Kenza eBookz

Daudar gora complete - Chapter 32

Daudar gora complete - Chapter 32

Daudar gora complete Chapter 32: Daudar gora complete Chapter 32. Har lokacin kwanciya barci Iffah bata samu wata makamar riƙewa na tunkarar Tajwar Eshaan…

2,620 words

Har lokacin kwanciya barci Iffah bata samu wata makamar riƙewa na tunkarar Tajwar Eshaan ba. Hasalima bata da tabbacin a inda zata samesa. Tambayar hadimai kuma tamkar gazawace a gareta matsayinta na Zawjata-almilk. Kusan ƙarfe ɗayan dare tana tsaka da kai kawonta da faman jan tsaki saƙo ya shigo wayarta. Kamar zata share sai kuma ta ɗauka dan koba komai kullum a cikin tsumayen ji daga su Babiy take. Mamaki ya sata buɗe saƙon da hanzari ganin Malikat Bushirat. _Ina alfahari da kasancewar ki tare da gudan jinina Ibnati. ALLAH yay miki albarka, yanda kika zama sanadin yaye damuwata kema ALLAH ya yaye miki taki yanzu na gama waya da shi_. "What!!". Iffah ta faɗa cikin ɗan zabura tana sakin wayar akan carpet. To mi hakan ke nufi? Ita da batama gansa ba taya har yay kiran mahaifiyar tasa da har ta gamsu itace sanadi. "Anya mutumin nan kuwa ba ifiritin aljani bane?". Ta faɗa a zahiri tana waige-waige a ɗakin da tunanin ko dai akwai camara, to inma camara ɗin ce itada sukai magana a sashen Malikat Bushirat ma ta ina camara ɗin zatai tasiri kenan...

Har waye war gari babu nutsuwata tattare da Iffah akan wannan al'amarin, dan ko barcin kirki batayi ba sam. Sai dai tuna a'a yau zata bar sashen ya saka mata ɗan jin sassauci ka ɗan a zuciyarta. Tana ko idar da sallar asubahi ta taattara kayanta waje guda tsaf tana jiran gari ya ƙara haske ta kama gabanta duk da kuwa wata zuciyar na bata shawarar take akan zuwa Tajwar Eshaan wai ko zata fahimci wata gaskiya saɓanin wadda zuciyarta ke tabbatar mata. Amma dai ta dake dan tana buƙatar damar keɓance kanta ko zata samu nutsuwa. A bisa al'adar masarautar kamar yanda ake kai Zawjata-almilk turakar Shahan-shan haka ake zuwa a ɗakkota cikin tattali da giramamawa tare da manyan ƙyaututtuka a randa ta cika kwanaki bakwai cif. Kowa ya ɗauka tunda an kai Iffah ba bisa ƙa'ida ba baza'ai wannan al'ada ba gareta musamman yanda tama karya doka a kwana ɗaya ta fito. Ga kuma a yanda masarautar take harmutse kwana biyun nan. Amma sai Malikat Haseena ta bama kowa mamaki ta hanyar haɗa komai na al'ada da akeyi, tare da mukulllin zabgegiyar mota ƙirar zamani da masu hidima har guda goma, da tarin turarurruka na musamman, Daneen Ammarah da tsaffin dake da hurumin gudanar da al'adar a masarautar suka yima sashen Tajwar Eshaan tsinke cikin busar sarewa mai tabbatar da isar da saƙon manufar al'amarin.

Tofa wannan fa shine an tsokalo tsuliyar dodo. Dan kuma masu rajin faɗa aji tuni sun sake buɗe shafin caccakar Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed da kakar tasa Malikat Haseena kan basu damu da ɓatan Sayeed Khairul-Bashar ba. Ko kuma ma dai sun san komai ɗin da gaske. Wannan al'ada ta sake saka jikin Iffah mutuwa da shiga ɗunbin mamaki na gaske, har aka maidata sashinta babu alamar tana cikin cikakken tunaninta ma. Bin dai kowa take da ido tamkar gunkiyar da aka ƙirƙira domin tarihi...

★Ashe duk wan can ƙarami ne a abin mamaki da Malikat Haseena ta tanada a yau ɗin. Dan ƙarfe tara na dare da kanta kamar yanda tayi akan Iffah ta sake jagorantar rakiyar ɗaya cikin biyun Zawjata-almilk dake gidan tun kafin zuwan Iffah. Duk da bata haɗu da Tajwar Eshaan ba yau bata dawo da ita ba kuma dan acewarta zai ma gaji ne itama ya kulata idan ya gama zaman kulle kansa a ɗakin kamar yanda zukatansu ke basu sakamakon sanin hakan al'adarsa ce a duk sanda ransa ke ɓace. A wannan gaɓar kam kowa ya saki jiki waccan matsalar ta shuɗe tunda ga Iffah tai kwanakinta lafiya ta fito. Maimakon shiga fargabar rasata itama sai kowa ya ɓige da ƙananun magana akan rashin dacewar hakan. Yau ɗin ma dai malikat Haseenat tayi kunnen uwar shegu da su, yayinda Malikat Bushirat da Daneen Ammarah suka shiga halin mamaki da hukuncin na Malikat Haseenat a karo na biyu saɓanin dukkan shirye-shiryen su. A wannan karon kam sun yanke ƙuirin tun kararta suji ba'asi, sai dai sun barma safiya komai....

★★

Surutai akan ɗimuwar da aka wayi gari da shi a masarautar ne ya farkar da Iffah dake fashin salla ɗan barcin daya figeta, dama da ƙyar ta yisa sakamakon kwana da tai neman Sir Fawzan da Sir Ajmaal a waya amma bata samesu a online ba hakama a kira. Sai abinda ta karanta da yay matuƙar tada hankalinta a ɗaya daga cikin littafan da take nazarta akan Tajwar Eshaan. "Tabbas babu lafiya" ta faɗa a zahiri tana miƙewa zumbur. Har ta nufi ƙofa ta dawo da sauri, toilet ta shiga a gurguje ta watsa ruwa ta fito. Sama-sama ta kimtsa jikinta ta fito. Hadiman ta da alamun sanyin jiki ya bayyana a agaresu suka dinga zubewa gaisheta. Maimakon amsa ta jefa musu tambayar da ruɗani ya bayyana kansa a cikin idanunsu da jikkunansu lokaci ɗaya. "Mike faruwa a masarautar nan? Da alama babu lafiya?". Duk sun rikice babu alamar wani zai amsa mata. Sai kaɗuwa suke kamar masu jin sanyi. Halin da take ciki ya assasa mata jin zafin hakan ta daka musu tsawa. Sake firgicewa sukai, sai dai wajibi ne a gare su bin umarninta, dan haka cikin ƙarfin hali wadda ke matsayin amintatta a gareta ta sanar mata cewar an wayi gari da rashin Zawjata-almilk ne ta farko da jiya ta kwana turakar Shahan-shan sai Sayeed Khairul-Bashar shima da aka samu gawarsa a wani ɗaki cikin masarautar. Iffah da bata san da hakan ba ta ƙame ƙam alamar sumar tsaye ta wucin gadi ce ta risketa. Sai kuma hajijiya ta fara juya mata falon da hadiman, a hankali duhu ya dinga lulluɓe idanunta data kafa musu tabbacin bata cikin hayyacinta..........✍️

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*

*DAUDAR GORA Billyn abdul*

*KI KULANI hafsat xoxo*

*A RUBUCE TAKE Huguma*

*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*

*IDON NERA Mamuh ghee*

_LITTAFI DAYA: 400_ _LITTAFI BIYU: 600_ _LITTAFI UKU: 800_ _LITTAFI HUDU :1000_ _LITTAFI BIYAR: 1200_

_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_

_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_

_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_

_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_

_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_

_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

MARYAM SANI ACCESS BANK 0022419171

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

09033181070

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09166221261

*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*

+227 96 09 67 63

Books biyar 1250CFA Books hudu 1050CFA Books uku 850CFA Books biyu 650CFA Bookk daya 450CFA

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨ (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)

𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻

*_44_*

..........A hankali ta shiga ƙoƙarin buɗe idanunta da takejin sun mata matukar nauyi, sai kuma ta yunƙura ta tashi da ƙyar tana mai bin ɗakin da kallo. Dishi-dishi take ganin amintacciyar hadimar tata dake rukuɓe gefe ta zabga tagumi, _(An wayi gari da rashin Zawjata-almilk ne ta farko da jiya ta kwana turakar Shahan-shan sai Sayeed Khairul-Bashar shima da aka samu gawarsa a wani ɗaki cikin masarautar.)_ kalaman hadimar na ɗazun suka shiga dawo mata tiryan-tiryan a zuciya. Da karfi ta rumtse idanun nata da sukai jajur, ga kanta dake matuƙar sara mata kamar zai rabe biyu. Amma haka ta yunƙura ta sauka a gadon cikin ƙarfin hali da jarumta, dan idan batai amfani da wannan lokacin ba tabbas damarta ta kuɓuce mata kenan, batajin kuma zata sake samun wata cikin sauƙi. Zumbur hadimar ta miƙe itama tana mata sannu, bata iya amsa ta ba, sai nuni da tai mata ta je. Jiki a sanyaye ta fice, ita kuma ta jawo mayafi ya naɗama jikinta. Hadimanta dake falon farko duk suka miƙe, hannu ta ɗaga musu alamar bata buƙatar rakkiyar ta fice ita kaɗai dan babu yanda zasuyi. Da gaske masarautar a hargitse take matuƙa, duk da ba wannan ne karo na farko da aka rasa Zawjata-almilk ba, sai dai haɗi da mutuwar Sayyid Khairul-Bashar ta sake girmama ta Zawjata-almilk ɗin itama a wannan karon, da kuma tsallakewar Iffah da aka fara kaiwa babu abinda ya sameta. Cikin dabara da amfani da harmutsewar gidan tai amfani wajen kutsa kai sashen Shahan-shan. Zuwa yanzu fuskarta ba ɓoyayyar fuska bace ga masu tsaron sashen, dan haka babu wanda ya dakatar da ita sai ma gaisuwar girmamawa da suke miƙa mata duk da ganin nata ya basu mamaki. Su kansu hadimai masu girka abincin Tajwar Eshaan ɗin data samu a falo na uku saɓanin na karshe da ta san suna zama ganinta ya girgizasu, musamman daya kasance har yanzu ba'a fita da gawar Zawjata-almilk ɗin ba. Hasalima babu wanda yaga Shahan-shan har yanzu balle jin motsinsa. Kamar yanda tun a ƙasa bata tanka gaisuwar kowa ba anan ɗin ma bata kulasu ba dan ganinsu ya tabbatar mata anan abun ya faru kenan, ita wannan Zawjata-almilk ɗin a ɗakunan barcin falo na uku aka ajiyeta. Duk da bata san ya suke ba babu ko ɗar tattare da ita ta shige abinta inda take kyautata zaton ɗakunan barcin nan ɗin suke. Ido rufe take bin ɗakunan ɗaya bayan ɗaya, sai dai har kusan uku duk a rufe suke, bata gajiya ba ta cigaba sai a na biyar ta samu a buɗe. Cikin rawar jiki ta afka ɗakin, yayi kaca-kaca tamkar anyi dambe a cikinsa, dan wasu abubuwan ma duk gasu anan a fashe ƙasa, sai ɗigo-ɗigon jini ta wasu wajajen da dama. Idanunta suka sauka akan ƙyaƙyƙyawar budurwar da a shekaru zata iya zama sa'ar Arfa shimfiɗe a ƙasa ta jikin gado. Yanda gashinta da jikinta ke a birkice zai tabbatar maka da ta jigata matuƙa kafin ta rasa ranta, dan hanunta na dama dake kaca-kaca da jini riƙe yake da wata kwalbar filawar doco... Alamar ta riƙe domin kare kanta, amma duk da haka sai da akaci galaba a kanta. Iffah da jikinta ke karkarwa ta durƙushe hawaye na rige-rigen sakko mata, dan ji take kamar Fariha da Arfa ne take kallo kwance. Ta jima tana kuka akan gawar kafin ta zabura sakamakon maganganu da takejin suna tunkaro ɗakin, zumbur ta muƙe ta fara daukar video recording ɗin ɗakin har gawar, sai kuma ta ɗauka hoton gawar ta kowacce kusurwa. Jin shigowar za'ai da gaske tai saurin fara neman wajen ɓuya....

Miran Jasim, tare da Miran Arshaan, shugaban jami'an tsaron masarauta, Daneen Ammarah sai Malikat Bushirat da a wannan karon ta kasa haƙuri itama suka shigo. Sai da suka gama bin ɗakin kaf da kallo kafin su ƙarasa kan gawar. Shiru babu wanda ya iya magana a cikinsu har tsahon wasu mintuna kafin shugaban jami'an ya nisa. "Exactly kisan irin na baya ne dai babu wani banbanci gaskiya, da alama kuma tayi ƙoƙarin kare kanta itama shine dalilin kasancewar ɗakin a haka harma da wannan jinin". "Wannan lamari daban mamaki yake, taya za'ai kisa amma babu wani alamar yanda akayisan, a wannan karon kodai za'a canja likita ne? Dan dole dole akwai abinda yake a ɓoye. Yarinyar nan itace ta goma sha biyar da aka rasa, kisan kuma iri ɗaya babu wani bambanci sai kace abun tsafi". "Haba haba wane irin kuma tsafi? Jasim Akh. Dole dai akwai abinda bamu sani ba ɗin kam gaskiya". "Zancena nakan hanya Ukhti Ammarah. Idan ba aikin tsafi ba mi zamu kira wannan al'amarin ne? Bagashi ita waccan da yake ta gagara ko kuma wani abu daban ta tsira babu abinda ya sameta ko ciwon kai ba". "Inaga yanzu duk ba lokacin yin wannan maganar bane, ayi abinda ya dace, a wannan karon kuma ya kamata Abni yace wani abu bawai ya cigaba da yin shiru ba kamar yanda ya saba". "Maganarka nakan hanya Miran Arshaan". Miran Jasim ya faɗa cikin son sake tabbatar wa. Shiru Daneen Ammarah da Malikat Bushirat basu tanka ba, hakama jami'in yanata cigaba da zagaye ɗakin alamar nazari.. duk wannan al'amari Iffah na maƙure a maɓoyarta tana sauraren komai hannunta danne kan bakinta kar kukan da take ya fito har su farga da ita. Koda suka gama abinda suke bayan shigowar doctor da fitar da gawar kasa fitowa tai, sai dai ta zame ƙasa da sake fashewa da wani irin kuka mai ban tausayin dan mutuwar yayunta biyu ta dawo mata ne a rai sabu a yau ganin ta hanyar da suma suka rasasu a zahiri gabanta...... "Kuka bashi zai kuɓutar dake ba kema..." A razane Iffah ta buɗe idanunta dake kaca-kaca da hawaye gasu jajur. Miran Jasim da tun ɗazun ya lura da ƙafar Iffah amma ya basar har sai da suka fice yayo sau da baya ne a gabanta. Duk da so ɗaya ta taɓa ganinsa ranar liyafar cin abinci da aka kawota nan hakan baisa ta shaida fuskarba a ɗan fisge. Kai ya jinjina mata cikin ɗage kafaɗu "Yanda ya kashe na baya kema babu tantama hakance zata kasance. Karki ga ya ƙyaleki zata iya yuwuwa shirinki na musamman ne. Amma in har kin shirya kuɓuta daga tarkon sa ni mai iya taimaka miki ne". Iffah dai kallonsa take kamar gunkiya, sai hawayen da suka kasa tsaya mata ne kawai ke tabbatar da ita a mai numfashi. Bai nuna ya damu da yanayin nata ba ya cigaba da faɗin. "Ni sunana Jasim Ibn Abdull-Majeed Aliy. Ƙani ga mahaifin mijikin kenan. Nasan kina buƙatar sanin abubuwa masu yawa akansa amma kinƙi samun kowacce irin dama saboda iyayensa dake zagaye da ke. Duk yanda kike zaton abin ko tsammani ya wuce nan, Malikat Haseena da Malikat Bushirat da kike gani sun san komai game da mutuwar matansa, hasalima da taimakonsu komai ke gudana, zaki iya lura da hakan a yanzu ta yanda duk muka nuna damuwa amma su ko'a jikinsu. Abinda zai tabbatar miki da sun sani kuwa duba da abinda kika ganema idonki ne, taya za'a kashe mutum amma a kasa gane hakan, sannan kuma a sake kawo masa gobe ta mutu hakan baisa an dakata ba. Waɗan nan likitoci da jami'an da kike gani duk an siyesu ne, shiyyasa suke pretending cewar basu san komai ba ko basu gane komai ba. Koda yake su a zahiri bazasuga komai ɗin ba, dan ana kashesu ne ta hanyar tsafi domin ƙarama ƙarfin mulkinsa iko....." yaja numfashi tare da fesarwa idonsa a kanta yana nazartar yanayin tasirin da maganarsa ke samu a wajenta. Da alama akwai nasara dan haka ya cigaba da faɗin, "Mu ajiye wannan, dan bashi da amfanin cigaba da faɗa miki. Ko kin san mahaifinki da ɗan uwanki ma anyi amfani da jininsu a maimakon naki shiyyasa ke kika tsira saɓanin wannan". Zabura Iffah tai jikinta na rawa. Sai dai ta kasa faɗin abinda ke son fita a bakinta. Ya ɗaga mata hannu da faɗin, "Kinga kwantar da hankalinki, amshi wannan ki kalla. Idan kin kammala sai ki yankema zancena hukunci. Amma ki sani tabbas ta hanyar da aka halaka iyayen nan naki da ita ake bi wajen halaka waɗan nan matan nasa shiyyasa likitoci basa gane komai na barki lafiya.."

Harya ɓacema ganinta Iffah bata iya ta motsa ba, sai dai rawar jikinta da karkarwa a bayyane take. Jin kamar motsin mutane ya sata ɗaukar flash ɗin daya ajiye mata ta sake ɓoye wa. Jami'in ɗazunne ya dawo ɗakin, a wannan karon sun ɗauka hotunan komai a ɗakin da ɗan sake bibbincikawa dan tare yake da yara biyu jami'ai suma. Dole Iffah ta sake lafewa har suka fice sannan itama ta fito.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull