Daudar gora complete - Chapter 33
Daudar gora complete Chapter 33: Daudar gora complete Chapter 33. ★ A yanzu kam masarautar a harmutse take fiye da ɗazun, hakan ya sake bama Iffah damar…
3,345 words
★ A yanzu kam masarautar a harmutse take fiye da ɗazun, hakan ya sake bama Iffah damar komawa sashenta cikin matuƙar tashin hankalin abinda ya faru da zantukan wannan mutumi. Kulle kanta tai a ɗaku ido rufe ta saka flash ɗin a jikin laptop ɗinta da bawani amfani dake da shi ba. Abin tamkar wani film video ya fara da shigar Babiy riƙe da Abu Moosa cikin gidansu a waccan ranar, shimfiɗa tabarmar Ummu da bayanin Abu Moosa da bai kammala ba har mutuwarsa. Zuwan matar Abu Moosa da jami'an tsaro abinda Hanash yay mata da tafiya dasu. Daga nan ya yanke. Da sauri tai playing na gaba. A yanzu kam su Babiy ne a mawuyacin hali duk sun rame sunyi baƙi a cikin wani ɗaki. Kan Babiy a saman cinyar Hanash alamar babu lafiya tare da shi, Hanash nata faman shafa masa ruwa a fuska yana kuka. Sautin dariya ne ya fara tashi a ɗakin, kafin shigowar wani mutum da iya jikinsa kawai ake gani babu fuska. A take su Hanash suka zabura yayinda sautin dariya ke tashi da tafa hannayen mutumin. Bayan anyi dariyar mai tsawo aka tsagaita, ƙirjinta yay wata irin bugawa jin muryar Shahan-shan. "A tunaninku bayan samun tagomashi a jinin yaronku ƴan baiwa zan haƙura ne. Ina bazai yuwuba, dan a kaf yaran dana halaka jinin ƴaƴankune na farko daya bani fiye da nasarar da nake buƙata, shiyyasa na fara bibiyar ta uku daku kanku saboda bincikena ya nuna min daga jinin ubansu ne". Hhhhhhh! Hhhhh!! Kune nasarata ahalin Zayyan. Kune nasarata dole ne kuma na samu hhhhhhh!!!". Kuka Hanash keyi da roƙonsa amma babu alamar zai sauraresa. Sai ma wani irin salon siddabaru da yakeyi da hanunsa a take ɗakin ya turniƙe da hayaƙi, sai kuma wata irin guguwa mai ƙarfi ta nannaɗe hayaƙin a tsakkiyar ɗakin. Su Babiy dai tuni sun maƙure a bango. Sai kuma suka shiga ihu ganin guguwar ta zama wani irin maciji daya kusa cinye kashi ɗaya bisa ukun ɗakin, sara ya fara kaima su Babiy da suka dunƙule waje ɗaya shi da Hanash, kafin macijin ya kafa kansa a wuyar Hanash dake ƙanƙama Babiy. Tuni duhu ya gama mamaye jikin Iffah dake karkarwa, ta rufe laptop dan zuwa yanzu ma kukan ya kafe ƙaf a idanunta. Sai wani irin mahaukacin ja da sukayi kai kace wuta aka haɗa a cikinsu. Tun tana iya jin surutan masarautar har ta daina jin komai. Daga haka sai farkawa tai ta ganta a gadon asibiti Daneen Ammarah tare da ita.. Gaba ɗaya ta tsani komai daya shafi Tajwar Eshaan. Dan haka tun buɗe idon farko da tai ta ga wadda ke tare da ita bata sake yarda ta buɗe ba. Hakan yasa Daneen Ammarah bata san ta farka ba. Dama itama kuma tayi matuƙar nisa ne a cikin tunani a kallo ɗaya ma zaka fahimci bata tare da nutsuwarta. Ga wata ƴar rama ta yini ɗaya sakamakon tashin hankalin da ake ciki tattare da ita. Dan tun kai gawar Zawjata-almilk da Sayeed Khairul-Bashar makwanci ba daular ruman kawai ba gaba ɗaya ƙasar ruman a harmutse take. Yau wasu a cikin talakawa sunyi ƙarfin halin fitowa zanga-zanga a wasu jahohin suna kiranyen Shahan-shan ya sauka ko su ɗauka doka a hanunsu. Fitsari daya takura Iffah ne ya tilastata tashi har Daneen Ammarah ta farga. Da sauri takai hannu ta riƙota tana mata sannu, dauriya kawai Iffah tai na dannewa dan tunanin datai a ɗan farkawar nan Tata zuciyarta ta bata shawarar ɓoye sirrin ranta domin samun cikar burinta. Dan tayi alkawarin a wannan karon sai ta halaka Shahan-shan, ta riga ta ƙuna bata tsoron mutuwa. In har burinta ya cika danta mutu ba komai bane a gareta a yanzu ma tafi buƙatar mutuwar fiye da rayuwa tunda har ta rasa sauran ahalinta kuma miya rage mata. "Ya akai na zo nan Mamy?". Ta faɗa cikin danne komai dake ɓoye a ranta. Daneen Ammarah da farin cikin farkawar Iffah ya sata sakin murmushi yaƙe da ita kuma Iffah ta fassara da wani abu daban ta amsa mata da faɗin, "Sakamakon abinda muke tunanin ya rikeki aka sameki a sume shine aka kawoki asibiti, amma Alhamdullah tunda gaki kin farka". Maimakon ta amsa mata wannan zancen sai ta jefa mata tambaya. "Mamy da gaske ta mutu ko?". Take idanun Daneen Ammarah suka cika da hawaye. Cikin ɗaci tace, "Sun kasheta Ibnati, sun sami damar da suke buƙata akansa. Gaba ɗaya ƙasa ta harmutse da bore akansa kamar yanda dama suke son cimma buri". Iffah ta ɗan lumshe ido ta buɗe zuciyarta na karajin tsanar Daneen Ammarah ɗin da mamakin salon yaudararsu, amma a zahiri sai itama ta marairaice fuska. "Mamy ban fahimta ba?". Hawaye Daneen Ammarah ta share, "Ibnati a yau ruman baki ɗaya a harmutse take, talakawa nata zanga-zanga a wasu jahohin akan sai Abni yayi murabus a kujerar Shahan-shan inba hakaba zasu ɗauki mataki. Gashi tunda abin nan ya faru babu wanda yaga idonsa ya kulle kansa a ɗaki anyi-anyi ya buɗe yaƙi". Iffah ta rumtse idanu da karfi tana taune lips ɗinta, yayinda take faɗi a zuciyarta da kakkausar murya. (Ni zan ƙarasa musu aikin da kawo musu ƙarshen matsalarsu. Dan ba murabus kawai ya cancanci yi ba mutuwa gaba ɗaya yabar duniyar ya cancanta da shi ba kujerar Shahan-shan da ƙasar ruman kawai ba)..........✍️
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*
*DAUDAR GORA Billyn abdul*
*KI KULANI hafsat xoxo*
*A RUBUCE TAKE Huguma*
*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*
*IDON NERA Mamuh ghee*
_LITTAFI DAYA: 400_ _LITTAFI BIYU: 600_ _LITTAFI UKU: 800_ _LITTAFI HUDU :1000_ _LITTAFI BIYAR: 1200_
_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_
_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
MARYAM SANI ACCESS BANK 0022419171
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
09033181070
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09166221261
*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*
+227 96 09 67 63
Books biyar 1250CFA Books hudu 1050CFA Books uku 850CFA Books biyu 650CFA Bookk daya 450CFA
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨ (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)
𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻
*_45_*
........Daneen Ammarah dake tunanin yanayin ma Iffah tashin hankaline kawai sai ta shiga rarrashinta. Dole Iffah ta cigaba da pretending da matsawa a sallameta taji sauƙi. Daneen Ammarah na rakata sashen ta wuce dan jikin Malikat Haseena ma dai babu daɗi sam. Dama Daneen Ammarah ɗin ta zauna da Iffah ne domin saka ido kar wani ya cuta mata itama. Hakan yama Iffah daɗi, dan ya bata damar nutsuwa a kallon videon data ɗauka ɗazun. Sosai tai zooming gawar Zawjata-almilk tana kai bin jikinta ta inda yake a waje daki-daki. Wata irin zabura tai ganin abinda take ma ɗin kuwa a saitin wuyan gawar ta gefen kunenta na haggu. Wato alamar ɗigon sarin maciji har biyu. Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un take ambata wata irin zufan na keto mata, dan kuwa tabbas zancen mutumin can ya zama gaskiya. Amma duk da haka tana buƙatar sake tabbatar wa. Cikin rawar da jikinta ke mata ta shiga laluben number ɗin Sir Fawzan. Bugu ɗaya kuwa ya amsa kasancewar dama a jirace yake da kiran, dan ya nemeta amma bai samu ba. Yaci kuka har ya godema ALLAH dan zatonsa ma ita suka rasa. Cikin rawar murya ya ambaci sunanta duk da yaji muryarta. Amsawa tai da kuka, bata jira cewarsa ba tace, "Sir kaji tsoron ALLAH ka sanarmin gaskiya akan iyayena. Na rokeka karka ɓoyemun komai". Zufa ce ta shiga karyo masa tako ina, dan baiyi tunanin jin wannan tambayar bazatanba a bakinta. Shirunsa ya sake tada hankalin Iffah, ta cigaba da masa magiyar da dole ya faɗa mata gaskiyar data buƙata. "Tabbas na ɓoye miki Iffah, amma tun bayan barinki gida baifi da kwanaki ba aka rasa ɗan uwanki da Babiy sakamakon......" Ya zayyane mata labari tiryan-tiryan kamar yanda ya bincika. Babu kuma banbanci da abinda ta gani a wancan video ɗin na farko. Ya kare da faɗin, "Wlhy har yanzu akan binciken inda aka kaisu ake amma babu labarinsu. Nima kuma a yanzu haka ina yin nawa ta ƙarƙashin ƙasa amma har yanzu ban samu wani bakin zaren ba...." Kukan data fashe masa da shi ne ya katsesa daga jawabin nasa. "Ba zaku gansu ba, ba zamu ƙara ganinsu ba, sun rabani da su kamar yanda suka rabamu da ƴan uwana. Wlhy nima sai na kasheshi kamar yanda ya kashesu. Na rantse bazan barsa ba, bazan taɓa barinsa ba. Yanda ya halakasu da macijin tsafi sai na halakashi da dafin maciji na gaskiya. Shima sai ya ɗanɗa......" kuka ya sarƙeta ta kasa cigaba da magana... Cikin tashin hankali daga can Sir Fawzan ke faɗin, "Iffah ban gane ba. Dan ALLAH ki daina kuka kimun bayani, kaina ya kulle dan ALLAH kiyi shiru kinji, wlhy na miki alkawarin taimaka miki akan koma minene, koda kuwa nima zan rasa rayuwata ne.....". "Babu wannan lokacin sir, bani da shi. Kai dai kawai ina zan samu dafin maciji mai haɗarin gaske?". "Ya ALLAHU! dan ALLAH ki faɗamin mike faruwa? a yanda zan fahimceki". "Idan bazaka samamin abinda nake buƙata ba na Barka lafiya". Yana hello-hello bata sauraresa ba ta yanke wayar, koda ya sake kira bata ɗauka ba, da taga zai dameta ma sai ta jefa shi a black list. Kaikawo ta cigaba dayi a ɗakin tana kuka. Komai ya cakuɗe mata, zuciyarta ta gama ƙeƙashewa da bushewa. Ta sallama duk wani ɗan sauran rangwamenta. Abinda kawai idonta da zuciyarta ke gani gawa huɗu ta ahalinta kwance duk a dalilin mutum ɗaya tak, lokaci yayi da zatai abinda ya kawota itama dan bai cancanci cigaba da rayuwa ba mutumin nan sam, tayi alkawarin tare zasu mutu, amma sai ta kasheshi ta kuma bayyanama duniya wanene shi. Yanda taci kuka ta fita hayyacinta dole ta bama duk wani tausayi, da ƙyar ta iya zaman rubuta komai da ya rage, ta tattare ga Ajmaal, a ganinta ta gama tattare dukan abinda ya dace ta tattare masa. Hatta ƙudirinta na kawar da Shahan-shan ta hanyar dafin maciji bata ɓoye masa ba. Ta kwashe videos ɗin dake wayar zuwa wayarta ta turama Ajmaal ɗin, takumayi gajeren video da kalaman masu girgiza zuciya har biyu. Ɗaya na Ummu da su Kaka ta roƙa ya bamawa, ɗaya kuma na al'ummar ƙasar ruman ne baki ɗaya. Shima tai masa godiya da fatan alheri da nasara har ƙarshen rayuwa.......
★★..... BARRISTER ★★.....
Barrister dake jin kamar ya ƙwaɗa wayar da ƙasa ya rumtseta a hannunsa da masifar ƙarfi, a karo na farko wasu zafafan hawaye suke silalo masa. Jarumar zuciyarsa zugasa take kada ya yarda ya amince koda zai rasa rayuwarsa, yayinda wani ɓangaren kuma ke haska masa iyalansa da yafi so fiye da komai a duniya a halin yanzun. Wannan shine tashin hankalin mafi ƙololuwar girma daya taɓa cin karo da shi a rayuwarsa....
Washe gari da safe wujiga-wujiga ya wayi gari, amma hakan bai saka ko gezau ga mutanen ba. Sai ma duk wani details daya shafi case ɗin da suka dire masa. Mamaki da tsoronsu ya sake mamayesa ganin duk wani abinda ke hannunsa ne. Kuma ya adanasu ne a mabanbanta wajeje. Akwai wanda a gidansa suke, akwai wanda a office suke, akwai na mota ma. Amma abin mamaki gasu duk a gabansa sun tattaro sun kawo masa. Tabbas ya sadaƙar, dan mutanen nan hatsabibaine na innanaha. In har zasu iya hakan a kankanin lokaci bayaji idan ya bijire musu iyalansa zasu tsira kuwa.... "Barrister baka da lokacin dogon tunani, ka shirya dan a yau oga ke son ka tattaro masa duk bayanin da yake buƙata a wajen mutanen can. Ciki har da sanin su wanene ainahin masu aikin, da inda suka ɓoye Abu Hanash da ɗansa". Karan farko Barrister ya dubeshi a razane, har ƙoƙarin taune harshe yake wajen faɗin, "Kana nufin dama baku bane ke riƙe da su Abu Hanash ɗin...?" Saurayin yay ɗan waige-waige alamar baya son wani yaji, cikin raɗa-raɗa yace, "Bamu bane Barrister. Muma kuɓutar da su muke son yi har ma da kai kanka. Sai dai ban san miyasa oga bai son ka sani ba ya zaɓi baka aikin a kife". Ba ƙaramin zabura Barrister yay ba jikinsa har rawa yake ya matsa gab da saurayin. "Dan ALLAH kada ka yaudareni ka faɗa min gaskiya". Da sauri saurayin ke masa nuni da yay ƙasa da murya kar wani yaji, "Barrister wlhy kaji na rantse maka abinda na faɗa maka shine gaskiya. Na kuma sanar maka ne saboda ka bani tausayi. Amma iyalanka kansu suna zagaye da tsaro ta yanda wani bazai taɓa iya samun damar cutar da su ba, kai kanka kusan sati uku fa muna tare da kai batare daka sani ba. Oga ba azzalumi bane ba, amma ban san miyasa bai son kasan taimakonku zaiyi ba. ya kamata kaima ai ka gane hakan tun farko musamman aikin daya baka ɗin, taya wanda zai cutar da kai zai kuɓutar da kai?, taya wanda zai cutar da kai zai ɗauraka akan hanyar abinda kake nema ya baka bakin zarensa haka cikin sauƙi?". "Hakane wlhy ɗan uwa hakane. Kaina ne ya kulle a ruɗani nake gaba ɗaya. Nagode nagode yanzu kam ka bani ƙwarin gwiwa, insha ALLAHU kuma sai na bada mamaki. Dan a wannan gaɓar sai su Abu Hanash sun fita da izinin UBANGIJI, zan kuma gano koma wanene da hannu a kan ɓoyesu". "ALLAH ya baka nasara. Ni bara naje kar wani ya fahimci ina anan har yanzu". Kai kawai Barrister ya ɗaga masa yana murmushi. Wannan tattaunawa ce ta bama Barrister duk wani ƙarfi da sabuwar himma na musamman, a yanzu kama baka iya ganin komai sai murmushi tare da shi, lokacin da aka kawo masa abincin rana ya buƙaci takarda da abin rubutu. Takardu aka kawo masa bama takarda ba, hakan ko ya masa daɗi, dan ya kwashe sauran wannan yinin da dare wajen tsara duk abinda ya dace. Washe gari har ya fisu zumuɗin son fita ma, sauran da basu san miya faru ba canjawar Barrister ɗin taita basu mamaki.....
★★... KAUYEN JUMNA ★★....
Tun kammala bayanin Abu Zainab ga su Kaka jikkunansu duk yay sanyi, Ummu ma hawaye takeyi, Barrister shine hope ɗin su a yanzu bayan UBANGIJI masanin abinda ke fili da ɓoye. Gashi a dalilinsu an rasashi. Idan har aka cutar da shi ta dalilinsu bazasu yafema kawunansu ba. Kaka dai jinjina kai kawai yake amma komai ya kasa cewa, sai Iyyani ce cikin ƙarfin hali da sharar ƙwalla ta dubi Abu Zainab da damuwa ke shimfiɗe a fuskarsa. "Zakariyya kuyi haƙuri dan ALLAH, mun jefa rayuwarku a haɗari, ya ALLAH ka bayyana Abdullahi da gaggawa". Ɗan murmushin yaƙe Abu Zainab yayi, cikin danne abinda ke masa kaikawo yace, "A'a mama ai mutum baya taɓa wuce ƙaddararsa, kuma har yanzu bamu tabbatar ba ko akan wannan case ɗin bane muka rasa shin, dan Barrister da kike ganinsa nan shima hatsabibin kansa ne, gaskiyarsa da tsayuwa akan ganin tabbatar da ita yasa yanada maƙiya da yawa akan cases daban-daban hatta a cikin abokan aikinsa ma. Kinga kuwa zama ta iya yiwuwa ba'akan wannan ɗin bane....." "Dole ya zama akan wannan ne" Kaka ya faɗa cikin katse Abu Zainab. Duk kallonsu suka maida a kansa. Ya jinjina kai batare da ya kallesu ba. "Ban san gaibu ba, amma inaji a jikina akan su Muhammad Zayyanu ne, sai dai kuma tabbas koma a ina yake har yanzu yana raye insha ALLAHU. Inajin wannan ƙwarin gwiwar ne a zuciyata". Ba ƙaramin mamaki kalaman kakan suka basu ba, sai dai kowa ya gagara cewa komai sun dai zuba masa ido. Kusan mintuna biyu gidan shiru kafin kaka ya miƙe, babu jimawa ya dawo da jakka a hanunsa. Su dai duk suna kallonsa kawai. Takardar daya zaro ya miƙama Abu Zainab. "Ungo duba wannan". Da sauri Abu Zainab ya amsa ya fara karantawa. Bakinsa cike da magana ya ɗago yana duban kaka da ke kallonsa. "Baba wannan kuma fa?". Murmushi Kaka yayi da kauda kansa kamar bazaice komai ba. Sai kuma ya ɗan taɓe baki da fara basu labarin yanda duk a kai a randa zai dawo. Ya ɗora da faɗin, "Saurayin daya kawoni gidan nan zuciyata ta bani ba haka nan ya kawoni ba...." "Amma baba shine ka amince harma da nuna masa gida?". Kaka yay ƴar dariyarsu ta manya. "Zakariyya kenan, to idan baka iya kama ɓarawo ba ai shi sai ya kamaka. Ka ganni nan barni kawai inda ka ganni. Idan na nuna nasan yanada manufa a kaina tun farko kamar yanda naso nuna masa a tasha ai bazan san sirrin zuciyarsa ba. Amma dana bashi dama fa? Yanzu a tafin hannuna yake, kuma jirace nake da zuwansa dan na tabbatar zai dawo, na masa talalar da tabbas sai ya dawo da izinin UBANGIJI". Abu Zainab kam a yau Kaka ya fara bashi tsoro. Sai dai ya danne bai yarda ya nuna ba. Kaka ma ya fahimci haka amma ya kanne, sai jakkar ya tura ma Abu Zainab yana faɗin, "Wannan sune kuɗin dake tare da takardar". Nan ma dai da mamaki Abu Zainab ke kallon kuɗin, kuɗine masu yawa sabbi ƙal sai ƙamshi suke na sabunta. "Baba waɗan nan mutanen kuwa anya...." Kaka yay murmushi mai bayyana haƙora. Sai kuma ya ɗan kalli sashen da Ummu ke zaune. Tuni ta tashi batare da sun farga ba har Iyyani..........✍️
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*
*DAUDAR GORA Billyn abdul*
*KI KULANI hafsat xoxo*
*A RUBUCE TAKE Huguma*
*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*
*IDON NERA Mamuh ghee*
_LITTAFI DAYA: 400_ _LITTAFI BIYU: 600_ _LITTAFI UKU: 800_ _LITTAFI HUDU :1000_ _LITTAFI BIYAR: 1200_
_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_
_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
MARYAM SANI ACCESS BANK 0022419171
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
09033181070
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09166221261
*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*
+227 96 09 67 63
Books biyar 1250CFA Books hudu 1050CFA Books uku 850CFA Books biyu 650CFA Bookk daya 450CFA
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_* 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨ (𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)
𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻
*_46_*
..........Lokacin da kaka yayi ma Abu Zainab rakkiya sukejin halin da ƙasar ke ciki, dan shima Abu Zainab kasancewar fitowar sassafe yayi sannan komai bai fasu ba. Hankalinsu yayi matuƙar tashi dan basu san wacece a cikin matan sarkin ta rasu ba. "Zakariyya zama bai ganni ba, dole ne mu wuce tare kenan, kayi haƙuri kaɗan jirani anan ina zuwa". Kaka bai jira cewar Abu Zainab ba ya koma gida da sauri, koda su Iyyani sukaga a yanayin da ya shigo suma hankalinsu ya tashi, amma tambayar duniya yaƙi ce musu komai kan abinda ya farun, sai cemusu da yay shima zaije Daular ruman ne.". jin wannan furucin nasa yasa jikin Ummu fara rawa, a hankali ta zube ƙasa dan zuciyarta ta gama bata kodai ta rasa Iffah ko su Babiy. Dama yau kusan gabbanin asuba tayi mafarkin Iffah na kuka da kiranta tazo ta ceceta, sai kawai ma zuciyarta tafi karkata akan Uffan..