayansa da tunanin ko Miran Jasim din ne kawai ya fiddo mata da nasa hali. Amma in bai manta ba ranar a kalamanta ta masa nuni ne da mutane biyu ko yace fiye da daya. Hakan na nufin bayan Jasim din akwai wani kenan. To miyasa ta boye? Bashi da mai basa amsa baya kuma bukatar son ji da gareta yanzu dan ransa duk babu dadi yake ji.Itama da kanta ta fahimci hakan, dan fuskarsa a tsuke take fiye da sanda suka fita kotun. Sai duk take jin kuma babu dadi. Dan haka kawai take jin tausayinsa. Idan har zai shiga damuwa saboda halin wancan karen uncle din nasa, yaya zai kasance kuma a randa zai san mahaifiyarsa da kanta ke halaka masa matan aurensa da duniya ke kallonsa a mai halakasu tsahon shekaru. Kai kai wannan al'amarin fa na taba mata zuciya why sosai matuka. Ajiyar zuciya ta dan sauke a hankali, sai kuma ta kai hanunta saman lallausan gashin sajen fuskarsa ta shafa. Murya can ciki ta ce, "Kayi hakuri? Ka amsa da hannu biyu jarabawace. Badan UBANGIJI baya sonka ba ya jarabeka da su. Shi kansa mulkin ma da kake kai ai jarabawa ce. Kai numfashinmu ma kansa jarabawace a garemu, dan UBANGIJI ya azurtamu da shine domin yaga zamu kasance masu bin dokokinsa ne ko kuwa masu bijire masa".
Idanunsa da ke lumshe tun sanda ta daura hanunta saman fuskarsa ya bude a hankali, sunyi zajur fiye da yanda ya shigo da su a dan birkice. Hannun ya kamo yana kallonta, cikin tsananin kasala ya daura lips dinsa a tsakkiyar tafin ya sumbata. Sai da ta matse jikinta tsabar la jininta yay wata irin yamutsawa har brain. Yunkurawa tai da nufin tashi a jikinsa ya hanata hakan, sai ma fuskarta da ya kamo cikin tafukan hannunsa ya manne lips dinsu waje guda. A tare suka saki ajiyar zuciya Iffah na rumtse idanu da karfi. A tsorace take matuka,amma ta danne ta karfin tsiya domin taimaka masa ya samu nutsuwar zuciya kamar yanda Mammy ta mata nasiha akan a duk sanda taga ya shigo da fushi tai kokarin gain ta cire masa wannan fushin da damuwar ta hanyar jansa jikinta da hira da raha ko nasiha. Idan kuma ya nuna bukatar wata hidimtawarta ko ita ta fahimci akwai abinda ke sakashi shagala ko kwaranyewar damuwarsa da wuri to tazama jaruma wajen aikatawa kota bashi hadin kai. Tunanin a iya abinda yake yi din baza'ai gaba ba ya sata sakar masa jiki harta fara bashi hadin kai. Gaba daya ta sake rikita masa lissafi, dan abune da bai zaton samu da ga gareta ba anan kusa haka. Tuni idanunsa sun rufe ya juyesu a gadon ya shiga yamutsata yanda yake so cikin nutsuwarsa, dan a rayuwa komai na Tajwar Eshaan babu gaggawa a ciki, koda kuwa yana a wani yanayi ne da zai iya canjawa sai kaga a zahirance babu wanna canjin a gaggawa garesa. Dan nutsuwa da kasaita a jinin jikinsa take yawo da harbawar bugun zuciyarsa. Jin al'amarin ya fara zarce karamin tunaninta tuni ta fara son kwatar kanta. Sai dai kuma babu hanyar samun wanna damar da ga jarumin ,Shin yaya lafiyar giwa da ma. Balle kuma ita da kanta ta balle likin. Duk yanda taso tuna masa dinkin dake a tare da ita babu alamar yana ma iya jinta balle fahimta. Burinsa kawai yake kokarin cimmawa a cikin rufewar idanu..
(* Tsun-tsun da ya ja ruwa (?))
***
Da karfi, karfin karfi yake buga kansa a bangon dakin kurkukun mai tsananin duhu da ta iya karamin windown kawai ake iya gain dan ziririn haske. Gaba daya zuciyarsa ta bushe, zafi yakeji a cikinta mai tsananin tururi dake kona zuciya. Shi shi Jasim ibn Abdul-majeed Aliy Qutb ne wata karamar yar iskar yarinya yar cikin cikinsa tai sanadin kawowa cikin kurkuku. Shi Arshaan da ya koya sanin kansa a wajensa zai yima cin amana? Shi hadiminsa da ya dauka tsahon shekaru yana kyautatama zai ci Amanarsa a gaban makiyansa. Wace irin wannan, mai tsananin duhuwa da babu lissafinta a cikin duka lissafe-lissafensa. Ta yaya shi Jasim in Abdul-majeed Aliy Qutb zai yi irin wannan faduwar bakar tasan a gaban karfin ikon dan makiyansa kuma makiyinsa.
Cigaba da buga kan yake da karfinsa yana ihu mai tsananin karaji da ya saka masu tsaron dakun kurkukun nasa da Tajwar Eshaan ya bada umarnin bama tsar mai tsananin tsauri tsora.Cikin karfin hali daya a cikinsu ya dan leko, ta dan hasken da ya hasko da ga karamin windown ya hango fuskar Miran Jasim da tai wani irin jage-jage da jini dan ya fasa goshinsa.A zabire yay baya yana zazzaro idanu. Yan uwansa ya sanarma, babu bata lokaci sukai kiran shugaban jami'ai suka sanar masa dai-dai da yanke jikin Miran Jasim da jini ke rinjayarsa va fadi kasa....
Rungumeta yay tsam-tsam a cikin jikinsa idanunsa a lumshe. Jin kukanta yake har tsakkiyar zuciyarsa. Dan kuka take sosai fiye dana daren shekara jiya kasancewar yau fami yay akan ciwo.
"Ni ka kaini wajensu Ummu".
Ta fada cikin kuka. Yanda tai magana tana sake barke masa da kuka ga hawaye shabe-shabe harda su majina ya sa yaji dariya na yunkuro masa. Kamar ba yanzu ta gama iyayi a kotu ba,dan duk abinda ta dingama Miran Jasim akan idonsa ne tsaf. Amma jiba yanzu a dan abinda bai taka kara ya karya ba ta koma abin tausayi.Ya fahimci sai ya dage matukar dagewa akan dorata a irin layin da yake bukata ta hau inba hakaba ragguwa za'ai, bakinne kawai cike da zance da tsiwa. Bashi da burin sake wani auren bayan ita, dan haka dolene ta shirya karbarsa a duk sanda yazo. Murmushin da ke neman kufce masan ya hadiye da kyar da saka hannu yana goge mata fuskar data kwabe da hawaye. Cikin dadisashiyar muryarsa data kara komawa can kasan makoshi a fusge ya furta, "Am sorrybazan kara ba".
"Wlhy zaka kara, ranar ba sai da kace bazaka sake ba amma yau ka kara, ni bazan sake zama a sashen na a kasheni kwana na bai kare ba". Ta kara barke ma sa da kukan tabara.
Yanzu kam kasa rike dariyar yayi, dole ya Murmusa har jerarrun fararen hakwaransa masu da siririyar wushirya na bayyana a zahiri Bashi da zabin da ya wuce sake rungumeta a jkinsa tsam-tsam yay murmushinsa iya san ransa. (Shi kam wannan Fitinanniyar yarinya ALLAH ya bashi, kuma yana so da kaunar abinsa fiye da zaton mai hasashe). A zuciyarsa yake maganar yana bata sumbata masu kyau a wuya. Kafin ya mike ya dagata cak zuwa bathroom. Idanunta ta rumtse sosai da kankamesa ita a dole karya gammata jiki kar kuma ta gansa itama.
Gashi yay mata mai kyau bayan ya duba yau baiyi barna ba dan ciwukan wancan ranar ma sun warke sai abinda ba'a rasa ba, taimaka mata yay tai wanka, hawaye kuwa da ya ga ba dainawa zatai ba bai sake ce mata komai ba kansu. Da zasu fito cewa tai ita why bazata iya ba sai dai ya dauke ta. Baice komai ba, illa murmushi da yay a zuciyarsa ya dauke ta cak suka fito tana faman tura masa karamin bakinta.Ga idanu sunyi luhu-luhu na kukan da tasha.
"Idan baki bar turamin bakin nan ba zan maimaita ni babu ruwana". Ya fada yana tsane mata laimar ruwan kanta da towel. Narai-narai tai da fuska zata sake masa kuka ya daura yatsansa saman bakinta ya ce, "Shilli!! Harda kuka ma". Babu shiri ta hadiye abunta da maida bakin da sauri. Murmushi ya saki da cigaba da tsane mata gashin…. kiran da ya shigo ta sashi dakatawa su duka suka dubi wayar, kamar bazai daga ba dan har tana gab da tsinkewa sai kuma ya kai hannu ya dauka batare daya matsa da ga gabanta ba ko dauke towel din da ga kanta.
Cikin girmamawa shugaban jami'ai ya shiga gaishesa da ga can, a takaice ya amsa masa murya a dake kamar bashine ke hidimtawa yar yarinya ba. Da ga can shugaban jami'ai ya kara nutsuwa sannan yay masa bayanin abinda ke faruwa. Shiru kamar bazaice komai ba kafin ya nisa a dan fisge da maganar nan tasa kasa-kasa ya ce, "Doctor Afif ya je ya dubasa a cikin kurkukun". Daga haka ya yanke kiran.
Kallonsa Iffah tai da jajayen idanunta, gaba daya ya sauya kamar bashi ba ya koma mata Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdul-majeed da ta fara gani a sashen Mammah. Muryarta a dashe saboda kukan da tasha ta ce, "Miya faru?".Kamar bazai kulata ba yana cigaba da goge mata kan tsahon minti biyu kafin ya motsa lips da kyar ya furta "Jasim"……….✍️
DAUDAR GORA Book 2 Chapter: 58
Bayan sallar isha'i cikin dauriya Iffah ta amsa kiran Malikat Haseenat. Tafiya take cikin dabara dan ko yau din ma dai tanajin zafin, ga zazzabi tun dazu yaki saukar mata. Ita bata san randa zatai sabo da wannan al'amari ba kamar yanda ya fada mata dazun. Ta dan yamutse fuska da cigaba da tafiyarta a hankali, dan ita kadai ta fito babu wani dan rakkiya, Tajwar Eshaan ma yana massalaci tunda ya tafi sallar magrib bai shigo ba. Kadan-kadan take dan cin karo da hadimai, duk da ko'ina na masarautar zagaye yake da haske ba ganeta suke ba, sai dai yanayin shigarta kansa su mata gaisuwar girmamawa kamar yanda suke ma duk wani ahalin masarautar babba ko yaro. Hannu ta dinga daga musu kawai dan batajin yin magana har takai sashen Malikat Haseenat din. Nan din ma bawani sun ganeta bane sosai, dan sanda take kokarin shiga falon Malikat Haseenat din da sauri Banou tai niyyar dakatar da ita. Sai dai mi, kallon ido cikin ido da sukai ma juna ya sa Hadima Banou din zubewa kasa cikin rawar jiki da tsananin kaduwa. Har taune harshe take wajen gaida Iffah da ke mata kallon tsaf kamar mai son gano ainahinta. Sai da ta mula dan kanta ta yamutsa fuska da watsa mata harara. "K! Har yanzu baki daina bibiyar mutane ba ko?Karki fasa ina tafe kanki ai". Ta fada tana wuceta batare data amsa gaisuwar tata ba.
Jagwab Hadima Banou ta zube zaune a wajen zuciyarta na wani irin masifar harbawa. Sosai take tsoron wannan baiwar ALLAH, dan ita kadai tasan mi take ganowa tattare da ita. Ta jima a wajen kafin ta mike cikin rawar jiki ta fita. Can baya ta nufa cikin karamin garden din Malikat Haseenat da takan hutawa, da ga cikin wasu dunkulallun fulawoyi ta zaro yar tukunyar kasa da bakinta ke daure da kyalla an nannade da zare. Warware zaren tai har yanzu jikinta na rawa, abubuwane a daddaure ciki kamar tsokokin nama, haka ta shiga fiddosu tana ware wasu a kasa, sai da ta gama zabowa ta maida sauran ta sake daurewa ta ajiye. Wanda ta fiddo din kam ta kwance hudu ta sakesu, biyu da ga ciki tasa a baki ta cinye tana faman tande lips. Duk abinda take yi tanayi ne tana waige-waige, har dai ta kammala ta mike da sauri ta fito..
Tarba ta mutuntawa Iffah ta samu da ga Malikat Haseenat. Dan an shiryama zuwan nata da zuwa na musamman kamar yanda akan yima Tajwar Eshaan idan zai zo. Iffah har mamakin hakan tayi, dan bata taba tunani ko tsammanin tanada kimar da wani zai mata haka musamman idan akai dubi da shekarunta da kuma gidan data fito na talakawa. Malikat Haseenat dame binta da Kallo kuwa a kallo daya da taima takunta ta fahimci halin da Iffah take, idanu ta dan lumshe tana mai jin tausayinta, dama tasan bazai iya hakurin barinta ta warke yanda suke bukata ba ai, dole ne sai ta dage ma yarinyar da abubuwan da zasu taimaka mata batare data dinga jigata ba. A zahiri kam hannu ta ware mata alamar tazo gareta. Iffah da ke murmushi kanta a kasa ta karasa a nutse ta ko shige jikin nata. Wata irin tagwayen ajiyar zuciya ta dinga saukewa a jajjere haka itama Malikat Haseenat din. Kusan minti biyu suna a haka kafin ta zaunar da ita kusa da ita gab-gab dan har cikin rai take jin kaunar yarinyar nan.
Duk yanda Iffah ta dinga nuna jin kunya Malikat Haseenat bata barta ba sai da sukaci suka sha a tare cike da farin ciki, suna tsaka da cin abinci ne ma Daneen Ammarah itama ta shigo. Cike da girmamawa Iffah ta gaisheta, ta amsa mata da kulawa cike da so da kauna. Bayan sun kammala hadimai suka gyara wajen, Malikat Haseenat kuma ta bama Iffah wata yar madara a kofi mai dadin tsiya data kasa gane ma wace irin madara ce, dan an mata wasu hadi ne na musamman. Dagawa daya ta shanye ta ajiye kofin, karamin bowl dake dauke da hadadden hadin zuma da dabino da kwa-kwa dama abubuwan da bata sani ba nan ma ta bata tare da karamin cokali a ciki da zata dinga diba kadan-kadan tana ci.
"Hafidah!"
Malikat Haseenat ta kirata a hankali. Amsawa Iffah tai kanta a kasa. Mammah bata damu ba ta cigaba da fadin, "Kin san miyasa nace kizo ki sameni?". Kai Iffah ta girgiza mata ta ce, "A'a Jaddah"., Malikat Haseenat ta kalla Daneen Ammarah suka dan sakarma juna murmushi kafin ta sake maidawa kan Iffah. "Magana nake so muyi mai muhimmanci dan nasan bazakimin karya ba".
"Insha ALLAHU Jaddah".
"'Dazun a zaman shari'ar can kinyi wata magana ce data kasa barin raina akan ganin gawar Zawjata-almilk da kikai. Shin ko akwai wasu alamomi da kika gani tattare da ita? Ko kuwa kisa ne kawai na kai tsaye da raunika?"
Shiru Iffah tai da dan mamakin tambayar a ranta, ta kasa gane wann al'amarin, shi mai matan yace bai taba ganinsu ba, bayanan suke mutuwa, kuma ko gawarsu baya gani. Shin itama Jaddah din du matsayinta a masarautar bata taba gain gawarsu kenan amma har wadan can rubabbun su Jasim ke iya gani ko mi?
''Ibnati"
Daneen Ammarah ta katse mata tunani. Firgigit ta kawo numfashi da kallonsu, sai kuma ta maida kanta ta risinar tana mai sauke ajiyar zuciya. "Jaddah zan fada miki duk abinda kike bukatar j, amma dan ALLAH ki gafarceni nima zanyi wat tambaya".
"Bismillah".
Malikat Haseenat ta fada kai tsaye cikin bata dama. Numfashi Iffah ta dan fesar ta nisa. Kafin tace, "Jaddah na kasa ganewa, shin duk matansa da suka rasu kuma baku taba ganin gawarsu ba kamar yanda shima yace bai taba gani ba kenan?".
Daga Malikat Haseenat har Daneen Ammarah kallon Iffah suke mamaki fes a kan fuskokinsu. Daneen Ammarah ta ce, "Shi Abni din ya fada miki bai taba ganin gawar matansa ba?".
"Har suna raye bai taba ganinsu ba ma yace".
Kallon juna Daneen Ammarah da Mammah sukayi, sai kuma duk suka dubi Iffah da itama su take kallo ta gefen ido. "Tofa babbar magana".Cewar Malikat Haseenat. Daneen Ammarah ta ce, "Babbar magana kam, ta gaske ma Mammah. Ni kaina ma ya sake kullewa akan Al’amurin”.
"Dole ne kam Ammarah. Amma Hafida-ti bara na baki amsar tambayarki, masarautar nan nada tsare-tsare irin nata da ka'idoji, a ciki harda zama iya huruminka, dan haka ni bana a cikin masu hurumin kan duk abinda ya shafi Zawjata- almilk na Hafidi, wannan hakkin mahaifinsa ce, ni kuma nawa hakkin a kansu yake tunda sune matan dana. Wannan ne dalilin da yasa ban taba gani ba. Kema da kike ganina tsaye a kanki saboda matsalolin da aka samu ne da har yasa ita Bushirat janyewa da ga al'amuran ki, ni kuma naga bazan iya yardawa ba na dauka na adana".
Cike da gamsuwa Iffah ta jinjina kanta. Sai kuma ta cigaba da basu bayani akan abinda suke bukata. Riko hanunta Daneen Ammarah tai kamar a razane ta ce, , "Cizon maciji kuma?". Cike da mamakin yanda suka razana Iffah ta gyada mata kai. "Eh Mamy saran maciji. Sai dai da alama kafin ma hakan tayi yunkurin kare kanta da har ya zamto dakin ya kasance a harmutse".
"Ya rabba! Uwa. Mammah tabbas wannan alama ne na UWA. Itace, itace azzalumar bata barmu ba. Bata barmuba Mammah, tana raye why tana raye". Daneen Ammarah ta fada tana rike kanta da ke mata wani irin sarawa ta fara layi kamar zata fadi. Da sauri Iffah ta mike ta riketa cikin tashin hankali. Hakam Malikat haseenat duk ta rikice, dan ta fahimci ma tsahon shekaru data shude ce da ga garesu ke neman dawowa ga Ammarah din kanta. Da kyar suka iya samu suka kwantar da ita, a tare suka dinga tofa mata addu'oi. sannu a hankali ta fara lafawa tana sauke ajiyar zuciya a jajjere sai kuma barci ya dauke ta mai nauyi.Ajiyar zuciya Malikat Haseenat ta shiga saukewa da sauri- sauri, yayinda Iffah sunan uwa da Daneen Ammarah ta ambata ke faman mata kaikawo kirjinta na wata irin bugawa..
"Jaddah waye UWA kuma?".
Kalmar ta subuto da ga bakin Iffah batare da ta shirya hakan ba. Idanu kawai Malikat Haseenat ta zubama Iffah batare da tace komai ba. Har Iffah ma ta fidda rai da ga cewarta. Dan tsahon kusan mintuna biyar kafin Malikat Haseenat din ta nisa. "Uwa. Uwa.. uwa…. sanin wacece uwa na kunshe ne a cikin labarin masarautar nan Hafida-ti. Labarine mai tsaho da ya zama a cikin manyan labaran da suka kasance da ZUCIYAR ahalin Aliy Qutb gaba daya. Duk da ya shude, shudewa ta tsahon shekaru da muke tsammanin karnin ya shafe da fatan daina tunashi koda a cikin tarihinmu da alama hakan bamai yiwuwa bane."
"Jaddah idan na dage akan son na sani ban shiga cikin hurumin daba nawa ba? Dan ina mutukar so da zumudin na sani din".
Murmushi mai ciwo Malikat Haseenat ta yi, sai kuma ta zuba idanunta akan Iffah tana dan jinjina kai. "Baki tsallake huruminki ba Hafida-ti, tunda kin rigada kin zama mu mun zama ke. Sai dai dokar wanna zuri'a ta dade da shardanta goge wanna tarihin domin mantashi da daina tunashi garemu har abada..." taja nannauyan numfashi mai hade da ajiyar zuciya. "Da zan iya wofantar da bukatarki da nace karki sake tambaya. Amma inaji a raina bazan iya ba, dan inhar dai da gaske baya ce ke son dawowa ta maimaita kanta kamar yanda nake hasashe a kanki tun zuwanki masarautar nan dolene labari biyu ya dawo a lokaci guda domin kasancewarsu cikin juna duk da raina namin wasi-wasin taya hakan zata kasance bayan anyi ruwa ne an dauke kasa ta shanye kayanta?"
Sam Iffah bata gane cudaddun kalaman karshe ba, dan haka ta tsurama Malikat Haseenat idanu kawai ko kyaftawa babu.Murmushi Malikat ta sakar mata tare da lumshe idanu ta bude a kanta lokaci guda. "Idan har zan samu warwarewar lissafina zan sanar miki abinda kike son sani Hafida-ti. Zan sanar miki tarihi da tushen kasancewar uwa a cikin tarihin wannan DAULA kamar yanda kike bukata".
A hankali Iffah ta saki murmushi mai kayatarwa maimaita kanta kamar yanda nake hasashe a kankii tun zuwanki masarautar nan dolene dayan biyu ya dawo a lokaci guda domin kasancewarsu cikin juna duk da raina namin wasi-wasin taya hakan zata kasance bayan anyi ruwa ne an dauke kasa ta shanye kayanta?"
A hankali Iffah ta saki murmushi mai kayatarwa da jinjina kanta. "Nagode sosai Jaddah, ALLAH ya kara girma da lafiya mai albarka da tsahon rai".
"Amin".
Malikat Haseenat ta amsa tana gyara zamanta cikin wheelchair dinta da fuskantar Iffah da kyau……….✍️
A muma to bara mu gyara zaman. @) 🥱😂
DAUDAR GORA Book 2 Chapter: 59
."Labarin ya fara ne tun zamanin iyaye da kakanni da ya kasance akwai karancin ilimin addini. Ba a daular ruman kawai ba hatta da sauran dauloli da ma talakawan kasar RUMAN kowa yasan ani matukar imani da tsafe-tsafe a karnikan da suka shude. Zaki samu duk talaucin mutum duk yawan arzikinsa yanada wani boka da ke fada masa motsinsa ko wani abu dake tunkarosa, ko bashi Sa'a a abinda zai yi ko yake yi. A lokacin da addinin musulunci ya fara kutsowa cikin wanna kasa tamu idan akaji ka amsa sai an halaka ka, dan kuma kai shugaba ne to fa za'a tubeka a koreka kai da duk ahalinka. ALLAH sarki, masu shiga musulunci da masu hidimar gain an shiga sunsha matukar wahala a wancan karnin. Komai ya canja da cajawar labarin wanna kasa dalilin wani fari da akai na tashin hankali, ruwan dake zagaye da wannan tsuburi da kasar RUMAN take ya zagaye komai hadda gidaje da dukiyiyi har ma da rayuka. Ba kasar ruman ce kawai ta girgiza ba, Africa da ma duniya baki daya wannan al'amari ya matukar girgizasu, inda aka shiga kawo mana dauki ta kowane bangare. Wannan shine mafarin fara samun canji, domin a cikin wanna yanayin ne tarin bayin ALLAH mabiya addinai daban-daban suka fara yakin ganin sunja ra'ayoyin mutane da dukiyoyi da wasu abubuwan kyale-kyale na duniya, harda masu yimusu tayin binsu kasashensu suyi rayuwa. Babu mai son yabar kasarsa tushensa dan haka mutane suka fara bijirewa, sai ko wani bawan ALLAH ya basu goyon baya mai suna SHEHU UTHMAN DAN-FODIYO da ga kasar NIGERIA. shine ya tabbatar musu kasarsu itace yancinsu, itace gatansu, itace martabarsu, su tashi da karfin kwanji su gyarata yayi alkawarin tallafa musu da karfin jiki da ga tawagarsa. Zantukansa sun kayatar da kowa sun saka karsashi a jikin mutane, musamman yarima mai jiran gado Miran Aliy Qutb. Ganinfa Miran Aliy Qutb ya amshi wannan tunatarwa tun ya samu mabiya. Abu mafi daukar hankalin mutane SHEHU UTHMAN DAN-FODIYO ya kasance MUSULMI ne, hakama almajuransa da sukayi masa rakkiya, amma sai bai taba cema wani dole sai ya shiga addininsa ba ko masa tayi da wata dukiyar da zai shigan, ya dage dai tukuri da taimakonsu yana ibadarsa. Hakan sai ya shiga birge mutane tuni suka fara karbar musulinci. Sai kuma cikin kankanin lokaci kasashen musulunci manya irinsu Saudi Arabia suma suka fara yunkurowa, mabiya addinin islam suka hada karfi da karfe wajen hidimtawa wanna kasa ta RUMAN ta sake ginuwa ta komawa kan kafafunta. A cikin abinda bai wuce shekaru kalilan ba abubuwa suka cigaba da canjawa acewar munada tarin tattalin arziki ka davan-daban. An dauki babban mataki akar ruwan dake zagaye da mu, aka kuma kara fadada kasar ilimin addini ya yawaita, kafirci ya fara nisa a cikin al'ummar mu. Masu bautar gumaka da yin imani da bokaye duk suka fara janye jiki, wasu bokayen ma da kansu suka dinga ajiye kayan tsafe-tsafen suma suka koma ga ALLAH. Masu taurin kan cikinsu kuwa sai suka bijire da jan tunga, wasun su suka koma dazuka wasu kuma suka koma yi a boye."
Ta dan ja ajiyar zuciya da daukar ruwa takai bakinta. Kafin ta cigaba da fadin, "Uwa diyar wata bokanya ce babba a wannan masarautar,bayan mahaifiyarta da ake kira bokanya Ta-bunu ta mutu itace ta gajeta. Shekaru masu yawan gaske da suka shude itake tafiya da jan zaren yi da hani na wannan gida harta mutu yarta ta gajetan (wato Uwa). Ta kuma gajeta ne ana gab da samun wannan iftila'i da ya faru,lokacin da abun ya faru tana farkon fara jin dadin kar fin ikonta dan tafi mahaifiyarta hatsabibanci. Domin kuwa komi za'ayi sai an sanar mata tace ayisa, idan ko ta hana akan dakata koda ana sonshi. Hatsabibiya ce matuka. Dan duk da mahaifin Miran Aliy ya yarda yan kasarsa suyi addinin da suke so shi ya kasa rabuwa da Uwa har ALLAH ya masa rasuwa Miran Aliy Qutb ya zama Shahan-shan. Shi dai men hirans da farbn amma hahmands yaso bijirewa da farko, amma babu wanda yasan miya faru hakan ta gagara ya cigaba mata biyayya akan abinda ta shardanta kota hana. Na takaice miki zance fa ikon Uwa sai da ya kasance itake kamar mulkar kasar ruman dan har shi Shahan-shan din sai da cewarta yake cewa ga talakawansa. Haka yay mulkinsa ya shude Miran Abdul-majeed dansa, mijina ya karbi kasar ruman. Muma mun cigaba da kasancewa a karkashin say na UWA, sai dai abun na matukar damuna kasancewar nayi ilimin addini mai zurfi. A lokuta da dama idan tace ai abu nakan kalubalanta har sai na fahimtar da Tajwar Abdul-majeed illarsa. Duk bayan wata uku takan saka ayi yanka na bakaken shanu da karnuka da rakuma wai tsarine na wannan daula. Takan tilasta daya daga cikin yayan Shahan-shan a aura mata wani talakan kasa ko bawa ta samu ciki ta hainu,da zaran ta samu cikin dole kuma ya saketa. Shi kuma abinda aka haifa zai cigaba da rayuwa a cikin masarautar bashi da wani karfin iko da shi. Sai dai kin san wani abun mamaki da ya fara jan ra'ayina harna bijirema wanna al'amarin?".