Kenza eBookz

Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul - Chapter 54

Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul - Chapter 54

Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul Chapter 54: Daudar gora book 1 & 2 by billyn abdul Chapter 54. Jiki a sanyaye Iffah ta girgiza mata kai. Nisawa…

4,417 words

Jiki a sanyaye Iffah ta girgiza mata kai. Nisawa Malikat Haseenat tayi da cigaba da fadin, "Duk wadan nan yaran da aka haifa ta wannan hanyar basa zarce shekaru bakwai a duniya suke rasa ransu. Na fahimci hakane ta hanyar bibiyar tarinhin wanna masarautar kasancewa mutum mai son sanin tarihi. Lokacin dana fara kalubalantar yankan da akeyi duk bayan wata uku na bakaken shanu da karnuka ne tasa Abdull-Majeed ya auro mahaifiyar su Jasim. Ban damuba dan wannan bashine gabana ba, ban kuma canja daga bijirewata ba da cigaba da nusar da su akan sanin ma'anar yankan nan.Alhamdullah naci nasara, naci nasarar dawowar hankalin wasu jikinsu akan hakan aka fara ja"injar a daina a canja da wani abu na sadaka bakwai sai yankan ba. Yayinda wasu kuma ke fadin ai yankan ma sadaka ne tunda raba naman ake wa talakawa da hadimai. A cikin tsaka da wannan dambarwa na haifi Haysam. Mahaifin mijinki kenan. Haysam yaci wahala sosai da cututtukan da aka gagara gane kansu, sai dai ALLAH ya kaddara kwanakinsa basu kare yana yaro ba. Bayansa na haifi Ammarah, Ammarah ta zo da wasu abubuwan ban mamaki a rayuwarta tun tanada karancin shekaru. Sai Waheeda, auta Nayyar, zuwa lokacin matan Abdul-majeed mu hudu ne, kowacce kuma ta haihu da shi, akwai maza kuma akwai mata. Bari na sake dawo miki akan yanka, bijirewata da mabiya dana samu yasa aka daina a zahirance,ashe a boye ana cigaba da yi batare da sanin Tajwar Abdul-majeed da ni ba. Sai da wata ranar juma'a da yamma fadan yara ya hada Jasim da Haysam shi da yan uwansa suka masa taron dangi Ammarah ta shiga dukan,mata kai da akai ta yanke jiki ta fadi ,abinka da yaro sai duk suka hadu kanta suna ihu ganin jini ta hancinta. An kinkimota an kawomin tana zubda wanna jini, cikin ikon ALLAH sai ban rude ba na fahimci habo ne. An bata taimakon gaggawa jini ya tsaya har tai barci, sai dai lokacin da take farkawa bayan sallar magriba sai ta tashi a firgice. Koda na tambayeta bayan na mata addu'a ta samu nutsuwa sai ta sanar min mafarki tayi ana yanka shanaye da yawa bakake da karnuka da rakuma. Ga mahaifinsu cikin bacin rai an dauresa da rufe masa baki. Da farko ban dauki wanna mafarki nata a komai ba, sai kawai nace tai addu'a mafarkine kawai. A'a bayan kwana biyu da hakan tai wata faduwa nan ma sai habo, akai mata magani dai ta kwanta sanda zata farka a firgice, nan mana tambaya ta maimaita min wancan dai mafarki da tayi. Abin ya dan fara damuna sai dai ban maida hankali ba. Da ga ranar kuma bata karayi ba har ta cika shekaru kusan goma sha biyar a duniya.Da ga lokacin kwanaki dai-dai ne bazaki samu Ammarah ta tashi a firgice a barci ba, idan ka tambayeta tace ba komai. Ban taba matsa mata ba duk da abun na dan damuna, sai dai ina binta da addu'oi akoda yaushe ita da sauran yan uwanta. Abu ya cigaba da faruwa daban-daban daga Ammarah naban mamaki, bamu fara sarguwa da ita ba sai a randa aka samu gawar Nayyar a cikin ruwa. Abubuwan data dingayi sai da ya tada hankalin duk wani mai numfashi a cikin masarautar nan, inda ta dinga ihu da jadada sai ta dauka fansar jinin dan uwanta. Anyi-anyi kuma ta fada miya faru take irin wannan magana taki cewa komai, harma abin ya ban haushi na tattarata na kyale, a kuma lokacinne ita kuma ta tattara ta tafi makarantar koyan aikin likitanci a kasar America, Sai lokaci-lokaci take zuwa mana hutu ta koma. Ta maida hankali sosai saboda tana so, gashi kuma makarantar da aka sakata makarantace ta musamman. A shekarar da take kammalawa a shekarar yayansu Haysam yay aure, hakama kanwarta Waheeda, anyi-anyi ta fidda miji itama tace a barta ba yanzu ba, ita akwai wanda take jira. Sam bamu takurata ba, dan tanada karamin jiki sosai, shekarun nata ma dai ba wasu bane masu yawa, in bama mun fada ba zaka dauka Waheeda ce babba gareta. Anyi bikin Haysam da Waheeda Ammarah ta cigaba da aikinta a cikin clinic din masarautar nan da kuma karatunsa a cikin wannan kasa ta ruman, a sati kuma takan zagaya jahohi biyu sau biyu domin bada gudunmawarta ita da wat kungiya da suka hada. Tsahon shekaru hudu babu haihuwa da ga matar Haysam, tadai samu ciki sau daya ya lalace bama ya haura wattani uku ba, harma Waheeda itama acan bata haihu ba. Nata bai damu kowa ba, amma na Haysam an fara kanan magana akan sai ya kara aure kasancewar shine Miran mai jiran gado. Bai son kara aure, amma mahaifinsa ya takura masa, ya nema damar a basa lokaci zai nemo da kansa. Anan kam sai ya bashi dama. Ba'a rufa watanni uku ba kuwa ya kawo sunan Bushirat, ta kasance kanwa ga wani abokinsa da sukai karatu, amma suma yan nan kasar ruman din ne, sannan kuma manyan mutanene dan mahaifinta babban malami ne masani sosai. Kyakykyawar nasabarta yasa bamu wani tsananta bincike ba akai biki. Sai dai me itama shiru, dan garama Ashwaq ta taba bari sau daya. Shekarar Bushirat biyu a masarautar nan itama babu labari sai ma Ashwag din ce dai ta kara bari, dan haka aka sashi ya kara auro Danish-Ara, cikin ikon ALLAH Danish-Ara bata rufa wata guda ba sai ga ciki da ga Bushirat. Kowa yayi farin ciki sosai musamman ma shi da ita da mu kammu, hakama Ammarah kai kacema ita keda cikin, dan gaba daya ta tattara ta koma sashen dan uwanta tana kula da Bushirat. Bamu hanata ba, duk da rashin aurenta na damunmu, sai dai mun fahimci akwai matsalar junnu tattare da ita, dan haka muka dage da addu'a gareta kawai"………..✍️

DAUDAR GORA Book 2 Chapter: 60

."An haifi ciki lafiya, kuma da namiji sanbalele da yaci suna *_Eshaan_*, Eshaan kyakykyawan yaro mai lafiya da ban sha'awa ga kowa, ga shiga rai. Wata irin makauniyar soyayya Bushirat ke nuna masa har takai Ni kaina sai nayi da gaske nake ganinsa, hakan da take yasa Waheeda yimata tas kafin ta dan canja aka dinga kawomin shi nan. Ya taso yaro mai wayo, miskili da baka iya gane abinda yake so ko baya so sam. Shi ko irin abokan wasan nan na kuruciya Eshaan bayayi, yafi so ya zauna shi kadai shiru ko yayta karance-karancen abubuwa musamman a litattafan tarihin wannan daula da suka shude. Sai dai yana matukar son wasan doki da basket ball, da wasan takobi, idan kuma yana tare da Kakansa ko mahaifinsa zaki dingajin maganarsa ko babu yawa. Al'adar wannan masarauta da Miran mai jiran gado ya kai shekaru bakwai zuwa goma ake kaishi can wani boyayyen waje ya rayu har sai girmansa, ko kuma sarki ya zabi murabus kafin ya mutu shi ya daurasa, idan kuma bazaiyi murabus ba za'a dawo da shi cikin masarauta da iyalansa dan su basa wuce shekaru ashirin basuyi aure ba gaskiya. Shiyyasa sai kiga yaro ya taso mahaifinsa bai wani tsufa ba. Da farko Bushirat ta tsaya tsayin daka akan baza'a rabata da danta ba, nima kuma na bata goyon baya dan banji dadi ba sanda aka rabani da Haysam, sai dai was tsurface-tsurfacen tsafi da Uwa ta fara kawowa a kansa yasa nace a kaisan, ta nuna bakin cikinta sosai akan hakan da nayi, har tai gargadi mai girma akaina da cewarta ni na cika shiga mata hanci ni da zuri'ata. Sam wani kurarinta da tsubbace-tsubacenta basa bani toro, dan da UBANGIJI NAna dogara akoda yaushe. Dan haka na cigaba da dagewa har sai da Tajwar Abdul-majeed ya yarda aka kaisa kasar Cuba. Haukane kawai Uwa da Bushirat basuyi ba, sai dai kamar ALLAH ya saka tsorona ne a zukatansu ni ban sani ba. Dan duk hatsabibancin uwa iyakarta borenta a kaina a bayan idonane, taci alwashi sosai a kaina dalilin dauke Eshaan har ma abin ya dinga daure mun kai amma sai na daukesa aikin banza dan bata isa mun abinda bai kasance jarabawata ba. Komai ya lafa kowa ya cigaba da harkokinsa aka shiga watan azumin ramadan. Azumi nada kwanaki bakwai sai Tajwar Abdul-majeed ya sameni akan zan masa rakkiya ya duba Eshaan da ga can muje umrah da shi bayan salla sai mu maidasa Cuba mu dawo gida. Ban kawo komai a raina ba na shirya mukai wannan tafiya har da Haysam. Munyi-munyi Ammarah ta bimu taki, ashe lokacin ta samu wani saurayi ne ya kuma mata alkawarin dinga zuwa shan ruwa wajenta. Sai da na nuna bacin raina kan rashin son binmu 12:47 Sai da na nuna bacin raina kan rashin son binmu a zatona bata son taje ne su hadu da yar uwarta, sai da ta zauna ta fahimtar dani. Naji dadi sosai, dan tace tana son bashi damane ta karanci halayyarsa anay in bikin sallah ai aurensu kawai. Muni farin ciki da hakan, mun kuma mata fatan alkairi."

Malikat Haseenat tai shiru tana jan ajiyar zuciya, yayinda Iffah kejin kaguwa matuka da son jin cigaba, sai dai batayi magana ba har sai da Mammah ta cigaba dan kanta bayan tasha ruwan zam-zam dake gabanta.

"'Tafiyarmu itace mafarin kaddarar Ammarah,sannan itace mafarin yakice uwa da ga wannan zuri' ar, sannan itace mafarin yin kuka garemu dama duk al'ummar kasar ruman, sannan itace mafarin hawan Haysam karagar mulki matsayin madadi ga mahaifinsa. Bayan wucewarmu umarah, bisa yarjewar Jasim UWA ta sakasu yin yankan nan dai dana sa Tajwar Abdul-majeed bijire mata akansa, ta kuma basu umarnin daura auren daya daga cikin kannensu da wani bawa ko cikin talakawan gari. Son zuciya da sanin makomar dan da ake so a samar ko ya ta wannan hanyar suka aurar da Ammarah ga dan mai dinka kayan dokin masarautar, domin a ranar sunzo kawo kayan kwalliyar dokuna na bikin al'ada dake tunkarowa. Babu waya a lokacin balle ta sanar mana ko wani ya sanar mana,hasalima sunyi auren ne a sirrance sai ita da suka dauka suka kai wa yaron bisa tirsasashi Ya kusanceta in ba hakaba zasu kashe dukkan ahalinsa da shi kansa. Dolene ya tsorata ya aikata abinda suke bukata yana kuka itama tanayi. Shi UBANG|JI mai hikima ne, sun taya ya kuma isar musu bisa ikonsa, badan baya son Ammarah da wannan bawan ALLAH bane, ba kuma dan yana son nuna Uwa a saman kokarin mu bane. A'a wannan itace kaddararsu. Kuma ALLAH ya rubuta sai an samar da wannan abun haihuwar ta wannan hanyar. Sai dai alhmallh, ina godema ALLAH da sake gode masa, dan kuwa koba komai ta hanyar biyan sadaki da sheda aure abinda ya farun ya faru. Mun dawo muka tadda Ammarah a wani irin yanayi, dan kuwa ta birkice musu matuka, a lokacin kowa ya sake tabbatar da iska a tare da ita. Muni kuka ni da Mahaifinsu da dan uwanta sosai, mahaifinsu kuma ya fusata a wannan karon har ya kulle Jasim a kurkuku tare da duk wanda suka goya masa baya akan aikata aikin, yayi kiranyen uwa amma taki zuwa, an sa malamai domin mata kiranye nanma taki zuwa. Har takai an hada da bokaye irinta amma amsa daya suke bamu tafi karfinsu. Hankalinmu ya tashi matuka, musamman bayan wasu watanni da ciki ya bayyana ga Ammarah, gashi lafiya taki samuwa gareta, tama koma wata iri kamar mai ciwon hauka, ta daina magana da kowa, sai kuka,abinci ma sai an tsaya kanta take ci.ALLAH ne kawai ya zama kariya ga wannan ciki har zuwa ranar haihuwarsa. Tajwar Abdul-majeed ya sakka a nemo masa mijin da suka aura matan, sai dai anje ba'a dace da samunsu ba, wai sun bar asalin kauyensu a wani dare. Iya nema da bincike kuma ba'a dace ba dole aka hakura. A daren wata juma'a ALLAH ya sauki Ammarah lafiya, sai dai tasha matukar wahala kafin ALLAH ya kawo haihuwar. Ta haifo yarinyarta mace kyakykyawa, sai dai babu ta inda take kama da ita sai tambarin tabon tawadar ALLAH da zuri'ar wannan gida ke da ita, bamu san mahaifinta ba kuma balle musan ko da shi take kamar. Mun amsheta hannu biyu, sai dai zagaye take da addu'ar neman kariyar UBANGIJI da ga sharrin uwa. A randa aka haifi yarinyar a ranar ALLAH ya kawo wani mai magani. Malikat Haseenat ta saki murmushi mai ciwo.Tare da fadin "kin san wani abu?" kai Iffah da ke sharar hawaye ta girgiza mata. Malikat Haseenat ta sake sakin murmushi. "Mai maganin nan hatsabilin kansa ne, dan kira daya yayma uwa a randa ya cika kwana uku a masarautar nan a take ta bayyana gabansa gaban kowa wujiga-wujiga. Ya tabbatar mata shi ba azzalumi bane, da sai ya wahal da rayuwarta ta yanda bata isa sake numfashi a duniya ba, amma ko'a yanzu bazai kyaleta ba sai ya nakasa rayuwarta ta yanda bazata kara tunanin cutar da Wani ba. Ya sakata ta warware duka wani tsafi data aikata zagaye damu batare da mun sani ba, sannan ya bude dukkan surukanta a gabanmu yay mata korar wulakanci da gargadi mai tsaurin gaske. Sosai ta dinga kuka da neman gafara da tabbatar masa ta zubda makaman yakinta bazata sake ba a barta taci gaba da rayuwa damu amma yaki saurarenta. Majiya karfin hadimai aka saka suka kwasheta zuwa can tsakkiyar dokar jeji mai tsananin rintsi da hadari suka jefar da ita. Wannan shine mafarin barin uwa tare damu, sai dai kuma a wannan dare ALLAH yay ma jaririyar da Ammarah ta haifa rasuwa, washe gari shima Shahan-shan Abdul-majeed yabar duniya sakamakon bugawar zuciya da saran macijin da aka rasa tushensa, sai kuma ya kwana da tashin hankalin abubuwan da Uwa ta dinga sakasu sunayi na shirka da yanda bayan ya tsawatar wasu suka zagaye sunayi ciki harda dansa Jasim. Abdul-majeed ya rasu, uwa ta shude,jinjirar Ammarah ta koma. Haysam ya zama Shahan-shan. Bayan duk faruwar wadan nan abubuwa da shudewarsu zukata suka hakura abubuwa suka fara komawa dai-dai. Saurayin nan da Ammarah ta shirya gabatar mana matsayin miji ya dawo da burin aurenta duk da ba'a boye masa komai da take ciki ba. Yace yaji ya gani, dan ko a baya da ya janye jikinsaJasim a samesa da gargadin karya sake zuwa an mata aure. Bayan kuma yaji an saketa dan auren kwata-kwata na sati biyu ne ya sake dawowa amma aka hana mishi ganinta ma kwata-kwata. Ammarah taso bijirewa, dan har lokacin bata dawo dai-dai ba, amma naita lallabata da mata nasiha ni da yar uwarta hatta hakura aka daura aure. Sai dai sam auren bai wani je ko'inaba ta fito, sakamakon wata sabuwar kaddarar data afka mata, a duk sanda mijinta zaije gareta sai a sauya halittar matancinta ta koma ta namiji.Dole babu yanda zaiyi ya rabu da ita ta dawo gida, daga nan bata sake aure ba, daga nan bamu sake jin labarin uwa ba, daga nan bamu sake jin labarin bawan ALLAHn nan da ya taimake mu ba akan Uwa ba, daga nan Jasim ya nuna mana ya tuba, sha'anin mulkin Haysam ya cigaba da tafiya a tsaftace dan a masa gargadin nisantar duk wan mushiriki akan al'amurin mulkinsa..

Hawaye sosai Iffah takeyi na tausayin Daneen Ammarah, da tausayin su Malikat Haseenat dan labarin nan ya matukar girgizata, al'amari haka kamar a wasan kwaikwayo, wannan wace irin duniya ce mai cike da son zuciya. Kowa burinsa ya kasance a sama, mai nasara bisa nasarar dan uwansa, kai kai rayuwar gidan sarauta dabance, dabance a cikin duk wani rikicin gidaje da zuri'arsu. YaYanda Iffah ke kuka sai Malikat Haseenat ce ta koma lallashinta. Sai da ta tabbatar ta samu nutsuwa sannan ta mikar da ita. "Hafida-ti, kinga tashi ki tafi dare yayi maybe ma mijinki nacan na jiranki".

Cikin share hawaye Iffah tace, "Ai bai san ma na taho nan ba".

Idanu sosai Mammah ta waro da fadin "Ya ALLAH, aiko kinyi laifi, maza wanko fuskarki muje na miki rakkiya to".

Bata musa ba taje ta wanko fuskar, Malikat Haseenat ta mika mata wata yar kyakykyawar jaka tana murmushi. "Kije da wannan, duk abinda ke ciki kiyi kokarin dinga amfani da shi kamar yanda na rubuta, ki yawaita shiga ruwan zafi har ki saba da daina jin ciwon".

Kai Iffah ta sunkuyar cike da jin kunya, sambatai tunanin Mammah din zata gane ba yau, musamman yanda take dauriyar dai-daita tafiyarta duk da zafin da take ji……..✍️

Hummmm babu abin cewa kam yau 🥱🚴

DAUDAR GORA…..I Book 2 Chapter: 61

Tunda suka shigo idanunsa kyam a kansu, yana zaune a falo zama na kasaita da izza da jiran ta inda zata bullo. Tun bayan dawowarsa sallar isha'i ya duba bai ganta ba. Shegen miskilanci ya hanashi tambaya har sai bayan kusan awa daya sannan ya bincika ta cctv camaras. Anan yaga fitarta harma da nufar sashen Malikat Haseenat ita kadai ko tsoro babu tattare da ita duk da darene. Yayi tsammanin zuwan bamai jimawa bane, amma sai gashi har yay wanka yaci abincin dare yay yan ayyukansa babu labarinta, harya kwanta da tunanin zai iya shareta sai hakan ya gagara, gangar jikinsa da zuciyarsa suka tabbatar masa bafa zai iya rayuwa babu mahadinsa ba. Shine ya dawo falo yay zaman jiran ganin ta inda zata bullo kusan awa daya kenan.

Gaba daya sai Iffah taji ta tsure da kallon nasa, dan haka ta koma da baya-baya ta labe a bayan Malikat Haseenat. Idanunsa ya dauke daga kanta ya maida ga Malikat Haseenat din shima. Cikin dan motsa lips dinsa ka dan ya furta, "Barka da dare Jaddah".

Amsa masa tai cike da kulawa, tare da juyawa ta kamo hanun Iffah da ke labe a bayanta ta maidota gabanta. "Ga matarka nan tane tare dani tun dazun, ALLAH ya tashemu lafiya". Daga haka ta saki hannun Iffah ta gara kekenta ta nufi Elevator.

'"ALLAH ya huta gajiya". Ya fada a hankali yana dan lumshe ido da risinar da kansa alamar girmamawa a gareta. Shiru falon bayan tafiyarta babu wanda ya sake kwakwkwaran motsi. Shi ya zuba mata idanun nan nasa masu kaifi, ita kuwa tana tsaye a inda Malikat Haseenat ta barta kanta a kasa tana wasa da yatsun hanunta, tsigar jikinta sai yamutsawa take dan har cikin jininta takejin tasirin kallonsa a kanta. Sun kwashi mintuna masu dan tsaho a haka kafin ya mike, gabanta yaje ya tsaya, ta rumtse idanu da karfi a tunaninta saukar mari ko wani abu dai mara kyau zata ji daga garesa. A mamakinta sai jin tattausan tafin hannunsa tai a saman nata ya zare jakkar hanunta, cikin takun nan nasa daddaya cike da izza ya rabata ya wuce.Numfashin da ta rike a kirji da makoshinta ta saki da karfi, sai kuma ta bude idanunta tabi bayansa da kallo har ya bace ma ganinta. Dan tarin dake neman rike makoshinta ta fara, dole ta nufi dining room ta samu ruwa ta sha. Daga haka takai zaune tana sauke numfashi. Sai da ta dan samu nutsuwa sannan ta tashi tabi bayansa tana addu'a a ranta.

Bata da tabbacin a inda yake, dan haka kawai ta nufi inda zuciyarta ke raya mata da fatan ALLAH yasa ba'a nan din yake ba. Sai dai kuma da alama ta taki rashin sa'ar. Dan tana shiga taci karo da shi zaune a kan gado da lap-top kan cinyarsa. Dakin babu haske mai karfi, sai hasken screen din laptop dinne ya haske kyakykyawar fuskarsa ma'abociyar kamewa da kwarjini. Sum-sum ta wuce hanyar bathroom tana dan turo baki. Sai da ta gama tsaftace kanta ta fito cikin bathrobe, yana a yanda ta barsa, hakan sai ya bata damar tsayawa ta bayansa ta shirya cikin kayan barci masu dan kauri da turarruka. A take kamshin dakin ya sake karfi. Fahimtar kamar fushi yake ya sata takowa inda yake cikin sanda, zaune takai gefensa amma ya share abinsa bai ko nuna ya san da zamanta ba. Cikin dan bata fuska da jin haushi sharetan da yay ta zame ta kwanta tare da dan ture lap-top din tasa kadan ta daura kanta a cinyarsa ta kwanta. Da kyar ya iya cigaba da rike kansa yaki kulata. Ganin ya cigaba da aikin dai ya sata kurama fuskarsa idanu, sai kuma ta kai hanunta kan kwantaccen gashin kumatunsa ta fara masa tafiyar tsutsa. (@) Yarinyar nan da tsokale-tsokalan masifa kike * ). Yayi kokarin ganin ya danne ya cije amma aikin na neman gagararsa, baima san sanda ya cije lips dinsa da rumtse idanunsa da dan karfi ba.

" ALLAH kayi hakuri bazan sake ba.ALLAH banyi zaton zan dade ba na samu Mammy batajin dadi ne fa".

(Yarinyar nan sai ta kasheni zata huta) ya fada a zuciyarsa dake faman bugawa da sauri-sauri cikin kaikawo. A hankali ya janye hannayensa dake sarrafa lap-top din ya daura na damar kan nata dake cigaba da shafa fuskarsa. Rikesa yay yana kokarin son gain ya janye amma sai tai wani irin juyi ta maida fuskarta saitin cikinsa ta sakalo dayan hanun nata a bayansa ta kankamesa.

'"Kasheni kawai ki huta" ya fada cikin subutar harshe jikinsa na saki gaba daya.

Iffah da bata fahimci ita mima yake nufin ba ta kyalkyale da siririyar dariya har yana jin dumin numfashinta a kan Fatar cikinsa. Ita a nata shirmen kankamesan da tai ne yaji zafi. "dan na kasheka dawa zan zauna?". Ta fada cikin dariyar tana kara cusa kanta jikinsa. Dole ya ajiye lap- top din ya kai kwance tare da dagota gaba dayanta ta hau saman jikinsa. Fuskarsa take kallo cike da dakewa kamar yanda shima yake kallon tata idanunsa a shanye. "Miyasa baki son a zauna lafiya?". Ya fada a hankali yana sake kankance idanunsa cikin nata. Idanun ta juya tana shagwabe fuska da dan cuna masa lips dinta. "Toni mi nayi? In dai zuwa wajen Jaddah ne ai nace kayi hakuri".

Dariya maganar ta bashi amma sai ya gimtse baiyi ba, ya dan tabe baki da tsatstsareta kaifafan idanunsa. Cikin dan dage gira "Har na kai ki?".

"Hu'um, ni a suwa kuma, kana kallon kanka a mirror kuwa da kyau?. Badan kar ace nayi karya ba sai nace kafi kowa kyau a kasar ruman". Harga ALLAH ta bashi matukar dariya yanda ta fadi maganar cike da yarinta, yayinda zuciyar sa tai wani irin shiga farin ciki, domin kuwa bawai yafi kowa kyau din bane kamar yanda ta fada a zahirance, ya fahimci ta fara caukar karatunsa son sa ya fara shiga zuciyarta. Domin abinda kake so ne kawai kake ma kallon kasancewarsa a sama dana kowa. Shi kansa duk da yasan akwai kyawawan da suka fita ganinta yake samada kowa saboda kawai ita kadai yake so,kyawuntane kawai ke kayatar da shi. Bai fahimci murmushi yake ba sai da yaga yanda ta kura masa ido. Ya dan waro idanun waje alamar miye kuma, ita kuma sai ta girgiza masa kai tana murmushi da dan kauda idonta dake cikin nashi."Murmushi na maka kyau, gashi kuma baka son yi".

Hannayensa duk biyu ya doro a saman bayanta ya sake matso da ita ta kwanto jikinsa sosai, fuskarsu ta koma gab-gab har hancinsu na gogar na juna. "A komai k ta dabbance my sohaa".

"Kaima haka ai".

Ta fada tana dan sumbatar lips dinsa, sai tai saurin jan jikinta zata sauka dan sai da tai babban kokari wajen masa kiss din, amma kunya take ji. A hankali ya rikota bayan ya fisgo numfashinsa da ya nema kufcewa da kyar.Mirginasu yay suka koma saman hannayensu suna fuskantar juna, batare da jiran wani abu ba ya manne lips dinsu waje guda..

🥱🏃‍♀️Anfi karfin alkalamina anan.

Babu alamar wasa tattare da shi, da ga tsayen da yake a kofa yana dubanta a yatsine ya ce,"Kifadi abinda zaki fada ina jinki, dan bazan wuce minti ashirin ba anan".

Rai bace Ameera Haifah ke duba Miran Arshaan mai maganar, tai karamar kwafa da tabe baki," Arshaan kenan, idan kana ganin Kanada mafitar da zata iya kwabemin ne ma,dan har da kai sai dai ka shirya mu duka zata kwabe Dar harda kai, idan har ban tsira ba da ga yarda ka maida Jasim kaima zan bude maka aiki ne. Zan kuma tabbatar maka na fika iya makirci dan mace sunana idan ka manta".

"hhhhahh! Ni kike tunanin zaki iya budema aiki Haifah? to ina baki shawarar fita a hanyata da ga yau, in ba hakaba why zan kasheki na binne gawarki a cikin masarautar nan kuma na kashe banza".

"Oh really? To Dan ALLAH ko zaka gwada ne? Nace ko zaka gwada kashenin muga!!!".

Tai maganar cikin tsananin hargowa tana wani hahhankada kirji a gabansa. Wani irin tafarfasa yaji zuciyarsa nayi, dama a wuya yake, a fusace ya kaima wuyanta wani irin shegen shaka na tashin hankali. Cikin kankanin lokaci manyan idanunta suka sake yowa waje ruku-ruku, ga kakarin mutuwa da ta fara da mutsu-mutsun ganin ta fisge hannunsa da ga kan wuyanta. Sai dai kuma hakan ya gagara, dan karfinsu ba daya ba. Tafiya ya dingayi da ita cikin rufewar ido har jikin bango, ya kara matse wuyan da karfi tare da wajigata ya buga kanta jikin bango. Wata irin wahalalliyar kara ta fasa da ta jawo hankalin Jasrah dake daki kwance ta farka tana nemansa, dan su suna'a falon baki ne kasancewar cikin shigar badda kama Ameera Haifah tazo a nufin bako tasa amintaccensa imata iso saboda baya daga mata waya yanzun. Sai da yazo yaga itace. Gaba daya idon Miran Arshaan da alama ya rufe, dan tuni ya sake jijigata ya buga a bango, jini ko ya samu hanya ya balle.

lya karfi da budewar murya Jasrah ta daddage ta kwalla wata irin kara na firgita, dan ganin jini ya wanke fuskar Ameera Haifah ga Mijinta shake da wuyarta sai ta dauka ta mutu.Wani irin wancakalar da Haifah Miran Arshaan yayi yana duban Jasrah data yanke jiki ta fadi. Har rige-rigen shigowa hadiman masu tsaron sashin keyi, ganinfa abinda ke faruwa tuni wani ya firgita ya kyalla a guje ya sanarma jami' an tsaron gidan dan wannan faninsu ne...✍️ DAUDAR GORA Book 2 Chapter: 62

...…….Tofa dan-dan-dan, da alama dama irin wannan damar Iffah ke jiran samu, dan cikin kankanin lokaci duk da darene masarautar ta dauki dumi, yayinda aka kwashi Ameera Haifah da Jasrah zuwa asibiti, Miran Arshaan kuwa da jikinsa ke tsumar toro gaba daya ya gama gigicewa, dan sai zuwa yanzu ya dawo a hayyacinsa. Tuni kuwa ya tsure da ganin abinda ya aikata, sai kawai ya bige da borin kunya. Sudai jami'an babu wanda yace da shi komai,sun tattara komai akan sai zuwa da safe za'a kai maganar ga Shahan-shan. Abu dai mafi daure kai shine miye tsakaninsa da Ameera Haifah din har haka a irin wannan tsohon daren, dan a kala fa karfe biyu na dare kenan.

大大

Readers Also Read